Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 44

Sponsored Links

Gudun zuciyarta ne ya qaru sosai,ta zubawa biba idanu tana kallonta tare da son gano abinda take fada,kawai don ta fadi cewa ta ganta tana kuka hakan saiya zama barazana ga rayuwarta,ta buda baki a hankali da niyyar yin magana biban ta rigata

“Kada kice zaki tambayeni komai,domin yin hakan shima qarin hadarine ga rayuwar dukkaninmu,kiyi haquri kattume,ba daga ni bane,na daga gareni bane” daga haka ta saka kanta waje da sauri,da alama wani abun ya sake taba zuciyarta ya kuma raunatata.

Kusan a kidime ta shiga daki,amma saita taras da jawahir tana rolling mayafinta a ka gaban mudubi,bata juyo ta dubeta ba tace

“Ki shirya zamu raka ya saraki gidan hajiya qarama,dama baki taba zuwa ba” a salube ta isa bakin gado ta zauna idanuwanta akan jawahir,saidai tunaninta yayi nisa da nan

“Anya ko jawa?,kice dai ina gaisheta idan kunje,wataran saiki rakani naje na gaisheta” barin abinda tayi ta juyo tana duban kaltum

“Hajiya qarama fa?,maman ya Aamiru?,qanwar daddy,bashi da ‘yar uwa a duniya sama da ita” yanayin yadda ta mata bayanin ya nuna tana son nuna mata muhimmancin hajiyan a wajensu ne,saboda haka saita miqe kawai ta jaqo hijabinta ta zura

“Dakata,wallahi kaltum kina da maida bara bana” fa fada tana zaro mata kaya cikin kayan sawarta,ta feshe da turare da kyau sannan ta miqa mata su

“Saka wadan nan,ni bakiga sai dana canza ba” kanta a cake yake,don haka bata ce mata komai ba ta saka din.

A tamface mai manyan zane da kaloli masu kyau a jiki,wanda suka haska baqar fatarta,wadda a hankali ta soma rikidewa zuwa kalar wankan tarwada,kala mai bala’in kyau da daukan hankali,batasan kalae fatar nata na canzawa ba saida taji daga bakin jawahir,don ita din ba kallon mudubi ta cikayi ba,takance me zata kalla a fuskar tata?.

Dukka idanunta mummy ta zuba mata sanda take shaida mata zasu gidan hajiya qarama,ta jinjina kanta a hankali

“Saikun dawo,kice ina gaisheta da kyau” ta fada tana miqa mata wani kwalin turare mai guda uku a ciki,mai tsadar gaske ne sosai,zuwanta dubai ta siyoshi,ta karba tana juyawa ta fice da sauri,da alama tafiyar tana mata dadi.

“Kin tsani zaman front seat,yau kam a nan zaki zauna” jawahir ta fada tana mata dariya bayan ta bude mata gidan gaban,kwanyarta cike take da kalamai da tunanin maganganun biba,don haka komai akace kawai yi take,saita shige a hankali ba tare data cewa jawahir komai ba,ta kwashe qafafunta zuwa cikin motar tana shirin jan qofar,qamshin lalausan turarensa tare da sanyin ac yana shige mata hanci.

A hankali ta waiwaya ta dubeshi sanda yake qoqarin aje wayar hannunsa da sauran tarkacensa a tsakiyarsu,wani irin takura da nauyinsa takeji,kusancin dake tsakaninsu takejin kamar yayi yawa,tana jinsu very close da juna

“Ina yini?” Ta gaidashi tana dan rusunar da kanta saboda nuna girmamawa,sabida yau gaba daya basu hadu ba.

Kansa ya dago da niyyar amsa gaisuwar,sai idanunsa suka fada fada cikin nata,ya janye qwayar idon nasa a hakali,fuskaraa kadaram kadaham kamar yadda suka saba ya amsa mata tare da dora fadin

“Kina lpy?” Sanda yake yunqurin daura seat belt dinsa

“Alhamdulillah” ta amsa masa itama kamar kullum,tana jin lallausan muryarsa mai dauke da wani heaviness irin na mazantaka can cikin kunnenta sanda ya furta bismillah ya kuma tayar da motar.

Lafewa tayi sosai cikin kujera sanda suke tafiyar,rabin hankalinta naga tunani,yayin da lokaci lokaci kuma hankalinta ke kaiwa ga hirarsu,musamman idan jawahir din ta sanyota a ciki.

Sun danyi nisa ya faka a store din daya saba yiwa hajiyan siyayya,ya dubi jawahir

“Muje ki rakani” ta amsa masa tana bude murfin motar,tare da cewa kaltum itama ta fito

“Zan zauna a nan kuje ku dawo” ta fada da wani irin sanyi da take jinsa har qashinta

“Ya kayi mata magana,ai tare zamu shiga ko?” Kai ya gyada yana duban kaltume din kadan kafin kuma ya soma yin gaba,dole ta zuro qafafunta ta fito tunda ta sakashi cikin maganar.

Waje ta samu ta jira jawahir ta gama daukan komai,don dama samir din daga can wajen biyan kudi yayi tsaye yana jiranta yana duba wasu roll on da deodorant.

Kwandon hannunta shaqe da kaya tace

“Muje kaltum” bayanta tabi,ta kuma yi tsaye dai a bayanta wajen biyan kudin,ba kowa saman seat din masu karbar kudin,sai sun dan jira kadan,saboda zagayawa da yayi bayan ya nema afuwarsu.

“Me zakiyi da wannan haka?” Tambayar da samir yayiwa jawahir,murya qasa qasa saidai ta yadda zaiji tace

“Kaltum na siyawa,waifa bata fara sawa ba yaya har yanzu” a hankali ya juya inda kaltume ke tsaye yana dubanta,ya tuna watannin baya,ganin da yai mata tsaye cikin dandali,tabbas bata isa fara sakawar ba,saiya sauke idanuwansa tun daga qasan qafafunta har zuwa muhallin da aka siyawa abar,zuwa yanzu bambancin kadanne da yadda ya gani a baya

“Kuma wallahi yaya ashe qarya takemin,nina gani kunyar sawa kawai take” maganar data dawo da kaltum hayyacinta kenan,takai dubanta kan kwandon da jawahir ta zuba siyayyar a ciki,me zata gani?.

Brassier ce kusan dozen guda,idanuwanta a warwaje taso maidasu ga jawahir sai suka hada ido da samir,kamar zata nutse a qasa haka taji sanda ta fuskanci kallonta yake saita jingina da kantar kusa da ita da sauri sanda shi kuma ya dauke idanunsa,yayi ma kamar babu abinda ya faru ya maida hankalinsa ga me karbar kudi sanda yake dawowa wajen.

Harara ta jefi jawahir dashi sanda take mata dariya qasa qasa,ita babu abinda ya shalleta da alama,mamakin jawahir din take,ta yadda batajin nauyi da kunyarsa take gaya masa wannan maganar,duk da tasan halinta dama faranse ce ita,amma ta sanyata jin wata iriyar kunya,wadda ta hanata sakewa har suka isa gidan hajiya qarama.

A falo suka taddata tana zaune tana kallon tafsirin sheik Dr Bashir Usman,gefanta lemo ne da cake a ajjiye,da alama ta fara ci ta ajene.

Da hanzari jawahir ta isa gareta ta zube a cinyoyinta,itama tana dariya ta dora tafin hannunta a gadon bayan jawahir din tana murmushi da murnar ganinta.

A nutse kaltum dake dauke da ledar siyayyar hajiyan tayi sallama a falon,sallamar data ja hankalin hajiyan,ta dago tana amsawa tare da zubawa kaltum idanu harta qaraso,ta zube ledojin a hankali sannan ta zauna ta soma gaida hajiyan.

A nutse cikin yanayi na karantar dan adam ta amsa,sannan ta sake maida kanta ga jawahir kafin samir ya shigo.

Yadda shima ta amsa sallamarsa zuwa gaisuwarsa zai tabbatar maka da cewa ba qaramar qauna bace tsakaninsu shida ita da jawahir din

“Ina waccar mai baqin halin?” Hajiyan ta fada sanda take miqewa zata kawo musu wani abun su taba,saidai da qyar ta miqe din saboda ciwon dake qafarta,kusan kuma shine silar zuwansu gidan su dubata.

“Tana gida hajiya,kema kinsan bazata zo ba”

“Nima bana gayyarta,randa duk taga dama tazo,bari na kawo muku abun sha” sai tayi hanyar kitchen,kaltum ta bita da kallo,wani abu na taba ranta,tana tuna mata da ummanta da nata ciwon dake qafarta,saita lumshe idanunta,tana sauke qaramae ajiyar zuciya.

Batafi minti daya ba ta dawo

“Yau ni nake ganin rayuwa a gidan nan,masu aiki biyu amma babu ko daya a ciki?,dambu fa nace ayi an hada komai amma ya gagara gasucan zube a kitchen?,ke jawahir duba store ki debo muku ruwa da lemo,na fridge dinma ya qare an rasa me zubawa,nikam qafa ta matsamin,bazan iya ba,inajin masu aikin da naqi dai su za’a qaromin din” ta fada tana zama,sai jawahir ta miqe tana cewa kaltum tazo suje,suka miqe dai dai sanda samir ke gyara zamansa yana tambayar hajiyan ina duka ‘yan aikin,ya za’ayi a barta haka ita kadai a irin wannan yanayin.

“Baraka dama ta tafi gida tun sheran jiya,ita kuma hansai zata dora girkin kenan akayi kiranta surukarta nakan gwiwa”

Kitchen ne me kyau da tsari sosai,kai baka ce kitchen din babbar mace bane kamar hajiya qaraman.

Tsaye tayi daga kitchen din tana dan kallonsa kallo irin na baqunta,jawahir kuma ta shiga ciki tana debo lemukan

“Zo mu wuce,wadan nan ai sun isa” tace da kaltume

“Jeki kai musu mu dawo nan mu zauna,wala’alla magana zasuyi da ita mu basu waje”

“A nan kuma?,ai akwai wani parlour din,saimu koma ciki” kai ta kada

“Kije dai ki dawo” tunda ta fadi haka tasan da dalili,saboda haka bata sake musa mata ba ta fice,babu jimawa ta dawo

“Tana da couse couse?” Kaltum ta tambayi jawahir

“Eh ba za’a rasa ba” saita gyada kai

“Dauko ko guda dayane na gwada wani ganganci mu gani,naga yana kama da barjajjiyar shinkafa da kuma tsakin masara,ko zaiyi mata dambun”

“Yes,correct…..dama anyin dambun couse couse din ai” jawahir ta fada tana murmushi,sannan ta ake shiga store din hajiyan ta soma laluboshu,babu jimawa ta fito dauke dashi guda biyun ta miqawa kaltum,ta karba ra durfafi inda taga an ajjiye duka kayan hadin ta janyo roba ta fara aikin.

A hankali ta dinga aiki da hankalinta da kuma hasashe na yadda take musu dambu a gida,tanayi tana fagabar kada yaqiyi tunda wannan din ba tsakin masara bane,bayan ta hada komai sukayi tsaye a kitchen din jawahir na mata hira,saidai ita hankalinta duka nakan girkin,da kuma kasadar da tayi daga zuwanta baqon waje,yanzu idan ya lalace baiyi bafa me zatace?.

A hankali ya soma fidda qamshi sosai,qamshin daya cika kitchen din gaba daya,mintunan data bashi kuwa na cika ta duba,saita kira jawahir tazo ta dandana.

Lomar farko ta fiddo idanunta waje

“Wow…wow, you make it kaltum…..”sai data sake kai hannu ta debo takai bakinta sannan ta sake cewa

“Kinji dan ubansun dadin da yayi kaltum,ya akayi kika iya har haka?” Murmushi kawai tayi mata tana zaro plate guda biyu,ta cikasu dashi,jawahir ta riqe hannunta

“Haba malama,ya zaki kwashe?,mu kuma fa?”

“Hajiya iya da saura ai,ba duka na debe ba” kaltum ta fada tana mata dariya

“Kikai musu saiki dawo kici” ta fada tana tura mata farantan.

“Wai nikam qamshin girki fa nakeji,ko hancina ne saboda yunwar da nakeji?” Hajiya qarama ra fada bayan ta dakata daga maganar da sukeyi

“Qamshin abinci ne,amma ina zaton iskar kitchen ke kadowa ko,bari na fita nan kusa daku akwai eatery na samo miki wani abun da zakici,kafin a san wadda za’a kawo miki ta zauna miki kafin masu aikin naki su dawo” yana fadin hakanne dai dai sanda jawahir ta fito da plates din a hannunta fuskarta fal fara’a.

Da kallo suka bita har ta iso gabansu,ta ajjiyewa kowa plate din sannan ta bude masa ta sanya masa spoon

“Kuci kuji don Allah” ta fada tana dubansu,duban plate din sukayi hajiya tace

“Meye wannan ne kamar dambu”

“Kici don Allah hajiya…. please yaya kada kace ka qoshi” ta fada tana marairaice masa,basu sake cewa komai ba kowa ya dauki nasa cokalin.

“La’ilaha illallahu….wai dambu kukayi haka a dan wannan lokacin me shegen dadi?” Dariya ta qwacewa jawahir,kafin ta dakata

“Hajiya dambun couse couse ne fa?” Idanu hajiyan ta fitar

“Couse couse dai da nake kallonshi a abun banza shine haka?” Dariya ta basu harda samir daya dan murmusa,dadin abincin shima yana ratsashi,duk da dama shi cimarsa ce couse couse,musamman da vegetable soup liver or kidney soups

“Wallahi hajiya aikin kaltum ne,ni kaina abun ya bani mamaki”

“Ikon Allah,wannan yarinyar dai da kuka shigo tare?” Hajiyan ta fada tana fara kai lomomi bakinta,gardin gyada dana zogale gami da wadatacciyar albasa da kayan dandano na hadewa a bakinta

“Ita”

“Ina kuka samota ne?”

“Na daukota ne daga garinsu” samir ya bawa hajiyan amsa sanda jawahir ke niyyar bude baki tace ‘yar aiki ce,kai hajiyan ta kada tana ci gaba da kaiwa cikinta abincin.

Ganin hajiyan ta nutsu da abincin,saita juya ta koma kitchen wajen kaltum don bata labarin yadda ta kaya tana dariyar yadda taga hajiyan na cafkar dambun babu qaqqautawa.

Tana mamakin ta yadda aka sarrafa couse couse haka aka baddan masa da kama.

Tana dab da cinyewa suka fito daga kitchen din,hajiyan ta daga kai tana kallon

“Sannu ‘yar nan,sannu da aiki kinji?” Murmushi kawai ta saka,ta qarasa tana daukowa hajiyan ruwan da take yunqurin daukowa hannunta baikai ba,ta bude mata ta miqa mata

“Aini mamaki ne ya kamani,kin samu ladana ba kadan ba” murmushi ta sakeyi tana samun gefe kusa da jawahir ta zauna

“Allah yayi albarka”

“Amin” ta amsa da muryarta qasa qasa,yayin data maida hankalinta ga jawahir dake nuna mata wata drama da ake nunawa.

“Yauwa….yanzu sai nafi fuskantarka,me kake cewa?” Tafin hannunsa yasa ya shafi sumar kansa

“Ba wani magana bane dama,yarinyar da xan aura ne muka daidaita kanmu,so inason shaidawa daddy,nayi magana da mummy sai tace na gaya miki,saiki gaya masa” bakinta ta tabe,kana ta dubi inda su jawahir take,sam hankalinsu baya wajen

“Waini za’a yiwa bariki,da ta zartar kawai ai yadda ta saba….wacece ita ya sunanta?”

“Jauhar ce”ya amsata a nutse bayan yin shuru na ‘ya sakanni,tsareshi tayi sosai da idanu

“Jauhar dai,yar wajen murjana?” Ta tambayeshi tana tattara hankalinta a kansa

Kansa ya jinjina mata yana kallonta,saita hade ranta tsaf

“Eh lallai….jidda taci alwashin daga qarshen rauwarka ma kenan itace zata zaba maka mata,to ba zata sabu ba,tunda shi yayan ya zama sai yadda aka juyashi,wannan wacce irin masifa ce ke bibiyar rayuwar raihana har yanzu bata huta ba?”

Idanunsa ya lumshe yana jin sunan har tsakiyar zuciyarsa,yana kuma jin wani abu me daci yana motsa masa,cikin muryarsan nan me cike da nutsuwa yace

“A’ah hajiya…,.ki fahimta mana,babu ruwan mummy a wannan maganar,amma idan baki gamsu ba kina iya tuntubar daddy da kanki” shuru hajiya qaramar tayi tana kuma karantar fuskar samir dake kallonta shima,tsahon wasu sakanni kafin ta gyada kai

“Shikenan tunda har kace haka….idan akwai alkhairi cikin lamarin Allah ya tabbatar,idan kuma babu alkhairi….ina roqon Allah ya watsa abun,ammafa ka sani,wannan ba yana nufin na gamsu duka bane na miqa wuya,daga yanzu zuwa ko yaushe ma,idan na gani ko.naji abinda baiyimin ba,to tabbas babu abinda zai hana a fasa ko a dakatar da komai” kansa kawai ya gyadawa hajiyan,har yanzu baisan me yasa ta kasa so ko jituwa da mummy jidda ba.

Sun dan jima a gidan,don har bayan sallar isha’i,sai da suka jira hajiyan ta kira wadda zata tayata zama,saidai har suka zo tafiya bata qaraso ba.

A sace kaltum take kallon hajiyan,itadai duk yadda jawahir ke cewa mafadaciya ce bata gani ba,hasalima saboda ciwon qafarta sai take jin kamar ummanta,duk wadda ta gani da ciwon qafa saita dinga ganin kamar ummanta

“Don Allah kice ya barni na zauna tunda me zaman bata zo ba” ta radawa jawahir,ta dubi samir ta gaya masa,saiya waiwayo yana dubanta

“Makaranta fa?” Ya tambayeta kanshi tsaye,sai sannan ta tuna

“Kwa dawo gobe” hajiya qarama na murmushi,cikin jin dadin yadda take ta nuna kulawarta a kanta tunda tazo tace

“Allah sarki yarinyar kirki,kada ki damu kinji,mubina na hanya,ba jimawa zaki ganta” da wannan sukayi sallama,bayan ta baiwa jawahir wani abu a leda tace su raba ita ba amfani dashi zatayi ba.

Saida suka shiga motar,samir yana qoqarin tada motar jawahir ta bude ledar

“unbelievable….” Saita saki dariya

“Wlh hajiya nada abun dariya,ta rasa yau kuma me zata bamu sai pad?,to ai wanna ni ta yiwa wannan kyautar,don kaltum ma yaa har yanzu bata fara period ba bare mu raba tare” tayi maganar tana ajjiye ledar gefanta

Kamar motar ta tsage ta fita ta qasanta haka kaltum taji,wai yau me ya samu bakin jawahir ne take ta bare magana haka?

“What?” Samir dake qoqarin tada motar ya fada bayan ya tsaida abinda yake qoqarin yi din

“Me kace yaya?” Jawahir ta tambaya,bai amsa ba,saiya waiwaya gefansa a nutse,ya dora idanunsa kan kaltum

“Shekararki nawa?” Ya tambayeta kai tsaye,tambayar data bata kunya

“Sha biyar” ta amsa masa a hankali,saiya janye idanun nasa daga kanta

“Akwai matsala” ya fada yana tada motar tashi,sannan ya fiddata daga jerin motocin gidan inda ya ajjiyeta,yana qissima lallai akwai wani matsalan,amma bata tadda za’ayi tana da 15yrs ta kasa period.

A komawan ma shuru tayi,saboda kunyar da jawahir ta gama bata,don damuwar maganar biba ma ta fita a ranta ba kamar dazu ba,bayan ta yankewa ranta yin shurun kamar yadda biban tace da ita.

Washegari ita da jawahir suka sake shiryawa zuwa duba hajiyan,bayan sunyi waya da saraki yace shima zaya biyo daga gurin aiki saisu wuce tare.

A falo suka tadda hajiyan,taji dadin ganinsu sosai,ta amsa gaisuwarsu cikin kulawa da tambayar yadda sukaje gida.

Suna tsaka da gaisawa yar matashiyar budurwar da kadanne bata qarasa sa’ar jawahir ba ta fito daga kitchen,hannunta jiqe da ruwa da alama aiki takeyi.

Qarasowa tayi tana dubansu,da alama sunsan juna ita da jawahir,saidai ba wani sanin can can ba,ta zauna kan daya daga cikin kujerun suna gaisawa da jawahir sannan ta dubi hajiyan

“Me za’a dafa?”

“Idan na gaya miki ma me nakeso quiya irin ta ‘ya’yan yau ba lallai ta barki ki iya dafamin ba” duban hajiyan tayi,tadan maida bayanta ga kujera ta jingina bayan tayi luu da idanunta

“Kamar kuwa kinsan na gaji,ga baqi mun sake qaruwa,kawai ayi spaghetti jallope” idanu ta fidda

“Wa?,Allah ya sawwaqe,bama ta shinkafa ba saita taliya,nikam ba dani ba,ni ason raina ma na sami lafiyayyen tuwon dawa da miyar kuka” daga jawahir har mubina dariya suka fashe da ita

“Allah ya sawwaqe,haba hajiya me kika rasa da zakici wani dawa?” Cewar jawahir,mubina ta dora da

“Tayani gani dai,wai makaho yaso gulma” baki hajiyan ta sake,kamar yadda kaltum ke binsu da kallo kawai,tana dan qaramin murmushin da bai bayyana a saman fuskarta ba,tausayinsu take da suka jahilci amfanin dawa da har suke ganin baikenta,gayu da gata suka sanya su hasarar alfanu me yawa,tabbas da sunsan amfani da Allah ya zuba a cikinta wawasonta za’a dinga yi,amma abunda ta fuskanta a rayuwar maraya shine,kawai duk gidan da akaga suna cin tuwon masara ko na dawa,to talauci ne yake damunsu,idan kuma masu wadata ne,tofa la shakka za’a lasafta mai gidan cikin sahun mutane masu rowa qanqamo da dan hannu.

Bayanin amfaninta hajiya qarama ta fara musu,amma saita fuskanci basa ganewa,jawahir na dariya tace

“Hajiya,abincin dokuna ce fa?,ita naga ana yamutsawa da wani abu ana bawa dokunan ya samir”

“Me yasa dokunan suka fimu qarfi da lafiya?” Kaltum ta jefa musu tambayar ba tare da tasan ta fito a bakinta ba,dukka sai hankulansu sukayo kanta,saboda funda aka fara maganar batace komai ba kallo ne nata,sai taji wani nauyi,amma kuma haka ta daure taci gaba da magana

“Dabbobinmu wani lokacin sun fimu lafiya qoshi da kuma kitse ajikinsu,saboda muna daukan dusar kayan amfaninmu dama tsabar muna basu,da sunan shine abincin daya dace dasu,mu kuma muqi ci saboda muna neman dadi,bamu damu da kyau ko ingancin abinda zamu ci ba,dadi kawai muke yiwa” sai sukayi shuru suna nazari,zuwa can jawahir tace

“Kuma fa hakaneeee kulsum na yadda dake wallahi” yayin da hajiya qarama ta zuba mata ido,tana mamakin fasaharta da kaifin hankalinta a shekraun da take dasu,duk kuwa da cewa.ba wami abun mamaki bane ga duk mutumin daya rayu cikin karkara,wata baiwar basira hikima da fasaha Allah ke musu,wala’alla kyan nature irin nasu da bata baci da hayaqin kamfanoni da ababen hawa bane,da kuma cimar ganyayyaki da zallar abinci masu gina jiki damu muke musu kallon banza da suke ta’ammali dasu

“To kundai ji” hajiyan ta dora da fada musu,ita dai mubina sam bata gama yarda ba,daga qarshe dai kaltum tace suje ta tayata ta dora girkin,sai gashi sun buge da barwa kaltum din girkin,wanda ita kuma ta sauya akalar abinda sukayi niyyar dafawa ta maida tuwan dawar da hajiya qarama keso,dawarta me kyau kuwa,jar dawa wadda tafi kowacce amfani,niqanta kuma yayi laushi yadda ya kamata.

Sanda ta jerewa hajiyan komai bayan sun gama sallar magariba,hajiyan don dadi kamar tayi me,albarka kawai take sawa kaltum din

“Hajiya mu ba zaki gode mana ba” jawahir daketa kai lomomi bakinta ta fada,don ita ba zata iya tuna when last data ci tuwon dawa ba,don haka ta manta dadinsa ma kwata kwata,saidai babban abun mamakin shine,ashe haka kaltum din ta iya girki?,eh tabbas don girki ummansu ta horesu dashi,tun tana da shekara goma take dora sanwa,shekararta biyar tana girki,girki kuma kowanne irin irin dai wanda suke tu’ammali dashi zata yishi fes aci ayita santi,abu daya ne zuw biyu dama bata iya shi ba,girke girken da tazo ta tarar suna yi na zamani,sai kuma kayan dandano dana qamshi kala kala dasu basa amfani dashi,amma zama da take yawan yi a kitchen yasa ta gane amfanin da yawa daga cikinsu,ta kuma iya sarrafasu,amma yanzun data tashi yiwa hajiya qarama girkin ma,dukka ajjiyesu tayi,tayi amfani ne kawai da komai a gargajiyace,nan ta barsu suna santi,tayi dakin da mubina ta sauka don daura alwalar magariba.

*SAƘONE MAI NAUYI,BUDE IDANUNKI DA KYAU KI KARANTA!!*

*_RAMUWAR SALLAH GAME JININ AL’ADA!!_*

*_Shin kinsan cewa,duk sanda jini ya dauke miki,minti biyar kafin rana ta fadi saikin RAMA SALLAR AZAHAR DA LA’ASAR?_*

*_Idan ya dauke miki minti biyar kafin alfijir ya keto,saikin rama sallar magariba da isha’i ta jiya?_*

*_idan ya rage saura minti uku alfijir ya keto ko biyu ko daya,ba zaki RAMA MAGRIBA BA AMMA ZAKI RAMA ISHA’I tana nan a kanki_*

*_idan ya rage saura minti daya rana ta hudo to SALLAR ASUBA TANA KANKI SAI KIN RAMA TA_*

_wadan nan wajibi ne ki riqe ki kuma ramasu,idan ba haka ba zaki tashi a littafin ayyukanki baabu su_

*_YAYA KIKE QARA KWANAKIN AL’ADA IDAN KIKA LURA DA QARIN KWANAKIN DA JINI YAKE MIKI KAFIN DAUKEWARSA???_*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

 

45

*_KIJI TSORON ALLAH,ki biya ki karanta cikin aminci,ba tare da kin taba haqqin kowa ba_*

08184017082
Ko
09134848107
___________________________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button