Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 45

Sponsored Links

Ana gama sallar magaribar daga masallacin layin gidan hajiya qaramar gidan yayo,a qasa yake tattakowa cikin nutsuwarsa har ya kawo gidan.

Sanda yayi sallama falon dukkaninsu ke qoqarin amsa mishi sallamar,amma banda mubina da tayi suman xaune,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare ne waje daya ya dauna zagayawa yadda ya kamata.

Babu wanda ya fahimta halin da take ciki,shima duba daya yayi mata ya ganeta,amma bataga alamar haka ba,saiya samu waje ya zauna yana duba hajiya qarama da jiki,yayin da jawahir ke masa sannu da xuwa,gami da yunqurin miqewa da gaggawa tayi ciki itama don tayi sauri tayi sallar kafin yace su fito su tafi,don tasan bayason jira.

Da wata shaqaqqiyar murya mubinan ta gaidashi,tana jin wani iri babu dadi da ganinsa qalau da tayi,don ta gwada kiran wayarsa yafi a qirga amma baya dagawa,ta rasa wacce irin rashin sa’a ce irin wannan,ta mallaki number dinsa cike da fata da burin samun soyayarsa,sai kuma ya datse hanyar da take fata da burin tabbatuwar hakan.

Ganin babu kowa a falon sai ita ya sanya dole itama ta miqe tabi bayansu,saidai dukka wanda ya kalleta yasan jikinta a matuqar sanyaye yake

“Kicewa kalsum tazo ta bawa yayansu abinci….yauma dai ita ta ciyar damu,wadan nan iyayen qyuyar ba abinda suka iya sai abincin bature mara inganci bare qara lafiya” hajiya qarama tace da mubina tana kuma yiwa samir bayani,gami da yunqurin miqewa itama don taje tayi salla.

Sanda take gayawa kaltum din taje takai abincin sai jawahir ta bi mubinan da kallo ganin yadda lokaci daya tayi laushi sosai,yanayinta ya canza.

Miqewa kaltum tayi daga saman abun sallar data kafu a kai tana addu’o’i,kwanakin nan kawai daurewa takeyi tana mazewa,amma ranta damuwa ce fal,tayi kewar gida kamar hauka amma babu wanda ta nunawa,bata kuma da yadda zatayi,kullum da tunaninsu take kwana take kuma tashi,uwa uba kuma ita din asalan da wuya kaga bata kwana gida kusa da ummansu ba,bako ina take zuwa ta tarda ta kwana ba,sai gashi yau wani qaddara ta kawo silar rugujewar zamansi,ta nesantata da gida zuwa wani waje me nisan da tunaninta bai taba dauko mata wannan ba.

Daga nan dakin kitchen din kawai ta wuce ta hado kayan abincin dai da yadda ya dace,don tasan qila samir dinne ya iso.

Tun kafin ta qarasa ta hangeshi yana amsa waya,sai tayi qas da kanta tana takawa a hankali zuwa inda yake zaunen.

“Barka da yamma” ta fada cikin wani yanayi fa batasan yadda akayi tayi magana a hakan ba,wala’alla kodon idanunsa daya zuba mata ne da sukayi mata nauyi?.

Zare idanun nasa yayi daga kanta,don baima san yana kallon nata ba,saiya amsa mata daka yana ci gaba da amsa wayarsa,shida jauhar ne,a yanzun tana jinta kamar tafi kowacce mace sa’a a duniya,ta fara sarewa daga samun samir din kwata kwata,duk kuwa da yadda yayi mata,saiga albishir kwatsam na dukkan dama ta samun mallakar tasa,wannan dalili yasa ta buse wutar mallakar zuciyarsa babu qaqqautawa.

Yadda taga jawahir na masa,saita duqa tayi serving dinsa,bayan ta gama ta yunqura zata miqe sai ya dakatar da ita da hannu yana ci gaba da amsa wayarsa,hakanan ta koma gefe ta zauna tana,ta takure waje daya tana wasa da yatsun hannunta,jinta take wani iri,saboda babu kowa a falon daga ita saishi,sai take ganin kamar ya cika falon shi kadai.

Batasan me yasa a duk sanda zasu kebe daga ita saishi ba saita dinga jin wani nauyinsa,tana auna hakan a ma’aunin girma da nauyin alkhairin da yake shigowa dashi a rayuwarta.

A hankali kunnuwanta ke dauko mata wasu daga cikin wayar da yakeyi,ta fuskanci da mace ne,haka kawai sai takejin wani abu mara dadi a qirjinta,amma tafi ta’allaqa hakan da ajjiyeta da yayi tana suraran sirrinsa,saita qara tsumewa a waje daya,tana ta faman murza yatsunta kamar wadda aka baiwa wannan aikin.

Shi da kansa ya gimtse hirar ta hanyar daukar excuse din zaici abinci,saboda bayajin wani dandano nata ko armashi,ya sauke wayar idanuwansa na sauka kan zara zaran yatsunta wanda ke nuna dukkan alamu na laushin da fatarta keda ita.

Sai da yayi bismilla alamun fara cin abincin sannan ta farga ya gama,a hankali ta gyara zamanta ba tare data iya kallonshi ba.

Hankali kwance yake cin abincinsa,tare da mamakin yadda girkin yayi dadi,dama can ta iya girki ne ko zuwanta ta koya,tunda tazo basu taba wata doguwar hira tsakaninsa da ita ba,saiya jefa mata tambayar

“Ya akayi kika iya girki?”
Ka ta jinjina masa sannan ta bude baki da ‘yar qamar muryarta ta amsa masa da eh

“Waya koya miki?”

“Ummana ce” ta amsa masa

“Madalla da umma,tayi qoqari sosai” maganarshi ta sanyata daga kai ta dubeshi,sannan murmushi ya qwace saman fuskarta.

Karo na farko da yaga wadataccen murmushinta irin haka,fuskarta ta qawatu matuqa,ta sadda kai murmushin taci gaba da wanzuwa kan fuskarta

“Na gode” ta fada tana jin dadin yadda ya yabi ummanta,sama sama yake kallonta,yana kuma karantar farincikin dake zuciyarsa dangane da yabon mahaifiyarta da akayi,sa yaji wani abu yana taba ransa sosai akan hakan,harma yaji ya qoshi,duk da dadin da abincin yayi masa,don bazai iya tuna yaushe yaci irin wannan tuwon ba,gidan hajiya qaraman yake samu dama,to ita kanta kwana biyu daya zamana yau lafiya gobe babu sai ta sakarwa masu aikin girkin duka,su kuma bason tuwo suke ba,kamar yadda ya fuskanci mummy bata sonsa,hakan ya sanya ba’ayinsa sam a gidan.

“Tunda kike baki taba period ba dama?” Ya tambayeta kansa tsaye,tadan daga ido ta kalleshi,sai tayi saurin sakewa,nauyi da kunya suka cikata,saita cure waje daya kamar mejin sanyi,ta kasa amsa masa tambayar,murmushin gefan baki ya saki,sabida ganin yadda tayi daga yi mata tambayar,saiya tuna sanda take bala’i lokacin da zata amsa haqqin dan uwanta,duk yadda suke hasashen bata da kunya ashe ba haka bane,abu daya ne zuwa biyu kawai,ita din bata bari a danne haqqinta indai tana da ikon karba,sai kuma zamantowar mutum me qaunar mahaifiyarta da yan uwanta.

“Ki dauko takalminki muje,yanzu zamu dawo,ki gayawa jawahir ta zauna” bata iya tambayarsa ba,sai kawai ta miqe kamar zata harde ta nufi daki,binta yayi da kallo kafin ya janye idanuwansa,yana tuna ganin da yayi mata a dandali ne,a sannan halayyarta ce ta gaskiya kenan?,kansa ya shafa yana ture tunanin gefe guda tare da duban hajiya qarama dake dawowa falon.

“bazan boye miki ba,sonsa nake kuma yayimin…….zaki iya taimakamin?” Wadannan ne kalaman da suka shiga kunne kaltum sanda take shiga dakin,duka sai suka juyo suka kalleta,kanta ta dauke tana nufar inda ta ajjiye takalmanta,ba tare data sak dubansu ba tace

“Yaya yace ki jirashi,zamuje mu dawo”ta fadi mata tana nufar qofa

“Ok,saikun dawo” ta amsa mata tare da maida hankalinta ga mubina,wadda gaba daya ta koma kalar tausayi,bisa kuma dukkan alamu zuciyarta a karye take sosai.

Ta cikin hasken gidan yake hangota yana zaune daga cikin motarsa sanda take fitowa,ya fuskanci bata da wani zafi ko kadan,komai nata tana yinsa ne cikin sanyi,saiya buda gida gaba kafin ta qaraso,ya kuma janye idanunsa ya maida ga wayarsa da tayi qara alamun shigowar saqo.

Sai data zauna sosai sannan ta rufe qofar,ya ajjiye wayar gefansa ya tayar da motar sannu a hankali suka fice daga gidan.

Tafiyar mintuna ashirin suka iso wani guri da tun daga waje yafi mata kama da asibiti,da suka shiga ciki ta daga kanta tana duba rubutun dake maqale a qololuwar ginin wajen,a nan ta tabbatarwa kanta a sibiti ne,tana jin sanda yayi waya da alama da wanda sukazo wajensa yake,kana ya bata umarni suka fito,yana gaba tana biye dashi har cikin asibitin.

Kai tsaye reception suka tsaya,wanda ke dauke da files na marasa lpy a tsare cikin wata kanta,sai tarin computers da suke amfani dasu wajen karbar kudi da bada receipt.

Da mutane a wajen don haka suka dan tsaya daga baya,hankalin samir na ga wayarshi yana qarasa duba saqon da ya samu dazun,daya hannun nasa kuma riqe da key na mota yana dan kadashi.

Tunda suka shigo wajen hankalinta ya dauko a kansa,ta juyo ta kalleshi yafi sau shurin masaki,saidai shi baisan abinda ke faruwa bama.

Kaltum kuwa duk abinda ke faruwa tana kallo,har zuwa sanda tadan matsa kusa dashi,da wata maqalalliyar muryarta dake nuna gayunta tace

“Hi” sai a sannan ya daga kanshi ya dubeta

“Hi” ya mayar mata yana qoqarin maida kansa ga wayarsa,ta yunqura zata sake magana muryar receptionist din ta katsesu

“Sir…..kaine muhammad samir?” Kai ya gyada mata

“Sorry sir…..Dr labaran yace ka shiga office dinsa ka zauna,zaka ha sama ne,daga hannun damanka daki na qarshe a nan zaka samu office dinsa”

“Thanks” yafada yana yin gaba,kaltum tabi bayansa,saidai koda bayan sun gota ta din sai data waiwaya ta kalleta,itama su take kallo,ta sakarwa kaltum murmushi tare da daga mata hannu,saita dayke kanta tana tabe baki,itakam koda a karkararsu tana ganin baiken irin wannan zub da kan,ashe har a nan ma da ake ganin matansu sun waye suma suna irin wannan dabi’ar?.

Tana biye dashi tana mamakin me ya kawosu asibiti?,waye baida lafiya?,kuma.taji ana zancan dr,koshi za’a duba?,duka bata da amsa,saita haqura taci gaba da binsa tana zubawa sarautar Allah ido.

Har suka shiga suka zauna yana duba wayar hannunsa,shuru yaci gaba da ratsa office din,lokaci lokaci tana satar kallonsa,abinda ke fado mata a rai kawai shine….maganar mubina data tabbatar tana da alaqa da shi,sai kuma yarinyar yanzu,mamaki ke kai kawo a ranta,me yasa kowa sonshi yakeyi?,idan bata manta ba mata kusan uku tana gidan sunzo ne kawai saboda shi,wasu su wuni su tafi,tana nazartarsa tsaf,tun asali mutum ne mai girmama kowa musamman mace,bashi da wulaqanci saidai ya iya jan aji da kuma mutunta kai,hakanan sauqinsa baisa ya zama me daukar raini ba.

Bata tsammata ba ya dago kai sai suka hada ido,da sauri ta janye idanunta ta mayar kan wani dan qaramin frame dake dauke da certificate of honor da aka baiwa asibitin.

Karamin murmushi ya saka,ya gane cewa ta iya basarwa itama,saiya maida wayarsa aljihu a hankali,yaji yana son qureta,don haka ya kafeta da idanu,so yake ya kamata red handed,ya kuma tabbatar mata da kallonshi takeyi,abinda ya fuskanci tana avoiding kenan,don tun dazu da idanunsa ke kan wayarsa jikinsa ya tabbatar masa da kallonsa ake.

Wasu mintuna ta diba da take da tabbacin ya koma sabgar da yakeyi,zuciyarta naci gaba da raya mata ta sake juyawa ta kalleshi ko zata gane abinda yasa mata ke sonshi.

A hankali take juyar da kanta kamar me ciwon wuya,caraf ya sake kamata,ta kuma dauke kanta da sauri tana jin kunya fiye da dazu,wannan karon murmushi yayi mai dan sauti,sannan ya hade hannayensa a tsakiyar qafafunsa,cikin lallausan muryarsa yace

“Me yasa kuka gwanance wajen iya satar kallon mutum,sai kuma an kamaku kuji kunya…..amma ke me yasa bakya son na kamaki kina kallona?”

Daburcewa tayi sosai,nauyi da kunya suna cikata,karon farko da taji wasu kalamai da suka samu matsugunni a ranta har suka rudata,itama batasan tsautsayin da yasa ta nace saita kalleshin ba,kame kame ta fara yi,tahau gyara fuskar hijabinta,gyaran da bashi da tushe bare makama,hakan yasa ya sake kafeta da ido.

Sosai ya lura baqin fuskarta dukka a yanxu babushi,sai wata kala da fatarta ke fitarwa ta daban.

Sauko da idanunsa yayi saitin qirjinta,har yau bai gasgata jawahir data ce wai ta isa saka breezier ba,cikin wani mugun sauri ya kauda da idanunsa sanda ya rage qiris ta ganshi,ya sauke boyayar ajiyar zuciya yana godewa Allah da bata ganshi ba,da girmansa ya zube.

Kafin wani a cikinsu ya sake wani motsi an turo qofar dakin anshigo.

Dogon likita baqi,mara jiki sosai,saidai akwai alamun nutsuwa sosai a tattare dashi.

Hannu ya bawa samir sukayi musabaha,sannan yaja kujerarsa ya zauna yana amsa gaisuwar kaltum.

File din dake gabansa wanda da alama sabone ya bude,ya fara yiwa kaltum din tambayoyi.

Da qyar take iya amsawa saboda nauyin da takeji,kusan tunda ta girma ba’a taba sakata gaba ana mata tambaya irin makamanciyar wannan ba,samir na zaune kam kujerar yana monitoring nata har likitan ya gama.

“CT scan za’ayi mata,shine zaifi nuna dukka abinda nake buqatar gani,saidai akwai ‘yar tsada” ya fada yana qarasa rubutunsa jikin file din.

Tunda suka shiga dakin scan din gaba daya tsoro ya kamata,musamman data kalli machine na scan din,har batasan sanda ta tara qwalla a idanunta ba,ta waiwayo tana duban samir dake tsaye a bayanta,hannunsa daya cikin aljihun wandonsa,yayin da daya hannun nasa yake dan saman kanshi yana shafawa a hankali gami da karanta wani rubutu dake manne a farar takarda jikin bangon dakin.

A hankali wata nurse ta tura qofar dakin tashigo,hannunta dauke da wata riga da tafi kama data marasa lafiya,ta ajjiye rigar saman wani dan abu,sannan ta isa wajen machine din tana goge gadon dake maqale dashi,gami da gyara shimfidar kai.

Sai data gama tsaf kaltum na tsaye tana kallonta,ji take kamar ta zura da gudu tabar dakin saboda tsoro,gefansu nurse din ta tsaya tana ajjiye wasu allurai,sannan ta fara hadesu waje daya a syringe

“Idan na gama miki wannan allurar,zaki cire abinda kikasan akwai qarfe a jikinsa da yake jikinki,kamar bra da rigarki da kuma skert tunda akwai zip a jiki,saiki sauya da wannan rigar” ta fada tana nuna rigar da yatsantsa.

“Bismillah qaraso” ta fada tana duban kaltum sanda ta gama hada ruwan allurar waje daya.

Kanta ya daga sai suka hada idanu da samir wanda ya kafeta da ido,tuni ya hangi tsoro muraran cikin idanunta,saiya taka a hankali,ya isa wajen,yaja wata kujera dake gefan nurse din zuwa gabanta,sannan ya yiwa kaltum din nuni kan tazo ta zauna.

Narai narai ta sakeyi da idanu ba tare data ko motsa ba,wani qaramin murmushi ne ya subucewa fuskarsa,ya gane tsoron allura takeyi,abunda ya bashi mamaki,saboda ya tuna tsiwarta,baiyi tunanin zatayi tsoron allura ba

“Hala madam din taka tsoron allura take,anya basa an riqe mana ita ba?’ matar ta fada tana murmushi hadi da miqewa riqe da allurar tata.

“Bari na taimaka miki” yace da matar

Hannunsa ya cire daga aljihun nasa,ya qara taku biyar zuwa inda take tsayen,ya tsaya daga bayanta,,dab da ita sosai,har tana jin hucin lallausan turarenta

“unhummm……remove it” ya fada a hankali kamar me rada,abinda yasa taji gaba daya ta diririce kenan,kusancin dake tsakaninsu tana jin yayi yawa,saita sanya hannu a hankali ta dage hijabin nata,ta kuma miqawa nurse din hannunta,gami da rintse idanunta sosai saboda tsoron tsinin allurar.

Wani qaramar qara ta saki sanda aka saka allurar,ta yamutse fuska sosai tana jin wani iri har zuwa sanda ta zare syringe din tana cewa

“Muna gab da tashi,da sauri madam ki canza kaya sai kuyimin magana”tana kaiwa qarshen maganar ne sanda take bude qofa ta fice.

Kanta a qasa tana mulmula wajen da aka yi mata allurar,tana tsammatar jin ya fita amma bataji ya motsa ba,harta gama ta cire audugar

“Be hurry” ya fada muryarsa qasan maqoshi yana kallonta,batasan ya zata ce masa ba,amma hannunta ya qage,batasan da yadda zata cire kayan ba.

Kamar ya karanci matsalarta ganin bata da niyyar motsawa saiya sake takowa zuwa inda take,ya saka hannu a hankali ya zare hijabin jikinta,wanda ya hado da dankwalin dake kanta gaba daya ba tare da yasani ba.

Sassalkan gashinta data matse da dan qaramin band ya ware gaba daya ya bazu daga baya zuwa fuskarta.

Idanunsa ya dauke da sauri yana lumshe idanunsa,saiya bude ya sake maidawa kan sumartata dake qyalli a hasken fararen qawayayen dake dakin,jiya jiya jawahir ta tirketa aka tsefe ta sake wankeshi,ta kuma sanya streacher ta ja mata shi,ita tana mitar bai tsufa ba kuma baiyi datti ba,jawahir din kuma tana mitar dama masu gashi basason kitso ko kuma a taba musu kansu,inama itace keda suma kamar tata da anyi kallo.

Hannunsa biyu ya sanya ya tattaro gashin dake qamshin man da akayi oiling dinsa dashi dake dukan fuskarsa,daure mata shi yayi,sannan ya sake qara taku biyu yana rage tazarar dake tsakaninsu,ya sanya hannuwansa duka biyu ya juyo da ita tana fuskantarsa.

Hannunsa ya dora saman zip din rigarta ya zuge mata tun daga sama zuwa qasa,idanunsa na kallon wani waje na daban,saboda qamshin turarenta da yake shaqa sosai,wanda baisan me yasa yake sauya bugun zuciyarsa ba.

Sai da yakai zip din qarshe sannan ya saketa a hankali,yayi taku biyu baya sannan ya juya yana takawa a hankali cikin wani mutuwar jiki zuwa bakin window din dakin,bayan ya maida hannuwansa cikin aljihun wandonsa,daya hannun kuma yana duba agogon hannunsa yana cewa

“Ki canza da sauri karmu bata musu lokaci” ya dage labulen yana kallon farfajiyar asibitin.

Bude qofar akayi,amma duk da haka bai waiwaya ba,har zuwa sanda ya sake jin muryar nurse din

“Sir,she need your assistance,allurar tana dan riqr hannu” gaban kaltum yayi mugun faduwa,wannan matar zata jiqa mata aiki,riga a bude tana kokawar cire bra,ta samu ya kalli wani wajen kuma tayi calling attention dinsa,a hankali ya waiwayo,idanunsa suka sauka a kanta sanda ta tsaya cak da abinda takeyi din,zuciyarta na harbawa a jajjere,bata iya sake daga kanta ba harya sake iskota,wanda taji kamar ya bace bat daga dakin,zuciyarta ta qara nauyi sanda dumin hannunsa ya ratsa fatar bayanta,ya saka yatsuntsa guda biyu ya balle damammiyar bra din jikinta,wanda hakan ya baiwa abinda ta takura din damar sakewa.

Ajiyar zuciyar data kusa fita ita ya subuce mata sanda yake sabule rigar daga jikinta,yanayin komai ne yana tsaye daga bayanta,ya dauki rigar ya zura mata yana cewa
“Hurry up”

Da saurinta ta saka rigar wadda take ta yadice,a tsaye kamar ta masu aikin shara a asibiti.

“Ya salam!!” Ya fada qasan ransa har sai da labbansa suka motsa,da wani irin amo mai nauyi sanda kaltum ta juyo ta soma takowa zuwa wajen machine din kamar yadda nurse din ta bata umarni,tana jin kamar zata fadi da saboda nauyi,tana iya jin yadda rigar ta lafe a jikinta,ta kuma bayyana surarta dukiyar fulanin da Allah ya mata baiwarsu,take kuma boyesu tun daga sanda suka fara bayyana kansu,saboda kunyar hakan da takeji,har da yawa suke mata kallon qwaila.

Wani irin laushi da yaji qafafunsa sunyi suna shirin gaza ci gaba da daukan nauyin tsaiwarsa sai yaja kujerar dake dakin ya zauna,yana kallonta har zuwa sanda ta kwanta saman gadon kwanciyar rigingine kamar yadda nurse din tace mata,hakan saiya zamana kamar dama ce suka samu ta bayyana kansu sosai ta cikin rigar,gaza ci gaba yayi da kallonta ya zare idanunsa ya maida ga machine din sanda gadon ya dagata sama ya kuma turata tsakiyar machine din.

Shuru ne ya ratsa dakin,babu komai sai qarar machine din daketa wasu bayanai,ko sau daya bai qara daga idanu ya dubeta ba,yayin da kaltum tsoron machine din da kuma abinda ya farun ya karya duk wani kuzari nata,tanajin wani nauyi na ratsata,tunda take wannan shine karon farko da wani ya taba ganin ainihin surar jikinta,saita lumshe ido tana tuna yadda taji hannunsa saman jikinta,zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri.

Duba takaddun likitan yayi ya ajjiye CD plate din da suka hado dashi,tsahon wasu mintuna sannan ya dubi samir

“Gwajin da nayi mata a nan,da kuma wannan scan din ya nuna komai,akwai qarancin sinadarai a jikinta wanda zasu taimakawa zuwan period a jikinta,kuma hakan zai zamana yana da alaqa da matsalar haihuwa,so amma ba wani damuwa in sha Allah,akwai magunguna da zata fara sha daga yau zuwa sati biyu,suna da kyau magungunan sosai,zasu taimaka wajen samuwar sinadaran isassu da zasu kawo mata al’adar a kusa,kuma ina saka ran insha Allah tana kammala shansu period dinta na farko zaizo”

Kai samir ya jinjina,likitan yayi rubuce rubucensa ya bashi takaddun,ya miqe ya bashi hannu suka sake musabaha,yayi masa godiya suka fice.

Shuru ne ya zame musu jagora cikin motar,kowa da abinda yake saqawa,abinda idanunsa suka gani sune kawai ke kai kawo a qwaqwalwar samir din,wanda yaketa kokawar ajjiyeshi a gefe,saboda muhimma ayyukan dake tunkaroshi daga office,amma ya kasa tunkude tunanin daga kwanyarsa,hakan yasa yadan juya a hankali ya kalli gefan da take zaune,sai yaga har yanzu tana mulmula inda akayi mata allurar ne,saidai a badini itama tayi nisan kiwo wajen tunani ne,tunanin yadda zataci gaba da hada idanuwa dashi bayan duka wannan abun kunyar daya faru tsakaninsu wunin yau gaba daya.

Sai daya tsaya a wani waje na wasu mintuna sannan ya dawo cikin motar ya tayar suka qarasa gidan hajiya qamar.

*_ASHA HUTUN WEEKEND LAFIYA_*

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button