Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 39

Sponsored Links

 

*_Bayan wani lokaci_*

Sannu a hankali kwanaki suka fara shudawa kaltume a gidan fiye da yadda ta zata ko ta tsammata,bata taba kawowa kanta cewa zata zauna cikin irin wannan gidan ta rayu cikinsa ba,saidai lokaci da kuma qaddarar rayuwa sun tabbatar mata da hakan,saita fara tilastawa kanta zama ta fuskanci rayuwar a duk yadda tazo mata.

Jawahir da kanta ta zauna tayi list da total na dukkan abinda ya kamata ace an siyawa kaltumen,haka kawai cikin ranta takejin yarinyar tayi mata,duk kuwa da cewa a qalla zata bata shekara biyu ko uku,amma yanayin halayya da dabi’un kaltume,wadanda suka kusa zuwa iri daya da nata tana jin dadin hakan.

Ba tare da bata lokaci ba da aikawa da saraki amount din da take da buqata,bai tambaya ba ya tura mata,don a sannan kansa ya dauki zafi,anata lissafe lissafe na qarshen shekara cikin kamfanin,bai wani samun zama sosai,kullum da sassafe yake fita,ya kuma dawo bayan duhu yayi.

Randa zata siyayyar ta sanya kaltume a gaba kan sai sunje tare tunda kayanta za’a siyo,da fari ta doje,tace ba inda zata,amma daga bisani da taga jawahir din ta matsa saita amsa mata.

A tamfa ta fidda riga da zani cikin kayanta ta baiwa kaltumen kan ta saka,ta kada kanta

“Zani da kayan jikina” ta fada with confidence,bata jin saka kayan,kasancewarta mutum me gudun abun hannun wasu, fuska jawahir ta hada

“Shikenan,na gode” tayi furucin ne a sanda take tattare kayan zata fita dasu daga dakin kaltume din,dukkan alamu sun nuna taji haushi,sai kaltumen taji bataji dadi ba,ko ba komai jawahir da biba,sune mutanen da kaf cikin gidan bata da kamarsu,sun damu da ita da kuma rayuwarta,tamkar wata halitta ce ita din me muhimmanci.

Ruqo hannunta tayi kana ta karba kayan,ta shiga bandaki a take ta sauyasu,sannan ta fito tana jin yadda kayan suka sake ta,ma’ana sun danyi mata yawa,duk da siranta jawahir,saidai ita tafi jawahir din sirantaka.

Murmushi jawahir keyi,atamfar ta karbeta sosai da sosai,dama kalar da zata haska kowanne mutum ce

“Kinga ko kyau bata yimin ba,tayimin yawa ma,gashi kin bata kayanki” murmushi ta sakar mata

“Fada dai kawai kike,yadda tayi miki kyau ma ni bata yimin ba,yawa tayi miki dan kadan shima,qarasa shiryawa muje mu dawo don Allah” ta fada tana ficewa don dauko mayafinta.

Sanda zasu fice najwa na makaranta,mummy kuma tana bacci,don haka babu wanda yasan da fitarsu.

Babban store ta kaisu,inda suke da dukkan wani abu na buqatar rayuwa,baki kawai kaltume ta saki tana bin komai da kallo,tunda ta baro garin dinya take kallon komai kamar a majigin film,kamar wadda tayi hijira daga wata duniyar zuwa wata,komai da take gani a yanzu babu hasashensa ko sau daya cikin hasashe na duniyar mafarkinta,sai gashi yanzu komai yana zuwa mata a zahiri.

Tana biye ne kawai da jawahir sanda take diban mata kaya,lokaci lokaci takan waiwayo ta tambayeta wannan yayi?,saidai kawai ta gyada mata kai,don ba wani ganewa lamarin sosai take ba bare ta tantance,har suka gama siyayyar suka taho mamaki na nan cike fal kanta.

Ko a mota ma jawahir nata mata bayanin amfanin wasu abubuwan data siya mata,ji kawai take ba ganewa ba,tunaninta ya koma baya can ya lulaqa gida.

Dauko rayuwarsu take tana hadata da wannan,tako ina babu misali,babu kamanceceniya,ta rakito rayuwar asiya da a sannan ake ganin tayi fice,sai taga tazarar dake tsakanin tamkar kwatankwacin misalin tazarar sama da qasa ne,da wannan tunanin suka isa gida,jawahir ta diba wasu ledojin kaltum ta diba wasu.

Da sallama suka shiga falon,fuskar jawahir dauke da dariyan kaltumen data kewa bayani tace mata itafa bata ganewa.

Mommy na zaune qasan carfet,sanye da wata doguwar riga mai taushi mara hannu,kana mata kallo daya zakasan cewa rigar ta lashi kudi,duk kuwa da cewa an mata zubin riga mara nauyi wadda ba zata takuraka ba,hannunta dauke da cup na tangaran da aka cikashi da lemo,mawuyaci ne ka sameta a zaune hakanan qalau babu kayan qwalama a gabanta,sai najwa da aka ajjiyewa dan tebur gabanta aka cika mata shi da abinci tana ci,da alama yanzu ta dawo itama daga inda taje.

Fara’ar fuskar kaltum ce tayi qasa sosai,gabanta ya tsananta faduwa sanda suka hada ido da mommy,haka kawai take jin wani abu game da matar,ita dai tasan ba tsoro bane,amma yafi kama da shakka,uwa uba kuma ga dodon tata najwa dake zaune a gefe,dukkaninsu suka bisu da kallo har suka is tsakiyar falon,jawahir ta zube kayan gefan mommy gami da zama tana cewa

“Wash Allah na”
“Daga ina kuke haka?’ mummy ta jefa mata tambayar,wani abu yana fita daga tsakiyar sautin muryarta

“Siyayya naje muka yiwa kaltum……” Sauke idanunta tayi akan kaltum din,saita sadda kai,ita daya ta hangi wani abu tsakiyar kallon data jefeta dashi

“Yayi kyau…..ku kwashe kayan daga nan kun cikamin waje” ta furta tana ci gaba da shan lemon hannunta.

Miqewa sukayi su dukka,jawahir ta dauka wasu kayan kaltum ta dauki wasu suka nufi dakin kaltume din.

Suna shiga tun daga bakin qofa kaltum din tace

“Yaya jawahir kibar kayan nan,zan qarasa dasu,kije wajen mommy” dubanta tayi da alamun tambaya kan fuskarta

“Naje nayi mata me?,yanzu fa muka gama magana da ita”

“Kije kamar tanason yin magana dake ne,don Allah kije” dariya ta saki

“Shikenan,ki fito da dukka kayan kafin na dawo,zanzo na miki bayanin amfanin wasu a ciki” kaita gyada mata ta soma jan ledojin,yayin da jawahir din ta juya zuwa falon,tana mamakin yadda akayi kaltum din ta fahimci tanason mata magana,amma ba’a qin ta mutum,bari taje ta gani.

Mugun kallo daga wajen najwa ne ya fara mata sallama,amma sai ta dauke kanta,ba wani baqon abu bane,sun riga sun saba,mommy ta bita da kallo har ta zauna kusa da ita tana daukar remote dake gefan mommy tana sauya tasha

“Yaushe kuka fara yanke hukunci keda saraki a gidan nan ba tare dana sani ba?” Ta tsinci muryar mommy tana jefa mata tambayar,saita sauke remote din tana duban mommy

“Mommy…..me mukayi?”

“Wannan siyayyar da akayi da izinin waye akayita?,wa kika shaidawa?” Shuru kadan jawahir tayi,ita a iya nata lissafin bata ga wani abun ba dai dai ba a cikin lamarin gaba daya,fadan da mommyn ta fara ya sanyata shuru bata bata amsa ba,ta kuma rufe da cewa

“Zan sameshi shima,zan ja masa kunne”

“Banza kawai wadda bata kishin kanta,kwata kwata kudi daraja arziqi da kuma mulki basu dace dake ba,ta yaya kina jinin professor rashid zaki dinga zubar da kanki cikin ‘yan aiki,ke baki da wasu abokan hulda sai ‘yan aikin gidanku?,common wasu fitattaun qawaye ‘ya’yan manya baki dasu?,zaki gane kuskurenki ne sai randa bikinki ya tashi,baki da masu fiddaki kunya, mommy saiki daura damarar yiwa ‘yan aiki anko a matsayin bridesmaids” cike da jin haushi ta jefawa najwa harara kana ta murguda mata baki.

Abinda ya fusata najwa kenan,kasancewarta mutum me bala’in dagawa da son girma,bata qaunar raini ko kadan,sai tayo kan jawahir din da sunan kai mata duka amma mommy ta tareta

“Banason wannan sakarcin naku fa,wai ku mene yake damunku ne?”

“Mommy baki gani abinda ta yimin,ni zata harara?”

“Ya isa,ke tashi ki bawa mutane waje” mommyn ta fada saboda raba rigimar,abun yana damunta arai sosai,ta rasa yadda zata hade kansu yadda takeso,so take su qaunaci juna fiye da yadda take imagining cikin ranta,amma abun yaci tura,jawahir ta kalli gabas najwa ta kalli yamma,kowa tsarinsa halayyarsa da dabi’arsa tasha bamban data dan uwansa,kai bakace ciki daya suka fito ba.

Sai data ga bacewar jawahir sannan ta soma magana da najwa

“Kullum ina gaya miki kibar biye mata,dukka wadannan halayen nata zata barsu,akwai lokaci,kuma lokacin na bata”

“Amma mommy ta yaya kina xaune,kina cikin gidan nan har wani lokaci yazo da wani daya zai fara yanke hukunci kan wani ba tare da tuntubarki ba?” Murmushi ta sake kawai tana gyada kai

“Yaro man kaza” shine amsar data baiwa najwa,taci gaba da surbar lemonta a hankali,yayin data xubawa waje daya idanu kamar me nazarin nau’in qasar da aka gina wajen da ita.

Ringing wayar mommy shi ya ratsa shurun daya sanya kowannensu cikin nazari. A hankali ta ajjiye kofin hannunta,ta miqa hannu ta dauki wayar tata tana duba sunan me kiran.

Da hanzari ta miqe ganin wanda yake kiran nata,ta daga kai ta dubi najwa

“Kyauro ne” ambatar sunan ya sanya najwa duban mommyn sosai,kafin tace komai mommyn tayi gaba da hanzari xuwa dakinta tana cewa

“Ina zuwa,Allah dai yasa lafiya” bata tanka ba tabi mummyn da kallo kawai,daga nan inda take tana jin sanda take murza key tana rufe qofar dakin.

Numfashi ta fidda tana kyabe baki,ita a nata ganin mommyn nata tana wahalar da kanta ne kawai,duka wadan nan hanyoyin sun mata tsaho da nisa.

Mintuna kusan goma sha biyar cikakku mommyn ta fito tana riqe da wayar a hannunta,yanayinta ya sauya kadan ba kamar sanda ta shige ba,xuba mata idanu najwa tayi tana jiran taji wani abun daga bakinta

“Dole naje ma’ajiya,kyauro yace kwanakin nan kamar suna hangen akwai matsala” wayarta ta aje gefanta sannan ta dubi mommyn

“Bazan iya bun turbar da ko da yaushe kike bi ba mommy,bani da wannan juriyar,me yasa ba zaki me gaba daya ba ki huta?,me kike jira?” Ta tambaya uwar tana kafeta da idanu.

Kai mommy ta girgiza

“Banason haqqin rai bisa wuyana,a yadda nake kallon abubuwan komai ya kusa kawo kansa da kansa qarshe ba tare da ina da wani jibi ko tuhuma akan abun ba” shuru ya sake biyo baya,kafin mommyn ta sake magana

“Ki shirya zamuje nan da kwanaki biyar”

“Ranar lahadi kenan?”

“Eh….hakane,kamar dai yadda muka saba”

“Ranar zan shiga makaranta clearance…….saidai ki zaba wani dan rakiyan,don already ma na soma qosawa da xuwan” harara mummyn ta watsa mata

“Kyaci qaniyarki,ko meye nake ba dominku nake ba” dariya najwan ta saka,cikin ranta tana jin koma meye mommyn take domin su,ya zame mata dama dole tayin,idan ma batayin ba,bata jin ita zata zauna bata yiwa kanta wani gata ba.

********** Dukka idanunta ta zuba tana kallon kaltumen sanda take maimaita karatun data gama yi mata shi yanzun nan kamar ta shekara da iyashi,sau tari takan cika da mamaki tare da shakkar anya kuwa kaltumen ba boye musu tayi ba ta iya wasu abubuwan?,wani lokaci kuma mamakin nata yakan ragu idan ta tuna cikin hirarrakin da sukeyi da biba,ta taba shaida mata,su yaran qauye mafi yawancin lokaci sunfi na birni fikira basira da kuma azanci,saboda yanayin cima da kuma muhallin da suka girma,mai wadatar korran tsirrai,wanda ke cike da wadatacciyar kuma tsaftatacciyar iska mai kyau.

Sannu a hankali yake takowa zuwa inda suke zaunen,kebantaccen waje ne da yake malale da tattausan koren grass carpet.

A nutse yake tafiya cike da ginshira,kai idan baka sanshi ba sai ka dauka wani jinin sarauta ne,komai nashi me kyau a tsare a killace cike da tsafta da kuma aji.

Qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar karbarsa,suka kuma fitar da siffar da Allah ya bashi,ta tsaho wanda ke tafe da murjewar jiki daya bayyana surar qarfi a tattare dashi sakamakon daga qarfe da yake yawan yi,iska ce ke raba turarensa mai tattausan qamshi zuwa kowacce kusurwa dake daura dashi,hakan yasa yana dab dasu jawahir ta shaqi turaren ta kuma daga kanta don tabbatarwa da kanta shi dinne.

Murmushi ta saki saiya maida mata sanda yake dab da su

“Yaya,u are welcome…”ta fada tana gyara zamanta.

Kiran sunan yaya da tayi yasa kaltume dake faman son fara hada sentence da kanta duk da karatun baiyi nisa ba ta daga kanta,idanunta ya sauka a kanshi.

Suna hada ido saita sauke nata idanun a hankali tana gyara zamanta,ba wai don zaman nata baiyi ba,hakanan kawai taji tana buqatar ta gyara din.

Yana murmushin dake qarawa fuskarsa kyau da kwarjini yaja kujeran guda daya dake wajen,wadda da alama wani ne ya kawota ya zauna a kai

“Auta,an fara karatun kenan?” Ya fada sanda yake zama saman kujerar,qamshinsa yana mamaye wajen

“Allah yaya ka zama kudi,wahalan gani kake?” Murmushin ya sake saki,yana duqawa ya diba litattafan kaltume dake zube a wajen

“Ina wuni” ta gaidashi da siririyar muryarta,ya daga kansa daga litattafan daya fara budewa ya amsa

“Kina lafiya?”

“Lafiya qalau” ta amsa masa

“Babu wata matsala ko?” Ya kuma tambayarta a karo na biyu sanda ya buda shafin farko,itakam anan bata ga wata matsala ba,bata da rashin ci,babu rashin sha,babu rashin muhalli me kyau,matsalarta daya ce zuwa biyu,tunanin ummanta da habi dinta,sai kuma najwa da bata qaunar taga koda giftawarta,a iyaka saninta babu wani abu data taba aikata mata na kuskure ko ba dai dai ba,matsalar mummy kuma bata jinta da wani girma can,tunda a qalla tunda suke bata taba buda baki ta gaya mata wata kalma mara dadi ba,saidai kallon da take yawan yi mata yana sanyata jin tsarguwa aranta da kuma rashin sakewa,sai taji kamar an dabaibayeta.

“Babu” ta amsa masa a taqaice,tana jin wani nauyinsa da kwarjini,itakam yafi mata kama da baiwa da uban gidanta,gaba daya ta zame kalmar miji daga kansa,kallon uban gida tafi yi masa

“Ma sha Allah” ya amsa tana ci gaba da duba litatafan,wanda tun baiyi nisa ba ya soma mamaki,don bai tsammaci komai zaizo haka da sauqi ba.

Tsahon wasu mintuna sannan ya kammala dubawar,ya daga kai yana kallom jawahir

“Auta ya dalibar taki?” Murmushi ta saki tana miqawa kaltume wani littafi data gama duba mata wani dan qaramin aiki data gama duba mata

“Yaya,wannan dalibar tawa ta kusan zama malama, to my surprise duk abinda aka karanta sau daya ta gama daukeshi,abun yana bani mamaki sosai” kansa ya jinjina,alamun qarfi yana ga me qiba,tun kan yayi tambaya idanuwansa suka gane masa komai

“It means zata iya zana common entrance kenan?” Murmushi me kama da dariya tayi

“Yaya saidai placement gaskiya,wata uku na gaba fa?,karatun namu yana sauri ne fiye da tunanin me tunani”

“Good,am happy to hear that” kafin su kuma cewa wani abu daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo.

A ladabce ta gaida samir,sannan ta dubi kaltume

“Hajiya najwa tana kiranki” shuru wajen ya dauka,yayin da qirjin kaltum ya soma bugawa cikin tsoron kiran nata

“Muje na rakaki” jawahir ta fada tana miqewa

“Barta taje ta dawo,zamuyi magana dake” da baya ta dawo ta zauna badon taso ba,tafi kowa sanin halin najwan,babu lallai saboda Allah tayi kiranta,saita dubi kaltume sanda take saka wani lallausan slipper,yana cikin siyayar da jawahir tayi mata

“Jeki kaltum,amma ki dawo mu qarashe karatun yau,tunda kin iya wanda akayi” kanta ta gyada ta soma takawa a hankali tana biye da jamila data zo kiranta.

Ajiyar zuciya jawahir ta sauke sanda kaltume ta bacewa ganinta,tana juyowa suka hada ido da saraki

“Ya akayi auta?”

“Tausayinta nakeji yaya,da mahaifinka da mahaifiyarka amma a kawoka wata uwa duniya da sunan aiki,ka daina ganinsu kwata kwata,tana da hankali sosai yaya,tana da sanin ya kamata,shi yasa ko yaushe take shiga raina take burgeni” hanyar yabi da kallo kafin ya dawo da hankalinsa ga jawahir,shi kansa yana jin she needs more attention daga wajensa,har ransa yana jin zai kula rayuwarta a madadin rayuwar bilal da yayi niyyar taimaka,tunda ita dashi duka abu guda ya yisu……..

“Ranki ya dade gata” jamila ta fada a ladabce tana matsawa gefe.

Waiwayowa tayi tana duba kaltume ita da sauran mutanen dake wajen,fuska a murtuke tace

“Ke,cikin dakina xaki shiga,qadangare ne ya shigomin ta window din baya ki ciremin shi,nasan ku qauyawa ba tsoronsa kuke ba mazanku da matanku” tayi maganar tana riqe da qugunta idanunta qir a kan kaltume.

Lokaci guda tsoro ya saukarwa kaltume,a duniya qadangare na daya daga cikin abinda bala’in tsoratar da ita,tund a gida basa hada hanya dashi,tun wani lokaci data yiwa inna laure laifi ta sanya mata shi a jikinta,sai dibanta akayi a sume.

Kai ta girgiza cikin rawar murya
“Wallahi ban iya cirewa ba,nima tsoronsa nake”

Zare idanu najwan tayi cikin salon masifa
“Ke ni zakiwa qarya,ku jimin yarinya da samun waje…..har a gayawa baqauye kama dabbobi,to wallahi yau saikin cireshi ko me zakiyi saidai kiyi” jin haka yasa kaltume dan ja da baya zuciyarta na bugawa tana girgixa kai

“Allah nima tsoronsa nake,da na iya dana cire miki” kafin ta ankara ta sanya hannu ta fincikota,ta kuma turata dakin ta maida qofa ta rufe.

Tsoro ne ya kamata,ta soma raba idanu,cikin rawar murya ta fara roqon najwa kan ta budeta bata iya cirewa ba,saidai tana jinta tana kuma tsaye bakin qofar dakin tana masifa tare da cin alwashin ba zata fito ba harsai ta cireshi,idan ba haka ba ta zauna a dakin,tsahon wasu mintuna amma najwan ta kafe kai da fata.

Razananniyar qara kaltum ta saki sanda qadangaren dake maqale jikin labulen ya fito yabi takan qafarta,gaba daya ta fita hayyacinta,sai kuka data saki mai qarfi.

Qarar ita taja hankalin samir da jawahir dake tattaunawa

“Yaya muryar kaltum ce fa?” Jawahir ta fada tana miqewa idanunta akan samir din,saiya miqe yace

“Muje”.

Dukkaninsu darewa sukayi da ganin shigowarsa,banda najwa da tayi ta maza ta maze,sam batayi zaton yana kusa ba.

Bai kalleta ba ya isa bakin qofar dakin sanda jawahir ke tambayar najwa ba’asin abinda ke faruwa,ya murxa muqullin a nutse ya tura qofar ta bude.

Tana ganin haske bata tsaya banbamce abinda ke faruwa ba tayi hanyar da gudu,babu bata lokaci sukayi clashing,tayi kyakkyawan masauki a jikinsa.

Hannu yasa ya zareta a hankali yana jin yadd zuciyarta ke mugun bugu,saiya kama hannunta ya fiddota bakin qofar dakin ya tura qofar ya rufe,don ya fuskanci akwai abinda take tsoro cikin dakin.

A hankali ya saki hannun nata ganin yadda suke bin hannunshi dake riqe da siririn tsintsiyar hannunta da kallo,fuskarsa a matuqar dinke ya dubi najwa

“Me kika mata?” Cikin son nuna dakiya tace

“Qadangare nace ta ciremin fa kawai”

“Ce miki tayi ta iya?”

“A’ah”

“Amma meya saki turata dakin harda rufe qofa?”

“Yaya bakaga daga inda ta fito bane,har tace bata iya cire qadangare ba saboda sanabe?”

“Meye nasabar inda ta fito da iya cire qadangare?” Ya jefa mata tambayar wannan karon cikin matuqar fushi

“To ai……”

“Mtsw common keep quiet!”

“Yaya kowa fa…..”

“Will you shut up ko sai na saki a dakin kema kinji yadda akeji?” Ya fada yana tura qofar dakin,wanda hakan ke nuna mata da gaske yake

“Am sorry” ta fada ba tare data shirya ba,don taga bacin ransa qarara.

Wani mugun tsaki yaja kamar xai cire harshensa,ya waiwaya ga jawahir da itama haushi da takaici ya cikata

“Ki tafi da ita dakinki”

“To yaya….” Ta amsa mishi tana kama hannun kaltume sukayi gaba,ya taka a hankali yabi bayansu ba tare da yabi takan matsalar najwan ba.

Bin bayansa tayi da kallo zuciyarta na quna,lallai ya tabbata mutumin nan bai qaunarta shima,tunda har zai barta da abinda take tsoro.yayi tafiyarsa,bayan yasan ko mommy bata a gida,saita juya fuuu tayi hanyar fita zuwa farfajiyar gidan,zata juyewa security nasu rabon.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button