Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 13

Sponsored Links

 

“Yaya….abincinka ya xama ready”jawahir ta fada da yanayin shagwabar nan tata,kai kace har yanzu bata rufa shekaru goma bama,da qaramin murmushi ya saki,akwai abinda yakeson sani amma ta hanyarta,don haka yace
“Thank you autar momy…muje ki hadamin,saiki koma cikin gida”
“An gama yaya”ta fada tana dariya,ya jinjina kai ya soma takawa tabi bayansa.

Baiyi taku biyar cikakke ba wayar tasa ta sakeyin qara,saiya dagata yana duban waye kuma ke sake kira,Hajiya hafsatu ce wadda suke kira da hajiya qarama,qanwa ga Professor rashid azare,qanwa ‘yar gaban goshi wadda yakeji da ita qwarai da gaske,kasancewarta diya mace qwaya daya kaf a fadin dakinsu da mahaifiyarsu ta haifa,har ta koma ga mahaliccinta,sai qanwarta mahaifiyarsu me suna karimatu da suke kira ya dikko da a yanzu suke kalla a madadin mahaifiyar tasu,wadda ke zaune a azare cikin ainihin gidan gadonsu da ayanzu professor ya qawata mata shi,babu yadda baiyi ta zauna kusa dasu ba amma sam taqi,tace tafison qasarta,tafison ta rasu a inda aka haifeta,amma halan baisa sunyi watsi da ita ba,lokaci zuwa lokaci suna ziyartarta,hakanan dukka yaransu suna daukarta kamar kakarsu ce wadda ta haifa iyayensu.

Hakan na mata dadi ba kadan ba,yadda yaran yayarta suka maisheta uwa,saboda dama yaro daya tal Allah ya bata,ya rasu yabar nashi yaron guda daya shima,wanda a yanzu suke tare dashi cikin gidanta,ita dinma tunda can macace mai kirki qwarai,ta hadasu ta rungume duka,saika rantse da Allah yaranta ne.

“Hajiya qarama?”ya fada qasa qasa murmushi na fita saman fuskarsa,babu abinda ya fado masa sai drama dinta,mutum ce mai rigimar tsiya,idan ta gaddame kan abu babu mai saukar da ita,idan bashi ba da Allah ya hada jininsu qwarai,ya kuma sanya mata qaunarsa saiko daddynsu,don ko yaranta idan ta hutsance musu saidai su nemi agaji a wajensu.

Sallama ya soma yi mata sannan ya dora da cewa
“Mamana..,maganin kuka na”
“Eh….kace haka mana,tunda ko ranar da zan dawo ma baka riqe ba?”murmushi mai dan sauti ya saka
“Kiyimin afuwa don girman Allah,wallahi abubuwa ne masu yawa suka sha kaina”
“Nayi maka,ka shigo gobe inason ganinka” saida fargaba tadan kamashi,saboda sanin halinta,ba kasafai take masa irin wannan kiran na gaggawa su qarketa ta dadin rai ba,dama ko kafij ta tafin akwai tsumammiya a tsakaninsu,amma don duka ya wanke kansa sai yace
“Ina nan zuwa in sha Allah hajiya”
“Allah ya kawoka lafiya,kafin ka tafi,kaje wajen babanka ka karbarmin man zafin nan a wajensa,don da ciwon qafa na dawo”
“To hajiya,babu damuwa”daga haka dukka suka gimtse layin,ya sauke wayar yana sauk ajiyar zuciya,sai suka hada idanu da najwa dai dai sanda take ajjiye kwandon hannunta a qasan makeken lallausa carpet din dake shimfide a falon,wanda kusan kaf gidan nan ne kawai babu tiles,dariya take tana fadin
“Ho hajiya qarama,don Allah yaya idan xaka goben na shirya na rakaka”. Girarsa ya dage sama yana neman wajen zama,sannan ya girgiza kansa alamar a’ah
“Ba zaki bina ki kwabamin al’amura ba”dariya ta saki sosai ta samu waje ta zauna ta fara zuba masa abincin,sannan kuma tana bashi labarin wasu dramomi da suka sha da hajiya qaraman,yanata murmushi yana saurarenta.

Bai katseta ba,haka baice da ita komai ba,yana cin abincin tana ci gaba da yiasa hira,wanda ta dauke masa kewa sosai.

Kusan dukka cikin gidan yafi kowa fahmtar jawahir,zahiri tana da surutu sosai,saidai kuma akwai hankali nutsuwa da sanin ya kamata,fiye dana ‘yar uwarta,tana da sauqin kai da tausayi fiye dana najwa,ta wannan fannin kam ta mata fintinkau,sabanin najwan dake da shegen daukan kai da fadin rai,da kuma miskilanci idan taso,harda na banza da wofi ma.

Sai daya tabbatar labarinta ya qare sannan ya dubeta
“Akwai wani abune da bansanshi ba?”ya mata tambayar data je mata a baibai,don bata gane abinda yake nufi ba,duk da dama tasan halayyar yayan nasu,gwanine wajen magana da kalmomi masu harshen damo
“Me kenan yaya?”ta tambaya kai tsaye,sai daya gyara zamansa sosai sannan yace
“Meya kawo sauyawar najwa fiye da yadda take a baya ne?” Take alhini ya bayyana sama fuskar jawahir,ita kanta abun yana damunta,sannan yana bata mamaki,duk da dama najwam ba kirki ta cika ba,amma a ya zu abun nata yana qara gaba ne,tamkar wani tunzuri,tsahom wasu sakanni tana tadi da zuciyarta da tunanun amsar da zata bashi,shi kuma tsahon wannan lokacin yana karantar fuskarta,yana kuma karanto amsar tambayarta ba tare data furta ba
“Ban sani ba yaya,nima abin yana ta banu.mamaki” ta bashi exactly irin amsar da yake sanya ran dama ita zata bashi,saiya dauke idonsa daga kanta yana jinjina kai gami da sauke numfashi
“Ohkey…ohkey….shikenan to”
“Amma yaya kona tambayeta,ko kumw na bincika?”ta fada har yanzu yanayin alhini baibar saman fuskarta ba,hannu ya daga mata yana fadin
“No auta….barshi,zan aiwatar da komai da kaina”saita sauke ajiyar zuciya mai nauyi,da alama itama abun na ci mata rai
“Shikenan yaya”….

*******. ******. ********

Idan banda qamshin daddadan turare babu abinda jikinsa yake fitarwa a yammacin,wanda dukkan wanda ke kusa dashi idan ua shaqi qamshinsa gamida sassanyar iska mai dadi dake kadawa,babu abinda xai haifarwa zuciyarsa sai wani yanayi na farincikin da baisan daga wace nahiya ya taho ba.

Sosai yayi kyau cikin shadda ruwan makuba,wadda koda ba’a gaya maka ba kasan cewa sabuwa ce,hakanan bata qananun kudi bace,saidai duk da tsadarta hakan bai hana ayi mata dinkin zamani ba wanda ya dace sosai da mamallakim shaddar,ya bayyanar da sunan na nasa na THE GIANT SARAKI wanda mafi yawan abokai ke kiransa tun ba yau ba.

Ainihin ginin gidan ya nufa,yana tafe yana daura gogo tare da amsa waya da zakayi tsammanin surutansa kawai yake shi kadai,saboda baka hangi ta inda wayar da yake magana da ita take ba,saika lura da kyau sannan zakaga abinda ya maqala cikin ramin kunnensa.

Koda yayi sallama cin falon ma ya kusa kashe minti uku yana wayar,da alama bayanin sa ake masa ta cikin wayar mai tsaho ne,amma ganin fitowar mommy saiya ginmtse wayar ta hanyar cewa zai kira,ya daga kai yana dubanta sanda take isowa,fuskarta kamar kowanne lokaci dauke da murmushin dake bayyanawa duk wanda ya mu’amalanceta koda na minti biyu ne bare wanda ya zauna tare da ita tsananin kirkinta
“Daka qarasa wayar son ai” kai ya girgiza yana sakin qaramin murmushi
“Umar ne,zan kirashi later….za fita ne nace bari na shigo na gaya miki…..zanje gurin hajiya qarama,ta dawo jiya” yayi maganar ne sanda yake sanya links din hannunsa guda daya da bai qarasa sanyawa ba,baima kula ba sai yanzu.

Da sauri ta gimtse abinda ke tasowa saman fuskarta ta maye gurbinsa da murmushi,muryarta a tsananin washe tace
“Ma sha Allah,amma hafsatu ta dawo babu wanda ta shaidawa cikin gidan nan saikai?,bana jin ko daddynku ma yasan da dawowarta,don inda ya sani zai shaida min”
“Ayyah…bansani ba,da nasan bai sani ba dana gaya masan” murmushi ta kuma yi
“Wala’alla har yanzun fushi dai take ci gaba dayi dashi…..idanma hakanne mu ba zamuyi fushi da ita ba ai,bari na baka saqo ka kai mata,duk da babu yawa,bansan da dawowarta ba”tayi zancan a lokacin da take gab da shiga kitchen.

Daga baki bakin qofa ta tsaya,ta riqe dukka hannayenta a qugunta,idanunta na yaw cikin kitchen din,ta zuqo iska daga hunhunta ta fesar,sannan ta sauke hannayenta ta taka zuwa ciki,sai a sannan kuma mutanen ciki suka ankara da shogowarta.

Katafaren kitchen ne wanda ya hada dukkan wani abu na buqata da kitchen ke da buqatarsa,masu aiki ne har mutum uku a ciki,kowa da abinda yakeyi.

Cikin nuna tsantsar girmamawa ta matakin farko kowa ke mata barka da shigowa,bayan kowa ya dakata da abinda yakeyi don jiran me zatace
“Zuwaira…”
“Hajjaju”ta amsa a ladabce
“Hada abinci maza ki miqawa samir yana falo zaici fita zaiyi,ki tabbatq kome kin zuba masa a tsaftataccen mazubi”
“Angama” ta fada da hanzari tana ajjiye abunda ke hannunta ta nufi aikin da aka sanyata
“Lami” ta sake kiran daya daga ciki
“Gani hajiya” tana matsowa dab da mommyn,duk da ta bada ‘yar rata a tsakaninsu
“Ina kilishin nan da aka kawomin jiya?”
“Yana inda kikaje na ajjiyeshi” saita jinjina kai
“Deboshi ki kawomin shi nan”
“Duka hajiya?” Ta tambaya a mamakance,saboda bata manta yadda tayita jaddda mata tayi masa ajiyar mutunci ba,don ma’abociyar son kilishi ce
“Gaba dayansa”ta fada mata yadda zatafi fahimta,da sauri itama ta wuce,minti daya bata rufa ba ta dawo dauke da leda,wanda ko a ido idan ka kalla zakasan yana da yawa basai ka duba ba,hannu tasa ta karba,sannan ta juya ta fice daga kitchen din,su kuma suka ci gaba da abinda sukeyi.

Duk da mamakin ganinsa a tsaye bai taba kwanukan ba,amma murmushi bai bar fuskarta ba
“Ya haka samir?,kai da zaka fita,ka zauna kaci mana”
“Babu komai mommy,zanci wajen hajiya,duk a yakema ba wata yunwa nake ji ba”,saita dan tsuke fuska kadan
“Samir,kanason ka jawomin hajiy qarama tayi tunanin baka samun kulawa kenan?” Murmushin daya bayyanar da haqoransa yayi
“Haba mommy,nidin kamar qaramin yaro,karki damu” bata amsa masa ba,ta miqa masa ledar hannunta
“Gashi ka kai mata,kace ina gaidata da kyau kafin na shigo” sai daya kalli ledar kafin ya amsa,idan ba mantawa yayi ba jiya aka kawo mata abinda ke ciki,kuma juyin duniya auta jawahir tayi ta diban mata amma tace sam,idan tanaso su niqi gari ta basu address sukai namansu suma yi musu,amma gashi kacokam ta kyautar ga hajiya qarama,duk da rugurgujajjiyar alaqa sa dangantakar dake tsakaninsu
“Xataji” ya amsa yana juyawa
“Saika dawo”ta furta tana juyawa itama don barin falon.

Gefansa ya ajiye ledar a seat mai zaman banza,ya saka muqulli yana yunqurin tada motar wayarsa ta katseshi.

Wani qawataccen murmushi wanda yake jimawa kafin ya fita daga fuskarsa ya bayyana bayan an karanto masa sunan wanda yake kiran nasa,amsa kiran yayi, bai kuma bari anyi magana daga wancan sashen ba shi ya fara cewa
“Kai….kada kacemin kun dawo” dariya aka saki
“Mun dawo,minti hamsin kenan” fuska yadan bata
“Amma baka kyauta ba, at least ai ka gayamin ko nazo na tarbi abba a airport”
“Idan kana free a sannan ba,nafa sanka?”saiya lumshe idanunsa sannan ya bude
“Jokes apart don Allah,abba ne fa?”
“I know,wasa nake maka nima”
“Ok ka tsammaci zuwa na,am on my way” bai jira amsarsa ba ya katse kiran,ya tada motar da hanzari,da alamu uzurinsa da saurinsa ya qaru akan nada.

Har ya gota supermarket din saiya rage gudu kuma,yayi reverse ya dawo a hankali,ya samu waje ya tsaida motar sannan ya kasheta ya fito.

Baya taba iya shiga wajen hajiya qaraman hannunsa haka,yana ganin girma da qimarta,yana girmama qaunar da take nuna masa,duk da yawan fadanta,saiya taka cikin nutsuwa zuwa cikin supermarket din.

A hankali yake duba abubuwan da yasan tafiso yana zabarsu daya bayan daya,har sai daya kammala gaba daya,sannan ya nufi inda suke ajjiye Madara don ya siya mata,yasan qaunarta da madara tun ba yau ba,musamman ta gari.

Yana shan wata kwana yarinyar na bullowa itama cikin gudu irin na yaran da basu rufa shekara uku a duniya ba,taqin dake tsakaninsu kadan ne,da alama akwai wanda ya biyota,saiya tsaya ya mata lamfo,tana qarasowa ya dauketa cak zuwa sama,suka hada idanu,saita qara sakin dariya sosai tana cewa
“Anty mubina ce….”ko kafin ta rufe bakinta daga maganar anty mubinan kuwa ta bayyana,siririya farar budurwa,wadda shekarunta basufi ashirin ba,sanye da abaya ruwan jinin kare,ta yafa mayafinta saman kanta ba tare da tayi rolling ba,wanda hakan ya bayyana wani daga sashen gashinta da yake a tsefe.

Tsaiwa tayi tana duban yarinyar tana kuma duban samir dake dauke da ita,tana kuma sake maqaleshi tunda ta hangi mubina din,rada yayi ma yarinyar a kunne,sai taga ta sakeshi,maimakon ya miqa mata ita,saiya dauki kwandonsa ya juya yabar wajen,ya nufi wajen biya,tilas badon taso ba ta soma binsu a baya,qirjinta na dukan uku uki,ganin yayi gaba da yarinyar mutane.

A saman canter ya dora yarinyar yana tambayarta sunanta
“Afra” ta bashi amsa,saiya ciro atm dinsa ya miqa musu ya sanya musu pin bayan sun buqaci hakan sannan ya maida hankalinsa kan afra yana tambayarta meya sakata gudu
“Wai don na cewa anty mubina…..mu bari sai dan anjima saimu tafi,ta barni na gama kallo shine tace a’ah” dariya sosai yarinyar ta bashi,yasaki faffadan murmushi yana dubanta
“Waye yace miki ana zama cikin shago?,ba anan ake kallo ba kinji?,idan kinason yin kallo akaiki wajen wasa” yanayin fuskar yarinyar yaga ya canza,saita narke fuska
“Aida abbana ke kaini”
“Yanzu fa?”ya tambayeta shima yana rage fara’ar fuskarsa
“Anty mubina tacemin ya rasu,kuma idan aka mutu ai ba’a dawowa ko?” Juyawa yayi ya dubi sashen da mubinan ke tsaye tana kallonsu,sosai ranshi ya baci,tausayin yarinyar ya kamashi,ta yaya yarinya qarama kamar wannan zata dinga gaya mata babanta ya mutu kuma bazai dawo ba,ba mamaki she’s mad.

Kafin ya sake cewa komai ya miqo masa katin yana shaida masa an gama cirewa
“Hold it…..ina zuwa”ya fada yana sake saba yarinyar a kafadarsa ya koma cikin shagon.

Siyayya ya dinga mata sosai,duk abinda ta nuna tana so saiya daukar mata,har sai data ce babu saura sannan suka dawo wajen biya,ya sauketa yana sake miqa musu,suka lissafa suka zari kudinsu suka zuba masa a leda,saiya riqe hannunta,suka qarasa inda mubina ke tsaye,wanda zuwa yanzu ta sake tsurewa sosai,ga tsoro ka fargaba,kamar ta dora hannu saman ka tayita ihu,tana qiyasta dukan da zata yiwa afra ne kawai da irin wannan giggiwar tata yau da takeson janyo musu tashin hankali.

Tura afra yayi gabanta,ya hangi hararar da take zabga mata,cikin husky voice dinsa yace
“Wawanci ne gayawa yaro wani nasa mai muhimmanci ya rasu,it hurts alot koda agun babba ne bare yaro da kanshi bazai iya dauka ko jurewa ba”saiya zame hannunsa daga cikin na afra,ya ajjiye ledar
“Don’t do it again…..” Ya fada sounding seriously Yana kaiwa haka ya juya ya soma takawa,sai kuma ya tsaya,ba tare daya waiwayo ba yace
“Karki sake ki taba lafiyarta koda wasa” saiya qara gaba,ya dauki ledarsa yabar shagon.

Bata dauke idanunta daga kanshi ba sai daya fice,taja iska sosai har cikin hunhunta tana jin sauran qamshin daya tafi ya bari a wajen,hakanan taji ta kasa dukan afran,tana shirin jan hannunta taji an dafa kafadarta,ta waiwaya a hankali,basma ce
“Waye wancan,wani mai zafin kika samo hala?”ta fada tana murmushi murmushi dariya dariya,sai datasa hannunta ta zame hannun basman daga kafadarta sannan tace
“Wannan me sanyi ne tako ina”
“Wannan uban kayan da kika debo fa mubina?kinsan dai maama tace kada mu diba kaya da yawa ko?” Basman ta tambayeta tana duban ledar gabanta
“Daga mai sanyi ne,shi ya siyawa afra”sai tayi hanyar barin shagon itama,yayin da basma ta biyota cikin mamaki tana jera mata tambayar ta sanshi ne
“Ko sau daya”ta amsa mata a taqaice sanda suke isa bakin motarsu,don a yanayin da take ciki bata buqatar dogon surutu da doguwar magana irin ta basman.

A farfajiyar harabar gidan yayi parking,kallo daya zaka fahimci gidan akwai wadatar rayuwa da kuma sukuni,yana kashe motar ma’aikatan dake farfajiyar gidan suka qaraso inda yake,dukkaninsu cikin sakin fuska,saiya fito ya maida murfin motar ya rufe,yana basu hannu daya bayan daya suna gaisawa,suna ganin girma da mutuncinsa,saboda yadda yake baiwa duk wanda ya cancanta irin girman daya dace dashi,kusan yasan darajar kowa,yana kuma mutunta kowa,kamar ba ma’aikatan gidan ba,ihsani yayi musu kamar yadda ya saba duk sanda Allah ya kawoshi gidan kana ya wuce zuwa cikin ainihin gidan.

,daya daga cikin ma’aikatan yana riqe da ledar daya mata siyayyar a ciki.

Da sallama ya shiga falon bayan ya karba ledarsa,ta amsa masa sanda take zaune gaban zainaba me mata kitso,tana lallabe mata kan nata da manyan kitso dan hannu biyu,duk da girma amma sumaeta tana nan,saboda sunyi gadon gashi sosai,duba da irin asalin jinsin yaren da suka fito.

Ana qarshe dama suke,don haka bai jima da zama ba zainaba ta gama tayi mata sallama ta tafi bayan ta sallameta,saiya zamo daga saman kujeran ya zauna qasam carfet sosai shima yana duban hajiya qarama tare da sake gaidata,gami da yi mata barka da dawowa,cikin kulawa da kuma jin dadi ta amsa,saita daga murya tana kiran ‘yar aikinta.

Ba jimawa ta qaraso,ta rage tsaho sosai tana gaida samir,duk kuwa da cewa ta girmeshi,ya kuma dade yana hanasu duqa masa wajen gaidashi amma sun kasa,saboda girma da qimarsa sosai da suke gani
“Ki kawowa samir abinci”ta umarceta,saita amaa tana juyawa da sauri zuwa ciki.

Ledojin gabansa ya ajye gaban hajiya qarama wadda ke qoqarin daure kanta da dankwalin atamfar jikinta
“Ga wannan hajiya,babu yawa,wannan ledar kuma…. mummy ce tace a kawo miki” yana kallon yadda ta tabe baki,sannan ta saka hannu taja iya ledar daya kawo mata tana cewa
“Ni nace ta kawomin wani abu ne?,saboda irin haka fa yas ako yayan bai gayawa na dawo ba,don karta cikani da kayayyakin da ba domin Allah aka shiryasu ba,sai don shegiyar riya da son iyawa” shuru samir kawai yayi baice komai ba,don dama bashi daya cewar,yana ganin tunda aka kai wadan nan tsayin shekarun babu jituwa tsakanin hajiar da mummy,baya tunanin nan gaba za’a samu,yana daya daha cikin abubuwan dake sanyashi a tunani,wadanda har yau ya gaza samun amsoshinsu,meye tsakanin hajiyar da mummy da har yanzu ta kasa qaunarta,duk da tarin kyautatawar mummyn a gareta,hakanan shidai da idanunsa bai taba ganin mummy ta damu game da abinda hajiya qarama take mata ba,bata taba nuna fushi gazawa ko qpsawa ba,amma hakan baisa hajiya qarama yin haquri ya zubda makamanta ba.

Abinda ba kasafai yake yinsa ba,tunda yana ganin sha’ani ne daya shafesu,hakanan na sama dashi ma sunyi sun gaji sun bari,amma a yau din saiya murmusa sannan yace
“Kiyi haquri hajiyata….. nummy kan da murna da kirkin nan nata ta bada saqon a baki,duk da kuwa har autarta ta hana,amma keta zabeki ta baki” baki ta sake tabewa tana dan jifansa da harara
“Yoni ina ruwana?,nina sanyata?,ai bani nace tayi kyautar ba,data sani ma auta din ta baiwa taci ta more,tunda na tabbata kudin uba nata ne,kirki kuma da kake maganarsa,ai ba zata gayawa aminatu kirki ba” ambatar sunan saiya hado da faduwar gabansa,wadda ta tilasta masa lumshe idanu yana furta
“La’ilaha illallah” zuciyarsa,tsahon wasu sakanni sanna ya bude idanun nasa,sai suka fada cikin na hajiya qarama,da yaga kamar tsareshi tayi da idanu tun dazun tanw kallonshi
“Ai wallahi Allah ya kyauta…..kuma duk nisan jifa qasa zai fado,kuma qauna nidai jidda ta samu soyayyata har abada,saidai ta wadanda ta rufewa idanu da wani hali wanda ni nasa shiga akayi kasuwa aka samoshi” daga haka ta miqe qafarta wadda da alama itace meyi mata ciwon,har tana shure ledar da mummyn ta batan,saika dauka da gayya tayi hakan.

Dai dai nan mai aikin ta dawo da abinci a shirye ta ajjiye gabansa,hajiya qarama tace
“Dauki wannan ledar ki shiga da ita ciki,idan abun kaiwa baka ne ki rabe muku keda jummai”godiya ta shiga jerawa hajiyan,sannan ta duqa ta dauka zata wuce da ita,a lokacin affan yayi sallama,dan hajiya qarama na qarshe wato autanta.

“Wannan ledar fa?”ya fada cikin salo na raha kamar yadda yanayinsa yake,yana amsar ledar daga hannun mai aikin saboda son ganin qwaqwaf,yana bude ledar ya bude idanu
“Hajjaju…..wannan lafiyayyen kilishin fa?” Fuska ta tsuke sosai,bata ko waiwaya ta dubeshi ba tace
“Daga inda ka aikeni,su sukace na kawo maka babana” ya fahimci kamar adan hasale take,saiya saki murmushi
“Allah ya huci zuciyar hajjwju” ya sanya hannu yana gutsirar kilishin ya jefa a bakinsa sannan ya bata ledar ta wuce shima ya qaraso inda suke zaune.

“The giant ya saraki” affan ya fada cikin salo na barkwanci,wanda ya sanya samir murmusawa,saiya miqa masa hannu,shima affan ya bashi hannun suka gaisa,sa’annan ya soma laluben wajen zama yana fadin
“Barka da warhaka yaya”
“Yauwa affan…..ya karatu?”
“Hmmmm….gashinan alhmdlh,yanata gasamu”ya amsa masa yana shafa qeyarsa zuwa wuyansa
“Ni yau ka ganni yaya ko cikakken abinci wallahi ban samu na zauna naci ba,yanzunma takaddun kawai na ajjiye na shigo nan” gyara zamanshi samir yayi sosai yana fadin
“Saika matso muci tare”ya bude murfin kwanim abincin yana ajiyeshi a gabansa,hakan ya baiwa affan damae matsowa yana cewa
“Kai amma fa na gode yaya daka bani damar cin abinci dakai” maganar affan ta sanya murmushi ya subucewa samir,idan ya biyewa affan abincinma bazai bari suci sosai ba,ya cika surutu kamar jawahir,shi yasa tasu tazo daya,wani lokaci har yakan tsokanesu da cewa zai musu baiko shida ita,zasu dace sosai,saboda yanayin surutunsu daya,saidai suyita dariya shi da ita,saboda su sam basa ganin surutun nasu da yake fada din,kawai dai qilan sabodashi bai bawa hira muhimmanci mai yawa cikin rayuwa da lokuttansa ba,yana selecting lokutan hira da abubuwan da sukafi muhimmanci ya ambata ne.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button