Sponsored Links
Hausa NovelsUncle Datti Hausa Novel

Uncle Datti 1-2

Sponsored Links

Page 1-2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

Yarinya ce y’ar kimmata shekara tara taci ado cikin English wear na gown an tufke mata kai da baby pink d’in ribbon mai kyau.
Ba wata fara bace cen amma ba laifi kakkyawa ce son kowa kin Wanda ya rasa, tana da dimple a kummatun ta da suke lotsawa a duk sanda take murmushi ko dariya hakan ba karamin kawata fuskan ta yake yi ba.
” Aunty aina!!!! Aunty aina ki bani chocolates d’in da uncle datti ya sayo min”, ta fad’a a lokacin da take nufar parlorn da mugun guru saboda har ga Allah tana mugun son chocolates hakan ya sa a kullum tazo gidan sai ta saka uncle Datti ya saya mata.
” Allah Khadija ba zan bayar ba, wai shin ba na hana ki shan zaki ba? ko zo kike yayi miki illah ne? ta fad’a a takaice tare da d’an had’e rai”.
“Eeeyyaaaa aunty na yi hakuri ki ban, yau d’aya kawai ki ban nashi daga yau ban k’arawa.
” Hmmmmm nana kenan ke yarinya ce ba za ki fahimci illan shan zak’i ma mace ba but tunda kin ce haka mik’a min eye glass d’ina na saka sai muje na d’auko miki”, domin Rana mugun fama da chronic ciwon ido bata gani sai da glass medicated, idan babu wuri duhu baka kirin yake koma mata hatta tafukan hannayen ta ma.
Kamar dama jira take yi ta d’au glass d’in a kan glass table ta mik’a mata ta karb’a ta kafa daga nan ta jawo hannun k’anwar ta suka shige d’aki tace ta tsaya a waje dan kar taga mab’oyan.
Guda d’aya ta fito dashi ta mik’a mata ungo wannan tafi kar ki kuma damuna.
Maimakon ta k’arb’a ta turo baki ta tare da sakin kukan shagwab’a wai ita baza ta k’arb’a ba sai an kara mata.
Jin kukan nata yayi yawa uncle Datti ya fito ranshi a b’ace, shi dai bai san me ya saka saffffff baya k’aunar b’acin ran baby angel ba balle kukan ta, a duk ran da ta saki kukan rigima bai da tsukuni a zuciyan shi har sai ya biya mata bukatunta tayi shiru.
So tari idan yana rawar k’afa a kan Nana Aunty Aina har mamaki take wai shin tsakanin ita da Nana was yake aure? Me yasa baya tarairayanta kamar yanda yake yi mata? ko dai Uncle Datti son Nana yake, duk wannan tunanin su suke mata yawo a kwakwalwar ta ba tare da ta samo amsar su ba.

Gani tayi ya nufo wurin Nana ba duk ya gigice ya susuce kamar wani wawa yana lallashin ta” shiru, yi shiru my angel fad’a min me ke damun ki, wa ya tab’o min ke”, ya jero mata tambayoyi a tare.
Baki wangalau aunty Aina ta bud’e tana kallon shi da mugun mamaki, abunda ya dad’a bata mamaki ji tayi Nana ta kuma rushewa da kuka har tana shid’ewa ala dole ita tayi fushi shi kam sai ma gabaki daya ya fita a hayyacin shi ya rasa ina zai saka kanshi yaji dad’i.
Zumb’uro baki tayi cikin shagwab’ar ta tace “Uncle chocolate zan sha, aunty Aina tak’i ta k’ara min”, ta fad’a cikin kuka tana langab’e kai.
” To to to yi shiru zo muje na saya miki, fita suka yi daga gidan shi da Nana suka bar Aina a tsaye jigum kamar gawa tana mamakin Datti.
Da taga abun ba mai k’arewa bane ta fad’a kitchen ta dafa had’add’iyar shinkafa jelof wanda yaji kayan had’i, ga wani uban k’amshi da ya gama gauraye kitchen d’in, tana gamawa ta fad’a d’aki ta rage kayan jikin ta kana ta fad’a bathroom. Tana gamawa ta fito ta shirya tsaffff cikin leshi mai ruwan toka d’inkin riga da zani. Kallo d’aya zaka yi mata ka san cewa ta had’u ba k’arya domin kyaun ba daga kayan jikin ta bane daga itan ce, cuz she is a kind of beautiful.
Parlour ta koma ta zauna shiru- shiru babu su babu alamar su har aka fara k’iran sallar Magrib, tayi alwala ta gabatar da sallar ta, tana idar da sallar kenan sai taji sallamar Datti a d’akin ta, ta amsa tare da juyowa sai ganin Aina tayi da kaya niki-niki a laida ta tare ta da ido tana kallon ta”.
“Heeeee madam wannan kallon na mene ne?, Datti ya fad’a yana tapping d’inta da hannu.”
Ta d’an had’e rai tana kallon shi haba dear d’ina for how long zan fad’a maka cewa ka rage saya wa yarinyar nan kayan zak’i? You now it ba sai na fad’a maka dalilina ba sanin kanka ne cewa akwai mai ciwon Suger a family d’in mu and ance ana gadon ciwon ko ka manta ne”.
Come on wife……., ya fad’a tare da jan maganar, i know ina sane ban manta ba sanin kanki ne nima ba zan so abunda zai cutar da ita, ciwon suger bata kama yara under ages da zarar mutum ya doshi shekaru 40 a lokacin ne aka bata shawara da ta dinga kiyayewa.”
Amma duk da haka ka rage, kana shagwab’a yarinyar nan da yawa.
Murmushi yayi mata yana cewa” duk abun da nayi wa Nana ban fad’i ba jinin mu ce ita”.
Ganin yanda ta had’e rai ya san ya tab’o mutuniyar hakan yasa yace wa Nana ta je d’aki ta jira su, hakan kuwa aka yi bayan fitan ta ya rungumo abar shi zuwa jikin shi ya hau lallab’a da kalan soyayya har sai da ya tabbatar ta sauko.
Kasancewar shi ma’aikacin gomnati hakan yasa washe gari da safe ya shirya ya tafi Office dan akwai wani aiki a gaban shi da yake so ya kammala. Kwararren likitane asubitin Plateau Hoptil da ke garin jos, yana isowa ya tarar an kawo musu patient da za’ayi mata surgery breast d’inta wacce bayan gwaji aka tabbatar da tana d’auke da breast fibro domain”, haka suka shigar da patient d’in suka hau yi mata aiki, tun shigowan shi surgery room d’in sai wajen k’arfe uku kafin nan ya samo ya huta cuz aikin yau ba sauk’i mutane sunyi musu yawa”.
Bayan ya fito ne ya soma nema number d’in Aina a waya cikin sa’a ringing d’aya ta d’aga tare da yi sallama ya amsa mata”.
“Wife kin ji wajena shiru ko?
” ummmm”, ta amsa tana mai dad’a manna wayan a kunnen ta”.
” Baby angle d’ina fa it has been long to hear from her”.
“Tana room d’in ta she is busy playing with her teddy”, hmmmm wait kitso take mata”.
” Dariya mai sauti yayi kafin yace” baby angel kenan sarkin rigima any ways nima yanzun nan na kammala aikina yanzu ma haka gida na nufa, me zan taho muku da shi?”
“Komai muna da shi my man domin kuwa baka rage mu da komai ba”.
Tsintar kanshi yayi da jin dad’in maganar ta, Aina mace mai tattausan lafazi, ta san k’almar da zata yi amfani da shi dan ta faranta mishi.
Bayan sunyi sallama ya kashe way an shi daga nan ya shige mota bai zame ko ina ba sai family house d’in su ya tarar da kakar shi Hajiya Rahane wacce suke k’ira da tsohuwa tana kallo a talabijin tana yi tana karkad’a kai”.
Sallama yayi mata bata ji ba har ya zauna bata san da ma ya shigowa ba, tsinkayo muryar shi tayi yana cewa” tsohuwa kallo ake yi ne nake ta sallama baki ji ba?
Ta juyo a hankali tana kallon shi d’auke da murmushi a fuskanta” ai film d’in ne tayi dad’i da yawa, Allah idan ina kallo mai dad’i har ban so na daina”.
” Dariya yayi, ya mik’e ya d’auki goran ruwan faro ya b’alle murfin ya kafa a bakin ya hau sha, tsohuwa kan ci gaba da kallon nata tayi cikin shauk’i tana murmushi. Sai da ya sha iya shan shi kafin ya cire goran a baki ya maida muffin ya rufe yana cewa” affff ashe ma bamu gaisa ba, ya gaishe ta ta amma ba tare da ta d’auke idanuwan ta akan TVn ba”.
Da yake daffffff take da ta gama kallon haka shima ya zauna jiran ta amma shi ba kallon yake ba, fito da waya ya shiga gallery yana watching hoton baby angel.
Bayan ta kammala ne ta tattara dukkan hankalin tace” Abubukar”, ya d’ago da sauri yana kallon ta da mamaki ji yayi ta k’ira sunan shi gasau babu sakayawa.
” Ya baka taho min da y’ar jikalle na ba,? Tana nan sai rigima take yi kin san halin Nana”.
“Y’ar neman nan ba ta samu kana biye ta ba dolle yayi, ni dai ban san ranar da zata yi hankali ba”.
” Tsohuwa kenan, dai-dai da rana d’aya bana k’aunar b’acin ran Nana shi yasa nake biye ma fitinar ta”.
Haka dai suke ta hira kusan rabin hiran akan Nana ya kare, bai wani dad’e ba yayi sallama da ita ya nufi b’angaren mum d’in shi ya gaida ta kafin nan ya shige sauran sauran b’angarorin ya gaishe su daga nan kuma ya nufi gida a ranshi yana jin tsananin kewan Nana na kama shi.

eedatou muje zuwa…………..

*๐Ÿ’ซSHINNING STARS WRITER’S ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡ *UNCLE DATTI*๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡.
JIKINA YAKE SO!
ยฉ
*eedatouโœ๐Ÿป*
”’Follow and โœ…ote me on Wattpad”’: *eedatou*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button