Sponsored Links
KyalKyalin Kauna Hausa Novel

KyalKyalin Kauna 60

Sponsored Links

Kulle hannun yayi da kyallen yafara kokarin tureta ahankali yace “cikani lemme get first aid box” sosai take kuka ajikinshi tamakemai wuya, rasa yanda zaiyi vasa yashiga tafiya da ita zuwa wajen wani drawer yajawo yaciro first aid box fess ya gyara hannun yaduba ganin luckily cut din bai samu vein ba yasa yasa bandage yarufe yanajin yanda takankameshi har lokacin kuka take ahankali yace “saken muje falo” makemai kafada tavi cikin kuka tace “guduwa zaka sakeyi, wih kasake barina saina kashe kaina”
shi
baimasan mezaiyi ba, tafiya yashigayi suka fito tana manne dashi zuwa cikin dakin bakin kujera yayi da ita yazauna itama tazauna tana rungume dashi tana kuka har lokacin tana sumbatu. “| love you Pablo, duk randa narasaka bazan iya rayuwa ba, kaine komi nawa, I can’t stand your hate, bazan iya jure ka kini ba koka tsaneni, Pablo kasan banda kowa saikai you are my only family aduniyan nan, idan ka kini ina zansa kaina? Ba gwara na mutu ba? Our lives has always been you and me wake kokarin rabamu yanzu? Mubar Nigeria to, u can choose any country muyi relocating zuwa wajen kaji” lumshe idanu kawai Maheer yayi duniya tamai zafi baitaba sanin zai sami kanshi a irin this situation ba on one hand is Yasmeen, his wife dayake balain so on the other hand is this woman, he can’t abandon her tanada ciwon zuciva gashi kaman ma yanzu harda tabin hankali, yaya zaiyi? Ya tambayi kanshi, yakaita
US aduba ta ne but tayaya zai iya that long distance tafiya yabar Yasmeen dan at this point baijin zaima ya tafiya nan da wani state a Nigeria babu matarshi tareda shi ba he can’t, but how is he going to handle Hajiya now? He can’t leave her like this koba komi she helped him, is because of her his brother is a doctor today, is because of her yay karatu, wani tunani ne yazo ranshi dasauri ya runtse idanunshi, yanajin yanda take kuka ajikinshi, shi yakasa lallashinta, yakasa magana yakasa komi yanadaijin yanda ta kwakume shi kaman zata koma cikinshi tana kuka sosai yana zaune kaman gunki ko hannunshi bai daga yasa abayanta ba.
2 dayace zaizo yadauketa yasa Yasmeen tafito amman bata ganshi ba har parking space saida taje wayanta taciro tai dialing number shi amman baya shiga hakan yasa takoma tazauna kan wani benci karkashin kujera dakenan gaban parking space din sabida ko yazo vaganta dan yanzu sun shiga wani lecture kotaje aji bazaa barta
tashiga
ba.
Jin wayan yahau ringing dasauri taciro daga jaka tadauka shine gain wata bakuwar number yasa ta amsa takai junnenta muryan Ya Sa’ a taji tace
“kinsan kwana nawa nayi ina kiran wayanki bata shiga yanzu ma tunanin kiran Ammi nayi shine take gayamin an sace wayanki ashe amman barita turamin number wayanda Ya Maher yabaki, ke yakike ya amarci?” Bin inda take
Yasmeen tayi dakallo akunyace tace/
“py lau”
Sa’a tace
“Yasmeen kinsan nifa nadauka na
mutu ne ranan, gashi ni kinsan ba’a kwanan mini ba Faisal zai kasheni wh kaman a gudu nadawo gida kullum ana abu daya” wani kalan kunya Yasmeen taji tama kasa magana dan dariya Sa’a tayi tace
“munafika kin shiru ni nasan kinma fini shan wahala dan yanda Ya
Maheer ke kallonki dinnan kaman yaga abinci, gashi da tsayi daga gani yacimiki kaniwa” dan murmushi Yasmeen tayi kafin ahankali tace “Ya Sa’a dama wai haka akejin zafi konine banda lafiya” dasauri Sa’a tace
“haka akejin zafi
amman kika daure akayi aka gama ranan shikenan, ni gashinan harna soma sabawa nadainajin zafi yanzu sai dadi dan kinsan bai dagamin kafaba kwata kwata tunda aka kaini, Yasmeen n yanzu nono nane ma yafi ciwo wai maza kigansu manya dasu suna auranka saisu fara abu kaman jarirai” akunyace Yasmeen tace
“ni Ya Sa’a kidaina magana haka kunya nakeji” tsaki Sa’a taja, tace “Yasmeen kenan munafukan yarinya, keda kinma fini nono nasan sunajin jiki wajen Ya Maheer” katse wayan Yasmeen tavi dasauri akunyace tana tuna yanda yau tatashi dasafe taganshi dasauri tasauke kanta kaman yana ganinta, tana zaune awajen har aka kira la’asar tashi tayi taje mosque tai salla tasake dawowa takira number shi still baya shiga wasa wasa har 6, takuma kasa tafiya batason tabatamai rai gashi wh batasan sunan anguwan da aka kaita ba, ranan da aka kaita tana kuka bama ta kalli hanya ba, yau dasuka fito hankalinta Sam baya kan titi, gain magrib yayi vasa tasake dialing number shi still baya shiga, tashi tayi taje tai magrib tana tunani toko tatafi gidansu ne amman Baba tasa shi zai iya kaida abin babban issue bakuma abin takira Ammi ta tambayeta sunan anguwan ba itama zatamata tambaya maybe kuma Baba nagida yaji, gain 8 na neman yi ga school sai one one take ganin dalibai yasa tashiga contact nashi gain number dayay saving da Yaya Hamad vasa tai dialing ringin daya yadaga dan yadauka Maheer ne yace
“ya akayi?” Daurewa Yasmeen tayi ta rike kukan datakeji anatse like a smart girl tace “Ya Hamad nine dan Allah ya sunan anguwan mu dama ina school ne inaso nadawo gida”? Dan shiru taji Hamad yayi saikuma chan yace “ina mijinki”? Ko kadan bataso tanunamai wani abu dasauri tace
“wayanshi baya shiga maybe vana inda ba network ne” shiru Hamad yasakeyi, kafin yace
“kina ina yanzu?” Ahankali tace “parking space namu ina zaune kan kujera” anatse yace “tashi kije mosque ganinan zuwa dare yayi is not good ki dawo gida dakanki” gyadamai kai tayi tacire wayan daga kunnenta ta tashi tafara tafiya zuwa mosque, ko, kadan batason tama Maheer mummunan zato tun farko data sanshi bata mai kallon abinda taga yanayi ba da sana’an dataga vanavi all she sees was a good person mai tausayi dakuma good heart, tasan cewa rayuwa ne yasa yake ayanda yake is just circumstance, and she really wants to change him to a better person, babu sallan dazatayi dabatamai addu’a sabida tasan yanzu tana sonshi she loves him and tanason ya shiryu, he told her yana sonta and ta yarda dan she felt it ajikinshi da zuciyanshi cus Maheer is someone da jikinshi and actions dinshi basa karya ta yanda tasan he was a good man kenan tun lokacin dayay kidnapping nata bata bakinshi ba dan he claims he’s a bad person.
So inhar dakanshi yace zai dawo yadauketa by 2 baizoba tasan akwai dalili koma ina yake May he be safe Allah yakare shi daga aikata ayyukan zunubi tafadi ahankali kafin tazauna kan dakalin
masallacin bangaren mata taciro wayanta tashiga text message kan numbershi tashiga typing.
“Ya Maheer…….
ta tsaya tana tunanin abinda
zata rubuta spelling din data iya da kyau kafin tacigaba da typing.
“Aaa u oo k”?
Saikuma tagoge dasauri tana tuna spelling na are danta haddace
“Ya Maheer are u ooo k? Tak kia”
Ta aika sakon tareda maida wayan jaka tazauna jin ana kiran isha’i yasa tashiga masallaci tai salla tana idarwa wayanta na ringing tadauka Hamad yace “ina gaban mosque” fitowa tayi akunyace ta gaidashi ya amsa yadanyi murmushi tashiga motan suka tafi yana tambayanta kan school harsukakai gida, har gaban flat nata vakaita yabude mata kofa da key dake wajenshi tashiga shikuma yawuce side dinsu. Wasa wasa har one nadare Yasmeen takasa bacci any motsi dataji har addu’ a take taganshi batason tai kuka amman saida tai kuka badan komiba saidan yanda shi bai kirata ba kuma kodan fada mata zashi aikin daya saba bai fada mata ba, bata taba sanin haka soyayya yake ba idan kanason mutum baka ganshi ba baka natsuwa, dazaran ta kwanta tajuya ga gadonta dake kamshin shi gabaki daya gain baccin yaki zuwa yasa ta tashi zaune tamike tsaye bayi tawuce ta tsaya gaban mirror tashare hawayen daya zubomata takunna tap zatai alwala saikawai tafashe da kuka sosai tana bude baki how could she fall for Maheer maisa take manta criminal ne why is she expecting so much from him? Why why why??? Why is she thinking normal aure tayi kaman nakowa bayan tasan circumstance na auren? Why is she thinking like this? Takai kusan minti biyar tana kuka tanama kanta fada akan tadaina sonshi tadaina damuwa dashi mutane irinsu Maheer bama susan meye so ba, so koya fadamata yana sonta baya nuna zai damu da ita ta iya hanashi yin rayuwanshi, alwala tayi tafito dadduma ta shimfida tai salla kusan gabaki dayan addu’an datayi Maheer tamawa kusan awa biyu tayi kan dadduma sannan takalli agogo hudu Saura yan mintuna wayan nata dake kan gado takalla, dudda bataso tamika hannunta tadauka kasawa tayi dake dialing number shi tayi ga mamakinta number yahau ringing.
Maheer da Hajiya bata barshi ba ko bayi zai shiga saita bishi ta tsaya agaban bakin kofan, tazaman mishi kaman maya yarasa vanda zaiyi da ita dan kallon mahaukaciya yake mata gashi taki bacci, yanzun nan yasamu tai bacci akan kujeran zare jikinshi yashigayi daga nata daidai wayanshi na vibrating wanda kawai jikinshi yaji yafadamai waye, awani kalan hankali kaman barawo yawuce yafita daga dakin tareda maido kofan yarufe karaf Hajiya tabude idanunta danta fara bacci amman vibration na wayanshi yatada ta, tashi tayi dasauri daidai Maheer yabude kofan dakinshi ahankali yashiga yamaida yarufe itakuma tafita ahankali tabishi danso take tasan wake kiranshi tanaso ta gasgata zarginta har gaban kofanshi takarasa tadaura kanta jikin kofan.
Zama Maheer yayi bakin gadonshi yaciro wayan daya gama ringing dasauri messege din
Yasmeen yafara gani dasauri yabude.
Maheer are

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button