Sponsored Links
Gidan Aunty Book 1Hausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 41-42

Sponsored Links

BOOK 1 📕

Page 41_42 💖

Karfe 11 na dare ya nufi part din dada ,lokacin ba kowa a cikin falon ko ina na wajan ya dau shiru, wani corridor ya nufa kusan tafiyar mintuna 2 kafun wasu kofofi su bayyana a wajan,kofar hagunsa yayi knocking ,kusan mintuna d’aya ba a amsa ba, kara knocking yayi nan ma shiru, juyawa yayi da niyar komawa wata kamilalliyar murya ta bashi izinin shigowa , a hankali ya tura kofar dakin ,babban falone a wajan me shegen kyau da haduwa,komai a cikin falon ya hadu iya haduwa, tsaye take cikin maroon din hijab dinta daya kara fito da kyawun fuskarta da alama sallah ta idar yanxu, murmushi ta sakar masa tana buda masa hannun,cikin takunsa na kullum ya karasa wajanta tare da rungumeta ba kowa bace face ZARMEEN wato kanwar abeey auta ga dada kuma .”mahma “ ya furta yana kallan kyakkyawar fuskarta,dungure masa kai tayi “babu wani mahma, se da ka ganni zakace mun wata mahma”, kunnuwansu ya rike “am sorry “dan tabe bakinta tayi “babu wani sorry da zan karba sai ka kawo mun daughter na ganta, tunda sai dai naji labarin auranka , ka kyauta son”, shiru yayi mata ba tare da yace mata komai ba” kama hannunsa tayi suka zauna kafun ta kallesa” yanxu son fadamun kana santa and ya kamanninta yake ” kallan aunty sa yayi na yan sakanni kalmar kana Santa na masa yawo arai “so!? Never, she’s too small for me”,ya furta cikin zuciyarsa ,kallansa aunty zarmeen tayi tana sakin murmushi” da alama dai ka fada santa da yawa tunda har ka kasa amsamun,gaskiya wannan daughter tawa ba karamun sa ‘a tayi ba and let’s go ,bari na nuna maka wani abu “ta kama hannunsa suna shiga wani daki , wasu designers din set din akwatunane acikin dakin milk colour masu shegen kyau, kallan mahma yayi alamaun karin bayani,murmushi mahma ta sakar masa “kayan legend daughter ne abeey yace a taho dasu sauran sai auntyn ka ta karaso gobe ,zauna se na bude maka” girgiza mata kai yayi “no need mahma” ta bude baki zatayi magana sha’aban yashigo dakin bakinsa dauke da sallama,tsayawa kallansu yayi kafin ya karaso cikin dakin “mahma yanxu kinga danki shine har kin fara mantawa dani” dan hararar sa tayi “ zaka shiga tsakanine “daga mata hannu yayi yana furta “toh mahma me kuke tattaunawa sannan wannan akwatunan na wanene “ budar bakin mama se cewa tayi “ka bari duk lokacin da ka kawo mun matarka kaima sai a dama dakai dan haka bamu waje “kyalkyalewa da dariya sha’aban yayi “Lalle Geee kana da farin Jini ,kowa kai yake so, basma ma sabida kai tazo gidannan Bawai gaishe da abeey ba kamar yanda ta fada, ga sauran yan matan gidan musamman wannan ne rawar kan”, wani shegen kallo king yabi sha’aban dashi kafun ya kalli mahma” good night mahma”murmushi mahma ta sakar masa “night too son”,kama hanyar fita yayi yana hararan sha’aban,cikin daga murya ya furta “ina gaishe da amarya”,Jan kunnansa mahma tayi,sai da ta bari king ya fita kafin ta furta “ka fita idona sha’aban”ouch ya furta yana kama hannun mahma din” mahma amma ba kya ganin king zai saki yarinyar nan d zaran ta dawo sense dinta,ko da ace yana santa mahma toh shi haryanzu ya kasa gane hakan,ya kamata kiyi wani abu akai”shiru tayi kamar me nasani kafun ta gyada masa kai “zan fara zuba masa ido tukunna” amma mahma basma fa kinsan ba dan kowa tazo gidan nan ba sai shi,gashi yana da mata”,gyada masa kai mahma tayi ,”wannan ba matsalata bane ,idan yace yana ra’ayin auranta fine, Inyace bayaso ai babu Wanda ya isa ya masa Auran dole ko” jinjina mata kai yayi alamar gamsuwa kafun su ci gaba da wata sabuwar hirar.

****tunda ya bar part din mahma zantukanta suke dawo masa ,”so!?? Din da tace shine abunda ya fi tsaya masa arai ga kayan lefe da suke shirin yi batare da sanin saba,yanxu shi yazaiyi ,dole yasan mafita tunkan abu ya kwabe masa Musamman idan small mom tazo gobe ,”ya Allah “ ya furta cikin ransa. Koda ya koma part dinsa be shiga dakin da take ba sabida hukuncin da ya Yankewa zuciyarsa dole ya nesan teta.hakan ce kuwa ta faru be shiga dakinta ba sai wani dakin sirrinsa da ya shiga , babu komai aciki sai na’urorin computers cike a wajan, d’aya daga cikin computers din ya nufa , a ciki ya hango yadda take bacci cikin kwanciyar hankali,abunda ya faru tun bayar fitansa ya duba, mamakine ya kara kamasa ya fuskanci duk lokacin da ya fita zai tarar an gyara ko ina , a tunaninsa masu aikine sai yau ya kara tabbatar da zarginsa , a nutse take yin sallarta,bayan ta idar karatun alkurani tayi cikin kira’a me dadi da natsuwa.mamakinsa be kare ba sai lokacin da ya ga ta gyara ko ina ,”Anya yarinyar nan ba aljana bace”. Kashe komai na wajan yayi tare da fita, lifter ya hau ya karasa 3rd floor dinsa , ko ina kamshin ac ne ke tashi kamar ba a amfani dashi, system dinsa ya dauka ,itama sosai yayi aiki akanta ya dade yana aiki akan system din har wajan karfe 3 na dare, har ya kwanta da niyar yin bacci kalaman mahma ya kara fado masa ransa “kana santa!?”, dogon tsaki yaja yana kokarin kawar da zancen amma ya ki barin sa , mikewa yayi tare da sakkowa dakin da take , har yanxu baccin ta take cikin kwanciyar hankali. Fuskarta ya zubawa idanuwansa, so innocent take baccinta kamar bata da damuwa, dan siririn gashinta da ya rufe mata ido ya sa dan yatsansa ya gyara mata kafun ya kara kallan kyakkyawan fuskarta,lips dinta da yayi ja sosai shine yafi daukan hankalinsa,daidaita fuskarsa yayi zuwa tata,sumbatan bakin nata yake kokarin yi ,kalmar “kana santa “ shine ya fado masa rai yayi saurin janye bakinsa kafun ya mike wajan gabaki d’aya yana rintse ido. Rana ta farko a rayuwarsa da ya kwanta akan sofa, sai faman rintse ido yake ko tunanin da yake ze bar zuciyarsa, ya dade yana kwance akan sofa din nan ,ganin kansa na sara masa ne yasa shi mikewa tare da komawa kan gadon, ko kallan inda take beyi a tunaninsa ko zai samu ya rintsa,abunda zuciyarsa ke kokarin kimtsa masa yake kokarin kaucewa,ganin yana kara wa kansa zafi ne yasa ya janyota jikinsa, a tare ko wannansu ya sauke a jiyar zuciya,a hankali kafin bacci ya d’auke shi.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

YOLA

9:30pm
Lokacin wani wahalallan bacci ne ya dauki mutanan dakin , TAHEER na gefe shima yana baccin wahalar, jiya yi kamar antabasa,a zabure ya mike yana kokarin kwace kansa, biyu daga Cikin mazajen da suke tare da sune suka rikeshi gagam bayan sun yi na saran bude kofar, idanuwansa kawai suka bar masa abude baya iya komai sai bin su da yake da kallo , komai suna yi ne cikin kulawa da taka tsantsan, sabida yadda gidan yake da wahalar futa amma duk da haka suka sha da kar, kamar sun san hanyar ko ina na wajan, sai da sukayi tafiya me Nisan gaske bayan sun fito dashi, wata mota da akai parking ne suka samu na sarar boyeshi a ciki kafun su juya da niyar tafiya, rike hannunsu yayi hawaye na zuba a cikin idanuwansa,a wahale ya furta “suwanene ku,me yasa kuka te makamun “, dayan guy din na kusa dashi ne ya kallesa amaimakon ya amsa masa tanbayarsa sai ya sakar masa yalwataccen murmushi”ka kula da kanka,wannan motar zata futar dakai daga Garin nan ,da zaran kafita kada ka sake ka kara waiwayota “ yana kammala zancan sa ya juya,kara rike hannun mutumin taheer yayi,”dan Allah ku fada mu suwanene ku”, dukansu murmushi suka sakar masa kafun Wanda ya rikewa hannun ya furta “SIF”,nagefansa kuma ya furta” LOLA”,basu kara bari ya furta wani abuba ,Wanda yace lola ya fesa masa wani farin abu a fuska take a Wajan bacci ya daukesa Daidai lokacin da motar nan ta soma tafiya, motar na barin wajan mutanan nan suka rikede tare da komawa macijansu.

🫧🫧🫧🫧🫧
➰➰➰➰➰
Washe gari da wani irin ciwon kai ya tashi, da gyar yake bude idanuwansa da suka kada ,wani irin jiri jiri ne yaji yana kokarin kamasa, yana tashi itama tahee ta farka kamar wacce tasan lokacin tashinsa, a hankali ta fara karanto adduar tashi daga bacci duk a kunnansa,be kulataba har yaje ya shirya cikin wata ash din jallabiya ne shegen sanshi, kansa har yanxu da lemar ruwa alamun wanka yayi,yau ko masallaci be jeba anan cikin dakin yayi sallarsa,a haka tahee ta fito itama sai kunbura baki take ganin yaki kulata,cikin nutsuwa tahee ta kabbara sallar ta , komai cikin nutsuwa da bin ka’ida take yinsa, duk abunda take yana kallo amma haryanxu be motsa daga inda yake ba,tana idar da sallar ta soma karatun alkurani cikin wata kira’a me shegen dadi, lumshe idanuwansa yayi dan jin dadin karatun yake har cikin zuciyar sa,sosai ya kasa kunne yana sauraran karatun da take, ta dau dogon lokaci tana karatun kafun ta idar,a hankali ta nufi inda yake tare da dora kanta a saman cinyarsa,cikin sanyin murya ta furta “dady”yi yayi kamar be jitaba, ko motsawa beyi ba daga yadda yake,kara kiran sunansa tayi,amaimakon ya amsa mata se cewa yayi” baki iya gaisuwa ba”da sauri ta furta “dady ina kwana” banza yayi da ita kusan mintuna d’aya kafun ya bude rinannun idanuwansa da suka kada,kwata kwata besan dogan magana yau,”tashi ki zaune”ya furta ba tare da ya kalletaba,da sauri kuwa ta mike zaune” zan tanbayeki , ki amsa mun kawai “, be jira ta basa amsa ba ya fara tanbayarta game da karatun alquranin da ta fara karantawa , wanene ya koya mata”,shiru tayi kamar me nazari kafun ta bude hannayenta biyu alamun itama bata sani, still tanbayar da yayi mata game da sallarta ,shima nan da hannunta ta nuna masa kafun ta furta “Nima ban sani ba”,tanbayoyi ya soma yi mata game da addininta, sosai kuwa take basa amsa ,shi kansa yayi mamakinta.a karo na farko daya furta “TAHEERA MOHAMMED”,be karasa kai zancen saba sabida yadda yaga tayi saurin dafe kanta,kallanta yayi kafun da kyar ya bude bakinsa “me ya faru” kanta kawai take nuna masa,shiru yayi yana binta da idanuwa tsawan mintuna daya kafun ya kara furta “taheera Mohammad “wannan karan kuka ta saka masa Sabida yadda taji kanta na mata zafi,tafukan hannayensa yasaka yana taba goshinta,babu zafi ko daya sai zufar da ta fara tsatstsafo mata,”ciwo yake miki” da sauri ta daga masa kanta, be ce mata komai ba sai mikar da ita da yayi tsaye ,direct kan bed din ya kwantar da ita, duk yadda take tsattsafo da gumi haka ta dage sai ta lulluba, be ce mata komai ba ya lullubetan,”karki bacci ina zuwa” ya furta mata a hankali,kanta kawai ta daga masa ,ya mike zai tafi kuma ta kara rike masa hannu,”dady kada ka tafi kaji”, lumshe mata eyes dinsa yayi “yanxu zan dawo” yana furta Hakan ya bar dakin , sunan da ya kira dazu take kokarin tunawa,ganin yadda kanta ya kara daukan zafine yasata rufe idanuwan nata, be jima ba ya dawo dauke da wani cup dan madaidaici, gefan fuskarta ya shafa , a firgice ta bude idanuwan ,Wanda ta ganine yasata binshi da idanuwa,mikar da ita zaune yayi kafun ya mika mata cup din hannunsa,”shanye ki ban kofin”,karban kofin tayi tare da kaishi Daidai bakinta, tana shakar kamshin sa tayi saurin janye bakinta, cikin marairaicewa tace “bana sha”kara hade ransa yayi kafin ya nuna mata cup din “kishanye kafun ran ki ya baci”kamar zatayi kuka tayi kurba d’aya ko hadiyeshi batayi ba ta fesoshi waje,sosai kuma ya batawa king farar rigar jikinsa,ta dago da niyar yi masa musu ganin yadda ya hade ransane yasata kara kafa kai cikin kofin, cikin sauri ta shanye abunda take ciki kafun ta mika masa kofin, ko minti d’aya batai ba ta mike daniyar barin wajan, hannunta na dama ya rike gagam tare da mayar da ita wajan da ta tashi,hannun ta fara kokarin kwace wa ,dayan hannun na toshe da bakinta, yana kula da ya na yinta sarai amma duk da hakan be sakar mata hannun ba sai ma janyota da yayi jikinsa,wani irin amaine yazo mata ba shiri ta fara kwarashi a jikinsa,lumshe idanuwansa yayi yana jin yadda take kwara bakikirin aman cikin fitar hayyaci,sai da ya bari ta gama kwarara aman kafun ya dagata a jikinsa gabaki dayanta ya nufi toilet da ita.

➰➰➰➰

Tunda suka watsa masa powder dinnan yake bacci cikin babbar motar da tayi kama da ta masu daukan kaya.tafiya ce me dogon zango tun suna tsayawa a hanya har suka dena ,cikin sharara gudu motar nan take tafiya har Garin Allah ya waye,har lokacin kuma taheer na cikin motar,cikin wani babban waje me cike da mutane suka tsayar da motar. Surutan mutanene ya farkar dashi,azabure ya bude idanuwansa ganin bakowa a Wajan sai tulun kaya yasashi fara rarraba idanuwansa,ga Duhun da ya toshe masa fuska baya gani, cikin fitar hayyaci ya fito daga cikin motar ba tare da kowa ya ankara dashi ba,cikin layi ya soma tafiya ,yana wuwwuce mutanan da ke babban wajan, ga tsakanin yunwar da ta haifar masa da jiri,ta fiya kawai yake baya kallan gabansa, gashi ko takalmi babu a kafarsa, Daidai wani babban titi ya soma ratsawa Kwata kwata baya ganin gabansa, motoci kuwa sai kauce masa suke, cikin sharara gudu wasu bakaken BMW suka shawo kwanar wajan ,ba tare da sun ankara dashi ba motar nan tayi sama dashi, ya fado ko motsi ba yayi, cikin sauri driver din motar ya fito,ganin baya motsine yasashi dora hannu aka ,”shikenan na zama gawa Nima”, tun kafin a tabbatar da mutuwar Wanda ya kade ya soma kuka, cikin Sauri wasu sojoji biyu suka fito daga cikin motar, cikin turanci suke tanbayar drivern yana basu amsa,a hankali aka bude bakar BMW din bayansu,da Sauri d’aya daga cikin sojan ya zo wajan kofar tare da sarawa na cikin motar, a hankali wata farar kafa ta zuro da kafarta,kafun ta fito da gangan jikin ta gabaki d’aya , fatabarakallahu ahsanin khalikin, kyakkyawa ce matar , gata fara sosai kana ganinta kaga cikakkiyar balarabiya , sanye take cikin jallabiya irin ta mata ash colour da ya rufe jikinta gabaki d’aya , a hankali ta soma ta ku sojojin nan suna take mata baya har ta karaso wajan da taheer yake a kwance,”ya salam “ta furta a hankali”kallansu tayi cikin bacin rai “me kuke jira ku sashi a car”cikin gaggawa kuwa daya daga cikin su ya dauki taheer zai sashi a motar su “on my car” ta kara firtawa,”mah” wani soja ya furta ,kallan da ta jefa masa ne yasashi sunkuyar da kai kafun ya shigar da taheer cikin motar ta,a guje suka bar wajan,Kai tsaye motocinnan basu tsaya a ko ina ba sai a cikin babban private hospital din cedarcrest hospital ltd dake sam mbakwe st ,ba bata lokaci a ka dauki taheer zuwa emergency. Wayar matar ne ya soma ringing cikin wakar larabci,dan guntun murmushi ta saki kafun ta dauki wayar cikin muryar larabci ta soma maganar da bana ganewa, bata dau dogon lokaciba ta kashe wayar.d’aya daga cikin sojojin ne ya nufeta ,cikin girmamawa ya furta “mah the flight is ready “,kamar bazata kulashiba sai kuma ta bude baki ta furta “cancel the flight “,sara mata kawai yayi kafun ya furta “yes mah”.

Kusan 40 minutes kafun fitilar emergency din ta dauke , kofar na budewa suka fito da taheer da akai w bandage a jiki ga abun oxygen a fuskarsa,wasu kwallar ne suka tarar wa matar ganin irin halin da dan karamin yaron ya fada , wani babban likita ne yazo wajan,cikin girmamawa ya gaisheta ,kafun ya nemi alfarmar ganinta, bin bayansa tayi har zuwa office dinsa, cikin harshen turanci ya kara gaisheta kafun ya soma tanbayarta menene alakarta da mara lapiyan,budar bakinta kawai ta furta “SON”,da mamaki ya kalleta ,har ya bude baki da niyar cewa wani abu ta dakatar dashi “straight to the point plx “,nunfashi ya dauke kafun ya soma magana “saka makon wahalhalun da yashane yasa shi samun bad injury a jikinsa,and gashi ana barinsa da yunwa dole yana bukatar abinci masu gida jiki,alamu sun nuna ana azabar dashi ta hanyar duka dan duk jikinsa shatin duka ne ganyu da ta bata masa ciki, buguwar da yayi ba sosai bace ,wahalar da yashane yasashi suma a lokacin amma Alhamdulillah yanxu an tseratar dashi and a matsayin ki na mahaifiyarsa yana bukatar kulawarki sosai ta uwa”,gabaki d’aya taji bayanin nasa amma mamakinta ina iyayan yaran ganin babu me bata amsane yasa ta kalli doctor din,”zan iya ganinsa “,gyada mata kai yayi kafun ya furta why not,a tare suka nufa wani special daki da aka kwantar da taheer .kwance yake yana bacci ga nunfashinsa dake futa a hankali,bin sa ta farayi da kallo ganin irin raunukan da yaji,sosai duk Wanda yaga taheer sai ya tausaya masa,”kamar zai kai Yaushe kafin ya farka “zai iya farkawa daga anjima zuwa gobe da safe “,jinjina masa kai tayi,doctor din na fita ta bada umarni a kawo abinci masu rai da lapiya na Gina jiki, ba bata lokaci kuwa suka cika umarninta, har a kai sallar azahar tana zaune a dakin da taheer yake lokaci zuwa lokaci tana amsa waya.

➰➰➰➰➰

Tunda ya shiga toilet din yayi sauri cire rigar jikinsa da ta bata,kallan yadda take lumshe ido yayi kafun ya karasa wajan ta hasken toilet din ya kashe gabaki d’aya kafun cikin rintse ido yacire mata rigar jikinta da ta baci itama , duk da ya kashe hasken futulan hakan be hanashi rintse ido ba,sai da ya tabbatar ya cire mata komai na jikinta kafin ya kara daukar ta suka shiga wata glass din kofa dake cikin toilet din tare da turo kofar,ya dau kusan mintuna 40 a cikin toilet din kafun ya kunna hasken toilet din, sanye yake cikin bathrobe din Riga fari tass da ita ,itama taheen Itace sanye a jikinta, har yanxu tana rike a hannunsa ,wannan karan daukar baby yayi mata kafun su fito daga cikin toilet din, a Wajan shiryawa ma ya dau dogon lokaci a wajan kafun su shirya ,wannan karan ma saida ya kulle idanuwansa kafun ya sa mata kayan,turaransa na imperial majesty da babu me amfani dashi ya fesa mata,kallan yadda yake taje kansa da ya taru tayi kafun cikin kwabe fuska ta cire scarf din da ya dauka mata akai,yalwataccen gashin kanta ya fito fili, itama nuna masa nata kan tayi “dady nima “,kallan kan yayi kafin kamar Wanda aka umartan ya tasoma taje matan,yana yi yana lumshe ido, cikin kankanin lokaci suka shirya ,kama hannunta yayi suka nufi kalansa bayan ya dora mata mayafi akai ,cikin kulawa dan sanyin murya kamar bashi ba ya furta” me ke damunki yanxu “murmurmur tayi da ido kafun ta furta “yunwa nake ji”,dun gure mata hai yayi ta kyalkyale da dariya kafun ya kama hannunta suna barin part din.

****Daddadan kamshin turaran sune ya karade ko ina na cikin falon dada, gabaki d’aya mutanan gidan yau sun hallara a babban dinning din part din dada, kowa kofa ya zubawa ido ta ganin ta inda zai bullo ,kowa da abunda ke ransa musamman su basma da tasha makeup,itama mahma da sha’aban sai faman zuba ido suke ,abeey ba kallan kofar yake, a hankali yayi sallama cikin muryarsa fuskarsa kwata kwata ba annuri,gabaki d’aya mutanan falon hada baki sukai wajan amsawa,basma har kusan kwarewa tayi sabida yadda ta zuba masa ido ko kunyar a ganta bataji, amrah na gefe sai faman hararar ta take ganin halin basman da tun bau ta soma zuwa gidan ba. Mikewa basma tayi cikin washe baki ta furta “welcome yaya king”,bata karasa zancan nata ba ganin hannunta rike da na tahee data buya a bayansa, kallansu ta tsaya yi cikin bacin rai , dada data hango tahee ce ta furta “yau naji saban muna furci,Menene na buya Kuma tahura”, kallanta mahma tayi”mahma wai ina take ni har ynxu bangan taba ,son ku karaso mana kukai muke jira”, ba tare da ya kula kowa ba ya janyo tahee dake faman boye jikinta ,hannunta guda daya ya kama tare da nufar dinning da suke, zuba mata ido mahma tayi banda Masha Allah babu abunda take furtawa cikin zuciyarta,tabbas Allah yayi halitta a nan ,a fili kuwa Masha Allah din ta kara maimaitawa tana bin tahee da kallo,kowa na falan zubawa taheera ido sukai ,sosai yau tayi kyau kamar ba ita ba, hatta fatar jikinta sai data kara washewa,”ummey da ammey ma sai faman murmushi suke saki, wajan dining din suka karaso har yanxu hannunsa na rike da nata,bayan ya gaishe da kowa na falon itama haka tayi kamar yadda taga yayi,cikin danne abunda yake taso mata basma taja masa kujerar kusa da ita kafun ta saki wani murmushin “yaya king ga waje Bismillah “,kallan second biyu kawai yayi mata kafun ya karasa wajan,ga mamakinta sai gani tayi ya kara Jan kujerar baya,a tunaninta shine zai zauna sai gani kawai tayi ya dora tahee awajan,tare da jan kujerar kusa da ita shima ya zauna,wani shegen murmushin mugunta sha’aban yasaki saura kadan dariya ta kwace masa ganin reaction din basma da wasu daga cikin yan matan gidan, hakan da yayi kuwa sosai ya saka wasu daga cikin yan gidan farin ciki musamman abeey da mahma da sai faman sakin murmushi suke, mikewa mahma tayi cikin sakin fuskta “yau ni zanyi serving amare ,me zakuce” d’auke kansa yayi daga kallan mahma ba tare da yace komai ba,ganin yadda take Kallan tahee ne yasa tayi saurin rike rigar king tana kokarin buya ,kallanta yayi kafun ya kalli mahma, fahimtar hakanne yasa ya kalli mahma” no need mahma”hararar sa mahma tayi “dan kai bata jin yunwa sai ita akace maka bataji”shiru kawai yayi ba tare da yace komai ba,da kanta mahma tayi serving din kowa na falan, basma da amrah ji suke kamar sukaiwa tahee duka,ita kuma tana rike da hannun rigarsa har yanxu,ganin kowa sun fara cin abincine bandasu yasa abeey ya kallesa, Daidai lokacin da shima king din yake dago fuskarsa,saurin janye fuskarsa yayi daga ta abeey ,kafun ya kalli tahee,itama mahma kallan taheen tayi “kici abincinki mana ko bashi kike soba”nan ma shiru taheen tayi, tana kallan king kamar wacce zatayi kuka,ta gefan ido ya dan kalleta kafun yasaka hannunsa ya debo farfesun kayan cikin dake faman tashin kamshi, Daidai bakinsa ya kai kamar Wanda zai ci sai kuma ya nufi bakin tahee ,da Sauri kuwa ta bude bakin nata, ba basma dake falan ba ,kowa na cikin falon dakatawa yayi dacin abincin dasu,ba Wanda be bawa mamaki ba,sha’aban baisan lokacin da ya furta “wow “ da karfi ba, mahma ma bakadan ba tayi farin cikin abinda king yayi ummey da ammey duk sun kuyar da kansu sukai cikin jin kunya, aunty kuwa ji tayi gabaki d’aya abincin ya fita ranta,su uncle 𝖘𝖆𝖑𝖊𝖊𝖒 ma duk murmushi kawai suke saki, kara tsuke fuskarsa king yayi jin alamun idanuwa akansa, a hankali ya dunga bata farfesun har saida ya tabbatar ta koshi kafun yayi kokarin mikewa, riko ta hannunsa tahee tayi yanxu ma kamar wacce zatayi kuka, da ido yayi mata alamun Menene,farfesun da ya bata ta kalla, ya dauka bata koshi bane yasashi komawa ya zauna ,spoon din da ya ajje take kokarin dauka, fahimtar abunda take kokarin yi yashashi saurin dauke spoon din”Lalle baki da lapiya “ya furta cikin zuciyarsa,kafun ya dauki farfesun ya kai bakin ta, girgiza masa kai tayi ,ajje spoon din yayi yana kokarin tashi a karo na biyu ,ganin ta kallesa tare da kallan spoon din ne yasashi fahimtar abunda take kokarin to , komawa yayi shima ya zauna kafin ya soma Shan ragowar farfesun da ya bata,sha’aban na gefe sai faman sakin murmushin mugunta yake musamman yadda yaga fuskar basma da saura kadan ta fashe, abeey sosai yayi farin cikin daga nin wannan ranar,tabbas ya kara yadda ita kadaice zata canza masa son dinsa, ummey ma murmushi kawai ta saki tana godewa Allah, ammey kuwa kunya ce ta Hanata dagowa,lokacin dada bata falon, mahma sai faman washe baki take, har aka kammala cin abincin kafin akoma falon dada, king da sha’aban basu zauna a falon ba suka fita, mahma kuwa ta katse ta tsare har saida tahee ta saki jikinta da ita, dada har tana mata tsiya ganin tayi saurin sabawa da mahma, ana gama cin abincin basma ta dauki wayar ta kamar zata tashi sama ta nufi masaukin ta tana danna number mahaifiyarta, itama mahma kama hannun tahee tayi ta nufi part dinta da ita, acewarta tun yanxu zata farayi wa yarta gyaran jiki, suna shiga kuwa wani abu ta dakko Cikin wani boil dan karami , me hade da kwakwa da dabino sai madarar da aka saka a ciki, cikin da bara mahma ta sa tahee Tasha,itama da taji dadin abun duka kuwa ta shanye kayanta, tana kammala sha kuwa mahma ta kara mata wani abu me kamar zuba cikin spoon ,shima tass tahee ta shanye kayanta. Gabaki d’aya yinin ranar tahee na Wajan, anan tayi sallah ta kafe ta tsare,a iya zaman da sukayi ta fara fahimtar halin tahee din, har lokacin kuwa king be dawo part din ba, suna hospital dinshi shida sha’aban kasan cewarsa shima kwararran likita, tun a mota sha’aban yake wa king dariyar shakiyanci, banza king yayi dashi kamar be san yanayi ba, cikin neman bala’I sha’aban ya kallesa kafun ya furta “MY GEE , MR ROMEO NA JULIET “.

Sorry 😞 for the late update 😞😞..

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Mss Lee 💖🙌
💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
(a heart touching love story)

Story & written
By
Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

PAID BOOK

Me bukatar complete din littafin gidan aunty ya tuntubeni ta wannan number 07041879581.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button