Dangina Book 2 Page 3
โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*~{{ MY FAMILY}}~ BOOK 2*
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{{UMMIEE ZARIA}}~*โ๐ผ
*Page 3.*
*AK d’an mai karfi, da Yusuf wase* kuwa kasancewar basu bar garin Kaduna da wuri ba hakan yasa basu samu damar shigowa cikin garin na Zaria ba sai gaban nin magariba,
Hakan nema kuma yasa koda suka iso basu samu damar shiga gidan na Hajiya ba sakamakon tsayawa gaisawa da matasan majalisar nasu da sukayi, wanda gaisuwan nasu shiya kai su har zuwa lokacin sallan Magriba to bayan an idar da Sallah din ma da kyar Mai Jama’a ya samu ya zare jikin shi a cikin jama’ar shi domin Yusuf dama suna fitowa daga masallaci ya wuce cikin gidan bai tsaya a wajen ba.
Kamar wanda magnet ke janshi haka ya samu kanshi da d’aukin zuwa sashen na Hajiya fatan shi dai kawai shine Allah yasa yarinyar nan itace abu na farko da zai fara yin tozali da ita a sashen,
Dan haka gudu gudu sauri sauri haka ya fad’a sashen shi turaren shi ya dauka ya k’ara feffesawa had’ida gyara zaman hulan shi kafin ya fito kai tsaye zuwa sashen na Hajiya cike da takun shi na mazajen dake ji da kansu,
Sai dai tun kafin ya k’arasa ya farajin hayaniyar Hajiya inda take cewa…
“Shike nan duniya ace mutum bazaici abincin kwarai ba rayuwa sai mace tasha tea da safe tea da rana tea da dare uwa dai wata jinin larabawa ko buzaye? Takwara indai baso kike ki k’arasa karmashewa ta yanda ubanki Almu zaiji dad’in fadamin maganar banza ba ai kamata yayi ki ceci kanki ki bani had’in kai ki dunga cin abunci masu gina jiki ta yarda ko mak’iyi yaganki yasan cewa zawarci ya amshe ki, ke bakiga mazan yanzun sun fison mace mai d’an mulmulallan jiki ba, ina amfanin mace ta zauna a rame uwa wata mai cutar yunwa, to nidai Allah ya sani gidan nan babu kishirwa bare ayi batun yunwa, so kike dai sai ubanki ya samu hanyar fad’amin maganar banza in ya ganki a bushe”
Murmushi ne ya subuce mishi a zuciyar shi yake cewa, kuji min tsohuwar nan fa, towa yace mata ni yar lukata nike so matata ta zama me?”
Mai makon yabi ta kofar falon sai ya juya akalar shi zuwa tacan baya yabi ta kofar kitchen, kamar yanda ko yayi tsammani a bud’e kofar take ba’a kulle ta da makulli kamar ko yaushe ba, dan haka ya bud’eta kai tsaye ya shige ciki.
Koda ya bullo cikin falon ta wajen dinning duk Sallamar da yake Hajiya da idon ta ya fure take tama meenal mita wacce ke zaune a kan kafet din dake tsakiyar falon manyan littafan tane na karatu kewaye da ita sai wani littafin dake yin jotting abubuwan da take tsinta a cikin littafan gefe d’aya kuma kofin shayi ne sai wani k’aramin bowl dake d’auke da dambun nama a cikin shi,
Lallai hausa sunyi gaskiya a yayin da sukace kubar rai da abunda yake so,
Domin ko hakance ta faru da Mai Jama’a tun bayan wanzuwar shi a cikin falon idanun shi basu sauka a ko inaba kai tsaye sai akan abar kaunar shi wacce daman ita din itace abunda yake da buri da fatan yin tozali da ita a daidai wannan lokacin,
Bai san yayi kewarta da yawa ba sai lokacin domin kuwa mai makon ya k’arasa inda suke duk da alamu sun nuna cewa sud’in basuji shigowar shi ba,
Ah ah kawai sai ya samu kanshi da gyara tsayuwar shi bayan daya jingina jikin shi da dinning din dake wajen kawai yaci gaba da bin fuskarta da kallo, bakin ta kawai yake kallo a yayinda take amsa ma Hajiya da cewa,
“Wai ke Hajiya waye ma yace miki yawan cin abunci shike sa mutum yin kiba ne? Kuma ni Allah ma ya sani cewa ko kadan bana son k’ibar da kike ambata min shi yasa ma yayo ni haka”
Daga kan bakin ta ya maida kallon shi zuwa kan dogon hancin ta dake nan d’an zuwat abunshi sai kuma kyawawan idanuwan ta dake kyalli akoda yaushe sakama kon ruwan dake cikin su hakan nema yasa abu kadan kesata kuka,
Kanta da babu d’an kwali sai wani d’an karamin hankaci da tayi amfani dashi ta dan daure kan dashi, saboda kasancewar hankacin karami ne kuma hakan yasa sai bai rufe mata gashin kan nata dake tsefe da kyau ba, sakamakon tea din da take Shane kuma zafin da tea din yake dashi hakan yasa zufa tsatsafowa a goshinta har ya zama silar da gashin dake kwance goshin ta kwanciya lambam a gaban goshin nata,
Mik’a tayi na alamar gajiya da zaman da tayi a wajen, mik’ar data nemi tarwatse mishi dan nutsuwar daya samu a yan kwanakin sakamakon bankaro k’irjinta da tayi zuwa gaba, gashi kuma dama ba wata rigar arziki bace a jikin nata half best ce a ciki sai kuma ta d’auko wata fibgilar shimi dake nan shara shara ta d’aura akan half best din wanda hakan bai wani rufe komai na daga ainihin surar jikin taba sai ma k’ara fitowa da surar nata yayi a zahiri, tasan cewa ba kasafai a yanzun hajiya ke samun bak’i mazaba tunda Mai Jama’a ya dena zama a garin sai bakin gidan suka ragu dan haka koda ta dawo gidan take zama a sashen na hajiya bata da shamaki shigar data keso shi takeyi sai dai yawancin lokuta in zata zauna a falon sai ta kullo kofar falon saboda gudun fad’owar wani cikin falon ba tareda ta kimtsa ba, yau kuma ganin dare ya fara kuma kofar falon yana rufe dan haka ta fito a bunta dan akwai abu mai mahimmanci da take son yin nazari akan shi, tun kafin magrib take zaune sakamakon fashin sallan da takeyi shi yasa koda lokacin sallan yayi bata tashi ba dan hatta da tea din da take sha Larai ta rok’a ta had’o ta kawo mata dan bata son abunda zai katse mata abunda takeyi din tafison sai ta kammala sai ta tashi gaba d’aya.
Runtse kwayar idanuwan shi yayi gam yana karanto kalmar innalillahi wa innah ilaihir raju’un, yasin inda ace yarinyar nan tasan da tsayuwar shi a wajen to da sai yace da gayya tayi mik’ar dan taga yana kallon ta, to amma ai koba kowa bai dace mace ta saki jiki tana wani gantsaro kirji da sunan mik’a ba๐ dan hakan d’aukar alhaki ne, kawai daga zuwan shi tana neman had’o mishi tarzoma,
*Ita ko Meenal* da fari kamshin turaren shi data dad’e da haddacewa ne ya fara sumame zuwa hancin ta, taso ta share dan a zaton ta kamshin ne kawai irin yanda wani lokacin idan mutum na zaune sai ya dunga jin kamshin abubuwa, sai dai kuma daga baya tsigar jikin tane taji yana tashi gaba d’aya sai takejin ta tsargi kanta kamar dai akwai idon dake yawo a jikin ta,
Dan haka sai ta d’ago kanta zuwa ga wajen Hajiya dan taga ko itace ke kallon ta, sai dai kuma sai ta iske gaba d’aya hankalin Hajiyar nakan shirin da ake gabatarwa ne a tv hannun ta kuma rik’e da carbin ta da take ja sakamakon azkar din da takeyi duk bayan idar da sallar magrib,
Da kad’an da kadan ta fara yawo da kwayar idonta a cikin falon har zuwa lokacin kuma tsigar jikinta bai bar tashi ba, kurrr idanuwan ta suka shige cikin nashi ga mamakin ta sai taga yana mata murmushi,
A zaton ta gizo ne yake mata dan haka sai tayi kokari wajen fusgar nata idanuwan daga cikin nashi ta runtse su da karfi sai dai kuma ilai dai koda ta bud’e shi din dai taci gaba da gani tsaye ya rungume hannayen shi a kirji yana sakar mata murmushin shi kai kayatarwa,
Baya baya tayi kafin ta bud’e bakin ta ta kwad’a ihu tana mai nuna inda yake da hannu, “fatalwa Hajiya! Fatalwa!! Wallahi fatalwa ne a falon nan”
Ta fad’a a yayin da ta isa wajen Hajiya da rarrafe ta wani irin cumuimuye kanta a cikin jikin Hajiyar,
“Fatalwar lafiya! Ke kin taba ganin fatalwa ne a gaske dan ubanki, kuma shi fatalwar duk ta rasa wajen zuwa sai falona da kullum yake cike da tsarki, dallah can ni cikani”
“Wallahi Allah da gaske nikeyi Hajiya ba gashi can a tsaye wajen dinning table dinki ba”
Kai duban ta zuwa wajen Hajiya tayi,
“Wannan ne fatalwar? Ikon Allah aiko da sai ince lalacewar zamani takai inda takai tafale da ado da kwalliya, kiga mutum a tsaye da kafafu biyu kice wani fatalwa, to waini uban wa ma na kashe da zaimin fatalwa? Yo ni ko shedanun aljannu ai sai sun shirya kafin su nufo inda nike balle wata tsiya can wai fatalwa,”
“Hajiya kalli fuskar shifa murmushi yakeyi wallahi”
“Ikon Allah, kai kuma dan mak’iyin uban mutum wani salon iya shegen ne wannan zaka fad’omin daki daga sama kamar wani dan aljannu? Kai tsaya ma ina fatan dai ba zuwa Kayi kaima ka amso shegiyar layan nan ta k’arya da ake cewa ana b’ata in an latsata ba?”
Dariya dukan su suka bashi,
Dan haka ya shiga kyakyatawa ba kakkautawa a yayinda yake karasowa wajen su,
Da kallo Meenal ta bishi domin dai wallahi tsayin rayuwarta ita bata tab’a ganin shi yana dariya harda kyakyatawa irin hakan ba, dan haka sai ta kure shi da kallo tana ganin yanda dariyar ya mishi kyau matuk’a sakamakon fararen hakoran shi da suke jere reras ga wushirya a tsakanin su sama da k’asa,
“Wai kema tsoron kikaji kamar wannan zabuwar jikar taki Hajjaju ta?”
“Allah ya sawake in tsaya jin tsoron wani abun halitta can da yawar ka”
Ta k’arasa fad’a tana aika mishi da harara.
“Ke kuma mai kikeyi a gidan nan?”
Ya tambaya a yayinda yakai zaune a kasan shima kamar yanda suma suke zaune,
“Oh wai meenal kake magana? Ai Allah yayi dai bana na kwato ta daga hannun wancan uban nata dake musu mulkin mallaka dan haka ta dawo hannuna, fata nike Allah ya fiddo mata da d’an dashe shen miji na nuna ma sa’a kwanan nan in wanke ta in kai mishi ita”
“Allah ya sawak’e ni bazan k’ara yin wani aure yanzun ba”
Meenal ta amsa dashi tana murgud’a baki.
“Ah ah wallahi karma Kiyi ka kanki mugun baki, aure ai ya zama dole, to so kike in saki a gaba inyi ta kallo bayan tako ina kinkai minzalin auren? Ina ce suma kawayen naki batun aurar dasu iyayen su sukeyi to so kike su suyi auren ke kuma kici gaba da zama a gaban mu salon Almu yasamu dalilin da zai kullaceni da kyau kinga kin bashi damar fad’amin magana kenan, zaice na baro ki daga gida na kawo nan kuma na d’aure miki gindi kinki aure,
Ah ah wallahi aure kam bari dai ki gani mijin dai ya fito”
“Hajiya tunda tace bata son auren ki barta mana har sanda ta shirya!”
“Kai matsa can bani waje, kai in ana maganar aure har ma kana da bakin tsomawa? Ka daiyi ta zama har mutuwa tazo tayi wuf da kai baka ajiye mana wanda zamu gani mu dunga fad’in cewa oh ga d’an Abdul Khareemu ba, kana nan kana sha shanci mtws duk dai ka gama tara kudin kana mutuwa kasafin su za’a mana muci kaji kaiko kana can an turbud’e a karkashin kasa”
“To wai dama ni Hajiya na taba zama dake ne nace miki bazanyi aure ba?”
“Oh to ka samu lafiyan kenan kwanan baya ai cemin kayi baka da lafiya yin aure saboda nika d’auka shashasha”
Shiru yayi wannan karan ba amsa,
Kuji hajiya fa tana neman tona mishi asiri a gaban yarinyar nan,
Sad’af sad’af Meenal ta mike a yayinda ta tuna cewa bafa kayan kwarai bane a jikin ta dan siket din dake jikin tama ko gwuiwar ta bai k’arasa ba dan haka ta bayan kujerun falon ta dunga bi harta fada cikin daya daga cikin dakunan dake nan k’asa dan bazai yuwu ta wuce zuwa sama da kayan dake jikinta ba alhalin shi din yana zaune a falon dan ba kadan ba duk take jin ta tsargu, haka kawai ya wani shigo ma mutane babu sallama.
Sabon gaisuwa sukayi shida Hajiyar bayan ta bace ma ganin shi, kafin suka d’aura da hira anan kuma Hajiya ta bud’e babin bashi labarin abubuwan da suka faru a cikin kwanakin da suka wuce da bashi a cikin gidan.
Suna kuma cikin hirar ne Yusuf ya shigo shida Musty wanda shima bai dad’e da isowa daga Abuja ba, dan haka suma suka zauna akaci gaba da hirar dasu har zuwa lokacin da akayi kiran sallan ishsha’i, hakan ne kuma yasa dole suka tsagaita da hirar da suke suka tashi da nufin zuwa su gabatar da nasu sallan, har sun kai bakin kofa Yusuf ya dawo baya,
“Hajiya yau fa ina da labari mai tsada da zan baki amma sai kin bani goron albishir kafin nan kuma yunwa nikeji๐”
Ya k’arasa fada yana narke fuska,