Dangina Book 2 Page 21
โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
*BOOK 2*
*PAGE 21*
Yau dai duk yanda Meenal taci burin su fita yawo hakan bai samu ba domin dai koda suka dawo gidan sun iske Mai Jama’a ya rigasu dawowa gida, ko bai fad’aba tasan da gayya yazo ya kafa ya tsare dan dai kawai karsu fitan tunda ya dawo daga sallan ishsha’i ko bakin gate bai k’ara lek’awa ba,
harma da wani ba Mansoor Umarnin cewa ya kulle gate d’in kawai shima ya wuce ciki wajen nashi iyalan saboda babu mai k’ara fita a gidan.
Da wuri ta mishi magana akan fitan da zasuyi, saboda kar yace yauma basu nemi izinin fitan ba amma sai wani cewa yayi ai dama abinci suke fita siya koh?,
Dan haka in dai dan abinci ne su shiga kitchen su girka duk abunda suke son ci ya riga ya tanadar musu da komai,
Duk yanda tasa shi a gaba da magiya k’iyawa yayi, sudai su Meelat tunda yace ba’a zuwa ko ina dama suka shafa ma kansu lafiya,
Hajiya najin Meenal d’in na ta faman magiya amma bata sa baki ba har saida shi d’in yabar wajen ya shige d’akin shi saboda yanda ta dameshi, sannan hajiya tace,
“Ina kuke batun zuwa yanzun da daren nan Meenal?”
“Hajiya wani shago muka gani a fitar da mukayi da dare jiya shine muke so muje dasu Meelat ko zamu samo abubuwan da zamuyi amfani dashi na biki”
“Shi shagon ba’a bud’e shi da rana ne?, lallai sai da darene zakuje siyayyar a garin da ba naku ba? Jiya mafa haka kuka fita kuma baku dawo da wuri ba, kunyi zaton ban sani bane tunda bakuji nace muku komai ba koh?
Ai Abdul ya kyauta min da yasa Mansoor ya kulle kofar sai inga ta inda zakubi ku fita!
In kuma ta katanga zaku ciccib’a ku fidda motar duk zan gani”
Simi simi suka shige kowacce ta kama abinda zai fishsheta Maryam da Meelat sune suka fad’a kitchen ita kuma sultana ciki ta shige ta tsalo wanka, dan ita hakan ma ya mata dai dai ta yanda abunda ta tsarayi zai tafi mata batare shamaki ba zata jefi tsuntsu biyune da dutse guda d’aya.
Wanka ta d’auka na d’aukar magana kamar wata mai shirin zuwa dinner riga da skirt na wani lafiyayyen bakin less d’in da aka mishi d’inkin daya zauna dai dai jikin ta ta sanya bayan ta fente fuskanta kuma saida ta b’ata lokaci wajen d’an d’asa d’auri kalar yan matan Abuja sannan ta rufe k’ofar wankan nata da turare mai d’ad’in shak’a kafin ta fito daga cikin d’akin da wayarta a hannu duk da kasancewar dare ne hakan bai hanata d’aukar kanta Selfie ba,tafa wanku tass wallahi
Kamshin turaren ta da kuma k’arar da takun takalmin ta ke badawa ne ya maido hankalin Hajiya da Meenal wad’anda ke zaune a falon suna d’an hira jefi jefi wajen ta,
cike da salon tafiyar ta mai d’aukar hankalin mai kallo ta k’araso inda suke kafin ta nemi waje a gefen Hajiya itama ta zauna,
“Hajiyar mu barka da war haka!” ta ambata a yayinda takai zaune.
Tun daga fitowar ta har zuwa sanda ta zauna da kallo kawai Hajiya ke binta, kasa shiru tayi har sai da ta mata tambaya cewa,
“Bak’o zakiyi ne hala naga daga dawowar ki kin wani shiga kin shawo wanka kamar wata mai shirin zuwa turakar miji ranar kwanan ta?”
K’aramin dariya Sultana tayi tana mai rufe idon ta da tafukan hannun ta alamun maganar na Hajiya ya bata kunya tace,
“Kai Hajiya sai masu mazane suke kwalliyar dare?
To su kuma matan da suke farautan wasu kuma fa? Nidai tarko nike d’anawa kuma ina fatan ganin ranar da tarkon nawa zai kama kurciya,
Nagode allah iyamu ne anan da kin sani a kunya Hajiyata ashe shike nan mu yan mata bamu da damar yin kwalliyar domin d’aukar hankalin abokin farautar namu kenan ko ya abun yake?”
Tab’e baki hajiya tayi kafin ta amsa mata da cewa,
“Zance na dai ya fito kenan tunda dai wani ne akayi kwalliyar domin shi!
To Allah yasa yana da rabo, amma ke ai in namiji zai soki ko bakiyi fente fente ba tsaf zaki kwaci zuciyar shi amma hakan ma ba laifin dama yan magana cewa sukayi ko kina da kyau ki k’ara da wanka,
ai gara kiyi kiyi kekam ki bada himma wallahi kiyi auren ki, karki biye ma halin yar uwarki gatanan ita da anyi magana sai tace wai ita ba yanzun zatayi aure ba, ko zaman me take nufin zata zauna tamin a cikin gida ni ban sani ba”
“Nidai Hajiya duk ba wannan ba,
Nidai dan Allah kimin kamun k’afa dan kece kawai nasan zakimin tsaye har in samu muradin raina”Sultana ta k’ara fad’a a marairaice tana kwabe fuska,
“To wani abun ne kuma yake faruwa hala?”
“Ah ah Hajiya bai farun ba tukun ina dai fatan faruwar hakan shi yasa nace gara kawai in sanar dake tun da wuri dan Wallahi ke k’adaice nasan zaki samar min da mafita cikin sauk’i”
“Ke nifa a rayuwa babu abunda ke b’atan rai irin mutum yayi ta kwane kwane bazaiyi magana dani kai tsaye ba,
To in baki fad’amin ba taya kike zaton zan gano”
K’asa sosai Sultana da duk’ar da kanta tana cigaba da murza yan yatsun ta data jerama zubuna guda uku, tace
“Hajiya dan Allah karkice bani da kunya, wallahi ba rashin kunya bane kawai nidai inajin tsoron kar wata tazo tamin shigar sauri ne idan nayi nauyin baki, kuma naga aiba laifi bane dan mace taga namiji tace tana son shi mai makon Inbar abun a cikin zuciyata ya zamar mini wani k’atoton cutar da zai iya Kaini gushewata bayan nasan idan na furta ana iya samar min da mafita”
Shiru tayi tana cigaba da mutsu mutsu dan gaba d’aya zuwa wannan lokacin tama kasa zaman da kyau kunyar k’aryar data aro ta d’aura ma kanta kuma ya hanata iya d’agowa ta kalli Hajiya duk da yanda takejin kallon da Hajiyar take mata,
Itama kuma Hajiyar k’in cewa komai tayi har sai da ita Sultanan ta gaji da mutsu mutsun ta aro ma kanta jarumta kafin taci gaba da cewa,
“Hajiya zaki taimaka min wajen samun abun da nike so?”
Bata jira hajiyar ta amsa ba taci gaba da cewa.
“Nidai ko bazan samu taimakon kowa ba zan fad’i abunda nike ji, Hajiya wallahi nidai ina son Ya Abdul Khareem Mai Jama’a dan Allah ki gabatar dani a wajen shi ko zan samu ya taimaka ya aureni! Wallahi ina son shi son da nike jin cewa bazan iya rayuwar aure dako wani mijiba inba shiba, dan Allah Hajiya kisa baki yanda zai saurareni su Meelat sun fad’amin duk yan matan dake nuna suna son shi basa sha ta dad’i amma ni kuma daga jiya zuwa yau son shi yamin kamun da bana jin zan iya jurewa ba tareda na bari ya gane ba shi yasa na fara tun karar ki dan ki tallafa min ko zan samu ya kulani”
Ta k’ara fad’a harda matso wasu k’ananun hawaye na munafunci,
Idan kunga yanda ta koma a gaban Hajiya dad’e duniya zakuyi zaton duk abubuwan da take fad’a gaskiyar su kenan bawai shirya su tayi ba, dan gaba d’aya ta juye ta koma kallar tausayi,
Meenal da tun d’azun kallo d’aya tama Sultanan ta d’auke kanta ta maida kan wayanta da suke chat da Ya Sa’eed wanda yake tambayan ta akan goben zata koma zaria ko sai anyi bakwai ne,
Jin wasu soki burutsun da tsinannun aljannun tsakar daren da suka hau kan sultanan suka sa ta hauka takeyi ne hakan ya sa Meenal d’in jan wani irin dogon tsakin daya fita da k’ara kamar zata cire harshenta,wani irin bak’in ciki mad’aukaki ne taji yana neman rufe ji da ganin ta, sai takeji kamar gizone maganganun na sultana ko kuma dai kila Sultanan ta shawo wasu kwayoyin da sukafi k’arfin kanta ne ko kuma dai aljannun gareta da gaske.
Bata tsaya ba Ya Sa’eed amsar tambayar shiba ta mik’e tsam daga inda take zaune jin surutan yana neman wuce abunda kwalwarta zata iya d’auka,
Zufa taji yana neman lullub’eta duk da ac da fankan da suke ta aiki a falon, d’aki ta shige kai tsaye dan tabbas tana buk’atar watsa ruwa masu sanyi a jikin ta k’ila ko zata dawo dai dai, Kai itafa sai takejin kamar ma dai aikin shedanu ne suka sa kunnuwan ta jiyo mata maganganun da ta tabbata k’ila ba haka Sultanan ta fad’e suba, inba haka ba taya ma sultanan da kwata kwata yaushe ma tasan Taubashin da har zata wani rikice da kukan cewa shi take so harda wani rok’on Hajiya akan ta taimaka mata, kai ina wannan ai sai dai aikin shed’anun wallahi,
Dan haka sai kawai ta maida hankali wajen karanto addu’o’in neman tsari daga shaid’anu kafin ta tub’e ta shiga makewayin ta yi kunna shower ta tsaya a k’arkashin ruwan sanyi tana ta k’ok’arin ganin ta ture tunanin nukan dake neman rikita mata kwalwa,
Ta dad’e a cikin bayin kafin tayi wanka ta fito,
Sai da ta fara tsane gashin kanta da ruwa yama jagab da towel duk da bawai ruwan jikin gashin nata ya tsane duka bane bata damuba tana fitowa gaban Mirror ta k’arasa tayi zaman shafan mai saida ta gama shafa man kafin ta taje gashin kan nata sama sama ta d’aure shi da jan ribom k’arami sannan ta mik’e ta k’arasa inda akwatin ta yake ta ciro wasu riga da wando masu fad’i sosai na bacci ta zura a jikinta kafinta fesa turare k’aramin hula ta d’aura akan nata,
Wayarta da tun shigowar ta cikin d’akin ta ajiye akan gadon ta d’auka dan yunwa takeji unin yau d’in bata wani saki jiki taci abinci a gidan rasuwa ba, tana ta tsumin sai sun fita sannan taci ma ranta abunda take so gashi shi wannan d’an iyan ya wani zo ya kejesu a cikin gida yasa an rufe mishi gate ta yanda bazasu samu damar fitan ba.
tunda dai yau Sarkin isa iko da mallaka mulkin nashi ya motsa yace bazasu fita ba to gara ta gama komai da wuri ta kwanta ta hutama ranta shi kuma idan yaso sai yaci kanshi,
Inyagan ta a arha yau ai gobe dai ba ganin ta zaiyi ba kuma daga ita har wancan mai shafar aljannun gidan zasu bari kowa yayi ta kanshi.
Koda ta fita wannan karan ba iya Hajiya da Sultana kad’ai bane a falon ah ah harda ma shi kanshi gogan shima ko kunya baiji ba ya wani dawo falon ya zauna cikin k’annin shi mata,
Tana fitowa falon bata kalli inda su Hajiya ke zaune ba kawai sai ta wani wuce su ta k’arasa inda shi gogan ke hakimce,
Tana zuwa bata jira komai ba ta mik’a hannun ta kamo nashi hannun ta kama janshi,
Ita nan a dole wai so take ta d’ago shi daga zaunen da yake ita nan ga yar mai k’arfi itama sai dai kuma duk yanda tasa k’arfin dan ta tadashi hakan ya gagara dan shima gogan zama yayi gingirim kamar wani gunki yana binta da kallo kuma baice mata komai ba,
“Kai Ya’ya wai dan Allah bazaka tashi ba kana ganin k’arfina sai k’arewa yakeyi๐ฃ” ta fad’a tana b’ata fuska kamar mai shirin fashewa da kuka.
“Me zan miki ne wai kike son damuna?”
“Kai yaya ka taso ka gani mana, ai kasan dai haka kawai bazan zo ince ka taso ba”
Mikewa yayi ita kuma taci gaba da jan hannun shi kamar wasu rak’umi da akala sai da suka gitta su Hajiya Sultana da magantu da cewa,
“Sister ina zaki kaishi kuma? yanzun nan fa na kirashi ya fito saboda muci abinci ke kad’aifa muke jira dama yanzun kuma kin fita kin janye shi kuna shirin komawa”
Sultana na saukewa Hajiya itama ta d’aura da cewa,
“Ah lallai kam, to da kika fito kike neman k’ara mai dashi cikin d’akin mai zai miki a ciki ne wai?”
“Uhmm nidai Hajiya ba ruwan ku ai takardun motana zamuje ya bani tunda gobe idan Allah ya kaimu idan muka fita da safe ba k’ara dawowa zamuyi ba,
To idan na manta ban k’arbi takardun ba kuma fa?
In ma abincin ne ku faraci kafin mu fito suma su Meelat ai naga basu gama ba balle su fito in kuma kunajin yunwa ne ai sai ku faraci ku biyun,”
Kamar da gayya haka tajashi fuuuu suka wuce ita ta bud’e kofar d’akin shi ta fara turashi ciki kafin tabi shi a baya,
Suna shiga ta nemi gefen gadon shi ta zauna tana wani irin cika tana batsewa,
Sai faman girgiza kafarta data d’aura d’aya kan d’aya takeyi, shiko tsayuwa yaci gaba dayi a gaban ta, shi bai zauna ba kuma bai tanka mata ba, dan bai sani ba ko laifin hanasu fitan ne yasa ta kawo shi d’aki take neman tsare shi saiya fad’a mata dalilin shi na hanasu fitan,
“Kambala’i wallahi da gaske yarinyar nan bata da hankali lallai nema, wannan ma ai rashin sanin darajar kaine kawai daga ganin mutum…. ”
Kyacci tayi tama kasa k’arasa fad’ar me tayi niyyar cewa,
“Wai me ya sameki ne kuma?”
Ak ya tambaya ganin yanda take ta wani girgiza uwa wata mai shirin tada aljannu.
“Eh aima dole ka tambayeni mai yake faruwa,
Allah kuwa Taubashi ina fad’a maka inma asiri kake ma yan mata shi yasa da zarar sunyi ido biyu dakai suke kware maka gara ka ceci kanka ka karya asirin nan inba haka ba wallahi wata rana yan matan aljannu ne zasu fara bibiyar ka, haba dan Allah shikenan rayuwa kai da zarar kayi ido biyu da mace tun tafiya batayi nisa ba sai kaji zance yana neman canzawa”
“Mai yake faruwa ne nace?” Ya k’ara tambaya a karo na biyu,
“Ba kana kallo ba ita wancan bak’uwar dake kama da shafar aljannu to wallahi d’azun nan taje wajen Hajiya tana kuka take had’a Hajiyar da Allah da annabi akan tasa baki wai ita Sultanan ke son kafa,
Kuma harda cewa ma tayi wai inba kai ta aura ba bazata iya rayuwa dako wani mijin ba,
kaji fa, to tunda yanzun aka fara samun wacce ta iya tunkarar Hajiya gaba da gaba ba kunya bare tsoron Allah tace mata sonka take to tabbas zuwa gaba ma sai an samu wacce zatace kunyi auren sirri”
Da kallo yake ta binta jama’a ga abun dariya amma kuma ba halin darawan, juyawa yayi ya maida kanshi gefe a yayinda dariyar ta nemi kubuce mishi karamin dariya mara sauti yayi yana rufe bakin shi da hannu kafin ya juyo inda take ya k’arasa ya zauna,
“Wai ita wacece Sultanar?”
“Yarinyar Yayan Baba Auta cefa, a abuja suke zaune nima ba wani sanin ta nayi ba sai wannan zuwan da sukayi, waya sani ma ko lafiyar kwalwa ne bai isheta ba”
Ta fad’a tana tsatsare shi da ido tana jin me zaice kuma,
Ga mamaki ta wai sai gani tayi fuskar nan tashi dake kwana ta uni a d’aure tamau amma sai ya wani saki fuskar yana murmushin shi mai narkar da zuciyar mai kallo,
Giraren shi ya d’age kamar yanda ya saba indan zaiyi magana da ita yace,
“Ashe ma yar uwarki ce, shi yasa tun jiya dana ganta nima na kasa nutsuwar kamar yanda naga itama ta rikice taga yaro d’an sawalwalin yan mata,
To ashema abun zaizo da sauki tunda harta gani kuma ta yaba aini kuma babu wani zancen jan aji kawai kice mata na bada gari, ta turo manya kawai ayi batun sa rana dama nima na gaji da zaman tuzurancin nan haka, dama jira nike inji wata ta taya, bari ki gani inje in same su muyi magana baki da baki in a shirye take aini sharr wallahi kinga ko anan gidan saita fara zama kafin in kammala wancan koya kikace?”
Ya k’arasa fad’a yana kureta da kallo ganin yanda tayi tsaye kawai tana bin bakin shi dake motsi da kallo kamar wacce bata gane me yake cewa ba,
“Kaiii Wai kaima nan son nata kakeyi?๐”
Ta tambaya a shekek’e tana jiran ya bata amsa,
“To me zai hana bazan sota bayan ita dake mace ta kasa boye nata son da take min duk da irin kunyar da aka san mata dasu,
gata da kyanta masha Allah aini ban san duk wancan zazzafan gayun data d’auka dan ni tayi ba da tuni na yaba,
Amma kinga d’an bawan allah sai komawa gefe mayi Ina Satan kallon ta”
Fuuuu ta mik’e bayan ta cika bakinta da iska tana shirin ficewa daga cikin d’akin ya rik’o kafadunta ya dawo da ita cikin d’akin,
Baya ta juya mishi tana kunkuni take cewa,
“Ni ka kyaleni inyi tafiya ta, badai Sultana kake soba kaje ai sai kuyi ta soyayyar ku can in kunga dama ma kuna iya konewa ni ba ruwa na”
Juyo da ita yayi ita kuma sai kokarin kwacewa take ya hanata damar hakan,
“Kishi Taubashiya?
Fad’amin kishina kikeyi ne?”
“Allah ya kyauta to akan me zanyi wani kishin ka, bayan kai ba mijina ba komai ba”
“Kishina kikeyi Meenal ko ki yarda ko karki yarda”
“Ni bana wani kishin ka kawai dai ina fad’a maka gaskiya ne”
Ta fad’a tana murgud’a baki batareda ta dena jijjige jijjigen jikin da takeyi daga tsayen ba,
“Kina son kiji gaskiyar abunda yake cikin zuciyata Meenal?”
“Akwai wani gaskiyar ne bayan wanda ka furta yanzun cewar kana son Sultana?”
Itama ta maida mishi da tambaya tana kauda kai gefe,
“Akwai Meenal!
Akwai gaskiyar dana dad’e ina shakkar fad’a miki ita,
Gaskiyar da aduk sanda mayi yunk’urin furta miki sai zuciyata tayi nauyi sai kuma inga kin min kwarjini ta yanda nake rasa kwarin gwuiwata a gaban ki,”
Zagayawa yayi zuwa gefen data juya fuskarta yakai kafafuwar shi k’asa yana mai kamo tafukan hannayen ta cikin nashi,
“Meenal ina son ki yarda da duk wata kalmar da zakiji ta fito daga bakina a yanzun zuwa cikin kunnen ki,
Domin sakon dake d’auke cikin zuciyata ne nike son isar ma taki zuciyar,
Ke ba k’aramar yarinyar da nayi ta ririta soyayyar ta a shekarun baya bane balle ince zaki kasa gane kalamai na,”
“Kara riko hannun ta yayi da kyau jin tana mutsu mutsu tana son zare hannun daga rikon daya mata,
“Ina sonki Meenal,
Ina matuk’ar kaunar, ina so ki sani cewa da kaunarki nike kwana a cikin k’irjina haka kuma da ita nike tashi,
Ita wancan yarinyar cewa tayi bazata iya rayuwa da wani namijin ba sai nikoh?
To ki sani cewa ni kuma bazan iya kasancewa a raye da cikakkiyar lafiya aduk sanda na k’ara rasaki a karo na biyu a cikin wannan duniyar ba,”
Sakin hannunta guda d’aya yayi sai ya d’aura duka hannayen nashi biyu akan hannun ta na dama,
Sai da yakai hannun nata kan lab’b’anshi ya sakar mata wani kalar kiss mai tsotse jinin jiki ba tareda ya saki hannun ba duk da yanda yake ganin jikin ta na d’aukar karkarwa, yaci gaba da cewa,
“Ina son ki Meenal wallahi ina son ki sona gaskiya da gaskiya bawai so na wasa ba, ki taimaka ki amshi tayin soyayya ta ki kuma bani dama ni kuma in gabatar da kaina a wajen iyayen mu su aura minke in tashi daga matakin tuzurun da kika dad’e kina kirana zuwa mijin auren ki.
Misalin k’arfe 8 da mintoci Salman ya iso kofar gidan AK domin yau bai samu damar zama a can gidan rasuwar ba gashi kuma yana ta cema Meenal d’in zai zo Allah baiyi ba kuma yasan gobe idan har suka koma Zaria to wuyan gani zata mishi,
Bai manta kwatancen da Meelat ta mishi ba dan haka koda zai taso bai kirata a waya ba har saida ya iso kofar gidan ya nemi waje yayi parking.
Kiran wayanta da yayi,
Hakan yayi dai dai da lokacin da AK yake durk’ushe a gaban ta yana koro mata kalaman da suke tsotse mata ruwan jiki,
Da kyar ta samu ta sanya hannun ta guda da yake free ya zaro wayar daga aljuhun wandon jikin ta jikinta na karkarwa.
No editing ๐ฅณ
*Ummiee ce*โ๐ผ