Dabi’ar Zuciya 9
cikin nutsuwar data zame masa jiki,kuma dabi’a yake tuqi,hankalinsa da kunnensa yana kan redion jikin motar daya kunna yana sauraren labaran safiya dake fita tar kamar yana wajen,yayin da wani sashe na hankalinsa ke jefo masa tunani iri daban daban kadan kadan,ciki harda sauyawar dabi’un qanwarsa,duk da cewa dama can halinta daban dana jawahir,ba zakayi tunanin ciki daya suka fito ba.
tafiyar minti kusan arba’in babu wani abu ta sadashi da inda kamfanin nashi yake,wato rukunin ma’aikatun dake sharada industrial area,ya sake rage gudun motar sosai,yana gangarawa sannu a hankali kan kwaltar dake shimfide tsakiyar hanyar,wanda hagunta da damanta dukka gine ginen masna’antu ne.
sa da yakai qarshe sannan ya karya wata kwana ya sake shiga wani titin,titine mai kyau,hakanan babu tarin gine gine barkatai kamae wanda ya baro,a hankali ya tsaya bakin wani babban katafaren gini,wanda yake dauke da bene hawa uku,iya ganinka gini ne daya amsa sunansa gini,wanda da gani ba tambaya kamfanine babba,wanda zaici jimillar ma’aikata masu dama,tako ina hasken gilasai da aka qawata benen me hawa biyu ne yake daukan hankali da idanun me kallo,yayin da manyan rubutun da akayi da manyan baqi can saman qololuwar ginin yake bada wani irin haske da kala me kyau,wannan shine M.S CONSTRUCTION COMPANY,kamfanin da ya shara yayi shuhura wajen karbar kwangilar gine ginen tituna,makarantu asibitoci ma’aikatu dama gidaje da suka amsa sunayensu,daga hannun mutane daban daban,kamfanine da ba’a taba samun kamarshi da yaro matashi ya mallakeshi ba,sannan kuma kamfanine da yayi suna ya danne sunan kowanne kamfani dake jin ya isa,hakan ya sanya yake da tarin abokan adawa da abokan takara bila adadin,saidai akwai wasu turaku dake riqe da kamfanin,wanda su wadancan sam basu san da wannan sirrin ba.
tsaiwar motarsa ba tare da ya dannan horn ba daya daga cikin securities dake tsare da katafariyar qofar shiga da fita ta kamfanin ya taso cikin gaggawa ya bude masa,yana rusunawa cikin girmamawa ya miqa gaisuwarsa,cike da kulawa ya amsa masa,sannan ya dage motar zuwa ciki.
kamar kowanne ma’aikaci,inda kowa yake aje abun hawansa nan shima ya aje tasa,ya kashe motar yana zare muqullin daga jiki,sannan ya waiwaya ya diba wayoyinsa tare da briefcase dinsa,ya dannan lock ya bude motar da niyyar zura qafarsa ya fita,saidai wata mota daga sako kai ta kuma faka da da tashi ya hanashi aiwatar da hakan,sai daya jira tsaiwar motar ta daidaita sannan ya bude ya fito,ba tare daya tsaya shaida waye a dayan motar ba.
saidai yana cikin rufe motar tasa yaji magana daga bayansa
“barka da warhaka yallabai,kaima yauka makara”duk da bai juya ba amma yasan wacece,saidai hakan ba hanashi juyawar ba,ya dubeta fuskarsa ba yabo ba fallasa
“Allah ko?,nima yau na dana,naji abinda kuke ji”saita fara rufe tata motar itama tana murmushi
“saboda mu sababbu ne ko?”kafadarsa ya daga yana watsa hannayensa
“eh kusan haka ne”
“shikenan,i surrender”
“good”ya furta yana dan qaramin murmushi,sannan cikin hanzari yayi gaba yana amsa gaisuwar datake miqa masa,saita rufa masa baya da sauri itama tana qoqarin dai daita tafiyarsun don kada ya kubce mata koya mata nisa,ta kuma fuskanci idan batayi da gasken gaske ba tsaf zai wuceta ne ya barta.
yana tafe yana amsa gaisuwar ma’aikatan cikin kamfanin cikin kulawa,gefe guda yana qoqarin handling surutunta daya soma damunsa,saidai ita bata kula da cewa ta fara damun nasa ba.
Suna gaban elevator,yana shirin sanys qafarsa wayarsa tayi qara,sai ya dakata yana zaro wayarsa,daya duba me kiran sai yaga PA dinsa ne, rejecting yayi kawai ya riqe wayar a hannunsa,don yasan wala’alla yace masa suna jiransa ne,don haka a gaggauce ya shige.
a ginin tsakiya babban dakin taron yake,wanda dukkan wani ma’aikaci daya kamata ace ya halacci wajen yana ciki.
tsaiwa yayi daga bakin qofar dakin taron,ya dubeta yana mata nuni data shiga,saita noqe tana kallonsa
“me yasa baka son jerawa dani ne saraki?”wayarsa yadan juya kadan a hannunsa,ba kasafai ya fiya son doguwar magana ba,amma saiya amsa mata
“tsarina ne hakan”ya amsa mata a taqaice,sannan ya daga kai ya dubeta,sosai idanuwansa suka yi mata nauyi,sarakin wani mutum ne na daban a zuciyarta da idanuwanta,shi kadai ne mutumin da zai dubeta da idanu tajinta rusuna,ta kuma sauka daga kan tsarinta cikin lokaci kadan
“ki wuce,saboda kinsan indai na rigaki shiga ba zaki shiga din ba,kin rasa zaman”wannan tsarinsa ne,shi yasa da wuya a sanya lokacin taro ya saba,yakanyi qoqari ya shiga kafin lokacin da aka sanya za’ayi din,ba yadda ta iya saitayi gaban cikin mutuwar jiki ta shige dakin taron.
kamar yadda ta zata a cike yake,kowa ya kama mazauninsa,a hankali ta shiga wulga idanuwanta,sai suka sauka akanta,FAUZA tana zaune kan kujerar dake daura data samir,saboda a tsarinsu iya matsayinka iya kusancin kujerarka da tashi.
Sam fauzan ma batasan me take ba,don ta tattara dukka hankalinta kacokam kan wayar dake hannunta,rubutu take da sauri da sauri,hasken wayar na bayyana qyallin faratan hannunta data qara dana kanti,ta matse sosai tayi kyau cikin suit na mata,siririn mayafi ne kadai ya nannade kanta zuwa wuyanta dashi,fuskarta tasha lite makeup,yayin data dora qafarta daya kan daya,hakan ya bayyana tsabar tsinin da takalmin qafarta keda shi,fauzan fara ce qal,saida bata da hanci bare idanuwa,amma haskenta ya santa duka wannan bai fiya bayyana ba,don tana da daukar ido,farar fatarta na haskata,tana kuma qara mata kyau duk kalar kayan data sanya.
fauza na daya daga cikin yaran abokan siyasar Prof,ta zabi aiki da kamfanin MS construction ne batare da kowa yasa dalilinta na hakan ba,shi kansa Prof din yayi mamaki sanda mahaifinta ke shigar da credentials dinta gareshi don a bata aiki,saboda kwata kwata ba abinda ta karanta kenan ba,ba fanninta bane,amma saboda girma da qimar da Prof yake ganinsa dashi ba ‘yar haka tsakaninsu,ya umarci samir ya bata vacancy.
qaramin tsaki taja,sannan ta lalubi kujera ta zauna,ta soma magana da mutanenta da suke wajen,batayi cikakken minti biyu ba samir ya bayyana wajen.
Idanuwanta na hango mata sanda fauza ta maida wayar jakarta,fuskarta ta wadata da murmushi,sannan ta miqe tsaye don girmamawa kamar yadda sauran mutanen dake dakin taron suka miqe gaba daya.
Sai daya tsaya gaban kujerarsa sannan ya baiwa kowa umarnin xama ba tare dashi ya zauna din ba,kusan tare suka zauna da sauran ma’aikatan,yana amsa gaisuwar da suke miqawa gareshi,saiya maida hankali yana duban kowa dake wajen,yana laluben wanda bai shigo ba cikin wadanda ya cancanci ace suna wajen,saidai kowa ya hallara,daga qarshe yana niyyar janye idanunsa suka fada kan fauza.
Murmushi tadan masa,saiya dan saki fuskarsa kadan yana janye idanunsa,mutum na hudu dake zaune daga hannun damansa ya duba
“salisu…..a bude mana da addu’a”ya fadi yana dora wayoyinsa saman teburin bayan ya kashesu,kamar yadda yake a dokarsa,ya hada tafukan hannayensa waje daya yana bin addu’ar da salisun ke kwararowa…………….
*BAYAN AWA UKU*
Zaune yake a qawataccen gidan abincin dake daura da kamfanin nasa,waje nw dake da wadatar iska mai kyau da kuma tsafta,uwa uba babu cinkuso a wajen,bayan samun hutun awa daya sanda ya kammala da taro kashi na farko,sai kuma ma’aikata kashi na biyu da zai zauna dasu,wanda kusan shine mafi muhimmanci ma a wajensa,already yasa an fitar da abincin da yazo dasi daga gida an bayar,a yanzun kuma yana buqatar wani abu da zai saka a cikinsa,idan suka kuma shiga a qalla yasan akwai kusa awa biyu kafin su kammala ganawar.
Gasashen kifi da chips yayi order yake kuma ci,a hankali cike da tarin nutsuwa yake kaiwa bakinsa da fork,gefe daya kuma fauza ce,wadda ganinsa zai fita ya sanya tace su fita tare mana,itama abincin zata je taci,baice mata uffan ba illa buda mata motar da yayi,ta kuwa bude gidan gaba ta shige,saidai tunda suka taho din har suka zo babu wanda ya cewa sa dan uwansa komai.
sanda aka bashi menu ya zaba abunda yake da buqatar ci saiya tura mata gabanta itama,baisan meta zaba ba,amma da aka kawo din,lemuka kawai yaga an aje mata da ruwa,duk da ya gani bai tanka ba,yaci gaba da cin nashi abincin,yana cin yana duba lokaci kada lokacin sallar ya qwace.
Ture farantin yayi yana goge bakinsa da tissue inda yakejin kamae ya baci,daya hannun nasa kuma yana yafito waiter din,ya saki abinda yake ya matso da hanzari zuwa wajen.
“gani yallabai”ya fada cikin girmamawa,hannu samir din ya sanya cikin aljihun wandonsa bayan ya tashi tsaye.
kudade ya ciro sannan ya miqa masa,ya saka hannu biyu kuwa ya karba ya soma lissafawa,zuwa sannan samir ya kwashe maqullin motarsa da wayoyinsa dake zube saman tebur din ya soma yin gaba
“yallabai,kuna da canji”
“ka riqe nabar maka” ya fada sounding seriusly yana sake dosar qofar fita
“hajiya a tayani godiya,Allah ya qara arziqi”ya fada yana duban fauza,wadda ta miqe tana rataya jakarta ganin zai wuce ba tare da yace da ita komai ba,bakin ma’aikacin kamar zai yage sabosa murna,don kusan albashinsa na watanni biyu ne suke cure dunqule a hannunsa a mazaunin kyauta.
sanda ta isa gaban motar har ya tadata,ta bude ta shiga ta gyara zamanta sosai,ya kunna motar sannan ya tasheta suka fice.
yanzunma kamar sanda suka zo,babu wanda ya tankwa dan uwansa komai,cike da qosawa fauza tadan muskuta kadan,tana jin wani bacin rai yana dan taba zuciyarta,bata taba kawo haka sarakin yake a ranta ba,duba da yadda ta sanshi da nuna kulawa ga duk mutumin da yake tare dashi,yanayinsa data karanta yasa zuciyarta ta bata tabbacin sauqi da saurin samun kansa,a yadda take da aji da kuma kyau kamar yadda ta saba ji daga bakunan mutane da dama wadanda batasan adadinsu ba,bata jin wannan tafiyar zata dore,tunaninsa daban nata daban,duk inda take tunanin mafita ce ko bullewa ce a tattare dashi,idan ta isa wajen saita taras a rufe yake ruf,samir din bashi da sauqi,karantarsa ta fahimci abune mai wahala,inda kake zatonsa daban,inda kuma zaka sameshi daban,batason taci gaba da aiwatar da abubuwan da zasu janyo mata zubewar ajinta,bata shiryawa hakan ba.
Batasan tayi tsaki a fili ba,har sai da sautinsa ya fito,ta waiwaya da sauri ta dubi sashen da samir yake,dai dai sanda shima ya waiwaya yana dubanta da lumsassun idanuwansa masu daukar hankali
“ar you okay?”ya fada kafin ya dauke idanuwansa daga kanta
“yeah”ta amsa murya qasa qasa tana jinjina kanta,daga hakan bai sake cewa da ita komai ba,yaci gaba da tuqinsa a nutse,har suka qaraso qofar company din.
A bakin gate taga ya ja burki,tadan dubeshi suka hada idanu,ta fahimta abinda yakeson nuna mata,da alamu yana son ta sauka ne,a hankali ta sanya hannnta ga mabudin qofar ta bude ta zira qafafunta ta fita,ta soma takawa a hankali tana shugewa ciki haushinyana cikata,tana jin sanda aka dage masa gate yabi ta gefanta ya wuce zuwa ciki.
qarfe biyu saura mintuna goma aka idar da sallar cikin masallacin dake cikin kamfanin,masallaci ne me yalwa da aka ginashi bisa tsari mai kyau saboda gudanar da ibada ga ma’aikata,aka sanya liman wanda ke jagorantar sallolin nann biyu wani lokaci har uku ma da suke ruskar ma’aikatan cikin ma’aikatar.
kamar yadda yakeyi wani lokaci,yakan badda kama,ya zauna daga can wani saqo na cikin masallacin,musamman idan yana sin yin addu’o’i bayason tashi da wuri,yauma hakkane,yana zaune sosai cikin nutsuwa,kansa a qasa yana azkar da yakanyi duk lokacin daya idar da salla,kusan masallacin babu kowa,sai wani lebura guda daya dake zaune daga bayansa,baisan me ya zaunar dashi ba,ya tabbatar daya fuskanci shine zaune a wajwn bazai zauna ba haka kusa da bayansa sosai ba,wannan na daya daga cikin dalilan da yasanya idan zai zauna din baya gani a gane fuskarsa ko a gane waye.
yana tsaka da addu’o’in ya duba lokaci,akwai sauran mintuna biyar da suka rage,ya sauke hannunsa yana ci gaba da irga tasbihinsa da yatsun hannunsa,dai dai sannan daya daga cikin leburorin dake aiki a kamfanin ya shigo,jikinsa da lema,da alama alwala yayi xaiyi tasa sallar,bai samu jam’i ba.
“malam labaran…..ashe har kun idar?”leburan daya shigo ya fada,muryar wancan din da alamun laushi da sanyi yace
“wallahi,nima ka ganni nan,tunanin duniya ya hanani tashi,damuwa ce fal raina,dama ina cewa zan sameka mun zanta”
“subhanallahi,to Allah yasa lafiya”ya fadi yana zama gefansa.
Tagumin ya cire,yana sauke nannuyar ajiyar zuciya,kafin ya soma magana
“wato malam tanimu takaka ya shiga uku a wannan zamanin……ka ganni nan na rasa inda zan dora raina,bikin yarinyata ne ake ta saka rana amma abu ya gagara,sau uku ana saka rana ana dagawa saboda babu kudin da zan mata kayan daki,yanzu mijin yace idan aka qara dagawa ana hudu to ya fasa,abu na biyu yarona bashir da na sanya raina da burina akan zai taimaka min idan ya qare karatunsa……shima yanzu saura kwana uku a rufe registration amma ban masa ba,saboda bani da kudin yi masan,munje neman taimako gidanjen ‘ya siyasan nan har mutum biyu amma saidai suce za’a kiramu har yanzu shiru,mutanen nan malam tanimu nasa tsoron Allah,sun gina manyan gidaje,suna hawa manyan motoci,sutura ta alfarma amma sun kasa taimakawa talaka dake nemam tsira da rayuwarsa koda da iya abincin da zai sanya a bakin salatinsa ne,kudin da bai gagaresu ba amma suna qyashi da baqincikin su dauka su taimaka maka,bayan duk wata qafafa tasu da suke da ita kudinka ne,da bazarka suke rawa,sai daka zabesu sannan suka zama abinda suka zama,sai da ka zabesu sannan suka je inda suke a yau,naje na yiwa murtala magana,ya taimaka min cikin albashina ya bani,ko katifa na samu da asiya mata da labulaye amma yace sam,ai wata sai yanzu yayi rabi ma,baza bani ba,na haqura waina jira har watan ya qare a soma albashi,ya ilahi ina mutum xai tsoma rayuwarsa ne?” .
wani abu ne yaja hankalinsa kan hirar da sukeyi din,saidai kafin yayi tunanin komai wayarsa ta shaida masa cikar sauran lokacin da ya rage masa,dole ya miqe ya dauki rigarsa ta sama daya cire ya cukuikuyeta ya taka a hankali ba tare da sun lura da shi ba ya fice.
ajiyar zuciya ya sauke,yana tsara abubuwa masu yawa cikin ransa,ran nashi yaji ya dan baci game da murtala,tun ba yau ba yana dan ji da samun qorafe qorafe a kansa game da ma’aikatan, akwai abubuwan da suka sanya yake daga masa qafa ne,banda haka da tuni ya dade da yanke masa hukunci,saboda shi din bai da wasa ka irin wadan nan al’amuran,dalilin da yasa kamfaninsa ya zama daban da sauran.
sai da ya zauna sosai kan mazauninsa sannan aka sake sabuwar gaisuwa,dakin ya dauki shuru,kowa ya nutsu yana jiran yaji daga bakin shugaban nasu.
fawwaz ya hanga cikin jerin ma’aikatan,ya masa kallon da bai wuce na sakanni uku ba saiya dauke kansa,cikin muryarsa Mai cike da kwarjini da wani nauyi dake cika kunnuwa,wanda ke nuna nutsuwa da confidence ya soma magana cikin harshen nasara,duk da yana jefa hausa lokaci zuwa lokaci a ciki
“abu na farko da zan soma bude taronnan dashi albishir ne…..”take fuskar duk wani ma’aikaci dake wajen ta washe da fara’a da kuma farinciki,tun basu ji ke zaya ce ba,sunsanshi tun ba yau ba,duk sanda yazo da albishir to kowa saiya dara
“akwai qarin albashi ga ma’aikata”take wajen ya hautsine da farinciki,duk da cewa m.s construction company yana daya daga cikin kamfanunuwan dake bada albashin da babu kamarsa a gadin Nigeria
“amma ga wadanda suja dace….akwai tantancewa da zamu aiwatar kafin faruwar hakan”farincikin sai ya dan ja baya daga fuskokin wasu,yayin da kowa ya cika da fata da burin ya zamana cikin wadanda suka cancanta.
sauyawar tasu bai hanashi kiran sunan murtala ba
“murtala”
“yes sir”ya fada yana miqewa tsaye, hannunsa dauke da wani littafi mai manyan shafuka,da rubutu birjik a cikinsa,yadan rusuna masa sannan ya miqe
“daga yau…..”ya dakata yana kallonsa,yayin da dakin ya dauki amsa amon na muryarsa
“daga yau……duk wani ma’aikaci,kama daga babba zuwa qarami,duk wanda yazo maka da buqatar albashinsa kafin lokacin bada salary yayi,a dauka a bashi”kallon kallo suka soma yi a junansu,kalamansa na yiwa wasu daga cikinsu dadi,yau kam zaman na musamman ne a wajensu,yazo musu da abubuwa masu dadi.
Duban fuskar murtalan yake yana jiran yaji abinda zai fada,muryar fawwaz ta maue gurbin muryar murtala da samir yake kira yaji yace wani abu akai
“amma samir…..hakan sai nakega baiyi tsari ba,ya ace tun ba’a ga performance na mutum ba a cikin watan sai a dauka salary dinsa kawai a bashi,bugu da qari kuma ma…..kowa ya sani cewa,akan iya samun asara a kamfani ko riba,duka ba zakayi duba da wannan ba zaka zaka yanke wannan hukuncin,idan asara ta samu kuma kenan kamfani shi kadai zai dauka bazai shafi ma’aikata da albashinsu ba”kallo.ya zubawa fawwaz na wasu sakanni,yana mamakin yadda fawwaz ke masa shishshigi haka cikin lamuransa,yana sane dashi,ya dage masa qafa ne saboda albarkacin wasu mutane guda biyu,saiya janye idonsa daga kan fawwaz din ba tare da yace masa komai ba,ya maida dubansa ga murtala
“this is an order”ya fada kai tsaye cikin salo na bada umarni,kai murtala ya gyada
“in sha Allah sir”ci gaba yayi da kallonsa yana jefa masa tambaya ta biyu, analysis ne na wasu abubuwa da suka shafi kudin dake shiga da fita a kamfani,murtalan da team dinsa suka soma bayani,tsahon wani lokaci da samir ya tabbatar komai yayi dai dai, bayani kuma ya kammala yadda ya kamata,murtala ya miqa masa takardun ya karba,da zummar idan yaje gida zai sake dubawa,ya kuma sanya hannu,saiya miqawa umar dake zaune daga gefansa,sannan ya sallami wasu daga cikin ma’aikatan,yabar wadanda suke cikin gaba ta biyu da zasuyi magana akanta.
“umar….ina da ina aka binciko bayan qauyen dan sarari?”samir ya fada yana shafa kansa da hannunsa,saboda gajiya da ya farayi da zaman,uwa uba kansa ya dauki chargy sosai,miqewa umar yayi a nutse shima da wasu takardun a hannunsa
“sir….akwai qauyuka guda biyu,qauyen É—inya da kuma qaunyen me saje,dukkaninsu suna buqatar makaranta da masallaci,koda na kamsus salawati ne”kai ya jinjina idanunsa qur kan file din dake gefansa
“cikin biyun wanne qauye ne sukafi buqatar hakan”bubbuda shafukan takardun hannunsa umar yayi sannan ya dago ya dubi samir
“qauyen dinya,don makarantar dake kaf qauyen guda daya ce,an ginata shekara talatin da suka gabata,kuma tun wancan lokacin ba’a ake sabuntata ko bi ta kanta ba,sannan qauyen basu da masallacin kamsus salawatin ma,suna salla ne qarqashin bishiya”kansa yake qara jinjinawa,ransa na baci,idan ya tuna shuwagabanninmu,me sukeyi?,meye amfaninsu?, duk wani abu da aka zabesu don su yiwa talaka shi bashi suke yi ba,yanzu wadan nan mutanen abinda sukafi buqatar ayi musu ba’a musun ba,kuma baya raba dayan biyun,suna iya shiga har can neman quri’unsu idan lokacin zabe yazo,amma a yanzun tamkar basusan akwai wata al’umma dake rayuwa a wajen ba
“i hate it”ya furta can qasan ransa,kamar yadda yake dukkan wannan tunanin cikin ransa.
Kwayar idanunsa ya daga yana katse shurun ta hanyar cewa
“murtala….a dubamin putting smile account aga nawa muke dashi,idan kudin baikai ba a sanya dukka albashina a ciki,a soma shirin zuwa yi musu aiki,idan ina free zani wannan karon,idan kuma akwai aikin dake da buqatata cikin kamfani zan turaku ku aiwatar kamar yadda aka saba”
“an gama sir”ya fada cikin girmamawa.
Kafeshi da idau fawwaz yayi,yana jin wani abu na taso masa cikin ransa,sam samir baima ga kallon da yake masa ba,har sai daya tashi daga kashingiae da yayi yana soke yatsunsa cikin na juna yana kallonsu daya bayan daya
“akwa mai wata magana qorafi ko qarin haske?”haka yake,duk sanda akayi taro irin wannan yana baiwa kowa dama ya tofa albarkacin bakinsa,yakan gayawa kansa dakansa cewa
“kowa ma mutum ne kamar shi,nawai saboda Allah ya bashi jagorancinsu ba kuma ya zamana shi kadai yake da abun cewa,kowa ma baida abun fada”.
Fawwaz ne yayi gyaran murya sannan ya zauna sosai yana duban samir
“akwai qorafin da zanyi”dubansa yayi na wasu sakanni sannan ya gyada kai alamun ya bashi dama
“amma ni a ganina mr samir kai ba gwamnati bane da zaka ce saika farantawa kowa,koda gwamanti bata iya aiwatar da komai da komai,kowanne lokaci kama kwashe kudaden kamfani kana zuwa kana wahaltawa wasu mutane da basu gama sanin dadin rayuwa ba bare susan ciwon kansu,ko wata biyu ba’ayi akaje wasu qauyukan aka musu aiki,kafin su ka yiwa wasu da dama da bansan iyakacinsu ba,hakan bai isa ba?”,cike da mamakinuake duban fawwaz,yasan za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya,naisan aninda ke damun fawwaz din ba,amma ya soma gajiya a wasu baqin halayensa,kusan maganar fawwaz din taja hankalin yawa yawan wadanda ke wajen,murmushin gefan baki samir din yayi sannan yace
“kana da matsala da hakkanne?,ko kamfani na tauyeka da wani abun?” kai ya girgiza
“ko kadan….amma….”hannunsa ya daga masa
“bana son amma….matsalarka nakeson naji idan akwaita,idan kuma babu fine,zamuyi addu’a mu tashi”shurun da ya biyo baya shiya tabbatar masa da cewa…..dukka qorafin da zaiyin ba mai ma’ana bane,ba kuma muhallinsa bane……