Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 55

Sponsored Links

55
Dz

A hankali cikin kasala da mutuwar jiki take takowa zuwa kitchen din gidan,kitchen din data jima rabonta dashi,saiko yau,tun bayan wayar da samir din yayi,ya umarci hajiya qarama ta baro gidanta su tattaro su dawo cikin gidan professor rashid din,bayan nan dinma ya sanya an qara securiy,wanda gaba dayansu babu wanda yasan abinda hakan yake nufi,don babu wanda ya yiwa bayani a cikinsu.

Baccin daya yanke mata tun cikin dare ne cike a idanuwanta,tun daga sanda tayi mafarkin matar bata sake rintsawa ba,don haka ta yanke shawarar fitowa zuwa kitchen din ta kama wani aikin ko hakan xai debe mata kewa,ya kuma qwarara jikinta.

Tun daga nesa ta hangi biba tsaye cikin kitchen din tana feraye dankali,sai tayi sallama,biban ta waiwayo fuskarta dauke da fara’a tana amsa mata.

“Ina kwana” kaltum ta gaidata tana zaro wuqa a ma’ajiyarsu,ta fara tayata firar dankalin,amsa mata tayi kamar kullum cikin sakewa,sai suka fara taba hira sama sama,duka hirar tasu akan ciwon daddy ne da makamantansu,saidai can qasan ran kaltum maganar da takeson yi mata tana tsunkulinta,bata samu damar yi mata ba har sai sanda suka gama gyara komai suka dora kan wuta.

“Ashe hotonki maman yaya saraki ce a jiki?,kuna da alaqa daman?” A birkice ta dago kanta ta dubi kaltum,razana da firgici suka bayyana baro baro saman fuskar biba,ta soma waige waige da hanzari,ta tabbatar babu kowa sai kawai ta wafci hannun kaltum ta tura qofar baya ta kitchen din ta jata ciki.

Idanuwa ta tsare kaltum dasu,kafin hawaye ya soma wanke mata fuska,cikin muryar kuka,kans murya can qasa ta fara magana

“Duk yadda nayi dake karki tona wannan maganar kaltume saida kika tono ta?,shin bakyason lafiyarki ne?,ko bakison ranki dana iyayenki?,to bari na buda miki komai ko hakan xaisa ki janye kika ki kuma yiwa kanki da yan uwanki gata…….tabbas mamar samir ce a jikin hoton,raihana……wadda ni ba kowa bace face ‘yar aikinta shekaru masu dama,yar aikin data dauketa kamar ‘ya uwa,ta yimin dukkan wani gata,ta bani kulawa da dan uwa zai baiwa dan uwansa,hakan yasa nima na dauketa kamar yar uwata,na kuma riqi samir kamar d’ana…..mutum ce iya mutum,wadda duk yadda za’a kwatanta miki kirkinta ba zaki fahimta ba sai zama ya hadaku da ita…..kwatsam dare daya hajiya jidda ta shigo rayuwar professor rashid…..ta zama matarsa,abinda babu wanda ya taba zato ko tsammanin zai faru,duk da cewa kusan auren cin amana ne jidda tayi da professor amma haka hajiya raihana ta karbi qaddararta…..” Dubanta kaltum tayi tana mamakin kalmar auren cin amana,kamar biba zuwaira tasan me take rayawa saita gyada kai

“Eh…..auren cin amana,domin kuwa jidda ‘yar aikin hajiya raihana ce” idanuwa kaltum tadan bude kadan alamun mamaki,wannan wanne irin labarine haka a birkice?

“Karki dauka gama garin me aiki” biba ta fada tana sake matsawa kusa da kaltum muryata a kwance

“A’ah,irin masu aikin da basu da kowa,suke da matuqar buqatar taimako,ta daukota ta kawota cikin gidanta,ta nuna mata dukkan gata da rufin asiri,ta sanyata taci gaba da karatun jami’a,bayan ta kammala,tasa Daddy ya bata aiki a wani kamfani nasa da alokacin yake gudanar dashi,duk da hankalinsa a sannan ya fara karkata ga siyasa…..amma jidda ta aure mata miji,ta kuma janye hankalinsa gareta ita daya qwallin qwal,munyi imani bata asiri bata kuma aiki dashi,bamusan da wanne siddabaru take amfani ba,amma ta juya tunanin professor gaba daya,bashi da cewa sai tata,kullum kwanan duniya akwai fada ko tashin hankalin da zai saukewa hajiya raihana,tun bata damuwa harta shiga damuwa,kwata kwata ta zama kamar ‘yar kallo cikin gidan,qalilanne cikin ‘yan uwan professor suka koma suna ta tata,kamar irinsu hajiya qarama,jidda ta janye komai ta kuma janye kowa……,lokaci mai tsaho ana a haka,har zuwa sanda jidda haihu yara mata guda biyu,tazararsu shekara biyu kacal,ba jimawa hajiya raihana ta samu ciki itama,wanda tunda ta sameshi babu zaman lpy,cikin da ta fita dashi kenan,rana daya muka tashi cikin gidan nan da maganar bacewarta,qaura wambai babu ita babu dalilinta,sai samir data bar mana,duba na duniya ba’a samu hajiya raihana ba,a sannan jikina ya bani ba mutuwa tayi ba kamar yadda mutane keta fada,saboda ganin girman cigiyar da akayi amma babu labari ko motsinta.

Zuciyata ta sake yarda da abinda take raya min ne na cewa ba bata tayi ba,akwai abinda ya faru da ita,saboda wasiqa dana samu saman gadonta,kuma bisa dukkan alamu tana tsaka da rubutata ne abinda ya sameta ya faru da itan,sirrine tsakanina da ita,bazan iya gaya miki ba…..a lokacin jidda ta shigo dakin kawomin samir daketa rigima akan na lallasheshi,taga wasiqar,ta karanta,a gabana ta duqunqune wasiqar ta kuma sakata a toilet tayi fuloshing dinta

“Dukkan abinda ta rubuta ki daukeshi ki watsar dashi gefe…..bari na gaya miki,yau ba watan raihana uku ba bata nan?,to ki sanya a ranki watanta uku cikin kabarinta…..domin ba zaku sake ji ko ganinta ba,wannan maganar ina gaya miki itane tamkar kana tona sirrinka ga wanda yake kan gargarar mutuwa,kinga ba wanda zaiji saidai ko qasar kabarinsa…….fitar wannan maganar dai da take rasa ranki,hakanan dukkan wanda kika shaidawa shima kin sakashi cikin babban hadari,babbar soyayyar da zaki nunawa dukkan wanda ke tare dake shine,ki kiyaye kunnuwansa daga sauraren wannan batun” maganar data gaya min kenan cikin kakkausar murya da yanayi me ban tsoro.

.

“Na tsorata sosai,don haka a sannan na roqeta kan zan ajjiye aiki,zan koma gida”

“Bismillah,kina iyawa indai kin shirya mutuwa keda duk wanda yake rayuwa tare dake” wannan maganar tasa nayi shuru ina tsuma saboda tsabar tsorata,ta jefeni da wani kallo,sannan ta matso gabana

“Bari na gaya miki wani abu….keda duk wanda yasan qamshi qamshin abinda ya faru bashi ba fita daga gidan nan,aiki kuma yanzu kuka fara har zuwa .lokacin mutuwarku,bance ba zaku dinga zuwa gida ba,amma babu tabbaci har sai abinda na gani” da wannan maganar ta fita ta bani waje……haka na rayu dukka shekarun nan ina kuka a boye na rashin raihana,ina addu’ar Allah ya bayyanata idan tana raye,idan kuma da gasken ta rasu…..to ina mata fatan samun rahamar Allah da dacewarsa,ina kallo take nunawa samir soyayyar da nasan bata gaskiya bace amma bani da abinda zan iya aikatawa…..sai taso sangartashi da lalatashi amma haqarta bai cimma ruwa ba,ban sani ba ko qarfin addu’ar mahaifiyarsa ke bibiyarsa,da kuma alkharin da tayi a rayuwarta ne yayi masa tasiri?……da wannan bata yiwu ba saita canza salo,ta sanya samir yana sabawa dukkan muradi ko buri da abinda mahaifinsa keso,ta wannan hanyar ta kauda dukkan wata jituwa da qauna da yakewa samir din,ya koma kallonsa a matsayin bijirarren da mara biyayya,a fakaice takeson ture samir daga zuciyarsa ta cusa najwa ta qarfi da yaji,taso hadawa da jawahir….amma yarinyar sai Allah ya halicceta daban,kusan ta debo dabi’un samir din,wannan yasa sukafi jituwa qwarai da gaske……abu daya ne yasa naqi shiga wannan yaqin kan rayuwar samir….” Shuru ta danyi,murmushi kuma ya subuce daga fuskarta ta tsakiyar hawayenta

“Duk abinda takeyi tana yine saboda ta raba samir da mahaifinsa…..tana qarfafa samir yayi abinda ya tsarawa ransa kar ya damu da abinda mahaifinsa yakeso……sai Allah ya bashi wata kariya,ya bashi wata zuciya ta alkhairi,wata zuciya ta hangen nesa,zuciya meson taimako……ya zamana dukkan abinda ya dage zaiyi din me kyau ne,tayi hakan don ta nisanta shi da ubansa,sai kuma hakan ya zame masa alkhairi ba tare data farga ba,samir…..bai manta ni ba,bai manta wacece ni a wajen mahaifiyarsa ba,duk sanda zai aiwatar da wani abu yana tambayata shawara koda aboye ne ba’a gaban idanun kowa ba,ina kuma bashi shawara dai dai gwargwado,duk da cewa….a wasu abubuwan hajiya jidda ta riga tayi tasiri a tunaninsa,misali,yabar zancan mahaifiyarsa sam ya daina daukoshi,ya daina yinsa,na rasa ta yadda zan dauko masa wannan tunanin na dawo dashi cikin kwanyarsa,na rasa yadda zan fahimtar dashi cewa hajiya jidda ba masoyiyarsa bace,hajiya jidda maqiyaya ce gashi da rayuwarsa……..” tana kaiwa nan wani kuka me nauyi ya taso mata,kukan daya sanyata komawa ta qofar kitchen da sauri.

Sulalewa kaltum tayi a hankali ta zauna sosai a qasa,yau tana ganin wata rayuwar bayan rayuwar ta data sani,ashe kowacce rayuwa da irin nata qalubalen?,tayi tunanin cewa matuqar kana cikin wadata baka da wani sauran qalubale,ashe karatun ba haka yake ba.

Amma wacece a gidan masu tabin hankali?,wacece ita?,anya sunsan da zamanta?,meye dangantakarta da raihana maman samir?,mahaifiya?,qanwa ce ko ‘yar uwa?,jikinta yana bata tabbas akwai wani abu a qasa,saidai kunnuwanta suna mata amsa kuwwa,tare da tuna mata maganar mummy a ranar da sukaje gidan,jan kunne da gargadi da kakkausar murya

“Ko ‘yar cikina ban yarda naxo da ita wajen nan ba,waje ne dake cike da sirri,waje ne kuma me hadari,kisa a ranki baki taba zuwa wajen ba,hakan shi xaisa ba zaki gayawa kowa kinxo din ba kinji kaltume?” Bata dauki komai ba a wannan lokacin,ta dai gyada mata kai a ladabce,ba tare data fahimci ko hasaso komai a kanta ba.

******Tun daga wannan ranar kaltum bata sake samun nutsuwa kan maganar ba,kullum maganar ke yawo cikin kwanyarta,gefe daya kuma hankalinta ya dauku ga mummy,haka kawai ta samu kanta da nazarin mummy,cikin nutsuwa da ankarewa ta dinga fuskantar wasu abubuwa da dacan hankalinta bai kai ba,yanayinta daban kam ciwon daddy a gaban samir da kuma sanda baya nan,yadda take mu’amala da masu aikin gidan daban da yadda take mu’amala da biba,mu’amalarta da qawayenta da sauransu.

A kwanakin duk sanda ta kalli Samir wani tausayinsa yake lullubeta,gaba daya ya fada yadan rame,saidai hakan bai fiddashi daga nutsuwarsa ba,nutsuwar nan tana nan,amma akwai tarin damuwa saman fuskarsa da ta gaza bayyanuwa,hankalinsa gaba daya ya tattara kan shirye shiryen fitar da daddy waje.

*******Karfe biyu na rana ta gama shirya abincin da zata tafi asibiti dashi,duk da cewa wadanda takeyi dominsu basa samun damar sanya koda loma guda a bakinsu,tanayin komai ne saboda jawahir samir hajiya qarama dama daddyn dake kwance,wanda zuwa yanzu am fitar dashi daga icu,saidai yana wani dakin daban na musamman.

Tsaf ta shirya cikin atamfa maroon colour,me torches na blue black,da hijab tayi amfani,wanda ya dace da kayan jikinta,ya kuma haskata sosai.

Fuskarta ta kalla a a mudubi sanda zafa gotashi,kullum kwanan duniya wani sake gogewa take gami da sajewa da al’ummar gidan,a yau sai taga abun har yafi na kwanakin baya,don tunda aka shiga wannan rudanin na ciwon daddyn rabon data tsaya cikin nutsuwarta haka,gefe daya ga tunanunnuka iri daban daban,fatarta sake fresh take tana bada color me masifar tafiya da hankali,a chocolate color din ma tasu skin din ba kowa ke samun irinta ba,saita qara gaba da sauri,saboda tuna inda zata je da tayi,ta kuma tabbatar driver na nan yana jiranta,hajiya qarama ma na can na xuba idon zuwanta,ko yaya taga batazo din ba saita damu,matsalar gabanta ta daddy baisa ta manta da ita ba,tana mamakin yadda take treating dinta kamar diyar cikinta.

Suna tafe a motar zuciyarta da qwaqwalwarta na nutso a duniyar tunani,tunanin daya zame mata qa’ida,har zuwa sanda zasu gifta ta gaban gidan,ta bishi da kallo kamar yadda ta saba,a wannan ranar……sai taji zuciyarta na tsananin bugawa,kamar xafa fasa qirjinta,ta lumshe ido sanda suka gota gidan tana furta

“La haula wala quwwata illa billah” saita maida idanun nata ta rufe,har zuwa sanda suka qarasa asibitin.

Sai data gaida dukkan wanda ya kamata ta gaida,suka hada idanu da wata baquwar fuska,tana zaune dare dare saman kujera tana danna waya,saita zare idanun nata kaltum din tana miqewa,ta isa gaban hajiya wadda suke zaune tare da jawahir ta zauna ta fara fiddo abincin tana zuba mata.

Sai data kammala zubawar hajiya tace

“Kinga kaltum,dauki abincin nan ki xagaya ta bayan dakunan can,samir yana can ki miqa masa,na jima rabon da naga ya sanya wani abu a bakinsa,dole yaci abinci ko yaya ne ai” kai ta gyada kana ta miqe tana sake daukan wani plate din abincin

“I wanna see him…muje na gani” jauhar ta fada tana sauke wayar dake hannunta,bata waiwayo ba hakanan bata tsaya ba,ta fara tafiya zuwa direction din da hajiya qaraman tace takai masan,haka kawai gaba daya yau takejin zuciyarta a rikice,bugun da take ya zarta qa’ida.

Su biyune xaune kan kujeru gufa ukun dake wajen,tun bayan fitowarsa daga wajen likita suka hadu da amiru a wajen

“Zuciyata tana gayamin akwai wata a qasa tabbas ba shakka,kuma zargina yafi karkata kan abokan siyasar daddy,kamar sun kutso cikin lamaransa da shirin kau dashi,sannan sun nema hadin kai da taimakon wasu nasa na jikinsa,saidai na rasa gano ko su waye?,amma ba shakka……tabbas bala suspect ne a wajena,duk da cewa bani da gamsassu da qwararan hujjoji…..amma inaji a jikina” ya fada yana kallon amiru da idanuwansa wadanda sukayi laushi,saboda qalubalen daya soma tunkaro rayuwarsu ba tare da shiri ba.

Kai amiru ya jinjina cikin dogon nazari,mamaki fal zuciyarsa da kuma shakku,bai bar abun a ransa ba ya dubi samir shima

“Dukka bayananka na gane na kuma gamsu,but samir…..bala fa tsohon drivern daddy ne,kuma amintaccensa,ka manta?” Miqewa samir yayi a hankali,ya sanya hannayensa duka a aljihun wandonsa,yayi taku hudu daga inda suke zaune,kana ya baiwa amiru baya

“Koya yana iya zama suspect amiru…..idan nace kowa ina nufin harda mommy…..zan sanya idanu akan kowa,zargina kuma zaibi takan kowa” miqewa yayi a hankali,ya taka shima zuwa inda samir din yake,ya tsaya dab da bayansa,sannan ya dora hannunsa saman kafadrsa

“Zaka samu dukkan wani gudunmawa da kake da buqata daga gareni,zamu fuskanci wannan challenge din tare kamar yadda muka saba,na maka alqawarin rufe sirri,da kuma dafawarka har sai mun cimma gaci” kai samir ke jinjinawa,baikai ga cewa komai ba ya hangi bullowarsu,tana gaba jauhar na bayanta.

A hankali ya zubawa kaltum din idanu,fuskarta sam babu alamu na fara’a ko walwala,duk da cewa tunda daddy ya gamu da wannan tsautsayin yadda walwala da farinciki ya yiwa familyn qaranci ita dinma haka,abinda ya sake daga daraja da qimarta gami da martabarta cikin idanu da zuciyarsa,hidima take bilhaqqi,zaka rantse mahaifin daya haifeta ne.

A hankali ya maida idanunsa ga jauhar,wadda take tafe tana latse latsen waya,baya ga earphone dake kunnenta,nazarinta itama yayi na wasu sakanni,yanason tantance wane interest ne dashi a kanta?,ya dauke idanunsa a hankali yana juyawa baya,sai suka kusa karo da amiru dake tsaye bayansa,da alama shima sashen da suka taho din yake kalla,hada idanu sukayi,kowa sai ya dauke idonsa,da alama akwai abinda ke zuciyar kowa,saidai kuma ba muhallin magana bane nan din.

Sallamarta ta mamaye wajen a zazzaqar muryar nan tata,wadda ta cika da sanyi da taushi fiye da lokutan baya,amiru ne ya amsa,samir kuma ya sauke mata idanunsa,bata kalleshi ba har ta gaidashi bayan ta ajjiye kayan abincin a gabansa.

“Sweet baby……kana ta nan ashe,hajiya tace ga abinci nan kaci…..ayi serving naka?” Jauhar ta fada sanda ta iso kujerar daya koma kai ya zauna,ta dafe bayan kujerar dab da bayansa tana kallonsa.

Idanunsa ya maida ga kaltum,wadda tuni tayi nisa wajen zuba masa abincin ba tare da taji da bakinsa ba

“Kadan…..hakama is ok” ya fada a tausashe ganin yadda kaltum din ke loda masa abincin bata ko kalleshi ba,daga isowarsu wajen kawo yanzu ta gane dawa suka taho,jauhar….sunan data riqeshi tsaf a kanta,tun wancan lokacin da jawahir ke yawan bata labarinta,a lokacin da batasan ciwon kanta ba,a lokacin da batajin komai don an ambaceta a gabanta.

Tura masa gabansa tayi ta miqe

“Ni ba za’a sanmin ba?,ko yayan naki kawai kika sani?” Amiru ya fada yana dan murmushi sanda ta miqe zata bar wajen,juyowa tayi,tadan saki murmushi,kana ta dawo a hankali shima ta soma zuba mishin.

“Kaci mana please sweet baby,ko sai na baka da kaina,bakaga yadda ka zama bane?” Kaltum ta tsinci muryar jauhar tana fada a wani mugun shagwabe,kamar zata saki kuka,abinda ya sanya hannunta kakkarwa kenan ba tare data ankara ba,ta ajjiyema amiru abincin ta miqe da hanzari ta soma barin wajen.

Haka kawai taji batason ma komawa wajensu hajiya qarama,saita nufi qofar fita daga asibitin,tana jin zuciyarta a matse,tare da wani irin nauyi,taci gaba da takawa a hankali tana barin harabar asibitin.

Batasan tayi tafiya me nisa ba sai data ga tana hango asibitin masu rangwamen hankalin,haka nan kawai taji kamar ana mata umarnin tafiya zuwa wajen asibitin,sannu a hankali sai gata a bakin gate din asibitin.

Idanun masu tsaron qofar a kanta

“Hajiya ina zaki?” Murmushi tayi qoqarin qirqirowa

“Akwai wanda nakeson gani cikin ma’aikatan?”

“Wa kenan?” Daya daga cikinsu ya tambayeta,shuru tayi na sakannin da basu wuce uku ba,tana laluben qwaqwalwarta ko zata iya tuna sunan daya daga cikin ma’aikatan da taji mummy ta kira sanda suka shigo

Idanunta suka sauka kan kyauron dake daure a hannun daya daga cikinau
“Kyauro” tayi caraf ta ambata

“Shiga,yana ciki” ya fada yana bude mata gidan,ta sanya qafarta a hankali,gabanta yana tsananta faduwa,zuciyarta nason raurawa,amma taci gaba da kutsawa zuwa ciki.

Kai tsaye taci gaba da sanya kanta,bata tsaya ko ina ba sai office din da aka saukesu wancan karan.

A hankali ta tura qofar ta shige zuciyarta na bugawa,babu kowa cikin office din,sai take ji a zuciyarta kamar wata dama aka bata,don haka cikin hanzari ta soma laluben qofar da aka bude musu suka shige wancan karon.

Tana kusantar dakin bugun zuciyarta na qaruwa,duhu ne sosai a wajen,da alama duk dakin dake wajen dakuna ne na wadanda ciwonsu yayo worst,aka kuma fitar da ra da samun lafiyar wasunsu,waje ne tsit mai rashin wadatar haske,kai kace maqabarta ne,tana kutsa kai zuciyarta na gargadarta,amma ta wani sashen kamar ana qara mata qaimi da kuma qwarin gwiwa,da haka har ta isa qofar dakin,saidai a kulle yake da kwado,hakan yasa ta matsa kadan zuwa bakin window din,a bude yake,saidai tsaho daya danyi mata kamar wancan karon,ta waiga kadan,saita hango wani dan katako,ta tabbatar zai qara mata tsaho yadda takeso,don haka ra daukoshi cak,ta ajiyeshi saitin window din,ta taka a hankali tana sanya idanuwanta zuwa cikin dakin.

Daga can take hangenta,xaune a daya daga cikij corners din dake dakin,a takure kamar wadda ke jin sanyi,habarta na saman gwiwoyinta,idanunta kuma alumshe suke,saidai tana hangen yadda take tattaba yatsun hannunta,kamar wadda ke irga tasbihi da su,hakan yasa kaltum din taji kamar ta sauka ta juya,saboda zuciyarta na tunasar da ita inda take,da kuma wajen wadda take tsaye.

“Salamu alaikum” bakinta ya subuce ta furta da sautin da dukka wanda ke cikin dakin xai iya jin abinda tace
“Subhanallah” taji ta furta tana daga kanta da sauri ta saukesu ga kaltum dake riqe da qarfe window din tana kallonta.

Idanu ta zubawa kaltum din tana kallonta,karo na farko data ga wata baquwar fuska haka tsaye a gabanta,yayin da kaltum ke kallonta tana karantar tsantsar kamanni da suke sake bayyana kansu a yanzun da suke kallon juna kallo irin na qurilla,yayin da wani gefe na zuciyarta ke cike fal da mamakin ambaton subhanallah din da taji tayi.

Zuciyarta ta sake raya mata ta aikata wani abu,cikin buguwar qirji ta buda bakinta a hankali

“Samir yana gaisheki” zumbur taga ta miqe kamar wadda wani abu ya tsikara,lamarin da yayi matuqar razana kaltum,har ta dan ja da baya,saboda tana ganin kamar zata rugo da gudu ta cafketa,saidai bata qara wani motsi ba illa zuba mata idanun data sakeyi

“Muhammad samir rashid azare?” Kunnuwanta suka tsinto kalaman da suke fitowa daga bakinta a sanda take ci gaba da tsaiwar.

Ta riga da tasan cikakken sunan daddy,ta kuma tabbatar cikakken sunan samir kenan,saboda haka saita gyada kanta suna ci gaba da kallon juna.

Jikinta yayi matuqar sanyi lokacin da taga hawaye yana saukowa daga fuskar matar daya bayan daya,wani busashen murmushi yana son mamaye fuskarta

“Ke wace?” Ta sake jifanta da tambayar da batasan amsar da zata bata ba,saidai kafin ta amsa din taji takun tafiya,abinda ya sanyata waiwaya da hanxari cike da tsoro da fargaba tana duban hanya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button