Dabi’ar Zuciya 54
54
A rude hajiya qarama taja mayafinta mummy ta biyo bayanta
“Mu tafi tare samir,muje tare” hannu ya sake daga musu
“A’ah hajiya,kuyi haquri ku zauna,zamuje mu duba,duk abinda ake ciki zakuji” da kalaman kwantar da hankali ya samu yasha kansu,duk da cewa shima a sare yake,hakanan zallar tashin hankali yakeji yana dawainiya da shi.
*_ƘAUYEN ƊINYA_*
Kowanne lokaci irin wannan tun bayan zamantowarta ita daya a sashen,lokacine da yake zame mata bata aikin komai,domin kuwa tana gama komai nata da wuri,sadai ta zauna tayi sana’arta,wadda kullum kwanan duniya take habaka,wanda ta samu kakkauran jari daga wani tallafi da wani bawan Allah ya bayar ga mata marasa galihu dake qauyen,kuma cikin ikon Allah sunanta ya fito a sahun farko,abinda bata taba zata ko tsammata ba,hakanan adadin kudin da aka batan ya bata mamaki qwarai,don kaf tsahon rayuwarta bata taba mallakar kudi makamancin haka ba.
Sai data gama kallonta daga dan nesa,sannan ta kwado sallama sashen tana tabe baki,sai data daga kanta ta dubeta kana ta amsa mata.
Qarasowa tayi tayi tsai a kanta,hannunta a qugunta,ta fara magana
“Ni wallahi zuwaira kullum kwanan duniya mamaki kike bani,ke kamar ma baki damu da bacewar diyarki ba sama ko qasa?,kin kama sana’a baji ba gani?,ko tunanin mijin nata ya saidata ko ya batar da ita bakya yi?”. Ajiye abinda take auna man qulin da aka kawo mata tayi,ta tada kai sosai ta kalli inna laure
“Ke kin taba ganin wanda yake da Allah….ya kuma yi imani da wanzuwarsa,da kuma cewa shidin yana cikin lamuran bayinsa ya girgiza?,kin taba ganin wanda yake addu’a bisa yaqinin Allah na jinsa ya kasance cikin damuwa?” Baki inna laure ta tabe,don ita sam ba haka taso taga zuwaira ta kasan ce ba,so tayi bayan tafiyar kaltume ta lalace ya daidaice,tunda dama itace me tagazawar,sannan kuma ya zamana ita kanta kaltum din batakai wannan lokacin ba babu labarinta,so tayi cikin wata daya biyu ko uku ta dawo gida a wulaqance tunda taqi auren auwalu,duk da cewa yanzun ma tana qasa tana dabo,tunda ba’asan duniya ko nahiyar da take ba
“Ai shikenan,zuwa nayi na gaya miki dama kada kice ba’a gaya miki ba,kinsan idan ana harkar arziqi kunya ake bawa tsiya,ajima kadan za’a kawo kayan lefe da na sa ranar asiyatu yarinya haihuwar la’asar” murmushi ummansu tayi
“Kai ma sha Allah,’yata asiya lokaci yayi,to ubangiji ya bada sa’a,ya kauda dukka abunqi” ta fada tana daukar abun awonta taci gaba da aikinta,don bata da abun fadan daya wuce wannan,tunda take bata taba ganin neman aure irin na yaran gidansu ba,daga asiyan har kaltume kamar yaran tsintuwa?,har gwara kaltum siya mata akayi?,amma asiya fa?,su sukace sunji sun gani,kaf maganar aurenta da alhj dauda har kawo yau babu wani magabacinsa,abokansa ne suke aiwatar da komai,ko kayan auren da za’a kawo din abokansa ke tsaye akan komai,amma ko a gefan silifas din kawu iliya ko ita inna lauren,iya kudin da yake barar musu kawai ya ishesu,ba abinda ya shafesu da yanayin yadda komai yake tafiya.
Kamar hadin baki,inna lauren bata jima da barin wajen ba ta jiyo gudar mutanen da xasu jeren wasila,wadda za’a daura aurenta a gobe da nasuru,nusurun da sai da umma tayi masa nasiha da gaske sannan ya haqura yabi abinda mahaifiyarsa lantai keso na auren wasila data wajabta masa,wanda ita tayi uwa tayi makarbiya ta gabatar da komai na auren.
******kallo daya zaka yi masa ka karanci zallar rudani gami da tashin hankali dake saman fuskarsa,gaba daya launin idanunsa sun canza,yana tsaye qyarrr a gaban gadon da daddy ke kwance sashe na musamman na intensive care unit,wadda na’urori ke faman aiki a kansa cikin cikakkiyar kulawa.
Tun ranar da aka kawoshi asibitin washegari ake sanya ran farfadowarsa,sai gashi an kwashe kwanaki biyar amma babu batun farfadowar tasa,abinda yasa aka daukeshi daga dakin da yake aka dawo dashi nan din tsahon kwanaki hudu kenan,wamda hakan ya sabbaba tashin hankali da rudani a family professor rashid,ba family dinsa kawai ba,hatta abokan siyasarsa dama kasuwancinsa gaba daya.
A hankali ya sauke hannyensa dake rungume a qirjinsa, yajuya a hankali saman qafafunsa ya fice daga dakin,yana jin wani nauyi na sake mamayarsa dangane da situation din da mahaifin nasa ke ciki,bai taba tsammatar soyayyar mahaifinsa na danqare a ruhinsa ba sai a wannan lokaci,bai tana tunanin akwai wani burbushin soyayya a tsakaninsu ba sai yanzu da yaga yana dab da rasashi.
Yana fitar farfajiyar dake gaba da dakin dukkaninsu suka miqe,ya bisu da kallo daya bayan daya,gaba dayansu ahalin professor ne,kowa ya sashi gaba da idanunsa,wasu na tambayarsa,kowa so yakeji yaji labarin wani canji ko ci gaba game da ciwon nasa,tunda shi daya ne mutumin da suke bari ya shiga wajensa.
Dauke idanunsa yayi daga fuskar hajiya qarama,wanda cikin kwanakin yanayinta kawai zai nuna maka tashin hankalin da take ciki,ya maida idanun nasa gefan hannun hagunsa inda sheshsheqar kukan jawahir ke tashi,ta dora kanta samam kafadar kaltum.
Idanunsa ya maida fuskar kaltum din,itama kamar sauran ahalin gidan,ya rame har a fuska,yana sane da yadda take dawainiya da zirga zirga kullum sau babu adadi tsakanin gida da asibiti,kawo abinci da sauransu,duk da abincin ba wajen kowa yake ciyuwa ba.
Yana ganin bai mata adalci ba idan ya barta tana ci gaba da ganin tashin hankalin da iyasu familyn professor rashid ya shafa ba,ya kamata ya kaita inda zatayi nisa dasu.
“Jikinsa alhamdulillahi,saidai yana buqatar addu’arku dai” itace amsar daya iya basu.
Cikin hikima da dabara ya kwantar musu da hankali,sannan ya waiwaya inda umar ke tsaye
“An samo drivern alhajin,yanzu haka yana wancan dakin ana bashi kulawa” dakin yabi da kallo sannan ya dawo ya dubansa ga umar
“Likita ya bada damar ganinsa ne?”
“Eh,saboda shi nashi raunin da sauqi,an fara bashi treatment a wani asibiti kafin a samu damar ganoshi” kai ya gyada ga dubi umar din
“Ka yiwa bashir magana,a tabbatar an maida kowa gida,saboda nan ba wajen xama bane,jiya likita yayi magana kan haka,zamansu anan xai sanya ‘yan dubiya suyita zuwa,idan ka gama kaima ka wuce kawai”
“Yes sir” ya amsa masa,sannan yayi gaba zuwa dakin da umar din ya nuna masa.
A hankali ya tura qofar dakin bakinsa dauke da sallama,ya amsa masa da murya irin ta mash ciwo.
Idanun samir a kansa ya janyo kujera ya aje gaban gadonsa,maimako n zama sai ya dogara da ita,sannu yayi masa ya amsa yana gaida samir din,hanunsa guda daya an saqalo masa shi ta wuyansa,kamar yadda qafarsa ke nade da bandage haka kansa ma.
“Wallahi yallabai…..kaga tsautsayi ko?,shekara da shekaru ina tuqa alhaji,sai wannan shekarar tsautsayin yazo……muna tsaka da tafiya irin motocin nan masu yiwa mutane overtaking ta dakemu,ban ankara ba kan motar ta qwace min muka gangara…..ashe ni na fada wata gona,sai manoma ne suka tsintoni,alhaji kuma.yayi wannan mummunar buguwar” ya qarashe maganar yana matse hawaye.
“Haka Allah ya qaddara,Allah ya rufa asiri” samir ya fada yana sauke qafarsa guda daya daya dora saman kujerar,dai dai sanda wayar dake aje gefan bala drivern professor ta dauki qara,abinda yaja hankalin samir din,ya waiga don taimaka masa wajen daga wayar,yana mamakin ma yadda akayi yake tare da wayar yana a irin wannan yanayin,saidai har bala ya daga wayar da daya hannun,ya tallafeta da hannunsa me ciwo wanda yake daure,yana kuma qoqarin dannan wajen amsa kiran.
“Kayi a hankali karka fama ciwonka” samir ya fada,saiya daga kai da sauri ya dubi samir din
“To yallabai”ya amsa masa yana dan sakin wayar,abinda yasa ta sulale kenan daga hannunsa.
Da dan mamaki tattare da shi ya baro dakin,sai ya zaro wayarsa,ya bada umarni aje gidan bala,a tabbatar an ajjiyewa iyalinsa kudi da kayan abinci wadatattu saboda yanayin jiyya,sannan yaci gaba da takawa a hankali ya isa office din likitan sukayi magana dashi,daga nan ya wuce zuwa bangaren ajiyar motoci,saboda yana son nan da gobe matuqar daddyn bai farka ba,kada ya wuce jibi a qasar nan.
Har ya sanya hannu zai bude murfin motar idanunsa suka sauka a kanta,tana tsaye riqe da kwando na kayan abinci,saidai kanta na kallon qasa,da alama ta shiga zurfin tunani ne ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,saiya fasa bude motar,ya fara takawa zuwa inda take a hankali idanunsa bisa kanta.
.
Bataji isowarsa ba har sai daya tsaya a gabanta,tana daga kai suka hada idanuwa,ya kafeta da idanun nashi yana hango wani rauni cikin qwayar idanunta,raunin da baisan na meye ba,yayin da ita kuma take kallon yadda lokaci guda ya sauya kamar bashi ba,tana da tabbacin cewa duk mutum me uba irin professor dole ya shiga irin wannan dimuwa a duk sanda irin haka ta faru dashi,duk kuwa da cewa ta karanci akwai wata bahaguwar alaqa a tsakaninsu,DABI’AR ZUCIYA ne damuwa dame kyautata mata,da kuma qin me munana mata,a kwanakin tana jin zuciyarta a matuqar matse,saboda duk abinda ya shafi jawahir ya shafeta,bare kuma uwa uba shi din,da takeji a ranta yayi tafiya me nisa ya nutse ciki.
Dumin hannunsa kawai taji saman nata yana qoqarin amsar kwandon,sai tasa daya hannun ta dafe
“Ka barshi zan dauka,ya najwa ce tace na tsaya a nan”
Ransa yaji ya dan baci,don yasan tana sane ta sakata tayita tsaiwa kenan?,tunda already babu kowa nasu a asibitin,duka sun wuce gida,duk da yanayin da zuciyarsa take ciki,yana jin cewa lokaci yayi da ya kamata yayi wani abu a kai,amma baisan yadda zai fuskanci daddy ba,bayason a irin wannan lokacin ya rasa daddyn ba tare da sun fuskanci juna ba,ba tare daya gaya masa komai ba,koda zai masa mummunan hukunci kuwa.
Karban kwandon kawai yayi yayi gaba,hakan ya sanya dole ta biyoshi a baya.
A hankali yake tuqa motar kamar wanda bashi da laka a jikinsa,motar ta dauki shuru,kowa da abinda ke kai kawo a zuciyarsa.
Ta qofar gidan motarsu ya gara a hankali zata wuce,saita daga kai tana bin gidan da kallo,a duk sanda zasu wuce ta qofar gidan sai taji ya dauki hankalinta,sai taji matar ta fado mata a rai,sai taji tana sha’awar shiga gidan,sai taji kamar akwai wata babbar mantuwa da tayi cikin gidan wadda bata daukota ba tun ranar da suka je da mommy.
Kallonta yazo yi saboda jin yadda ko motsinta baya ji,saiya dauke kansa yana duban inda take kalla,gida ne da yasha attempting ziyartarsa amma har yau ya kasa zuwa,ko a yanzu a kullum idan yayi yunqurin zuwa sai wani abu ya dauke hankalinsa,bai sani ba ko tana kallon gidanne saboda tana tuna rakiyar data taba yiwa mommy?.
“Kina kewar gida ne?” Ya jefa mata tambayar cikin ba zata,abinda ya dauki hankalinta harta waiwayo ya dubeshi,suka hada idanu,saiya maida kansa ga tuqin da yakeyi.
Shuru tayi ta kasa bashi amsa,sai qas da tayi da kanta,maganar ma ace tana kewar gida ai bata baki ne,taje gida taga ummanta da habibanta wannan shine babban burinta,to amma a irin wannan yanayin da take ciki,shin kyautawa ce ta nisanci jawahir daya kasance ita ke bata baki da kwantar mata da hankali?,ko kuma dai dai ne tayi nesa dashi din?,wanda bashi yake da buqatar ganinta ba,zuciyarta ce keda buqatar gani tare da sanin halin da yake ciki.
“Ki shirya zansa gobe a kaiki” idanunta ta lumshe da sauri,wannan shine furucin data jima tana son ji daga bakinsa,saidai yazo a lokacin da ba zata iya tafiya gidan ba
“Bazanje yanzu ba…..ba yanzu ba” ta furta da lallausar muryarta da har kwanan gobe yake mamakin zaqinta,maganar tata ta daure masa kai,baiyi shuru ba ya tambaya
“Saboda me?” Sai data danyi jinkiri sannan ta amsa masa
“Sai Allah ya bawa daddy lafiya” sosai maganar ta dokeshi ta kuma bashi mamaki,ya waiwaya yana duban sashen da take,kafin ya maida kansa zuwa titi,dai dai lokacin kuma ya fara qoqarin taka birki saboda matar dake gabansu,saidai abun mamakin,duk yadda yayi qoqari ya taka burkin abun yaci tura,hankalinsa yadan tashi,yayita yunqurin tsaida motar amma bai cimma nasara ba,har sai da tayi gab da motar sannan ya samu nasarar tsaidata.
Gefen titi ya gangara ya kashe motar gaba daya yana sauke numfashi tare da godewa Allah daya sanya ba gudu yake ba,ba shakka da saidai aji mummunan labari.
Tsahon minti daya idanunsa na a rufe yana fidda numfashi tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya buda dukka idanun nasa kamar wanda aka yiwa allura lokaci guda saboda shigar wani tunani qwaqwalwarsa.
Wayarsa ya zaro da sauri kaltum na binsa da kallo,don kusan batasan me ya faru ba,ya dannan wasu numbers ya kira wani,ya masa kwatancen inda suke,yace yazo da mota akwai wanda zai dauka,sannan ya kashe ya sake kiran umar,ya bashi umarnin zuwa inda suke shima,amma ya taho masa da abdulganiy mechanic su taho tare.
Wayar ya ajjye,ya bude motar ya fita zuwa waje,zuciyarsa na hasaso masa al’amura da dama,tabbas idan hasashensa gasky ne to akwai lauje cikin nadi,tabbas there is something he needs to know,ya gayawa kansa yana gyada kai.
Motar daya fara kira ita ta fara isowa,saiya yiwa kaltum umarnin ta shiga,tana iya hangen fuskarsa koda bayan barinsu wajen,yanayin fuskarsa ya sake sauyawa fiye da yadda suka baro asibitin,wanda ita batasan silar afkuwar hakan ba.
Dukka motar ya bude bayan isowar umar da bakaniken kamfaninsu
“Ka duban min ita da kyau,ina cikin tafiya na laluba birki naji babu” cewar samir,wanda ke tsaye yaui folding hannayensa a qirji
“Ok sir” abdulganiy ya amsa masa yana nufar motar.
Daga shi har umar bin abdulganiy suke da kallo,har ya gama bincikensa ya dawo inda suke tsaye
“Birkinka aka kwance maka sir” ya amsa masa da gurbatacciyar hausarsa.
A mamakance suke kallonsa,umar ne ya motsa baki
“Kamar yaya?” Ya tambaya yana tsareshi da idanu
“Eh haka nima na gani,kusan awa daya kenan da tsinkeshi,alamu sun nuna bawai ya tsinke bana a kan kansa ba”.
Kai samir ya jinjina,sannan ya dakatar da abdulganiy
“Shikenan….umar,ka kira hashim yazo ya dauki motar ya biyomu da ita garage din company…..muje can,ka duba min motar daddy dake aje wajenku,inason sanin abinda ya sameta itama”.
Cikin qananun mintuna suka isa company din,wanda kusan amiru ne yake gabatar da komai,don bashi da cikakkiyar nutsuwar zama cikin office dinsa.
Ta qofar baya ya sanya suka shiga,saboda baya buqatar kowa yasan cewa ya shigo din,sannan suka wuce inda suke ajjiye tsofaffin tractors dinsu,inda aka ajjiye motar daddy bayan an daukota daga inda abun ya faru.
Yana tsaye jikin wata mota still hannayensa goye a qirjinsa sanda abdulganiy ke yiwa motar binciken qwaf,tsahon awa kusan guda kenan kafin ya fito,ya hada gumi saboda aikin,yana share zufa ya masa bayani
“Itama tsinkewar birki ne,saidai na kasa tantance tsinkawa akayi koda.kansa ya tsinke,duk da dai gaskiya duba da lafiyar motar,da kuma ‘yan watannin da tayi bata jima ba,nake ganin kamar shima kwanceshi akayi,amma ba lallai ne hakan ya zama gaskiya ba”
“Ya salam” ya furta yana yin qasa da kansa,tabbas…..babu ko shakka haka na nuni da cewa akwai wadanda ke farautar rayuwarsu,shi da daddyn kenan?,xai iya yiwuwa da duk wani wanda yake kusa dasu?,lallai ya zama dole yayi wani aiki,ya zama dole ya aiwatar da wasu abubuwa,don haka bai iya amsawa abdulganiy ba ya fara takawa yana ficewa daga warehouse din yana zaro wayarsa daga aljihunsa.