Dabi’ar Zuciya 51
51
D/Z
Tana sake matsawa kanta da tambayar tana sake jin maqogoronta yana bushewa,wanda ya sake tabbatar mata da cewa ruwa take da buqatar sha,cusa hoton ta kuma yi qasan filon,ta miqe jikinta na rawa a hankali cikin sanda ta doshi falon.
A hankali ya murda qofar falon ya turata kana ya shigo,jikinsa ko ina yana fidda zufa saboda mafarkin da yayi,babu abinda yake da buqatar sha illa ruwa,sanda ya niyyaci shan ruwan,saiya taras babu komai a fridge din sashen sai drinks,wadanda ba zasu kashe qishirwar da yakeji ba sam.
Idanu ya zuba mata daga nesa cikin mamakin ganinta a dai dai wannan lokacin,duk da cewa babu wadatar haske sosai a falon amma ya ganeta sosai,baqin gashinta daya ware ya sauka a bayanta yanata qyalli,ci gaba yayi da takowa a hankali yana nannade hannayen rigarsa ko zaiji raguwar zufar dake sauka a jikinsa.
Da hanzari take zuba ruwan cikin cup tana daga tsaye a bakin fridge din bayan ta budeshi,alamun takun sawayen da taji ya sanyata firgita sosai,hakan ya sabbaba mata tsoron daya tilasta ruwan da robar faduwa gaba daya a qasa ruwan ya soma malalala a qafafunta,sannan ta waiwayo tana duban bayanta.
Fararen idanunta sun fito tarwai wadanda suka cika da tsoro,tsoron daya bashi mamaki,saiya qarasa gabanta a nutse,ya sunkuya ya dauke ruwan kana ya dago yana duban tsakiyar idanunta,fuskarta tayi wani fayau, fresh babu komai saman fatarta,gab suke da juna har suna iya musayar numfashi,still yana kallonta a tausashe muryarsa can qasa maqoshinsa yace
“Wannan tsoron fa?” Qas tayi da kanta tana son dai daita kanta,tana kuma jin nauyin yadda yake tsaye gab da ita,ta fahimci kuma idanunsa na yawo ne a kanta,har zuwa qirjinta da maballan rigarta guda biyu na sama suke a bude,hakan ya bawa qirjin nata damar fitowa kadan ta saman
Ganin ta kasa cewa komai saiya dauki wani cup din daga saman fridge din,a hankali taji ya kama hannayenta,ya sanya mata cup din a hannu days,daya hannun kuma robar ruwan bayan ya budeta,dora hannayenshi shima yayi saman nata hannayen,ya tayata riqe cup din da robar ruwan,suka fara tsiyaya ruwan a tare,kowannensu idanunshi na ka robar da cup din,saidai kowa da abinda zuciyarsa ke saqa masa.
Sai daya cika shi da ruwan sannan ya tayata daga cup din zuwan bakinta ta hanyar ci gaba da dafe bayan hannunshi cikin tafi hannunta,a hankali take aika ruwan daga bakinta zuwa maqogoranta cikin wani yanayi,sanyin ruwan na kai mata ko ina,jikinta na mutuwa saboda wanzuwarsa a wajen.
Rabi tasha tadan janye shi daga bakinta,ta tsammaci zai sake mata hannu ne amma sai taga ya sake sauke hannun nata tare da sake zuba ruwan ya kuma cika cup din,wannan karon bakinsa yakai ruwan,ya fara sha shima a hankali, Adams apple dinsa na sama da qasa,yayin da idanunsa masu haske da girma ke zube cikin nashi,qas tayi da kanta,tana ji ya gama shan ruwan,ya zare hannunsa cup din da kuma gorar ruwan gaba daya ya ajjiye.
Bata ankara ba taji ya kama tsintsiyar hannunta,haka kawai.mafarkin ya birkita shi,yaji yana da buqatar wani abu da zai daidaira bugun numfashinsa,yana buqatar wanda zaiji yadda zuciyarsa take bugawa,sai ya sake taku sosai ya hade jikinsa da nata,hakan bai masa ba,sai daya dora qafafunta saman nashi,hakan ya qara mata tsaho,sai taji ya zagaya hannayensa zuwa bayanta ya rungumeta gaba daya cikin jikinsa.
Qamshin turarensa laushin fatarsa da dumin dake fita daga jikinsa da kuma ba zatar da yayi mata yaso tafiya da numfashinta gaba daya,bugun zuciyarsu ya cakuda waje daya,kowanne a cikinsu yana iya jin yadda zuciyar dan uwansa ke bugawa da wani irin gudu.
Numfashi mau nauyi ya dunga saukewa ajere,a hankali a hankali har zuwa wani lokaci,cikin jikinta ta karan kanta ta dinga jin wata nutsuwa,kamar yadda shima nutsuwar ta dinga ratsashi ta kowanne sassa na jikinsa,nutsuwar da bai taba jin kamarta ba duk sanda yayi irin wannan mafarkin
“Me ya tsorataki?” Ya kuma jefa mata tambayar cikin wata murya dako a falon kake baka isa kaji abinda ya fada ba,saboda wani feelings dake tsarashi,yana iya jin tudun komai na jikinta a jikinsa
“Mafarki nayi”
“Na umma?,ko na bilal?” Tambayar data sosa mata wani tabkeken miki dake danqare a zuciyarta,wanda dare da rana taketa qoqarin ganin ta sayashi,kiran sunan da yayi ya shiga sosai cikin kunnenta,ya kuma motsa zuciyarta,duk da mafarkinta bashi da alaqa da umman,amma sai taji a take hankalinta ya karkata zuwa gareta,hakan ya bawa hawaye damar taruwa cikin idanunta,cikin qanqanin lokaci kuma suka fara sauka saman fuskarta.
Batasan yadda akayi ya fahimci ta soma kuka ba,saidai hannunsa data ji saman fuskarta yana share mata,batasan cewa yaji sauyin fitar numfashinta da bugun zuciyarta ba,yana sharemata yana runtse idonsa,akwai wani abu daya sanyashi ya zama qwararre wajen gane fitar hawaye ba tare daya kalli fuska ba matuqar a jikin mutum yake,hawayen AMMAnsa,daya daga cikin abinda yasa ya tsani kukan mace,abu guda daya dake sanya rauninsa bayyana.
Yana da burin kaita gida,a yadda aqarta take da yan uwanta da mahaifiyarta yasan cewa tayi namijin qoqarin zama har zuwa wannan lokacin bataga kowa nata ba,bayan an daukota a lokacin da take tsaka da jinyar rashin dan uwanta,to amma a wanne matsayi take?,wacce amsa ce gareshi na matsayinta a wajensa?,MATA KO QANWA?.
**********Tunda drivern ya daukota takejin wani farinciki cikin ranta,kammaluwar jarabawarta cike da alamun sa’a da nasara,nan bada wani jimawa ba zata tsinci kanta a ajin qarshe na secondary,abinda bata taba mafarkin kasancewarsa kaf tsayin rayuwarta,tafi mafarkin gata can gidan nasuru,gatacan a matsayin matar nasurun,sai gata yau cikin wata mota da take hange a baya daga can qololuwar nesa,bata taba sha’awar hawanta bama saboda tasan ba zata hau ba.
Abu daya ne a yazu yake dan motsa mata,daga sanda ta fara karatun litattafan nan ta gane meye aure?,meye ma’ana da manufar aure?,tun daga ranar daya fara rungumeta cikin jikinsa yabar mata wani abu,ya kuma dauki wani abu daga zuciyarta yayi gaba dashi,to amma ta ina zata fara yaqi da qoqarin karbarwa kanta matsayinta?,wannan shine matsalar da takeji lokaci zuwa lokaci tana motsi a zuciyarta.
Yana tsaida motar ta fito zuwa cikin gida,tana da masaniyar gobe zasu wuce azare kamar yadda ya shaida mata cikin wancan daren data yi masa kyakkyawar ajiya a zuciyarta,don haka tana son hada komai nata aka tsari,ta ciri kayan da take da buqata cikin siyayyar da yayi mata wancar ranar.
Ta saba duk sanda zata shiga waje tayi sallama koda babu kowa,yauma sallamar tayi,duk da tasan mawuyacine ta samu masu aikin cikin falon.
Ga mamakinta sai taji an amsa mata,abinda ya daure mata kai kenan,ta maida dubanta ga wajen da taji an amsata din,sai suka hada ido da mubina tana sakar mata murmushi
“Sonshi nake da gaske jawahir,ko zaki taimaka min?” Kalaman mubina a ganinta da ita na qarshe ya dawo mata,hakanan taji yawan farashin fara’ar da takeson maida mata ya ragu,yaqe taji tana mata,amma duk da haka saita dakata suka gaisa kamar yadda suka saba
“Hajiyan suna azare gaba daya” kaltum ta gayawa mubina tana miqewa bayan ta dauki takardunta
“Eh na sani,ai har mama itama tana can,tare suka tafi,kinsan mama aisha kishiyar yayata ce,ni kuma a hannun yayar tawa nake” dan dubanta kaltum tayi ta gyada kai kawai
“Dama ba wajen hajiya nazo ba ai wannan karon….wajen ya saraki nazo,ancemin yana gidan nan ko?,na taras ana masa gyara ta can bangarenshi na gidan daddy professor”
“Eh…..bari na qarasa ciki” kaltum ta amsa mata a gaggauce kawai,wanda sam mubinan bata kula ba,saita miqe
“Tun dazu nake zaune ba abokin hira,tunda kin dawo muje tare,na samu abokiyar hira” bata hanata ba kamar yadda batace mata komai ba,ta bita a baya tana mata surutu,nata eh ko a’ah.
Da suka shiga dakinma bayan ta aje jakarta bandaki ta wuce,sai tayi tsaye gaban mudubi tana kallon smoothy skin dinta cikin dan qaramin hijabin makaranta dake jikinta,fararen idanunta take kalla tana son gano ko akwai wani abu daya bayyana cikin idanunta?,wani abu take ji ya tokare mata wuya tunda taji me mubina ke fadi?,to me kenan hakan?,tana da tabbacin mubina batasan wace ba ita ba,batasan alaqarta dasu hajiya qarama ba,hakanan batasan matsayinta a wajen muhammad samir ba.
Kayanta ta cire kawai gaba daya tayi wanka,ta fito,tana shiryawa mubina na janta da hirarraki,tana da zaton akwai dangantaka tsakanin kaltum ne dasu jawahir,dangantakar da zata iya taimaka mata ta samu waje a zuciyar samir.
Koda ta gama shiryawa ma hada kayanta ta fara yi,har zuwa sannan mubina nata binta da hira,ita kuma tana qoqari qwarai wajen amsa mata ba tare data yarfa ta ba,duk da zuciyarta na mata wani iri babu dadi.
“Wai tare zaku tafi?,ai kuwa inajin dani za’ayi tafiyar nan” mubina ta fada tana dariyar jin dadi,murmushi kawai kaltum tayi mata,saita miqe daga aikin tana dosar qofar fita tayi kitchen.
Ba kowa a kitchen din,da alama sun gama aikinsu ne sunfice,tasan tazarce sukayi abincin,haka suke yawancin lokuta da hajiya qarama bata nan,sai taji sha’awar shirya masa abinci,don tunda yazo gidan bataga ya zauna yaci wani abincin kirki ba,hakan ma zai taimaka mata ta rage lokacinta sosai,ta kuma rage zangon hirarta da mubina.
A nutse ta fiddo komai ta fara aikinta cikin nutsuwa,cikin wani yanayi me burgewa na tsafta da sanin makamar aiki.
,bata jima da farawa mubina ta biyota,ta sanyata a gaba da hirar da sam ita bata jin armashinta.
Har ya gota sassan hajiyan qaraman sai ya dakata saboda jin qamshin favourite food dinsa,da baya ya koma a hankali yake takawa zuwa ciki,fuskarsa na ga fuskar wayarsa sanda jauhar ke kiransa,ya maidata silent ya sanyata a aljihunsa,kwata kwata baya qaunar wannan nacin kiran nata ko yaushe ba tare da wani specific time ba,baisan me take nema haka dashi ba.
Sallamarsa qofar falon tayi dai dai da qaruwar bugun zuciyarta,ta daga kai daga yanka lettuce din da take tana taya mubina da tuni ta saki hirar ta maida hankalinta kanshi amsa sallamar da yayi
“Ya saraki….sannu da zuwa” mubina ta fada taba murmushi gami da miqewa tsaye
“Yauwa,ya kike?” Ya tambayeta a gajarce,idanuwansa nakan kaltum dake kallon qasa,dankwalinta ya zame kadan,kwantaccen gashin gaban kanta ya fito sosai saman chocolate colour skin dinta
“Sannu da zuwa” ta fada tana qoqarin dai daita heart rate dinta ba tare data iya duban idanuwansa ba
“Yauwa,sannu” ya fada yana duban kitchen din,alamu sun nuna masa cewa itace keyi girkin,agogon hannunsa ya kalla
“Ana gama sallar magarib a kawomin abinci” ya fada yana lalubar qwayar idanunta da taqi bari ya gani
“Tohm” ta amsa mishi a tausashe,saiya juya yana niyyar barin kitchen din,da sauri mubina takai hannu xata karbi brief case dinsa
“Ya saraki….kawo na tayaka mana”
Batasan ta daga kai ta dubi sashen da suke ba saida suka kusa hada ido da samir,saita sauke kanta,tana jin wani abu na matsar zuciyarta,kunnuwanta naga amsar da xaya bata
“Nop,na gode” ya amsa mata yana yin gaba,binsa da kallo mubina tayi,saita koma da baya ta zauna jikinta na mata sanyi,kada fa ace sauqin kan da take hanga tattare dashi ba haka bane?.
Tun sanda suka baro kitchen din kowanne a cikinsu kuzarinsa ragagge ne,ga kaltum bata da tabbacin abinda ya sanya yanayin jikinta sauyawa,saidai tana jin zuciyarta da gangar jikinta duka babu dadi,hakanan ta kasa sakewa da mubina.
Mubina kuwa hasashenta daya ne,a yau din ta shirya ta kuma tattara dukkan wani qwarin gwiwarta na fuskantar samir din,a yau ta shirya shaida masa abinda yake cikin zuciyarta,durqusawa wada ba gajiyawa bace,matuqar zata samu samir a matsayin mijin aure zata iya aikata dukkan wani abu da bai taka kara ya karya ba irin wannan,bai kuma kasance kauce hanya mabayyaniya ba.
Tana saman abun salla bayan ta idar amma tayi nisa a tunani,maganganun saliha ke dawo mata tar a kwanya tun daxu,idan itace da miji irin samir kenan sai taga abinda ya turewa buzu nadi?,ita din zata iya itama kamar yadda saliha tace?,wannan tamkar tunkarar wani babban yaqi ne wanda batasan ya tsakiyarsa zata kaya ba,qarshensa dama nasara ce ko akasinta,batasan wanne matsayi take dashi ko ta taka a zuciyarsa ba bare ta dora daga nan,tafi kowa sanin yawan ‘yamnatan dake qaunarsa suke kuma farautar soyayyarsa,tun kafin ta soma jin cewa itama ya kamata ta tabbatarwa da kanta matsayinta a wajensa,tana ji da ganin komai daga wajen jawahir,wani lokaci ita kanta jawahir din takan qi daga wayar wasu da dama daga cikinsu,wadanda ke kamun qafa da ita,to amma idan ta saddaqar…..hakan na nufin zai auri wata a gabanta kenan kamar yadda ta soma jin qishin qishin?,haka na nufin warwarewar igiyar aurensu kenan?, Ta koma ta auri wani?,idan kuma qudurinta ya tabbata fa?,ta yayq zai kalli idanun family dinsa ya shaida musu cewa ita din matarsa ce daya aurota a wani qauye waishi dinya ba tare da sanin magabatansa ba?,idan maganar ta fito waye da waye zai amsheta?,waye kuma zai mata mummunan kallo da mummunan fassara?.
Samun kanta tayi da runtse idanunta sanda sunan mommy da najwa ya darsu a ranta
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil” labbanta suka motsa a hankali,kalmar ta kwarara cikin zuciyarta,sannu a hankali kuma hancinta ya cika da qamshin turaren data tabbatar a zahiri take iya jiyoshi,kafin kuma fa bude idanun nata muryar mubina ta cika kunnuwanta.
“Kaltum da magariba fa yace akai masa,nidai a ready,ki debo kayan na tayaki kaiwa,dama inason muyi magana dashi” a nutse ta daga kanta ta sauke ga mubina dake gaban mudubi tana sake fesa turare baya wancan data fesa,wani abu ya matse zuciyar kaltume,amma saita aro jarumta ta miqe tana nannade abun sallarta ba tare data cewa mubina komai ba ta fice izuwa kitchen.
Tana tsaka da harhada kayan abincin mubinan ta shigo,tayi shar cikin wani riga da skert da yadin material na mata me sulbi,sai baza qamshi take kamar tayi barin turare.
Ita tayi uwa tayi makarbiya ta amshe kwandon kayan abincin,kaltum din najin wani abu me kama da haushi yana son sauka a zuciyarta ta sakar mata kwandon,ko banza ita din macace,ya kamata kuma ta mutunta tare da martaba darajarta da mutuncinta na diya mace,bata tanka mata surutanta ba ta dauki flask na tea data hada masa ruwan zafin da bata da tabbacin zaisha tunda batasan zabinsa ba ta bita dashi.
Sanya yake da fara qal din long sleeves shirt,wandon jikinsa ash ne me turuwa,wanda iyakacinsa qauri,sun sameshi zaune da jibgin files a gabansa da alama aikin office ne ya deboshi zuwa gida,waya yake amsawa,amma idanunsa na kan qofar sanda suke shigowa.
Amsa sallamar mubinan yayi yana mamakin shigowarta sashen,saidai kafin ya dauke idanunsa ya hangi kaltum daga bayanta,sanye da madaidaicin hijabi light blue,wanda ya haska zagaggayar fuskarta,ya kuma qara fito da hasken qwayar idanunta.
Duk da amsa waya yake amma yana karantar sanyi cikin yanayinta,daga sanda yaji karatu akan girman amana gaba daya hankalinsa ya sake karkata a kanta,yana jin ashe wani babban nauyi ne akansa daya kamata ya bashi dukkan wata kulawa iyaka qarfinsa.
Ya gama wayar ya katseta yana ajjiyeta gefe,yana daga kai suna hada ido da mubina,saita saki murmushi tana sunkui da kai ita dole taji kunya.
Bai kula da wannan ba,ya fara janye hannun rigarshi zuwa baya tare da lanqwashe qafafunsa sanda take aje masa abincin a gabansa
“Sannu” ya furta can qasa,yanayin da sautin maganar ya fito ya tilasta mata daga kai ta dubeshi,saboda yayi maganar ne tamkar me rada.
Fridge ta nufa da niyyar dauko masa ruwa,sai yace
“Dawo nan ki zauna….jeki cikin gidaki daukomin ruwa mara sanyi” yace da mubina.
Dadi ne sosai ya rufeta,ta miqe da saurinta ta nufi qofar fita,saiya maida dubansa ga kaltum dake laluben wajen zama
“Dawo nan” ya fada yana nuna mata gabanshi,a sanyaye ta dawo ta zauna din inda yace mata,duk da cewa zaman kusa dashi irin haka ya mata nauyi amma ba zata iya kaucewa umarninsa ba
“Mene yake damunki?” Ya jefe mata tambayar yana bin fuskarta data dan cika ta murje da kallo kusan irin na qurilla,dan mitsitsin bakinta yana motsawa kadan kadan, Tambayar ta isketa a bazata,don bata zaci jin haka daga bakinsa ba,saita girgiza kanta
“Babu komai” ta amsa mishi,baice mata komai ba sai yaja abincinsa ya fara ci,ba jimawa mubina ta shigo da ruwan,hakan yasa kaltum miqewa tana neman izinin tafiya,don bata jin zata iya zama mubinan tayi maganar da take da qudurin yin a gabanta.
“Ki jirata ku wuce tare….uhmmm,ina jinki” samir ya fada duka lokaci daya.
Bai fasa cin abincinsa ba sanda take koro bayanta cike da kunya da kuma É—ar É—ar,saidai ya kafeta da manyan idanunsa,zuciyarsa cike fal da mamaki,yana kuma qoqarin danne mamakin da kuma dariyar data bashi har ta kammala bayananta.
Abincin ya aje gefe yana kallonta,ya karanci mata wani bin duka tunaninsu iri daya ne,basa kallon abubuwa a yadda suke,sau tari komai suna kallonsa a baibai a maimakon zahirin yadda yake
“Shekarunki nawa?” Tambayar data jita banbarakwai,saita tsargu,ta saci kallon kaltum,wadda tunda ta sunkui da kanta bata dagashi ba
“Sha….sha,ashirin” yadda ta bashi amsar ya tabbatar masa ta dan qara wani abu akan ainihin shekarunta,murmushin gefan baki ya saki
“Karki bari matata ta san ainihin abinda kike nufi ko fada a kaina,if not kuma…..saita zaneki,ku tashi kuje ku kwanta,gobe akwai tafiya a gabanmu” daga haka ya balle murfin ruwa ya soma sha a nutse.
Tuni kaltum takai qofa,saboda amsar daya bayar tamkar saqo ne zuwa ga mutum biyu kenan,wacece matarsa?,me kuma hake nufi da ita,mema maganarsa gaba daya ke nufi?,wadan nan sune ire iren tambayoyin data kwana tana yiwa kanta.
Tana iya jiyo kukan mubina bayan ta gama gayama kaltum din cewa
“Me yasa ya dauka abinda nake gaya masa bada wani muhimmanci ba?,bayan ni ina gaya masa saqo ne mai muhimmanci?” Ba zata iya cewa da ita komai ba,don itama ta kanta take,har ta gama maganganunta ta barke da kuka,tun tana jin kukan mubina har taji shuru,da alama tayi ta gaji,ko kuma bacci ya dauketa,saita sauka a hankali ta zura qafafunta qasa tayi bandaki.
Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana ture ayyukan dake gabansa,duk yadda yaso ya tilastawa kansa yin aikin abun ya gagareshi,fuskar kaltum din yake hangowa sanda mubinan ke isar mishi da saqon,yana sane ya zaunar da ita,akwai abinda yakeson gani da kuma karanta daga gareta,saidai kuma iya zamanta da tashinta taqi bashi damar komai.
Mirginawa yayi ya koma rub da ciki,yana tallafe fuskarsa da tafukan hannayensa,gami da lumshe idanunsa,yana jin yadda sukayi masa nauyi saboda baccin da ya cikasu,amma zuciya da qwaqwalwarsa sunqi bashi hadin kai.
Saidai shi bacci ba’a ci masa bashi,kamar yadda ba’a qayyade masa lokacin yinsa,a hankali idanunsa suka dinga rufewa har sukayi nauyin da bazai iya budesu ba,ya lula duniyar bacci.
*_DUNIYAR MAFARKI_*
A firgice ya farka,saidai bakinsa dauke da addu’a,a hankali yake karanto addu’o’in da ma’aiki ya bayar ga duk wanda yayi mafarki mara dadi,saiya miqe ya nufi bandaki,idanuwansa na haska masa fuskar mahaifiyarsa da yake gani tsugune a gefansa,tana kuma masa nuni da mahaifinsa dake tafiya zuwa wani wawakeken rami wanda wuta ce fal keci a cikinsa.
******Babu wani cikakken kuzari a jikinta take qarasa hada jakar kayanta,banda hajiya qarama da jawahir da suka damu da zuwan nata da babu inda zata.
“Ya na ganki a zaune?” Kaltum tayi qarfin halin yiwa mubina magana sanda ta dauki jakarta bayan samir ya aiko a shaida mata ta fito,kaita girgixa qwalla na sauko mata
“Bani da nutsuwar da zan iya binku,saikun dawo” bata iya ce mata komai ba ta soma takawa tana ficewa,mafarkinta na jiya na sake tsaya mata sosai a rai,duk kuwa da cewa kusan maimaici tayi na abinda ya faru a mafarkinta na wancan karon,amma abun sai ya tsaye mata a rai fiye da wancan.
Ga hoton matar har yanzu a wajenta,amma bata da wanda zai gaya mata wacece ita?,ta kasa fassara ma’anar yawan ganinta da takeyi cikin barcinta,saidai a yanzu zuciyarta ta karkata da zuwa gidan masu lalurar tabin hankali taje ta ziyarci matar data gani a gidan,wadda take mata kama da.matar dake zuwa mata a mafarki,duk da cewa waccar ta gida masu lalurar tabin hankalin shekarunta sunfi na wadda take cikin hoton da kuma wadda take gani a mafarkin tsufa……..