Dabi’ar Zuciya 50
50
DZ
Wani littafin ta sake karba wajen salaha,tanaji suna mata tsiya amma batabi ta kansu ba,ita kadai tasan yadda take qaruwa da karatun da takeyi din,wanda ya haska mata abubuwa da dama
“Husna muje tare mu taru napep,nima yau mai daukan nawa baya kusa” kaltum tace da husna,saida husnan ta tsaya ta siya agwaluma daga bakin makarantar sannan suka soma takawa zuwa bakin titin
“Nikam husna…..wata tambaya nakeson yi miki”
“Duk yadda kike ja kaltum?,kece fa kike daukan 1st position a ajinmu duk term” kafadarta kaltum ta daka tana murmushi me kama da dariya
“Ke dalla,ba akan karatu bane,wannan karatun kun fini ilimi ta fanninsa” murmushi tayi mata itama tana gyara saqalen jakarta
“To ina jinki,ai wai don karki qureni ne” sukayi dariya gaba daya,sannan shuru ya biyo baya,kaltum din cikin ranta tana juya yadda zata gabatar mata da tambayar,tsahon wasu mintuna sannan tace
“Asa misali kece kika tashi cikin rayuwar rashin wadata,baki da ilimi kyau ko arziqi,kwatsam sai Allah ya kawo wani kyakkyawan matashi,wanda ya fiki kyau kudi ilimi dama wayewa nesa ba kusa ba,irin nesan nan can can can,kawai tausayinki yasa ya aureki,yazo ya ajjiyeki a gida,ba abinda ke hadaku,kuna zaune kamar yaya da qanwa……”
“Wai,wanann shi ake kira da tsintar dami a kala” husna ta katse kaltum na tare data bari kaltum din takai qarshen maganar ba,tana ta murmushi tare da sake bawa kaltum hankalinta.
,ganin yadda husnan ta bawa zancan muhimmanci hakan ya bata nutsuwar ci gaba da magana
“A hankali kuna zaune kika fahimci yadda mata ke rububin sonshi,da kika lura da kyau,sai kika gane bayan dukka wadancan siffofi…..yana da kyawawan dabi’u kuma”
Hannayenta sama husna ta daga
“Wallahi ta fadi gasassa…..wannan mata idan nice sai inda qarfina ya qare wajen janyo hankalinsa ta dukkan wata hanya data dace,duk namijin da ya hada wadan nan siffofin tabbas babu shakka ya isa,ya kuma cancanci a soshi,rasashi kuma babbar hasara ce” maganganun da suka sanya kaltum nazari kenan,tayi shuru tana sauraren yadda husna keta wassafa kanta cikin lamarin har suka qaraso titi.
Tsaki yaja a hankali yana rufe file din gaban nasa,tare da dora bironsa akai,ya maida bayansa ya jingina da kujerar yana relaxing a jikinta,kana ga furzar da iska me dumi daga bakinsa,a hankali kuma ya soma juya kujerar daga hagu zuwa dama,daga dama zuwa hagu.
Tun daga lokacin har kawo yanzu ya kasa jin qwarin jikinsa kwata kwata,yanajin kowacce jijiya ta jikinsa ta zama weak,ya dunqule hannunsa waje daya kamar wanda ya boye wani abun yana kallon hannun,jijiyoyin dake tsintsiyar hannun sun tashi rada rada,har yanzu yana iya tuno laushi da dumin fatar cikinta,tun a lokacin jikinsa ke shaida masa da matsala,amma burinsa na ta samu relief na pain din yasa yaci gaba da abinda yakeyi.
Idanunsa ya lumshe,saiya dinga gano fuskarta wadda bayan ta gama jigata bacci ya dauketa har sai da kanta ya karkace,shi ya gyara mata kwanciya amma har ya gama yabar dakin batasan anyi ba.
A hankali aka tura qofar, secretary dinsa ya bayyana yana shaida masa neman izinin shigowa da fawwaza keyi,shuru ya danyi,sam baison hayaniya yau din,a niyyarsa yace ya shaida mata yana da ayyukan da yake dubawa,kuma suna da muhimmanci da kuma buqatar nutsuwarsa,saidai kafin yakai ga furtawa har ya hangi fawwazan tsaye daga bayan secretary din,da alama a shirye take ta shigo koda bai bata dama ba,don haka yace
“Ok, let her” ya fada yana tura kujerarsa baya,sannan ya miqe tsaye yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa kafin daga bisani ya fara takawa cikin nutsuwa zuwa sashen da fridge dinsa yake.
Tunda ta shigo ta kasa zama,ya bata baya amma kallo take qare masa,tako ina samir din yakai namiji,tana jin sonsa yakai mata ko ina cikin rai da rayuwarta,amma ta fuskanci har yau ya kasa gane hakan.
A duk sanda zata dauko maganar saiya sako wani abun da zai kauda gaskiya da kuma qarfin maganar a ranta,ta rasa me zata masa ya tabbatar masa da dukkan abinda take fada da nunawa a kansa gaskiya ne?,tun tana ja masa aji da kuma shan qamshi,har ta daina ta sauko,da a tunaninta baiwar kyan da Allah yayi mata da iya gayunta kawai sun isa suja mata ra’ayin saraki,saidai kuma a hankali ta gane cewa tayi bahagon tunani ta kuma canki kuskure.
“Have a set” ya furta bayan ya juyo dauke da kwalin lemo da kuma cup yana nuna mata empty kujerar dake gaban table dinsa,saita dauke kanta a hankali ta qarasa ta zauna.
Gaban kujerarsa ya tsaya ba tare daya zauna ba yace
“Allah yasa lafiya” yana dan kurbar lemon kamar wanda aka yiwa dole,fuskarta fal da damuwa ta girgiza kai
“Ba lafiya ba samir,kuma babu lafiyar sam a tattare dani?” Dukka girarsa ya dage bayan ya dakata da shan lemon,abinda yayi masa kyau sosai
“Me ya faru kuma?” Kai take kadawa tana hadiye wani abu
“Hakafa….haka kullum kake pretending kan cewa bakasan komai ba,baka gane komai ba,bayan na maka bayani basau daya ba basau biyu ba,to yau zan gaya maka baro baro, Muhammad samir sonka nake,ni fawwaza ina sonka” a hankali ya sauke cup din hannunsa saman table din,tabbas yana daga cikin tsarinsa mace tace tana sonshi,irin hakan idan ta faru yasan cewa zai samu dukkan wata kulawa fiye da yadda yake da buqata,gidansa kuma zai sarrafu fiye da yadda yake tunani ko hange,saidai kuma bata wannan sigar da fawwaza tazo da ita ba,abu na farko totally fawwaza batayi masa ba tako ina,sannan yasan waye mahaifinta sarai,bashi da sha’awar hada zuri’a dashi.
“Da farko dai nan wajen aiki ne,ba muhalli bane na irin wadan nan maganganun,amma inaso na fara da gode miki kan qaunata da kikeyi,naji dadi na kuma yaba miki,amma ina me baki haquri…..am sorry to say…..na fitar da matar aure,yanzu haka kwanaki kadan suka rage a saka ranar aurenmu,ina mai baki haquri akan hakan,tare da miki addu’ar samun miji na gari” sam batasan sadda ta barke masa da kuka ba
“Ya salam…..mene haka?” Samir din ya fada,iyakar qoqarinsa don tayi shuru amma taqi,kuka take sosai tare da fadin dukka abinda yake zuciyarta,har sai daya zauna saman kujerarsa,ya tsiyaya sassanyar lemo ya tura gabanta
“Sha wannan sai muyi magana” tana goge qwallarta ta dauka tasha kadan ta ajjiye
Cikin siga ta lallashi ya soma magana
“Banga abinda zaisa hankalinki ya tashi ba,bayan a cikin maza nidin ba kowa bane,akwai dubban maza da suka fini komai da komai,don na gaya miki hakan ba yana nufin yankewar rayuwarki ba,idan kikayi haquri kikabi komai a hankali sai Allah ya kawo miki wansa ya fini komai da komai…..”
“Ba ruwana da kowa,ni kai nakeso” ta fada zuciyarta na sake yin zafi .
Sake birkicewa tayi gaba daya,daga qarshe ma tana kukan ta zari muqullin motarta ta ficw daga office din,kiranta yake amma taqi saurararsa gaba daya.
Ya tabbatar tuqi zata je tayi a hakan,kuma idan tayin a yadda take din komai na iya faruwa,don haka ya koma da sauri,ya dauki wayarsa ya kira umar,ya bashi umarnin ya tabbatar yayi qoqarin settling komai,sannan ya kife wayar ya koma ya zauna yana fidda iska daga bakinsa,hannunsa saman kansa yana shafashi kadan kadan.
Ya jima zaune a hakan,kafin yaja qaramin tsaki ya miqe a hankali,yana jin jina qaramar qwaqwalwa da kuma wauta irin ta wasu matan.
Dukka abinda yake da buqatar wucewa dasu gida ya tattare ya fice daga office din.
Duk da cewa hankalinsa a rabe yake,amma hakan bai hanashi ganin alamun wahalar abu hawa ba,saboda yawaitar jama’a tsaye a bakin tituna,baisan ya akayi ba,saiya tsinci kansa da sauya akalar motarsa zuwa hanyar makarantarsu kaltum,bayan ya duba lokaci.
Tsaiwarsu basu rufa minti biyu ba ta hangi bullowar motar,da fari harta dauke kai saboda bata taba kawowa kanta shine din ba,amma sai taji zuciyarta nason tabbatarwa,hakan yasa tadan bi motar da kallo.
Sai daya tsaya gabansu ya rage tsayin glass din sannan ta tabbatarwa kanta shine.
Da idanunsa ya mata nunin ta shigo,kamo hannun husna tayi,tana sarrafa wanne suna zata bashi wajen husnan,har tayi ta maza duk da batason tafiya tabar husnan kada taga rashin kyautawarta,hakanan batason azarbabin cewa tazo suje tare
“Husna,yaya na ne yazo”
“Ayyah to sai ranar final kenan?” Kai ta gyada bayan ta mata sallama,ta bude gida gaba ta shiga.
Yana zaune sosai kam seat dinsa,ya cire ‘yar saman suit dinsa ta farkon da takalmin qafarsa,saidai har yanzu mayen qamshin nan nasa na manne da motar kamar wanda ya fesa turaren yanzu bawai tunda safe ba
Taja murfin motar a hankali ta rufe,sannan ta fara gyara rigarta tana dan janta kadan don ta rufe mata cinyoyinta sosai yadda zataji dadin zaman.
Dubanta yayi suka hada ido,kowa ya dauke kanshi,ya tayar da motar suka soma tafiya.
Ya a faka motar ta fita zuwa cikin gidan,saidai kamar yadda yace dinne babu kowa cikin gidan sai ma’aikata,don haka tana ajjiye jakarta ta soma neman biban cikin gidan,bata ganta ba,saboda haka ta nufi dakinta.
Kadan ta tura qofar,sai taji kamar ana kuka,don haka ta leqa da kanta ta yadda zata iya hango cikin dakin.
Biba ce,zaune saman carfet,hannunta riqe da hoto,data duba sosai sai taga hoton nan ne dai data saba ganinta riqe dashi,hoton da har yau bata taba katarin ganin fuskar waye ba.
A hankali taga ta ajjiye hoton,ta miqe ta nufi bandaki,ta tura qofar bandakin ta shige.
Qarasa tura qofar dakin tayi,ta shiga a hankali har ta isa inda biban ta tashi,idanunta suka sauka kan hoton,ta miqa hannu a hankali ta dauka.
Kyakkyawar macace wadda a qalla zatayi shekara talatin da takwas zuwa arba’in,wankan tarwada mai dogon hanci da manyan idanuwa,kanta babu dankwali sai qananun kitso da aka yiwa sassalkan gashinta,tana sanye da atamfa dinkin riga da zani,rigar mai kwala ce,irin dinkin mutanen da,fuskarta a wadace da murmushi,har wushiryarta tana fitowa,kana kallonta kasan macace ‘yar kwalliya da son ado.
Sosai ta zubawa hoton idanu,fuskar na mata yawo a qwaqwalwa,tana jin kamar tasan fuskar,kamar ta taba haduwa da me irin kamannin,amma ta gaza gano a ina?.
Motsin fitowar biba ya sanyata saurin tura hoton aljihun rigarta cikin firgici da tsoron kada ta ganta,da murmushi tambayar kaltum din yaushe tazo,tace yanzun nan,tana takawa zuwa inda ta ajjiye hoton gaban kaltum na faduwa,cikin ikon Allah daya daga cikin ma’aikatan ta turo qofar,tace tazo maza mummy ta kira wayar gida tana nemanta,saita dubi kaltum
“Muje ki tayani rubutawa,wasu abubuwa takeson a siya mata a baku ku tafi mata dashi”
Da to ta amsawa biba,ta kuma bi bayanta gabanta nata faduwa.
Sam ta mance da cewa ta taho da hoton,sai bayan ta koma gida,tana hada uniform din xata sanya cikin laundry basket ta zaro shi,komawa tayi ta zauna tana sake nazarin hoton
“Tabbas tasan fuskar,ta taba ganinta,amma ba zata iya tunawa a ina ba,to amma ya meye alaqarta da matar da har zatasan fuskarta?,bayan idan bata manta ba,biban ta gaya mata cewa ‘yar uwarta ce data rasu,wadan nan abubuwa biyu yasa ta saddaqar bata santa din ba,saita cusa hoton qasan pillow dinta,ta gama dukka shirin kwanciyarta,saita janyo ledar da saraki ya bata a dazu bayan ya sake dakkota daga gidan mummy sun dawo gida.
Murmushi ta saki bayan ta gama kallon kazar,saita tuna sanda hannayensu suka hadu waje daya sanda yake miqa mata kazar,ita ta fara zare hannunta saboda wani yarrr dataji,saiya aje mata ledar daga gefanta.
Gasashshiyar kaza ce da chips a ciki,kadan taci ta rufe,ta kwanta,tun tunani kala kala na bijiro mata har bacci ya saceta.
_DUNIYAR MAFARKI_
Sannu a hankali take takawa cikin sanda tsakiyar hanyar dake dauke da dakuna hagu da dama,hanyace mai duhu sosai,sai wani dan siririn haske data hangowa daga can gabanta kadan.
A hankali take dosar hasken,harta cimmasa,qofa ce yar siririya sosai,sai taga kamar jikinta bazai iya shiga ta qofar ba,don haka ta koma ta window,tayi dage ta leqa cikin dakin,fetal hake dauke da gado guda daya,sai wata mace dake zaune kanta a qasa,kamar matar tasan ta tsaiwarta a wajen ta daga kanta a hankali tana yaye rufin mayafin data lullube fuskarta dashi,sai suka hada ido.
Tarwai taga fuskar matar,kamar matar rannan ce,ta sake duban dakin,kamar dakin rannan ne shima,saita maida kallonta ga matar,sai taga ta zuba mata idanuwa qurrrr,wanda daga bisani kuma hawaye ya fara fita daga idanuwan matar shar shar babu qaqqautawa,a hankali kuma sai hawayen suka fara canza kala kamar kalar jini,ta miqe a hankali matar ta tako zuwa inda take tsaye hawayen naci gaba da fita daga idanunta.
A bakin window din ta tsaya,ta daga hannunta ta dorashi saman nata hannun,take kaltum taji wani irin sanyi yana shiga jikinta ta kowacce gaba dake jikinsa.
Ci gaba da kallon juna sukayi ita da matar,ta bude baki tana magana amma kaltum din bata iya jin abinda take fada,gashi dai a haka bakinta yana motsawa sosai,magana takeyi amma bata iya jin koda harafi guda
“Kaltum!!!” Taji an qwala kiran sunanta daga bayanta,sai tayi maza ra waiwaya,mummy ta gani tana nufota da sassarfa,sai taji ta zame daga dagen da takeyi,data daga kai kuma sai taga babu wannan matar daga gabanta,babu komai a gabanta sai wani mutum dake tsaye,shi kuma bata iya ganin fuskarsa sai bayansa
“Samir!” Taji bakinta ya kira da mugun qarfi,wanda sautin kiran ya shiga kunnenta ya kuma farkar da ita daga nannauyan baccin da ya dauketa.
A mugun firgice ta tashi,zuciyarta na bugawa da sauri kamar wadda tayi tsere,haki ra fara yi tana maida numfashi,qirjinta yana dagawa,ta fara bin dakin da kallo,babu abinda ya canza,yadda ta kwanta haka komai yake,hatta qwan fitilar da bata kashe ba yana nan a hakansa a kunne
“La’ilaha illal lah,wahdahu la sharika lah,lahul mulku wa lahul hamd,yuhyi wa yumitu wa huwa ala kulli shai’in qadir” ta dinga maimaitawa qasa qasa a hankali.
Sannu sannu taji nutsuwarta na dan dawowa,tasa hannunta a hankali ta zame dankwalin kanta saboda gumin da takeji,maqogoronta ya bushe sosai,don haka ta zame daga gadon da niyyar sauka,hakan yasa pillow din data tada kanta dashi ya biyota saboda santsin zanin gadon.
Duqawa tayi ta daukw pillow din,idanuwanta suka fada kan hoton data cusa anan kafin ta kwanta,idanu ta zuba masa sosai,kamar yanzu ta fara ganinsa,take jikinta yayi sanyi ta koma dirshan ta zauna,saboda sak kamannin matar da tayi mafarkinta a yanzu su take ganin a wannan fuskar dake jikin hoton
“WACECE ITA?” Tambayar data yiwa kanta kenan,wadda bata da amsarta,batasan ma inda zata samu amsar ba,tabbas!,akwai wata a qasa,wannan hoton shike saka biba kuka,kukan da biban tace matuqar ta gayawa wani tana yinsa to rayuwarsu na cikin barazana,barazana a wajen wa?,wa zata tambaya ya gaya mata wacece wannan matar?,meye hadin mommy da ita har da zata bayyana cikin mafarkinta?,me yasa suna sa siffar samir suka fito cikin mafarkin?,kukan me matar takeyi bayan biba tace mata ta mutu?.
Miqewa tsaye tayi wani abu na dawo mata,dakin dataga matar shine dakin dataga wannan matar randa ta raka mommy gidan masu tabin hankali,saita sake kallon hoton da kyau,da matar data gani a asibitin mahaukata,da matar data gani a mafarki,da matar dake jikin wannan hoton kamarsu daya,tabbas kamarsu daya,saidai banbancin shekaru,amma suna tsananin kama,to me kenan?,meye wannan?,su wadan nan matan su waye su?.