Sponsored Links
Hausa NovelsKurkukun Kaddara Hausa Novel

Kurkukun Kaddara 3

Sponsored Links

Boss Bature*

Cigaban Labari

Bayan sun samu natsuwa, Aneelerh ta basu shawarar su ta fi asibiti don ta duba lafiyar babyn, Ta kuma Yi mata injections ɗin da ake yiwa kowani yaro da zarar an haifeshi, domin bashi kariya

Atare suka tafi asibitin wanda Ya kasance Mallakin Aneelerh ne, Ƙaramin privet hospital acan aka duba Lafiyar babyn, tana da ƙoshin Lafiya bayan dawowarsu gida Aneelarh taso ta shayar da babyn Amma Taj ya hana saboda gudun kada Ya haramtawa ƴarshi auren ɗansu,wanda burinsu ne shi da Uzair, su haɗa Ya’yan su aure, duk da ita aneelerhn har yanzu shiru,

A ƙarshe sai dai ƙanwar maigadin gidansa ce Inna kuluwa Take shayar da ita, dama Tana Cikin shayar da jikanta da mahaifiyarshi ta rasu tabar mata, watan shi shida a duniya shima yabi mahaifiyarshi, baba maigadi ne ya bashi shawarar ya bata Babyn ta shayar da ita, baiyi gaddama ba ya amince, a ranar tazo daga ƙauyen su, Sai da aneelarh taje da ita asibitin su aka duba lafiyar jikinta tukunna aka bata Rainon Babyn, Acikin gidan taj ya ware mata haɗaɗɗen bedroon ɗin da zata zauna,

Ranar suna Yarinya taci sunanta *UNAISAH* shine sunan da mahaifinta ya naɗa mata Amma Yana kiranta da *ANGEL* a matsayin Nickname dinta, Bayan kammala sallar juma’a akayi naɗin sunan,

Tun ana saura kwana Biyu suna, Mutanan Buzaye suka zo, daga Ciki hada Mahaifiyar tajuddeen Yahanasu ta tsufa tukuf tare da mahaifinshi malam zahiru, hada kakarsu deeeje suka zo, tare da wasu daga Cikin danginshi, a daren ranar da suka ƙaraso, kowa Ya soma tunanin ina Uwar yarinyar take ne, sai a lokacin yake sanar dasu game da guduwar benazir da ta tafi tabarshi da yarinyar, Ran danginshi ba ƙaramin 6aci yayi ba, sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata,

A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai,

Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA* duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri,

Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta,

Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan

A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba’a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu,

A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta,

Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare,

Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum,

Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba,

hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa”Come In”

Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,

Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi,

Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala,
fuskarshi ɗauke da murmushi,

Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel,

Fuskar taj ɗauke da murmushi ya miƙe tsaye Yana kallonshi, kowannan su da abunda yake saƙawa aranshi,

“Taj nasan ban kyauta ba, wlh naji kunyar haɗa ido dakai,” cikin sanyin murya yayi maganar, da sauri uzair ya qarasa inda yake a tsaye, ya miƙa mashi hannnu don su gaisa,girgiza kai yayi tare da cewa,

“Bana jin zan iya haɗa hannu dakai don bancancanta ba”

Tausayinshi ne ya kama Uzair, cikin sanyin murya yace”kada ka sanya damuwa aranka komai ya wuce,”

Damuwace ƙarara akan fuskarshi”ɗane ka haifeshi baka haifi halinshi ba,”

Murmushi taj ya ɗan saki, kafin ya ruƙo hannunshi zuwa cikin Falon, Suka zauna saman Sofa suna fuskantar Juna,

“Baba yaushe kuka dawo ƙasar bansani ba? ya kuma Jikin naku”?

“Jiya muka dawo, Jiki yayi kyau Alhamdulillah,wlh taj naso nazo tun lokacin da ka kirani waya ka sanar dani rashin Hankalin da benazir tayi maka, Naji takaicin abun nan ƙiris Ya rage in kwashe mata albarka” yakai ƙarshen maganar fuskarshi duk a hautsine, bawan Allah da alama Yaji jiki, tun lokacin da Taj ya haɗu da benazir kafin auransu mahaifinta baya qasar saboda lalurar da ya ke fama da ita, Na ciwon ƙafa mai raɗaɗin gaske,

Alhaji ubaid tsohon gomna ne, bai jima da hawa mulkin ba, Shekara ɗaya kacal Lalurar ta sameshi,Ba ƙaramar wahala yaci ba, Don kowa yayi tunanin bazai rayu ba kullum Ciwon nashi ba sauƙi,ƙara gaba yakeyi,Gashi mutane suna matuƙar sonshi,Yana da farin Jini sosai, adalin shugaba ne mutumin kirki Mai son talakawa, Ga kyautata masu dayawa suna tunanin Abokan hamayyarsa ne suka Yi mashi Asiri, wanda hakan yasa shi ajiye shugabancin, kuma tun daga lokacin zama Nigeria ya gagares hi,da zarar yabar ƙasar Sai yaji sauƙi, da zarar ya dawo sai ciwon nashi ya dawo sabo,tun daga nan ne yabar ƙasar gaba ɗaya tare da Iyalinshi ya koma Dubai da zama, benazir kaɗai Ya bari anan saboda auran da tayi,

“Allah ya ƙara Lafiya, Allah kuma ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada,”

“Ameen ameen tajo, ae ina ganin saƙon gaisuwarka da kake turamun kullum ta waya, Inajin dadi sosai,” shiru suka ɗanyi kafin Alhaji ubaid yaci gaba da magana”Abu biyu ya kawoni wurinka, Na farko ina mai baka hakuri game da abunda Benazir ta aikata mata, yanzu haka maganar da nake yi maka, Na yafeta acikin zuri’ata Saboda bata jin maganata, tafi karfina……”tunkan yakai ƙarshen maganar, taj yayi saurin katse mashi hanzarinshi”kada ayi haka baba, Ayi mata uziri, dukkan mu nan babu wanda yasan dalilin dayasa benazir ta gudu tabar jaririyar ta, Kowa yasan tsakanin Uwa da ɗanta akwai soyayya mai karfi, Ni nasan ba hakanan benazir ta tafi ba, Dole akwai wani abu da yayi silar tafiyarta,

Girgiza kai Alhaji ubaid yayi”bakasan halinta ba ne, ni da na haifeta ni nasan halin kayana, Tagagari kowa, halinta sak dana jatumarta,dama ƙaddara ce tasa na aurota,

Murmushi taj ya ɗan saki”Adaiyi hakuri baba,”.
“Bazan bari ayi 6arna ina kallo ba, Benazir so take tajamun zagi a idon jama’a, tana so ta zubarmun da mutuncina da kuma ƙimata,sai kace ita ta haifi kanta? Babban abunda yafi damuna, bansan a ina take rayuwa ba,Gaba ɗaya ta kashe layinkan wayarta, nasa A binciko mun ita amma an nemeta ƙasa ko sama babu, Ita kaɗai tasan uwa duniyar data shiga,”dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,

Mu haɗu a Next Page, yanzu wasan ya fara gaba ɗaya book one Introduction ne wannan story ɗin cakwakiyar dake acikin shi, is hardly to make a prediction about what wll happen next😂 ……………….

*Boss Bature ✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button