Dabi’ar Zuciya 42
42
Window din yadan kerewa tsahonta,don haka ta danyi dage don takai ga bakin window din.
Dakine fetal dake malale da siminti,babu komai cikin dakin da zaka iya hanga,sai wani gado guda daya mara kyan fasali,daga gefan gado kuma saman daben simintin dakin kana iya hangen wata mace zaune jingine da bango,fuskarta ta nuna tarin shekaru sosai,tana sanye da wasu tufafi da ba lallai ka gane ainihin kalarsu ba saboda tsufa da rashin wadatar haske,kanta na lullube da mayafi da yayi kalar kayan,fuskarta na fuskantar window din,saidai bashi take kalla ba, mommy dake tsugunne gabanta ta zubawa idanu
“Me zaki gayamin?” Mommy ta furta tana ci gaba da kallonta,kamar yadda itama matar ta zuba ma mummyn idanu,kallon dake ratsa jiki da jijiyar mommy,kallon da zata iya cewa bata taba ganinsa a idanuwanta ba irin yau.
Shuru ne ya biyo baya,sai kallo dai da take binta dashi,irin kallon da zaka iya kiranshi da kallon qurilla.
Sake tashin ringing din wayar mummy dake hannun kaltume ya tsoratar da mutum hudu,mummy da mutane uku da suka shigo dakin tare,wanda suka juyo zuwa window da hanzari,sai kuma kaltume datayi saurin xamewa daga dagen datayi,ta sake daga wayar tana duba me kiran,tare da qoqarin hada alphabet ta karanta sunan me kiran dadan guntun karatun data fara samu.
Kafin takai ga aikata haka dukka sun fito
“Me kike a nan?” Mummy ta dakawa kaltum tsawa tana dubanta cikin fushi,kafin kaltum din ta bata amsa ta sake jefa mata wata tambayar
“Wa ya baki izinin biyoni?,bakiga yanayin wajen ba?,ko su kike su miki illa?”
“Mommy,ki haquri,alasa ne yace wai furofesa yana kira,shine yace na kawo miki kada kiyi fada” da hanzari ta tako,ta fusge wayar daga hannunta ta soma duba kiran,kafin takai ga kiran kuma wani ya sake shigowa,saita daga da hanzari tana kaiwa kunnenta,gami da yin gaba ta soma barin wajen,bayan ta yiwa kaltume nuni da idanu kan tayi gaba.
Professor ne ke shaida mata cewar yana hanyar dawowa daga yanzu zuwa yammaci
“Naje duba marasa lafiya,amma ina hanyar komawa gida yanzu in sha Allah” ta fada cikin salo na kwantar da kai,basu jima ba a wayar sukayi sallama,ta katse wayar,ta juyo tana duban mutanen da take tare dasu.
“Miqomin jakata” ta bawa kaltume umarni tana jifanta da harara,a ladabce ta miqa mata jakar,sannan ta wuce ta koma bakin motar inda su alasan ke jiranta suma.
Fuskarta cike da yanayu na bacin rai tace
“abunda mukayi magana dakai a kanshi ni ba ganshi ba,ban sani ba ko kunnenka ne yayi maka gizo,amma abinda nakeso guda daya shine,aci gaba da sanya kula ta ninka ta baya,gaf zuwa sanda hali zaiyi,saidai abu daya zan sake maimaitawa,banason matsala,na tsaneta,hakanan bansan kalmar sakaci ko kuskure ba,nafi yarda da ganganci” kai kawai yake gyada mata namijin,da alama maganar tata na shigarsa sosai
“Yadda matsala bata gifta ba tsayin shekarun da suka shude,bana jin a yanzu da komai ya riga da yayi nisa matsalar zata faru” macen ta maida amsa.
“Haka nake fata” ta amsa musu cikin yanayin izza da isa,sannan ta sanya hannu cikin jakarta bayan ta zugeta.
Kudi ta irgo kudi masu yawa ta miqa musu
“Duk sanda kuka karanci wani abu da bai muku ba komai qanqantarsa,bana buqatar jinkiri a shaida min”
“In sha Allah…..sai batun kaya”
“Nakune kamar ko yaushe,amma kuna iya cirar wani abu a ciki da zai iya amfanarta ku san mata” da wannaj furucin ta soma takawa zuwa waje,suka rufa mata bata,haka ta keta tarin marasa lafiyan har zuwa bakin motarta.
Sai data shiga sannan suka rufe mata motar,sukayi sallama suka juya, driver yaja motar suka bar gidan.
Waya taci gaba dayi,kafin ta isa tana bada umarnin cewa a tsaida komai dake gudana cikin gidan,a shiga aikin tarbar professor da dukka abinda ya dace,gata nan a kan hanya.
Kaltum na daga zaune,ko qwaqwwaran motsi ta gaza yi,hakanan takejin jikinta a mugun mace,ba abinda ke kai kawo a idanunta sai bayin Allan nan dake fama da lalurar tabin hankali,lokaci lokaci kuma fuskar waccar matar na dawo mata a kwanyarta,shin da wannan tsufar lalurar ta sameta?,ko kuma tun quruciya ne?,me yasa take tsare a nan?,ta fara samun sauqi shi yasa ba’a hadata da sauran ba ko kuwa?,duka ko daya cikin tarin tambayoyin nan bata da amsar kowacce.
“Dakata” muryar mummy ta sauka a kunnen kaltume,baya driver ya tsaida motar ya kasheta,harma shi ya fice daga motar.
A sanyaye ta tsaya daga qoqarin daukar mata jakar da takeyi
“Kamar yadda na gaya miki,karki sake kada kuma ki yarda naji wata magana data danganci inda mukaje daga bakinki,kome kika ji ko kika gan,kiyi kamar baki ji ko bakiga komai ba,wannan ni shine doka da qa’idar xamana cikin gidan nan,kowa da kika ganshi akwai tashi dokar,toke taki kalar dokar kenan,kin fahimta?”
Tun tasowarta tasan cewa biyayya ga uwar miji a tasu karkarar dolene,tunda itace mahaifiya ga mijinta,to binta ya zamar mata dole,kamar yadda zata bi wanda ya kawota gidan,don haka ta gyada mata kai gami da cewa
“Eh in sha Allahu” saidai ta shiga cikin gida cike da saqe saqe,da kuma tuna tunane masu tarin yawa,tunani da hasashe masu toshe basira da qwaqwalwar mutum,duka kanta ya kwance,duka iya yanda taso ta dora lamarin bisa wani mizani da zatayi masa duba na tsanaki abun ya gagareta.
A iya sani da ganinta,kai bama ita kadai ba,ganin dukka mai hankali,tattakin da mommy tayi aikine na alkhairi,wanda tasan mutane masu halin qwarai gami da dattako ke yin aiki irinsa,to amma me yasa batasan ‘yar cikinta ma tasan taje wajen?,ko kuma wani zuhudu ne da gujewa riya?,wadda ke rusa aikin bawa?,tayi kuma tafiyar ruwa da dukka wani lada daya cancanci bawa ya samu?,ko ita take gudu?.
Ta samu gidan kuwa ya dauki harama kamar yadda mummy ta bada umarni tun kafin isowarta,itama tana ji da daukar kanta a matsayin me aikine kamar yadda taji uwar mijinta na kiranta da wannan sunan da batasan daga ina ta samoshi ba,don haka ta shiga cikinsu,ta karba aikin biba,matar da take jinta tamkar mahaifiyarta,saboda sunan ummanta da take dashi,uwa uba kuma yadda ta damu da al’amuranta,take kuma kulawa da dukkan komai nata.
Tana bala’inson ta shiga cikinsu ana aikin girki,tana matuqar qaruwa da abubuwa masu tarin yawa,wadanda batasan dasu ba a duniyarta sai a yanzu,duk da cewa wasu abubuwan da yawa idan aka dafa din bata iya ci,wani abun ma ko kwata ci ma batayi,sabida tana ganin bazai ciwu din ba,duk da yadda jawahir ke mata dariya gami da ciwon baki.
*_7:00 pm_*
Zaune yake cikin qawataccen falonsa,sanye da da jallabiyya ruwan makuba me santsi.
Kallo daya zaka masa kasan cikakken dan boko ne kuma dan siyasa,wanda ya wadatu da ilimi da kuma gogayya ta sanin duniya.
Daga gefansa najwa ce zaune,ya bata dukkan hankalinsa,da alama wata magana take dashi mai matuqar muhimmanci,saboda kana iya ganin yadda fuskarsa ta wadatu da murmushi.
Dai dai sannan hajiya jidda ke shigowa falon,cikin kwalliyar wani dandaqeqen lace maroon,kai baka ce safiya bace,bayanta jawahir ce ita da kaltum,wadda jawahir din ta tada tun safiya kan zasu shiryawa daddyn abun kari,kasancewar jiya bai shigo gidan da wuri ba,so kusan dukkan abinda aka tanada masa ma bai sami ci ba ya kwanta saboda gajiya.
Sallamarsu kawai ya amsa yana ci gaba da kallon su sanda suke shigowa,har fuskarsa ta fada kan baquwar fuskar kaltume.
Saida jawahir ta aje farantinta ta gaida daddyn ta koma gefansa ta zaunsa sannan kaltume ta qaraso.
Cikin nutsuwa da tsantsar ladabi,saboda duban da take masa na uba a idanunta ta duqa ta ajjiye kayan nata hannun,sannan ta zube har qasa tana gaidashi,saiya amsa yana dorawa da tambayar wacece?.
Najwa daketa hararar kaltum kamar ta hadiyeta tayi saurin bashi amsa
“Me aikin da ya samir ya kawo kace ya maidata kafin ka dawo”
Gyara zamansa yayi sosai sanna ya dubi kaltum
“Tashi kije” a sanyaye a kuma salube ta miqe ta fice daga falon,sai a sannan ya maida dubansa ga mummy,cikin yanayi na bacin rai yace
“Ban gayawa samir ya maida yarinyar mutane ba kafin na dawo?,rainin dake tsakanina dashi har yakai na bashi umarni yaqi bi?” Cikin taushi bisa salo na kissa mummy tace
“Kayi haquri professor,don Allah kada ka bari qaramin abu irin wannan ya bata ranka,abunda ka riga ka sanshi ne ka kuma saba dashi,meye baqo a halin samir a wajenka?” Banbarakwai maganar ta yiwa jawahir aka saita maida dubanta ga daddyn sanda yake cewa
“Duk wani iskancin samir da daurin gindinki yake yinsa,rashin uwarsa a gidan nan ba hauka bane da zan dinga shinfida doka yana takewa,har ya zamana cewa qanwar bayansa ta zama kusan itace makwafinsa,tanayin fiye da abunda ya kamata ace shine yayishi,sannan kice naci gaba da qyaleshi jidda….to ya fara isata”.
Idanu mummyn ta lumshe kana ta bude cikin sakannin da basu wuce biyu ba,yayin da najwa ta saki wani boyayyen murmushi sannan tace
“Kayi haquri daddy don Allah ka qyaleshi,amfanin haifar yara da yawa kenan,idan wannan bai share maka hawaye ba wancan sai ya share maka,pls ka manta dashi daddy,haka ya zabawa rayuwarsa”
“Ke banson shirmen banza,waya sako bakinki a nan?,wa shin bama fita zakiyi ba?,tashi ki bama mutane waje” mummy ta fada cikin hade rai,don sam har yanzu najwa bata hau saiti yadda takeso ba,batason ta soko wani zancan daban
“Bamu gama da daddy bafa”
“Naji abinda kikace,anjima idan kin dawo zamu qarasa maganar,kafin lokacin nayi magana dashi”
“To daddy” ta fada tana miqewa,fuskarta na nuna zallar annuri da farincikin data samu.
“Daddy….don Allah kayi haquri ka fuskanci ya saraki,kome yayi saraki yayi idan ka tsaya ka duba sosai….yanayin abinda ya dace ne,kawai don dai baka fuskantarsa ne,amma yaya samir yana da zuciya me kyau……”
“Wa yasa dake kema?,me yasa kuka son shiga maganar manya ne?,tashi ki bamu waje kema ko na sabar miki” mummy ta fada cikin hade rai tana duban jawahir,wadda ta tattabe fuska kamar zata saki kuka. Har ga Allah ta saba da kaltume adan taqin,tana fuskantarta irin fuskantar da ‘yar uwarta ma bata taba yi mata irinta ba,tana fahimtarta sosai,tana zama ta saurari hirarrakinta wanda ko mummy bata samu wannan sakewar da ita ba,tana son zamanta tare dasu,saboda ta hangi tarin baiwa masu yawa tattare da ita
“Um…um,qyaleta ta qarasa” professor ya samu kansa da fadin haka,najwa tafi kowa bin tsari da ra’ayinsa cikin gidan,amma kuma sau tari yakanji nutsuwa a zantukan jawahir,da kuma dadin saurare
“Daddy kaltum bata da gata,yaya ya daukota ne don ta samu gata,ba shi ya gayamin ba,na fuskanci hakanne a hirarrakin da mukeyi da ita,da labaran da take bani,sunashan wahalar rayuwa abba,idan ka riqe kaltum lada zaka samu,ya samir bai bijirewa umarni da ra’ayinka ba,yasan tsarinka,bisa hakanne ma ya sanyani nake koya mata karatu,yanxu haka cikin satin nan zata zana placement zata tafi ss one” shuru yayi yana farfasa zantukan jawahir,shurun daya jefa hajiya jidda wani tunani na daban,ya akayi jawahir tasan dukka wannan ita tana zaune?,yayin da jawahir din kuma ya bata qwarin gwiwar bawa daddyn labarin yadda kaltumen ta iya zane abun mamaki,hakan yasa ma ta bata shawarar ta zabi fannin zane tun daga nan har zuwa gaba idan Allah yayi zata din.
Nan ta zage tana bawa daddy labarin zanen datayi wanda ya bata mamaki sosai
“Idan ka biyewa shirmen jawahir ba zaka ci komai ba prof,tashi ki tafi hirar ya isa haka,Allah ya bada lada” mummy ta fadi tana miqewa zuwa gaban kwanukan da suka ajjiye tun dazu.
Kallon da mummy ke aike mata yasa ta miqe tana yiwa daddyn sai anjima zata kawo masa zanen.
Murmushi ya saki
“Duk da jawahir auta ce,amma tana da hangen nesa da nutsuwar da batayi kama data autoci ba” baki mummy ta tabe sanda take maida murfin tea flask din data zubawa daddyn zazzafan shayi.
Cikin nutsuwa yake takowa zuwa cikin gidan,sanye da wasu blazers ruwan sararin samaniya,sunyi matuqar haskashi da qara masa kwarjini,jikinsa na fidda qamshin turarensa da koda yaushe,zatinsa na tsaho da murjajjen jiki ya fito sosai,hannunsa daya dauke da wasu takardu dake qunshe cikin files dinsu.
Cikin lallausar muryarsa yayi sallama cikin falon,daga can inda take tsaye gaban katafaren teburin cin abincinsu da taje dinan kofunan da biban tace ta kawo ta jiyo kamar muryarsa,duk da bata tantanceta sosai ba,saita waiwaya a hankali tana amsawa.
Amsawarta yaja hankalinsa yakai duba inda take,saita tako a hankali riqe da kofunan,ta iso gabansa ta durqusa qasa tana gaidashi,cikin yanayin kulawa yace
“Lpy alhmdlh,ya karatun?” Dan murmusawa tayi kadan,karon farko da yaga fara’arta tunda yake ganinta
“Alhamdulillahi” ta amsa masa
“Ina jawahir” sai data kalla sashen dakinsu sannan tace
“Tana ciki”
“Kiramin ita” ya fada yana dan zama hannun kujera,tace to tana miqewa da hanzari.
Da sallama ta tura qofar dakin,tsaye ta samu jawahir gaban tarin kayan shafarta,hannunta riqe da wata zungureriyar roba,ta amsa tana ajjiye robar.
Tun kafin tace wani abu jawahir din ta soma magana
“Fada kawai kikeso muyi dake kaltum,kayan nan har yanzu banga kina amfani dasu bafa,yanzu man wanke kan nan banga alamar kin taba amfani dashi ba” dan murmushi tayi,batasan me yasa ta damu da lamuranta da yawa haka ba
“Kiyi haquri jawa,ki fara zuwa wajen…..”sai kuma tayi shuru,don batasan da wanne suna zata kirashi ba,daga bisani ta yanke tayi kiransa da yaya kawai
“Ok,ina zuwa” ta fada tana juyawa ta nufi qofa da sauri.
Sai data fice itama tabi bayanta don kaiwa biba kofunan.
Kamar ko yaushe ta gaida samir din cikin girmamawa,ya amsa mata shima cikin kulawa
“Idan baki komai ki shiga ki gyaramin sashe na”
“To yaya” ta amsa tana masar muqullin bangaren nasa,shi kuma ya wuce zuwa sassan daddy.
Kitchen ta duba bata samu biba ba,saita wuce zuwa dakinta don ta gaya mata takai.
A nutse ta daga labulen dakin,idanuwanta suka fara sauka kan biba dake tsaye riqe da wani dan qaramin hoto a hannunta,wanda bata iya hango wanda ke ciki saboda da kadan ya wuce girman passport.
Sallamar kaltum yasa ta soma qoqarin boye hoton,a hankali ta qarasan gaban biban tana cewa
“Nakai kofunan kitchen,amma saina taras bakya nan,nama wanke na mayar dasu inda suke” kai ta gyada mata ba tare da tace komai ba,sai kaltum ta lura da hawayen dake idanun biban da take qoqarin gogesu,cikin mutuwar jiki tace
“Baki da lafiya ne?”kai ta gyada mata
“Kaina ne yake dan ciwo kadan,shi yasa na taho na huta” duka sai kaltum taji babu dadi
“Ayyah,sannu,Allah ya sawwaqe,gwara ki huta kam,Allah yasa kaffara”
“Amin”ta amsa tana sake goge idanunta da kyau,tayi kamar zata zauna tare da ita,amma biban tace babu komai taje,itama yanzu zata fito,tunda ciwon ba sosai bane,bai matsa mata ba.
*_SHIN KINSAN CEWA AKWAI RAMUWAR SALLA A KANKI ME JININ AL’ADA?_*
________________________________
*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar