Dabi’ar Zuciya 31
31
Daga ita har ummanmu shuru sukayi a dakin likitan,suna jiran suji bayanin da zaiyi musu,kowanne a cikinsu zuciyarsa dukan uku uku take,a haka har likitan ya dago ya dubesu.
Wani irin kallo yayi musu,wanda yake nuni da raini raini irin da kuma qyama,irin wanda aka sabawa mutanenmu ‘yan uwanmu al’ummarmu ta karkara
“Baaba,yaya akayi kuka barshi haka a gida,har ciwonsa yayi tsanani haka?” Tashin hankali ne ya fito baro baro kan fuskar umman,cike da nuna damuwa ta zakuda zamanta kan kujerar tana cewa
“Likita?,me ka gani?,me yake damunsa?” Sai saya jujjuya takardar hannunsa,cikin shan qamshi sannan yace
“Eh to…..yanzu muna buqatar kuje ayi masa scanning tukunna…..”
“Me kenan likita?” Ummanmu ta tambaya a rude tana kallon yadda jikin bilal din ya saki gaba daya,ya daina juye juyen,sai kallo da sauraren abinda likitan yake fada.
Goshinsa yadan sosa sannan yace
“Oh,sorry,hoton cikinsa….sannan zamu gane ainihin inda matsalar take,ayi kuma abinda ya dace” ya fada yana sakeyin wani rubutun saman takardar ya miqa mata.
Kaltum ce ta karba,sannan ta isa inda umma ke qoqarin sauko da bilal daga saman gadon,sukayi masa kama kama,ya dogara da kafadarsu suka fara tafiya don ficewa daga office din.
Tun basuyi nisa a tafiyar ba ya zame
“Bazan iya takawa ba” ya fada yana kallon ummanmu,hankalin kaltum ya sake tashi,dukkansu matane,bata tunanin zasu iya daukan bilal,har gwara ita akan ummanmu,saita dubu takardar hannunta, ayanzu burinta kawai shine sune wajen hoton a samu a gano abinda yake damunsa a cikinsa
“Ka daure bilalu muje,kaga likitannyana jiranmu” kansa ya mirgina yana ajiyar numfashi
“Bazan iya ba yaya,Allah bazan iya ba” ya fada a raunane,babu wata sauran mafita data rage musu,don haka kaltun ta miqawa ummansu takardar
“Riqe ummanmu.na goyashi”
“Anya ko zaki iya kaltum,ki barshi dai ya sake gwadawa”
“Zan iya ummanmu in sha Allahu” ta fada tana juyawa bilal bayanta,da taga taga umman ta tareshi ya shau bayan kaltum,duk da nauyin da bilal din yake dashi amma sai data ar jarumtar data shanye wannan nauyin,saidai daqyar take iya taka qafarta,hakanan kafin sukai wajen scan din ta huta ya kusa sau biyar,a haka har suka isa wajen.
Sun tadda layi,suka tambayi mutum na qarshe a wajen,suka zaunar da bilal suna tsaye a kansa
“Ruwa” ya fada qasa qasa,idanuwansa na kan al’ummar dake kai kawo,ummanmu tace kaltum din taci gaba da tsaiwa dashi,bari ta samo masa ruwan,cikin hanzari ta miqi hanya.
“Amai zanyi” bilal din ya sake fada,saita cafko wata baqar leda dake yawo a qasa kusa dasu,tana tara masa kuwa ya fara shara aman,yana aman tana kallonsa tana kuma kallon aman,hakana jama’ar dake kusa dasu,saboda wani irin baqin amai da yakeyi,harda gudaji gudaji kamar na nama ko fasashiyar mahaifa,a haka ya kammala tsaf,dai dai sanda ummamu ta dawo,ta balle pure water din data zo dasi guda uku,ya shanye biyu daga ciki.
Tafi tafi layi yazo kansu sannan suka shiga,kaltum na daga waje ummansu ce ta shiga tare da bilal din,yadda taga ya natsu ya zubawa na’urar idanu sai taji jikinta ya sanyaya haka kawai,ya daga kai suka hada ido
“Kece mamansa?” Kanta ta gyada a maimakon ta amsashi,saiya maida kansa yaci gaba da aikinsa da sauri sauri ba tare dayace da ita komai ba,yana gamawa ya linke takardar bayanan ya bata
“Kuyi hanzarin kaiwa likita wannan”
“To na gode” ta fada tana karba hannunta yana rawa,sannan ta kama bilal suka fito.
Kai likitan yake jinjinawa sanda ya karbi bayanan yana dubawa,kansa ya daga ya dubi umma
“Baiyi amai ko sau daya ba?”
“Yayi likita yanzu babu jimawa” sai taga ya dafe goshi,ya ajjiye takardar ya dubi nurse din da a yanzu take tare dashi
“Kuje dashi a bashi gado, a daura masa drip….baaba,kuje ku nema kudin aiki dubu takwas,za’ayi masa operation ne na gaggawa,kada ya dara awa daya”
Gaba daya kamar an kwarawa jikinta ruwan sanyi haka ummanmu taji,kaltum kuwa mutuqar tsaye tayi,saboda sunfi kowa sanin cewa basu sa wannan kudi,basu kuma da hanyar samunsu,data laluba jakarta ma kudin da suka rage a ciki wanda suka taho dashi na jarin nata dubu daya ce,banda haka basu mallaki komai ba,don haka bayan an masa duk abinda likitan yace,sai ummanmu ta kalli kaltum
“Bari na fita daga waje ko zan samu wajen buga waya,na kira ado ko indo,ko Allah zaisa a dace a samu koda wani abune daga wajensu”
“To ummanmu” ta amsa mata idanunta nakan bilal,wanda nashi idanun suna kan umman
“Don Allah ummanmu kada ki dade”
Takowa tayi a hankali gabansa ta tsaya,ta kamo hannunsa da babu qarin ruwan ta riqe gam sannan tace
“Yanzun nan zan dawo in sha Allahu”
“Ayimin aikin nan ummanmu ko zanji dadin cikina”
“Da yardar Allah yau ka rabu da ciwon nan” saiya gyada kai kawai yana lumshe idanu,umma ta zame hannunta ta fice da sauri.
Kujerar roba da ake ajewa guda daya a gaban kowanne gado kaltum ta jawo ta zauna gaban bilal,duk a darare take,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa waje irin wannan,sai take ganin kamar kowa kallonta yakeyi,duk kuwa da cewa ba haka bane,kowa ta mara lafiyansa yakeyi
“Zanyi amai yaya” bilal ya sake fada,saita miqe da sauri ta sake samo masa leda,kamar aman dazu ya sakeyi,itadai kaltum ta zubawa aman ido cike da mamaki,ganin wani abu guda guda kamar hanta hanta a ciki da yake ta fita,gashi yayi wani baqi kamar ajiyayyen jini,haka ya gama ta rufe ledar taje ta yar.
Tana dawowa ta taras da wani ma’aikacin lafiya a kanshi yana dubashi,ya kammala yayi rubuce rubuce ya bata takardar,yana barin wajen yana mata bayani
“Magunguna ne,aje a siyasu yanzu” fakare tayi da takardar a hannunta tana juyata,ita da zuciyarta suna qiyasta adadin kudin maganin da babu su babu dalilinsu
A hankali ta daga idanunta,sai suka hada ido da bilal din,hannu yasa ya yafitota,ta taka a hankali zuwa gab da gadon ta sunkuya sosai daidai kansa,saboda yadda muryarsa take fita yanzu a hankali,da alama dukkan wani qarfi da kuzaru nasa ya qare
“Yaaya,inabin lawandi kudi,don Allah aje wajensa,ya bayar da kudin ayi mini aikin dasu,ni kadai nasan abinda nakeji,idan basu cika ba ko baba ne ya taimaka ya cikamin” wasu hawaye ne suka zarto mata,saita miqe tana gogesu daga fuskarta,tsananin tausayin dan uwan nata yana cika qirjinta,ta yadda har takejinnkamar ta fiddo zuciyarta waje.
Roqo abune da bata taba yi ba tunda take,amma ayau zata yishi saboda ceto rayuwar dan uwanta,don gabas da yamma,kudu da arewa a yanzu batasan inda zata sama masa kudin magani ba idan bata wannan hanyar ba
“Ki kiramin ummanmu,tazo ta zauna a kusa dani” ta sake jin muryar bilal,saita juya da sauri don yi masa abinda yace din,sai kuma ga umman ta dawo
“Kin kirasu ummanmu?” Tayi tambayar tana duban yanayin umman
“Ban samu ba,amma wani bawan Allah yace na jira ya karbo wayarsa daga wajen chargy,saina koma ya kiramin.
Kai kaltum ta girgiza,tana ji lokaci yayi tsaho da yawa,tana ganin gwara ta fita su roqa,koda basu cika ba a ciki tayi kudin mota ta koma qauyensu ta amso kudin bilal din a hada a cire masa ciwon dake damunsa
“Ina zuwa ummanmu” kaltum ta fada da sauri tana bin hanyar waje,sai umman ta saki ajiyar zuciya ta maida dubata ga bilal daketa binsu da ido
“Me yasa kika tafi ummanmu?” Ya tambayeta a hankali,tana qoqari maye gurbin da kaltum ta tashi ta amsa masa
“Kayi haquri bilalu,inacan wajen nema maka kudin aiki,amma gani na dawo” saiya gyada kai yana miqa mata hannunsa
“Riqemin hannuna”
“To bilalu” ta amsa masa tana saka hannunta cikin tafin hannunsa.
Abunda baka saba ba,diri diri ta shiga yi a dan filin asibitin,ta rasa ta ina zata fara?,wa zata fara roqa?,saita fara takawa a hankali zuwa nahiyar da mutane ke zaune,wasu suna jinyar ‘yan uwansu,wasu kuma dubiya suka zo.
Duk wanda ta dosa katin take miqa masa tare dayi maaa taqaitaccen bayani.
Bata taba sanin duniyarmu ta cika tab da marasa tausayi ba…..bata taba tunanin duniyarmu ta cika da nau’in jama’ar da basa jin qan junansu ba sai a ranar,mutane da yawa saidai suce Allah ya sawwaqe suma basu dashi,idan ma taci sa’a kenan an mutuntata,duk kuwa da cewa mafi yawa a cikin masu fadin hakan,ba za’a rasa kudi koda qanqani a jikinsu da zasu iya bata ba,wanda inda sunyi hakan….kadan kadan din su zasu hadu su bata yawan adadin abinda take buqatar.
Wasu daga cikin mutanen ma saidai su dauke kai,ta gama bayaninta ba tare da wani daya cikinsu yace komai ba,a haka taci gaba da jarraba sa’arta.
A hankali motar tasu ta ratso cikin asibitin,matasan zaratan samari,wadanda kudi da ilimi suka yiwa ginshiqi,samir tare da amini kuma dan uwanshi aamiru,dukkansu suna sanye da shadda,wadda aka yiwa wani nau’in dinki mai qayatarwa,wanda yayi musu kyau,ya kuma fidda sigarsu da zatin da Allah yayima kowannensu.
“Wannan wanne irin asibiti ne haka?” Amiru ya fada yana bin asibitin sa kallo,sai a sannan samir ya aje wayarsa saman cinyarsa,kasancewar bashi ke tuqin ba amiru ne,shidai yana zaune kawai a gefansa.
Ajiyar zuciya mai nauyi saraki ya sauke,tsahon wasu sakanni sannan ya magantu
“Bakaga komai ba….wannan asibitin da kima da darajarsa akan saura,bansan me shugabanninmu keyi ba,totally basu san responsibility dinsu ba,yanzu wai a irin wannan muhallin ake neman lafiyar dan adam….Allah ya kyauta” ya fada tare da bin bayan maganar tasa da tsaki bacin rai yana cikashi,saiya buda murfin motar ya zura qafarsa waje yana sake qarewa harabar asibitin kallo.
Cak ya tsaida idanunsa yana dubanta waje daya sanda take kai kawo a tsakiyar asibitin,da yadda take tsaida jama’a jefi jefi,sannu sannu har ta iso dab da motarsu,sai yaga ta zagaya daga baya inda amiru ke tsaye yana amsa waya,bai waiwaya ba amma yana iya hango black face dinta ta jikin mudubi,wadda ta qara duhu da shining.
“Lafiya?” Yaji amiru ya fada,wanda bai gama wayar ba,ya dakata ne saboda tsaiwarta a wajen
“Taimaka mana zakayi fisabilllahi da kudin magani,don Allah,bamu da kowa bamu da komai sai Allah…..”
“The giant,are you there?” Gyaran murya kawai samir yayi masa
“Ok,miqo wani abu” ya fada yana dariya dariya,saboda tuna wani abu da yayi,baice komai ba ya bude aljihun motar,ya ciro kudi a ciki,cikin ransa yana tambayar waye nasu a asibiti babu lafiya?.
Har zai miqawa amiru kudin saiya tuna yadda aka tabayi da ita akan sabon kudi,saiya maida,ya laluba ciki ya dace da samun wasu,sai ya miqawa amiru su gaba daya.
Har zaiyi magana da yaga yawan kudin sai kuma ya fasa,ya miqa mata,tsayawa tayi turus tana duban yawan kudin
“Ki karba mana” kanta ta girgiza
“Sunyi yawa ai” ta fada adan tsorace tana ja da baya,dariya da mamaki suka tasowa amiru amma ya dannesu
“Nawa kike so to?” Kamar ta taka da sauri tabar wajen,sai kuma ta tuna bilal yana da buqatar kudin,a hankali kamar wadda batason fadi tace
“Duka har kudin magani da kudin aikin dubu goma da dari biyar ne,na samu dubu daya,saura dubu tara da dari biyar” da boyayyar dariyarshi ya irga kudin dake hannunsa,ya zare dubu goma a ciki ya bata
“Ga dubu goma nan,dubu dayan kai sai ku sayi wani abu” hannu biyu tasa ta karba tana godiya har qasa,saita baiwa amiru tausayi,yana dariya bayan ta wuce yace sa samir
“Kaida ka kawomu nan kuma kayi zamanka kaqi ka fito,gashi na fara haduwa da mutanenka,ka ganemin yarinya?,iya abinda takeso shi zata karba?”
“Haka take” ya bashi amsa sanda yake fitowa daga cikin motar
“Ka santa ne?” Da mamaki amiru yatambayeshi
“Kusan hakanne” ya amsa masa yana gyara rigarsa data dan tattare ta baya
“Kodai daya daga cikin ‘yammatan daka yone daga qauye ka yaudaresu bayan ka gama aiki?,kai….no wonder mafa naga kaqi fitowa har sai data tafi” amirun ya fada yana dariya,tilas ya sashi murmusawa,daga baya qaramar dariya ya subuce masa,har haqoransa suka bayyana,babu abinda ya tuna sai fuskar kaltume,da qwailan jikinta
“Kaci abinci amiru,amma babu laifi,zan rama ne” yana fadar haka ya danyi gaba da hanzari,amirun ya bi mashi a baya zuwa ciki,suka fara tambayar inda mai gadinsu malam salahu yace an kwantar sa dan nasa,don dama dan dama shi suka zo dubawa.
Shan gabansu da wata mace mai dan wadatar shekaru tayi yasa suka tsaya cak
“Yallabai,kune gwamnatun ta aiko da tallafi?” Ta tambayesu tana kallonsu,duban juna sukayi a tare,amiru ya dagewa samir gira kana yaja baya,alamun ba ruwansa,yaji da ita.
Murmushi samir yayi mata sannan yace
“Mune iya,me ya faru?” Zaro idanu amiru yayi jin abinda samir ya fada,ai kuwa matar ta kaikaice tana ta fadin matsalolinta,wanda kusan duka nakudi ne,sai data gama sannan ya zaro kudi masu dan dama daga aljihunsa ya bata,wayyo,zo kaga murna,kamar zata zuba ruwa a qasa tasha,tausayinta ya kama saraki,tausayin halin da takalan qasata yake ciki.
Godiyar da take zabga musu yaja hankalin mutanen wajen saika marmatso,saita hau gaya musu gwamnati ta turosu,saifa aka fara tururuwar fadar matsaloli,tun yana raba kudin aljihunsa har suka qare ya karbi na amiru,shima suka qare,daga bisani dai wanda bai samu ba sai alqawarin kawo tallafi daga baya yayi musu.
Amiru na biye dashi a baya yana kwasar dariya,shi kansa yanda sukayin ya bashi dariyar,saidai kuma tsantsar tausayinsu ya danne dariya,saiya dakata,suka jera da amiru,ya fara masa wasu bayanai da yanayi da halin da al’ummar karkara ke ciki,wanda duka ya karanci hakane a makarantar duniya,da dan shiga garuruwansu yi musu aikin da yakeyi,kafin su qarasa dakin da zasu saiga amiru yana gyada kai,sau tari shi kansa yana yaba halayya da dabi’un samir,yana kuma yaba kaifin tunani da hangen nesan da yake dashi.
A gaggauce kaltum ta tsallaka can wani wajen saida magani dake da da tazara da asibitin ta karbo dukan abinda ke rubuce jikin takardar,cikin tsananin sauri ta dawo asibitin,saboda so take akaiwa likitan kudin da wuri ya yiwa bilalunsu aiki ya huta.
Tun daga farkon qofar babban dakin ta hango ummansu zaune gaban gadon da bilalun yake kwance,ya canza yanayin kwanciyarsa ba kamae dazu ba da yayi kwanciyar hannu daya,kuma ma kamar a rufe yake yanzun,amma me yasa ummanmu ta rufeshi har saman kansa bayan tasan bashi da lafiya?,ta tambayi kanta,idanu da hankalinta a kansu har ta isa gaban gadon.
Kafin tace komai ummanmu ya dubeta,wani abu kakkaifa data hanga daga idanun ummansu,yasa dukkan wani sassan na jikinta yayi sanyi qalau,hatta maganar data furta a sanyaye tace
“Ummanmu ya samu bacci ko?” Kai ta gyada mata
“Yayi bacci kaltum,babban baccin da babu wanda yasan ranar tashinsa sai Allah,yayi kwanciyar da zai huta,irin hutun da muka gaza samar masa” kasa fahimtar maganar ummansu tayi kwata kwata,kamar ma ba hausa take mata ba,muryarta na rawa tace
“Kamar yaya ummanmu?”
“Allah ya karbi ran bilal,ina fatan kuma ya huta kenan har aljanna” batasan ledar hannunta ta fadi ba,batasan ta zame ta fadi ba ita kanta,qafarta ta bugu da qarfen gadon,abunda ta iya sani shine wani kuka data saki wanda ya amsa kuwwa a dukka ilahirin lungu da saqo na dakin,kukan da yaja hankalin dukka mutanen dakin,har ma da wadanda basusan bilal din ya rasu ba,ya kuma ja hankalin su samir dake bakin gadon dan malam salahu suna dubashi,ya waiwaya yana tuna inda yasan wannan muryar da irin kukan,sai idanunsa suka hange masa ita.
“Ya salam” ya fada yana jin qirjinsa yana bugawa,tabbas wani ne ya mutu,juyawa yayi a hankali zuwa inda take ummansu da wasu mata na qoqarin dagata tare da bata baki,bai tsaya ba sai daya isa gaban gadon,ya saka hannu ya bude rufin,saiga bilal,the hard work boy title din da yake masa.
Sakin abun rufar yayi yayi baya yana fadin
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” yana jin wani abu yana zaga kwanyarsa,bai taba tunani ko kawowa ransa haka ba,duka duka yaushe sukaje dubashi,ya daga kai ya sake kallon gawar,ko a haka cikinsa ya nuna kumburin da yayi harta saman mayafin da aka rufeshi
32
D/Z
*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*
08184017082
Ko kuma
09134848107