Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 30

Sponsored Links

“Mun amince indai wannan shine sharadin” da mamaki kawu ado ya kalleta,amma duban data yi masa ya sanya yayi shuru baice komai ba,ya tabbatar akwai sauran bayani a bakinta

“Shikenan,wasalam wa kitabihi,kina iya komawa dakinki” baban ya fadi yana miqewa yana kade babbar rigarsa,kawu iliya shima ya miqe,suka bawa kawu ado hannu,baiqi ba ya basu hannu sukayi musabaha kana suka fice daga dakin.

Shuru neya biyo baya,sai tashin kukan kaltum,wadda ta kasa haquri jin umman batace komai ba,kamar yadda kawu ado yayi shuru,cikin muryar kuka tace

“Yanzu ummanmu,da bakinki zaki amince na auri auwalu?”

“Abinda ya bani mamaki kenan,dukkan wata doka da sharudda da naso gindaya masa sun rushe,saima shi daya bada tasa dokar da qa’idar,bansan meye mahangarki ba zuwaira” kawu ado ya fada cike da mamaki kamar yadda kaltum itama ta cika da mamaki,dukkansu suka zuba mata idanu suna jiran jin abinda zata fada

“Ba zaki auri auwalu ba kaltume,ba zaki auri auwalu ba da izinin ubangiji,ado……kasan gayawa jini na wuce?” Saiya gyada kanshi yana mamakin tambayar data yi masa.

“Sallar dare nada tasiri mai ban mamaki,tasiri mai matuqar yawa,hakanne uasa kadanne daga cikin bayinsa ke ribantarta,take da wahalar da kuma wuyar jurewa,duk kuwa da cewa dukkanmu akwai buqatun da muke nema wajen ubangiji,wanda da zamu tsaya mata…..ba shakka dukka kuka da damuwarmu ta qare,saidai idan har qaddarar hakan bai qare ba cikin kundin qaddararmu,kamar dai qaddarar aurena da amadu…….zanta gayawa ubangiji,….zanta roqarsa,zanta masa magiya game da lamarim kaltume,ina ji a jikina ubangiji zai mata musaya mafi alkhairi,inaji a jikina ubangijina xai share min hawayena,inaji a jikina kukana na shekara da shekaru watan watarana zai zama dariyata,danme zan bata wannan lokaci mai tsaho?,don me zan yanke doguwar tafiyar da jikina ke bani na kawo qarshenta?” Sosai maganganunta suka shigi kawu ado,amma ga kaltum bata fahimci komai ba,bataga wata mahanga ko mafita dange da auren auwalu ba,wanda idan har ya tabbata batajin zata ci gaba da rayuwa a duniya gaba daya,bama iya cikin qauyen ba.

Kawu ado ya shirya musu komawarsu gida,gidan da suke masa kallon wani kurkuku mai tarin qunci takura da kuma tsanani,saidai a hakan ummansu ta zabar musu su koma ciki,basu kuma da wani sauran zabi ko ta cewa.

Sayayyar kayan abinci masu yawa kawu ado yayi mata,sannan ya damqa mata kudi

“Wannan jari na baki,ki nemi abin sana’a don Allah yaya zuwaira,kada ki yarda wannan karon ya amshe miki jarinki ya karyaki bayan bai taba doraki ba” murmushi tayi,ta karba ta kuma yi godiya,tana godew mahaliccinta daya bata ‘yan uwa dake qaunarta saboda Allah,ya kuma sanua hadin kai a tsakaninsu,duk da tushiyar bata so ba.

Tun daga sanda suka koma kaltum ta lura da wani binbininta da auwalu yakeyi,bini bini saiya mata siyayya ya faki idanun laure ya aiko mata dash,abun yana bata mata rai da kuma ci mata tuwo a qwarya,da alama an fesa masa cewa shi za’a baiwa nan da sati biyu.

Idan ya aiko da kayan bata ko kallonsu,saboda ummansu ta hanata ta dinga maida masa,saidai idan bilal ya dawo,ya dauka abinda yakeso a ciki ya qara gaba abinsa,don ya riga ya gayawa kaltume

“Yaaya,ki dauka kici,wahalar banza yakeyi kawai,waye zai bashi ke?ni tun sanda ummanmu ma tace bazai aureki ba hankalina ya kwanta,don ummanmu bata magana biyu” a lokacin gani take ba zasu gane abinda takeji ba,kullum kwanan duniya tana kwana ne sa fargaba ta tashi da ita.

***********Zaune take saman kujera ‘yar tsuguno daga can magangarar ruwansu tana musu wanki ciki harda kaya bilal,umma tana daga bakin qofar daki tana tsefe kanta,duk da tsaho da yalwar gashinta bata bari ya dade bata sabunta kitson kanta ba.

 

Sharaf sharaf sukaji tafiya,duk sai suka maida hankalinsu bakin qofa.

Bilal ne ke shigowa da takalman aikinsa a hannu,ya qaraso tsakar gidan ya sulale ya zauna

“Acici mala’ikun tauna,yunwar ce?” Kaltum ta tsokaneshi,don yau koda safe ma baisa komai a cikinsa ba,data yi masa maganae karyawa ma sai yace zaici saiya dawo,baya jin dadin bakinsa ne.

To a nan ma kansa ya girgiza
“Bana jin yunwa,bakina da cikina ne babu dadi wallahi” ya fada yana yamutsa fuska,tare da qoqarin kashingida kan gwiwar hannunsa

“Wannan neman kudin daka sanya a gaba ne,kullum babu hutu,awa a shirin da hudu amma kana bautar da jikinka?ya kamata dai ka dinga hutawa” umma ta fada tana ci gaba da tsifarta

“Zan huta ne umma,nima sai naji inason na huta” ya fada yana zamewa,tare da kwanciya rigingine,amma ya miqe sambal,yayin da kaltume da umma sukaci gaba da hirarsu,har zuwa sanda kaltum ta gama wankin ta soma shanyawa a gurguje a gurguje,saboda koda kiran sallar la’asar da aka fara.

Har umman ta miqe,saita ankara dashi
“Kai bilalu?,meye haka?,kazo ka wani mimmiqe ka rufe fuska da riga kaman wata gawa,tashi kaje kayi sallar la’asar gashi can ana kira” miqewa yayi ya zauna yana dafe da cikinsa

“Umma zanyi a gida,baza iya zuwa har masallaci ba,ciwo cikin yake min”

“Wannan ciwon ciki Allah ya rangwanta,ya yaye shi,saika tashi ka watsa ruwa a jikinka ka daura alwala kayi sallar,sai kazo kasha sauran magungunanka” amsa mata yayi da to,sannan ya miqe cikin dauriya da dakiya,kaltum ta bishi da kallon tausayi irin na ‘yan uwantaka.

A iya kwanakin ta lura har dan fadawa yayi,tana yawan ganinsa da daddare idanu biyu,idan ta nema ba’asi sai yace tashinsa kenan.

********”jiya da yau duka banga hard working boy din nan ba…..” Saraki ya fadi sanda yake takawa zuwa inda motarsa ke ajjiye tana jiran qarasowarsa,yana kuma cire lethier hand socks din dake hannunsa,wanda yayi amfani da ita yanzu wajen duba ingancin wani sumunti da za’a qarasa plaster ginin makarantar daya kawo qarshe a yanzun

“Kamar bashi da lafiya fa,don shekaran jiya daga nan aka maidashi gida ma,ya fadi ciwon ciki” dakatawa da tafiyar samir yayi,ya waiwayo yana duban umar

“Amma me kukayi akan hakan?” Dan sosa kansa yayi kadan,don yasan amsar da zaya bayar kuskurece a wajen samir

“Babu komai,munyi magana da murtala yace tunda akaji shuru lafiya ce” kadan adams apple dinsa ya motsa,alamun abun ya masa ba dadi,yadan lumshe kyawawan idanuwansa da Allah yayi musu wani irin yanka mai daukar hankali da kwarjini,kamar zaice wani abu saiya fasa,yaci gaba da takawa zuwa inda motar tashi take umar na biye dashi cikin fargaba har suka qarasa.

Budeta yasa akayi,saiya cire ‘yar saman rigarshi ya jefa ciki,ya fidda takalmin qafarsa shima ya maida cikin motar,saiya zari slippers dinsa da yake sakawa idan zaiyi alwala a wajen ya sanya,yana nade hannun lon sleeve shirt din dake jikinsa yace

“Kiramin hannafi” ba tare daya waiwaya umar ba,ajjiye litattafan hannunsa yayi ya juya zuwa sashen da makarantar take da hanzari,don suna daga bayan makarantar ne,inda ba wanda yake iya ganinsu,yawancin lokuta anan yake ajiyar motarsa,hakan yasa har yanzu da gini ke daf da kammala ba kowa ne yasan matsayinsa ko kuma waye shi ba.

Minti uku sai gasu tare da hannafi,takawa ya fara yi sannan ya gayawa hannafin inda zasuje

“Gidansu yaron nan…..bilal”

“To mai gida” hannafi ya fada yana shigewa gaba da hanzari.

Shuru ya ratsa tafiyar tasu,hakan yasa samir yin amfani da wannan damar

“Ba abu bane me kyau ba mutum na aiki qarqashinka,ka jishi shuru ka kasa bincikar lafiyarsa,idan lafiya lau yake to alhmdlh,idan kuma bashi da lafiya….sai kayi tattaki kaje ka duba lafiyarsa,wannan shine halin ma’aiki S A W,yayi cigiyar matar dake share masallaci kullum bayan ya jita shuru,aka shaida masa ta rasu,yaje kan kabarinta yayi mata addu’ar samun rahama,yayi cigiyar mutumin da yake ba musulmi ba,wanda kullum sai yazo yayi wani abun cutarwa ga ma’aiki,aka shaida masa bashi da lafiya ne,yayi tattaki yaje dubashi,qarshe ya laqqana masa kalmar shahada,ya karba ya musulunta,ya mutu a musulmi” saiya tsagaita yana tuna daga inda ya samu wannan karatun,yana tuna sanda take karantar dasu,yana hango lokaci da yanayin tarrrr a idanunsa,amma me yasa komai ya goge?,me yasa komai ya shafe?,me yasa dukkan wani abu da zai tuna masa da ita babu shi?,tambayar da yakewa kansa kenan a wasu lukutan.

“Allahu akhbar…..Allah ya bamu ikon yin koyi” hannafi ya fada

“Ameen ameen” umar ya amsa masa,girma da qimar samir na qaruwa a idanuwansa,ba dan kasuwa bane kadai,badan babban dan siyasa bane kawai,ba jagora bane zalla,ba mai kudi bane tsantsa,a’ah….yana da wata nagarta,nagartar da sai a tara mutane dubu masu irin abinda Allah ya bashi a rayuwa basu da ita.

Tafiyar minti biyar takawosu qofar gidansu bilal,shuru a yashe babu kowa

“Tab,kada Allah ya kawo wannan mafadacin uban nata……” Hannafi ya fada yana leqe da kansa ko zai hangi wani

“Kamar yaya?,daga ganinmu sai yahau fada?”

“Bakasan amadu ba,tosu kansa matar da yaran ba dadinsa suke ji ba,bashi da kirki bashi da mutunci….”

“Hannafi…..”muyar saraki ta ratsa tattaunawarsu

“Yallabai” ya waiwayo yana amsawa cikin girmamawa

“Muyi abinda ya kawomu”

“To…to yallabai,bismillah mu shiga mana” wani kallo samir yayi masa

“A musulunce haramunne ka shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba,Allah cewa yayi kada ku shiga gidajen daba naku ba,har sai kunyi sallama kun nemi izini daga masu gidan……koda kunyi sallamar ma idan suka ce ku koma to ku koma”

“Afuwa ranka ya dade,bari ayi sallama” ya fada yana yaye muryarsa ya doka sallama,yayin da samir ya koma gefe ya goye hannayensa a qirji yana nazarin gidan,gajeriyar katanga wadda idan anso haurawa ba wani abu bane mai wahala,tako ina zagwanyewa take,da alama tafi samun wannan matsalar da damuna,ita kanta qofar gidan kyakkyawan bugu guda daya rak ya isa ya kaita qasa.

Leqowar inna laure yasa hannafi ya dakata da doka sallamar,sunsan juna,sai suka fara gaisawa da ita su samir na tsaye a gefe,da fari cikin fara’a fuskarta take,amma sanda taji wajen wa sukazo sai fara’ar ta dauke dif daga fuskarta,ta koma qarewa su samir kallo.

Ajiyar zuciya ta saki a boye sanda ta gama kallonsu,a haka dai fea suke,amma bataga alamun nera a tattare dasu ba,duk da hakan tanajin ba zata iya yi musu iso wajen zuwaira ba,sai tace

“Ka jira” kawai ta juya zuwa ciki.

Minti daya biyu shuru,dai dai sanda asiya ta keto cikin shigar wani lace,lace ne mai kyau amma an masa dinkin ganin dama,tana tafe tana tauna chewing gum,tana taku ɗai ɗai,tana jin kaf qauyen babu yarinyar data kama qafarta,sani da iya gayu,da kuma morewa rayuwarta,kallo itama ta bisu dashi,daga bisani ta sauke idanunta kan fuskar samir,ido ta zuba masa,can qasa kadan kadan tana hangar wani kyau da tsarin halittar da bata taba ganin irinta ba,wanda ba kowacce mace zata tantance hakan ba,sa irinsu da suka fara gogewa da duniya da sanin maza.

Kwarjinin daya zuba mata da idanunsa su suka sanyata janye nata idon ba shiri,ajiyar zuciya na qwace mata ba tare data sani ba,sai tayi cikin gida,wanda shigarta yayi dai dai da budar bakin hannafi

“Yar kusun uwa mara kunya,kin addabi ‘yar uwarki da rashin mutunci,ke ko koyi da ita bakya yi……” Kallon da samir din ya sake watsa masa yasa yaja bakinsa ya tsuke,saiya waske ta hanyar qarawa gaba ya cusa wuyansa cikin soron yana sake kwarara sallama.

Kaltum dake wankin kayan umma a magangarar ruwa,ta waiwaya ta dubi umma dake zaune saman kan bilal dake kwance,wanda ta gama bawa maganin data jiqa

“Ummanmu kamar sallama ake a waje ko?”

“Eh nima naji,sa hijabinki kije ku duba” dan jim tayi,sam ita yanzu bata son fita ko nan da can,saboda kada ta hadu da auwalu da take ganinsa kamar wani baqin kumurci

“Ummanmu,idan kuma baqin asiya ne fa?”

“Babu lallai,tunda kikaji basu amsa ba” saita tsame hannunta daga ruwan dattin,ta goge jikin tsohon zaninta,ta janyo hijabinta da bata rabo dashi ta zura sannan ta durfafi soron.

Ganin baquwar fuska haf biyu saita ci gaba da takawa a hankali,haka kawai gabanta na faduwa,tana addu’ar ya rabbi ya kauda matsala,ubangiji yasa ba wata sabuwar wutar bace ta kunno kai.

Shi ya fara hangota,tana tahowa a hankali,iska na kadata kamar zata fadi tsabar sirantaka,ba ita kadai iskar ke kadawa ba,harda tsumman zanin jikinta,da hijabinta da yake mannewa a jikinta saboda yadda ya fara tsufa,ga kuma yanayin sanyi da aka fara shiga.

“Ina yininku?” Ta fada a tausashe tana dan rusunawa,muryarta cike da fargaba,karon farko da yaji muryarta dab dashi,karo na uku da mamakin yadda Allah ya bata murya ya mamayeshi,koda yake…..ya tabajin wata hira tasu auta cewar….. majority masu kyan fuska ba kasafai suke da murya mai dadi ba……wadanda kuma suke basu da wani kyau,Allah yakan basu baiwar murya

“Lafiya lau” hannafi da umar suka amsa,sannan hannafin ya dora

“Ya jikin bilalun?,munzo dubashi ne daga wajen aiki” kanta tada sosa sannan tace

“Bari to na fara gayawa ummanmu,saiku shigo”

“To babu laifi”cewar hannafin,saita juya da dan hanzari fiye dana dazu,da alama ta samu qwarin gwiwa ne.

Hijabi ummansu ta saka,ta sanyata kuma ta sake shinfida musu wata tabarmar daban,tare da aje musu ruwa a kwanon sha,sannan ta koma tayi musu iso.

Sosai bilal yayi mamaki,ya kuma ji dadin zuwansun,duk da yadda yake jin jiki.

A nutse kuma cike da hikima samir yake karantar yanayin yaron,yanayin yadda yaga jikinsa a nasa ilimin ya kamaci a kaishi asibiti,saboda yadda yanayin launin idanunsa suka dan jirkita.

Da gani koda ba’a gaya maka ba yasan suna cikin rayuwa ta buqata,saidai babban abinda ya burgeshi,yanayin yadda komai nasu yake a killace a kuma tsaftace,daga inda yake yana hangen yadda take zaune tana wanki da sili silin hannunta,wadanda suke juya kayan da qyar,da alama ba nata bane,tunda ta musu iso ta koma saman kujerar ‘yar tsuguno taci gaba da wankinta.

Yanajin ya kamata ya tallafi rayuwarsu da abinda zai iya,duk mutumin da kunnensa ko idanuwansa suka nuna masa shi a muhallin mabuqaci,kawai yana gayawa kansa Allah ne yayi nufin nuna masan domin ya taimakeshi da abinda ya hore masa na arziqinsa,bare bilal…..haka kawai yakejin yaron ya kwanta masa tun daga wancan lokacin da tazo amsar haqqin dan uwanta har wajen aikin,bai fahimci abinda tayin ba sai daga bisani,daya dinga shiga cikin ma’aikatan yana rayuwa dasu a matsayin ma’aiakaci,ya gane cewa wani zalunci akayi tazo ta dakusar dashi.

Tunaninsa ya katse sanda malam amadu ya danno gidan da wata iriyar sallama,dukkansu su ukun sai yaga reaction dinsu ya canza,har kaltum dake wanki a zaune ta kasa ci gaba da zama,ta saki wankin tana masa sannu da zuwar daya amsa da qyar ta wuce quryar daki.

Bai ankara dasu ba sai daya gama shigowa,saiya kuma saki fuska,kamar ba shine wanda ya shigowa iyalansa a wani yanayi ba.

Suna gama gaisawa samir ya miqe daga tsugonnan da yayi a gaban bilal,don dama bai zauna ba,duk da cewa fes tabarmar take,umar ya kalla kana ya fice bayan ya sake yiwa bilal da umma fatan samun sauqin bilal anan kusa,ya fahimci abinda yake nufi,don haka yana fita ya soma qoqarin ciro kudi,sai hannafi ya qyara masa ya cusawa bilal din qasan filo,don yasan halin malam amadu,haka kuwa akayi,don har suka fice bai lura da kudin ba.

“Bashi da tausayin iyalansa,shegiyar masifa da shegen son kudi kamar tsohon bazawari” maganar data bawa unar dariya kenan suka fito suna darawa,saidai suna iske saraki tsaye a qofa gidan kowa ya kama kanshi suka sake takawa zuwa inda suka fito.

“Gida zamu wuce,inason nakai gida nan da minti talatin” saraki yafada bayan ya gama kallon agogon hannunsa,a mamakance umar ya kalleshi,har ya kasa boye abinda ke bakinsa

“Yallabai kai da bakason gudun wuce qa’ida?”

“Yau nace maka kayi?” Qaramin murmushi yana subuce masa,yau din babbar rana ce mai mihimmanci a wajensa,yau Aamirunsa zai dawo gida,bayan tsahon lokacin daya dauka basa tare,yana buqatar bawa amirun mamaki bayan ya kashe wayoyinsa gaba daya ya kasa samunshi,saidai kawai ya ganshi.

Kamar yadda ya buqata haka kuwa umaf ya tsula gudu iya son ransa a yau din,duk da haka sanda suka iso mintunan ba zasu iseshi ya koma gida yayi wanka ya shirya ba sannan ya tafi tarar amirun ba,don haka yacewa umar su wuce kawai airport din da kayan jikinsa,duk da cewa sun diba qura ba laifi.

Su uku ne a tafe dukkansu sanye da doguwa riga abaya,yammata uku sai qaramar yarinya daya,daya daga cikin ‘yammatan tana riqe da hannun yarinyar daketa faman tsalle tsalle tana son qwacewa

“Laaaa uncle?” Yarinyar ta fada tana qoqarin xame hannunta daga cikin hannun budurwar,abinda yaja hankalin mubina kenan daketa faman hira,ta waiwaya tana dakawa yarinyar tsawa

“Meye hakane afra?” Kafin ta gama maganar ma tuni ta kubuce ta durfafi inda samir yake tsaye,wanda sam hankalinsa ma baya wajen bare yaga tahowar yarinyar,saiji yayi kawai an kama qafafunshi ana cewa

“Uncle….ina ka tafi?” A hankali ya sauke kansa yana kallon fuskar yarinyar,ya tunata,murmushi ya wadaci fuskarsa,saiya tsugunna a gabanta ya kama hannayenta

“Umm….ummm” ya fadi yana qoqarin tuna sunanta

“Afra” ta amsa mishi tana dariya,sai dariya ta qwace masa,shegen wayo ne da yarinyar da alama,gashi harta fahimci abinda yakeson cewa,ta kuma tuna masa

“Keda wa kukazo?” Waiwaya tayi inda mubina tayi mutuwar tsaye tun sanda ta ganshi,tana nuna mishi ita da hannunsa,suka hada idanu na sakanni,saiya janye qwayar idonshi daga kanta,kallonsa kawai ya sanya tayi suman tsaye,taja numfashinta da qyar,ta tattaro dauriyarta tana takawa zuwa inda suke tsugunne,mamaki yana cikata na irin yadda ya gwanance a iya shariya.

Sau daya tak ya daga kai ya kalleta ya maida ga afra sukaci gaba da hirarsu kamar wadanda sukayi mugun sabo da juna,ganin da gaske kamar bai ganta ba saita dan gyara muryarta kadan sannan tace

“Ina wuni” daga kansa yayi kadan ya amsa yana sake maida kansa ga afra,kusan minti uku tana tsaye daga gefe,a nutse take qare masa kallo,da alama yana da son yara,ya sakewa afran sosai,har sai data ji wayarta tana ringing a jaka,saita zaro ta duba,nan ta tarar da tarin missed calls din basma,tana shirin bi wani kiran ya shigo

“Wai ina kuka shiga ne keda afra?”

“Gani nan” ta fada tana maida wayar jakarta tare da cewa

“Zamu tafi” a yangance,saiya miqe tsaye yana saka hannunsa a aljihunsa,yana fatan samun sauran alawar da ya siya daxun yasha,ya kuwa samu guda biyu, chocolate ne,da yake baya rabuwa da alawoyi masi Coco,ya miqa ma afran,hannu biyu ta amsa cikin murna,sai yayi waving hannayensa yana maida mata bye din da take masa har ta isa kusa da mubina.

A sanyaye ta kama hannun afra,tana neman dalilin da zai sanya ta samu number dinsa.

Tsugunnawa tayi gaban afra a tausashe

“Ba zaki karbi number uncle ku dinga gaisawa ba?” Har ya juya zai fara takawa yaji abinda ta fada din,saiya tsaya cak sanda yarinyar ke cewa

“Ehhh kuwa anty,uncleeee” saita diba da sauri tayi wajensa

“Uncle, your phone number please” dauke idanunsa yayi ya maida kan mubina a karon farko,saiya janye idanunsa sanda suka hada ido,ya sakarwa afra murmushi.

“Yes!” Mubina ta fada sanda taga ya ciro biro daga aljihunsa,ya zari qaramar paper ya fara rubutu akai,yana kaiwa qarshe ya miqa ma afra

“Ga number wata antyn taki nan,gidanmu daya,ki dinga kiranta kuna gaisawa,idan kika kira nima zan kiraki, alright?” Kai ta gyada tana murmushi sannan ta sake daga masa hannu ta juya a guje.

Fuska mubina ta bata sanda take kallon jerin gwanon numbers din da wani irin rubutunsa mai kyau,ba haka taso ba, number dinsa taso samu kai tsaye,to wai shin wacece ma antyn afran da yace gidansu daya?,kada dai ace matarsa cema?,saita girgiza kanta da sauri

“No…no it can’t be……” Tunaninta ya katse sanda taji su basma na kiranta,saita kama hannun afra da hanzari suka nufi inda suke tsaye suna faman yi mata mita.

Qyam yake tsaye hannayensa saye cikin aljihun wandonsa,idanunsa gaba daya ya tattarasu ga ina fasinjoji ke fitowa.

A hankali fuskarsa ta washe sanda ya hangi amirunsa,dan uwa kuma babban aminin da bashi da kamarsa,giant ne kamae sarakin,saidai yafi saraki qiba da duhun fata.

Duk yadda yaso shawa amiru kunu saiya kasa,murmushi ya wadata a labbansa,abu guda yaqi masa shine ya taka ya isa inda yake su riski juna har amirun ya cimmashi.

Hannu yasa ya daki kafadar samir

“The giant saraki….wallahi da gaske….ka zama dan qauyen, you are looking qauyis…..kalli kayanka fa?” Dole ya sanya saraki sakin murmushin da yafi kama da dariya,sai ya bashi hannu suka tafa,sannan suka rungume juna.

Suna riqe da hannun juna har suka isa bakin mota,sarakin ya bude musu da kanshi suka shiga,umar ya tashi motar suka bar airport din.

Ko a hanya ma hira suke sosai da sosai,irin hirar dake nuna yadda sukayi kewar juna,kamar ma babu kowa cikin motar saisu,da haka har suka iso gidan professor rashid.

Sanda suka danna horn sai malam datti ya dage musu qofar a maimakon malam salahu,saboda ranar ranar aikin malam salahu ce,suka gaisa a mutunce yana wa zaratan samarin barka da zuwa,fuskarsa cike da annashuwa,don sunyi kewar matasan suda tarin alkhairinsu.

 

*******Tun kusan bayan qarfe goma na dare yake matagugu yana juye juye,tare da fadin sunan Allah

“Cikina ummanmu,cikina….don Allah ku kaini asibiti,akwai matsala a cikin nan nawa” shine abinda bilal din yaketa fada,wanda hakan ya hana idanuwansu bacci,daga umman har kaltume,don tuni kaltume ta fara kuka tana riqe da bilal din tana jera masa sannu,hankalinta yayi matuqar tashi,saboda bata taba ganin bilal din cikin yanayi irin wannan ba na matuqar ciwo,duk da yadda wani lokaci yake da raki.

Duk wani magani da ummanmu take ganin ya kamata ta bawa bilalun ta bashi a daren,amma abun yaci tura,don babu abinda ya sauya daga matagugun da yakeyi na ciwon dake addabarsa,bugu da qari ga wani kumburi da cikin nasa yayi.

Tun babansu na sharewa harya bankada dakinsa ya fito,fada ya farayi,amma da yaga yadda bilal din yake saiya ja bakinsa ya tsuke. Ya dan zauna na mintuna kafin dare ya qara nisa,daga bisani ya tattara ya shige dakinsa ya barsu nan,lokaci lokaci yakan farka,ya leqo yaga bilal,wanda babu wani canji game da jikinsa na samun sauqi,face lafawa da ciwon yakeyi ya dawo.

Hakan ta tilasta musu suna kammala sallar asuba ummanmu da kanta ta shiga maqota,gidan malam sale mai amalanke,ta roqi alfarmar ya fitar dasu can bakin titi,inda zasu samu motar da zata kaisu asibitin cikin birni.

Babu komai malam sale yace,kasancewarsa mutum me matuqar kirki,uwa uba su kansu suna duba kirki irin na umma zuwaira,suna kuma tun alkhairinta a garesu.

“Nidai bani da ko asi,idan zaku iya zuwa to,saidai nace Allah ya kiyaye hanya” cewar malam amadu yana muzurai

“Allah zai rufa asiri” ummanmu ta fada tana duqawa gami da dago bilal,wanda gaba daya jikinsa yayi yaushi,hatta da mazagin wandonsa saida kaltum ta sake daure masa shi,sukayi masa kama kama ita da ummanmu,bayan ta tattaro ‘yan kudadenta da kawu ado ya bata yace taja jari,batakai ga jan jarin ba,tana nazarin sana’ar da zatayi sa wannan lamarin ya ratso.

Babu wanda suke dashi bare suyi masa sallama,malam sale ya daukesu a amalankensa,cikin matuqar nuna tausayawa,bai saukesu ba har sai da aka samu motar da zata kaisu har bakin asibitin sannan ya taimaka musu suka sanya bilal,yana musu fata alkhairi har suka daga,sannan ya juyo cike da tausayawa,yana tuna son aiki da kazar kazar irin na bilal,amma lokaci guda kamar bashi ba,ya tuna sanda sukayi masa aikin katangar gidansa,kusan shine jigon aikin,amma daga baya ma kason da sauran suka samu na kudi shi bai samu kamarsa ba,bai kuma damu da hakan ba.

 

31
D/Z

*wannan littafin na kudine,sharinga dinsa zuwa wasu gurare tamkar zalunci ne garemu,kiyiwa girman Allah ki barshi a inda kika ganshi,idan kin da buqatar karantawa ki biya naki ta wadannan numbers din dake qasa*

08184017082
Ko kuma
09134848107

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button