Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 3

Sponsored Links

Dai dai sanda take kalmashe jela ta qarshe daga kitson data yiwa ummansu yaran sukayi sallama,umman tasu ta janye kanta daga tsakanin qafafun kaltum din tana amsa sallamar kana ta qarashe mitar ta data fara dazu
“Daga yau ba zaki sakemin kitson dare ba” ta fada tana janyo dankwalinta me santsi ta daure kanta dashi.

Hannun kowanne cikin yaran uku riqe yake da littafi exercise da kuma pencil,idanunta a kansu,tana binsu da kallon mamaki,mamakin yadda akayi suka sake dawowa gurinta bayan tataburzar da aka gama yi wancan satin,wanda ya tilast ummanta tayi magana akai,duk da kasancewarta mai matuqar kara da kawaici,ba kasafai akejin bakinta ba kan al’amura da dama ba,wannan yana daya daga cikin dalilin da ya sanya azzaluman mutanen dake tare da ita suke amfani da wannan damar suna cin karensu babu babbaka a kanta,daya daga cikin tarin abubuwan dake ciwa kaltum tuwo a qwarya.

Dukkansu suka haye saman tabarmar suna rige rigen miqa mata littafin hannunsu suna fadin
“Ni zaki fara yiwa,dabbobin dake cikin gidansu kowa akace kowa ya zana,yasa kala” a hankali ta maida dubanta ga ummanta dake zaune daga gefan tabarmar,wanda ta matsa ne ta basu waje ta yadda sararin wajen zai ishesu,a duniya babu abinda take qauna kamar zane,duk da cewar batayi karatun boko ba,amma Allah yayi mata baiwa ta iya zane,wanda dukkaninsu basu isa suce ga daga inda ta samota ba,idan ta zana maka abu zaka rantse da Allah an zanashi ne bisa ilimi da kuma qwarewa,wannan dalilin ya sanya duk sanda aka baiwa yaran zane a makarantar boko basu da wanda suke kawowa sai ita,kusan mafi yawan yaran maqotansu ita ke musu,kota kwatanta musu yadda zasuyi.

Kallon da ta yiwa umman tasu a yanzu ta yishi ne cike da kwadayin ta bata umarni kan tayi musun,saidai ko kallo inda take umman batayi ba,hakan ya sanyayar mata da jiki,ya kuma bata amsar hukuncin daya kamata ta yanke,don haka murya a sanyaye ta dubesu
“Kuje ku kaiwa asiya,ta iya zata zana muku” sak dukkansu sukayi,sai daya daga cikin yaran ne yayi qarfin halin yin magana
“Nidai ki zana min don Allah,Allah wancan karon data zana mana babu wanda yaci,malamin ma sai daya zanemu” ajiyar zuciya ta sauke,cikin sigae lallama tace
“Habibu….kuje,wannan ba mai wuy…..” Kafin ta qarasa taji muryar umman nata sanda take miqewa tana barin tabarmar tana fadin
“Zana musu” wani dadi taji ya sauka har qasan ranta,ba bata lokaci ta miqa hannu don amsar littafin daya daga cikinsu nan fa rigima ta kaure,da qyar ta sasanta su akayi quri a,wanda yaci ta karba nasa,ta qwalawa habiba kira ta basu aron wata fitilar aci bal bal din,ta ajjiyeta a tsakiyarsu,sannan ta duqufa ya fara zanen cike da nishadi.

Boyayyar ajiyar zuciya umma ta saki,daga nan inda take zaune tana iya hango komai yadda yake faruwa,tana iya hangen zallar nishadi a fuskar kaltume din da yadda take zanen cike da karsashi suna hira da yaran,batasan me takeji ba,batasan meye a zane ba har haka da take qaunarsa,saita kuma sakin wata ajiyar zuciyar karo na biyu,zuciyar tata na cika da fata na alheri ga iyalan nata.

Suna tsaka da zanen sallamar wasila ta cika sassan nasu,kaltume da umman tasu suka daga kai suna amsa sallamar,sanye take da atamfa riga da zani sai wani yalolon mayafi saman kanta daya dan soma tattarewa,saboda rashin damuwa da guga,sai data fara gaida umman tasu sannannta durfafo inda kaltume ke zaune,bakinta a washe tana kallonta
“Sarkin zane zane,an fara aikin kenan,ho kaltume kina son zane alqur’an,kamar wata mai iska” ta fada tana cire silifas dinta bayan ta zauna gefan tabarmae da suke zaune a kai,murmushi kaltum tayi mata tana sake saita ruler din dake hannunta tana jan layi saman takardar sannan tace
“Inason zane wasila,dadi nakeji idan inayi,idan na gama kuma nima sai nayita mamakin nice nayi wannan” baki ta tabe
“Aiko….wanda kika yiwa habu rannan ma yana nan ya maqaleshi a dakin babarmu,kowa yazo sai yace waye yayi?,kina da basira sosai kaltume” murmushi tayi kacokam tana sake tattare hankalinta akan zanenta,yayin da wasila taci gaba da yi mata hira ita kuma tana aikinta,tsahon wasu mintuna sannan tace
“Wai ba zaki dandali bane?,yau fa akwai gada me kyau wallahi,nima suwaiba ce ta biyomin,nace su wuce saina biyo mun tafi tare,kada ayi babu ke,don sababbin waqe yau za’ayi” kai ta daga ta dubeta sannan ta mayar ga zanen
“Dama kinyi tafiyarki kawai,kin san ba wani fiya son zuwa nake ba,kuma ko naje ma zuwan nawa bashi da amfani,tunda ba rawa nake ba,kema kin sani” fuska wasila ta bata
“Amma dai duk da haka ko tsaiwa kikayi a wajen kinga mutane suma sun ganki ko?….Allah sai kinje” kai ta kada
“Daina saurin rantsewa mana wasila” bata ankara ba taji wasilan na qwalawa ummansu kira tana kai qararta
“Idan kinkai wannan ki tashi kuje,ai babu dadi tazo takanas don ke amma kice ba zakije ba,amma kada ki jima,ki dawo da wuri” ta gama magana tunda ta hadata da ummansu,itama tasan hakan,dalilin da ya sanya kenan tana kaiwa din ta tattarawa yaran takardunsu ta basu,tana jinsu sunata ihun murna da shewa saboda yadda dukka zanen nasu yayi kyau,ta shiga dakinsu ta dauko dan yalolon hijabinta,wanda ya soma rage kauri saboda yawan wanki da ake masa akai akai,sabili da rashin wadatarsu,dole ya zamana kusan kullum shine dai ɗan ɗaya ɗaya.

Kafin su fice saita tasa qeyar auwalu da sani suka fita tare,don kada babarsu ta fahinci suna sashen nasu qilu ta jawo bau,sai data tabbatar sun shiga sannan suka durfafi zauren gidan dake a bude fayau kamar tsakar gida don ficewa zuwa dandalin.

Zasu fita zai shigo,sai sukayi kacibus dashi,yaya ashiru ne,yayanta ne wanda suke uba daya,shine ɗa na farko a wajen mahaifinsu da matarsa ta farko,wanda tana haifar yara uku zaman aurensu da shi ya qare,saboda wasu tarin dalilai wanda sai a yanzun suke fuskantar wasu daga ciki,dalilan da ita ba zata iya jure musu ba,a yanzun kume sune suka zame musu suda mahaifiyarsu qarfen qafa cikin rayuwarsu.

Baya taja ta gaidashi fuskarta kadaran kadaham,saboda babu wani cikakken shaquwa tsakaninsu,ba wata mu’amala bace can mai zurfi take hadasu ba,iyakarsu dama gaisuwar,shi ashirun baya gidan,yayi aure shida matarsa,gidansa yana can bayan gari,lokaci lokaci yake zuwa gidan,ya gaida mahifinsu ya bashi ihsanin daya kawo masa,zuwan nasan ma kusan asha ruwan tsuntsaye ne,yakan dan dauki wasu kwanaki bai zo ba,hakama me bi masa zubairu,shima kusan kalar tashi rayuwar kenan,qaninsu ne yakubu bai kai gayin aure ba,saidai yana nema har ma ankai kudin na gani ina so,shima dai duk da baiyi auren ba ba kasafai yake zaman gidan ba,wani lokaci yazo yayi kwanaki sannan yayi tafiyarsa,saboda kusan ya fisu rashin kirki ma duk cikin su ukun,duk da suma bawai kirkin suka cika ba,don sau daya basu taba kallon umma a matsayin mahaifiyarsu ba,abinda yasa kaltum ta shata musu layi gaba dayansu,daga gaisuwa ba abinda ke shiga tsakaninsu,saidai idan sunso su din sun qara daga saman hakan.

Basu fiya jure halaye da dabi’un mahaifinsu kamar yadda su kaltume ke dauka ba,hakan ya sanya suke nesa nesa dashi,sai lokaci zuwa lokaci yake ganinsu.

Kadaran kadaham shima ya amsa,suka wuce bayan wasila itama ta gaisheshi,suka jera zuwa dandalin,jefi jefi suna hira da suwaiban,har suka soma gamuwa da wasu daga cikin ‘yammatan qauyen da suma suka makara basu fito da wuri ba,don haka suka rankaya gaba daya da duk wadda suka hadun suka nufi filin.

Sanda suka isa wajen ya cika,samari na hannun hagu a tsaitsaye,yammata na hannun dama,gada ake sosai,kowacce na baje basirarta,yayin da daga bayan fage kuma masu saida rake ne,gyada,balangu da sauran kayan maqulashe,wajen akwai haske sosai,duk da babu wutar nepa,amma sun haskaka wajen da wuta ta kara da kuma fitilun aci bal bal dama fitilun qwayaye na masu siye da siyarwar dake filin,sun riga dasun saba dama,wutar nepa wahala take musu,sukan jima kafin suga wulgawarta,ba kasafai suke damuwa ba,tunda ba wani amfani da ita sosai dama sukeyi ba.

Suna isa kaltume taja ta toge
“Ki shigo don Allah,kin dade bakiyi mana waqarki bafa” magiyar da wasu qwayensu guda biyu nana da basira suka fara yi mata,wanda taja hankalin wasu yammatan suma suka fara roqarta,saboda basira da baiwar murya da Allah ya bata ya sanya kusan kowa keson waqenta,duk da tana tsaiwa ne kawai a filin,bata rawa sam,zata basu wajen su kuma suna juyawa
“Dalla ku qyaleta….don taga tana da murya shine take jawa mutane rai” kubra daya daga cikin qawayen nasu ta fada cikin jin haushi tana komawa cikin filin.

Ko kallonta kaltume bata yi ba tace dasu
“Yau ban shirya yin waqa ba,amma kuyi haquri,duk randa na sake zuwa a shirye,zanzo da wuri nizan fara yi ma” dole suka qyaleta,saboda sunsan halinta,tunda tace ba zata din ba to ba zata ba,saita zauna saman wani kututturen dabino da aka sareshi qasansa yayi saura,tana kallon yadda suke gudanar da al’amuransu.

Kiran sunanta da taji anyi daga gefanta ya sanyata daga kanta da sauri,nasiru ne,saurayi guda daya tilo a garin daya samu damar zuwa jami’a,saurayin da ‘yammatan garin ke rububi qwarai da burin ganin sun mallakeshi,saboda ruwan karatun boko daya fara wankeshi,ya kuma fara sauya masa yanayi da kamanni da ‘yan garin.

Basarwa tayi kamar bata ganshi ba,tana boye murmushin fuskarta,saboda ita din gwanace dama a wannan gefan,tana tuna yadda ya cimmata sanda take samowa inna ruwa a rafi,ya gabatar mata da soyayyarsa,yace a yanzun zai koma makaranta ne zaiyi jarabawa,amma idan ya dawo zai dakaci amsarta.

Saidai zuciyarta ta rabu biyu gami da kokwanto da kuma shakka,saboda wasila data shaida mata cewa kowa na masa kallon kafiri dan wuta kuma dan iska,idonsa ya bude da yawa wai a yadda takejin labari,saboda sudai babu wata makaranta da akeyi me dadewa haka har shekaru masu yawa irin nasa,anfi kyautata zaton kawai sheqe ayarsa da iskancinsa yake tafiya yi birni,amma haka kawai taji jikinta bai bata abinda wasilan ke fada haka bane,saboda tasan jama’ar qauyensu,gwanaye ne kuma qwararru wajen yada jita jita da kuma qadar da abinda basu sani ba,basu da tabbas ma akan hakan.

Kiran sunanta daya sakeyi ya katse mata tunaninta,saita sake waiwayawa ta kalleshi,murmushi ya sakar mata,wanda ya tilastata sassauta fuskarta itama
“Ko zaki daure ki taso mu koma daga can,saboda muryoyin wadan nan basa bari aji maganar mutun sosai,don Allah ba jimawa zakiyi ba,gaisawa kawai zamuyi” shuru tayi tana nazari,tun daxu dama takeson tafiyar,inda ace ma da habiba suka zo da tuni tayi tafiyarta,to habiban ciwon kai takeyi,dalilin da yasa ta barota kenan,ta yiwa wasila magana tun daxu yfi sau uku sai tace mata bari tayi waqar qarshe saisu tafi amma shuru,tana ganin wannan ce damarta kawai da zata koma gida,saboda dare na sakeyi,don haka ta miqe,cike da farincikin yadda ta amsa masa ya motsa yabi bayanta,wani gefe na zuciyarsa yana hango masa banbanci qarara tsakaninta da yammatan garin.

Tana jingine da wani teburin me rake tana sauraren yadda yaketa qoqarin tsara mata kalamai,ba laifi ya burgeta fiye da sauran samarin qauyen,wadanda a cikinsu har yanzu babu wanda ta taba tsaiwa dashi a matsayin saurayinta,duk wanda ta kalla sai taga nutsuwa da hankalinsa baikai mata yadda takeso ba,wani irin fata ne mai girma ya ginu cikin zuciyarta,tun daga lokacin data budi idanu ta fahimci sarai rayuwar gidansu,ta karanci wanne irin miji mahaifiyarsu ke aure,saita samu kanta da gayawa kanta da kanta,lallai ya zama tamkar wajibi a garesu ita da ‘yar uwarta….yin dogon tsinkaye da nazari,sanya hankulansu cikin jikinsu kafin fidda mijin aure.

Abu daya zuciya da qwaqwalwarta ke gaya mata shine….namiji mai ilimi shine haske kuma mafitarsu,duk da ita din ba wata me karatu bace,bata tsira da komai ba banda karatun muhammadiyya da take nema a kullum,amma wata iriyar qwaqwalwa mai zurfi da nauyin tunani….gamida quality na auna dai dai da kuma akasinsa Allah ya bata,a tsahon nazarin data debe lokutta masu tsaho da batasan adadinsu tana yi ba,zuciyarta ta gaya mata jahilci na taja rawa wajen kauda danne haqqin mata,da kuma zaluntarsu.

Idan akace ilimi bawai ana nufin karatun boko ba,a’ah,ana magana ne kan karatun addini,wanda shine tsanu na farko dake saita rayuwar namiji,ya karbi iyalinsa ya kula dasu ta hanyar data dace,tunda shine na farko daya fara koya mana yadda zamu mu’amalanci junanmu tsakanin mutum da mutum hary zuwa gidan aure,ta hanyar haska mana madubin rayuwar gidan ma’aiki S A W(yake ‘yar uwata,indai kinason kubuta daga sharrin kurkukun gidan aure,da baqincikin namiji,a farkon zabin abokin rayuwarki,kiyi qoqari ki zabi namiji me ilimin addini me kuma aiki dashi sama da kowanne irin miji daya mallaki koma wanne irin qyalqyali na duniya,haqiqa idan kikayi hakan kin samawa kanki kyakkyawar mafita da makoma ke da yaran da zaki samarwa al’umma).

Ya dade yana tsara mata kalaman da taji ta gamsu dashi,ya kuma kwanta a ranta,yace ta jirashi minti kadan,bata ankara ba sai gashi ya dawo gareta da tarin siyayya fal leda
“Muje na rakaki,kinga hanyoyin sun soma duhu” ya fada yana murmushi,batace komai ba tayi gaba,ya biyota riqe da ledar da baikai ga miqa mata ita ba.

Basuyi nisa ba idanuwanta suka hango mata asiya cikin wata duhuwa,sosai ta zubawa wajen idanu da kyau,abinda ta gani ya sanyata dauke idanunta babu shiri tana kiran sunan Allah,abu daya da zai hanata riskar asiyan shine nasiru,ba zataso ya gani koya fuskanci wani abu ba,tunda baqo yake ga rayuwarsu,zuciyarta tayi mata baqiqqirin,har bata iya fahimtar abinda nasirun kece mata sosai,a haka suka qarasa qofar gidansu,saiya miqa mata ledar yana murmushi,bay taja kawai ba tare data amsa ba tana kada kai
“Ka barshi na gode”
“Don Allah ki karba,haba kattum,duka saboda na siya fa,indai bawai baki amsa tayina bane” ganin ya damu ya sanyata ta saka hannu ta karba,bata fiya son amsar abu daga hannun samari ba,sabida tasan halin ummansu sarai,ta musu iyaka,hakanan ta shata musu layi daga amsar abun hannun wani,sa’annan tana tsoron karbar abun hannun wani ya zamana aurensu baiyuwu ba,kamar yadda ta faffaru a baya.

Tun a sannana akwai ragowar zumunci tsakaninta da asiya,ita ke feqewa tana zaqalqalewa
“Wallahi karbi abunki,ai bake kika roqa ba,baki sukayi” to koda bata karba din ba asiyan zata karbar mata ita,ta kuma fita ci ma.

Godiya ta yi masa sukayi sallama sannan ta nufi cikin gidan,tun kafin ta isa sassansu ta jiyo muryar kawu iliya shida matarsa,tambaya yake ina asiya,tana kuma shaida masa cewa ita ta aiketa gidan kuluwa,bata dade ai da fita ba,kuma yanzu zata dawo.

Wani abu mai kama da tausayin kawu iliyan ya ratsa kaltum,duk da kasancewar shi dinma babu wata qauna da kulawa da yake nuna musu,shida uwar dakin nasa xamuje ta tadda mujemu,wanda su kansu har yanzu basusan meye ainihin wannan tsana kyara da tsangwama da suke nuna musu ba,amma duk da hakan….abun tausayi ne mace ta rufi uba game da yaransa,rufewar kuma da zata iya zame musu cutarwa me girma cikin rayuwarsu….dama rayuwar wadanda ke kusa dasu.

Sallamar da takeyi ne ta maqale a fatar bakinta sanda ta cusa kai sassan nasu,sakamakon ganin mahaifinsu zaune saman tabarma daga gefan dakinsa,ummanta na duqe daga gefan nasa,idanunsa ya zube fes bisa fuskarta yana mata wani kallo mai nauyi da ban tsoro.

“Kin dawo daga yawon karuwancin naki?” Taji kalmar mai azabar nauyi ta sauka a kunnuwanta,da sauri ummanta ta cira kanta tana kallonshi,habiba dake kwance cikin dakinsu ta miqe ta zauna sosai ba tare data shirya ba,yayin da itama kaltume take kallonsa a matuqar tsorace,kafin ta duqa a wajen a hankali jikinta yana rawa.

Kalaman nashi na yau sunyi tsauri fiye da kullum,a baya yakance kin dawo daga yawon naki!,amma a yau abin nasa yaci gaba,har ya iya dangantata diyar cikinsa da yawon karuwanci?,wannan wanne irin alkaba’i ne?,ledar hannunta ta zame daga hannun nata,saita fadi a wajen ta tarwatse,kayan da suke ciki wanda itama batasan meye da meye a ciki ba suka sukayi dai dai a wajen,ita umman tasu da baban nasu sukabi kayan da kallo.

Tsam baban nasu ya miqe,yana sake cika yana duban ummansu
“Oho….kin gani ko?,kin gani da idanunki,to wallahi bazan yarda,baku isa ba daga ku har uwarku,wallahi zuwaira baki isa ba,gaba daya kin lalatamin yara,banda yawon karuwanci take ina ta samo wadan nan kayan,nidai Allah ya isa tsakanina dake zuwaira,kin cuceni,kinyi amfani da talaucina kin lalatamin yar,yanzu ina bilalu….ace har yanzu yaro bai shigo gidan ubanshi ba?,to idan yazo ki gaya masa ya fita yabarmin gidana,yaje ya kwana a duk inda zai kwana” daga haka ya banka dakinsa ya shige,a guje itama ta miqe tayi dakinsu,tanajin nauyin kalaman mahaifin nasu a kanta da kan mahaifiyarta yana mata yawo tsakiyar kai,kamar ana yamutsa qwaqwalwarta.

Zubewa tayi saman yaloluwar katifarsu data fi kama da tabarma saboda sudewa ta saki kuka mai nauyi,ita kuka habiban kuka,kowa yanajin zafi da radadin kalaman baban nasu har cikin zuciyarsa.

Wani irin kuka take mai cin zuciya,wanda batasan adadin lokacin data kwashe tana yinsa ba,har sai da habiba ta gama nata kukan ta dawo lallashinta,a tsakiyar hakanne sukaji shigowa da kuma fitar bilal daga gidan,da alama umman nasu ta shaida masa cewa kada ya kwana gidan kamar yadda me gidan ya bada umarni,sai kukan kaltumen ya tsagaita,bilal takeji a yanzun ba kanta ba,ta kalli habiba sabbin qwalla na fito mata
“Idan bilal be kwana a gida ba a ina zai wana habiba?,fisabilillahi yana da gidan wani uban ne bayan nan?,a filin gidan nan zai kwana ko a maqota?,ko a jejin Allah ko a gona?” Kafin habiba tace komai ummansu ta daga labulen dakin ta shigo,dukka sai suka bita da kallo har kaltume.

Gefansu ta samu ta zauna,ta kuma ajjiye ledar hannunta a tsakiyarsu,sai data bude sannan kaltume ta gane ledar data saka ce dazun,umman ta maida idanunta kan fuskar kaltum ta kafeta dasu
“Nidai nasan ban baki kudin da zakiyi irin wannan siyayyar ba a dandali,hasalima bamu da arziqin da zaki iya irin wannan siyayyar….kaltum,kada halin matsi da talaucin da muke ciki ya jaki ki aikata abinda zai janyo miki fushin ubangiji da namu gaba daya….kaltum ina kika samu wadan nan kayan?” Ta fada tana kaurara muryarta alamun da gaske take,muryarta cike da tuhuma,abinda ya sanya kaltume sake sakin kuka kenan
“Ba kuka nace kimin ba,ki amsa min tambayarki” ta fada kamar a dan tsawace,muryarta cike taf da kuka ta soma magana
“Ummanmu…..wallahi wallahi wallahi tunda nake ban taba koda sha’awar aikata wani abu makamancin abinda kike tunani ba,idan qarya nake na mutu yanzu a nan,nasiru ne ya siyomin,sai dana ce bazan karba ba yayita yimin magiya,idan kuma har qarya nake Allah…..” Hannu ta daga mata,tana jin tsoronta da firgici daya cika zuciyarta yana kwaranyewa yana sauka daga zuciyarta,duk da cewa tana da qarfin gwiwa da kuma yaqini cikin zuciyarta kan yaranta,yaqinin da kusan rabin qauyen basu dashi akan nasu yaran kamar nata,saidai ta sanyawa ranta ba’a shaidar dan yau,kuma ba zata taba shaidar nata ba,duk sanda wani abu da taji zuciyarta bata gamsu dashi akan yaran nata ba,taci alwashin bin diddigi har sai ta gano gaskiyar lamarin
(Yake uwa!!!,ki xama me yiwa kanki adalci….ki guji shaidar yaranki a duk sanda akacemiki sunyi abu,ki amsa laifin da akace miki sunyi koda zuciyarki bata gamsu da sun aikata ba,ki tsaya kiyi amfani da shekaru da kuma hankalin da Allah ya baki,kibi diddigin wannan maganar har saikin gano gaskiya,idan har abinda aka fada din haka ne,saiki miqe tsaye ba dare ba rana kiga kin gyara,ki hada da addu’a da neman agajin ubangiji,idan kuma kika taras ba hakan bane,saiki godewa Allah,kici gaba da nema musu tsari da kuma addu’ar neman shiriya,Allah ya dafa mana bisa tarbiyyar yaranmu,ubangiji ya iya mana🤲🏽🤲🏽)

“Ya isa,daga yau ban amince ki sake karbar komai daga hannun kowa ba,sannan ki sake kiyayewa,ku tsare kanku,ku tsare mutuncinku,idan ni bana ganinku kuma bana tare daku,Allahn da yayini yayi ku,ya kuma wajabta mana biyayya a gareshi yana tare da kowanne bawa,kudin ‘ya’ya mata ne,sau daya tak aka taba rayuwarku an cuceku,cuta ta har abada,wadda ba zata kankaru ba,wallahi wallahi wallahi duk wadda a cikinku taje ta aikata abinda Allah da manzansa basaso Allah ya isa tsakanina da ita ban yafe mata ba” daga wannan ta miqe,tana jin zuciyarta na samun nutsuwa,ta yarda da tarbiyyar data bawa yaranta,saidai hausawa suna cewa,ana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro,sannan Allah yana cewa:ku tunatar,domin tunatarwa tana amfanar da mumini.

*_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥🔥🔥
*_Bononza kashi na hudu !!!_*

*Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!*

*Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal*

*MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN*

6019473875
MUSAA SAFIYA ABDULLAHI
keystone Bank

*Saiki tura shaidar biya ta nan*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
08184017082

*Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*👇🏾👇🏾👇🏾
09134848107

*_ALLAH YA BAWA ME RABO SA’A_*

 

*ƊABI’AR ZUCIYA*
*Free page*
04

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button