Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 2

Sponsored Links

Saida habiba ta qara hanzari sannan ta cimmata
“Ga kudin yaaya” waiwayowa tayi ta dubi kudin sannan ta kalleta tana ci gaba da tafia
“Saura kadan na daina yiwa mutane da yawa kitso cikin qauyen nan” kai habiba ta kada tana sake matsowa sosai kusa da ita
“Kada kiyi fushi yaaya,indai kana sana’a dole ka sanya haquri”
“Na fara gajiya da wulaqancinsu da cin fuskarsu,ta yaya za’ayi ace kaida haqqinka sai an wulaqantaka sannan a baka,sai kace bara kayi ko roqo?”
“Kiyi haquri,komai mai wucewa ne,watarana sai labari” shuru tayi bata amsata ba,haka suka ci gaba da tafiya tana hadiyar bacin ranta,tana son ta cinye abinda ke ranta kafin su isa gida,don bataso ta koma wa ummansu a haka bare ta damu da sanin abinda ya faru.

Kanti lawandi suka nufa da niyyar siyan garin kwaki da suger su isa gida dashi,saidai sun taras kantin nasa a rufe yake,saboda rana ta tasa,wala’alla sai wajejen la’asar kuma zaya sake budewa,tsaki kaltum taja
“Kinga,zo mubi ta gidansu wasila,baabarsu tana siyarwa saimu siya a can” da haka suka karkata suka bi wata hanya dake hannun hagunsu.

Wasila itace qawa daya tilo wadda kaltum keda ita kaf fadin qauyen,kusan kowa ya sansu tare,kasancewar bata da tarin qawaye bare ta sanyasu a jikinta,shi yasa wasilan ce kawai za’a iya kiranta qawa ta sosai ga kaltume,akwai sauran ‘yammata da take hulda dasu,saidai mu’amalarsu ta tsaya ne kawai iya gaisuwar mutunci,koma bayan wasilan da takanyi shawara da ita,kuma sukanyi musayar sirri a wadansu lokuttan.

Kusan tare sukayi sallama ita da habiba a tsakar gidansu wasilan,gidan nasu su sassa uku ne,daya hada da nata sassan dana qannen babanta su biyu,babar wasila da daya matar qanin baban nata ta samu qarqashin rumfar da suke girki,an sauke tukunya ana kwashe abincin rana,a ladabce kamar yadda halayya da dabi’arsu take suka duqa suka gaidasu,suka amsa suna tambayar ummansu
“Hala kin biyo qawartaki ne,yau baki ganta ba ko?” Babar wasila ta fada tana dariya,murmushi kaltum tayi,sannan ta amsata
“Dama munyi magana da ita jiya,tace zata shiga talla yau har ɓaure,bata dawo ba kenan?”
“Wallahi,inata dai zuba ido,nasan tana kan hanya” kaltum din bata amsa ba saita miqa mata kudin hannunta
“Kwaki zaki bamu baaba na hamsin sukari na hamsin”
“To…to” ta fada tana karbar kudin,sannan ta miqe tana dosar sassanta.

Tana shiga babu jimawa wasila ta kwada sallama farfajiyar gidan,kanta dauke da babbar kwalla wadda akw cika mata ita da awara kusan kullum kwanan duniya,abu guda daya tak da basu taba yiba tsahon rayuwarsu shine talla,ko kusa ko alama ummansu tace bata da sha’awar dora musu tallan koda tana da jarin yin abun sana’a,ta gwammace tayi koma meye a gidan,idan da rabo za’a shigo har inda take a siya,abinda mutane da dama sukewa kallon ba komai bane illa zallar girman kai da ganin tafi wani,ganin cewa kusan mafi yawa mafi akasari ‘yammatan qauyen suna talla,kuma dashi suka dogara,don yawancinsu dashi sukewa kansu kayan daki kaf harda sauran canji da za’ayi shagalin biki dashi.

Da sauri kaltum ta qarasa tana tayata sauke kwallar daga kanta,ta duqa suka ajjiyeta a qasa a tare,saita dago tana kallon wasilan cikin murmushi
“Sannu…yanzu muke zancanki da baba” gammon dake kanta ta sauke ta riqe a hannunta tana gantsarewa,alamun bayanta ya riqe,fuskarta a yatsine tace
“Wallahi wahalar abun hawa,sai da muka sha wahala yau kafin mu samu abun hawan daya qaraso damu cikin qauyen nan”.

Kafin kaltum tace wani abu baabar wasila ta fito da baqar leda a hannunta,ta miqawa habiba da tafi kusa da ita tana kallon diyar tata
“Yar halak kinqi ambato,yanzun nan muke maganarki nida qawar taki” bata amsa mata ba sai data isa saman wani turmi dake girke a wajen ta zauna sannan tace
“Ni yau babarmu ba abinda nasha sai baqar wahala,saboda kaf masu abun hawa kin qarasowa sukayi wallahi” ganin sun shiga wata magana daban yasa kaltume motsawa,don itama saurin take,kaf hankalinta ya tafi gida inda suka baro ummansu,fatanta su isa su samu su jiqa garin susha ko zasu toshe wata kafar
“Baabar wasila sai anjima,wasila munyi gida” saita dan zabura
“A ah ki tsaya mana mucu abinci,gashi babarmu ta gama?,kuma ma inaso muyi zance dake wallahi” kaita girgiza,duk da cewa yadda kayan cikinta ke qugi,suna kuma haduwa su cure waje daya,kana su saki bayan wani lokaci,ba abinda suka fi buqata kamar abinci me zafi irin wannan,amma saidai duk da yadda suka kai ga buqatar abu,zaiyi wuya su amsa hannun wani,ummarsu ta riga ta horesu,ta kuma tarbiyyancesu da gudun abun hannun mutane,da gujewa dabi’ar kwadayi,tasha gaya musu sau tarin da babu adadi
“Indai kanaso kayi qima da mutunci a idanun al’umma,to ka guji abun hannunsu,saboda shi kwadayi shine mabudin dukkan wani sharri”,wannan yana daya daga cikin karatun data riqe ram a kanta
“Ki barshi kawai suwaiba,ummanmu nacan na jiranmu,nace mata ba zamu dade ba….kada ki damu,idan mun hadu mayi maganar” ta qarasa fadin maganar tana kama hannun habiba dake tsaye kusa da ita
“Shikenan,an jima a dandali mayi maganar….don Allah yau kada kice ba zaki fita ba kamar yadda kika saba” qaramin murmushi tayi wanda ya fitar da lobawar kumatunta data mallaka a daya daga cikin kumatunta
“Idan dai banyi bacci da wuri ba ba” taja hannun habiba suka wuce,tana jiyo suwaiba naci gaba da yi mata magiyar fitowar tata.

Layi daya ne a tsakaninsu,don haka babu jimawa suka qarasa gida,a bakin inda suke tara ruwa ta hangi bilal durqushe yana wanke qafafunsa,wadanda sukayi futu futu suka kuma yi jazur da kwababbiyar qasa,da gani babu tambaya yauma wuni sukayi suna aikin kwaba laka tayin bulon qasa,yayin da umman tasu ke zaune a wajen da yawanci suke kashe wuninsu a nan,qafafunta miqe har mai ciwon,idanunta akan bilal,wanda kallo daya zaka mata ka canki cewa akwai wani dan tunani dake kai komo cikin ranta dai dai wannan lokacin.

Sallamarsu ta sanya bilal dagowa yana dubansu,kusan lokaci daya suka amsa sallamar da ummansu wadda ta bisu da kallo bayan sun shigo din,fargaba tana cika qirjinta kan cewa Allah ya sanya ta samo biyan bashin,idan har ba’a samun ba kuwa ta tabbata zasu wuni sur ba tare da qwayar gero ta ratsa cikinsu ba.

Ledar hannun habiba ta sanyata sakin boyayyar ajiyar zuciya,dai dai sanda ta jiyo muryar kaltum tana yiwa bilal fadan data saba lokaci zuwa lokaci
“Shikenan kai ba zaka dinga zama kana hutawa ranka ba,ba dare ba rana kullum cikin bautar aikin al’umma kake,duk da suna biyanka amma aikin yana yin yawa a matakin shekarunka,idan an ganka zaune haka kawai baka komai saidai idan dare yayi ko kuma baka da lafiya” dai dai sanda ya gama wanke jikin nasa,ya soma tube rigarsa ya cilla saman igiyar da suke shanya idan sunyi wanki
“Saina zauna yaaya zuciyata ta mutu tun yanzu?,nifa a ganina amfanin lafiyar da Allah yayimin kenan”
“Eh haka fa…..shi yasa baka iya tattali ba,komai ka raruma ka kai cikinka?” Ta masa tambayar sanda habiba ke qoqarin juye garin cikin wata madaidaiciyar roba yadda zasu jiqashi da kyau ta yadda zaifi musu auki,maimakon ya amsa tambayar kaltume sai yace
“Kai kai…..habi,Allah karki jiqa dani,haka kawai,ace kullum aikinmu kenan sai kace awaki,gaskiya bazanci garin nan ba na gaji dashi”
“Kajimin dan rainin wayo,idan baka ci ba saika gayamin me kake dashi da zakaci?” Habiba ta fada tana jifansa da harara,yayin da umma da umma ta zuba masa ido,kaltum kam kota kansa bata biba,don ta saba da halayyar bilal din,matuqar taji ya fadi haka to la shakka an biyashi kudin aikinsa ne.

“Hakanan zakayi haquri bilal kaci,idan yaso ko zuwa anjima idan babanku ya shigo sai a sarrafa wani abun”
“Ai wallahi kawai ku rufe garin nan,umma bari naje na samo mana shinkafa….an biyani kudin aikina na shekaran jiya jiya da yau”
“Bilal” umman ta kira sunansa
“Amma shine zaka barnatar da kudin a wunin yau kawai?” Fuska ya narke yana kallon umman
“To umma dama ba don aci ba ake neman?” Sai a sannan kaltum data dauko kofuna ta kalleshi,koda yaushe tunanin bilal din daban yake,abinda ya dameku sau tari shi bashi ya dameshi ba,babbar damuwar bilal din yaji yunwa cikin cikinsa,koda ace bashi da kudi….matuqar zai qoshi to yayi maganin dukkan matsalarsa,abu daya takejin dadi,kamar yadda suke zuwa makarantar allo da sassafe haka shima ke zuwa,duk da karatun nasa baya sauri kamar nasu,amma yana bakin qoqarinsa wajen zuwan da bibiyar karatun.

“Ba saboda ciki ba kawai ake nema….bilal baka sha’awar karatun boko?,kamar yadda yaran kowa keyi?,tunda su ‘yan uwanka duka mata ne,kuma su basu samu damar yi ba?” Kai ya rausayar yana nufar qofa
“Wanne karatun boko umma……kawai….kawai…..” Bai qarasa furta abinda ke zuciyar tasa ba ya fice daga sashen nasu,kai kawai ta girgiza tana dauke idanunta daga kanshi bayan ya fice,ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana sauke idanunta qasa,tsahon wasu sakanni tana saqar zuci,kafin ta tsinto muryar habiba na fadin
“Umma…an gama” muryarta na nuna ba kiran farko kenan data yi mata ba,kanta ta daga da sauri,da kaltume suka fara hada idanu,tun dazun da tabar musu gangar jikinta,ta dauki zuciyarta ta lula duniyar tunani kaltume ke nazartarta,kullum kwanan duniya cikin damuwa zuciyar mahaifiyar tasu take,damuwa ta zama daya daga cikin abubuwan dake damfare da rayuwarta,takan jima cikin rauni tausayi da wani irin narkewar zuciya a duk sanda ta daga idanu ta kalli mahaifiyarta,macace mai tarin haquri nutsuwa ibada da hangen nesa,saidai matsaloli sun taru sun dabaibaye mata rayuwa,suka kuma hada harda tasu rayuwar sukayi tafiyar ruwa da su.

Duk da nata kofin na riqe a hannunta amma ta kasa shan garin,sai juya cokalin ciki kawai da takeyi,kamar yadda ta karanci ba wani ci sosai umman tasu takeyi ba itama,ita kadai tasan tarin abubuwan dake cunkushe cikin qirjinta,wanda girma da nauyinsu yake sanyata wani lokaci kamar ba zata iya dauka ba.

Bai jima ba bilal din ya dawo da shinkafar hausa gwangwani uku,dai mai da barkono da dunqulen maggi,sai kuma ya zauna ya amshi garin shima ya soma sha,yana yi yana basu labarai wadanda duka kusan abubuwan da suka faru ne a wajen aikin da yakeyi.

Kaltum ce ta karbi shinkafar ta juye saman faranti ta soma tsince dattin dake ciki,tana yi tana sauraren hirarrakin bilal din,wanda a ciki take nazartar abubuwa da dama da suke da alaqa da rayuwar bilal din,wanda wala’alla shi din qarancin shekaru ya sanya hankali da tunaninsa baika ga hango hakan ba.

Kakkaurar muryar data karade filin tsakar gidan nasu zuwa sassan nasu cikin furucin sallama ya sanya kowanne cikinsu ya tsaya cak,yanayin kowannensu ya soma sauyawa daga ainihin yadda yake a dazun zuwa wani nau’i na daban.

Ga kaltum dai sake duqar da kanta tayi sosai ga farantin da tak tsintar shinkafar bayan ta sake riqeshi da hannu daya,habiba wadda ke a kashingide saita tashi ta zauna sosai,ta jingina bayanta da katangar dakinsu,yayin da bilal wanda ke riqe da kofin garinsa,wanda surutu ya hanashi gama sha da wuri ya soma kai garin bakinsa sannu a hankali kamar me tsoron tauna wani abu,ummansu kuwa saita janye qafafunta dake a miqe a dazun,duk da cewar akwai mai ciwo a ciki,amma bata kula da wannan ba.

Dattijo ne wanda a qalla shekarunsa zasukai hamsin da bakwai zuwa da takwas,yana sanye da wani farin yadi da kana masa kallo daya na tsanaki zakasan ba farin Allah da annabi bane,ko ince ba farinsa kenan na ainihi ba,hadda farin dadewa da kuma yadda yake shan wanki,qafarsa slippers ne da ake kira dan madina,wanda wa’adin rayuwarsa yakai tsakiya,ba wani tsufa yayi na azo a gani ba,amma ya dauko hanyar tsufan.

Tun daga yanayin fuskarsa zakasan cewa ba ma’abocin wasa ko sakin fuska bane,wala’alla haka yanayinsa yake?,ko kuma shine ya maida kan nasa hakan?.

Kusan a tare kamar hadin baki suka amsa sallamar daya sake kwadawa,a qoqarin da kowa yake na ganin cewa ya kaucema zama mai laifi na farko a wajensa daga isowarshi cikinsu.

“Sannu da xuwa baaba” habiba da bilal suka hada baki wajen fada
“Yauwa” ya amsa yana sauke kallonsa mai kama da harara kan bilal
“Kai…..” Da sauri bilal din ya daga kai yana dubansa hadi da aje kofin hannunsa,don ko bai gama cin garin ba hakanan yakejin ya qoshi
“Uban waye ya daure maka gindin daukar min takalmi ka saka?” Ya fada cikin fada,dukkansu suka kai dubansu ga takalmin dake qafar bilal din,takalmi ne da dadde wanda mahaifin nasu ya jima yana cin duniyarsa dashi,ya kuma kakkatse saboda gajiya da yayi da yadda ake morarsa fiye da kima,dalilin da ya sanya baban nasu ya jefashi cikin tarin shirginsa dake aje dafa’an gefan qofar dakinsa,baiko sake bi ta kansa ba,har sai dazu da bilal din zai fita aiki,bashi kuma da takalmin da zai sanya din,ya dauki takalmin ya fita dashi aka diddinke masa,ko kudin bai samu sukunin biya ba,sai daya dawo daga aikin aka biyashi,sannan ya biya ta rumfar shu’aibun ya biyashi kudin gyaran,amma shine a yanzun daga shigowarsa,ko kyakkyawar iskar gidan bai gama shaqa ba,idanunsa suka sauka kan takalmin,ya kuma dira masifarsa akai.

“Wato kana jina ma ina magana kayimin shuru ko?,ga dan iska yana baloqoqo….koda yake….ba laifinka bane,laifin uwarku ne,ita ta sanya kuka rainani,saboda bani da komai ban mallaki komai ba,to duk tsiya dai nine ubanku,bata isa ta canza muku wani uban ba”.

A hankali umman ta saukar da idanunta qasa,tana jin yadda idanunta keson tara ruwan hawaye su fito zuwa saman fuskart don rage radadin da take ji cikin zuciyarta amma ta hana hakan faruwa,kome amadu zaiyi mata,koda yankar naman jikinta zaiyi zata iya jurewa ta shanye,abu daya ne da bataso,takejin tarin tozarci,rashin daraja da qimarta na ratsa har cikin qashinta shine ya tashi wannan tijarar gaban yaransu,yaran da ako da yaushe take tattalin tarbiyyarsu,take yaqi da fadin tashi tsaida martabar ubansu daram cikin idanunsu,koda basu so hakan ba,saidai a kullum shi dinne mutum na farko dake fara hawa kan kyakkyawan gini da tubalin data azasu ya rusa komai da komai,ba gaban yaran ba….hatta da faccalarta kusan haka ne,daya daga cikin abinda ya zamo tushe na zallar raini qanqanci da kyara da take mata ita da yaranta ba dare ba rana,kuma babban makamin gori da tayi riqo dashi,take gallazawa da gasa zuciyarta dashi
“Ahaf….aiki cika mace har a wajen miji shine kika ci sunan mace” wadan nan qayyadaddun kalmomi ta dade tana amfani dasu wasu cutar da zuciya da tunaninta,batakai ga fita daga wannan ba ta sake jin muryarsa yana fadin
“Saboda tsabar iskanci da ganin dama keda ‘yarki ban isa kuyimin sannu da zuwa ba ko?,gaku riqaqqu tatattu…..ke dama sababbiya ce cikin yarana kaf kin fita zakka….” Bai sauke numfashi ba bare ya basu damar furta komai ya dora kan gaba ta biyu ta zancansa
“Wannan shinkafar kuma a ina aka samota?,ko yauma anje an saidamun mutunci ne aka baku sadakarta?” Yayi tambayr idanunsa akan kaltume,kamar wanda ke jiran qiris yakai mata bugu,itace mutum ta biyu data fi kowa karbar bahagon halayyarsa baya ga mahaifiyarta,sau tari idan yana wasu halayen a kanta sai taji shakka da tantamar kasancewarsa mahaifinta yana shigarta,cikin sanyin jiki data murya tace
“Bilal ne ya kawo…..,sannu da zuwa” ta hada harda gaisuwar da yake mita a kanta,duk da cewa dama ce bai basu ba da zasu marabceshin,maimakon ya amsa duk da ya nuna muradinsa na yi masa maraban….a’ah….saiya waiwaya ya sake duban bilal wanda ta miqe tun dazu yana jiran ya gama fadan ya shige daki,shi kuma ya samu ya fice,don ya tabbatar ya kuskura ya fitan yana tsaka da fada,ya sake jawa kansa wani sabon al’amarin
“Wato kai na fuskanceka,mugu ne kai wani lokacin,ni ina can ina fafutukar sama muku abinda zakuci,kai kuma kana nan kana kashewa uwarka da ‘yan uwanka duniya,tunda kake nemanka qwandala baka taba kawomin na sanya albarka ba,saboda tsabar baqin hali irin naka,shegen yaro dan iskan banza da wofi,fitarmin daga gidana kafin na sanya itace na sauke maka gwiwoyi”idanu umma ta rintse sosai,tana jin wani zafi yana ratsa qirjinta,koda zaiyi sala sala da namansu ‘ya’yansa ne,bata data cewa,bata kuma da wani iko saman nasa,saidai bata qaunar kalaman da yake yawan furtawa akan bilal da kaltume,kalamaine da duk yadda takai ga jurewa dauke kai da alkunya amma sai sun taba can cikin zuciyarta,tana tsoro….tana tsoron wani abu…..wani abun da bame kyau bane da zai iya faruwa watan watarana,ko ba komai shi din mahaifi ne,daya kamata ace shi ya zama garkuwa ta farko a garesu.

Bin bilal yayi da kallo.harya fice sannan ya dauke idanunsa,ya taka ya nufi dakinsa dake a kulle da muqulli,dakin da dukkansu haka suka taso suka ganshi,koda yaushe a rufe,baya barin kowa ya gitta ta qofar dakin bare akai ga batun shiga ciki,koda mahaifiyarsu kuwa tana da geji a dakin,baresu karan kada miya da basusan komai ba,banda kalar labulen dakin babu abinda zasu iya dorarwa a cikinsa.

Suna jin sanda ya wulla taliya qwaya biyu daya shigo da ita a baqar leda cikin dakin,wadda dama bai taba basu sama da hakan ba yana mitar
“Tunda kunyi gaban kanku kun samowa kanku abunci aini gaba ta kaini” sannan ya dauko butarsa daga cikin dakin ya wuce bayi.

Shuru ne yaci gaba da wanzuwa a tsakaninsu,kowanne da irin tunanin dake kai kawo tsakanin qwaqwalwa da zuciyarsa.

Sosai wani irin bacin rai yake ratsata,har bata qaunar koda motsawa ne ma tayi bare tayi tozali da fuskar mahaifiyarta,fuskar data tabbatar babu abunda ke yawo a samanta illa bacin rai wanda ke cike maqil a zuciyarta,duk da kasancewarta jaruma,mai qarfin hali juriya da jumurin cinye duk wani bacin rai,saidai kasancewarta cikin ‘yan adam da aka halitta da ajizanci….qoqarinta wani lokaci yakan gaza kaiwa ga gaci.

Duk da irin cin zarafin da yabita dashi ita yaran nata,hakan bai sanya farar zuciyarta ta daina girmamashi ko sauke dukkan wani haqqi daya rataya saman wuyanta ba,matsayinsa yana nan babu abinda ya canza…..kamar dai yanzun,data yunqura ta miqe bayan fitowarsa daga bandaki,duk da ciwon dake qafarta,duk da bata da abun bashi kamar yadda bai basu komai ba,face bacin rai cin fuska da rashin tabbas.

Cike da sanyi da nutsuwa tayi sallama tana yaye labulen dakin,dai dai lokacin da yayi hanzarin cusa kudin daya fiddosu cikin aljihunsa yana zare idanu gami da sake hade rai,dai dai kuma lokacin da kaltume ta dauke idanunta daga kan mahaifiyarta data yi mata rakiya dasu har zuwa sanda ta daga labulen dakin mahaifinsu,saita sauke idanun nata kan habiba,suka hada idanu,wanda hakan ke bayyana mata yadda abunda ke faruwan yake sukar zuciyarta haka yake sukar zuciyar habiban,banbancin kawai ita din ta iya hadiyewa da kuma cinyewa.

A tare suka janye idanun nasu daga na junansu,da alama kowanne abun ya masa nauyi tun daga baki zuwa zuciya,cin zarafin mahaifiyarsu a gaban idanuwansu,abune da har yau zukatansu suka kasa sabawa dashi………..

“Ya zaki fadomin daki haka kai tsaye ba tare da neman izini ba,wannan wanne irin halin banza ne amina?”

Wadan nan sune kalaman daya taryeta dasu sanda take samun waje tana tsugunnawa saman qafafunta,kanta a qasa ta furta
“Sannu da zuwa…..kayi haquri” shuru yayi yana maida numfashi,tare da tunanin abu na gaba da zai janyo,wanda zai janye tunaninta daga kudin da taga yana turawa yanzu yanzu a aljihunsa,ya nema abun laifi sama da qasa ya rasa,kuma har ga Allah so yake ta fita ya samu ya sake ya lissafa kudadensa ya musu ma’ajiya,don haka ya yunqura ya janyo ledar taliyar daya wurgar ya jefa mata saman cinya
“Idan don taliyar dana adana muku ce keda ‘ya’yanki saboda gobe kika kasa haquri kika biyota…gatanan,tashi ki bani waje” cikin matuqar karaya ta girgixa kanta
“Ba ita na biyo ba yaaya,ko kadan kada ka kawo haka cikin ranka”
“To meye na biyonin zungui zungui na shigo xan huta” mamaki ya rarrafo a guje ya rufeta,me yasa shi kullum a hagunce yake?,koda yaushe ba’ayi masa dai dai?,me tayi masa ne haka ya maisheta wata babbar abokiyar adawarta?.

Bata manta ba ajiya akan haka ya sauke mata dukkan wani sababi iya son ransa,sanda ya shigo tana can tana fama da qafarta,duk da irin zogi da radadin da take mata haka tayi qoqari ta yunqura ta iskeshi,maimakon ya yabata mata….a’ah…..sai yahau masifa da tashin hankali,dan jinkirin kawai da tayi bata qaraso wajensa da wuri ba,amma sai gashi yau awannin da basu haura ashirin ba yana kuma qalubalantarta akan hakan,kawai saita miqe tsam,hannunta dauke da ledar taliyar,saboda ta tabbata barinta a wajen kamar ta sake jawa kanta wani sabon tashin hankalinne……..

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

 

 

*DABI’AR ZUCIYA*
03
*Free page*

*_GARABASA DAGA ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥🔥🔥
*_Bononza kashi na hudu !!!_*

*Mun saurara koken masoya,mun kuma amsa,domin farincikinku shine namu!!!*

*Daga yau zuwa TALATA zuwa gobe LARABA,zaki iya samun litattafan zafafa biyar bisa farashin ragi wato 700 kacal*

*MAZA GARZAYA KAFIN RAHUSAR TA QARE,KI TURA 700 DINKI ZUWA WANNAN LAMBAR ACCOUNT DIN*

6019473875
MUSAA SAFIYA ABDULLAHI
keystone Bank

*Saiki tura shaidar biya ta nan*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
08184017082

*Ga masu tura katin waya ko kuma VTU,saiku tura ta nan,kudi da shaidar biya*👇🏾👇🏾👇🏾
09134848107

*_ALLAH YA BAWA ME RABO SA’A_*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button