Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 1

Sponsored Links

FREE PAGE_ 01

Rana ce sosai wadda ta qwalle daga kowanne sashe na sararin subhana zuwa fadin filin duniya iyakar hangen dan adam,wadda take bada tsananin haske da kuma zafi,irin zafin dake sanyawa kowanne mai rai wala mutum ko dabba neman mafaka da zai samu inuwa da zata hutashshehi ta kuma dauke zafi da radadin da ranar ta haifar tun daga gangar jiki izuwa qwaqwalwa.

A irin wannan lokacinne ummukulsum ke tafiya cike da bacin rai da wani irin fushi,yarinya matashiya,wadda gaba daya shekarunta ba zasu haura sha biyar kacal a duniya ba.

Baqa ce ita,ba irin wuluk din nan ba,saidai tafi chocolate colour duhun fata,tana da yalwar gashin kai dana gira,madaidaicin baki da matsakaitan idanuwa,tana da baiwar fararen idanuwa,haqoran bakinta milk colour ne masu qyalli,madaidaicin baki da matsakaiciyar haba wadda ta qawata shape din fuskarta,a taqaice ummukulsum na cikin mata masu matsakaicin kyau.

Zafin da take ji a zuciyarta yafi wanda takeji a tsakar kanta sanda ranar ke kwadarta,idanunta cika yake da hawaye tana ta qoqarin maidashi,saboda sam batason tayi kukan,mutum ce ita mai jumuri da dakakkiyar zuciya,wanda wasu suka fassara hakan da tsananin taurin kai da kuma baqin hali.

Tana tafe tana hadiye abinda ya dunqule mata a wuyan,tana kuma duban yadda hanyoyin layukansu ya dade qwal babu jama’a,da alama kowa ya nufi gona,wadanda kuma basu da gonakin zuwa ko basu da abinda xasuyi cikin gonar sun tafi sabgogin gabansu.

Hannun hagunta ta kalla sanda take gab da gota wani siririn lungu,saita yanke shawarar tabi tanan din,don zaifi mata saurin isa gida,duk da ba kasafai ta fiya son bin lungun ba saidai dole,hatta da mahaifiyarta wani lokaci takan ce su haqura da bin hanyar,saidai a yanzun tana son isa gida da wuri ne,don ta baro mahaifiyar tata tana dakon dawowarta.

Ko tsakiyar lungun batayi ba ta soma hangota,asiya,’yar uwarta ta jini,wadda suke ‘ya’yan maza zar ita da ita,da mahaifinta da nata mahaifin uwa daya uba daya suke.

Ci gaba tayi da nufosu yayin data kafesu da idanuwa tana kallonsu.

Ita da ayuba,daya daga cikin matsan qauyen wadanda suke ji da tashen samartaka,ta gefe guda kuma sukeji da tashen rashin kunya,rashin ganin girman kowa,iskanci rashin tarbiyya da badala iri iri,saidai duk da wannan halayya tasa kusan babu wanda yake iya bugar qirji ya qalubalanceshi,shi din ko kuma daya daga cikin abokansa,sakamakon mahaifinsa ya kasance mai abun hannunsa cikin fadin qauyen,ta daya gefan kuma,mahaifiyarsa qanwa ce ga mai garin garin nasu,hakan ya sanya yake iya aikata dukkan abinda yaso,ya kuma taka dukkan wanda yaga dama,cike da gadara da kuma ganin karensa yakai tsaiko.

Asiyan na sanye da uniform na makarantar boko,makarantar da suka sha gori baqar magana gami da habaici kala kala a kanta,makarantar da ake mata wani kallo na musamman,aka dora dukkan buri na ci gaba kyautatuwa da gyaruwar rayuwar asiyan ita da duk wanda ya jibanceta a kanta.

Gefe daya ayuba ne tsaye gab da ita,kamar zasu shige jikin juna,magana suke da juna,saidai ba zata iya jin abinda suke fada ba,sakamakon ‘yar tazarar dake tsakaninsu,sosai ranta ya sake baci fiye da dazun lokacin da ta hanhi ayuban ya kama hannun asiyan ya riqe cikin nasa,wannan ba shine karon farko da taga asiyan cikin wani yanayi da yayi kama da wannan ba,saidai babu wanda ta taba furtawa bayaga mahaifiyarta,kuma har yau har kwanan gobe itace mutum daya tak data taba shaidawa abinda idanun nata ya gani,wanda daga bisani data fuskanci mahaifiyar tata batason dukka wata magana daya danganci wannan sai ta daina gaya matan,saidai a kullum kwanan duniya,duk sanda zata ga asiyan a yanayi irin wannan,tana jin ciwo sosai cikin ranta,tana jin baqinciki,amma ita din babu yadda zatayi da ita,saboda bata da wani iko ko qarfi wajen yanke hukunci cikin al’amuranta,haka taci gaba da takawa harta iskesu,ta kuma rabasu ta wuce ba tare data ce da kowa cikinsu komai ba,yayin da asiya da ayuban suka bita da kallo,har sai data kusa bace musu sannan suka dauke dubansu daga kanta lokaci guda
“Yar gidanku ta ganmu asy,kina ganin ba zata kai maganar gida ba?” Baki ta tabe tana gyara tsaiwarta sannan ta dubeshi
“To saime don ta ganmu?,zancan kai magana gida bata taba ba,don ba yau farau ba” wani duba yayi mata,a zahiri yayi kama dana burgewa dana qauna,saidai can qasan ransa yana taɗinta shi daya
“Ashema fanko ce,ballagaza,bani kadai ma kenan na saba latsawa ba,bari na saki jiki kawai na kwashi rabona,indai kudi ne matsalarta ta samu”, da wannan zancan zucin ya jefeta da murmushi,wanda ya sanyata itama ta maida masa martani.

Tana gamutsa wadan nan abubuwa guda biyu cikin kwanyarta ta fuskanci gidansu,gidan da kullum tsanarsa ke qara darsuwa cikin ranta,ana cewa da uba ake ado,itakam anan ta qalubalanci wannan karin maganar,a nan a bigiren da take….tana ado ne da mahaifiyarta ba wai mahaifinta ba,hausawa na cewa gida mai dadi…banda nasu gidan,bata hangi wani dadi nutsuwa ko kwanciyar hankali dai dai da qwayar zarra cikin nasu gidan ba,batasan yaushe ne zasu kalli gidansu suji farinciki kwanciyar hankali ko alfahari dashi ba.

Duk da cewa babu lallai a iya jiyota amma bakan bai hanata yin sallama ba sanda take shiga gidan,saidai kamar yadda ta zata ne ba’a jiyota din ba,har sai data qaraso babbar harabar gidan nasu mai yalwa sosai,kamar yadda mukasan gine ginen gidaje na ‘yan uwanmu ‘yan karkara,sashen dake hannun damanta,wanda aka gewayeshi da dangar kara saboda a rabashi daga kasancewa wani yanki na babbar harabar gidan ta nufa,tana iya jiyo tashin sautin qarar redio daga daya sashen dake hannun hagunta,yake kuma kallon nasu sashen,wanda shikam yafi nasu,don ko babu komai ya samu ariziqin katangar bulo na jar qasa kamar yadda ilahirin ginin gidan yake.

Sallama ta sakeyi karo na biyu,kusan a tare suka amsa mata,mata guda biyu qarqashin rumfar buni dake a tsakar gidan nasu,zaune suke saman tabarmar kaba,matashiyar da batafi shekara sha hudu ba,da kuma mahaifiyarsu wadda nata shekarun zasu kai arba’in,saidai idan bakayi mata mallo na tsanaki ba,zaka tsammaci tafi hakan,sakamakon hudowae furfura saman baqar sumar kanta,wanda hakan yake da nasaba da yanayi da hali na rayuwa.

Tana dosu su amma hankalinta yana ga ‘yar qaramar rumfa da suka tayar suke girki a cikinta,qamas take,ba’a hura wutar kara da sukanyi amfani da shi ba,hasali ma tukwanen a kife suke gaba daya a wanke qal kamar yadda ta barsu a dazun,alamu na nuna mahaifin nasu tunda ya fita bai waiwayosu ba kenan?,saita dauke kanta ta qarasa saman tabarmar da suke kai ta zauna,zuciyarta na qara dagulewa da baqin ciki.

“Har kin dawo?” Mahaifiyar tata ta jeho mata tambayar,idanunta ta soma saukewa saman ciwon dake saman qafarta,wanda a kullum yake dada rami,qafar tata tana sake kumbura,kowanne dare zuwa wayewar gari na duniya da wannan ciwon take kwana cikin zuciyarta tana tashi,tana jinsa tamkar a jikinta yake
“Ta yaya umma zaki tsammaci dadewata dama a wannan gidan?” Ta fada sautin muryarta yana nuna alamu na fushi.

Tsam mahaifiyar tata ta daga idanunta tana dubanta,ta wani fannin tana nazartar yanayin fuskarta na wasu sakanni,saita sauke boyayyar ajiyar zuciya,sannan ta kira sunanta a hankali
“Kaltume…..wannan gidan dai da kike magana a kanshi mahaifiyata a cikinsa ba wani ba kin manta ne?” Saita dauke idanunta daga kan ciwon karon farko tun daxun data zuba mishi idon,kamar wanda hakan zai taimaka mata wajen janye ciwon daga qafar mahaifiyar tata
“Na sani umma,na sani,amma saidai kiyi haquri umma,saboda bakina bazai daina fadar maganganu makamancin wadan nan ba,saboda shine gaskiya kuma ainihin abinda yake cikin zuciyata,matuqar ba zata daina ba itama….matuqar ba zata canza ba,nima banajin zan canza umma” sosai ta sake kafeta da ido,sannan ta buda baki a hankali tace
“Kaltum……”
“Kiyi haquri umma” tayi hanzarin fada ba tare data bari umman ta sake cewa komai ba,ajiyar zuciya umman tata ta sauke,sannan ta janye idanunta daga fuskar diyar tata,ta sani cewa kaltum yarinya ce mai fushi idan aka tabata,tana da zafi,tana da fushi idan aka tabata,saidai tana da tausayi da kuma sauqin hali a wasu lokutan.

Shuru ne yaci gaba da ratsawa tsahon wasu mintuna,sannan ta bude baki a sanyaye tace
“Ya kukayi da ita?”
“Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,yau ma abinda ta saba tayimin,na samu kawu labaran….yaji maganar da mukeyi da ita,ya dauko kudi zai bani amma ta saka hannu ta karbe,tace ba zai bayar ba,idan ma an baki a gindinmu da babanmu kike qarewa…..wai umma me yasa ayi bata sonki?,anya kuwa mahaifiyarki ce da gaske….?” Wani kallo ta jefawa kaltum,wanda ya hanata qarasa fadar abinda tayi niyyar fada din,saidai duk da haka labarin abinda ya farun data shaida mata ba abinda ya hanashi tasiri saman fuskarta,duk da cewa wannan ba shine farau ba,ta saba da dade da sanin wannan dabi’a ta mahaifiyar tata,har kusan ya zame mata jiki,amma ta kasa sabawa,duk sanda wani abu mai kama da wannan ya faru sai taji zafin hakan har cikin zuciyarta.

“K’nnnnn” habiba qanwarta wadda ke xaune tun dazun gefan mahaifiyarsu ta fada,ita din mutum ce mai tarin haquri fiye da kaltum,bata da yawan magana,tana da sanyin hali tamkar na mahaifiyarsu,saidai duk da haka ita din ma abun na damunta matuqa da gaske,yana ci mata tuwo a qwarya,saidai bata fiya tankawa ba,amma idan hira ta tashi tsakaninta da ‘yar uwarta wani lokaci takan fada.

Kallonta kaltum tayi,iya saman fuskarta kawai tasan itama ranta ya baci,ci gaba da maganar tata kuwa tasan bashi da wani alfanu,hakanan bazai haifar da da mai ido ba,don haka ta sauya akalar zancanta zuwa neman mafita
“Yanzu umma ya za’ayi kenan?” Shuru nadan sakanni tayi kafin ta amsa mata
“Babu komai,zanci gaba da nema kawai har Allah yasa a samu,idan ban samu din ba….zanci gaba da amfani da wannan maganin muga abinda Allah zaiyi” shuru kaltumen tayi tana hadiye wani yawu mai tauri,saita kalli sashen da suke girki wanda yake a bushe ba girki babu alamarsa,ta maida dubanta ga umman
“Baba bai dawo bane har yanzu?,naga baku dora komai ba” kamar ba wata tambaya tayi mai muhimmanci ba haka umman tata ta bata amsa
“Bai dawo ba,amma nasan yana kan hanya in sha Allahu” miqewa kaltum tayi,saboda ba abinda ranta ke sakeyi sai baci,tasan umman ta fada ne kawai,umman ta fada ne saboda ta bashi kariya a idanunsu,bayan babu wata kariya data rage masa da zai samu a idanuwansu,ya gama wargaza komai,ya kuma gama kwancewa kansa zani a kasuwa,don ba zata iya tuna sau nawa ta fita tayi kitso ta dawo ta kawo kudin sukaci abinci dashi ba,to kuma me yayi saura?.

Buta kawai ta dauka,har zata wuce bayan gida ta juyo ta dubi umman tasu
“Umma ina bilal ya shiga ne?”
“Bai jima da fita ba kika shigo,yacemin zaije wajen dan bala,yace kamar akwai aikin da zasuje yau” kai kawai ta gyada,bacin ranta yana sake ninkuwa,bilal da gaba daya bai cika shekara sha biyar ba amma yasan dukkan wata wahala ta duniya,yaro ne da gaba daya kamar baisan ciwo ko dadin jikinsa ba,Allah ya zuba masa tausayin mahaifiyarsa da son ‘yan uwansa,dukkan wani aiki da za’a kirashi na wahala bilal ya iyashi,kama daga kwabin bulon qasa,aikin gini,kwasar qasa,haqar masai ko rijiya,kai hatta da kiwon dabbobi idan mutum nada buqata zaije ya karba yayi masa,burinsa kawai a biyashi kudin,burinsa kawai su samu abinci suci,tun yana aikin wahala ya dawo gida yayi jiyya har ya saba.

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

Duk wannan aikin da yake baisan tari ko adani ba,burinsa daya samu kudin ya siya abu mai dadi yaci,ya kuma kawowa mahaifiyarsa a boye,baya taba bari mahaifinsa ya gani,don yana da tabbacin indai ya gani ba rabonsa bane kudi ko abinci,koda na nawa ne kuwa,zai karba ya kalmashe a aljihunsa,rashin kawo musu baisa yaji kunya yaqi amsar nasu idan sun samu.

Sosai abun ke cima kaltum tuwo a qwarya,tana qaunar bilal sosai,yana da sauqin kai,bashi da rashin ji ko hayaniya irin ta yara,wahalar da yakeyi tana ganin tayi yawa,saidai kusan ta zame masa jiki ma,ya zama tamkar bawa,don baya iya zama wuni guda a gida ba tare da yayi aikin komai ba,saidai idan bashi da lafiya.

Shi dinma da kaltum taso yayi karatu koda su din basuyi ba,tunda shine da namiji guda daya tilo da mahaifiyarsu keda shi,amma sam yaqi,ya nuna aikin neman kudinsa ya fiye masa,koda ta zauna tayi tunani,sai taga idan ta takura dinma sai yayi karatun dame zaiyi?,su din da kullum sai sunyi fafutukar abinda zasu ci?,saidai taci alwashin dagewa tuquru ta tara kudin da bilal din zai koma makaranta,koda baya so,saboda tana kallon shi ne tamkar shine madubin rayuwarsu,kuma wani tsani da zai kai rayuwarsu izuwa tudun mun tsira anan gaba.

Har azahar suna zaune zaman jiran gawon shanu,babu baban nasu ba alamarsa,dukka sun ukun idan ka kalli fuskokinsu babu tantama yunwa suke ji,daga nan sashensu suna iya jiyo qamshin man ja,wanda da alama ana soyashi ne daga sashen baba iliya,wato sashen dake fuskantosu,amma ba qamshin manja ba,ko qamshin me zasuji babu lallai a miqo musu koda babu yawa saboda haqqin maqotaka dana zumunci,saidai idan Allah ya tsaga da rabonsu.

Tana idar da sallar azahar ta miqe tana karkade baqin hijabinta daya kwashi qasa,ta dubi ummansu
“Ummanmu…..na tuna ina bin ladingo kudin kitson da nayi mata tun rannan ita da ‘yarta,bari naje ko zan samo,saina siyo mana ko gari ne” cike da tausayi ta dubi diyar tata,wannan rayuwar da suke sam bata qaunarta,to amma ya zatayi da ranta,ita ba sana’a gareta ba,hasalima bata da jarin kuma bata dame bata,bata da wata kadara da zata saida ta zame mata jari,kai koda ta fara sana’arma mai gidan shike amshewa da wayo har sai ya durqusar da ita,dolen dole ta zuba idanu komai ma ke faruwa.

Saidai ko kadan bata bari ba,bata sanya idanu ba,hakanan batayi sanyi ba kan tarbiyya ‘ya’yanta,bata da sauqi ko sanya wajen kula da tarbiyyarsu,kuma kowa yasan da hakan
“Karki dade,idan baki samu ba ki maza ki dawo gida”
“In sha Allahu….habiba zo muje” tace da qanwar tata,itama bata dade da idar da sallar ba,don haka ta miqe suka fice a tare.

Suna tafe a hanya saidai babu wanda ke magana a cikinsu,kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa,basuyi nisa ba suka hangi asiya tana tahowa,dauke da jakar makaranta kamar gaske,wato yanzun yayi dai dai da lokacin tasowarsu kenan,shine ta dawo gida.

Suna hada ido da kaltum tayi kicin kicin da rai,ta kuma dauke kanta bayan ta gasa mata harara,wanda kaltumen batasan daga inda ta faro kota samo asali ba,saidai hausawa sunce….tabarmar kunya da hauka ake nadeta,wala’alla abinda tayi shirin yi kenan.

Sai da suka giftata sannan habiba tace
“Wai yaya bakiga kallon da asiya tayi miki ba?” Kai ta jinjina
“Na gani habiba,tana son nannade tabarmar kunya ne da hauka” cikin alamun son qarin bayani habiban tace
“Me ya faru?” Kamar ba zata gaya mata ba,sai kuma taga cewa barin kashi a ciki baya maganin yunwa,hasalima duk duniya bata da kamae habiban,hakanan tafi kowa sanin halin habiba,bata da yawan surutu ko yarin qawaye,hakanan nutstsiya ce bare tace zata yi zancan da wani,abinda yayi habiba shi yayita.

Ta yadda zata fahimta ta gaya mata komai,ga mamakinta sai habiban ta tabe baki
“Na saba ganin asiya a wannan yanayin yaaya,saidai fatan Allah ya shirya” cike da mamaki da kuma baqinciki ta ware idanu tana dubanta
“Amma habiba kin sani baki taba yin wani abu da zai daqile ‘yar uwarki daga fadawa halaka ba?,kinsan cewa kema kina da kamasho duk abinda ya faru tunda baki taimaka mata kin tunkudeta daga cutarwar da takeson jefa rayuwarta ba?” A sanyaye tace
“To ya zanyi yaaya?,na gayawa umma,tace mu tayata da addu’a kawai,kada nayi magana,saboda ita batason tashin hankali,don babu lallai baaba lami ta fahimci abinda zan gaya matan,kinfi kuma kowa sanin halin jarabarta,da yadda ta tsangwamemu hakanan babu gaira babu dalili” shuru kaltum tayi,ta kasa furta komai,hankalinta na wani irin tashi,jininta ce keson fadawa wannan hanyar?,me yafi wannan tashin hankali?,sam bata jin zata iya shuru koda baba lami zata tsireta,duk da ma basu da tabbacin zataqi amsar maganar,don babu wata uwa ta gari da zataso ganin lalacewar diyarta,itace mutum na farko da zataso ta gyaru,don haka taci alwashi cikin ranta ba tare data furtawa habiba ba.

Basu sake magana ba har suka iso gidansu ladingo,shima dai babban gidane irin na karkara,mai dauke da sassa sassa,ta gaida mutanen data taras a harabar gidan ta wuce sashen ladingo.

Zaune ta sameta daure da zani da riga mabanbanta,yaronta na saman cinyarta yana shan nono,ita kuma tana irgen kudi,fanteka ce a gabanta wadda take duqun duqun,ba’a jima da dawo mata da ita daga tallar awarar da take bayarwa tana biya ana yi mata ba,kitson da kaltum tayi mata har ya fara soshewa,amma har yau ta kasa biyan kudinsa,kamar yadda wasu daga cikin matan qauyen keyi mata,takanyi kitson ne kawai saboda ko banza yana toshe mata wata kafar,duk da cewa su din talakawa ne tilis….basu mallaki komai ba,amma mutane ne masu tsananin tsafta,kamar yadda suka gada daga mahaifiyarsu,ita dinma haka take,ta washi qazanta gaba daya,tana da tsafta qwarai,ta yadda duk kodewar kayanta da rashin kyansu ba zata ga datti kowani abu mai kama da qazanta ba,dalilin da yasa da qyar take iya kama kan wasu ta kitse saboda tsabar rashin gyara da tsafta,da yawansu suna ganin cewa zallar wulaqancine kawai da girman kai,saidai ba haka take ba,qazantarsu ce kawai ke damunta,tana mamakin yadda basu damu da jikinsu da kawunansu ba,mace saita wuni a tsaye tana aikin neman kudi,amma gyaran jikinta saiya gagareta,ba zata iya siyan man shafawa dangwali yaba ko turaren abulbula ta siya ba saboda kauda wari da qarni,duk da talaucinsu wanda da yawansu wasu sun fisu,bata taba ganin qazanta jikin mahaifiyarsu ba.

Tana jin sallamarsu ta soma qoqarin boye kudin ta hanyar cusasu cikin zaninta,sarai kaltum ta gani,amma saita dauke kai kamar bata gani ba,ta soma washe musu bakin qarfi da yaji.

Da qyar habiba ta samu wajen da yayi mata ta zauna,kaltum kuwa kasa zaman tayi,saita jingina da bango kawai tana gaida ladingo,yarinyar macace mai haihuwa daya tak,amma qazanta da zafin nema sun qara mata yawan shekaru a fuska da jiki gaba daya.

“Don Allah kudin kitson nan nazo ki bani ladingo,na matsu ne zanyi amfani dashi” kicin kicin tayi da fuska
“Kai kaltume…..ke kam baki da kara wallahi,kudin kitson nan har yanzu baki manta dashi ba fisabilillahi?,kwana wajen nawa?,ki rage son abun duniya gaskiya” sosai kalaman nata suka bata haushi da mamaki,uba uba yanayin yadda tayi zancan a wani gadarance,kamar ita ta tsuguna ta haifeta
“To ai da nazo cemin kikayi nayi miki kitso zaki biyani kudin,baki gaya min cewa kyauta kikeso nayi miki ba,kinga kenan ko kwana dubu sukayi ai haqqina ne ko?”
“Kinga kada kimin rashin kunya….ungo kudinki” saita zaro naira darin daga cikin kudin da take ta boyonsu cikin zani ta miqa mata,sauke qafafunta tayi ta soma zura takalmanta,a yanayin data nuna yasa habiba ta gane tsaf zata wuce bata amsa ba,saboda cin fuska daya shigo ciki,don haka ita ta miqa hannu ta karba,ta miqe tabi bayan kaltum suka fice daga gidan,suka bar ladingo tana mita.

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

 

*DABI’AR ZUCIYA*
_FREE PAGE_
02

*Zafafa biyar books 2022*🔥🔥🔥🔥🔥

*SO DA ZUCIYA* _miss xoxo_

*DEEN MARSHALL* _Mamuhghee_

*HALIM GIRMA* _Hafsat rano_

*TAKUN SAƘA* _Billyn abdul_

*DABI’AR ZUCIYA* _Huguma_

*KU TUNTUBI WADAN NAN NUMBERS DIN*

08184017082
KO KUMA
09134848107

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button