Dabi’ar Zuciya 19
Ƙarfe hudu saura minti uku a unguwarsu tayi masa,dai da lokacin da masallacin layinsu suke haramar tada sallar la’asar,don haka sai ya sanya umar ya faka motar daga gefan masallacin,suka sauka suka bi ta famfunan masallacin dake jere reras suna bada ruwa suka daura alwala,wanda aikinsa ne,shi ya sanya akayisu tare da borehole ba tare da mutane da dama sunsan shi ya sanya ayi din ba.
Bai lura a gefan daddyn nashi ya tada salla ba sai da aka idar,daddyn baice dashi komai ba,bayan ya gama addu’o’insa sai ya miqe,don haka samir ya miqe da hanzari yabi bayansa suka jero a tare,ya yiwa umar inkiyar ya shiga motar ya qaraso gida da ita.
Tun daga gaisuwa ba maganar data kuma shiga tsakaninsu,takatsantsan samir din yake,yana tauna abinda zaice din,baiso daga isowarshi ya fadi wani abu da zaisa daddyn ya qalubalanceshi kamar ko yaushe,don haka shuru yaci gaba da yi musu rakiya har suka isa gidan.
Falon nasu masu aiki ne suketa shige da fice a cikinsa,mommy na tsaye tsakiyar falon tana bada umarni tare da nuna yadda takeson komai ya kasance daman dining table din dake shaqe da nau’in girke girke kala kala,wanda da alamu an tanadi komai ne saboda baqin da aka kirashi saboda su.
Dandatsetsen lace ne a jikin mommyn,wanda aka yiwa dinkin buba,akabi bakin hannun zuwa wuya da wasan rigar akasa bakin lace din aka masa wani ado me azabar kyau.
Suna hada ido da samir din ta saki murmushi cikin nuna zallar farinciki
“Sannu da zuwa son” gefanta ya qaraso
“Yauwa mommy,na sameku lafiya?”
“Lafiya qalau alhmdlh,ya hanya?”
“Alhmdlh mommy” fitowar jawahir dauke da wani babban tray ya dakatar da gaisuwar da sukeyi,tuntuni daddy ya wuce sashensa
“Yayaaaaa” ta fada a shagwabe cikin farinciki,sannan da hanzari ta dora farantin saman dining ta dawo inda yake tsaye
“Yaya sannu da zuwa,i missed you yaya” murmushi yayi yana duban jawahir din,she cares so much,tana masa qauna ta ‘yan uwantaka na haqiqa,shi yasa shima yake ji da ita
“Me too our auta,ya makarantar?” Sai data dan sosa kanta kadan tana tabe fuska,don ita sam ba wani son makaranta take sosai ba,tun daga yarinta izuwa girma,abun mamaki wani irin so da sha’awar sana’a da kuma kasuwanci Allah ya sanya mata,ba kamar najwa ba,abinda ke hadasu fada kenan ko yaushe da mummyn,saboda ita tafi son suyi karatu,tace koma meye daga baya ayishi idan an gama karatun
“Makaranta ba dadi yaya?” Qaramin murmushi ya saki yana girgiza kai
“Ba zaki canza ba auta” saita saki dariya shima ya tayata da murmushi
“Gafara…..kin cikashi da surutu,kuma ke baki kawo masa komai ba” cewar mommy tana dan jefa mata harara
“No mummy,ta manta ne,amma banda haka saina ce ya isa haka,i need to take bath ma before I eat something”
“Ba damuwa,hakan yayi,daddynku ma yace na shaida maka tare za’aci abinci”
“Ohkey” ya amsa yana duba lokaci a agogon hannunsa,ya daga kansa dai dai sanda jawahir ke cewa
“Mommy,i have finished….nima wanka zanje nayi”
“Good,hakan yayi……idan kin shiga ki turomin waccar uwar bokon tazo” dariya jawahir tayi kamar kowanne lokaci kafin ta juya zuwa ciki.
Tun daga dan medium falonsa ya soma rage agogon hannunsa zuwa suit din jikinsa,ko ina neat kamar yadda yakeso,bai taba dawowa daga tafiya ya sami bangaren nasa ba dai dai ba,wanda wannan kusan dukka aikin mommy ne,ta kula da duk wani buqatu nashi tun kafin yakai ga furtawa.
Kai tsaue toilet dinsa dake bedroom dinsa ya shiga ya hada ruwa me zafi yayi wanka,sannan ya dawo dakin don ya shirya,a sannan ya lura da wayarsa tana haske,koda ya duba screen din missed call din Aamir ya samu,ba tare da bata lokaci ba yabi bayan kiran.
“the giant saraki” shine abinda Aamirun ya fara fadi,wanda yasa murmushi subucewa daga fuskar sarakin,indai yaji amirun ya fadi hakan yanason shafe laifinsa daga wajensa
“Zaka fara kamun qafar ne?,malami idan zaka yanki ticket ka dawo tun ban biyoka ba gwara ka dawo”
“I almost done guy, don’t worry,am on my way very soon…..meye labari?” Murmushi ya kubce masa daya tuna waccan qauyen da irin abubuwan da suka faru
“Labarai zaka ce….but babu ko daya da zan baka a yanzu,idan na samu chance may be zan kiraka,but not now” dariya Aamiru yayi,yasan samir din duk yayi haka ne saboda yana jin haushin rashin dawowar tashi,kafin ya ankara ma ya kashe wayarsa abunsa,sai yabi wayar da kallo yana jinjina kai kawai.
Gaban yalwatacciyar ma’ajiyar kayan sawarsa ya nufa,yafi ta’ammali da qananun kaya fiye da manya,saiya fidda wata shirt light ash da baqin jeans.
Yana tsaka da shiryawar ya soma jin shigowar baqin motoci cikin gidan nasu,yaja dan qaramin tsaki,saiya koma shiryawa slowly,koda ya kammala shirin ma zama yayi ya buda safe dinsa yana ajjiye wasu muhimman takardu.
Kira ne a jejjere ya dinga shigowa wayarsa,wanda ya tilasta masa barin abinda yake din,ya nufi wayar ya daga yana duba me kiran.
Da fari daddy ne,sai kuma ya koma number mommy, lastly kuma jawahir,sai ya zabi ya fara da kiran number jawahir din
“Yaaya,ka fito inji daddy,baqin suna gab da shigowa” yaji jawahir din ta fada,muryarta qasa qasa,
“Ok” ya amsa can qasan maqoshinsa,fuskarsa da alamun gazawa da rashin walwala ya janyo wani tattausan baqin takalminsa da yafi zubi da slippers ya sanya,kana ya miqe ya sale feshe jikinsa da turare,hannunsa riqe sa wayarsa ya fice zuwa ainihin cikin gidan nasu.
Da sallama ya shiga falon nasu,saiya samesu dukka a zaune saman kujera,banda daddy dake tsaye hannunsa daya riqe da wayarsa,daya hannun nasa kuma na a cikin aljihun rigar shaddar jikinsa dinkin tazarce.
Da daddyn suka fara hada idanu,ya jefa masa wani kallo me kama da harara,wanda ya sanya samir din yin qas da nasa idanuwan,kafin ya tako a hankali ya giftashi
“Duk wani qoqari da nake mafi yawancin lokuta saboda kai nake yinsa,amma kuma kowanne lokaci baka da wani qoqari kuma babban farincikin da ya wuce ka bula min qasa a idanuna……” Ya fadi cike da kamalar dake muna tsahon lokuttan daya shafe a duniya,daga haka ya juya a hankali ya nufi qofar barin falon,najwa ta miqe da hanzari ta rufa masa baya.
Shima hannunsa na cikin aljihun wandonsa,ya dunqule su waje guda cike da zuzzurfan tunanin abinda ya aikatawa daddyn daya cancanci qorafi,amma tunaninsa kaf ya gaza gano hakan,saiya maoda idanuwansa kan mommy cike da fatan ta warware masa abinda yayin?,saidai kamar kowanne lokaci taqi basi damar karantar komai,hakanan batace dashi komai din ba,saiya sauke ajiyar zuciya yana yiwa damuwar tasa mazauni na daban,ya maida idanunsa kan teburin dake shaqe da kaya sannan daga bisani ya dubi jawahir daketa buga game
“Hope kowa ya samu abinci a gidan nan?” Earpiece din kunnenta ta zame guda daga ciki sannan ta dubeshi
“A’ah yaya,abincin baqi ne gaba daya,zuwa anjima zasu dora nasu ya nasu” shuru yayi na sakannin da basu wuce biyar ba,still idanuwansa akanta,saiya fara takawa zuwa gaban tebur din,ya ciro hannunsa daya daga aljihu ya dafe teburin yana irga adadin yawan nau’ikam abincin da aka tara,wanda yana da yaqinin ko baqo ashirin ne zasu zo a yau din ya musu yawa
“Taso ki duba wasu daga cikin wadan nan ki zuba musu suci” ya furta kansa tsaye yana duban jawahir daga inda take zaune,idanuwansa da jikinsa na nuna zallar zararrasa da kuma cikar kwarjini.
Daga kai mummy tayi cikin murmushi
“Yanzu zansa zuwaira ta dora musu wani abun,wannan na baqim daddynka ne,ai ba’a taba ba son” kai ya girgiza alamun a’ah
“Indai zamu farantawa wasu daga waje…..na cikin gida da suke tare damu koda yaushe suke qoqarin hidimta mana,su yafi cancanta su fara cin gajiyarmu…..taso ki dauke waccar golden warmer din” ya sake baiwa jawahir umarni.kai tsaye,idanuwan mummy saman fuskarsa tana dubansa,tana son nuna masa tata zararra amma wani abu daga fitowa daga gareshi ya taso ya danneta,ta tsani wannan raunin nata daya jima yana cutarta,duk kuwa da yadda take yaqi dashi babu dare babu rana,rauni ne wanda ada batasan dashi cikin halittarta ba sai yanzu.
Kamar yadda yace haka jawahir ta aiwatar yana tsaye har komai ya kammala,saiya samu daya daga cikin kujerun falon shima ya zauna bayan ya fidda wayarsa yana duba wasu sabbin tractors da aka tura masa da zasu qara cikin kamfaninsu, bulldozer ce da sauran wasu kayan aikin.
Miryoyine a cakude cike da hirarraki dake nuna farinciki da walwala suka doso qofar falon,cikin sakannin da basu wuce biyar ba suka bayyana daga qofar falon zuwa cikinsa.
Mahaifinsa ne,gefansa wani dattijo ne kamarsa,wanda a qalla zasuyi shekaru kusan daya,baikai hasken mahaifinsa ba,saidai kusan tsahonsu daya,duk da cewa daddyn ya dan dara masa,daga bayansu wani matashin saurayine mai kama da mutumin dake gefan daddy,sanye da wani yadi na maza mai tsada da aka yiwa dinkin zamani dai dai jiki,duka duka bisa qiyasi bai wuce shekara sha bakwai ko sha shida ba. Daga can bayansu kuma matane su biyu,matashiyar budurwa da wadda ta data,kana gani kasan mahaifiyarta ce,cikin wani lace dake nuna alfarmar wadda ke sanye dashi,hakanan diyarta dake gefanta,itama lace dinne,saidai nata straight gown ce,tayiwa kanta wani irin dauri daya zauna das a goshinta,sai.mayafin da kwata kwata tsahonsa iyakacin wuyanta zuwa saman kanta ta nade dashi,hannayenta sunsha fixing na faratan kanti,wanda aka yiwa ado da nail polish kalar lace din dake jikinta.
Mommy najwa da jawahir dukkaninsu suka miqe tsaye don nuna farincikin ganinsu,yayin da budurwa tadan taho da sassarfa zuwa inda momy ke tsaye ta rungume kafadarta,itama mummy ta tarbeta fuskarta qunshe da fara’a madaukakiya,ta sanya hannunta a gadon bayanta tana bubbugawa tare da fadin
“Oyoyo daughter jauhar”
“Oyoyo mommy” wadda aka kira da jauhar din itama ta fada fuskarta dauke da fara’a.
Duk wannan abun da ake samir na zaune,hankalinsa saman wayarsa,qasa qasa yaji kamar an kirayi sunansa,daya daga kai kuwa sai yaga daddy ne,wani kallo yake masa da yafi kama da harara,tsam ya miqe tsaye,dai dai sanda baqon me suna honorable bukari mustapha yake duban samir din
“Ah….yarona kana nan ashe” qoqarin sakin fuskarsa yayi kana ya qara taku uku zuwa gabansu,ya miqa masa hannu gami da cewa
“Ina nan abba” qwaqwalwarsa tana tuna masa mutumin,duk da cewa ya dauki wasu shekaru rabon da ya ganshi,hannun ya miqa masa shima sukayi musabaha,yana jaddada yadda yaga samir din ya sake zama babban mutum,cikakken mai hankali fiye da shekarun baya,qaramin murmushi samir din ya saka yana dan ja baya.
Tunda ya miqe yaja dukkan wani hankali nata,ko na minti daya saita kasa janye idanun nata daga kanshi,abinda tunda aka fara zancan tahowarsu wasu kwanaki da suka shude bata taba kawowa zaya faru ba,dui tsahon lokacin da maama ta dauka tana mata bayani bata tsammaci haka ba,cikin dan qaramin taqin lokaci irin wannan.
“Hi”ta fada da zazzaqar muryarta ganin bai lura ma da wanzuwarta a bigiren ba,waiwayawa yayi a hankali,suka hada idanu,ta sakar masa murmushi,shima saiya maida mata martanin murmushinta,yadan daga hannunsa kadan ya maida mata amsa da
“Hi”
“Son……ga hajiya murjana” mummy ta fadi,ya sake juyawa zuwa sashe da take tsaye,cikin girmamawa ya gaidata,ta amsa fuskarta dauke da fara’a farinciki,gami da gamsuwa kan lamari da kusan shi yayi silar takowarsu zuwa cikin gidan,yayi jagoranci kan tafiyarsun,muryar jawahir ta ratsa falon sanda take fadin
“Daddy……. food is ready”
“Da kyau auta… honorable bismillah,mu fara da cin abinci kada lokacin sallar magariba ya shigo”
“To….to babu laifi”sune a gaba,suna takawa zuwa wajen yana jan samir dake gefansa da hirarraki,wanda hakan ya faranta ran daddy qwarai,yayin da mummy maama jauhar najwa da jawahir suka rufa musu baya.
Da kansa samir din ya jawa daddynsa kujera,sai ya bawa honorable damar zama,don haka ya sake ja masa wata,sannan shima yaja tasa ya zauna,su mummy suka qaraso suma kowa ya yiwa kansa wajen zama,duk da hira dake tashi tsakanin mummy da maama,sai kuma jauhar da najwa.
Jawahir itace ta soma serving din kowa, mummy ta dubi najwa
“Tayata mana saboda kufi sauri” hakanan taji kawai kaman mummy ta rage mata qima wajen jauhar,tasan yarinyar sarai,yar hutu ce kuma ‘yar gata ta qarshe,komai yi mata ake,cewa tayi serving nasu kamar wani ragin qima ne a wajenta,haka dai ta miqe saboda babu damar musu saboda idanu ta soma zuzzuba abincin a yangance,tanayi kamar ba zata kai ba,yayin a jawahir ke komai bisa karasashi da walwala.
Cikin mintuna qalilan kowa abincinsa ya isa gabansa,kowa ya soma qoqarin kaiwa cikinsa,banda samir da yaji sam zaman wajen bai wani yi masa ba,karo kusan na uku kenan suna hada idanu da yarinyar,saita sake masa murmushi,yana qoqarin maida mata koda shi nashi murmushin baikai zuci ba,yana ganin kawai idan ya maida matan kamar ya girmama baqin daddyn ne.
Game dinsa daya saba yi lokaci bayan lokaci idan kansa ya dauki zafi musamman wajen aiki ita yake bugawa,duk abinda ke faruwa hankalin mutum biyu na tare dasu,daddy shi da mummy,duk suna ankare da samir din,tsayin mintuna kusan goma
“Am son” muryar mummy ta ratsa kunnensa,saiya cira kansa a hankali
“Ko zaku koma cikin parlour kaida jauhar…….kaman sai tafi sakewa a can taci abincin sosai ko?” Maganar mommyn ita ta sanyashi maida qwayar idanunsa kan yarinyar da suke kira da jauhar din,tana cin abincinta yadda ya kamata,duk da batayi nisa a cin ba,so baiga wani abu da zaisa su kebe ba kuma,saidai kuma bazai iya musawa mummyn ba,don haka muryarsa can qasan maqoshi ya furta
“Ok” dai dai sanda murmushi ya kubcewa jauhar din,da idanu tace da mummyn
“Thank you” saita gyada kai kawainta dubi jawahir
“Jawahir saukar musu da abincin qasa” da murmushi ta miqe tana dan boye dariyarta
“Ok mummy” idonta kan yayan nata,suna hada idanu saita waske,hakan ya gaya masa da wata a qasa,shima basarwa yayi yana miqewa,cikin takunsa mai cike da wata nutsuwa data cakuda da qasaitar data gadar masa da sunan saraki ya sauka daga wajen.
Kujera daya mai cin mutum biyu ya zaba ya zauna,dai dai sanda itama ta qaraso tiqe da cups guda biyu data cika da lemon inibi,gabansa ta qaraso idanuwanta a kansa tana yana kamewarsa da ginshira irin tashi ta miqa masa cup din,sai daya kalleta ta jefeshi da murmushi,yasa hannu ya karba,qasa qasa ya furta
“Thanks” saiya aje cup din gefansa hannun kujerar da yake kai,ita kuma ta koma a hankali ta zauna kam kujerar dake fuskantar tasa,har yanzu idanuwanta a kansa,tana qoqarin karantarsa.
Komai najwa ta jere musu,daga qarshe ta tsiyaya coffee mai zafi data dafa saboda yayan,kuma taga baisha ba ta miqa masa tana murmushin dai,harara ya jefe mata data sanyata kintsa bakinta,ya miqa hannu ya amsa cup din,ta juya tabar wajen,sanda shi kuma ya gyara zansa sosai saman kujerar ya aje wayarsa gefe ya fara surbar coffee din a hankali.
“Hi”ya kuma ji ta ambata,saiya dora idanuwansa saman fuskarta,hakan ya sanyata sauke nannauyar ajiyar zuciya a boye sannan tace
“Am jauhar,daughter of honorable bukhari mustapha…… Muhammad samir isn’t it?” Kansa yadan kada yana dubanta,saita saki murmushi,sannan ta kurbi lemon hannunta
“Nice meeting you”
“Me too” yayi qoqarin fada,kai ta sake jinjinawa,shuru ya sake ratsa tsani,kafin daga bisani ta gyara zamanta,ta dora qafarta daya saman daya
“Kasan dalilin da yasa mummy tace mu sauko nan…….?” Kafadunshi ya dage kafin ya girgiza kai,duk da cewa ya jima da fuskantar komai,saita sake gyara zamanta sosai tana fuskantarsa,bayannta hade tafukan hannayenta waje daya
“Dukkaninmu iyayenmu manyan mutane ne,munyi ilimu me zurfi…..mun samu gata da kulawa daga garesu,kasantuwar mu yaran farko a wajensu nida kai gaba daya….inaga abun zaiyi kyau idan muka fuskanci juna,muka kuma qulla alaqar auratayya,kamar yadda yake buri da mafarkin iyayenmu”