Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 17

Sponsored Links

*_manzan Allah S A W ya kasance…bai taba aibata abinci ba ko sau daya a rayuwarsa,idan an kawo masa ya qayatar dashi yakan ci,idan baiyi masa ba saiya barshi ba tare daya ci ba,ba kuma tare daya aibatashi ba(don haka mu kula,mu kuma hana yaranmu aibata abinci saboda bai dace da ra’ayinsu ba)_*
_____________________________

 

“Alhamdulillah” kaltum ta fada tana rufe kwafin qur’ani bugun qira’ar warsh dake gabanta,tare da janye fitilar aci bal bal din da tayi amfani da ita gefe,ummanta dake zaune a gefanta tana gyara saitin gidan redion da takeson jin ta daga kai ta dubeta
“Kunkai izifi nawa ne a yanzu?” Murmushi kaltum tayi,tana jingija bayanta da bango bayan ta miqe qafarta
“Ummanmu…..idan na gama haddar nan zakiyimin walima amma?” Murmushi umman tayi itama,tana jin in sha Allahu zatayi iya bakin qoqarinta ta tabukawa kaltum din wani abu,duk iya tsahon zamansu tare bata taba tambayar wani abu wajenta makamancin wannan ba,a wannan karon itama tana son ta mata wani abu koda guda daya ne da zata dinga tunawa dashi,kaltum din yarinyace da tayi imani cewa samun irinta sai dai daiku,duk da fushi da zafin zuciya a wadansu lokutan,amma kuma ta wani fannin tana da zurfin hankali haquri juriya gami da kawaici mai yawa,da sannu kake fahimtar hakan idan zamanku da ita yayi nisa,fatanta kawai Allah yasa nasiru ya fahimceta yadda ita din ta fahimci diyarta
“Me zai hana kaltume?,in sha Allahu”
“Allah yasa ummanmu,yanzu shine kadai burina….naga haddata ta hadu” ta fadi tana fidda murmushi saman fuskarta,da alamu da gaske take har qasan zuciyarta burin nata kenan.

Kafin wani daga cikinsu ya sake cewa komai lantana tayi sallama,daya daga cikin yammatan qauyen da aka sanyama rana,kuma za’a sha shagalin bikinsu bada dadewa ba,kasancewar qauyen nasu bashi da wani girma mai yawa,saiya zamana kusan kowa yasan kowa,sa’annan idan aka tashi bikin yammatan da suka kai aure,sukan yishi ranaku a jejejjere koda ba ranaku daya ba,akan lwashi sati daya koma biyu ana aurar dasu kafin a tsagaita,sai kuma zuwa wani lokaci idan an sake samun wadanda suka tasa.

Kamar yadda ta sabawa duk wanda suke mu’amala dashi,fuskarta da fara’a ta matsawa lantana gefanta,ta zauna tana gaida umma,sannan ta maida dubanta ga kaltum
“Kattume wajenki nazo”
“Ni?,Allah yasa ba wani abu nayi ba” dariya lantana ta saka,sannan tace
“Ba wani laifi,tashi dai zakiyi mu tafi dandali,haba kattume….kullum sai naga wasila,idan na tambayeta sai tace batasan meya hanaki zuwa ba”
“Wallahi har kin tsoratani,saboda ummanmu ne lantana nabar zuwa,ciwon qafar nan da take fama dashi,kinga mikin wajen kullum qara…….”
“Tashi abinki kije,nima kwanciya zanyi,amma kada ki jima” cewar umman tana duban diyar tata cike da qauna da tausayi,duk da cewa kaltum din ba gwanar zuwa dandali bace tun a baya,amma a sati takan leqa sau biyu sau uku,saidai a yanzu gaba daya ta tauye kanta saboda ita,ta rufe babin abubuwa da yawa a rayuwarta saboda kula da ita.

Bata musa ba ta miqe,ta shiga dakinta neman hijabinta na gado,saidai ta sameshi ya jiqe da ruwan da tasha dazu a moɗa ta barshi,tsaki taja,taji haushi sosai,don batason yafa gyale,amma ya kamata dole ta janyo wani yamutsatstsen baqin mayafi,tadan budashi kadan saboda nannadewar da yayi ta yafashi saman dankwalin kanta dake daure tamau.

A tsakar gida ta samu lantana,suka yiwa umma sallama suka rankaya suka fice,lantana ta kalli sassan su asiya sanda suke kan ficewa
“Oh,su asiya manya,itakam rannan cemin tayi wuce nan,ta girmi zuwa dandali yanzu,saimu da bamu waye ba,bama zuwa makarantar boko”
“Uhmmmm” shine abinda kaltum ta fada kawai,don a yanzun lamarin asiya ya daina bata haushi,sai mamaki da tsoro,yadda kullum likkafarta ke qara gaba,bata jin kunyar kowa,harkarta take gaba gadi,kuma a hakan idanun baba laure kamar suna a makance ne ita da kawu iliya,sam basa ganin wannan aibun da yanzu yawan jama’ar karkarar idanunsu ya fara kaiwa kai.

Itama lantana ba gwanar surutu bace sosai,don haka hirar tasu jifa jifa sukeyi,lantanar na bata wasu labarai da suka shafi qauyen nasu,wanda ita kaltum din batasan dasu ba,wasu kuma tasan dasu,har zuwa sanda tace da ita
“Wai nikam kaltume ba munafunci ba,wai meye gaminki da wasila?” Cikin mamaki kaltum tace
“Wasila kuma?,qawance” dakatawa da tafiyar da sukeyi lantana tayi
“Ba wannan ba,ai kowa ya sani,kuma shine abinda yake bawa mutane mamaki,yadda wasilan ke nunawa idan akayi zancanki,ko aka tambayeta ina kike,duk maganar da aka kawota indai a kanki ne saita kusheta,abun yana matuqar bamu mamaki,sannan yanzu ko a dandali ita kadai take zuwa ta koma ita kadai,idan ance ma kina ina cewa take,oho,bata sanmana ba” shuru kaltum tayi cike da mamakin wasilan,wasilar data gaya mata cewa itama ba zuwa dandalin take ba sanda tayi.mata qorafin ko biyo mata ta daina yi?,itakam har yau ta gaza gano dalilin da ya sanya wasilan ta canza haka ba
“Saiki kula kawai,saboda dan adam mugun icce ne” cewar lantana,bayan ya duqa ta dauki daya daga cikin karan dake zube a qasa,da alama wadanda sukayi sharar gona suka deboshi ne ya dunga zuba kafin sukai ga ma’ajiyarsa,bata iya cewa lantanar komai ba sai binta da tayi a baya tana juya zancan cikin ranta,tasan halin lantana sarai,bata da gulma ko jada gurmi,inda wata ce ma ba zata fsaya sauraran abinda take fada ba,to amma har yanzu tana mamakin sauyawar wasila,kamar basu taba wani abu waishi aminci ba,da wannan tunanin suka qarasa babban filin dake shaqe da yara da yammata da kuma samari,sai masu siye da kuma siyarwa da suka qarawa wajen haske da armashi da hasken fitilu dana cinikayyarsu.

Kusan ‘yammatan da yawa sunyi murnar ganinta,saboda kusan kowa tana zaune dashi lafiya ne,wadanda nasa jituwar dasu qalilan ne,su dinma kuma ba’a karon banza ne hakan ta faru ba,akwai dalili,tana iya hangen wasila daga inda take tsaye tanata sharfinta da sabbin qawayenta,saidai ta nuna bataga kaltum a wajen ba,hakan ya sanya kaltum din sanya mata idanu taga iya gudun ruwanta,sam bata sha’awa waqa yau,dama can bata rawa koda zata bada waqa saidai tadan rausaya,don haka sai ta samu gefe guda ta tsaya,ta kuma jingina da wani kututturen dabino da aka jima da yankeshi sai saura,ta harde hannayenta tana kallon abinda ke gudana cikin filin,yayin da samari masu tarin yawa dake da muradi a kanta da kuma sha’awar qulla alaqa da ita hankalinsu ya dunga yawo a kanta,duk da cewa wasunsu suna mata kallon mai girman kai,mai wulaqanta samari,amma tana burgesu,saboda yadda dabi’arta da halayyarta ta banbamta data ‘yammatan qauyen,da dama da basusan alaqarta da nasuru ba suna qulla yadda zasu tunkareta,don shima ba kasafai yake zuwa dandalin ba bare kowa da kowa ya fahimci alaqar dake tsakaninsu.

Batasan cewa tayi kewar wajen ba sai data zo shi,ta dinga tuna abubuwa da suka wuce,baya kadan sanda take ziyartar wajen,komai akayi saiya tuna mata da jiyan ta,jiyan tata data sauya izuwa yau,batasan kume me zata haifar mata a gobe ba,har wata cikin qawayensu mai suna lube ta shiga ta fara rero wata tsohuwar waqarsu.

Sosai waqar ta tuna mata lokacin daya shude,ta tuna mata da qanwarta habi da takan riqo hannunta su taho nan din,hakan yasa ta tashi daga jinginar da tayi daga jikin yankakken dabinon,ta fara tafa hannayenta a hankali itama tana murmushi,kamar yadda saura ‘yammatan ke tafa hannuwansu.

Shadda ce a jikinsa wadda ta dace da yanayin yawancin jama’ar qauyen,a yanayin shigar da yayin ba zaka kalleshi kace ya mallaki dubu hamsin ta kanshi ba,jikin shaddar ya koma kamar atamfa saboda tadan kwana biyu,babu qyalli ko maiqon sabunta ko kadan.

A nutse yake kewaye filin yana nazari da duban sana’o’in da jama’ar waje ke gudanarwa,wanda da alama itace rayuwarsu,sun kuma ta’allaqa jin dadinsu kacokam a wannan wajen,hannafi wanda ya zama shine idonsu cikin garin yana biye dashi a baya,gefansa kuma umar ne da yasha jeans da shirt,ya zuba kyau shi kam,kuma yaci gaba da tafiya cikin dandalin yana daukar hankalin yammata da yawa,hanafin shike musu jangora a duk wani abu da suka shiga duhu game dashi,tun bayan saukar saraki a wani kebantaccen gida na musamman da aka bashi ya sauka,bayan ya nuna sha’awar zamansa a wajen,ya gudanar da hutun daya rubutawa kansa da kansa zaiyi na sati uku,wanda hakanan ya tsiri hutun saboda target dinsa.

Duk inda ya kewaya yana lura da abinda ke faruwa,wani abun ya bashi mamaki,wani ya bashi sha’awa,wani ya bashi mamaki,bazaice basu da qauye ba,suna dashi,amma ba irin wannan ba,ba irin wadan nan jama’ar bane kuma a ciki ba,wannan qauyen yasha banban da nasu nesa ba kusa ba,akwai abubuwa da yawa da yake gani masu tarin ban mamaki da al’ajabi,basusan duk wani abu najin dadi ko more rayuwa ba,yana mamakin yadda mutum xai rayu kamar haka.

“Ga tacan haka,ko zaka leqa kaga fasahar ‘yammatan qauyen ɗinya?”murmushin gefan baki ya saki,cikin nutsuwar nan tasa yace
“Me zai hana,muje mana,ka sani kona samo mata a ciki ma” dariya sosai hannafi ya saki,don gani yake yadda aljanna ta haramta ga kafiri,haka yallabai saraki ya haramta ga duk wata mace wadda ba ‘yar gayu irinsa ba,inda ace da gaske sarakin zaiyi muradin hakan,da babu shakka sai inda qarfinsa ya qare wajen bashi qanwarsa ‘yar uwarsa ramatu,da wannan tunanin nasa suka qarasa inda samarin qauyen ke zaune,sun yiwa filin qawanya daga bangare daya,daya bangaren kuma.mata ne matasansu da yaransu,saiya kutsa a hankali ya isa daga gaba,inda idanunsa zasu fi ganin komai.

A hankali yake zagayawa da idanunsa wajen yana ganin abinda ke faruwa,tsayin wasu mintuna kafin ya janye idanun nasa ya lumshesu,kana ya budesu gami da sakin numfashi,yaga abubuwan burgewa da yawa,yaga kuma gyarararraki daya kamata ace an gyara din,saiya sake bude idanun nasa don maidasu cikin filin.

Wannan karon a kanta suka fada,tana tsaye daga gefe daya tana tafa hannuwanta,karon farko daya soma ganinta bata fada,bata kuma rashin kunya
“Ka ganta can dan dali,har yanzu bata tafi ba,don Allah ka gayamin yadda zan tunkareta,kwarjininta yayi yawa wallahi,ta hadu kaf yammatan karkarar nan Allah ta tsere musu,ta musamman ce” kalaman da yaji wasu samari dake gefansa suna fadi kenan,hakan yaja hankakinsa,yadan waiwaya don ganin su waye.

Samarine guda biyu,daya yana riqe da kafadar dayan,da alama shike maganar,gaba daya hankalinsu kacokam sun azashi kan kaltum daketa tafi batasan ma wainar da ake toyawa ba,hakanan saiya samu kansa da maida hankalinsa kan fuskarta,yaci sa’a kuwa wutar wajen ta hasketa sosai,baqar fuskarta sai shining take da maiqo da baisan na meye ba a hasken wutar,mayafinta a nade yake har yanzu yayi spring spring saboda rashin guga,alhali wanda ya qerashi yayi rayuwarsa ta tabbta bisa kyaune tare da taimakon gugar,rashin samun hakanne ya sanyashi nannadewa,kanta a daure yake tamau,kwamae wadda ta boye quli quli a ciki,ya sauko ga kayan jikinta,tsingilallen zani wanda bai qarasa ko idanun sawunta ba,wanda ta daurashi saman rigar jikinta,hakan ya taimaka wajen fitowar shafaffen qugunta da bashi da wani shape,sai zallar sirantaka data cikata tako ina,don hatta qirjinta shikam bai hango komai ba,duk da cewa ta cukuikuye mayafinta sosai ta wajen,da alama sirranta wajen takeyi wanda hakan yaso bashi dariya,don baiga abun boyewar ba,daga qasa kuma qafafunta na sanye da wasu sidaddun silifas,wanda idan ka kallesu a tsanake zakaga ba kala daya bane,da alama wari da wari ne,uwa uba kuma sunwa siririyar qafarta yawa,dukka wannan nazarin ya qarashe shi ne cikin wasu taqaitattun daqiqu,sai kalaman saurayin ya fado masa
“Ta hadu ne……kwarjininta yayi yawa” dariya ce taso subuce masa,saiya dan dake tare da qoqarin maidata,ya furta
“Astagfirullah” qasan ransa,indai har tafi duka yammatan karkarar haduwa toba shakka baisan wanne irin gari bane wannan,yana tunanin dai kawai soyayya ce ta rufe masa idanu,amma gashi wanda baqar mace sam bata burgeshi,ya hangi ‘yammatan da suka fita dama dama da yawa tsakiyar dandalin.

Mutum ne shi maison barkwanci wani lokacin,don haka sai yadan matsa gefan samarin,ko banza daren yau zai samu abunda zai sanyashi nishadi yadda ya kamata,gyaran muryar da yaja hankalin samarin guda biyu yaja,haqarsa ta cimma ruwa kuwa,don waiwayowa sukayi suna dubansa
“Ammm,abokina salamu alaikum”ya fada yana miqa musu tattausan hannunsa,duk da ya hangi nasu hannun daqal daqal da raken da suka gama danqa,cikin yanayi na rashin sani da baqunta suke kallonsa,kafin suyi qarfin hali bashi nasu hannun sukayi musabaha sannan ya dora da cewa
“Kuna bayana naji duk abinda kuke tattaunawa,yawa ne abokina ka dinga tsoron tunkarar mace,haba kamar ba namiji ba?,be a man mana” tsaiwa sosai haladu yayi saman qafafunsa jin an samu mai bashi qwarin gwiwar daya dade yana nema,duk da bai gane jimlar samir ta qarshe ba,ya washe haqoransa talatin da biyu yana duban samir,duk da baisan wayeshi ba
“Alqur’an abinda naketa gayawa kaina kenan,amma yarinyar ce abokina ba sauqi fa….”maganar data sake sanyawa samir ya kuma maida idanunsa kan kaltume,wanda zuwa yanzu ya tsayar da tafin,ta goye hannuwanta a qirji kamar maijin sanyi,still amma tana tsaye tana ci gaba da kallon masu gadar,haladu yaci gaba
“…….bata kula kowa,bata sakarwa kowa fuska,qawance ma bada kowa takeyi ba,bata taba saurayi ba sai yanxu,na dade ina sonta na kasa furta mata”
“Wannan din?” Samir ya samu kansa da furtawa cikin subutar baki idanunsa har yanzu saman fuskar kaltum
“Ita din fa”haladu ya fada yana qura masa ido,sai sannan ya fahimci yayi subutar baki,don haka ya waske da sakin murmushi
“Aita hadu” hakan yasa haladu sake washe bakinsa sosai
“Allah ko abokina,shi yasa na dage fa,amma kayi a hankali karka fada tarkon sonta,don ina kishinta sosai” kamar samir ya bushe da dariya amma saiya dake yana fadin
“Ai taka ce,kada ka damu,idan kana so zan tsara maka ita yau din nan” dubansa haladu yake sama da qasa cikin kokwanto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button