Dabi’ar Zuciya 16
*_Muna siyarda kaya kala kala kamar_*
*jaka da takalmi kamfanin* *lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers ‘yan yayi dominku da yaranku*
*Muna order kaya daga kasashe daban-daban na duniya*
*Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti*
*Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria*
*Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi*
*_ku tuntube mu awannan number kamar haka_*
07039773001
*Muna turawa ko Ina a fadin Nigeria da wasu kasashen ketare*
_LOCATION_= Kano ND gusau
*NAGARTA DA INGANCI SHINE TAKENMU*
*MIERAH’A DUKKHAN farincikin customers dinmu shine namu*π€π½π€π½π€π½
________________________________
Karfe biyu na rana ra gama duk abinda tasan umman nasu na buqata ayi mata,ta shirya tsaf cikin atamfarta wadda tasha wanki,fes da ita,ta sanya hijabinta wanda bata da kamarshi,tunda a qalla kala biyu gareta kwata kwata hijaban data mallaka kenan,duk da cewa su fatsima da yaran kawu ado suna basu suttura ita da habiba,amma nasa samun isowa garesu,inna tana amshewa ne ta saida,kota bada kyauta ga wadansu bayan su gasu a zaune,cikin lefan habiba kuma babu yadda batayi da ita ta dauki guda daya cikin kala biyar din da akayi mata ba amma sam taqiya.
A idanu fes take,saidai kayan sun nuna kodewarsu matuqa,wanda ga duk mai kallo yana gani yasan cewa anajin rayuwa yadda ya kamata.
Gaban ummansu ta tsugunna tayi mata sallama
“Saikin dawo,don Allah idan kin tadda aiki,kada kice ba zakiyi mata ba saboda bana wajen..,kinji ko?”umman tafada,saboda tasan halin kaltum din sarai,kaita jinjina
“In sha Allah” ta furta tana kallon qafar umman,da alama yau din tana mata radadi sosai fiye da kullum,tsabar haquri irin nata ya sanya bata furta ba bare ma ayi mata sannu,da wannan tunanin ta fice daga gidan,ta yanki hanyar unguwarsu inna.
Tana kashingide baya fitar kaltum din da minti goma malam amadu ya shigo,riqe da jakar buhu da muke kira da bacco,miqewa tayi da hanzari ta zauna tana masa sannu da zuwa,gabanta na faduwa,saboda yanayin data ga fuskarsa,ba shakka akwai wani abu,daga sanda tayi masa maraba kuma bai amsa ba ta tabbatar da zarginta.
Sa daya jingine jakarsa can qofar dakinsa sannan ya dawo inda take zaune,ya riqe qugunsa da hannayensa biyu yana dubanta,kai kace ya tsaya ne don ya tausayawa qafarta dake dauke da mikin ciwo,wanda kullum kwanan duniya azabtar da ita yakeyi,hakan kuma bai hanata yi masa dukkan wata hidima ba,qas tayi da kanta,tana jiran taji da wacce yazo,ciwonta ko akasinsa baisa amadu ya taba sassauta mata ba,wanda kaf iyakar lalube da bincikenta da tayi ta gaza gano wani qwaqwqwaran laifi guda data yi masa wanda harta cancanci irin wannan tarayyar tashi,bata sauke wannan tunanin ba kuwa amsa kuwwar muryarsa ta cika mata kunnuwa
“Can na hango kaltume hanyar bayan gari…..ta tafi yawan ta zubar dinne?,kin aikata kenan yauma ko?” Idaunta ta rumtse sosai,tana jin saukar furucin nasa har tsakiyar zuciyarta,ta tsani wannan kalma da yake yawan jifan diyar cikin nasa da ita,tana tsoron watan watarana ya fada gaban wasu,wasu dun da bazasu iya rufawa kaltum asiri ba,koda ba gaskiya bane maganar,tana tsoron yadda za’a lanqwasa zancan a sauya masa fuska da ma’ana,ya zama wani zance abun tattaunawa da yiwa juna albishir cikin qauyen
“Ba wani waje ta tafi ba,inna ce babu lafiya,ni kuma qafata tana ciwo,shine nace taje ta dubata,ta rage mata wasu ayyukan” tsaki yaja yana sauke hannayensa,sannan ya juya yana barin wajen,saidai fa baiyi shuru ba,bambamin masifa ya soma yi
“Koma ina taje dai wannan ya rage naku,ana fakewa da suna kitso,yau kuma da sunan inna aka fake,to wallahi ta dawo ki shaida mata,na gaji da ganinta haka,ta gayawa nasirun,ya fito kawai da iya abinda Allah ya hore masa ayi auren a huta,idan kuma bai shirya ba ta fitar da wani,kai koda bata fitar da wani ba,to zan aurar da ita ga duk wanda naga dama” daga haka ya bude qofar dakinsa ya dauki jakarsa ya shige ciki abinsa.
Hannunta daya tasa ta dafe kanta dashi,tana jin yadda zuciyarta ke wani ciwo kamar ana matsata,hasbunallahu ta dinga ambata babu qaqqautawa,har zuwa sannan tana jin yadda yake mita yana daga cikin daki,tsahon wani lokaci kafin ta samu relief,a haka ta rarrafa ta dauki kwanon abincinsa,wanda dama tazarce akayi mai kama da cin lokaci guda,saboda duka duka abincin sun kusa cinyeshi a iya rana kawai,saboda qanqantarsa da rashin wadatarsa,tana ajjiye masa kwanukan ta fito,ta tattare abin zamanta ta wuce dakinta,don ba zata iya jurar ci gaba da zama a wajen ba.
*********** Tana iya hango yadda taja murfin kwanon ta rufe da qarfi sanda taji tayi sallama,fuskarta kicin kicin ta amsa sallamar tana miqe qafafunta bayan ta hardesu waje guda.
Takalmanta ta cire sannan ta qaraso cikin rumfar tsohuwar,wadda kana ganinta,duk da cewa a qauye take ‘yar gatar tsohuwa ce,don ‘ya’yanta suna mata hidima babu laifi,duk da cewa ta ware wasu daban ta bari duniya ta musu radin suna da shafaffu da mai,inda Allah ya taqaita,dukkaninsu ubangiji ya kula da halayya da kuma tarbiyyarsu,basu tabarbare ba sakamakon abinda ta aikata din.
“Ina yini inna,ya jikin?” Sheqeqe ta kalleta sannan tace
“Da sauqi”
“Ummanmu tace ayi miki sannu,ciwon qafarta ne ya matsanta mata shi yasa ba zata iya zuwa ba”
“Madalla” ta fada a banzace,sai xaman nasu ya zama zaman kurame,kamar basusan juna ba,innar nata muzurai,saboda so take kawai kaltum din ta matsa ta bata space da zataci namanta,don ba zata iya san mata ba.
“Mara mutunci,kin gama min gorin kudin da basukai komai ba a cikin arziqin da Allah ya yiwa ‘ya’yana,shine yanzu babu kunya ba tsoron Allah kika kwaso qafafu kikq min gida ko?,xuwaira ta daure miki gindi” dubar innar tayi sosai,sai taji dadi da umman bata kusa,yau xata sauke magana yadda ranta yakeso,babu mai taka mata burki
“Ai yanzun ma dana zo badon wani abu naki nazo ba,saboda ni nasan hannun ‘yan dambe ne dake,baya bayarwa saidai ya karba,indan ta abun hannunki ne kinsan ba zamu rabeki ba,kuma haushina da kikaji kan kudi Allah inna yanzu kika fara ji,don inda arziqi nane karki saka aka ma kan cewa zaki cishi” hasala sosai innar tayi,don kafin ma ta fara magana sai data janyo wani sandan mariqin maficinta daya cire ta wurga mata
“Dan uwarki don ubanki kada naci arziqin naki,basaima kinyi arziqin ba?,shegiya me baqar aniya,nida ubanki ai aga wanda yafi wani hannun ‘yan dambe,kuma idan zuwaira ce ta daure miki qarqashin kimin diban albarka bari na warware,daga ke har ita sai naga uban daya tsaya muku,nice fa nusaibatu,wallahi dai dai nake da kowanne dan iska da shegen gari” baki kaltum ta tabe,ko banza burinta ya cika ta kunnota,saita miqe tana cewa
“Oho dai,shi wanda kike zagin ko banza baya rufa sati baice mana ungo ba,ke kuwa fa?,ni idan kina da wanki tattaro min na miki,idan kuma babu na qara mai”
“Anqi a baki wankin don ubanki,ba zakiyimin ba”
“Allah sai nayi,gwara ma kiyi haquri tunda bake kika sani ba” daga haka ta sanya kai uwar dakan innar,saita fara yunqurin tashi tana cewa
“Kada ki kuskura fa ki tabamin kayana kattume,zanci ubanki fa” ta qarasa maganar sanda take komawa ala tilas ta zauna,saboda amsawa da gwiwarta tayi,tana daga zaune ta babbakun masifa kaltume na hado kayan wanki,batabi ta kanta ba ta hada kayan kaf ta fita dasu,sai daya fara share mata farfajiyar gidan sannan ta zauna ta fara wankin,har a sannan tana iya jiyo yadda innar keta surfa bala’i,ko gajiya bakinta ya kasa yi,tabe baki kaltum tayi
“Ba banza ba ake ce miki ‘yar azaba” kaltum ta fada cikin ranta,don sunan da kaf unguwarsu suke kiranta dashi kenam,sanoda yadda tayi shuhura wajen masifa,ba’a tabata ta qyale,shi yasa wasu ke mamakin yadda ta haifi mutum mai haquri irin ummansu,umma altine ce kawai tadan dauko fada da masifar inna,duk da cewa dama kadanne daga aikin ubangiji,don yana fitar da rayayye daga matacce.
Ana tsaka da haka kawu ado yayi sallama ya shigo gidan,yaransa mata biyu suna biye dashi,sahura da karimatu wadanda sa’anni ne ga kaltum,kuma sune manyan ‘ya’yanshi,sam babu haduwar jini ko jituwa tsakaninsu da kaltum,su din suna da rashin kunya da ganin sunfi kowa,musamman daya kasance inna tana ji dasu fiye da kowa cikin jikokinta,hakan yasa suka bala’in raina su kaltum din,su da suke Ζ΄aΖ΄an bora,duk da cewa ba haka mahaifinsu yake ba,wannan dalilin yasa kwata kwata kaltum bata sabgarsu,bama kasafai suka fiya magana ba.
Cikin matuqar girmamawa ta gaida kawu ado,ya amsa mata yana mata sannu ganin aikin da takewa innar,wanda kaf cikin jikokinta dama yaranta su kadai suke mata irin wannan hidimar,ganin har zasu wuce daga kubra har sahura babu wanda ya kula kaltum din,sai kawu ado ya kallesu
“Bakuga ‘ya uwarku bane xaku wuce baku gaisheta ba?”kasancewar tadan girmewa sahura da watanni,karimatu kuma kaltum din ta bata shekara dindi,sama sama suka gaidata,ta amsa musu da yanayin da suka gaidatan itama,ta debesu ta watsar.
Tana jiyo yadda kawu ado ya dinga mata mita kan fadan da taketa faman yiwa kaltum din,bata ko duba da aikin da take mata,da qyar ya sanyata tayi shuru,a halan ma don shalelenta ne shi din,da bai isa ba.
Sanda ta gama wankin ta shanya ta gyara waien,saita daura alwalar sallar la’asar data dan kubce mata,ta shimfida dankwalinta anan tsakar gidan daga gefe tayi sallarta,ganin har a sannan suna cikin dakin basu fito ba.
Sanda ta idar tana saman dankwalinta tana addu’o’in data koya daga makarantar darensu su sahura suka fito suka fice,da alama tafiya gida sukayi duba innar ne dama ya kawosu,ko da can su dama basu fiya zama wajenta ba ida sunzo,ita din ce ke qalatarsu.
Itama tashi tayi ta maida dankwalinta ta daura sannan ta rufa hijabinta,saita matsa daga qofar dakin innar ba tare data shiga ciki ba tace da ita
“Zan tafi gida,Allah ya bamu alkhairi”
“Har zaki tafi kattume?”kawu ado ya fada yana karkacewa,da alama wani abu xai zaro ga aljihun wandonsa
“Eh kawu….zan koma ne saboda umman namu itama bata jin dadi sosai”
“Ke banason qaryar banza da wofi,ita kullum cikin ciwo take?,ko kuma salon maular ne ya koma haka?” Ba wanda yace mata komai,sai zaro kudi da kawu ado yayi ya miqawa kaltum din
“Allah ya sawwaqwe,zanje in sha Allahu na dubata,na jima aima rabona da gidan”
“Kar ka bada wanna kudin ado,na gaya maka” da mamaki ya waiwaya ya dubi innar
“Kamar yaya inna?,kattume ce fa?,yar gidan yaya zuwaira”
“Ka fini sanin hakan kenan?,ina sane,kuma nace kada ka bayar,indai albarka kake nema ai wajena zaka sameta,miqo min nan”ta fada tana kaiwa kudin warta,sai gasu a hannunta,kota kanta kaltum bata biba ta juya tana sake musu sallama ta fice daga gidan,batasan ya suka qarke ba,saidai tana tafe mamaki na dada kamata,wanne irin shegen son abun duniya innar ta dorawa kanta?,don ba za’a ce Allah ya dora mata ba,wanne irin gagarumar qiyayya kuma take musu saboda kawai basu da abun duniya?
“Ba komai,akwai Allah” kaltum ta fada tana qoqarin hadiye bacin ranta.
Ta kusa da gida taga tabiyo ta hanyar gidan yaya muxammilu,saita yanke shawarar ta shiga ta karbo kudinta data bawa matarsa ajiya,idan yaso ko chemist din dake maqotaka da unguwarsu taje ta samowa ummansu maganin rahe radadin qafar,tunda kudin sunqi haduwa yadda takeso.
Da sallama ta shiga gidan,saita samu fiddau matar muxamillun xaune a tsakar gida,daga ita sai daurin qirji,don ko dankwali babu saman dagargajajjen kanta,dif fara’ar fuskarta ta dauke,amma hakan bai damu kaltum ba,saboda sam bata kawo zuwanta ne yasa fara’ar fuskarta daukewar ba,hasalima daurewa zuciyarta tayi,ta duqa ta dauki qaramin danta zakari dake rarrafe,kai kace an qwatoshi ne daga ire iren garuruwan da akaci da yaqi,futu futu dashi,ga zarni yana zubawa,bayaga majina da tasono data cika masa hanci.
Da qyar ta amsa gaisuwar kaltum din
“Kudin nan nazo karba”kaltum tace da ita,tana qoqarin ragewa zakari majinar hancinsa da wani tsummansu mai da ubansun dauda.
“Aiko kudin nan dai kattume saidai ince Allah ya baki haquri,don wallahi matsuwa ta sameni nayi gararin gabana dasu” ta fadi maganar kanta tsaye,saboda tasan cewa babu wani abu da zai biyo baya,inda asiya ce tafi kowa sanin bata isa ta karba koda tsinken sakacenta ta cinye ta kuma gaya mata hakan ba.
Sauke zakari kaltume tayi a qasa tana duban fiddau
“Ban gane bafa”
“Inaji cewa da hausa nayi miki bayani ko?,meye a ciki baki gane ba?”
“Kudina fa dana ce ki ajjiyemin,shi naji kina cewa matsuwa ta sameki kinyi amfani dashi,to aro kikayi,ko kuwa?” Wani kallon banza tayi mata,kana ta gatsina fuska
“Aro kamar yaya?,kinyi sadaka dai kawai,don babu ranar biya” danqari!,kaltum ta fada cikin ranta,ta dade da sanin fiddau bata da kunya ko kadan,tana da labarinta,amma tasu bata taba hadosu ba,tadai taba hadosu da asiya,itama kan ajiya data bata,amma salin alin ta biya asiyan abinta,sabida sanin ta fita iya tijara,batajin koda kyauta zata barwa fiddau din bai kamata ta biyo ta wannan fuskar ba,tunda ba’a kyauta dole,tana mamakin yadda mutane basa kunya ko tsoron Allah,hakanan basa shayin danne haqqin wani,amma tunda ta biyo mata ta hakan,ita kuwa zata nuna mata ainihin kalarta,zata ajjiye matsayinta na matar wanta
“Wallahi wallahi banyi niyya ba,saboda haka bazan bayar ba,ki nemo kin kudina tunda wuri wallahi,na baki kwana uku” daga haka ta miqe ta nufi hanyar fita.
Saidai kuma hausawa sunce tabarmar kunya da hauka ake nadeta,ba kunya ba tsoron Allah fiddau ta biyo bayan kaltume ta soma zuba mata masifa da bala’i,kai kace itace ta cinye mata kudin,daga bisani ma sanda suka kai qofar gidan,taga tana shirin tafiyarta ne ba tare da anyi uwar watsi ba,saita soma zunduma mata ashar,cikin rashin sanin halin kaltum ta kirayi sunan umma tace ko ita bata isa ba.
Cak kaltum ta tsaya,sannan tayi wani reverse cikin wani irin zafin nama tayi niyyar komawa gaban fiddau din don ta banbance mata aya da tsakuwa,sai mutanen da suka fara tsaiwa saboda hargowar fiddau din suka rirriqeta
“Wallahi wallahi zaki gane kinyi kuskure,kuma karki wuce kwana uku baki dawomin da kudina ba”saita qwace hannunta daga wajen mutanen tayi gaba tana fidda numfashin bacin rai
“Ke zaki gane kinyi kuskure,zakisan dani fiddau kwalba kike magana” cewar fiddau din tana dukan qirjinta da hannunta.
Dogon tsaki yaja yana sauke hannayensa daya nade a qirjinsa,saiya juya zuwa hanyar da suka baro din,wanda hakan ya baiwa umar dake tare dashi mamaki sosai
“Ya naga ka juya sir”
“Na fasa fitar” samir ya bashi amsa,saroro umar yayi,a iya saninsa baisan meya bata ran sarakin lokaci guda ba,saiya dubi wajen da aka gama rabiyar fada da yarinyar ranar nan,ya dauke idanunsa ya maida kan samir da har ya soma bada tazara da inda shi yake tsayen,ya cira qafarsa da sauri yabi bayansa,babu jimawa ya tarad dashi,a lokacin yana qoqarin cusa earpiece a kunnensa
“Am sorry,ya fahimci abunda ya bata ransa,mutum ne shi da yaqi jinin rashin baiwa na gaba girmansa master……kasan duk inda akace akwai rashin ilimi da rashin wayewa sai ana ma mutum uzuri” baice masa komai ba,illa kunna abinda yafi yawan saurara lokaci bayan lokaci saboda debe kewa,bai taba zama a wani qauye ba idan za’ayi aiki irin wannan ba sai a wannan qauyen,shima zaman nasa yana da nasaba da wani tarko daya dana,wanda yake saka ran kama abinda ya danawar kafin komawarsa gida……….