Bakar Ayah Book 2 Page 43-44
Page 🖤 43••44🖤
Anyi kimanin wata biyu kenan lubna na yanda taso a cikin gidan.
Jabeer ya rame yayi vaƙiƙƙirin,ba iya gashi ba harda ma Hajiyah Zeenah,wacce a neman magani babu abinda batayi ba amma abu yaci tura,kullum abu cigaba yake kaman jinyar ajali.
A tsawon lokacin duk hanyar da bombee zatabi su haÉ—u da Jabeer ta daina yin wajen,dan haka kawai zuciyarta bata jure ganinsa a hakan,yayinda kullum tsanar lubnah da danginta ke cin ranta.
Gashi har yanzu Duk azabar datake ganawa Zilliyyah ta gagara cire abinda ta ƙullawa innarta,a duk lokacin data yi ƙoƙarin kaita wajen magani kuma saitaji gaba ɗaya bazata iya ba,tasan baya rasa nasaba da yanda itama ba ƙalau take ba.
Abinda yafi dauremata kai ma shine ita kaɗaice a cikin damuwar,su waɗancan matannasa shirye shiryen barin ƙasar suke yi,kullum basuda aiki sai facaka da dukiya,musamman ma Jaleelah,ita da take ƴar talakawa to a ina tasamu kuɗi,ko kai a dukiyar Jabeer suke ɗiba,sannan duk wani bincike tayi akan ta,har yanzu bata gano wani abu da ta tabayi mai kawo kuɗi haka ba..
Ta sanja kayan ɗakinta ta sai mota,kaya kuwa inta saka bata sake sakashi,masu aiki ma biyar ta ɗauka nata personal,a yanda aka faɗamata dai ustaziyah ce bata damu da duniya ba,tabbas akwai wata a ƙasa,musamman yanda suke yawan fita kusan duk dare itada Jawaheer.
Inka gansu bazaka ce ma wai abinda lubnah take yashafesu ba sam,ko kallon inda Jabeer yake idan suka haÉ—a hanya basayi,shima dayake abi yana kansa ya haushi ko magana bayayimusu idan zasu fita.
A zaune take ta ɗora kanta a jikin majinginar kujerar,tana jiyo gwarancin haidar wanda yake koyon tafiyah kaɗan kaɗan,ƙarar wani abu tajiyo ya zube,amma bata buɗe idanunta ba,ta tafi cikin kogin tunani.
Muryar maleekah tajiyo a tana yimasa magana a corridor,
“Anty maryam allah mai sunan babannan nawa bayaji,kiduba kiga abinda yayi a kitchen”
“Uhm to ya zanyi dashi maleekah,ya jarrabawar dai?”
“Hmmm ba’a cewa komai ai,so nake muyi muyi mugama kafin bikin anty Madeenah da yah khaleel. Naso bikinnan yazo da raji amma nasan bazayyiyu ba,tunda ga can babban abokinsa baya hayyacinsa sam”
“Ba nan da wata biyune bikin ba?”
“Uhm nan da wata biyune”
“Kafin sannan ai zai warke inshaallah,zakusha raji kam sosai”
“Zamu sha bazaki je ba ai anty,taya kika san zai warke,dan allah faÉ—amin kin samo mafita,nasan bazaki gagara samu ba dan Allah ki taimakeshi anty maryam kinji”
“Kinga ki kyaleni yanzu tukunna,in akwai mafitar ma zaki gani ai,bari lokaci ya nuna”
“Yawwa kiji wani zance wai Jawaheer da Jaleelah zasuje Egypt a jirgin Yaj Jabeer,Hajiyah Zeenah suka tambaya tacewa yah Jabeer yabasu izini.
Sai yace wai lubnah bazata amince ba,bakiga ba kaman zasuyi kuka haka sukayi booking kawai na jirgi normal”
“Yaushe akayi zancen?”
“Uhm jiyane naji Jawaheer tana faÉ—awa Hajiyah Zeenah wai ita tagaji da wannan abin”
“Duk acting ne,babu wacce ta damu a cikinsu inkinga barin kuÉ—in da suke zakisha mamaki,duk kallonsu nake kafin nazo takansu,kowa barshi nake ya mori lokacin sa,ina so ki jiyomin yaushe zasu dawo idan suka tafin?”
“Tam bakida matsala,nasan bazasu gagara faÉ—awa mommah ba,ni barina je waje iyah sayyada,abinci nabiyo ci kuma naga baki gama ba,kuma fah saida Innayi tace na shiga naci hilyan ta dafa amma naÆ™i”
“Kinyiwa kanki,ni yau ba lallai ma nayi abinci ba,ki zama cikin shiri akwai gagarumin aiki a kwanannan”
“Wow really wanne iri”
“Kin fiye tambaya fah,zaki gani”
Tana shiga bacci bai daÉ—e da É—auke ta ba taji muryar mutum a falo,batayi kama data su hilyan ba ko maleekah.
Tsuka taka tareda tashi tafito,da Dr Rahama sukayi ido biyu wacce take yimata dariyah.
“Ahh dakyau mrs JJ,baccine haka da rana,kina hutunki kice”
“Rahama kece,daga ina haka?”
“Uhm daga asibiti nake,Nagama aikin yau shiyasa na shigo miki,iya gaisawa zamuyi na wuce”
Zama tayi bombee ta kawo mata ruwa da abin motsa baki,kaman yanda kuwa tace bata daÉ—e ba ta tashi akan zata tafi.
“To nikam zan tafi Captain i hope kema zaki zomin koh”
“Zanzo idan har baki sake Æ™irana da wanann sunan ba,banason abinda zaisa na dunga tunawa da rayuwar baya rahama,shiyasa na zabi mantawa da komai,saidai hakan bazai yiyu ba indai har bangama aikin dayaÆ™i Æ™arasuwa ba”
“Hakane kam Maryam,nidai duk sanda kike buÆ™atar taimakona Æ™ofa a buÉ—e take”
Sun fito har inda motar rahama take,tana magana sai bombee taji tayi shuru tana kallon Jawaheer da Jaleelah waÉ—anda suka fito da trolly a hannunsu zasu fita,da alama jirgin rana zasu bi kenan zuwa egypt É—in.
Basu kulada su bombee ba sunata surutu har suka bar gidan.
Kallon Dr Rahama bombee tayi wacce take kallon hanyar da su Jawaheer suka bi,idonta cikeda mamakin ganinnasu.
“Yadai kinsansu ne naga kina wannan kallon”
“Umm to kusan hakan,su É—in suwaye a gidannan,sannan ya dama Æ™awayene?”
“Ƙawaye kuma,sune fah matan da Jabeer ya aura wata uku da suka wuce”
“Aure…..aure kuma,waÉ—annan ya aura,dama sune Jawaheer da Jaleelah danakejin sunan matan daya aura,duk tsawon haÉ—uwata dasu bantaba sanin sunansu ba shiyasaka.
Indai kuwa hakane to da akwai babbn matsala,ina tausayawa Jabeer da Allah ya haÉ—ashi ba iya da guda É—aya ba harda biyu”
“Meyafaru ne a ina kika sansu?”
“Zancen bana nan bane muje ciki kiji,dama ina cewa duk taimakon dakikeso da gareni to zanyi miki in baifi Æ™arfina ba,to ga wani anan muje ciki kiji shi kuwa”
Jan hannun bombee tayi a fusace suka koma falonnata,da falon bayyi musu ba suka cike can ɗaki,da alama koma menene yana buƙatar babban sirri.
Bayan dr rahama tagama fesawa bombee labari kafin ta tafi,Dariya take tana tafi a falo ita kaÉ—ai kaman mahaukaciya.
“Ohhh dama hakane……kai ni bombee mai sa’a ce,mai yasa idan mutum ya binne abinsa saina samu hanyar dana bankaÉ—oshine??,A da nayi tunanin kuba matsala bace,ashe kuma manyan tantiraine,zakuwa kuzo hannun boss É—inku ni nan bombee”
Message taga maleekah ta taturo mata,akan Sati guda zaauyi su dawo.
“Good satin bazayyi kaÉ—an ba na gama shirina,amma kafin su sai an gama da waccar ishashiyar tukunna”
*Conrad Hotel Cairo__Egypt*
Banɗakine amma yafi wani falon ma girma,gurare daban daban,na wanka,na rage pressure da kuma ƙaramin swimming pool duk a ciki.
Jawaheer ce a cikin ruwan tana linƙaya,yayinta ita kuma Jaleelah take zaune a bakin wajen daga ita sai bikini tana sipping lemo.
Fitowa tayi daga cikin ruwan tana taku zuwa inda Jaleelah take zaune.
“Uhm no wonder kin amsa sunan cat lady É—in”
“Kaman yanda kema kika dace da black slender ba,wai ya akayi kina da waÉ—annan kuÉ—aÉ—en kika iya boyesu haka?”
“Uhm saboda na iyah kafce shiyasa,dama wanann lokacin nake jira,na auri mai kuÉ—i nayi facaka da dukiyata,a gida aga kamar da tasa nakeyi. Ya kike ce toh”
“Abin yayi kam,nikam ban fiye yin harka domin kuÉ—i ba,sai dan inaso”
“Tun mukazo kwanannan mu uku amma bamu fita ba,yau kam yakamata mu shaÆ™ata sannan mu haÉ—u a wajen meeting É—in gobe”
“Ohk shikenan,nifah Æ™ungiyar nan tafara isa ta yanzu,anya kuwa bazan fita ba”
“Uhm zaki iya fita kekam,amma nikam ba yanzu ba,musamman da yansu nake haskawa a cikinta,dan da duk cikin takura nake komai,ko meeting ma sai ayi biyar bansamu zuwa ba,koyaushe sai waccar islamiyyar”
“Uhm to amma ita fareedan yana ga yanzu bata fiye zuwa meeting ba”
“Nima yanda kikaga tanayi,ba’a tashi take tafiya haka nakeyi,nima irin taki ce na Æ™ara class yanzu,da burina Æ™arbar kuÉ—in kawai amma yanzu babu wanann maganar”.
*** ***
Motsin mutum take gani yana wulagawa ta window.
Can kuma sai taji an buÉ—e cikin falon an shigo a hankali.
Tashi tayi ta tsayah tareda yin hanyar inda makunnar wutar take,dan data shigo falon bata kunna ba,saboda ganin iya ruwa kawai zatasha ta koma.
Yau daya tabar Jabeer yayi tafiyar kwana É—aya,shima saida ta kafa masa sharaÉ—in ya tabbatar ya dawo dawuri washagari.
“Waye anan,Jabeer kaine ka dawo,idan kaine kadaina wannan wasan yanzunna bana so”
TafaÉ—a cikin sigar umarni, tafiya takeji ta bayanta,saita juya taga babu kowa,gashi duk sanda tayi hanyar wajen socket sai a jawota tabaya.
“Wai wanene mai kuma kakeso?”
TafaÉ—a cikin sigar karaya.
“Ohh kin karaya yanzu babu sigar umarnin ne,a zaton wancan ne dakika shanye shi koh,tun shakaranjiya nake auna ki sai yau nasamu bayanan,lokacin dana baki ki shaqata yaÆ™are lubnah”
“Maryam mai namikine kike shiga rayuwata,kefa kikace kowa yayi harkarsa ba zama kikazo da mijina ba”
“Eh haka ne ba zama dashine maÆ™asudin zuwa na ba,dalilin zuwana gidannan shine fatattaka rayuwarki,domin haka Hajiyah Zeenah tayi yarjejeniya dani”
Shuru ne yaratsa wajen kafin taji bombee tana cigaba tacewa.
“Ohh wai sanÉ—a kike zaki É—akko wuÆ™a ko kuma zaki gudu,hhhhh kidaina wannan wautar,don ke bakya ganina sai akace ni bana ganinki kenan,Mai kika É—auki kalar idona na banza kenan?.
In baki yadda ba saina faÉ—amiki duk abinda kika yi yanzu,ina ganinki kaman yanda kike gani idan gari ya waye rana ta kusa fitowa”
“Ki rabu dani ki fita harkarta,dama nasan ke ba mutum bace ke mayyace”
“FaÉ—i ki Æ™ara bake kaÉ—ai bace kika faÉ—a,yanzu haka ma barina yimiki aikin mayun ”
Tana gama faɗin hakan lubnah taji an shaƙa mata abu a cikin towel,daga nan ba iya ganinta ne ya ɗauke ba,harda jinta da kuma hankalin ta.
Wajen dokar dajine babu mutum gaba babu shi a baya,sai iya wani kangon gida wanda babu mai zaton akwai wata halitta a ciki.
Bombee a cikin gidan a zaune kan kujerar katako tana lilata,gefenta kuma hilyan ce a tsaye da kuma khmees,baƙaƙen kayane dukkansu a jikinsu. Har sannan gari bai gama waye ba,amma kana ganin komai tarau.
“Ke hilyan É—auki ruwan sanyin can ki sheÆ™a mata,lokaci yayi dazata farka daga mafarkin datake ciki ta fuskanci zahiri”
Aikuwa kaman jira take ta É—auki ruwan mai uban sanyi ta sheqawa lubnah shi ta sama,wacce take É—aure tamau kaman za’a yanka dabba.
Wani razanannen numfashi tasake tana zazzare ido,da bombee tayi arba a gabanta tana zabga mata murmushi.
“Yadai Hajiyah lubnah kingama baccin kenan,yanzu kuma keda baccin daÉ—i kingamashi kenan,dan a kabari ma nasan keman baza’aga dadai ba”
“Wayyo Maryam Mai nayi miki kika kawoni nan wajen,dan allah konawa kikeso ki faÉ—a zan baki,amma ki sinceni na koma gida”
“Kinga dakata ni babu abinda zanyi miki,kawai É—aureki zanyi anan wajen na wata guda saina sakeki,ko Æ™wandalarki bazan karba ba”
Zaro ido lubnah tayi jin jawabin da bombee tayi mata,wata guda?? In hakan tafaru shikenan tata taƙare kenan?.
“Meyasa dole sai na kai wata,ko nawa kikeso ki faÉ—a zan baki ki sakeni,in so kike ma zan bar Jabeer ya dunga zuwa wajenki,amma naroÆ™eÆ™i ki kwanceni na koma”
“To wai menene na tada hankalin ne,nace fah ba abinda zan miki,kinayin wata guda zaki tafi.
Ko kai akwai abinda kike boyewa?”
“Ni ba abinda nake boyewa kawai…..”
“To shikenan zakiyi zamanki anan wajen har wata guda tacika,ni barina tafi kar a gane nina É—aukeki koh,ke hilyan ku dunga bata abincinta hankali kwance tanaci,iya kawai wata zatayi takoma wajen mijinta”
Ihu lubnah tasaka tareda jijjiga sarƙar da bombee ta ɗaureta dashi.
“Wayyo na roÆ™eki ko dukana ne kiyi,ke ko hannuna kikeso kicire,amma kada ki É—aureni anan wajen harna tsawon wata guda,na yarda ki gana min azaba inyaso ki sakeni nan da sati uku”
“Wata guda nake so nagama magana”
Har bombee taje bakin ƙofah zata fita tajiyo wata magana.
“Idan har baki sinceni ba nakoma to Jabeer zai mutu a cikin wata gudannan,dan haka inkinaso yarayu to ki sinceni na tafi,saboda banason ya mutu nake roÆ™onki daki sinceni na koma”
“Hhhhhhhh kutt yau bayan tsawon lokaci an samu wacce ta É—aukeni shashasha,ni zaki raina wa wayo lubby,kowa yaga mai kike ai yasan dan kanki kike wanann magiyar.
Kuma ki kwantar da hankalin ki ma,wlh inkinga kinbar wajennan to wata guda yacika ciff,saidai in allah ne yayi ikonsa akanki,wanda nasan hakan ma bazata faruba,saboda baya bayan mutane irinki,shiyasa ma yabani ƙarfin gwiwa da lasisin ɗaiɗaita rayuwarki.
Ki zauna nan da sati zanzo na ganki kinji,barinaje naga yanda za’ayi ta yawon nemanki a can”
Tunda lubnah taji abinda bombee ta faɗa batasake cewa komai ba,banda ruwan hawaye babu abinda yake bin kuncinta,a iya mintunan da basu fi uku ba gaba ɗaya saitin ƙwaƙwalwarta ya karkace,dan bata hango hanyar fita daga hannun wannan mai zubin sheɗanun ba .
Lokacin data isa gida babu wanda ma ya tashi,abinka da zubin rayuwar Æ´an gayu,itama gado ta hau tayi kwanciyarta hankali kwance,tsawon lokaci sai yau taji rayuwarta tayi sanyi.
Muryar maleekah tajiyo tana ƙiranta,wayarta ta duba shabiyu da rabi,lallai ta kwashi bacci.
Dan dama Haidar tun jiya takaishi wajen innayi.
Fitowa tayi tasamu maleekah a zaune a falo,tun kafin su gaisa tashiga koro mata bayani.
“Anty kinji wani labari,wai Jiya masu garkuwa da mutane sun shigo gidannan sun É—auke anty lubnah,harda gwalagwalai da kuma takardun gidajenta data siyah duk aka É—auke.
Dafe ƙirji bombee tayi tareda cewa.
“Yaushe haka tafaru,nikam ti basu shigomin nan ba,sauran sashen fah sun shiga”
Ahah wai iya nata suka shiga,sukam basanan ai,amma mommah tayi musu waya kan su dawo suma,zuwa yamma zasu iso a duba ko anshiga sashensu”
“To ina Jabeer kuma fah yadawone”
“Hmmm ya dawo É—azu,babu abinda yake sai Æ™iran sunan lubnah yana kuka,gaba É—aya ya tadawa kowa hankali”
“A wanne waje yake yanzu haka?”
“Uhm yana sashen momma,itama kukan take ganin yanda yake yi,anty maryam abinfah ba kaÉ—an bane ba.
Itama brr na’imah yanzu da tafi daga nan,sojoji da masu bincike sai fama suke tun safen”
“Amma har yanzu babu wani clue na inda take?”
“Eh babu fah anty maryam,gashi har yanzu basuyi maganar nawa suke so ba,inaga dan anga brr na’imah na neman minister ne shiyasa aka saceta saboda kuÉ—i”
“Ba mamaki kam To Allah ya kare”
“Ameen ni ba zafin batanta nakeji ba,abinda Jabeer yake duk shiyafi damuna,barina je wajen mommah Anty maryam”
“Ohk to nima barina shirya nashigo yanzunnan”
Maleekah tana fita Bombee tayi murmushi tareda cewa.
“Hmmm saikun jure wahala kafin ku samu sauÆ™i,brr na’imah yanzu ma kika gani,keda ganin Æ´arki sai kamanninta sun juye tukunna”
ÆŠaki ta koma tasaka goduwar riga da mayafinta,kafi ta fito ta nufi sashen Hajiyah zeenan dan ganin mai yake wakana.
*** ***
Waya take gabaÉ—aya banda gumi babu abinda yake zuba a jikinta.
“Wai kan nufin har yanzu ba’a ganta ba,duk Æ™arfinka a bangaren tsaro ka kasa gano inda Æ´arka take,kai wanne irin ubane,to kada ka dawo gidannan har sai ka samomin Æ´ata a duk inda take”
Tana cikin wayar Inayah a cikin shigarta ta tsofi tasake miƙomata wata wayar,nan ma detectives ne masu bincike suke ƙiranta.
Karba tayi ta danna suma tacigaba dayin waya dasu,tanajin babu labari lubnah ta buga wayar a ƙasa.
Kallon Inayah tayi tareda cewa.
“Kema wata tsohuwar marar amfanin,ina ammar ya shigo gidannan?”
“Eh yashigo hajiya amma yayi sashensa,dannaga yasaka akaimasa abinci ma irin wanda madam juliet take ci”
Tana jin haka taja tsuka tareda yin sashennasa.
Lokacin data shiga daidai zai sakawa juliet abinci a baki,wacce take ta narkewa tana shafa cikinta.
Ƙafa tasaka tayi ƙwallo da plate ɗin abincin a falon,sai huci take kaman kububuwa.
“Ammar kaikuwa mutum ne,anya kuwa baka samu tabin kai ba,Æ´ar uwarka tana can a hannun bata gari bamu san inda take ba,kaikuma kana nan da wannan fatalwar matar koh”
“Haba to mommy yakk so nayi,tun safe fah ake ta neman ta ba’a sameta ba,Æ™inÆ™i kici abinci,kin hana abba yaci nima kin hanani,to sokike shima babyna bazai ci ba kenan.
Dan Æ´arki ta bata shikenan nima sainawa É—an yashiga matsala”
“ÆŠan ka a gidan ubanwa É—in,waye tacemaka É—anka ne a cikinta,kodan kaga nayi shuru na zuba muku ido kai”
“Whatt…..mommy mai kike nufi wai,ba É—ana bane nawaye toh”
“Bansaniba ka tambayeta mana ta baka amsa”.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________