Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 6

Sponsored Links

Page 06

“Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za’a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin”,tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata.

Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa’a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita.

Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa

“Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma’il ba(mahaifin mahfood)” murmusawa alhaji yayi

“Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za’a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma’ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu” kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa.

Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa

“Tashi……ruwa sarkin kwanciya” sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan

“Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa” da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma……ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki.

Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa

“Zaki qarasani ‘yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin ‘yan uwanki” ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau.

A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka ‘yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo.

Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi ‘yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi

“Ga barka da sallah ta nan” rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki

“Na gode ummu” sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu.

Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata

“Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?”

“Wajen anty madina zani” ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan.

Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin ‘yan uwanta ayi mu’amala da ita kamar kowa.

Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu ‘yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya.

Sai bayan isha’i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru.

Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama

“Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?” Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta

“Bari kawai hauwa’u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi”

“Wa fa?” Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece

“Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun” baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen

“Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba’a yi wasa ba gaba sai abinda tace za’a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta” fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan

“Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan”

“To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba” shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba.

A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai

“Banason wannan maganar,ku qyaleni haka” yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar.

Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma’aruf,ma’aruf dai,ma’aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma’aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba

“Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma’aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma’aruf,jika ne shi cikin gidan,d’an mace ne)tamkar ‘ya take a waje na”.

Ci gaba tayi da sabgoginta abinta,ta.maida kanta ga islamiyyar da take zuwa,don tunda aka koma hutu boko bata koma ba,alhaji yace ya isa hakanan,su maida hankalinsu ga islamiyya,ita dasu Aafiya,yayin da zancan bada ita ga ma’aruf ya fara yawo cikin gidan.

Zancan ya zowa anty madina ta bakin mijinta uncle mulhim,ta jinjina lamarin sosai

“Tirqashi” ta fadi,saboda tasan irin rashin jituwar dake tsakaninsu,duk sanda widad ta shigo tana binta da kallo yadda take sabgoginta da alama batasan abinda yake faruwa ba,tana tausayinta itama,tana yarinyarta amma sai abubuwa ke zuwar mata kamar wata babba?.

Bata tashi sani ba sai wata rana suna dawowa daga islamiyya,a hanyarsu ta zuwa gida sun biyo ta wani layi,tun daga nesa suka hangi ma’aruf din yana tahowa shi da wani abokinsa,kunnensa maqale da earpiece suna hira kadan kadan da abokin nasa,kafin su qaraso Aafiya tasa hannu tadan bugi widad,wai tanason mata nuni dashi,saidai ko daya ita widad din bata ma fahimci me take nufi ba har suka qaraso dab dasu.

Aafiya ce ta gaisheshi tana rusunawa,ya amsa mata suka wuce,widad kam da idanu ta bisu har suka wuce din,sai taja tsaki

“Yanzun ya kusa zama angonki ma ba zaku fara magana ba widad?” Wani kallo tayi mata cikin quruciya da sakalci

“Waye angon nawa?,ni ba wanda zan aura na gaya miki ina wajen ummu na,tare zamuyita zama”

“Tabdijan,ni kuwa ana cewa aure za’a yimin zan yarda,bakiga kayan lefen da aka kawowa su anty ramziyya ba?,ga kayan girki da gadajen da aka siya musu masu yawa fa,ke don har yanzu bakije gidajensu ba,baki gani ba gwanin sha’awa,su dafa abinda sukeso,suyi kwanxiyarsu a gadonsu,ba duka ba aike ba fada,ke…..hmmmmm” Aafiya ta fada da alama abun yana burgeta,fuskar widad ta dan sauya zuwa fara’a

“Su ai sun girmemu,ko auren za’ayi mana ba za’a yi mana irin nasu ba” kama baki Aafiya tayi tana fidda ido gami da kallonta

“Inji wa?,wallahi momma tace qila ma mu samu abinda yafi nasu”

“Allah?”

“Wallahi” sai widad din tayi shuru tana jinjina kai,hadi da tuna yawan kayan da aka fitarwa kowacce cikinsu ramziyya daga gidan aka sa amota zuwa jeren gidanta.

Sam ta manta ma da wani zancan ma’aruf,har suka isa gida suna zancan kayan auren,a harabar gidan suka rabu kowa ya shige sassansu.

*RUMBUN K’AYA*πŸ”₯

*DAUDAR GORA*πŸ”₯

*IDON NERA*πŸ”₯

*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

*KI KULANI*πŸ”₯

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

0022419171
Maryam sani
Access bank.

Shaidar biya tananπŸ‘‡πŸ»
09033181070

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+227 90 16 59 91

Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*πŸ”₯[2/3, 4:25 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button