Arubuce Ta Ke 39
Page 39
Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata ‘yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa.
Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa
“Lafiya dai ko?,ba wani matsala?” Gyara tsaiwarta kadan tayi
“Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba”
“Ya salam” ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda
“Matsala kan matsala” ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki.
Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate.
Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa
“Tashi muje” ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa
“Gida zaka kaini wajen ummu?” Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu
“Wait….zo mana kiji” ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau
“Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu”
“To” kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa.
Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah…..a sanda kake buqatar ka huta……wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?.
Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa
“Allah ya kiyaye hanya,saina taho” ta zura hijab din tayi gaba abinta.
“Na shirya” ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa.
Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta.
A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun.
Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau.
Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida.
Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri.
Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad’i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa.
Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi.
Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar
“Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru” ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar.
Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska
“Barka da dare” ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi
“Tana ciki ne?” Kai ta girgiza
“Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye” saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu.
Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?.
Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace
“Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha’afa” hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la’asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye
“Qanwarki keta rigima nadan fita da ita” sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa
“Ayyah…..haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba” ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din
“Ka wuce ka huta,bari na rakata” ta fada tana kallonsa.
Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi buqata a yanzu irin ya watsa ruwa a jikinsa ya kwanta.
Sai data tabbatar tayi nesa da widad daga inda abbas yake sannan ta fito tabar sashen,bayan ta gama mata lallashin qarya da nuna kulawa,wanda qasan zuciyarta cike yake fal da tsana da kuma qiyayyar yarinyar,tana jin kamar ta budi idanu taga babu ita kwata kwata cikin gidan.
Latifa ce ta sakata a gaba kan sai taci abinci,da yake a gajiye take,kuma yunwar take ji da gaske saita zauna taci din,tana tsaka da cin ma baccin ya kwasheta ko.hannu bata wanke ba,sai tatifa ce ta gyara wajen ta kuma tasheta ta koma dakinta.
Washegari tunda wuri latifa taga kiran ummu,bata yi jinkiri ba ta daga,don dama tana da niyyar kiran nata,bayan sun gaisa widad ta fara tambaya,bata boye mata ba ta gaya mata yadda suka wuni jiya,muryar ummun ta canza,da alama ita kewar widad din tata takeyi,sai tace takai mata wayar.
Bacci takeyi amma sanda tace mata ummu ce sai gata ta wartsake sarai,ta karba wayar tana kiran sunanta hawaye na shirin balle mata,tausayinsu duka ya kama latifan,sai ta fice tabar mata dakin bayan taja mata qofar.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)