Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 38

Sponsored Links

Page 38

“Don Allah ki dauramin,na kasa wallahi” tayi maganar tana miqawa latifa dankwalin ba tare data lura da hafsa dake zaune a gefe ba,tana jin kamar ta mutu,abbas ya gama cutarta,yaje ya auro yarinyar data kusa haifa?, sannan kumata fita komai da komai na siffa?,duk da tana qoqarin qaryata kanta da kanta,tana qoqarin gayawa kanta idonta ne yake ganin hakan

“Kawo,Allah ya gyara min ke,bansan sanda zaki koyi daura kallabi ba” dariya tadan saki

“Ni nauyi Allah,banda anty deena ta takura”

“Ga antynki nan baku gaisa ba” latifa ta fada bayan ta karba dankwalin tana lanqwasashi.

A sakarce ta waiwaya ta dubi hafsa din da irin kallon da takewa kowa,ba tare da ta bawa matsayinta muhimmanci ko matsar dashi gaba daga matsayin da take bawa kowa data fara saninsa ba

“Ina kwana?” Ta furta cikin girmamawa kamar yadda ta saba gaida dukkan wanda ya girmeta

“Lafiya lau qanwata,ya kwanan baqunta?” Hafsat ta fadi da wani murmushi da takejin kamar na sossoka qayoyi ne cikin bakinta.

Murmushi ta danyi tana maida dubanta ga latifa,saboda batasan amsar da zata bayar ba,don batasan amsar da ake bayarwa din ba,ta dan ranqwafa kadan latifa ta soma daura mata dankwalin.

Cas ya zauna a kanta,ta daga kai latifan tana kallonta

“Ehen…..yauwa,yanzu kikai dauri” latifa ta fada cikin tsokana.

Idanunta hafsa takai kai,cikin sakanni taji ba zata iya ci gaba da zama tana kallon yarinyar ba,wani irin mugun kyau da kwarjini daurin yayi mata,saita miqe cak tana cewa

“Bari na koma,yau jiki yayi nauyi ban samu dafa muku komai ba,kuyi haquri” murmushi inna laila tayi

“Lah,babu komai fa,yaran ma suna gab da kammala dafa abun karyawan,ai ansha hidima wallahi,mun gode,Allah dai ya qara hade kanku,ya kade fitina,gata nan sai ayita haquri da ita,har yanzu akwai quruciya sosai a tare da ita,sai ana yi mata nuni,ana kuma gyara mata inda tayi kuskure,ayi haquri da ita don Allah” ta fada zuciyarta na danson naqaltar mata fuskar hafsatun

“Aiba komai wallahi” ta fada a taqaice,can wani sashe na zuciyarta yana jin kamar ya zundumawa inna laila ashar,babu zancan quruciya uzuri ko daga qafa ga duk wadda ta aurar mata miji,koda kuwa widad din qyanqyasar yau ce,tunda har ta iya sanin meye so?,ta banbance tana sonshi,ta kuma iya sanin meye aure ai magana ta qare,babu daga qafa babu ragi babu kuma rangwame,haka ta dinga jefa qafarta zuwa sassanta idanunta basa gani sosai,fatanta Allah yasa abbas ya wuce sashensa,ya kamata ta rage kukan dake damunta a qirji.

Cikin awannin da suka biyo baya suka sake shiga qalqale sassan nata da kyau,duk sauran abubuwan da ba’a gama kintsawa ba suka kammalasu,sun gama kuwa da wuri,saboda wadanda ke presidential lodge din da aka kaisu motoci sun kwasosu sun dawo dasu gidan,nan da nan sashen ya dan qara cika,anata hira da barkwanci,kusan kowa gidan widad djn ya tafi dashi,saboda babu ce kawai babu.

Duk da wannan jikinta ya mata wani mugun sanyi,babu wannan hayaniya ko kazar kazar din,tana lafe a waje daya kusa da inna laila,itace ta zame mata kamar ummun nata,mugun kewar ummun take,gaba daya zuciya da jikinta babu dadi,duk da yadda suketa qoqarin janta da hira da kuma wasanni.

Qarfe sha biyu har sun fidda jakankunansu harabar gidan,sun kuma fito waje,zuwa sannan idanun widad fararen nan sun fara kadawa suna tara ruwan hawaye,hakanan ta riqe hannun inna laila gam.

Sanda suka fara shiga motocinsu dai dai lokacin ya iso,shi ya fara qarasowa wajen sannan hafsat wadda keta yashe baki tana sake binsu da murmushin yaqe.

Cikin nutsuwar nan tasa yake tsaye gaban motocin,yana sanye da wani soft yard na maza gray color da yayi matuqar kwantawa a lafiyayyar fatarsa,jikinsa na fidda soft scent mai kwantar da hankali.

Tsaf kowa ya shige,saura inna laila da latifa,a sannan tuni ruwan hawaye ya gama wanke mata fuska tsaf,zame hannunta da inna laila ta soma yunqurin yi ya sanyata fashewa da kuka sosai

“Don Allah inna zan koma,karku tafi ku barni” ta fada tana sanya hannunta saman fuskarta,saita karya zuciyar kowa,inna lailan ta dubeta

“Ga latifa nan widad,zaku zauna tare kafin wani lokaci,kiyi haquri” daga haka sai ta matsa gaba,ta kuma shige motar da sauri,gaba tayi zata matsa hafsat ta rigata,ta kuma riqota,a zuciyarta tana jin kamar ta rufe widad din da duka sannan ta hadasu su wuce kanon tare,amma sai ta shanye ta kuma hadiye wannan,cikin sigar lallashi tace mata

“Haba mana widad,kiyi haquri,ai saiki karya musu zuciya,ba gani ba?,ga yayanki ma,sannan ga latifa an bar miki,kome kikeso ki gaya mana kinji,babu mai takura miki, kiyi shuru mana haba,yanzu inda su nawwara na nan ai sai su tsaya kallonki antynsu tana kuka” ta fada tana rungumota jikinta,ta rintse idanu tana jin kamar ta kara wuta ne a jikin nata.

K’asa k’asa take kukan har zuwa sanda motocin suka gama ficewa a gidan,shikenan sun tafi sun barta…..shikenan sun rabata da ummun ta…… shikenan bata da kowa…..haka zuciyarta ta dinga gaya mata.

Hafsat dince ta matsa gaba da ita wajen latifa tana miqa mata ita

“Ki kaita ciki ta zauna ki lallasheta” sai latifa ta gyada kai tana kama hannunta tare da jawota jikinta suka fara barin wajen tana yiwa widad din magana qasa qasa,saidai da alama ba zata iya jurewa ba,saboda qarfi da kukan nata ya fara yi.

Da kallo hafsat ta bisu har suka shige,tsinuwa da zagi kaka kala cikin zuciyarta akan widad din,sai data tabbatar sun shige din sannan ta matsa gaba inda abbas ke tsaye suna magana da rabi’u yaron gidan dake musu ‘yan aike aike da aikace aikace na filin gidan.

Hannunsa zube a aljihun wandonsa har ta qaraso Inda yake tsayen,musayar murmushi sukayi,wanda murmushin dake kan fuskar hafsat din tasa ma’anar ta dabance

“Sannu da qoqari madam” ya fadi har cikin ransa,don duk abinda je faruwa kan idanunsa ne yana gani,sai ta saki qaramin murmushi tana jin yadda zuciyarta keta mata ciwo

“Yauwa sannu,amma kaima ya kamata ka shiga ka bata baki fa,kuka taketa yi,abun tausayi” ta fada tana canza yanayin fuskarta zuwa kalar tausayin.

Da ido ya kalla sashen sannan ya maido kanta

“Tunda kin rarrasheta aikin wakilceni” wani sanyi yadan sauka a ranta,ta juya idonta kadan

“A’ah,ai matsayinka daban,inaga kaje din da kanka sai yafi” baice komai ba,sai ya kalla agogon hannunsa kawai sannan yace

“Zan dan fita,inajin zan iya kaiwa magariba kafin na dawo,rabi’u zai kawo cefene komai da komai,ki duba abinda babu saiki gaya masa ya hado dashi” fuskar ta a wadace da fara’a,duk da sanda take ita daya ba haka takeyi ba,duk sanda yace za’a kawo cefene cikin bacin rai take,saboda tasan yana buqatar sauyin abinci kenan,zai kuma yita mata tsirfar kala kalar girki,tafi jin dadi idan cefanensu ya qare,zata girka abinda duk ranta yakeso babu wahalar da kai.

Ita ta masa rakiya har bakin motarsa,ya shiga ya kunnata ya fice,ranta yayi mata dadi sosai,ganin ya share batun shiga sashenta

“Wannan abun yana aiki,sai dan banzan wahala” ta fada a ranta,bata taba kawo zai fice bai shige ba,to amma auren soyayya ne kuwa hakan?,anya ba hadin hajiyar bane kamar yadda taketa jin qishin qishin tana qaryatawa?.

Duk yadda latifa tayi kan widad tayi shuru amma abun ya faskara,yadda suke hanya suna ta cin kwalta har zuwa garin kano,haka ta lafe cikin kujerun ta ta dinga rera kuka,tun tana zaune tana aikin lallashi harta haqura ta zuba mata idanu,sallah kawai ta tashi tayi ta koma fa kwanta taci gaba da kukanta,koda latifan ta gama girkin rana wajen qarfe biyu da rabi na rana tayi mata maganar ta tashi taci qin tashi tayi,tayita lallabarta amma tayi funfurus,har akayi la’asar,ta sake lallabata amma taqi koda kallon abincin sai ruwan hawaye,bayan wasu mintuna ta gwada bata baki,saita tarar bacci yayi awon gaba da ita cikin kujerun

“Gwara ma kiyi baccin kya samu salama,wanann kuka haka?” Ta fada tana jin tausayinta cikin ranta,saita samu dama ta shirya abincin dare mai rai da lafiya,tunda bata ga alamun girki daga wajen hafsat ba,tunda rana ma da jama’ar kano suka tafi bata sake jin duriyarta ba,tana sanya ran a nan zaici abinci indai abun ya tafi kamar yadda yake a tsare a shari’a,don haka ta tsara abincin da kyau.

Dab da sallar magariba widad din ta motsa kadan,sai ta tsaya cak tana qarewa falon kallo tana daga kwance,kwanaki biyun nan mantawa take ba’a gida take ba,duk sanda tayi bacci ta farka saita zata zata farka ne ta ganta a dakin ummu.

Tuna komai da tayi cikin yinin yau sai ta fara tara sababbin hawaye,sannan ta miqe daga kwanciyar tana zuro qafafunta qasa,dai dai lokacin latifa ta fito daga daya dakin da ta zabi zama a ciki
“ai gwara da kika tashi,kwanciyar tayi yawa” ta fada tana qarasowa inda take zaunen,sai kuma ta dubeta

“Aah,kukan dai widad?,to kiyi haquri mana,tashi kiyi sallah kizo kici abinci” kamar jiran me tanka mata takeyi wasu sabbin hawayen suka fara sauka,da qyar latifa ta lallabata ta shiga bayinta ta dauro alwala tayi sallar,amma qememe taqi daukan abincin ko cokali daya taci,sai dan banzan kuka da takeyi,abinda ya daga hankalin latifa kenan,tayi lallashin duniya amma widad din taqiyin shuru,tana kuma tsoron kira mata ummu taje ta birkice mata fiye da yanzu,a haka suka zauna ta sakata gaba har aka idar da sallah isha’i.

Koda ya dawo a masallaci ya tsaya,sai da aka gama sallar isha’i sannan ya qaraso gidan,yau din shi daya ne,shi yayi driving abinsa,ya tsaida motar a parking lot na gidan ya kashe motar ya fito.

Tsayawa yayi yana duban sassan guda biyu,baisan yadda akeyi ba,baisan wanne zai shiga ba,tsahon wasu mintuna kafin ya zare hannayensa daga aljihu,ya soma takawa zuwa sassan hafsa,tunaninsa ya bashi ya fara da babba tukunna.

Yana tura qofar falon muryar mimi ya fara ji,sallamarsa ta ja hankalinsu,suka watsar da kayan wasan dake hannunsu suka nufoshi a guje,kowacce na kiran

“Daddy oyoyo” dukka su biyun ya hada ya rungume a jikinsa,yana kallon yadda sukayi fes dasu suka canza,da alama suna samun kulawa da tafi ta mahaifiyarsu

“Yaushe Kuka dawo?” Ya fad yana barewa nawwara chocolate

“Dazu anty maamaa ta dawo damu” dai dai sannan hafsat dake kitchen tana ta faman yadda zata hada masa abinci me kyau da zai janye hankalinsa ta fito.

“Sannu da zuwa” ta fada tana goge hannuwanta a jikin zanin jikinta,ya kalli zanin,kayan jikinta ne tun na safe,ya kuma tabbatar bata sake wani wankan ba,ya dauka zaiga canji ko yaya ne,amma ba wani abu daya canza,hatta da falonta a birkice yake,har da sauran maqalallun dattin yinin bikin da tayi da ba’a gama tsaftacewa ba,duk da haka ya danne shima,yana kallon yadda itama taketa qoqarin danne komai,duk kuwa da irin mugun baqin kishinta

“Yauwa madam,kun yini lafiya ya yara?” Ya fada yana kashe mata ido,saita dauke kai tana jin wani zafi a ranta,duk sanda ta tuna akwai wata cikin gidan fa wai itama matarsa ce,sai taji kamar ta shaqeshi

“Lafiya qalau” ta bashi amsa a gajarce tana nufar kitchen din

“Bari na kawo maka abinci” ajjiye nawwara ya fara qoqarin yi,shekaru kusan bakwai ta kasa haddace me dame yakeso idan ya dawo

“Noo,zan fara zuwa nayi wanka tukunna,kin kunna min heater dinne?” Da zaiyiwu ashar ya kamata ta qunduma,saidai tasan ko giyar wake tasha wannan shine kuskure mafi muni da zata aikata,me yakeson maidata?, baiwa?,wai da wanne ma zata ji?,da hidimar yara ko da ta kitchen ko kuma da tasa hidimar?

“Ban kunna ba,banma shiga sashen ba yau kwata kwata” kai yadan kada,yanzun kenan yadda ya baro sashen haka zai koma ya tadda shi,babu shara ba komai,duk da cewa dama ya saba da hakan,sai ya sake kada kansa yana nufar qofa

“Okay,ki shirya abincin,sai ki shiga ki kira qanwar taki kafin na fito” da harara ta bishi,sai taja tsaki bayan ya fice

“To ubana,ga jaka tayi mata girki ko?” Buguzum buguzum tayi hanyar kitchen din tana mita hade da bala’i kamar zata fashe

“Ni gaskiya na gaji,na gaji wallahi,dama hausawa sunce abun aro baya rufe katara,wannan attitude din dana ara ya fara isata,pretending din ya fara kaini bango” ta qarashe fada tana jan kwanon data gama hada coleslaw,bata kula ba santsi yasa ya subuce a hannunta ya fadi qasa ya tarwatse,abinda ke ciki yayi nasa guri

“Innalillahi,kai jama’a” ta fada qwalla na cika idanunta,sai gasu kuwa sun gangaro,ta duqa a wajen ta fashe da kuka,dukka yaran da suka biyota sai sukayi carko carko suna kallonta.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
[3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button