Alqiblq Hausa Novel
23/10/2021, 08:34 – Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
23/10/2021, 08:35 – ๐๐ป๐๐ป: *ALKIBLA*
_(THE BATTLE OF LOVE)_
*_HUGUMA_*
01
*_Da sunan Allah mai rahama mai jin ฦai_*
*dukkan godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bamu aron rai da lafiya,tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu annabi muhammad S A W*
*_littafin ALฦIBLA,labari ne dana qirqeshi mafi rinjaye kan soyayya,saidai kuma hausawa sukance ba’a rasa nono a ruga,akwai wani sashe na matsalolin da mafi yawan ‘yammata ke fuskanta a wannan zamanin game da samarinsu,wanda kusan basu san daga inda matsalar take ba_*
_a wannan karon ina neman afuwan masu karatu,littafin alqibla bazai kai yawan littafin siradin rayuwa ko alqawarin Allah,saidai ina fatan zai nishadantar ya kuma qayatar daku in sha Allah,ASHA KARATU LAFIYA_
*ALLAH YAYI RUQO DA HANNAYENMU๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ*
โ๐พโ๐พ *KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA*โ๐พโ๐พโ๐พ
____________________________
*GOVERNMENT GIRLS UNITY COLLAGE KACHAKO*
Makekiyar harabar makarantar ‘yammatan ta kwana dake garin kachako wato government girls unity collage cike take da dandazon al’umma,wanda mafi akasarinsu dalibanta ne,da kuma wasu daga cikin iyayen yaran dake ta faman qoqari dakai kawon kwashe yaransu zuwa gidajensu don gabatar da hutun zangon karatu na uku wato third semester.
Daga can gefe daya na harabar makarantar kana iya hangen yadda matashiyar ke tsaye goye da hannayenta sanye cikin wankakku kuma gogaggun unifoarm da suka amsheta sosai,ta zubawa harabar makarantar tasu idanu,kamar wadda aka baiwa aikin qididdige yawan al’ummar dake karakaina a wajen,kyakkyawar fuskarta babu alamun fara’a ko kadan.
Duk da cewa duka duka shekarunta ba zasu haura goma sha biyar ba,amma kana iya tantance kyan zubi diri gami da siffa da Allah ya bata.
Mai matsakaicin tsaho ce,ma’abociyar doguwar fuska da fata wadda bata cika haske ko duhu ba,ta yadda ba zaka iya kiranta da baqa ba,hakanan ba zaka kirata fara kai tsaye ba,tana da manyan idanu wanda ba’a fiya gane girmansu ba idan ba budesu tayi sosai ba duk sadda taso hakan,daga cikar girarta kawai zai gaya maka tana da yalwar gashin kai,Allah ya yi mata ado da dimple guda biyu a kumatunta hagu da dama,wadanda sukan bayyana duk sanda ta bude baki da niyyar magana,walau tayin ko bata yi ba.
Sake gyara tsaiwarta tayi idanunta na tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga xuba ba amma duba daya zakayi mata ka gane hakan,iya damuwa ta damu ta kuma matsu,burinta kawai ta ganta a gida,Tana da burin son ganin mutane a rayuwarta da suke da gurbi na musamman a zuciyarta,duk da cewa ta rasa babban bango kuma jigo a rayuwarta,amma duk da haka bata rasa wasu daka iya xama makwafinsa ba bawai madadi ba.
Abinda ya qara mata zaquwa da son ficewa daga makarantar tunda wurwuri kamar sauran dalibai shine,komawar ‘yar uwa kuma qawa a wajenta gida tun lokacin yin hutu da fitar dalibai baiyi ba,sakamakon lalura data sameta,wadda ta tilasta aka maidata gida,banda haka,bata da wata damuwa mai yawa kan jimawar tata.
“Fatima sa’id dabo,fatima sa’id dabo” daga bayanta taji ana kwarara kiran sunanta,a nutse ta waiwaya tana duban mai kiran nata,daya daga cikin ‘yan ajinsu ce ladifa hamza,ci gaba tayi da dubanta har ta iso dab da ita
“Anzo daukarki,tun dazu ‘yan gidanku ke nemanki” da mamaki ta maida dubanta farfajiyar da take tsayen sannan ta dawo da dubanta kan ladifa,tayi tsammanin inda ta tsaya din zata iya ganin shigowar motar da tazo daukar nata,bata tanka ba saita fara takawa kawai don barin wajen,ladifa ta rufa mata baya tana tsokanarta kan rashin kuzarinta,da yadda ta zama wani sukuku kamar ba ita ba tun tafiyar munira gida ta barta.
Tunga taja ta tsaya lokacin data kusa isa dab da motar da akace tazo daukarta din,mamaki bayyane qarara a fuskarta,wannan ba daya daga cikin motocin gidansu bane,duk wani ahali na gidansu yasan wannan motar waye,ya kuma san da zaman motar,yaushe yazo?,ya akayi ya yarda ya bada motar a daukota?,shine da kanshi?,saita girgiza kanta da sauri,bashi bane,don ko a mafarki tasan bazai taba zuwa daukar wani daga cikinsu ba.
Murfin motar da aka bude yasa ta maida hankalinta sosai ga motar,wani matashin saurayi ne ya fito,wanda dukka a qalla shekarun haihuwarsa ba zasu rufa ashirin da biyar zuwa da shida ba
“Ko baki shirya komawa gidan bane?” Ya dan daga murya yana fadi idanunsa a kanta,hakanan fuskarsa babu yabo ba fallasa,kai ta kada tana son tambayarsa da yaren kurame kan shi da waye sukazo?,saidai bata kai ga tambayar ba murfin sit din baya ya bude shima,wata matashiyar ta sake fitowa,wadda a qiyasce suna iya yin shekaru daya da ita,fuskarta washe da fara’a tana duban zahra dake tsaye.
“Suprise ko?” Matashiyar ta fada cikin sautin qyalqyala dariya,ba tare data shirya ba itama qaramar dariya mai qaramin sauti ya kubce mata,wadda hakan ya baiwa dimple din dake kumatunta damar bayyana,sa’annan kamar wadda aka qarawa qaimi ta doshi motar,tunda taga hafsat cikin motar ta tabbatar ba abinda take zargi bane
“Wallahi kun shammaceni,na farko na zaci daga gidan abban gwammaja za’azo daukana shi yasa na zauna jiran motar gidan,na biyu kuma saina ganku anan,ya akayi haka…?” Cikin dariya hafsat tace
“Shigo daga ciki kisha labari….dama naci alwashin koda gold akayi motar nan saina shigeta ai”
“Mayya….saida kika shiga din kuwa” zahra ta fada tana dariya
“Sarakan surutu…zaki kama mata sauran kayan ku shige mu tafi ko kuwa har sai lokacin da ya diba mana ya cika bamu koma ba?” Cewar daya matashin saurayin dake a mazaunin driver,cikin shadda dinkin zamani.
Leqensa zahra tayi ta window,saita fashe da dariya tana cewa
“Wai,congratumatur ya musty…..yaudai an dana,kaga ko yadda motar tama kyau kamar taka?,anya ba zakayi ratse ba kaje kadanyi shawagi ka dawo ba?” Murmushi mai kama da dariya shima ya saki yana cewa
“Bari kawai…..don dai kawai nasan yana sane da lokacin daya bamu ne,wallahi yau da sai na tsatse motar nan son raina…ke kinga yadda ‘yammatan makarantar nan ke wani kallona…..”
“Basusan duk bige bane baba” zahra ta fada tana qyalqyalewa da dariya gamida shigewa gidan baya,ya soma qoqarin tada motar bayan duk sun rufe murafun yana cewa
“Aina miki dare xakimin rana,tunda na kankaroki nazo daukarki a wannan dalleliyar motar ba”langabar dakai tayi ta koma kalar tausayi
“Haba ya musti,ni dakai fa bata baci,kada kasa ‘yan uba suyi mana dariya”
“Dariya kuma ta nawa?” Wancan saurayin dake daya site din ya fada yana sake kwanciya sosai jikin kujerar motar
“Kaji ko?” Zahra ta fada tana bata fuska
“Rabu dashi,duka adawa ce,ba wanda zai ganmu a rana” mustapha ya fada yana harar shamsu dake gefansa zaune,wanda bai sake tankawa ba ya yamutsa fuska kawai gami da cewa
“Oho dai,maji ma gani”.
Kusan wannan ‘yar tsamar ba wani sabon abu bane a wajensu,sun riga da sun saba da hakan,wanda ba komai bane ya kawo haka ba face fahimtar juna da sabo dake tsakaninsu,duk da cewa akwai banbancin iyaye,duka sun fito daga mahaifa daban daban.
Saida suka hau titi sosai sannan ta gyara xama tana duban hafsat
“Wai ya akayi ne haka?” Dariya hafsat tayi kafin tace
“Wallahi ya hajja ce tace ya bada a daukoki,da yaqi ma tace to bari ta kira mas’udu ya bada tashi tunda shi ta isa dashi,to sai da yaji haka sannan ya bayar……zahra ma tana kusa sai data saka baki” tabe baki zahra tayi tana juyar da kanta xuwa window,tadan dubi titi kadan sannan ta dawo da dubanta ga hafsat
“Sai kace xai mani gafara motarma sai an roqeshi,ni wallahi ya hajja data sani bata roqa ba…..bama wannan ba,na dawo hutu da farinciki da burin samun sake,musha soyayyarmu nida hafiz,zuwansa nasan komai saiya rushe wallahi,babu wani sauran sake,bayan shi har gida ake biyoshi,ya kuma baje kolin soyayyarshi babu jin kunyar kowa,amma mu ya hanamu katabus babu gaira babu dalili,bayan yafi kowa sanin tsarin gidan,yanzu daka yi candy za’a zuba maka idanu ka kawo wanda zaka aura,idan babu ya zama jarraba,yanzun kuma kana tsaiwa dasu shiya hana ruwa gudu,haba” ta qarashe masifar dajan tsaki,dariya hafsat keyi abinta tana qarawa,kafin tace komai shamsu ya waiwayo yana dubanta
“Ke yarinyar nan da gaskene fa zaki qone tun kafin ki tafasa” hararar wasa ta jefa masa
“Saimu zauna ai ku jiqamu kusha,kunfi kowa daga murya idan bamu tsaida miji ba….”
“Meye a ciki,sadaka kawai zamu bada ku a masallacin malam ayuba” ya fada cikin shaqiyanci yana qyalqyalewa da dariya,wanda ya saka mustapha ya dara shima,baki ta tsuke ita kuwa kana tace
“Allah ya kiyaye ya sawwaqe,wuce nan wallahi”.
Da ire iren wadan nan hirarrakin suka ci gaba da tafiya cikin motar,tana tambayar hafsat wasu abubuwa da bata nan akayi,da kuma wadanda ta tafi ta bari,shamsu dai bai gaji da tsokanarta ba ya sake cewa
“Sai tambaya kamar makahon daya warke daga makanta,kamar wadda aka sallamo daga gidan yari” fuska ta narke wanda da alamu lokaci zuwa lokaci tana da dabi’ar shagwaba wanda batasan ita kanta tana dashi ba,kusan a jininta abun yake
“To ya shamsu don Allah meye maraba,kowa an barshi yana jeka ka dawo amma ni an turani boarding saboda shawarar da wannan mutumin ya bada,kuma wai aka amince masa”
“To ya za’ayi sai haquri,kinsan shi,idan ya kafe akan abu,amma kuma da wuya idan ya kafe din a kasa ganin alfanun hakan” baki ta zumburo tana mita
“Kaidai kawai kana goyuwa da bayanshi ne a fakaice”
“Ko kadan,ke dince kin fiya qorafi a kan lamuransa,bayan dukka mun riga mun saba da halayyarsa”
“Ai shikenan” kawai ta fadi,don batason zancan yayi nisa,saita kamowa hafsat wani zancan suka shiga.
Tafiyar a qalla awa daya harda wasu mintuna masu dan dama a kai suka isa unguwar gadon qadon qaya dake qwaryar birnin kano,bakin wani gida mai manyan kagantu tsaho da kuma fadi suka tsaya,wanda kallo daya zaka masa tun daga waje kasan cewa ba mace ko mutum daya zuwa biyu bane kawai ke zaune cikin gidan.
Zaka sake gasgata hakan lokacin da gate din gidan ya bude motarsu ta kunnu xuwa ciki,sassane daban daban qunshe cikin gidan,a qalla akwai sashe hudu zuwa biyar,kowanne na mazaunin gida mai xaman kanshi.
Kamar mai jira,tun kafin ya kammala daidaita tsaiwar motar ta balle murfin motar ta kwasa da gudu tamkar qaramar yarinya ta nufi daya daga cikin gine ginen dake tsakiyar gidan,madaidaicin gini guda daya dake hannun dama.
Baki dukka suka sake suna dubanta,duk da cewa sun sani ba tun yau ba halin xahra din na daban ne,quruciya da rawar kai kamar bata qara komai cikin shekarunta.
Da sauri saurinta take kutsa kai zuwa sassan ‘yar tsohuwar,burinta kawai ta cimmata,don ba qaramar kewarta tayi ba,sabo da shaquwa ne mai yawa tsakaninsu,wanda babu makamancin irin wannan tsakaninta da kowanne jika nata koma bayan zahrar.
‘Yar kyakkyawar dattijuwa tsaye gaban freezer tana yunqurin ciro wani abu tana magana da wata matashiyar budurwa dake xaune kan daya daga cikin kujerun falon sanye da hijabi mai hannu kalar blueblack,kallo daya zaka mata kasan shekaru sun fara tura mata,saidai yanayin tsafta da son gayu irin nata ya qawata tsufan nata sosai,don kana iya hangen ragowar jan lalle dake qafarta wanda bai gama fita ba,da tajajjiyar sumarta dake cikin dankwali,wadda ke cike da furfura,saidai kuma awanke take fes cikin tsafta da tsari,sam bata lura da shigowar xahra cikin falon ba sai sautin muryarta daya karade ilahirin falon.
“Hajja!” ta fada cikin nuna zallar farinciki tana nufarta,kafin takai ga juyowa tuni zahran ta isa gareta,ta kuma cukuikuyeta gami da rungumeta tsam ta baya tana dan tsalle
“Yan makaranta….barka,barka” ta fada fuskarta na fadada da fara’a,wanda ke bayyana farincikin dake cikin zuciyarta,yake kuma alamta tarin qaunar dake tsakaninsu
“I miss you my hajja” zahran ya fada tana dariyar farinciki
“A’ah,sauya harshe dai,ni ba gane wannan surkullen naku nake ba,yanzu yayanku ya gama nashi ya fita” dariya zahran ta saki tana sakin tsohuwar,saidai sautin ‘yar dariyar da taji daga gefanta yana hankalinta ya kuma hanata furta abinda tayi niyyar fada din,ta waiwaya tana duban sashen.
Kusan a tare suka sakarwa junansu murmushi
“Kicemin keda kishiyarki ne hajja……anty takwara ina yini” ta fada tana qarasawa inda matashiyar ke zaune,wadda fuskarta ke fadade da fara’a tana duban zahran gami da gyara mata wajen xama ta hanyar tattare hijabinta zuwa jikinta ta duban zahran itama
“Lafiya lau takwara…..ya makaranta?”
“Alhamdulillahi….gamu yau mun samu ‘yanci”
“Aikuwa dai kam,gida akwai dadi” daga haka ta maida dubanta ga ya hajja wacce ta samu waje ta zauna
“Hajjata….me dame aka tanadarmin?” Tayi maganar a shagwabe kamar yadda ta saba
“Duk abinda takwarata keso” hajjan ta fada tana dariya,qaramin tsalle najin dadi ta doka ta fada saman kujera tana cewa
“Allah yabarmin hajjata”
“Eh qwarai,kafin ki shukamin wata tsiyar taki ba” da sauri zahra tadan bata rai tana wulqita idanu,kana ta maida dubanta ga hajjan
“Haba hajja….Allah yasa ba gaban ‘yan adawa kika fada ba,da kin saka sunmin dariya,musamman su o’o” ta fada tana dan satar kallon zahra.
Sarai zahran ta fahimci wa take nufi,saita murmusa tana qunshe dariyarta gami da girgiza kai,kasancewarta mai sauqi da sanyin hali,marason yawan magana da rashin daukar al’amura da zafi
“Inna wuro….inna wuro rigima” ta ambaceta da sunan da yawanci akafi kiranta dashi cikin gidan,saita waiwaya tana duban zahran
“Eh ai nasan kin fahimta…..don nasan bakison laifinsa” ta fada tana sake bata fuska kamar wadda aka zaga,hakan ya sanya zahra yin dariya dole tana kada kai cikin jin nauyin ya hajja dake zaune a wajen.
“Sarkin neman magana,idan ya jiki kuma ya hukuntaki kice wani abu daban,shin kin shiga ma cikin gidan ma kin gaisa da mutane ko kuwa kkka zauna neman magana….” Kafin xahran ta baiwa hajja amsa hayaniyar ‘yammatan gidan ta soma dosowa falon
“Tofa,Allahumma salli ala,aikin dawo,yanzu zaku taru ku dinga hanani sakat,sauqin abunma dodonku yana gari shima”
“Ni wallahi hajja ki dinga hanashi zuwa duk sanda zanzo hutu,tsakani da Allah fa hanani sakewa yake,hutun wata daya kacal din da nake samu saina qareshi cikin rashin jin dadi” baki hajjan ta kama tana dubanta,ta rasa wanne irin abune haka irin na zahran,qara kusantowar hayaniyar tasu alamun suna bakin falon yasa ta dauke kai ba tare da tace komai ba har suka qaraso cikin falon riqe da hannuwan jakankunan zahra guda biyu,wanda ta barsu a farfajiyar gidan bata samu daukosu ba saboda tsabar zumudi.
Kyawawan matasan ‘yammata su biyar rigis sanye da unifoarm,wanda yafi kama da unifoarm din islamiyya,hudu daga cikinsu farare ne ba kamar kalar fatar zahran ba,yayin da daya ce kawai ta dauki kalar fatar zahra,dukkaninsu shekarunsu ba zasu wuce suma sha shida sha biyar din ba,saidai duk wadda ka kalla a cikinsu a ganin farko xaka tabbatar basu kama qafar zahra wajen kyau da zubi ba,duk da cewa babu mummuna duk cikinsu,kowacce da irin nata kyan,amma saiya zamana zahran ta zama zahara sosai a cikinsu.
Wani ihun murnar ganin juna suka saki kowacce na neman wajen zama
“Kai amma naji dadin dawowarkin nan wallahi,kinxo akan gaba” salma daya daga cikin ‘yammatan ta fada,harara yusra ta jefa mata daya daga cikin fararen ‘yammatan
“Eheen,kedai kin shiga uku wallahi”
“Ke kuma fa,tara kika shiga?” Salma ta fada itama tana maidawa yusra hararta duk da cewa mai kama da dariya dariya ce
“Kinga manta da ita,bani nasha ya akayi?”
“Bari mu saka labule tukunna saboda ‘yan saka eyes…..”
“Kunga ku tashi ku bani waje tun ban kira yayanku ba” hajja ta fada saboda sanin hali,ta sani sarai labarin nasu baya wuce na samarinsu shi yasa tayi musu haka,sosai suke wasan jika da kaka da ita,tun tana fada da fushi harta haqura ta qyalesu ta zubawa sarautar Allah idanu,harya zamana ma yanzu bata damuwa ya zame mata jiki,mutum daya ne tak da idan yana nan take samun salama,saboda dukkaninsu shakkarsa suke,kuma tsoron hukuncinsa suke.
“Idan wajen mama zaki don Allah ya zahra kice mata yanzu zan shigo na mata bayanin aiken” yusra ta fada tana duban zahra wadda ta miqe da wayarta a hannu tana murmushi
“Bafa can zata ba” hafsat wadda ta shigo daga qarshe ta fada
“Kema ai tunda kika ga ta miqe tana doka murmushi ai kinsan kwanan zancan” hafsat ta sake fada tana yin fuska,cikin dan jin kunya da nauyi zahra tace
“Kamar a kunnenshi kika fada” saita soma yin gaba cikin sauri sauri yayin da hafsat ta bita da magiyar ta tuba tayi haquri ta fice abinta tana dariya.
“Ni ina mamakin yadda soyayya ke gudana tsakanin yaya da yaa zahra”
“Ahto ai haka Allah ke lamarinsa,ku kuke masa wani kallo da bahagon hukunci,saboda ALฦIBLARKU ta bambanta ta wajen ra’ayi,kowanne bawa komai irin halinsa akwai yadda Allah ya sallada wanda zai iya zama dashi ya kuma rayu dashi”.
Tsam zahra ta miqe tana maida hijabin unifoarm din jikinta,wanda har yanzu bata kai ga cirewa ba tana cewa
“Bari na shiga ciki kan ku gama lacture din” don sam bata son irin wannan dogon sharhin na hajja,gani take koda yaushe aikinta shine bashi kariya dason wankeshi a idanunsu,bagan sun riga dasun gama sanin halayyarsa ciki da waje,kuma kowacce cikinsu ta kwana da sanin wannan,so tana ganin babu buqatar dagiya wajen bashi kariya da yima halayyarsa kwaskwarima a tsakaninsu.
Kamar hajjan zatayi magana sai kuma tayi shuru kawai ta bi zahran da kallo sanda take ficewa daga falon abinta ko a jikinta,har takai bakin qofa saita dakata
“Don Allah hajja wayata,tunda na dawo nake jina ba dai dai ba,na tabbata nuruddeen nacan yana nemana wallahi,tunda yasan yau zamu dawo” daquwa wannan karon ta watsa mata
“Qaniyarki,yanzu nake muku nasiha kika tashi kika barni zaune wajen,shine yanzu kikeso naje na dauko miki waya,idan kin damu ai kinsan mazaunarta kije ki dauko da kanki” dariya tayi cike da nishadi,ita da hajjan sun saba hakan,suyi tsiya suyi dadi,duk yadda suka kai ga shaquwa da juna amma indai akan irin wannan batunne sun saba haurawa,ita sam dole saita sanyata sun jitu da juna,ita kuma tana jin wannan shine abu na qarshe a rayuwarta da bazai taba yiwuwa ba,komai nasu yasha banbam,tun kan ta mallaki hankalin kanta yadda ya kamata ta fahimci alqiblarsu tasha banbam,hakan ya haifar da duk wani abu dake gudana a yanzu.
Kanta tsaye ta nufi dakin gadon ya hajjan,harta kusa sai kuma ta sauya akalarta zuwa kitchen dinta,inda take jin qamshin abinci na fitowa.
A nutse ta tura qofar tana wara idanu don ganin wace a kitchen,kamar kullum gaji ce,’yar aikin hajjan qwaya daya tilo data jima da ita,takun shigowarta ya sanyata waiwaya tana duban qofa,cikin fara’a da washe baki ta qarasa waiwayowa gaba daya
“A’ah,ashe kina hanya inna wuro…..marhaba da uwar dakina” murmushi zahra ta saki,saboda gaje ta wajenta ce sosai,yadda ya hajja ke ji da ita haka itama gaje ke ji da ita
“Yauwa inna gaje,na sameku lafiya”
“Lafiya qalau alhmdlh inna wuro,ya makaranta?”
“Mun gode Allah” zahra ta fada tana neman wajen zama saman kanta,kusa da wasu kwanuka data gani a rufe,hannu ta miqe tana shirin budewa gami da cewa
“Me aka tanadar mana haka yaketa zabga qamshi”
“Gasunan bude ki gani,duka naki ne hajja tace a yi miki” a nutse ta dinga budewa tana dubawa,sosai taji dadi har ranta,hakan kuma ya bayyana zuwa saman fuskarta,batun yau ba ta shaida da soyayyar da kakar tata ke mata,bata san me yasa ta fita daban cikin jikokinta ba,ko don sunanta taci?,ko kuma don ita din ita daya ce ta zama marainiya a cikin tarin jikokin hajjan?,saita ture wannan tunanin ta sanya hannu ta soma daukan abinda ke cikin kwanon tana sawa a bakinta.
Duk sai data gama dandanawa sannan ta fara lashe yatsunta tana cewa
“Ashe dai ‘yar tsohuwar nan na sona haka,bari naje cikin gida na gaida mutane inna gaje na dawo” ta fada tana ficewa da dan sauri saurinta ba tare data saurari abinda inna gajen ke cewa ba.
Sai data fara biyawa ta dakin ya hajjan ta dauko wayartata hade da charger,ta shiga dakinta dake sassan ya hajjan ta jona chargy sannan ta fito.
*MAMUHGHEE* _UBAIDMALEEK_
*BILLYN ABDUL*
_MAKAUNIYAR QADDARA_
*HAFSAT RANO*_MABUDIN ZUCIYA_
*MISS XOXO*_DALAAL_
*HUGUMA*_ALฦIBLA_
*ZAKU IYA BIYAN NAKU KUDIN TA WANNAN HANYAR*
ฦaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903ย 234ย 5899
23/10/2021, 08:35 – ๐๐ป๐๐ป: *KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA MALLAKARKI BANE*
02
Falon yanzu babu kowa duka sun yoye sai ya hajjan kawai,tana zaune tana gyara falle fallen littafin dala’ilu,da alama ta karantasu ne suka kuma hargitse mata take gyarawa,don ita din har tsufanta bai hanata bibiyar litattafan addini ba.
Ta baya ta rungumeta tana cewa
“Ashe dai har yanzu ana yi dani ‘yar tsohuwa mai ran qarfe,bari naje na dawo na kwashi gara,Allah dai ya jiqan tsohon mijinki” daga haka ta juya cikin sassarfa tana barin falon.
Wannan karonma da kallo ya hajjan ta bita,cikin ranta ta amsa addu’ar data yiwa mijinta kuma masoyinta,tana jin yarinyar cikin ranta sosai fiyr da sauran jikokinta,su biyu kacal suka samu irin wannan babban matsayin,duk da qoqarin boyewa da take da kuma nuna duka dai dai suke.
Tana yawan godiya ga Allah daya sanya qauna da zumunci mai qarfi tsakanin ahalinta,tun daga kan yaranta zuwa jikokinta,tsabar son su zamaTsintsiya madaurinki daya ya sanya tun mijinta na raye suka yanke zaman dukka yaransu maza tattare a waje daya,matanne basu da wannan ikon ko qarfin a kansu,hakan kuma yayi tasiri wajen sake maida zuri’ar tata tsintsiya madaurinki daya,duk da ance zaman tare zo mu zauna zo mu saba,hakanan baka rasa banbancin halaye da ra’ayi wanda kan kawo sabani lokaci zuwa lokaci,saidai a nata ahalin akwai qarancin hakan sosai,don bazai yiwu ace babu ba,kusan halayya ce tadan adam,kuma sunna ce ta zaman tare.
Duk da wannan babban abinda ke bata mamaki da daure mata kai shine rashin jituwar dake tsakanin zahran da yayanta,kusan abune daya dauko dogon tarihi ya kuma samo asali da tushe tun da dadewa,tun abun bai zama wani abun damuwa kallo ko dubayya ba har takai a yanzun yana damunta lokaci zuwa lokaci,saidai tana saka ran watarana komai zai zama tarihi,kamar akwai sauran quruciya ne jikin xahran.
Sashen yayan mahaifinta da suke kira da abba babba ta fara shiga,sashe ne mai kyau kamar yadda ainihin ginin gidan ya nuna,babban falo wanda ya cinye set din kujeru har guda biyu,dakuna a qasa kitchen da bandaki,sai dakunan matan gidan dake sama,duk da kowacce tana da guda daya a qasa.
Mommy ta tadda a falon ,wanda ke mazaunin amaryar abba babba tana cirewa yara da dawowarsu gidan kenan unifoarm,wanda dukkansu yaran gidan suna makaranta guda ne,akan daukosu tare a kuma kaisu tare,bisa jagorancin drivern gidan a wadatacciyar motar da aka ware musu don wannan hidimar.
Kanta ta daga tana amsa sallamarta sanda take cirewa yaronta safarshi,fuskarta fadade da fara’a tace
“Maraba da ‘yan boarding” qarasowa tayi tana murmushi,ta zauna hannun kujerar tana amsawa gami da yiwa mus’ab da ake cirewa safa tsiya
“Wai kai bakasan ka girma bane,saura kadan kayi shekara goma fa,amma har yanzu safa ake cire ma”
“Murmushi mommy ta saki
“Kema kya fada inna wuro,kullum sai an cire masa kamar yaron goye…” Dariya ta sakeyi tana kuma dan tsokanarsa kafin daga bisani ta juya tana gaida mommyn,fuska a sake take amsata,ta tambayi abba babba
“Abbanku ai kinsan ba zama,tun sassafe ya fita kasuwa”
“Mama fa?” (Uwar gidan mommy)
“Yau suna hidima ne,ita dinma tun dazu ta fice” jin haka yasa ta miqe tana zura hannu a aljihun rigarta,ta soma zaro alawa masu dan girma tana rabawa wadanda ta taras a falon,duk data girmesu amma ba wani girma ne me yawa can ba,shekarun data basun bazai gaza biyu zuwa uku ba,idan yayi yawa hudu
“Baki gajiya,keda kika dawo daga makaranta harda wata tsaraba” murmushi kawai ta yiwa mummyn tana ficewa.
Sashe na biyu ta shiga,sassan abba yusuf,wanda keda matan aure biyu shima da yara tara,amarya nada uku,uwargidan nada shida,shima dai kamar shigen ginin waccan sashen,komai cikin tsari,da alama kusan dabi’ar jama’ar gidan ce wato tsafta,su dinma faran faran suka gaisa ta wuce sashen abba abu wanda cikakken sunanshi shine abubakar,matarshi daya da yara bakwai,sai abban tsakiya shima matarshi daya,daga nan sai sashen mahaifinta.
Sashe ne dake da girma da qima a idanunta,yake kuma da dimbin tarihi cikin rayuwarta,sashen da a shekarun naya suka rayu kamar sauran sassa dake gidan,cikin walwala farinciki da qaunar juna,qarqashin inuwar adalin uba kuma mahaifi a wajenta,saidai ta farat daya mai rabawa ta raba mai raba soyayyar iyaye da ‘ya yansu wato mutuwa,a lokacin da suke tsaka da gudanar da rayuwarsu.
Mahaifinta uba ne da ya zama daya tamkar da dubu,wanda bashi yiwuwa ta manta soyayyarshi garesu,musamman ita din da take ‘yar fari a wajensa,ta kuma ci sunan mahaifiyarsa,saiya zamana soyayya da kulawar da yake bata ta dabance,har kullum mutuwarshi sabuwa ce a ranta,rana da lokacin basu taba bace mata ba daga idanunta.
A hankali tayi sallama cikin falon,qannenta dake xaune suna cin abincin rana suka amsa,cikin farinciki qauna irin ta ‘yan uwantaka suka miqe suna mata oyoyo,fuskarta washe da fara’a take amsa musu,wanda hayaniyarsu ta fito da mahaifiyarta dake kitchen.
Kyakkyawar mace mai kyan zubi da haiba,ma’abociyar tsafta nutsuwa da kyakkyawar dabi’a,wanda kyawun dabi’arta ya sanya koda bayan rasuwar mai gidanta dangin mijinta suka kasa rabuwa da ita,suka roqi alfarma taci gaba da xama dasu har zuwa sanda xata buqaci aure,su kuma zasu tsaya mata tamkar nata dangin.
Duk da cewa bata rasa wani gata ko kulawa daga nata dangin ba,amma hakan bai hanata amsar tayinsu ba,saboda tsantsar dattako irin na uwar mijinta,da yadda ta nuna mata qauna da kulawa tun haduwarsu har xuwa yau din,bugu da qari kuma,bata jin xata iya sake aure a sauran rayuwarta data rage,tunda ta rasa miji daya tamkar da dubu irin sa’id uban ‘ya’yanta.
A nutse ta qarasa daura da inda mahaifiyar tata ke zaune
“Ina wuni ummi”
“Lafiya qalau,ya makaranta ya kuka barosu”
“Lafiya lau ummi,wannan karon duka babu dadi,ni kadai aka bari a makaranta,yasira ta rigani dawowa” tana zare carbin hannunta ta amsa
“Eh ai jikin nata alhmdlh da sauqi,jiya na shiga na dubata” ajiyar zuciya tadan saki
“Tana raina ummi,gobe in sha Allahu nima zanje na dubata”
“Ya kamata kuwa,don dazu yaayan ma ya kirani yace an daukoki ko?”
“Eh su ya musty ne ma suka je a motar wancan mutumin” sosai ummin nata ta tsareta da idanu tana kallonta,sai a sannan ga gane tabargazar data tafka,saita dauke nata idanun tana son wayancewa
“Inna wuro?,waye wancan mutumin?,yayan naku?,ashe qara lalacewa kike?,duk fadan da nake miki bakiji kenan?” Marairaice mata tayi,don idan da sabo ta saba da fada daga wajen ummin indai a kanshi ne,abu na qarshe kuma data fi tsana kenan a rayuwarta
“Kiyi haquri ummi,mantawa nayi,bazan sake ba” kanta ta dauke kawai daga gareta,tasan ta fada ne kawai,amma wannan halayyar ta jima dason rabata da ita amma ta kasa,ta zame mata jiki,rabuwa da ita sai a hankali,bata tashi daga wajen ba sai data ji tace
“Allah ya kyauta,Allah ya rabaki da wannan halin”.
Dakinta dake sashen wanda ba kasafai ta fiya kwana a ciki ba ta wuce,tsaf yake kamar ko yaushe,duk da bata kwana ciki amma kullum saita gyarashi,’yar madaidaiciyat cupboard dinta ta bude,ta zabi kayan sawa adadin wanda takeso,ta debi kayan kwalliya mayafanta da sauran muhimman abubuwa don maidasu sassan hajja,saboda muddin ta dawo hutu tafi xama a can,bama ita kadai ba duka ‘yammatan gidan dakin dake sashen hajjan suke tarewa har sai ta koma.
Ita dinma tafison zaman can din,saboda tafi sakewa sosai fiye da sassansu,hajjan na barinta tayi yadda takeso koma bayan ummin nata dake da tsauri da kuma dokoki iri iri.
Kai tsaye ta koma sassan hajjan,duka sun fice da alama kowacce akwai abinda zatayi,hakan ya mata itama saboda wanka takesonyi ta kuma rama bashin baccin da batayi ba daren jiya a makaranta,don su kwana waqe waqe na murnar tafiya gida hutu,gabanin asuba koma kowa ya shiga sabgarsa taci gaba da hada kayansa da kuma bin layin wanka.
Sai data fara zuwa gun wayarta dake chargy,hopefully ta taba screen din ya kawo haske cikin zumudi,don ta tabbatar zata iske texs ko miscal na nuraddeen kamar yadda ya saba mata a kullum idan ta dawo hutu.
Saidai kuma ga tarin mamakinta babu kiran hakanan babu saqon nashi,sosai abun ya daure mata kai,amma saita bashi uzuri,ta shiga ta duba balance dinta.
Naira hamsin ce tayi ragowa a layin nata,ta tuna zahra takwararta ce ta mata transfer kyauta ana ya gobe xasu koma hutu,tunda tace ga wanda ya tura mata kudin ta raba musu 50/50 a ciki sai taji credit din bai burgeta ba,amma yanzun zai mata amfani,don haka kai tsaye ta shiga rubuto lambobin nuraddeen daka wanda ta jima da haddacesu ta danna kira,take sunan my happiness ya bayyana saman screen dinta,ta kalli sunan ta saki murmushi tana kuma sauraron yadda wayar ke ringing.
Dab da zata katse aka daga,sallama ya fara yi mata,saita sauke a jiyat zuciya cikin shagwaba tace
“Nayi fushi”
“Afuwa,kaina bisa wuyana,kina raina inata son na karki,damac ce ban samu ba”. Duk da uzuri ya nema amma sai taji banbarakwai,don wannan shine karon farko daya soma neman uzuri irin haka a wajenta,amma saita saki murmushi
“Nayi maka,amma fa lasam nayi kewarka da yawa”
“Nima haka princess,an dawo lafiya?”
“Lafiya qalau alhmdlh”
“Ya makarantar,ya mutan gidan?”
“Kowa lafiya lau” zai soma magana taji ana mata warning cewa kudinta sun kusa qarewa,daga bisani ta tambayeshi me yace
“Nace ne ina hajja da ummi”
“Duk lafiya na samesu…..” Ta kasa kunne taji yace xai shigo a yau din,saidai tuni kamfanin waya suka katse kiran saboda qarewar kudin wayar tata,saita aje wayar gefanta tana dan dubanta,tasan cewa babu jimawa xai biyo sawun kiran nata,don haka ta zauna daura da wayar tana dan gyaran kayanta tana dakon kiran.
Harta gama gyaran bataji shigowar kira ba,sai data miqe tana shirin shiga bandaki ta watsa ruwa taji sautin shigowar saqo,ta miqa hannu da hanzari tana dubawa,saqon daga nuradden dinne
“Zan kiraki” abinda ya qunsa kenan,saita maida wayar ta ajjiye ranta tana cewa
“Lallai yau wanne irin busy happiness ya shiga haka” ta wuce bandakin bayan ta daura towel din wanka.
Aqalla minti goma sha biyar ta shafe a bandakin sannan ta fito tana mita
“Haba,babu inda yakai gida dadi,me za’ayi da makarantar kwana,babu abinda yakai gida dadi wallahi,inda a school ne ina ka isa ka dade haka,da tuni an matsanta miki daki fito,mtseww…wallahi badan yaaya da kuma ummi da bazan koma ba” da wannan qananun mitocin mata ta qarasa gefan qatuwar kafitar dake dakin ta zauna,wanda daura da ita ‘yar drower ce dake jere da kayan shafe shafenta,zahra ba daga baya bace wajen son ado da kwalliya,hakanan idan ta fannin yawan sutura da kayan qyale qyalen rayuwa ne tana sahun gaba cikin ‘yammatan gidan,saboda ta kowanne fanni yi mata ake dalilin maraicinta,qannen mahaifiyarta mata da yayan mahaifiyar nata dake matuqar qaunarta,wanda dukkan abinda xaiwa yaransa to lallai fa saiya yiwa zahran,hakanan ‘yan uwan mahaifinta dake gidan,duk sanda wani xaima iyalinsa saiya hada da ita,ga hajja a gefe itama da ba’a barta a baya ba.
Sa’annan uwa uba wani irin farinjini da Allah ya yiwa zahran tun tana mitsitsiyarta,don mahaifanta ma sam basa yarda a karbi abun hannun kowa akan yarinyar,haka halittarta take,tun abun na baiwa mamanta mamaki harya koma bata tsoro,hakan ya sanya tun kan ta mallaki hankalinta ta tsaya kai da fata wajen mata addu’ar samun kariya da samun miji na gari,don ita kanta tasan Allah ya yiwa diyartata baiwar wani asirtaccen boyayyen kyau,tana tsoro n kada hakan ya zama wata sila da za’a shiga rayuwar diyartata a cutata mata babu dalili,ta sani cewa sautari baiwar kyau jarrabawa ce,qalilan ne kuma cikin mutane ke iya cinyeta,musamman mata.
A nutse ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar atamfa cotton mai budadden dinki,ta gyara kanta da ribbom wanda da wahala kaga kitso a kanta,duk wanda ya santa yasan bata qaunar kitso tun yarinta har zuwa yanzu data girma,duk sanda xa’a mata kitso saita tarawa mai kitson jama’a saboda tsabagen kuka,daya daga cikin abinda ya sake sawa basa jituwa da yayanta kenan,yana ganin kamar an bata ta ne an sangarta ta.
Tana tsaka da fesa turarenta mai sanyin qamshi wanda ta saba ta soma jiyo sautinsa.
Sassanyar murya mai zaqi,amma cike da kaushi da kuma fada yake magana,da alama wani abun ya faru ne,baki ta tabe tana aje turaren nata,maimakon ta fito yadda tayi niyya da farko sai kawai ta fasa,ta koma gefan katifar ta zauna tana sauraren fadan nashi,duk da cewa bata iya fuskantar me yake fada.
Baki ta sake tabewa karo na biyu
“Ayi mutum sai shegen kaushin hali da fushi,Allah ya kyauta” ta fada tana jawo filo bayan tayi rub da ciki saman katifar,sannan ta janyo wayarta tana sake duba kira ko saqon nuraddeen,saidai har yanzun babu ko daya,saita maida ta aje tana ayyanawa wala’alla bai gama uzurinsa bane.
Shigowar hafsat dakin kamar wadda aka tunkudo ya sanyata miqewa ta xauna,fuskarta a hade da alamun kamar ma hawaye ta gama yi
“Yaya?” Zahra ta jefa mata tambayar tana gyara zamanta idanunta kan hafsan
“Yaa haidar mana……shikenan da zarar ya dawo mutum bashi da sauran sakewa,kome kayi baka masa dai dai ba,haba?” Koda bata tambaya ba tasan kwanan zancen,don halayyarshi ba baquwar halayya bace a wajensu,don haka baki ta tabe
“Hmmmm,ai ni shi yasa nake godewa Allah dasu abba basu dauko aqidar sai munyi karatu ba kafin aure,inda haka ne Allah kafin mubar gidan nan saiya sa mana hawan jini” dubanta hafsa tayi
“Ni kuma kinsan hakan baimun ba,nafison naci gaba da karatu kafin ayimin aure,inda xasu sauya shawara wallahi hakan yafimin,amma ya haidar kusan yafi kowa na’am da wannan tsarin tun xamanin su ya khairiyya” hararara zahra ta jefeta dashi tana cewa
“Bakinki ya sari danyan kashi,ni da kike gani na nan ba’a da candy qalilan ce inji ‘yan arabiyya,babu wani karatu da xan tsaya wahal da kaina inayi,me yafi aure dadi?,kaida masoyinka?,ka samu ‘yanci babu me takuraka?,tabdijan,ke ai saikita zama kici takarda da biron” ta fada tana komawa zuwa kwanciyarta ta daxun.
Dariya hafsa ta saki tana daka mata duka,tana sane ta sako wannan zancan,don duk cikinsu kowa ya san ra’ayin mahaifansu ya dace da ra’ayin zahran,kuma ita hakan yayi mata dai dai
“Allah ya shiryeki zahra”
“Amin….ai dan sunna bayaqi sunna ba ko”
“Wannan haka yake malamarmu”
“Kyaji dashi” ta amsa mata tana sake jawo wayarta ta fara buga game,jifa jifa suna hira,tana kuma dakon daina jin motsinsa a falon hajjan data samu ta fita taci wani abun kafin ta dawo ta kwanta tadan matse gajiya.
23/10/2021, 08:36 – ๐๐ป๐๐ป: *KIJI TSORON ALLAHโ๐พ,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
03
Kusan minti talatin kafin ta daina jin duriyarsa,zuwa sannan bacci ya soma fisgar hafsat,saita aje wayarta ta miqe a hankali tana gyara daurin dankwalin kanta,ta isa bakin qofar dakinta ta zura takalmanta sannan ta wuce kai tsaye zuwa falon.
Kyakkyawan matashin saurayin da a qalla bazai wuce shekara talatin bane zaune cikin falon,saman lallausan center carfet din dake shimfide tsakiyar kujerun,ya miqe dogayen qafafunsa ya kuma hardesu waje daya yana kadasu a hankali,kallon farko da zakayi masa zaka fahimci wani irin kwarjini shimfide saman fuskarsa,wanda ke cakude da rashin fara’a da kuma daurewar fuska,wanda ko a yanzun da yake zaune shi kadai cikin falon wayarshi qirar iphone 12 na tsakiyar tafukan hannayenshi dake saman cinyoyinsa yana amfani da ita fuskarshi a hade take,da alama gwanin iya tsare gida ne qwarai,gefansa kwanukan abinci ne a jere,bata sani ba ci zaiyi ko kuma baida niyyar ci ya ajesu ne kuma baxai magantu yace azo a dauke ba.
Kallo daya tayi masa ta tabe baki,duk da bata samu nasarar ganin fuskarsa ba sai sumarshi dake gyare,ita bamai yawa ba ba kuma saisaye ba,saidai tafi kama da saisayen irin sama saman nan,tayi wani spring kamar zubin indomie,baqa sidik tana sheqi,da alama ana bata kulawa yadda ya kamata,don ba qaramin qara masa kyau da kwarjini takeyi ba,ta kuma dace da kalar kwantacciyar skin dinshi da hausawa ke cewa wankan tarwada,ga duk wanda ya dubeta yasan ya samu cikakken hutu dajin dadi,duk da kalar aikinsa bawai na hutawa bane waje daya,saboda aikine na hidimtawa qasa,da bada kariya da tsaro wa dukiyar al’umma da rayukansu.
Saษaf saษaf take tafiya saboda bata da buqatar ya ganta,dab da zata gotashi ya daga kanshi,saida gabanta yayi mummunar faduwa,kallo daya tak ya mata ya maida kanshi ga wayarshi,kamar baisan Allah yayi wanzuwar wata halitta ba,tilas ta fasa qudurinta na wuceshi da tayi niyya,ta dawo da baya
“Ina yini yaa haidar” kamar bai jita ba,hakan ya bala’in ษata ranta,ta tsani wannam halayyar tasa fiye da kowacce,ita idan zai shekara zaune a waje baiyi magana ba ba damuwarta bane,amma don me mutum zai gaidashi ya watsar.
Ganin bai amsa ba ya sanyata miqewa donta wuce abinta,sai a sannan ya magantu
“Lafiya…..zoki zubamin” ya fada ba tare da ษago daga duban wayarshi ba yana mata nuni da fulasan gefansa.
Kamar tayi tsako don takaici amma tasan bata isa ba,wato saboda tsabar izza yana jiran wanda zai zuba mishi ne,akan ya zuba da kansa ya gwammaci yayita jira har sai mai zuba masan yazo,laifin bana kowa bane saina zahra,ita ta batashi,don tana fara zuba abincin ta tabbatar girkin ma nata ne,ita ta dafa mishi.
Tana wannan tunanin zucin naman data debo a serving spoon daya ya subuce ya koma cikin miyar,take ta fantsamo man dake saman miyar,ya kuma samu kyakkyawan masauki saman farar shirt din dake jikinsa.
Da sauri ya daga kai daga danna wayar da yakeyi,ya dubi jikinsa sannan ya maida idanunsa saman fuskarta,zallar bacin rai ta hanga qarara,ta soma motsa baki da niyyar yi masa bayani saidai ya rigata magantuwa
“U r very stupid….baki da hankali ne?….”
“Ashsha…..inna wuro garin ฦaฦa?” Muryar hajja ta ratso falon,duk rashin tsoronta amma sai da taji kamar anyi mata rahama,kafin ta bata amsa ta iso
“Tashi maza ki samo omo da dan toli fefa a goge mishi” tsaki ya saki kawai yana miqewa,ba tare da yace da kowa komai ba ya soma takawa yana nufar qofar fita
“Ka tsaya a goge maka mana zaki(haka takan kirashi dashi ita da wasu mutanen,sakamakon sunan mijinta da yaci,bata iya kiran sunanshi)”
“No,barshi kawai”
“Abincin fa?” Ta fada sanda yake gab da ficewa
“Ku amfaneshi”ya amsa a taqaice yana qarasa ficewa.
Bugu hajja ta kaiwa zahra wadda ke tsaye tana yiwa qeyarsa gwalo gamida murguษe murguษen rawa
“Ja’irah,hala kina sane ko?” Dariya ta saki tana zama gurbin daya tashi,wanda ke fidda qamshin turarensa ta soma sake bude kwanukan tana baiwa hajja amsa
“Inda ina sane ai da sai abun yafi haka…..arashi aka samu,kuma hakan yamin dai dai”
“Zahra….zahra….kinga ki fita daga idona akan yayanku,kamar ba jininku daya ba”
“To hajja ko kinfi sonsa yanzu a kaina ne?,babu inda nake sakewa fa sai nan,haka kawai sai nan dinma yazo ya zauna ya hanamu sakewa,idan na koma wajen ummi canma yana nan,da nayi wani abu itama ta hauni da fada itama,don ya girmemu kawai saiya damemu” daga haka ta jawo fulasan tahau zubin abinci Abinta tabar hajja da kallon ikon Allah”
“Allah ya shirya” hajjan tace tana sauke ajiyar zuciya kawai,bata amsa mata ba taci gaba da zurin abincinta.
Salma ce tayi sallama cikin falon tana tsaka da cin abincin,sanye da atamfa dinkin A shape,sai dan kwalinta data zarga a kanta,hannunta riqe da qaramar wayarta me keyboard itel,wanda akafi kira da rakani kashi,kusan dukka gidan zahra ce me waya torching,ita dinma sai da aka hau rimin gafiya kafin a samu lamuncewar oga kwata kwata haidar ya barta da wayar,a hakanma bisa goyon bayan hajja,saboda abban gwammaja ne ya kawo mata,ita kuma tace sam ba za’a watsa masa qasa a idanu ba,tunda wayar bawai wata babba bace can,sannan uwa uba an hanata walwala an dauketa an kaita makarantar kwana aiko ba’a hanata riqe waya ba a duk sanda tazo hutu,tunda hutun ai baya wuce wata guda kacal,uwa uba kuma ma rashin riqe wayar yafi riqeta yawa,hakan yasa dole aka barta da abarta.
“Lalalaaaa……lallai zahra…..wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin hadawa yaa haidar abinci bane?” Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta dubeta
“Sune mana….kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki” kamar wadda ta danawa wuta a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido
“Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka”
“Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari” cewar hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki
“Ko iya haka ma alhmdlh” dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta
“Daษina dake hajja baki iya samun magana daya ba…..muje sister ki bani labarin daxu”
“Zakici ฦaniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki” ta fuskanci sarai me take nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin ฦarshe sai tafi kowa mita da jin ciwon hukuncin da za’a matan.
Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan
“Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci” ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane salma
“Ki saurara min ‘yar baqincikin baccin mutum” daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
“Wai kinsan meke faruwa kuwa?”
“A’ah saikin fada” inji zahra
“Sabon kamu fa nayi” sosai zahra ta maida kallonta ga salma
“Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?” Farr tayi da idanunta
“Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman” idanu dukka zahra ta fiddo waje
“Keee salma…..kiji tsoron Allah,sulaiman din?” Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta
“Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?” Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami
“Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba”.
Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban zahra
“Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata…..idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba’a samun wanda hakan bane…..amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha’inta ne,basu da *ALฦIBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba…..na shafa rana guda naji wayam” ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.
Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma ‘yar tamore
“Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba” zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
“Eh….kekam taki zuciyar na daษe da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan” kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu ga musu.
Saidai basu ja da yawa ba dakin ya soma cika da ‘yammata,hakan ya sauya akalar hira suka shiga hirar sabgogin da suka shafesu,kamar qawayensu na unguwar dana islamiyya wadanda aka kawowa kudi da wadanda aka sawa rana,jarrabawar qualifying da suke fuskantarta,candy da zasuyi nan gaba da kuma aurensu da sauran hirarraki da ba’a raba ‘yammata dasu.
Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana tsumayin nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda lokacin ษora girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai masu aiki ษai ษai a kowanne sashe amma ba’a barsu sun zauna sun ta’allaqa komai a kansu ba,babu nuradden ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura mata updated watsapp,don nata yayi expair.
Ci gaba da hayaniyarsu ta hira suke har suka zo zasu gifta ta ma’ajiyar motocin gidan.
Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu wanda bai ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da rage sautin muryarta.
Sanye yake da wata farar riga ฦal me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa murษaษษen dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa da iska ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma wanka yaje ya sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya zaka masa kasan cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi kasan cewa shi din SOJA NE.
ฦasa ฦasa zahra taja tsaki cikin ranta
“Da wannan kayan yafi kamata ma ace jikinsa ya ษaci dazu naga ta qaryar gayu da ฦyanฦyami” ta qarashe maganar tana fitar da tsakinta a sarari dai dai sanda ta hangi ya musty na qarasawa inda yake tsayen bayan ya baro wajen me gadi wanda da alama wani saqo ya bashi.
Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji muryar ya musty na nufosu yana fadin
“Yaa haidar na magana fa ‘yammata” dukkansu babu wadda cikinta bai murษa mata ba,yusra da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace
“Wa yake kira a cikinmu?”
“Dukanku” ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba kasafai kiran haidar ke musu daษi ba.
Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya jisu
“Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?”
“Idan kunzo kwaji” daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.
“Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje” inji hafsat qanwarsa wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma a tsorace take,haka suka nufeshi sum sum kamar waษanda suka ษauko gawa.
Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa yana latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.
Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani saraki ya jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa
“Wace inna wuro a cikinku?” Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda sunsan dai duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka kasa amsashi suka hau kallon kallo.
23/10/2021, 08:36 – ๐๐ป๐๐ป: 04
*KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พ,KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
___________________________
*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kintaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what’s app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* *@turare_by_awwaba mungode*
_______________________________
Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin hali yasa suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba tsawarsa ta mamayesu wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.
A hankali ya dora birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza a kanta na sakan daya kana ya janye yana cewa
“Itace ta dawo yau daga boarding ba?” Haushi tambayar tasa ta bata fiye data dazun,baqo ne shi,ko yau ya soma zuwa gidan nasu,tuni suka amsa masa da eh
“Good” ya fada yana kashe wayarsa ya zurata a aljihun wandonsa na baya,idanunsa dake ladabtar da mutum na bisa kanta.
“Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?” Ya jefa mata tambayar da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me yake nufi da hakan
“Am asking you!” Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira amsarta ba ya dora da
“Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna son mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko malaman naki ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba zaki qone?,to i wil deal with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida ya mana fada saina masa daurin da za’a kasa ganeshi,ba gidan ‘yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?” Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
“Kinji ko bakiji ba?”
“Naji” ta amsa cikin muryar kuka
“Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!” Ya kuma fada cikin tsawar.
Tuni suka miqe har suna rige rigen barin wajen,sai da suka tabbatar sun bar inda zai iya jinsu suka fara bawa zahra dake kuka haquri,kasa amsa musu da komai tayi,ta kuma kasa zuwa tura watsapp da zuwa sassan umminta don tayata dora girkin da mafi yawancin lokutta nata girkin dana hajja take hadawa,duk da itama hajjan idan tayi sha’awar wani abun tana dafa abinta,sai kawai ta juya ta koma sassan hajjan da sassarfa kuka Na sake qwace mata,maganganunsa na dawo mata.
Me yake nufi kenan?yana mata kallon ‘yar iska ne koko meye?,bin maxa take a makarantar kenan har suke biyota gidan ubanta yake nufi?ko ita ta kirayesu tace suzo,bayan batama san kosu waye sukazo din ba,fatanta daya Allah kada yasanya da nuraddeen dinta akayi hakan.
Saman kujera ta zube a falon tana qoqarin tsaida qwallarta duk da taqi tsaiwa,daidai lokacin hajja ta fito daga dakinta tana riqe da carbi,da alama zikirinta data saba takeyi.
“Ke lafiya?,kukan me kike bayan qalau kuka fita?” Hajjan ta jero mata tambayar tana tsaiwa kan zahran tana rungume da hannunta fuskarta cike da damuwa da fargaba.
Kasa bata amsa tayi saboda yadda zuciyarta ke suya,sai data dauki wasu mintuna kana cikin sheshsheqar kuka ta gaya mata abinda ya faru,sannan ta dora da cewa
“Ki masa magana hajja,ki shiga tsakanina dashi”
“Ya isa,amma karna qara jin kince haka saboda yayanki ya miki fada,kawai maganganun daya fada dinne basu dace ba,tunda an jima ana wannan case din,kuma duk sanda irin haka ta tashi ina masa bayani,dole su dinga haquri wata macen haka Allah ya halicceta da farinjini,kome qoqarinta na ganin ta kaucewa samari bata isa ba musamman idan tana kan ganiyarta,yanzu dai ki tsaida kukan nan haka,zaizo ya sameni har inda nake”.
Da qyar hajja ta sha kanta,duk da tsaida kukan amma saitayi kwanciyarta saman doguwar kujera tana ta hadiyar zuciya gamida tuna maganganun daya gasa mata,ta jima zaune anan har akayi sallar magariba sannan ta shiga dakinta ta daura alwala ga bada farali,bata cire hijabin jikinta ba ta miqe da niyyar taje ta tura watsapp din da bata samu damar turawa dazu ba.
“Ga abincin dare fa an gama,ki tsaya kici sannan ki fita”
“Yanzu zan dawo hajja,ba dadewa zanyi ba” ta amsa mata tana ficewa,don tana son taga nuraddeen koda online ne,shurun yayi yawa,bataso kuma ta sake kiranshi da kanta.
Da sallama ta shiga babban falon sassan,kusan duka yaran gidan na zaune a falon,ba kums komai suke ba sai kallon tashar arewa 24,abinda ita sam bai ษaษata da qasa ba,sau tari tafi ganewa tayi charting da qawayenta a watsapp,don idan baquwar number ma tayi mata magana sau tari tana blocking dinta ne,don wayar tata a kowanne lokaci umminya na iya karba babu notice ta binciketa,hakanan yayanta ammar,idan ba watsapp ba kuwa sai tahau facebook ta karanta labarai kota kalli vedio,ko instagram ta kalli hotuna da gajerun labarai,duk da ba kasafai ta fiya hawa instagram dinta ba,saboda tattalin data dinta.
Dan zama cikinsu tayi aka dan taba cafta,don ta tadda ya musty da adam,wadanda dukkaninsu gwanayen raha ne da barkwanci,ba zaka ce ciki daya suka fito da yaa haidar ba,shi kadai kusan ya fita zakka a cikinsu
“Ina yaa zahra ne?” Zahran ta tambaya unaisa dake wani assigment,duk kuma rabin hankalinta nakan tv
“Tana ciki ita da ya hafsa”
“Abba babba fa?”
“Ya fita masallaci bai dawo ba”
“Ok” ta fada tana miqewa,kanta tsaye ta nufi dakinsu hafsat din.
Su uku ta samu a dakin,yasira ‘yar mommy hafsa da kuma zahra din.
Zahrar na zaune saman dressing chair dake gaban mirrow din dakin,sanye da purple din hijabi mai hannu,ma’abociyar sanya hijabi ce,zaiyi wuya ka sameta babu hijab,duk wanda ya santa a haka ya santa,yasira na qasan dakin zaune tana cin abinci,hafsa na zaune saman katifa,hannun zahran riqe da wasu takaddu,fuskarta cike da fara’a,da alama cikin farinciki take,jifa jifa suna taba hira dasu yasiran zahra tayi sallama.
Dukkansu suka amsa mata zahra na sauke qafarta data dora daya saman daya tana gyara takardunta dake riqe a hannunta
“Yanzu nakeson gama cin abinci naje na amso tsarabata” yasira ta fada tana dauke hannunta daga kwanon abincin,murmushi zahra tayi wanda ya bayyana jerarrun haqoranta tana jifan yasira da harara
“Wai wuni guda don Allah ina kika je?”
“Au basu gaya miki ba?,wallahi shirye shiryen bikin huda muketa yi,mommy tace naje ayi dani,tunda hudan nata naci da mitar naqi cewa komai” idanu xahra ta fidda
“Wayyo,kada dai kice babu ni za’ayi sabgar?,saura sati nawa?”
“Sati biyar ya rage” saita narke fuska kamar zata sanya kuka,harga Allah taji babu dadi,don taso ace tana nan za’ayi bikin,don suna shiri da huda sosai
“Sati daya da komawata school kenan fa?,kai ya rabb,ka rabani da wannan boarding din” dariya dukka suka saka mata,saboda kullum bata rasa abun qorafi dangane da makarantar,amma sun sani dole tayi haquri ta qarasa,tunda tazo tsakiya.
Neman wajen zama tayi bayan ta yiwa yasiran fatan alkhairi a bikin ta dubi xahra
“Takwara….zuwa nayi ki turan watsapp,nawa yayi expeir…..amma naga yau fuskarki kamar gonar auduga” caraf hafsa ta karbe
“Yo ba dole ba…..ta samu admission fa a kust wudil” cikin mamaki zahra ke duban hafsa,abu biyu ya bata mamaki,na farko ya haidar data tsayar a matsayin wanda zasuyi aure ita dashi ya sani ya kuma aminta cewa zatayi?,abu na biyu indai kuwa hakanne su me yasa harda shi cikin masu dokar ba zasu ษara daga secondry ba?”.
Kamar hafsa tasan me take tunani cikin salo na mita tace
“Kinga aikin dan adam ko?,mu nan ya tsaya an saka mana dokar aure muna candy amma shi xaibar matarsa ta soma jami’a,saiya wani fake da cewar zuwa sanda zata gama ko tayi nisa a karatun ta qara girma da shekaru…..zuwa sannan shine dai dai aurensu”.
Maida dubanta tayi ga zahra dake murmushi kawai tana dubansu,tana kuma mamakin yadda suke sanyawa yayansu tsanani da yawa haka,duk da ta sani cewa shi dinma ba kanwar lasa bace,baida sauqi ta kowanne bangare,hakanan bauษaษษen mutum ne me wuyar sha’ani,wanda idan baka fuskanceshi ba baka kuma karanci ALฦIBLArsa ba zaka ci wuyar zama dashi,amma kuma yana da dadin xama qwarai idan ka ganeshi ka kuma gane wayeshi,ka tsare doka da qa’odojinsa,ita din shaida ce,don bata tunanin soyayyarsu xatayi tsahon rai haka ba,bata taba tunanin zasu shaqu da zazzarfar soyayya a tsakaninsu haka ba,bata taba masa kallon qwararre kuma gwani a fannin soyayya ba saida suka fara son junansu,bata jin a duniya akwai wani namiji da yakai haidar dinta iya sanin makamai da matakan mallakar zuciyar mace,ya kuma tafi da dukkan tunani da imaninta lokaci qanqani.
“Allah ya kyauta” zahra ta fada cike da mamaki da ganin cewa ya raina ma zahran wayo kawai,wato kallon yarinya da bata isa ma aure yake mata ba kenan?,abinda a qalla dukkansu ta basu shekara biyu wasu ma uku,tana mamakin wanne irin so take masa haka?,tana kuma jinjina mata yadda ta iya juriya da tafiyar da halayyarsa,sam ita ko zancansa ma batason yi,don haka ta dora mata wayar saman cinyarta kawai tace ta tura mata,ta kuma amshi takardun hannunta tana dubawa gami da kautar da wannan hirar.
Kusan awarta guda a dakin sannan ta karbi wayar ta musu sallama ta fito,tana fitowa mama na fitowa daga kitchen dauke da fulasan abincin mai gidan,qarasawa tayi wajen mama ta russuna cikin girmamawa tana gaidata
“Lafia lau inna wuro ‘yan makaranta,ashe kin dawo?” Kaita gyada
“Eh na shigo daxun ai mommy tace min baki nan”
“Ban ko jima da shigowa ba,matar auwalu ce a akwance a asibiti ba lpy,kuma kwata kwata ban samu zuwa dubata din ba sai jiya”
“Ayyah anty laraba,Allah ya sawwaqe”
“Amin amin”
“Abba ya shigo kuwa?,ban samu gaisawa dasu ba duka wannan karon ba wanda na samu a gida”
“Eh ai kuwa duk suna tare yau zasuci abincin dare tare,muje saiku gaisa” maman ta fada ta fara yin gaba,zahran ta bita ta amshi kwanukan daga hannunta ta riqe,maman tayi gaba ita kuma ta bita a baya.
Tun kafin su shiga take jiyo muryoyinsu cikin raha da barkwanci,hira irin ta ‘yan uwantaka,’yan uwan da kansu ke hade suke kuma ฦaunar junansu.
Cikin qanqanin lokaci Idanunta suka tara hawaye,ba abinda ya fado mata sai mahaifinta,da tuni yanzu haka yana cikinsu anayi dashi,duk da cewa suma din sun riqeta tamkar su suka haifeta,kamar yadda itama ta daukesun a haka,amma duk da wannan babu wanda zai cike maka gurbin mahaifa a yayin daka rasa daya daga cikinsu.
Sallama tayi bayan mama tayi tata,dukka suka amsa,kowa kuma ya soma nuna murnar ganinta,yayin da nauyi da kunyarsu duka ta kamata,ta qarasa tsakiyarsu ta aje kwanukan,sannan ta matsa gefe a nutse tana gaidasu daya bayan daya cikin girmamawa,kowanne na amsawa cikin nuna kulawa,suna kuma mata tambayoyi kan karatu da sauransu.
Kusan a qalla minti biyar kafin ta tashi tana cewa
“Abba saida safe,saida safenku abba”
“To Allah ya bamu alkhairi” suka fada kusan a tare,ta juya a hankali cikin nutsuwa ta fice.
Har ta nufi sassan hajja sai kuma taga ya kamata ta sake zuwa taga mahaifiyarta,don haka saita sauya akala xuwa nasu sassan.
Da sallama ta shiga kamar yadda dabi’arta take tana saka kai cikin falon,sai kuma ta soma rage fara’a da walwalar kan fuskarta ganinsa zaune darashe darashe tsakiyar falon nasu yana cin abinci hankalinsa a kwance shida qaninta rafeeq,ta gefan idanu ta saci kallonsu tana qarasowa cikin falon,ranta cike fal da mamakin shaquwa da sabon dake tsakaninsa da umminta,kusan kaf fadin gidan bata taba taba ganin inda yake zama ya sake haka yaci abinci ba bayaga wajen hajja sai wajen ummi,duk da cewa dama can tun tasowarta ta budi ido da ganinsa a sassan nasu da kuma kalar wannan alaqar tsakaninsa da ummin nata,saidai kuma bayan rasuwar mahaifinsun wata sabuwar kulawa yake sake bawa ummin da duka qannenta.
“Bakiga mutane bane da zaki shigo ki samu waje kizauna kanki tsaye baki gaidasu ba?” Ummintata ta jefa mata tambayar da tafi kama da akwai wata a qasa kenan,a sanyaye tace
“Aina gaisheshi tun dazun?”
“Ok,shi yasa yanzu ba zaki qara ba kenan?” Kaita girgiza kawai dolenta a sanyaye tace
“Ina wuni?”sai daya sha qamshi sannan yace
“Riqe abarki kawai,tunda sai kinyi jayayya da na gaba dake sannan zakiyi abinda aka saki” wani ษacin rai ne taji ya riqe mata wuya,cikin ranta tace
“Wato ko dakin mamarka munafiki ya rigaka shiga sai kaga sauyin fuska,yanzu gashi babu gaira ba dalili daga zuwa ganin mamarta zai hadasu,bayan shi babu wanda ya hadashi da tashi mamar.
Miqewa tayi kawai tace
“Zuwa nayi yi miki saida safe”
“Allah ya bamu alkhairi” ta amsa mata ciki ciki,jikinta ya bata akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ta yiwa ummin,saidai kanta ya kasa kawo komai,tubda ita dai tasan awanni kadan duka duka da dawowarta gia,don haka sawunta a likkafa ta fita a sashen.
A falo ta sami hajja ita da mariya da halima yaran wajen umma matar abba abu suna kallo,dubanta hajja tayi
“Kin dawo kenan?”
“Eh wlh….yunwa bari na samo abinci” tayi gaba da sauri zuwa cikin kitchen
“Ahto tun dazu nace ki tsaya kici ai” hajja ta fada tana gyara kashingidarta,ita dai zahra tuni tayi kitchen,ta samu faranti ta zuba abincin,sannan ta dawo falon ta zauna sosai saman carfet.
Kafin tayi lomar farko ta soma da bude data dinta sannan ta aje wayar gefanta ta soma cin abincin tana kallon wayar tare da jiran saqonnin su gama shigowa,duk da wasu sun yayyanke,wasu kuma waiting suke nuna mata,don haka basu jima ba suka gama shigowa tsaf,sai tasa hannun hagunta ta dauki wayar,daya hannun kuma tana diban abinci dashi.
Duk yawan saฦonnin dake kan wayar bata bi ta kansu ba,sunan data sanyawa nuraddeen taje ta lalubo ta shiga inbox din tana qoqarin duba last seen dinshi ko kuma yana online.
Ga mamakinta saita ganshi online,dole tayi mamaki,don bata taba ganinsa online ba ba tare da ta tarda saqonshi ba koda kuwa na sallama ne.
Ba jinkiri ta rubuta slm ta tura mishi,yayi mata tick guda biyu alamun yaje,saita tsaya ta zubawa sallamar data tura din idanu kamar ba ita ta rubuta ba,tana jiran taga ta sauya launi zuwa blue,saidai kafin hakan ta faru ta lura daya sauka.
Goshinta ta dafe,sam sai takeji banbarakwai,wannan karon kamar nuradden din ya canza,tunda sam basu saba haka ba dashi,zama tayi sosai ta tura masa saqon cewa tayi fushi dashi,daga haka ta kashe data gaba daya ta maida hankalinta ga abincin,tana son ta gama ta wuce daki kawai ta kwanta gaba daya.
Da wayar da kwanon ta miqe gaba daya a hannunta,hajja ta dubeta
“Yau babu hirar dare kenan?” Fuskarta tadan yamutsa
“Wai so nake nadan huta,tun dazu nasoyin bacci ban samu dama ba” kai hajjan ta gyada
“Ya kamata…..yau banji duriyar nuraddeen ba?” Sai data dubi wayar hannunta sannan ta maida dubanta kan hajjan
“Nima yau na rasa me ya riqeshi haka,kwata kwata bamuyi waya ba”
“Ai yau da gobe sai Allah” bata ce komai ba ta juya ta wuce kitchen ta aje farantin sannan ta wuce dakinta,tasan me yiwuwa su salma nacan na jiranta zaman hirar dare yadda suka saba,idan kuwa basu jita ba zasu biyota ne sassan hajja ayi a nan yadda sukanyi mafi yawancin lokutta,ita kuwa yau sam bata jin wani karsashi.
Kaman jira yake ta gama gyara kwanciyarta saiga kiranshi ya shigo,murmushi ta sake cikin zumudi ta daga kiran
“Kimin afuwa ranki ya dade tuba nake” cikin shagwabar nan tata tace
“Aini tuni nayi fushi ma”
“Kimin rai,karkisa cikin daren nan na kamo hanya”
“Na yi maka” ta fada murmushi na qwace mata,yayin dashi kuma ya saki ajiyar zuciya yana cewa
“Kinsan duk duniya ke daya ce fushinta ke daga min hankali,gwara ran kowa ya baci,hankalin kowa ya tashi indai naki yana a kwance”
Farr tayi da idanunta cikin jin dadin yadda take da girma da matsayi cikin zuciyarsa,kullum kwanan duniya sake nuna mata matsayinta yake a wajensa,hakan yana mata dadi qwarai,tana jinta cewa itama takai mace,ba kamar yadda ko yaushe ya haidar ke nuna musu suna mata bane.
“Baby ina zuwa,minti biyu,mama tayi kirana zan kiraki”
“Kace ina gaisheta” ta fadi,bata ji amsarsa ba amma taji qit wayar ta katse,saita sauke wayar daga kunnenta tana murmushi,soyayyarsu da nuraddeen koda yaushe ta dabance a zuciyarta,gyara kwanciyarta tayi ta bude inbox nashi tana bitar saqonninshi da ita,fuskarta wadace da murmushi,ta jima a haka sannan taji hayaniyar ‘yammatan gidan,tasan zuwan zasuyi su dasa hira,wala’alla ma idan nuraddeen ya kirata su hanata dagawa,don haka ta cusa wayar qasan filo ta runtse idonta ta gyara kwanciyarta kamar me bacci,tana jinsu suka shigo suka qaraci nacin tashinta suka haqura suka shiga hirarsu.
Tun tana jinsu sama sama har har bacci ya kwasheta.
Bata tashi farkawa ba sai da aka kirayi sallar asuba.
Misalin sha daya da rabi na safe ta gama dukkan abinda zatayi,tana gaban madubi tana qarasa kwalliyar fuskarta,bayan ta shirya kanta cikin wasu riga da skert na atamfa da suka yi mata cif a jikinta,abu na qarshe datayi gaban mudubin shine feshe jikinta da turare,ta kalli kanta ta tabbatar komai yayi,saita sakarwa kanta murmushi,saboda ita kanta tasan tayi kyau.
Hankalinta ta maida kan wayarta dake gefanta,tun daxun take trying number nuraddeen,tana son gaya mishi xata fita,don kada yace zayazo kuma bata nan,gwadawa ta sakeyi tana fatan ta sameshi,tun jiya da yace zaya kira bai biyo din ba,amma ta masa uzuri,mai yiwuwa basu gama magana da maman nashi da wuri bane.
Cikin sa’a wannan karon ta sameshi,sai daf da zata tsinke aka daga,muryarshi can qasa kamar mai bacci suka soma gaisawa
“Zan je gidan abban gwammaja ne nace bari na gaya maka kada kazo gida baka sameni ba”
“Ok,babu matsala,na tarad dake acan kawai”taji dadin hakan don tana da muradin ganinsa,amma saita boye murnar tata da cewa
“Ok fine,yayi” daga haka sukayi sallama ta aje wayar tana sakin murmushi tare da sake duban kanta sosai,nufar ma’ajiyar sarqoqinta tayita cire dan kunnen kunnenta ta saka sarqar da dan kunne harda abun hannu,wanda ada batayi niyyar sanyawa ba,data sake duban kanta sai taga kwalliyar ta sake qawatuwa fiye da daxun.
“Kince karna bata mana lokaci,kuma naga kamar kedin xaki bata mana” ta jiyo mitar salma daga can falon hajja
“Ina zuwa” ta fada da sauri tana daukar mayafinta dake saman katifa ta yafashi saman kafadunta,ta maqala hand bag dinta a hannu ta zura takalmi ta fito.
“Wannan mayafin fa salma?” Zahra ta fada tana duban salma
“Hmmmm…kin manta yaa zaki yana nan,baki nan ranar daya kora mana warning kan saka irin wadan nan mayafan,wai bama ganin zahransa,ita bata ishemu darasi ba” baki zahra ta tabe,zata ce wani abu hajja ta fito
“Ma sha Allah…” Ta fada tana duban kyawawan jikokin nata
“Amma innawuro ki koma ki canza mayafi” baki ta tabe kamar xata saki kuka tace
“Ni bani da wani babba irinsa da zai shiga da kaya na,don Allah hajja ki barni”
“Ni ina dashi,kije kibude adaka ta ki dauka nawa” dariya sosai zahra ta qyalqyale da ita,salma na dan tayata,sai data tsagaita sannan tace
“Haba hajja,haba don Allah,mayafinki fa?ai sai a nannademu duka nida salma a ciki,ki qyaleni don Allah,wannan ma meye aibunsa tunda ya rufemin duka baya na,kuma ba mai shara shara bane”
“To Allah ya baki sa’a,idan kuka hadu dashi ai kya dawo ki dauka ko ba don Allah ba” daga haka tayi gaba ta barsu
“Muje don Allah salma,su na fuskanci kowa ma bin dokarsa da tsoron fushinsa yake,kamar shine uban gidan gaba daya” ta qarashe xancan tana barin falon,salma tabi bayanta tana dariyar zancan hajja na zahra ta yafa aron mayafinta.
Sassan umminta ta nufa don gaya mata zata wuce,sai data tsaya daga baya ta bawa salma riqon mayafinta sannan ta shiga ta mata sallama ta fito suka wuce,salma nata tsokanarta Allah yasa su hadu da ya haidar,ita kuma tana ramawa
“ฦดar baqinciki,bakinki ya sari ษanyen kashi” suna hira kadan kadan har suka isa bakin titi suka tsaya don samun abun hawa.
Tun daga nesa salma ta hangi motarshi,damqe hannun zahra tayi
“Xahra,ya haidar” ta furta idanunta na kan motar dake qara kusanto inda suke tsaye,duban wajen tayi,tabbas motarshi ce,to amma su ina ruwansu dashi,don haka ta zame hannunta daga na salma
“Ina ruwanmu dashi?,share kawai,karma ki nuna kin ganshi” daga haka taci mur ta maida fuskarta wani sashe,saidai kuma zuciyarta na dan bugawa saboda tsoro.
23/10/2021, 08:37 – ๐๐ป๐๐ป: 05
Masoya ga abdulrahamaanโค๏ธ
Kโaramin yaro masoyi kuma mahaddaccin alqurโani mai girma
Yana matukโar son karatun alqurโani duk kankancin shekarun sa, Ya haddace surorin alqurโani da dama hizb biyu na ammah.
Dan Allah a shiga a danna masa subscribe, Aunties, uncles ๐ฅฐ๐ฅฐ A saurara a kalla a kuma sanyawa channel dinsa albarka โค๏ธโค๏ธ
Yaro kโarami yataso da zuciar son karatun AlโQurโani mai girma. Kullum burin sa bai wuce a kyalla shi a camera yana rangada karatu cikin kiraโarsa mai dadi, ๐๐ป๐๐ป
Toh yan uwa dan Allah a hanzarta a danna kararrawar subscribe ta tashar YouTube na ABDUL-RAHMAAN… โค๏ธโค๏ธDomin samun sabon karatun da yai a duk sanda Aka dora ๐๐
Mungode kwarai da zabโin zafafa biyar..๐๐ป๐๐ป
Channel name Abdul-rahmaan.
He’s a very young boy who’s passionate about becoming one among the huffaz, he loves reciting the Holy Qur’an even at his younger age. He has memorized so many surahs within juz ammah.
please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair..
*KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พKARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
5
Cikin nutsatsen tuqi motar tazo ta giftasu,wata ajiyar zuciya zahra ta saki,can qasa muryarta tace
“Thank god….Allah ya tsaremu daga masifar wannan masifaffen” tayi maganar a afili sanda tasa hannu tana tsayar musu da dan adaidaita sahu,ba tare da tsayawa dogon ciniki ba ta shiga salma ta bita a baya tana cewa
“Addu’arki taci bai ganmu ba,Allah ya tsallakar dake”.
Tafiyar minti talatin da mintina suka isa gwammaja gidan abban gwammaja,matarshi daya da yara tara,gidane na masu rufin asiri qwarai,matarshi hajiya halimatu macace mai mutunci da zumunci gami da son dangin mijinta,hasina itace kusan sa’ar zahra,tsiransu watanni biyu kacal zahra ta bawa hasina,daga khadija mahaifiyar zahra saishi iyayensu suka haifa,su biyu kacal a duniya,hakan ya sanya abban gwammaja yake kulawa da ita sosai,ya zame mata tamkar uba,kamar yadda itama take girmamashi sosai,duk wani hukunci daya yanke ko ya zartar a kanta ko yaranta dai dai ne,shi take dauka a matsayin uba,kamar yadda yaranta suma suke daukarshi haka,shi ya dauki nauyin karatun zahra da yayanta tun mahaifinsu ma yana raye,yanzu haka yayan zahran dake a ji daya a jami’ar ibadan shike masa komai da ya kamata uba mahaifi ya yiwa yaransa.
Da sakin fuska kamar kullum umma ta tarbesu,saida suka gama gaisawa sannan suka wuce dakin hasina suka kafa tasu hirar,wanda kusan rabi tambaya hasina take mata kan makaranta bayan ta dawo gida jiyya
“Wallahi ji nayi nima kamar nayi cutar qarya a maidoni gida,amma nasan halin ummi da abba,tsaf xasu gane,kuma raina saiya baci fiye da kima,shi yasa kawai na haqura,don Allah sis ki warke mu koma tare” dariya hasina ta danyi
“Sanin hali….shi yasa nima duk tunanina yana kanki,ai naji sauqi sosai,in sha Allahu tare xamu koma” daga haka suka shiga hirarrakin da suka shafesu,sai da akayi sallar la’asar sannan nuraddeen ya kirata yace yana hanya,tuni ta isa bakin mudubi ta soma gyara fuskarta,su hasina nata tsokanarta,ita dai bata kulasu ba taci gaba da abinda takeyi.
Yaro ne yayi sallama yace ana kiran yammatan da suka shigo dazu,murmushi tayi tace
“Kai nuradden” ta tsammaci shi ya aiko,don haka ta yafa mayafinta tace dasu
“Ina zuwa minti biyu” harararta salma tayi
“Kedai kawai sai mun ganki”.
A hankali ta tsaya qofar gidan tana waige waigen neman nuraddeen,sallama taji anyi daga bayanta,cikin mamaki ta juya tana duban mai sallamar,don bata son muryar ba bare fuskarshi
“Ni na aika a kirawoku,kuma sai naci sa’a ke din ce ta fito,naga shigarku gidan tun dazu,saina kasa sukuni sai nayi magana dake” dubansa kawai take ba tare data iya cewa komai ba don ta rasa abun cewar,tasan cewa nuraddeen na dab da isowa,kuma tafi kowa sanin halayyarsa na tsananin kishinta,don koda waya ya kira yaji busy ya dinga mita da qorafi kenan yana tambayarta dawa take waya.
Tunaninta ne ya yanke lokacin da taga nuraddeen tsaye daura dasu,a hankali ya tako ya raba tsakiyarsu yana fuskantar saurayin
“Malam me kakeyi a nan?” Yadda ya tsare gida yasa ya tsammaci wani makusancinta ne ko kuma yayanta,don haka yace
“Magana nakeso muyi da ita ne”
“Bace daga wajan nan tun kafin ranka ya baci,don tuni an mata miji,saura kwanaki kadan aurenta”
“Ayyah,ai ban sani ba kayi haquri don Allah,fatan alkhairi” ya fada yana juyawa yabar wajen.
Sai da yayi nisa da wajen sannan ya waiwayo inda take tsaye,fuskarshi da alamun fushi yake dubanta
“Waye wannan zahra?,dama zaki iya tsayawa da wani ki saurareshi bayan ni?” Ya fada yana nuna kanshi da yatsa,kai take kadawa cikin damuwa
“An aika ne ance naxo,na tsammaci kaine,koda na fito ma babu wata magana data hadani dashi,kayi haquri”
“Zahra…kinsan yadda nake sonki?,kinsan yadda nake kishinki kuwa?,da kin sani da ko na second daya ba zaki tsaya da kowa ba”
“Kayi haquri nace,nima ban zaci wani bane daban” sosai nuraddeen ya dinga fushi,da qyar ta lallabashi ya sauko.
Kusan hirar tasu ma batayi tsaho ba yayi mata sallama ya wuce,ta tsammaci zai dade dayawa tunda shine haduwarsu ta farko bayan dawowarta daga makaranta,haka ta shiga gidan tana tunani hannunta dauke da siyayyar daya saba kawo mata lokaci lokaci idan zaizo,basu sake wani jimawa ba suka wuce gida suma,saboda sanin dokar gidansu na hanasu yin dare a waje.
Sanye yake da wadansu irin t.shirt da trouser masu azabar kyau,wadanda suka dace da jikinsa,suka kuma bayyanar da kwarjininsa haiba gami da kyawun surarsa da na jikinsa,kyakkyawar fuskarsa sanye da wani glass mai duhu daya sake qawata adonshi ya kuma qara masa kwarjini wanda yakanyi amfani dashi lokaci zuwa lokaci idan yaso hakan,ko kuma miskilancinsa ya motsa,qafafunsa cikin wani hadadden takalmi both,motarshi na fake daga gabanshi kadan,da alama fita zaiyi,wayarsa daya na a kunnensa,daya kuma yana danne danne da ita,ma’abocin amsa waya ne,da wahala ka sameshi ba kan waya,wanda kusan fiye da rabinta yana yine kan abinda ya shafi aikinsa.
Dab dashi mai adaidaita ya saukesu,saida gabansu dukka ya fadi,musamman zahra data soma gyara yafen mayafinta sanda suka hada idanu dashi,yayin daya kau da kai kamar bai lura dasu ba yana ci gaba da amsa wayarsa.
A gaggauce ta amshi canjinta sannan ta biyo bayan salma zuwa hanyar gate din gidan
“Barka da yamma” salma gadan russuna kanta tana gaidashi,sai itama ta motsa bakinta kamar ta gaidashin tana mintsinin salma,so tayi kawai ta basar su wuceshi tunda waya yake amsawa,gaidashin tana ganin kamar callig attention dinsa ne a kansu.
Hannu kawai ya daga musu ba tare daya dubesu ba,tuni zahra ta zagaye ta wuce salma,tayi gaba zuwa cikin gidan tana murnar da baice komai ba.
Saidai kafin takai ga shigewa ta jiyo sautin dakakkiyar muyarsa mai cike da kwarjini irin ta soja yace
“Ke!,zonan” kasa waiwaya tayi sai salma ce ta nuna kanta
“Ni?” Banza ya mata yana latsa wayarsa,hakan yasa ta waiwaya tana yiwa zahra inkiya akan taje da ita ake.
Tilas tunda su biyu ne a wajen ya sanyata nufar inda yake tsaye,daga can gefansa ta tsaya,tana motsa bakinta,cikin ranta tana fadin
“Allah ka rabamu da masifa da jaraba,Allah ka kadashi wannan mutumin ya koma inda ya fito,yaje can ga qaraci baqin ranshi”tambayar daya jeho mata kan mayafin jikinta ya katse dukka tunaninta,ta soma bin jikinta da kallo,kafin ta gama nazarin abinda yace ya sake fadin
“Idan basu gaya miki ba nida kaina zan gaya miki,daga yau….kinji me nace?” Kai ta gyada kawai sannan ya sake cewa
“Daga yau sai yau,kada na sake ganinki da mayafi irin wannan na jikinki,bazan tsawaita bayani ba,amma idan kunne yaji jiki ya tsira” daga haka ya soma takawa yana yin gaba,hannunsa daya soke a aljihun wandonsa.
Miqews tayi da sauri gana gunaguni qasa qasa ta yadda bazai jiyota ba,tana shiga taga salma tsaye jikin gate,da sauri ta iskota tana cewa
“Bai dai miki komai ba ko?”
“Nifa gsky na soma qosawa da halinsa,fisabilillahi yayita bamu doka da order kamar ance masa a brrack ake ko a filin daga,shikenan a gidan nan baka da damar sakewa kamar a sansanin bada horon sojoji” dariya salma ta saki harda riqe ciki
“Kece son rayuwar ‘yancin naki ne yayi yawa,hala shi yasa duk yawan qorafinki yafi namu”
“To a prison muke da zamu dinga rayuwa haka,Allah na kusa fara murje idona ina masa musu” dariyar salma fin ta dazu tayi
“Kema kinsan mafarki kike,amma….dama zaki gwada wallahi” ita kanta saita murmushi ya subuce saman fuskarta duk da yanayin bacin ran da take,hakanan bata shiryawa hakan ba
“To muguwa,ya azabtani kina gefe ko haquri babu lallai ki bayar”.
Zahra suka hango na tahowa cikin shigarta tako yaushe hijabi mai hannu,a hankali take tafiya,tadan janyo hijabin kadan yadan rufe mata rabin fuska
“Lover yaaya ina zuwa haka?” Salma ta fada cikin salon tsokana,murmushi mai sanyi tadan saki,hakanan muryarta da sanyi tace
“Asibiti xanje”
“Waye ba lafiya?” Inji xahra tana dubanta,sai data dan dafe kanta kadan sannan tace
“Nice wallahi,ciwon kaine ke damuna tun jiya”
“Ke kadai xaki,ko nazo na rakaki?”
“Yauwa,da kin taimakeni kuwa,tare da yaa haidar zamu,ni kuma kunyar fita mu biyu nakeji,banda ya matsanta ma dasai gobe kawai nahau adaidaita ta kaini ta dawo dani” baki salma ta wangale
“Kaga shugabannin masoya,saikun dawo Allah ya kiyaye hanya,amma wannan rakiyar tafi qarfin salamatu” waiwayawa tayi ga zahra
“To takwara ke taimaka don Allah” fuska ta yatsina ta nuna kanta
“Ni?,Allah suturu buฦui inji kishiyar me doro,idan kin ganni a lahira kaini akayi,yanzu ya gama cimin mutunci,a dawo lafiya” murmushi zahra tayi tana kama baki
“Na gode dacin fuskar da kukemin Allah,babu komai watarana saina rama dukka akan mazajenku,har yanzu kun kasa fahimtar yayanku,amma ina da yaqinin wataran idan kukayi aure zaku fahimceshi kamar yadda su anty asiya suke ganeshi kadan kadan yanzun,kuma gaba zaku gane cewa he is the best and d most kindly gentle man in d world” dariya sosai suka sanya,zahra tace
“Kekam ai dole ki yabeshi,ai masoyi baida laifi sam a rayuwar masoyinsa,ta nan kam banga laifinki ba” daga haka tayi gaba abinta.
Dab da zasu shige sassan hajja sukaci karo da hafsat
“Kun dawo kenan?”
“Mundan tsaya ma da yaa zahra,tana ta koda masoyinta,wai asibiti yaa haidar zai kaita take neman dan rakiya….wa zaije?” Salma ta fada tana kama haba
“Ah haba don Allah,ai ko bari naje na mata kara” daga haka tayi gaba da sauri,zahra ta bita da kallo tana son hanata amma tuni tayi gaba,dole ta barta ta wuce sassan hajja,salma ta wuce nasu sassan,tana son ta fara watsa ruwa sannan takaiwa mamanta saqon da abban gwammajan ya bata ta kawo mata.
Tana tsaye tana gayawa hajja ta dawo saiga hafsat ta shigo,kallo daya tayi mata ta sheqe da dariya
“Allah ya qara,hala an tallo qeyarki ne?” Cikin fuskar takaici ta bata amsa tana miqewa saman doguwar kujerar hajjan
“Inda qeyata ma ya tallo kawai da da sauqi,yarfani yayi kawai gaban abu sufyan(abokinsa)” dariya sosao zahra tasha harda buga qafa,ta samu abun tsokana,bata qyaleta ba har sai data yunqura takai mata dundu sannan ta wuce dakinta da gudu hajja na musu addu’ar shiriya.
Cikin kwanakin hutunta tayi hutunta kamar yadda ta saba cikin ahalinta,saidai abu daya daya mata tarnaqi a wannan hutun,ya kuma zame mata baqon lamari wanda bata saba dashi ba shine,rashin samun cikakken lokaci daga wajen nuraddeen,duk wasu qa’idoji na yaa haidar da matsinsa sam bai dameta kamar yadda take samun rashin cikakken lokaci tare da nuraddeen din ba,koda yause cikin bashi uzuri take a karan kanta,bata son ko daya zuciyarta ta tuhumeshi,tunda ada ba haka yakeyi ba.
ยถยถยถยถยถยถ ยถยถยถยถยถ ยถยถยถยถยถยถ ยถยถยถยถยถ
Kwanaki uku duka duka suka rage hutunsu ya qare su koma makaranta,anata mata shirye shiryen komawa makaranta kamar kowanne lokaci,hakanan itama ta hada kusan duk abinda tasan zata tafi dashi,saidai duk wani abu da takeyi jikinta a sanyaye yake,saboda tabarbarewar tarayyarta da nuraddeen,wanda har yanzu batasan dalili ba,batasan meya kawo hakan ba,bata minti goma cikakke bada wannan tunanin a ranta ba,hakan ya janyo raguwar walwala da karsashinta.
Da yammacin ranar suna sassan abba babba,dan malele suka hada nadiya na kitchen din tana musu,mama nata mitar suyi su gama za’a dora abincin dare,saura na zaune a falon suna hira,hafsat na yiwa zahra kitson komawa makaranta.
Duk wannan hirar da ake zahra na jinsu,rabin tunaninta yana kan nuraddeen,wanda a baya duk lokaci irin wannan da take gab da komawa makaranta basa rabo da yin waya,hakanan bai gajiya da aiko mata da siyayya na abubuwan qwalama don tsarabar komawar,duka ba wannan ne ya dameta ba kamar rashin jinsa da kuma rashin samun kulawarsa a gareta kamar baya,duk sanda ta masa qorafi yakan bata lokaci yana rarrashinta kan cewa busy ne yayi masa yawa,ta masa uzuri,yana son ya kammala ne,komai zai daidaita in sha Allah.
Yadda yake lallamar nata ya dan sanya take samun relief kadan.
Suna tsaka da kitson wayar tata dake tsakiyar cinyarta ta dauki ringing,tuni ta gane waye,saboda kida na musamman ta saka masa.
Dan qwace kanta tayi daga hannun hafsat cikin hanzari tana cewa
“Ina zuwa” ta miqe da sauri ta nufi dakinsu hafsat.
A gyare kuma atsaftace dakin yake kamar yadda kusan dukkansu haka aka horar dasu sanin muhimmancin tsafta,duk da girman gidan da girman kowanne sashe amma zaiyi wuya ka shiga ka tadda qazanta.
Salma ce kawai a dakin,da alama itama waya take,saita samu gefan katifar ta zauna tana amsa wayar.
Taji dadin kiran don bata tsammaceshi a lokacin,kusan minti talatin suka dauka suna waya kafin suyi sallama ta koma wajensu hafsat,ta tadda an gama dan malelen,ita kadai ake jira,hannunta kawai ta dauraye ta zauna suka soma ci suna hira.
Sun kusa rabi mai da yaji ya qare,don haka zahran ta miqe da plate din a hannunta tana cewa
“Bari na qaro mana” mommy dake zaune a falon tace
“Eheenn,wannan dan malelen kawai kun tarkeshi ne don ku cinyema mutane yaji,idan ance ku daka kuma ku dinga gudawa da ษai da ษai”
“Zamu daka mommy bari mu qoshi dai” suka fada
“Dan malelen ne baya tafiya sosai idan babu yaji” cewar xahra data doshi kitchen da babban tray din a hannunta.
Tana sanya qafarta cikin kitchen din babu zato ba tsammani taci karo dashi sanda yake qoqarin fita ita kuma tana yunqurin shiga.
Gaba daya farantin hannun nata ne ya kife tun daga gaban rigarshi zuwa saman qafafunsa,duka dan malelen ya masa ado gaban riga da takalminsa.
Dukkansu suka ja baya shida ita,kallon jikin nasa ya soma yi daga sama har qasa,zallar bacin rai yana bayyana saman fuska da idanunsa,yayin da itama tsoro ya darsu a ranta saboda ba qaramin aika aika tayi masa ba,farar shirt da ash din trouser din jikinsa gaba daya manja ya sauya musu kama……
23/10/2021, 08:37 – ๐๐ป๐๐ป: *KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พKARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BA*
6
Kallon da ya watsa mata ya sanyata ja baya da sauri,take jikinta ya dauki rawa,saboda ita kanta tasan ba qaramar barna tayi masa ba.
“Ar u mad!….baki da hankali ne?,wacce iriyar mahaukaciyar y……” Sautin muryarsa dake fita cikin kaushi da fushi ta katse sanda muryar mama ta ratsa tsakani tana fadin
“A’ah haidar…..” Waiwayawa yayi yana qoqarin hadiye fushinsa ya dubi maman,adams apple dinsa nayin sama da qasa alamun ranshi ya baci
“Hala karo kuka ci….ke inna wuro ungu,bashi wannan ya rage na rigarsa” ta fada tana miqa mata wani towel
“Ina zuwa” yadan fada a zafafe bayan ya dubi maman ya taka ya nufi qofa ya fice.
Ta falon ya ratsa don isa sashensa,cikin rashin sani saboda yadda ranshi ke a bace ba zato ba tsammani yayi fatali da sauran wanda suka bari cikin faranti,hafsat ce ta ajeshi daga gefanta,nufinsu idan sun cinye wancan saisu qara,take ya fantsama har saman takalmin nasa dai.
Dif falon yayi kowa tamkar anyi ruwan sama an dauke,sam basusan yana gidan ba da basu tarki yin dan malele ba,dukkansu sunsan halinsa,ya tsaneshi wai kayan qazanta ne,tsantsaminsa yake kuma ba tun yau ba haka yake.
Mari kawai ya kaiwa hafsat da farantin dake gefanta,wani huci yabi ta gefan fuskarta,duk da cewa ta samu ta kauce amma sai daya dan sameta
“Uban waye yayi wannan abun!” Ya tambaya cikin bacin rai yana nuna farantin da yayi nasa waje,kasa amsa masa sukayi saboda basu da amsar bashin
“Ok….baku da bakin magana ko?,i wil deal with u!” Ya fada yana gyara tsaiwarshi,kowacce saida cikinta ya duri ruwa,har inna wuro dake kitchen,gashi mama ta fita ta qofar baya bare taji abinda ke faruwa tayi masa magana.
Sallamar xahra ce ta ratsa falon cikin sanyin nan nata,sanye da hijabinta har qasa mai hannu da madauri,hannunta riqe da jaka,fuskarta wadace da murmushi da kuma alamun jin kunya take duban haidar dake tsaye,sam bata ankara da abinda ke wakana ba saidata taka dan malelen daya fantsama saman door mat,ta kuma tsinci muryar haidar din yana basu umarnin dukkansu su wuce zuwa farfajiyar gidan.
Ko ba’a gaya mata ba ta fuskanci akwai matsala,tasan kuma halin kayanta,don haka ta qaraso gabanshi tana qunshe dariyarta bayan ta gama satar kallonsu suna roqonta da idanunsu da suka raina fata kan ta nema musu afuwa.
Qasa qasa tayi masa magana ba tare da sunji me tace ba,idanu yadan xuba mata shima na ‘yan sakanni,kallon dake narkar mata da zuciya ya kuma sake sanya mata tsananin qaunarsa a zuciyarta,wani sanyi ya mamaye ilahirin jikinta,saita dan lumshe ido kadan tana kauda kanta cikin murmushi,takawa yayi a hankali ya nufi qofa ya fice daga falon.
Wani irin ihu suka saki gaba dayansu,ta musu nuni da yatsa zuwa qofa da sauri,sai kowacce ta saka tafin hannunta tana toshe bakinta gami da raba idanu,suna tsoron kada ya jisu kashinsu ya sake bushewa karo na biyu,ihun ne ya jawo hankalin innawuro ta dauko farantin da sauri ta fito
“Wallahi anyi babu ke sister!” Salma ta fada da sauri tana dariya sanda innawuro ta fito,idanunta dukka a waje tace
“Aina godewa Allah da akayi babu ni din,ina kitchen ina muku jaje da addu’ar Allah ya rangwanta muku izayar da zaku sha yau”
“Dalla banza,ba wannan ba,ke kinga wani scene da akayi yanzu tsakanin ya zaki da yaa zahra?,gaskene da ake cewa soyayya ke sawa me qarfi ya sunkuya saman gwiwoyinsa” bata tsaya ba sai data kwashe mata yadda akayi,zahra nakai mata duka tana
“Banason sharri fa,banson haka”
“Allah ya zahra ki bamu sirrin,dama akwai sanda ya zaki zai russuna haka?”murmushi kawai ta koma binsu dashi da taga abun nasu bana qare bane.
Saida suka gama zolayarsu son ransu sannan ta gaya musu abinda ya shigo da ita
“Gida zan wuce,mama naketa nema in yiwa sallama,ta dauka na daga tafiyar,to kuma dazun abba ya dawo,yace yana son ganina,duk da umma ma tace sunyi waya ta gaya mata”
“Kai yaa zahra har tafiya?”cewar inna wuro data aje farantin tsakiyarsu
“Haba ina laifi,ku kun tabamin kara nema kunxo kamar haka?” Murmushi inna wuro tayi
“Nidai ayimin uzuri ba maxauniya bace”
“Eh amma ai kuna samun hutu ko?”
“Zanzo ki kwantar da hankalinki” ta tari numfashin zahran tana dariya
“Allah yasa da gaske ne” ta fadi itama tana miqewa
“Bari na shiga na fito” zahran ta fada tana yin gaba,yayin da su kuma sukaci gaba da shan dan malelensu suna tattauna abinda ya farun yanzun,da sa’ar da sukaci yau basu sha purnishment wajensa ba,Allah ya cecesu.
Dab da magariba suka gama kitson,kowacce ta soma miqewa,wasu nayin sassansu,wasu kuma na haramar daura alwalar sallar magariba,ita da take fashin salla saita wuce dakinsu hafsat,tayi kwanciyarta saman carfet bayan ta dauko wayarta da tayi full charge ta kunna data,suna da matsalar network na mtn wani lokaci,amma a lokaci irin wannan akan dan samu qarfin network,bayan ta kunna saita aje wayar gefanta ta miqa hannu tana sake dauko filo ta qara saman kanta yadda zataji dadin kwanciya sosai.
Kamar kowanne lokaci inbox na nuraddeen ta fara dubawa,last seen dinshi 5minutes ago,amma ga mamakinta bata tarda saqonsa koda na sallama ba,abun ya fara daure mata kai game da lamarin halin ko.in kula dinsa,gashi ba wani isashen lokaci ne da ita ba bare ta bibiyi komai taji inda matsalar take,nan da jibi zuwa gata zata koma inda ta fito.
Gaba daya sai taji bata sha’awar hira da kowa,madadin ta kashe data din ta sauka saita shiga wajen status ta fara bin status din mutane tana kalla,wani ya bata dariya ta murmusa,wani ya bata haushi,wani kuma tayi tsokaci akai ta turawa wanda ya dora status din.
Katsam!sunan nuraddeen ya bayyana bayan ta gama kallon status din wata qawarta ga islamiyyarsu da take zuwa duk sanda akayi hutun makaranta zuwa sanda zasu koma.
Wani irin zabura tayi ta miqe ta zauna daram tana raba idanu,zuciyarta na wani irin bugu,tabi wayar tata data subuce daga hannunta saboda miqewar da tayi da hanxari da kallo.
Kamar me tsoron wayar haka ta miqa hannu ta sake dauko wayar a karo na biyu,bugun zuciyarta na sake tsananta,addu’a take cikin ranta Allah yasa idanunta gixo suke mata,Allah yasa saqe saqe ne na zuciyarta.
Saidai dukka fatanta bai zama gaskiya ba,don sauran hotunan har sun bude kansu da kansu.
Cikin rawar jiki ta fara komawa da baya ta fara daga hoton farko,nuraddeen ne shida wata budurwa,wanda kallo daya kafin kakai ga karanta rubutun dake qasan hoton xai gaya maka tabbas ango da amarya ne cikin yanayin hotunan nan da ake kira da free wedding pictures,rubutune a qasa kamar haka
*SAVE THE DATE 22/07 IN SHA ALLAH*
Wani kakkarwa hannayenta suke kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi tana ci gaba da buda hotunan ba tare data iya tsaiwa ta duba rubutun dake qasan kowanne hoto ba,abunda ta iya dubawa shine lokacin da aka dora,6minutes ago,kenan shi ya dora da hannunsa da kansa,tunda sanda ya sauka da sanda ya dora tazarar minti daya ce.
Hafsa ce ta shigo tana dariya abunta riqe da hijabi tana qoqarin sawa,da alama daga waje ta baro abunda ya bata dariyar,sam bata lura da yanayin da innawuro ke ciki ba sai dataji tana kiran sunanta da wata iriyar shaqaqqiyar murya tana yafitota da hannu.
Qarasowa tayi tana dubanta,ba wanda ya iya magana cikinsu sai wayar da zahra ta miqa mata cikin rawar murya tana cewa
“Dubamin don Allah…..dai dai idanuna suke ganemin?” Hannu tasa ta karbi wayar,hoto daya tak ta kalla saita koma saman qafafunta ta zauna itama tana ci gaba da kallon hotonan cikin matuqar mamaki da sanyin jiki,kalamanta a sanyaye qwarai tace
“Nura ne zahra,nuraddeen dinki fa” rasa abu na gaba daya kamata tayi tayi,sai kawai tasa dukka tafin hannunta biyu ta rufe fuskarta dasu kamar wadda bata da muradin ganin duk wani haske dake cikin duniya,tana jin kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,daidai sanda salma ta shigo,da sauri hafsat tace
“Yauwa,zo kigani don Allah,zoki tayani gani” da hanzari salman ta qaraso tana amsar wayar daga hannun hafsat.
Wani ashar salman ta dura,da yake itadin batakai haqurin hafsat ba,ta lalubi waje ta zauna tana cewa
“Meke shurin faruwa kenan zahra?laaa,kinga ana goge hotunan daga status…..sunyi disappearing gaba daya”ta fada tana kallon hafsat tare da nuna mata wayar
“Tabbas gogesu akayi,don ba’afi minti goma da dorasu ba,bajci ace har lokacin saukarsu yayi ba,me nuraddeen ke nufi?” Tambayar da bata da amsarta data cilla mata ita ta sanyata sakin wani irin kuka me ciwo,kukan daya daga hankalinsu gaba daya,lokacinne yasira itama ta sako kai,cikin yanayi na tsoro ta isa wajensu tana tambayarsu abinda ke faruwa,basu kai ga bata amsa ba kira ya shigo wayar zahran,duk da bata duba tasan me kiran,salma cikin fushi tace
“Bari na daga naji dan gidan marasa mutuncin me zaice?”kai hafsa da yasira wadda batasan ma ainihin meke faruwa ba suka daga mata,ta daga wayar ta sakata a handfree tayi shuru ba tare data ce komai ba,muryar nuradden ta bayyana
“Dear…..don Allah karki hukunci da abinda bakisan ainihin menene ba,ki bani dama inyi miki bayani pls”
“Ai karka damu,saqone ka bayar ya kuma iske inda kakeso ya iske,yo meye kuma wani abun damuwa a ciki?,kaci gaba da shagalinka kawai,amma ka sani,indai da haqqin zahra a wuyanka Allah saiya mata sakayya”
“Ki tsaya kiji don Allah,wacece?,hafsat ce ko yusra?”
“Ban sani ba dan gaba da rainin hankali,karka sake kiran wannan number” qit daga haka ta katse wayar,wanda kafin ta kuma cewa komai wani kiran ya sake biyo baya,haka suka sanya wayar gaba kowa ya rasa abun tabukawa,yanata faman kira ba qaqqautawa kamar yadda zahra ke kuka itama babu qaqqautawa,yasira ce ta karbi wayar daga qarshe bayan sun zayyana mata abinda ke faruwa ta kasheta gaba daya,har cikin zuciyarta tana jin wani irin suya da bacin rai,wannan wacce iriyar yaudara ce haka kai tsaye ta rashin mutunci da cin fuska,yana sane ma yayi posting hotunan a status dinsa?,abinda yafi tsaya musu a rai kenan.
Su hudun gaba daya suka hadu suna bata baki,harda nadiya data shigo daga qarshe gami da maimaita zancan cike da mamaki,don dukkansu bama su ba kusan kowa yasan da zaman nuraddeen a matsayin wanda zahra inna wuro ta tsaids zata aura,abun yazo musu matuqa a ba zata.
Ita kadai tasan yanayin data tsinci kanta da zuciyarta a ciki,wani yanayi da tun tasowarta bata taba jin irinsa ba saiyau,jin lamarin take kamar a mafarki,wai ita?,nuradden?,wanne irin abu haka tayi masa dafa cancanci irin wannan yaudarar mai ciwo?,har yana da bakin cewa ta saurareshi?,ta jima cikin wannan rudun,daga qarshe taji babu abinda take da buqata illa kadaicewa tayi kukanta ita kadai ko hakan zai sa ta samu gurbin da zata zuqi numfashi yakai har zuciya da hunhunta,tana jin kamar numfashinta zai katse ne.
Yanayin yadda suka shigarwa hajja zahran na kuka lullube da fuskarta ya sanyata miqewa da sauri cikin firgita tana tambayar
“Kai…meye haka?,lafiya?” Itakam zahra bata iya tsaiwa ba saita wuce kawai zuwa daki,waje ta laluba ta kwanta gami da sake rushewa da sabon kuka.
Bayan minti biyu tajiyo muryar hajja na rafka salati da salallami,da alama sun gama gaya mata komai,sai kawai taja filo ta rufe kanta tana sake fashewa da wani irin kuka,tanajin sanyi na ratsa gabbanta,kafin kace meye wannan zazzabi ya rafketa.
Ba’a rufa awa guda ba hajjan ta shigo dakin
“Takwara…..kukan kike har yanzu?” Ta fadi tana qarasawa inda take kwancen,ta saka hannu ta yaye abun rufar tana kamo hannunta
“La’ilaha ilallahu,ke tashi,kwanciya kikayi xaki kashe kanki,kinji yadda jikinki ya rine da zazzabi?” Cikin daren dukka hankalin hajjan ya tashi,wanda hakan yasa hankalin yaranta su abba babba suma ya tashin,ta matsa lallai lallai saida su shamsu suka dau mota suka kaita asibiti,wanda basu dawo ba sai wajen sha biyu da rabi na dare saboda yadda zazzabin ya mata mugun kamu ya sanya suka dan riqeta sai daya sauka jikinta yadan daidaita.
Washegari duka tana kwance a daki,ko falo baga fito ba bare taga hasken rana,tana kwance tana bitar duka rayuwarsu ita da nuraddeen,bataga ta inda ta gaza ba da xai gujeta,bata ga me ta masa da zai saka mata d a wannan ba.
Duk yadda hajja taso ta fito da ita ta xauna koda a falo ne amma taqi,hankalinta kaf nakan zahran,duk bayan wasu mintuna saita leqo dubata,dukka jama’ar gidan kowa ya shigo ya dubata babba da yaro,amma banda mutum biyu,ummanta dai tasan kara ce da kawaici ya hanata leqoww,don koda hajja ma ta aika mata cewa tayi ace tana gaidata kawai,data sake aikawa sai tace ai tasan tana wajenta babu komai,shi kuwa dayan dama bashi a lissafinta,tama manta dashi cikin jerin jama’ar gidan.
Hajja da kanta ta yiwa abban gwammaja waya sanda yace zaya aiko a maidasu makaranta ita da hasina ta shaida masa bata da lafiya,a barta koda zuwa satin sama ne idan ta sake murmurewa,ya mata sannu da jiki,ya kuma ce zaisa a shaida hukumar makarantar idan ankai hasinan.
Sai da akayi kwanaki biyar da komawa makarantar sannan ta soma jin qwarin jikinta,don ta tattara dukkan wasu lamura na nuraddeen tayi qoqarin yin watsi dasu,a yadda ta lissafa kwanaki uku kenan da daurin aurensa,yana can wala’alla shida amaryarsa cikin farinciki,yama manta da lamarinta,hakan ya sanya washegari da azahar tayi wanka da ruwa mai dumi sosai,tasha dukka magungunanta,ta shirya cikin atamfa riga da zani sannan ta fito falon.
“Yauwa,ko kefa?” Hajja data taras zaune cikin falon ta fada cikin farinciki,tana kallon yadda zahran tadan fada,hancinta da fuskarta suka qara qara tsaho.
Mirmushi tadan yiwa hajja,cikin qarfin hali ta tsokaneta
“Ashe kina tsoro kada na mutu na barki”
“Zaki fara ko?” Hajjan ta fada tana watsa mata daquwa,dai dai sanda inna gaje ta fito daga kitchen zuwa falon
“Aah,ma sha Allah uwar masu gida jiki yayi kyau”
“Eh wallahi inna gaje” ta fada tana dan murmushi
“Alhamdulillahi,mun godewa Allah,Allah ya qara lafiya”
“Amin inna,akwai abinci ne?” Zahran ta tambaya
“Eh yanzu aka gama na rana…bari a zuba miki” inna gaje ta fada tans komawa kitchen din,sai zahran ta bita a baya ta amso abincin ta dawo inda ta tashi ta zauna
“Wannan abincin kamar na wasan yara wuro?” Hajja ta fada tana duban plate din
“Ya isheni hajja” saita qyaleta,tayi bismillah ta fara ci,lokaci lokaci idanunta nakan tv dake aiki.
Sallamar abubakar ce ta karade falon,abubakar shine yaro na farko a sassansu,daga shi sai ita,sai sauran qannenta maza guda biyu,sulaiman da yusuf,sai mace daya ilham,akwai tazarar shekara kusan biyar tsakaninta da abubakar,hakan ya wanzar da girmamawa sosai tsakaninsu,don haka umminsu ta tarbiyyancesu da bawa na gaba dasu girma.
“Maraba da saddiqu…..saukar yaushe?” Hajja ta fada tana dariya
“Ko minti biyu banyi da shigowa gidan ba” ya fada rabin hankalinsa nakan zahra data aje cokalin hannunta tana qoqarin gaidashi
“Lafiya lau….” Ya amsa a taqaice ya dora da
“Me kike a gida,duk ‘yan makaranta sun koma makaranta?” Kafin hajja takai ga bada amsa an sake sallama cikin falon,muryarsa ta cika wani irin sauti mai sanyi,saidai tana cike da wani kwarjini mai ratsa kunne.
“Sannu da zuwa yaya” abubakar saddiq ya fada cikin salo na girmamawa,fuskarsa washe da fara’a
“Malam…..kana lafiya?” Ya fada yana miqawa saddiq hannunsa dake daure da wani rantsatsen agogo ruwan zaiba,wanda ya dace da lafiyayyar fatarsa da hutu da kuma kwanciyar hankali ya ratsata.
Da sauri sadiq ya miqa masa nasa hannun sukayi musabaha,saiya soma qoqarin zama hannun kujera yana gaida hajja cikin girmamawa,don shi sam baya wasan jika da kaka da ita,ta amsa cikin kulawa,don shi dinma dan gaban goshinta ne,sakamakon sunan maigidanta da yaci,sannan ta dora da fadin
“Kamar tare kuke da sadiq?” Yana dan latsa wayar hannunsa yace
“Tun dazun na shigo,na shiga ciki ne nadan huta”
“Auto ma sha Allah,ya aikin,da fatan an samu abinda ake bida?”
“Alhmdlh” ya fada hade da ajiyar zuciya yana maida wayarsa aljihun lafiyayyen trouser din jikinsa,wanda kallo daya zaka masa kasan me tsada ne,hakanan mai kayan yasan takan kaya masu aji.
Ido suka hada da xahra,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanunsa duka cikin sakan biyu,ya harde hannayensa a qirji yana duban hajja dakewa sadiq bayanin dalilin xamanta a gidan,cikin sauri tace
“Ina yini” can qasa ya amsa kamar yadda ya saba
“Wallahi yaron ya bani mamaki,a haka kamar na Allah ashe bana arziqi bane,yaudara ce kawai ta kawoshi,yau ne mafa kawai na samu kanta ta fito falo ta zauna” ta qarashe zancan cikin nuna jimamai qwarai kan fuskarta idanunta kuma saman fuskar haidar,wanda ya dauke kansa zuwa yanzu daga kansu kamar ma baisan me ake ba.
Ajiyar zuciya sadiq yayi
“To Allah ya kyauta ya rufa asiri,abinda ya faru ya riga daya faru,sai kiyi qoqarin komawa makaranta…..hajja bari naje mu gaisa da sauran mutanen gidan,ummi ce kawai tasan da shigowata,zuwa anjima zan dawo abani abinda aka ragemin”
“Ka taho dai da abinda ka kawomin” dariya ya saki kana ya juya ya fice daga falon.
“A kawo maka abinci ne?” Hajja ta tambayeshi,kai ya kada alamun a’ah,sannan a nutse ya furta
“Idan akwai fura kawai ta isa” sai ta waiwaya wajen zahra,wadda tana son barin falon,amma kuma tana son kallon programe din da ake yi a wani gidan tv,bata so ya wuceta don yayi mata
“Duba fridge wuro akwai damammiya….kayi sa’a kuwa nonon me kyau ne,wanda aka kawomin ne daga can gida adamawa” yunqurawa tayi ta miqe,ta isa fridge din ta ciro furar,saita miqawa hajjan tasa hannu biyu ta amsa silver da nonon ke ciki,wanda har tsatstsafa yake saboda tsabar sanyi ta miqa masa tana cewa
“Kanaji muna magana kan case din inna wuro baka ce komai ba?” Sai daya amsa furar ya bude yasa ludayin dake kai sannan ya daga shanyayyun idanunsa ya kalli hajjan
“Me zance……i dn’t know what to say” duk da bata fahimta qarshen zancensa ba amma saita gyara zamanta
“Na zaci a matsayinka na babba zaka nema yaron kaji komai daga bakinsa….tunda a a zahirin gaskiya suna son junansu” kamar bazai amsa ba,don itakam zahra har tayi nisa da hanyar barin falon,tana ta zumbura baki,sam bataji dadi ba data tuntu eshi da zancan,zata zubda mata aji ne kawai,kuma ma ai yana ji akayi maganar da ya sadiq amma baice komai ba,sai daya dan kurbi furar sannan ya amsata
“Ana aure dole hajja?,kika sani ko batayi masa bane?”.
Kamar saukar mashi haka zahra taji maganar a qahon zuciyarta,don sai data kasa jurewa ta waiwayo ta dubesu,shikam shan furarsa yake kamar ma baisan me ya fada ba,cikin bacin rai tayi gaba da sauri ta shige dakinta,batasan dai me hajjan tace masa ba,amma ta jiyo muryarta tana magana,saidai bata iya tantance me take ce masa.
23/10/2021, 08:38 – ๐๐ป๐๐ป: *KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พ,karki taba kayan daba naki bane,ba kuma mallakinki bane*
7
Saman madubi ta samu ta zauna cikin fushi ranta na wani irin suya
“Shifa ya haidar din nan rainin wayonsa yawa ne dashi,ya rainama mutane ajawali,meya daukemu ne?,duk laifin hajja ne,ai tasan bana hada shirgina dashi me yasa zata masa zancan matsalata,aikin banza kawai,don yaga mata na hauka akanshi snine hake raina ajawalin mata,koya dauka kowa baka yake,baisan suna mata suka tara ba,mtsewww……aikin banza kawai” a sarari tayi maganarta,kamar da wani a dakin take magana,taja tsaki tana gyara zamanta saman madubin.
Ji tayi xaman dakin gaba daya baiyi mata bama,gwara ta shiga cikin ‘yan uwanta ko zata samu sassauci,saita zaro gogagge cikin hijabanta ta saka ta zira silifas dinta ta fito.
Har yanzu yana zaune falon riqe da babbar abokiyarsa wato waya,ya wani miqe qafafunsa saman center table,gefansa furar da yace a kawo masa ce,ya ajjiyeta ba tare da yayi mata wani shan kirki ba.
Harta giftashi bai daga kai ba,sai data kusa qofar fita taji yace
“Ke!” Tasan da ita yake,dole ta dawo
“Ki tabbata gobe a makaranta kika kwana” abinda ya fada kenan a taqaice,dole ta amsashi da to,duk da kuwa ji take kamar ta rufeshi da duka saboda takaici,haka ta fita tana tura baki gaba,ita sam wallahi babu innamal din komawarta makaranta,so tayi ma ta laฦe da wannan ciwon taqi komawa gaba daya,don itakam gaskiya ta gaji,amma yana son rusa mata plan,to Allah yasa babu kowa a falon sanda ya fada bare a tilastata,shuru kawai zatayi da bakinta,suyita wasan buya harya koma hutunsa,tunda dak ai shima ba dawwama zaiyi ba,da wannan tunanin ta shiga sashensu salma.
A kitchen ta sameta tana kwabin doghnout,sosai taji dadin ganinta
“Gwara da kika fito ai,shi yana can wala’alla yana sha’aninsa keya barki kwance,dama yanzu nake cewa bari na gama kwabin nan naje na fiddoki,na kunna wayarki dazun naga kamar ma ya tura miki saqo” baki zahra ta tabe,tana jan daya robar kwabin ta tattare dogon hannun rigarta ta fara tayata tana cewa
“Can masa….gaba daya ma kamar Allah ya fidda minshi a raina,idan ma ya cuceni yaje shida Allah”
“Kawai yafi” daga haka suka shiga wata hirar,zahran na bata labarin abinda ya faru yanzu a falon hajjan,da kuma cewar da yayi lallai gobe ta koma makaranta
“Kinsan Allah ki rufawa kanki asiri ki tattara goben ki koma,kinfi kowa sanin halin ya haidar ko?” Salma ta fada tana dubanta
“Wallahi wannan karon saidai yaci kansa da kansa yasha baqin ruwa,don ni ko zan koma badai gobe ba ehe,ke saima anyi bikin huda dani” dariya salma ta danyi
“Zahra,zahra kafiya,to Allah ya kauda bacin rana”
“Amin” ta amsa mata,salman ta cire hannunta daga flower data gama kwabawar ta wanke a fanfo,tana goge ruwan a rigar jikinta tace
“Bari na dauko miki wayar” baki ta tabe ba tare data ce komai ba,salma ta juya ta fice.
Kafin ta dawo ta gama kwabin itama ta wanke hannunta,harta samu waje ta zauna,ta dawo ta miqa mata wayar tana cewa
“Ga saqon nan,duba ki gani”,still baki ta tabe kana ta sanya hannu ta karba din,ta buda saqon ga fara duba tsahonsa kafin ta koma farko da niyyar karantawa hafsa tayi sallama cikin kitchen din riqe da plate din abinci
“Gawa taqi rami,yanzu hajja tacemin aikin fito” murmushi tayi tana maida idonta kan wayar kana ta amsawa hafsa
“Ke kyaso na mutu tun yanzu?” Kai ta girgiza itama tana neman wajen zama
“A’ah ina fa…..salame zubamin miya don Allah inji umma,haka kawai suka mana tuwo da rana”
“Kya samu wata salamen ta zuba miki kuwa amma bani ba” dariya ta saki,tasan sarai bata son sunan
“Afwa tuba nake”
“Kina da hannu ai sai kizo ki diba” tashi tayi ta isa gaban tukunyar ta bude ta zuba miyar,daidai sanda zahra ta fara karanta saqon a fili
_assalamu alaiki,ina me neman afuwa da gafara daga gareki,nasan cewa na miki ba dai dai ba,amma tuntuni naso na samu lokaci mu tattauna kafin zuwan rana irin wannan amma Allah bai nufa,duk da haka ina mai baki haquri,ki sani matar mutum kabarinsa,kuma Allaj yayi keba matata bace shi yasa ban aureki ba,amma idan da hali kuma zai yiwu ki bani dama ki zamto mata ta biyu a wajena,ina dakon amincewarki_
_nuraddeen_
Wani ashar salma taso zundumawa sai kuma ta katse
“Lallai gayen nan yakai qarshe a rainin wayo”
“Tayani gani don Allah” inji hafsa tana kama haba,yayin da zahra ta saki wani murmushi mai ciwo,da kuma nuni da rainin wayon nuraddeen din ya bata mamaki,don daga haka ta zare sim din wayar kawai ta ballashi biyu ta watsa cikin sink din dake kusa dashi,ta kunna famfo ruwa ya korashi
“Na dauki tarayya ta dashi kamar mafarki,kuma ku saka hakan a ranku,mu shiga next chapter da Allah” ta fada cikin dakiya.
Shigowar yusra kitchen din shi ya tada sabon hira,haka nan suke da wuya kaga mutun daya shi kadai,saidai idan dukka basa gidan
“Na zaci munafuntata kukayi ai kuka zauna kuna wainar fulawa aka rasa me kirana”
“To ba ita akeyi ba kwaษai….” Dariya ta saki
“Allah qamshin manja na dinga ji,kuma naji kamar daga nan ne,kwanan nan sha’awar wainar fulawa nake wlh,mu kuma cikinmu an rasa me soyawa,kowacce sai tace idan ta soya ba zata iya ci ba,ai shikenan”
“Ni kinma tunamin” hafsa ta fada tana ane farantin data gama cin abinci
“Gidansu zainab ahmad din nan?” Tayi maganar da sigar tambaya tana side hannunta
“Eh” suka amsa a kusan tare
“Wallahi suna wainar fulawa da daddare,harda me qwai dame kifi,ke kinji dadinta kuwa?”
“Wayyo Allah,har kinsa yawuna tsinkewa,yaushe zamuje”
“Yauma idan da kudinki”
“Mu bari sai gobe,yau ya usama yamin alqawarin kyautar dubu daya gobe”
“To kuwa muna aljihunki” inji salma
“Allah ya kaimu” ta amsa musu,daga haka suka sake shiga wata hirar kafin kowa su watse.
Bata koma sassan hajja ba,saita wuce sassansu wajen umminta,tunda ta kwanta ciwon bata ganta ba.
A hankali tayi sallama falon nasu,ita daya ce zaune qasan carfet,gabanta da wata babbar baqar leda tana ta fiddo kayan dake cikinta,wanda suka hada dasu madara bournvita,Klein,corn flaks,sabulai,mayukan shafawa,turaruka,maclien,cream salad,suger na qananun jakankuna da sauran kayan amfanin gida na yau da kullum.
Kayan tabi da kallo sannan ta samu waje ta zauna
“Ummi ina yini?” Kai tadan daga ta kalleta kana ta maida ga abinda takeyi tare da amsa mata
“Lafiya lau,ya jikin naki?”
“Da sauqi alhmdlh”
“To Allah ya qara lafiya”
“Amin amin” ta amsa mata,sai shuru yadan biyo baya,wani lokaci ummin nata kaman tana mata halin fulani na kara da alkunya kamar na diyan fari,duk da cewa ba itace ta farin ba,amma itama abun ya shafeta.
“Haka abu kuma ya faru?,sai ki addu’a Allah yasa hakane yafi alkhairi” ta fada cikin yanayi na rashin bawa abun muhimmanci
“Amin” ta fada tana murxa yatsanta.
Bayan shudewar wasu sakanni ummin ta sake cewa
“Kinga irin hidimar yayanku,shi koda yaushe baya gajiya damu,kowanne lokaci alkhairinsa a tafe yake,ko iya hakan ya isa ya bayyanar da nagartarsa,fatana Allah yasa sauran ‘yan uwanshi suyi halinsa”
“Ba amin ba,kura ce da fatar akuya” ta fada a ranta,amma a fili don ta farantawa ummin nata sai tace
“Amin” a taqaice.
Ita ta taimakawa ummin aka raba kayan zuwa ma’ajiyarsu,kowanne abu aka sashi a muhallinsa,tadan jima ranar wajenta,ita kuma a fakaice tana jan hankalinta tare da sake nuna mata girman haidar din,sai da suka gama komai sannan tayi mata sallama gab da za a kira magrib ta baro sashen.
Daga nesa ta hangoshi can inda masu gidan dake da mota ko babur suke ajiyesu,tsaye jikin motarsa,booth din a bude ana fidda kayan ciki zuwa sassa sassa na gidan,baki tadan tabe kana ta nufi sassan hajja.
Canma raba kayan ta tadda hajjan nayi,ita da shafa’atu husna da amira dukka jikokinta ne,sai tayi wucewarta cikin daki,bata tsaya ba ta zarce bandaki,ta daura alwala,saboda gab ake da akira sallah.
Kamar yadda taci alwashi kuwa a washegarin bata gayawa kowa yadda sukayi da yaa zaki ba,sai tayi kwanciyarta luf a daki,wuni guda,hajja tana ta mita da yawo tsakanin falon da dakin kan ta fito,ko kuma jikinne?,saitace lafiya lau take,tana ramuwar baccin da bata samu yi ba,har hajjan dai ta haqura ta qyaleta.
Sai bayan sallar magariba su yusra suka shigo,kowacce sanye da hijabinta
“Zamuje gidansu xainab ahmad,na gayawa yayarta ta soya mana wainar gamu nan zuwa”inji yusra tana isa gaban madubin zahran gana gyara wuyan hijabinta,fuska ta yatsina,don batason fita bare suyi karo dashi,tasan haduwarsu ba zatayi kyauba,tunda ya bata umarni taqi ji
“Kuje kawai kwa tahomin da tawa,banajin fita”
“Ki tashi kawai malama mu wuce,babu mai miki dakon komai” tashi tayi ta zauna sosai tana duban yusran
“Kinsan fa akwai jagwal,ya haidar,banaso mu hadu,so nake har sai ya koma tukunna”
“Dazu naga fitarsa ma….ina jin wajen ya zahra ma ya tafi,kinsan ko ba yanzu zai dawo ba” inji hafsat dake gaban madubi tana shafa powder,jin hakan yasa ta miqe ta zaro hijabinta ta ware ta saka,ta sanya slippers dinta sannan suka fito.
Da kallo hajja ta bisu sanda suke fitowa daga dakin suna ‘yar hayaniyarsu,har sunyi gaba hafsat tadan dawo da baya
“Don Allah koda ya haidar zai tambaya ina ina kice kece kika aikemu” baki ta tabe tana dubansu
“Babu ruwan fadimatu zahra’u,ku qarke qalau”
“Hajja mu dake fa bata baci” ta fada tana dariya tayi gaba suka fice.
Kusan awa biyu suka kwashe,har kusan bayan isha’i sannan suka fito,suna tafe suna hirarsu har suka qaraso qofar gidan.
Salma ce a gaba,ita ta fara tura qofar gidan,da sauri ta dawo da baya har tana bige yasira
“Dalla meye haka…kefa kin fiya abun haushi wani lokaci”
“Ya haidar…..wallahi ya dawo,suna baranda shida dasu ya abu sufyan” sak kowaccensu tayi,aka koma kallon kallo tsakaninsu,aka rasa me magana har tsahon wasu sakanni.
Zahra ce ta soma jan tsaki,sannan ta soma yin gaba tana jan hannun hafsat
“Tsoron wai na meye,muje don Allah,fuska kawai xamu masa” qarfafa musu gwiwan da tayi yasa suka soma takawa zuwa ciki.
Zaratan samari ne guda hudu saman wasu fararen kujerun roba,aliyyu na biyar dinsu,dan qaramin teburi ne a gabansu dauke da lemuka da cups,sai dan qayataccen qaramin flask din tea da kofunansa.
Kana dubansu xaka gane akwai abinda suke tattaunawa,saidai aliyyun kacokam hankalinsa nakan wayarsa kamar kullum,lokaci lokaci yana dan sanya bakinsa ba tare daya daga kanshi daga wayar ba,hakan yasa sukaji dadi,sannu a hankali suka fara takawa zasu wuce zuwa sashen da yafi kusa dasu.
Kaman an umarceshi ya daga kansa,idanu biyu sukayi dasu,take kowacce tasha jinin jikinta,yayin da zahra ta fara qoqarin boyewa sosai ta bayansu yadda bazai iya ganinta ba.
Sunan hafsa ya kira,ta amsa kana cikin hanzari ta nufi inda yake,bata wuce sakan biyar ba ta dawo
“Ya haidar yace kuzo” ta fada tana narai narai da ido muryarta na rawa,tilas suka taka zuwa inda suke zaunan,suna hangoshi daga inda suke yana ci gaba da danna wayarsa,yayin da sauran abokan nasa suka dakata da maganar da sukeyi din,wasunsu suka dauki drink suna sha,wasu kuma suka tsiyaya black tea.
“A’ah,yammata…..daga ina haka?” Daya daga cikin abokan nashi mai suna saif ya fada cikin sakin fuska,kasa amsa masa sukayi,sai suka maye gurbin tambayar tashi da gaisuwa cikin sanyin murya dake nuna tsoro,ba wadda ta isa tayi gigin yin wani abun da bai dai dai ba,don dukkansu sun haddace dokokinsa da abinda bai dauka,suna girmama abokanshi sosai kamar yadda suke bashi girma,saidai akwai dan bambanci,kusan sunfi sakewa dasu fiye dashi,don a cikinsu akwai masu sakin fuska ba kamar shi ba.
Shanyasu yayi suka ci gaba da hirarsu,wanda mafi akasari abinda ya shafi aikinsu ne na soja,a qalla sun kusa awa guda a duqe qafafunsu har soma tsami,sai da daya daga cikin abokan nashi qasa qasa yace
“Man,ka ajjiye mutane fa,ka sallamesu idan baka da abun cewa” tsaki yaja yana gyara zamanshi,ya sauke qafarsa da tun dazun daya ke saman daya ya zauna sosai kamar wani saraki sannan ya jefa musu tambayar daga ina suke,cikin rawar murya hafsa tace
“Hajja ce ta aikemu nan baya….”
“Kunci sa’a ta gayamin,amma daga yauu….kada ku sake na sake ganinku kamar i yanzu a waje….ku bacemin a gun” da sauri dukkansu suka miqe,hakan ya sanya ta manta da cewa boye masa take ta miqe itama da sauri.
“Ke!…zonan” ya fada da wani dakakken sauti daya sanya cikinta bada wani sauti na quuuu,ko ba’a fada ba da ita yake babu neman qarin bayani
“Ba daku nake ba…..ku bace daga nan kafin na tashi” ya baiwa sauran umarni,hakanan tana ji tana gani suka wuce suka barta.
A hankali take takowa zuwa inda suke kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,duk yadda taso baiwa kanta qwarin gwiwa amma ta kasa tattaroshi,batayi tunanin zai ganta ba sam
“Kina cikinsu dama zahran hajja?” Daya daga cikin abokan nasa mai suna fahad wanda sai yanzu yayi magana ya furta,wani kallo aliyyun ya watsa mishi kafin ya maida dubansa a kanta yana jifanta da wani kallo yace
“A ina nace miki yau ki kwana?” Shuru kamar ba zata amsa ba sannan tace
“Makaranta”
“Da kyau!,me kike a gida yau din?”
“Babu komai”
Kanshi ya gyada shuru na wasu ‘yan mintuna,sannan ya zira hannunshi a aljihu ya ciro key din mota ya wurga mata
“Ki cewa labaran ya kunna miki ruwa ya baki mesa” muqullin tabi da kallo tana maimaita abinda ya fada cikin qwaqwalwarta.
Ta fahimci abinda yake nufi tsaf,wato taje ta wanke mishi mota kenan koko yaya?,so yake ya disgata gaban abokanshi,data sake daga kai ta kalleshi ya maida qafafunsa yadda suke yaci gaba da sabgarsa.
Tsam ta miqe riqe da muqullin ta juya ta soma takawa
“Fahad…..kana so ka jawa mutane raini wajen yaran nan,na gaya maka tun ba yanzu ba banaso ko?” Ta jiyoshi yana fada cikin miskilanci,sai taja qaramin tsaki tana tunanin aikin daya sanyata yanzun,kuma tabbas yana hangota indai motarshi da take hangowa muqullinta ne a hannunsa,bama shi ba har duka abokan nashi suna iya ganota…..
_kuyimin afuwa jina shuru kwana biyu,hidima ce ta biki ta riqeni,naso muku bayani amma hakan bai samu ba,Allah yayi mana jagora_
23/10/2021, 08:38 – ๐๐ป๐๐ป: 8
*KU MATSO MAZA KUJI LABARIN*
*_Oumahmad collection’s_*
*_Shin kina buqatar waje daya tattare dukkan abubuwan buqata da kike son saye ba bata lokaci ko rarraba waje?_*
*to ga OUMAHMAD COLLECTIONS*
*_wadanda ke saida_*
_kayan kitchen_
_kayan sawa nau’i daban daban_
_jakankuna da takalma ‘yan ubansu_
_wayoyin hannu kala daban daban na zamani_
_mayafai na gani na fada_
_kayan sawar yara na alfarma_
_kayan daki daga qasashe daban daban,irinsu dubai,china,India,turkey,Malaysia_
_ADRESS DINSU_๐๐ฝ๐๐ฝ
*_Kano hotoro_*
*Ko ku dubasu a facebook da sunan*
*_Maryam muhd_*
*Ko kira kai tsaye ta lambar waya kamar haka*
07014488636
*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ
__________________________________
*KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พ,KARKI TABA ABINDA BA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*โโโ
Kamar yadda yace bata fasa ba ta isa wajen labaran din,ta kuma buqaci ya hada mata famfon kamar yadda aka saba idan za’a wankewa wani cikin gidan mota,sai daya gama ta kalleshi
“Ance ka bani klien”
“Ah’ah….ai indai motar yallabai Aliyyu za’a wanke yana da carwash dinsa da ake wanke masa dashi,bari na dauko miki” har ya juya zai tafi ta dakatar dashi da sauri tana cewa
“Klien yace a bani,shi zaka daukomin” jimm yayi kadan sannan ya gyada kanshi yayi gaba,babu jimawa ya dawo dashi ya miqa mata,ta bishi da kallo har sai da taga bacewarsa sannan ta taka zuwa wajen mai musu aike aike cikin gidan,wanda wani lokaci yakan zauna a gidan na wasu kwanaki idan yana da ayyuka da yawa har zuwa sanda zai ragesu kana ya tafi gidansu
“Soson qarfe nakeson ka bani aro don Allah hayatu” ta fada tana dan waigawa taga yana ganinta?.
Ba tare da tunanin komai ba ya shiga ciki ya dauko ya miqa matan,ta karba tana jin dadin samun soson sannan ta durfafi motar tana qwafa,gami da qiyasta irin barnar da zatayi masa,yau saita fanshe dukka haushinta akan motar,koma me zai faru ya faru.
Sosai ta zambada klien cikin wani ruwa dake cikin botiki,saboda taji ance ba’a wanke mota da klien,don tana kodar da fentinta,to ba motar ba,shi kansa me motar da zata iya saita kodar dashi,taga kya da gayun da yakewa taqama,kamar wani yafi kyau,itakam ta tsani yadda mata ke kodashi,tana ganin kamar suke tunzurashi ma suke yake sake jin kansa wani,kofi ta ciko ta miqe da niyyar soma watsawa motar
“Zahra’u” taji an ambata sunanta daga bayanta,saita waiwaya,abba babba ne,riqe da maqullin mota da leda a hannunsa
“Na’am abba?….sannu da zuwa” kai ya gyada
“Yauwa….me zakiyi da ruwa kika tarashi haka kamar zakiyi wankin mota” saita marairaice sosai,ta sani cewa mafita tazo,duk da tana son taga ta bata wannan ‘yar kyakkyawar motar taga ta tsiya,duk da ta sani ba abune mai sauqi ba,hakan zai iya janyo mata tsatstsauran hukunci daga wajensa,amma ita duk ba damuwarta bane wannan
“Ya Aliyyu ne ya sakani wankin motar” ta fada tana wani sunkui da kai
“Haidar dai?” Ya tambaya cikin mamaki,saiya gyada kai kanta a qasa
“Wannan wanne irin shirmen banza da wofi ne……mace da wankin mota?,ina shi haidar din?” Saita nuna mishi inda suke zaune shi dasu abu sufyan,duk da yanzun shi ya miqe tsaye ya basu baya yana amsa waya,murya ya daga ya kirayi sunanshi,dukkansu hankalinsu ya dawo wajen,sai suka miqe gaba dayansu suka nufo abban.
Cikin girmamawa suka gaidashi sannan suka koma suka barshi da aliyyun,juyawa yayi inda zahra ke tsaye ta baza kunnuwa taji ya zata kaya,ya miqa mata ledar hannunsa
“Qarasamin da ita wajen hajja” hannu biyu tasa ta karba sannan ta juya zuwa sassan hajjan,taso ace a gabanta abban zai masa fadan taga ya zaiyi,amma ko hakan ma ai tasha dashi,tunda ba haka yaso ba.
Dukka suna sassan hajjan kowacce tayi tsuru tsuru,tana ajjiye ledar suna cikata da tambayar yata kaya tsakaninsu,sunga ta dawo da wuri,sai data samu waje ta zauna sannan ta gaya musu yadda akayi,dariya harda masu saukowa daga saman kujerar
“Gaskiya na yadda ya haidar qarshe ne” yasira dake qyaqyata tata dariyar ta fada,cikin dariyar salma ma tace
“Lallai kice ya samu babbar mawankiyar mota,ai kawai a soma biyanki cikin gidan nan an huta biyan su labaran,to wallahi Allah ya qwaceki abba ya qwaceki,don da kin sake kin masa wankin mota da sosan qarfe kashinki ya bushe a gidannan,ke kinsan kudin wannan motar kuwa?” Kafada ta daga cikin rashin damuwa
“Oho,koma nawa ce ai shi ya janyo,haka kawai gaban abokan nan nashi masu shegen ji da kansu da isa saiya yarfani saboda ya raina mana ajawali”.
Suna tsaka da wannan hirar abban ya shigo,kowacce ta masa sannu da zuwa suka fara qoqarin fita bayan hajja data fito daga daki yanzun ta iso falon,dakatar da zahra yayi,ta qaraso gabansa ta durqusa
“Ya akayi yayanku yace ki koma makaranta amma baki koma ba?” Marairaicewa ta sakeyi
“Abba bani da lafiya ne shi yasa ban koma ba”
“Amma kuma aikin warware ko?,yace ya tambayi hajja?” Bata da ikon musawa tunda ya taddasu ana wasa da dariya da ita,da alama boarding ta aureta kenan har sai ta gama,don haka saita gyada masa kai
“Shikenan,zuwa gobe da safe ki sake gyara abinda baki gyara ba…..nasa ya maidaki” batasan sanda ta daga kanta ba tace
“Wa?”dan kallonta yayi sai kuma yace
“Yayan naku” sai kuma taji nauyin hakan,don haka bata sake cewa komai ba ta amsa da to,sannan kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta wuce zuwa daki,yayin da hajja ta bita da kallo harta shige.
“Har yanzu uwata batason makarantar nan hajja” nannauyar ajiyar zuciya hajja ta saki sannan tace
“Damuwar data shiga na jin cewa Aliyyu ne zai maidata…..yafi damuwar komawarta makarantar yawa…..bansan wanne irin nau’in rashin jituwa bane tsakanin inna wuro da haidar ba” shima ajiyar zuciyar ya saki a boye yadda ba zata jishi ba,sam basu son abinda zai taba ran tsohuwar ko ya bata ranta sam sam,don haka cikin salon son kwantar da hankali yace da ita
“Quruciya ce ke dawainiya da dukkaninsu,wataran zai zama labari” dan qaramin murmushi ta saki tana kada kai
“Haba muhammadu…..idan kace innawuro quruciya ce na yarda shi kuma haidar fa?”
“Sai muyi addu’ar samun jituwa tsakaninsu ai hajja” kai ta gyada
“Hakane….don babu abinda ya gagari addu’a”
“Wannan haka yake” ya fada yana janyo ledar daya bawa xahra ta shigo masa da ita.
Washegari qarfe shida na safe ta gama shirinta gaba daya,saidai tana ta faman kumburi saboda wanda zai kaita,qarfe bakwai tana falon hajja tana karyawa da kayan karin da hajjan ta tashi da wuri ta hada mata don kada ta tafi da yunwa.
Shamsuddeen ne yayi sallama falon hannunsa riqe da maqullin mota
“Baki gama shiryawa bane?” Ya tambaya bayan ya gama gaida hajja
“Kai zaka kaini?” Ta tambayeshi itama
“Eh….ya haidar yace na kaiki” baki ta tabe,ita hakanma yayi mata dadi,don haka ta qarasa abinda bata qarasa din ba cikin hanzari,tayi sallama da duk wanda ya dace sannan suka wuce.
Komawarta makaranta duk data koma da tabon nuraddeen cikin zuciyarta amma hakan bata bari yayi mata tasiri ko ya hanata karatu ba,ta tattara hankalinta kacokam kan karatunta,musamman da suke shirye shiryen fara zana jarabawar qualifying,duk da cewa batason makarantar amma shima bata bari ya hanata karatu ba.
Wata iriyar baiwa da basirar karatu Allah ya bata,tana da qwaqwalwa sosai,wanda hakan yasanya tayi tasiri sosai a zuciyar malamai da kuma daliban makarantar ma gaba daya.
Sannu a hankali lokaci ya dinga juyawa yana tafiya da wani sauri da kuma hanzari,wanda yakan fauci abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bayi yayi awon gaba dasu,wasu tare da saninmu wasunsu kuma ba tare da saninmu ba.
‘Yan kwanaki ya rage musu su fara zana jarabawar suka samu baquncin sabbin malamai da aka sauyasu da wasu malaman dake koyar dasu wasu darussan,ciki kuwa harda malamin da zai dinga koya musu yaren turanci wato english,saidai su dinma na wucin gadi ne,sunzo ne sakamakon horaswa ta musamman da wadancan malaman suka samu damar zuwa suyi na wasu watanni.
*_ALฦIBLARSU_*
Malam nasir,matashin saurayi,ma’abocin iya ado gayu da kuma jan aji,uwa una qwarewa da gogewa wajen iya yaren turanci,wanda tun farkon zuwansa shine abu na farko daya soma jan hankali dalibai mata da dama dake cikin makarantar a kansa,yadda yake da gwalli ya hade da qwarewarsa wajen iya turanci,sai hakan ya zame masa tamkar ado,yana da jan hankali da kuma daukar hankalin kamar mace,da dama daga cikin ‘yammatan makarantar yana burgesu,yayin da shi kuma izzar sa tasa bai duban kowacce mace cikin makarantar,har zuwa ranar da Allah ya qaddara haduwarsa da zahra,shigarsa a jinsu na farko,a lokacin da suka fara extra lesson saboda jarabawar dake gabansu.
A ranar ta tashi da ciwon mara,wanda a baya ita sam bata sanshi ba,bata taba yi bama sai a lokacin,haka ta dinga daurewa saboda nacinta da karatun,da kuma burin samun sakamako mai kyau,duk da cewa hasina tace da ita ta zauna,bata da matsala tunda ita zata je amma ga qiya.
Zuwanta ajin saita kasa hasala komai,hakanan ta kifa kanta saman table din da take kai tana jin yadda mararta ke zugi.
Tana iya jiyo sautin sallamar malamin,tashinsu da gaidashi da sukayi,yadda ajin yayi dif sanda yake zagaya daliban,ya tsaya gefan table dinta yana tambayar wacece wannan?,bata jin zata iya dagowa bare ta amsa mishi,tana jin sanda hasina dake gefanta ke masa bayani
“Allah ya sawwaqe” ya fada yana barin wajen bayan ya basu umarnin zama,sannan ya isa gaban allo ya fara aiwatar da abinda ya tarasu.
Rabi da rabi takejin komai,har zuwa sanda jin da zaman saman teburin ya gagareta,ta fara nishi saboda ciwo,wanda ya fara jan hankalin hasina kafin kuma sauran daliban zuwa malamin su ankara,shi ya bada umarnin hasina da wata hasana jibril su dagata su kaita a bata magani,sai a sannan da suka dagata yaga fuskarta,ya kauda kai bayan sun fice yaci gaba da yiwa sauran daliban karatu.
Kwananta uku kafin ta samu sauqi,ranar da zata koma shiga lesson din,da yammacin ranar suna shirin tafiya,ta fuskanci yadda daliban kowa keta qoqarin hada wani assigment wanda batasan na meye ba,saita dubi hasina dake zaune gefan gadonta riqe da nata assigent din tana sake dubawa
“Wai aikin me aka baku,naga kowa hankalinsa a tashe?” Rufe littafin tayi tana murmushi,ta daga kai ta dubi zahra
“Wallahi malamin nan zahra ya hadu tako ina,mugun kaine dashi,da alama yana ja sosai,ga gayu ga iya koyarwa” baki zahra ta tabe tana saka hijabinta
“Nifa ba wannan na tambayeki ba hasina” murmushi ta sakeyi
“Ko baki tambayeni ba ai dole na gaya miki,aikin daya bamu yace zamu iya cin karo dashi a jarabawarmu,zai gani ya zamuyi dashi idan mukaci karo da tambaya makamanciyarta,shine ya bamu yace mu gwada,bari ki gani” bude mata tambayar tayi tana mata bayani iya yanda ta fahimta tsahon wasu mintuna,murmushi zahra tayi bayan ta gama bayanin,saita koma ta zauna,ta jawo jakar litattafanta ta ciro littafi da biro,dai dai sanda hasina ta miqe
“Mu wuce zahra,naga an fara tafiya”
“Jeki kawai zan taho” ido ta fidda
“Kai…wallahi ya hana,yace kowa ya tabbatar yana rigashi shigowa”
“Kije yanzu zan qaraso”
“Idan ya hanaki shiga ke kika jawa kanki,nidai nayi gaba” ta fada tana qarasawa cikin wadanda basu kai ga tafiya ba suka rankaya suka fice tare.
Da sallama ta shiga ajin wanda ya cika da dalibai,malamin dake gaban dan tebur da kujerar zama ta malamai,saidai shi yana tsaye ne bai zauna ba ya waiwayo yana amsawa,dubanta yake ganin tana qoqarin shigowa,fuskarsa a hade yace
“Dakata….ina zaki?,ban hanaku zuwa a irin wannan lokacin ba?”
“Malam kayi haquri…..saida na tsaya nasha magani ne”
“Baki da lafiya?” Ya tambayeta yana dubanta,kanta a qasa ta gyadashi
“Eh,yau kwana uku ban taba samun lesson dinka ba,sai yau na samu sauqi” a sannan ya gane itace,ya tuna fuskarta,don haka yace
“Allah ya qara afuwa…..wuce”
“Na gode sir” ta fada cikin farinciki sannan ta wuce zuwa mazauninta.
Karatu suka ci gaba dayi,ta bada dukkanin attention dinta ga malamin,shi dinma ya fuskanci hakan,don haka saiya zamana karatun kamar da ita yakeyi,saboda kusan dabi’ar malami ce,bada hankalinsa ga dalibin daya fuskanci yana fahimtarsa yadda ya kamata.
Eh tabbas hasina batayi qarya ba,ya iya karatu ya iya koyarwa kamar yadda tace,hakanan taji dadin karatun na yau sosai,ta kuma qaru sosai.
Sai daya gama ya fara amsar aikin daya basu din,da kansan yake bin teburin kowacce daliba ya amsa littafin,ya tsaya a wajen ya duba sannan yayi mata marking ya wuce na gaba har ya qaraso nata teburin,ganin zai wuceta saboda tsammanin batayi aikin ba yasa tayi saurin miqa masa nata littafin,sai daya kalleta sannan ya amsa littafin,ya dawo da baya zuwa wajen mazauninta ya bude ya fara dubawa.
Lokaci lokaci yana daga kai daga littafin ya dubeta harya gama karantawa,saiya rufe littafin kawai ya riqeshi a hannunsa ya wuce teburi na gaba,hakanan taji babu dadi,ko bata rubuta dai dai bane?,tasan iya bakin qoqari tayi wajen ganin tayi assigment din daidai duk da bata zo ba a sannan,mutum ce ita da bata bari assigment sam ya wuceta,saboda tasan hanya ce ta sake samun wani sabon ilimi ga dalibi,hasina dake gefanta qasa qasa tace
“Hala baki rubuta dai dai bane?” Kafada ta daga cikin damuwa
“Ban sani ba nima,ina jin dai hakane” daga haka suka bar maganar harya gama duba na kowacce daliba ya koma gaban allo ya tsaya.
“Fatima sa’id dabo” ya fada yana karanta sunan daga jikin bangon littafin nata
“Yes sir” ta fada tana miqewa,ya kalleta sosai sannan ya mata umarni ta fito gaban aji.
Littafin ya bata yace ta karanta abinda ta rubuta ta kuma yiwa ‘yan aji explanation,cikin sanyi jiki ta karba,tana nauyin kada ace shirme tayi,hakanan ta baiwa kanta qwarin gwiwa ta soma karantawa tanayin bayanin kamar yadda ya umarceta,yayin da shi kuma yaja gefe daya ya tsaya jingine da bango yana qare mata kallo,yanajin tana wani birgeshi haka kawai.
“Sauran qarin bayani ga wanda bai gane ba kuma….saiya tambayi sir” ta gama bayanin nata da fadin haka,kana ta maida idanunta kansa,sai suka hada idanu,janye idanunta tayi sanda yake sakar mata murmushi ya tako a hankali ya soma tafa mata yana fadin
“Very good fatima…..every body clap for her” take ajin ya rude da tafi,saida suka tsagaita sannan yace
“Wannan shine karatunmu nayau gaba daya fatima ta gamashi,assigment dinta koni iya abinda zan rubuta kenan,ta dace da class captain….kuma itace headgirl dinku da zarar kun shiga ss 3” da wannan bayanin nasa aka tashi daga aji ranar.
Tun daga lokacin sai ya zamana ya ganeta sosai fiye da zatonta,yakan kama sunanta sau tari idan suna karatu,hakanan itama takanyi tambaya har kan abinda bashi suke karantawa bama saboda qaruwarta,hakan yasa sabo yadan soma shiga tsakaninsu,hakan yasa ta soma samun abokan adawa daga ajinsu dama ajin sama dasu wato ‘yan ss 3,wadanda keda muradin nasir din.
Randa wata mardiyya taso takalarta da fada akan sir nasir din abun mamaki ya bata da dariya,don itadai tasan babu komai tsakaninsu daya wuce alaqar malami da dalibi,saitaqi biye mata,ta dinga dariya kan abinda ta fada din,saidai kafin sukai ga rubuta jarrabawa su tafi gida hutu tuni ya bayyanar mata da soyayyarshi.
Da farko tayi dari dari da abun,saboda wasu dalilai da suka hada da dokar makaranta,tsoron abinda ya faru tsakaninta da nuraddeen da kuma sa’idon dalibai,amma daga baya data zauna tayi nazari,ta fuskanci dukka halaye da dabi’un malam nasir din masu kyau ne,sannan ita kanta bawai bata sonshi ba kamar yadda ba zata ce wai tana sonshi kai tsaye ba,amma a qalla a yanzu suna gab da shiga ss 3,wanda ba zasu wuce wata 9 ba zasuyi candy,kuma kafin suyi candy dinne kowacce wanda zata aura zai gabatar da kanshi da magabantansa asan dashi,suna gama makaranta kuma sai maganar aure,tana ga mafi kyau shine ta bashi dama su fukanci juna,ba lallai abinda ya farun ya kuma maimaita kanshi,da wannan tunanin ta soma dan bashi dama kadan,duk da ta gaya masa abu mafi kyau ya bari suyi hutu ta koma gida tukunna,shima hakan ya masa,saboda haka bai zura jiki da yawa ba,ya bari har zuwa sanda suka gama jarabawar suka koma gida sannan ya fara kafa kanshi a zuciyar zahra din.
Cikin wani lokaci taqaitacce ya samawa kansa wajen zama,saboda mutum ne daya qware wajen iya tsara lafazi da iya jan hankali,uwa uba kuma iya ado,yana da faran faran,sa’annan da kansa ga buqaci ya gaisa da hajja tukunna kafin su abba,ta bashi dama suka gaisa,sai gashi cikin lokaci kadan kamar sun dade da hajjan,saboda ita dinma tana da son jama’a da saurin sabo.
Abinda yasa ta kuma sakewa dashi shine,akwai sanayya tsakaninsa da salim dan abban gwammaja yayan umminta,bai kuma fadi wani aibu ko mummunan hali tattare dashi ba,hakan yasa ta sake jin cewa ta samu abokin rayuwa kamar sauran ‘yan uwanta……
_to masu karatu…..ya zata kaya?,muje zuwa,mu hadu gobe da izinin ubangiji_๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ
23/10/2021, 08:38 – ๐๐ป๐๐ป: 09
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
_____________________________
*_BAYAN SATI BIYU_*
Karfe goma na safe ta kammala duk wani aiki da xata yiwa hajja,kasancewar idan tana nan ita da baba gaje suke mata duk wani aiki,koda taje da niyyar yiwa umminta wani abu takance ta bari taje ta yiwa hajjan,ita ilham zatayi mata wato qanwarta.
Tana gaban madubi tana shafa ma take tunanin zuwa gidan abban gwammaja wajen hasina,amma kuma daxun sir nasir yace mata zaya zo ganinta,tana mamakin yadda baya gajiya da jinta ko ganinta,har kunya yakan bata wani lokaci,ta samu tattali da kulawa wadda ta dara ta nuraddeen,sai a yanzu take ganin ma nuraddeen kamar shidin ba komai bane bai iya komai ba akan nasir din,ita kadai wani lokaci idan ta tunashi da kulawarsa gareta takan saki murmushi.
Cikin doguwar rigar swiss atampha cotton ta shirya mai yarfin stone a jiki,tana tsaka da fesa turare bayan ta taje gashinta ta daure wanda takeson hasina ta mata kitso taji hajja na qwala mata kira,saita aje turaren ta dauki dankwalinta a hannu ta fito.
Ita da abban tsakiya ne,sai haidar dake kallon labarai a VOA,yadda sojoji suka samu nasara a jahar borno cikin satin kan yaqi da ‘yan ta’addan boko haram yana kuma magana da abban tsakiyan.
Da sauri ta ware dankwalinta ta daura tana qarasawa inda suke,Allah yasa bai ganta ba,shida abban ta gaida sannan ta maida hankalinta ga hajja dake mata bayanin
“Hadowa Aliyyu abincin kari maza da sauri…..” Daga haka ta waiwaya tana mita
“Ku hakannan kuke bakuson cin abinci musamman da safe,koda yaushe sai an tilasta muku kuke ganewa….tafiya daga nan har dawakin kudu amma ciki babu komai,haka zaka tuqa iyayen naka kaje ka kasa qarasa tuqin saboda yunwa……tsabar zumudin zakayi sabon aure?” Kansa ya shafa yana cewa
“Kamar ba namiji ba?,karki.manta soja nake hajja…..nakan iya kwana uku banci ba wani lokacin sama da haka ma idan wani aikin ya taso mana”.
Baki zahran ta tabe tana shigewa kitchen,cikin ranta tana fadin
“Ni ki qyaleshi kawai hajja ya tafin haka….yanzu da wahala yaci abincin nan baice wani abu ba akai sarkin qaqale” haka nan ta hada musu abincin daidai yadda zai ishesu shida abban tsakiya,ta isa falon ta dire musu tayi komawarta daki.
Bata sake fitowa ba sai da taji alamun fitarsu sannan ta fito riqe da mayafinta,sai data shiga kitchen ta hada kayan nata karin sannan ta dawo falon ta zauna kusa da hajja,tana tsaka da cin abincin hajjan tace
“Ina tunanin kafin ku koma makaranta fa iyayenku zasu nemi ganawa da magabatan samarinku,saboda yayanku ya tada maganar aurensa,yanzu haka can suka nufa garinsu yarinyar” duban hajjan tayi tana cin abincinta
“Shi zai kaisu da kanshi kenan?”
“Eh” ta bata amsa tana dauko remote don ta canza tasha,saita tabe baki
“Ey…da yake shi idanunsa da kwalli ai ba laifi bane,inda kaine da ka shiga uku” duka hajjan ta kai mata ta kuma sameta,ta gantsare tana cewa
“Wayyo Allah na…..hajja saikin karyani tukunna?”
“Eh gwara ai na karya ki din….tunda ke baki gajiya da dan banzan qorafi,zancan da ake miki daban wanda kike daban”
“Shikenan tunda haka kika ce,kullum nice me laifi” daga haka ta miqe da farantin a hannunta ta wuce kitchen tana zumbura baki,ta ajjiye sannan ta fito ta yafa mayafinta
“Zan wuce hajja” tayi maganar da alamun jin haushi har yanzu akan fuskarta,kudi hajjan ta miqa mata tana gaya mata kada tayi dare.
Kamar yadda hajjan tace kuwa a ranar akaje dawakin tofa dangin mahaifiyar Aliyyu haidar ko ince zaki aka tambaya masa aurenta hannun iyayenta da suke kawunnai a wajensa,mahaifinta qanine ga mahaifiyarsa,ba tare da wani bata lokaci ba aka basu auren,tunda shima kamar d’a ne a wajensu,suka dawo cike da farinciki da murnar yadda akayi komai cikin girma da karamci.
Washegari abba babba ya bada sanarwar kowacce cikinsu ta yiwa maneminta magana,indai da gaske yake yazo ya gabatar da kanshi tare da magabatansa,don suna so nan da shekara daya su hada su duka a aurar,mata biyar namiji daya.
Ba bata lokaci ta shaidawa sir nasir,wanda ya bayyana murnarsa sosai fiye da zatonta,don har mamaki ta dinga yi yadda yaketa farinciki,kusan ma kamar ya fita so da daukin abun,ya kuma tabbatar mata idan basu zama na farko ko na biyu a zuwa ba…..to ba zasu zama na uku ba.
Saurayin salma shi ya fara zuwa rana daya dana yusra,bayan kwana biyu saurayin yasira da magabatansu sukazo,washegari na hafsat ya bayyana shima,a ranar ne zahra ta karbo wayarta daga gyara,wadda ta matsu qwarai ta gyara din,don tafi kyautata zaton rashin wayar ne ya hana zuwan sir nasir kamar yadda yayi alqawari,tana jonawa a chargy ta lalubo number dinsa ta kira.
Bugu daya ya dauka,sai daya saki ajiyar zuciya sannan yace
“Kin wahalar dani fa”
“Me nayi kuma?”
“Kinsan tafiya ce ta kamani zuwa garinsu mama bagtatan….sai da muka dauki hanya na dinga kiranki ban sameki ba,yanzu haka ina kan hanyar dawowa….dama cewa nayi indai harna sauka ban sameki ba gida kawai zan zarto nan na ganki,idan ba haka ba nasan naci qarya yau na iya barci” murmushi ta saki cikin jin dadin kalamanshi
“To ai gashi na kiraka,nima shurun ya bani mamaki ya kuma daga min hankali”
“An rigani zuwa kenan?,nida naci burin na zama mutum na farko saboda girmamawa a gareki….amma duk da haka bata baci ba” hira suka fara daga haka,a qalla sun kusa kwashe awa daya sannan sukayi sallama,da zummar gobe zai shigo da magabatan nasa,idan yaso ya ganta gaba daya.
Kunya yasa ta rasa yadda zata shaidawa su abban cewa nasir din zaizo,sai da gari ya waye taga indai bata fada din ba zasu fice harkokinsu,dabara ta fado mata ta shaidawa hajja,ita kuma ta gaya musu.
Saidai tana shiga falo da niyyar wucewa dakin hajjan saboda bata kai ga fitowa ba wayarta dake hannunta ta dauki kuwwa,ganin sunan nasir yasa ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana amsa wayar.
Tun daga sallamarsa taji alamun muryarsa ba daidai take ba,kafin takai ga tambayarsa shiya tambayeta
“Kin gayawa su abba zuwan namu ne yau?” Kai ta kada
“A’ah,yanzu dai nake shirin gaya musun” saiya sauke ajiyar zuciya mai nauyi,cikin alamu na damuwa tace
“Lafiya?”
“Fatima…..wallahi tun jiya nake fama da mama kan maganar….ashe turani garinsu da tayi akwai yarinyar data turawa ni wata na’ima….tunda naje yarinyar take rawar kai a kaina take kuma dawainiya dani,ni ban kawo komai ba sai yanzu dana dawo na kawo wannan maganar mama da abba duka sukace basusan zance ba,sun turani naga na’ima ne don mu hada kanmu”.
Kasa magana zahran tayi,tayi shuru kawai tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,gabanta ke faduwa
“Fatima….bana gaya miki wannan maganar bane don ki saka damuwa cikin ranki ba,na gaya miki ne don kada muyi jinkiri wajen zuwa ki zaci wani abu na daban….ba abun damuwa bane,nasan yadda zan shawo kan mama in sha Allah….kuma zanzo na samu abba nayi masa bayanin komai”
“To” abinda ta iya furtawa kenan a sanyaye,sallama tayi masa da kanta,don bata da qwarin gwiwar ci gaba da hira dashi,saita zame ta kwanta kawai cikin wani irin yanayi data kasa tantance wanne iri ne,bata fatan fa rasa nasir sam,saidai kuma tanajin tsoron faruwar hakan can qasan ranta.
Sannu sannu kwanaki suka soma shudewa,nasir yaci gaba da zuwa….ya kuma ci gaba da kiranta a waya kamar yadda suka saba,saidai bai sake tada wancan zancan ba,hakanan maganar ganin abba ma bai kuma tada ita ba,itama bata kuma ce masa komai ba,bata sake tada maganar ba,tana gayawa zuciyarta cewa yana qoqarin sanya mamanshi ne ta amince,tana tsoron ma a tada maganar ya zama silar rasa sir nasir kenan a wajenta.
To daga gida ma ba wanda yayi mata maganar nata manemin,baya ga hajja data yi sau daya,ta kuma yi mata bayanin cewa yana sane zasuzo,ya shaida musu yana jiran su saka rana ne su magabatan nasa.
Ta sani cewa tana da alfarma wajen iyayen nata,sabida tausayawa maraicinta da sukeyi,shi yasa basu matsanta mata kan maganar ba,hakan yasa hankalinta yadan kwanta kadan,a haka har suka koma makaranta,suka kuma shiga ss 3 ajin qarshe na makarantar secondry,wanda abubuwa da dama sun faru,ciki harda bata muqamin shugabar dalibai,bunqasar soyayyarsu da sir nasir,harda kuma kammala abinda ya kawoshi makarantar shida sauran malaman,saboda dawowar malamansu na asali suka miqa musu aikinsu,wanda hakan ya farune saura wata guda su tafi hutun first term.
Randa zai bar makarantar ta shiga damuwa sosai,shi ya ringa lallashinta a inda ha nemi ganinta
“Karki damu mana,saura sati hudu kacal ki taho gida kici gaba da ganina,sannan zanyi qoqari kafin ki koma wannan hutun naga su abba a daidaita maganar aurenmu” da haka ya samu ta rage damuwarta,sannan yayi mata sallama suka rabu cikin kewar juna.
Sati hudun kuwa na zuwa suka fara jarabawa,suna gamawa sukayi gida hutu kamar yadda aka saba sai gida,saidai ko bayan sun koma dinma dai shuru shuru zancan turowar tashi,saidai suna waya kamar yadda suka saba dashi.
*_04:30 pm_*
Kwance take a falon umminta ita daya,babu kowa daga ita sai ilham wadda zahran ta aikata kitchen ta juya mata miyar data dorawa ummin tata,bata nan ummin,ta tafi barka na matar cousin dinta data haihu,ta tafi kuma da duka yaran,don haka ta bar mata girkin,don hajja itama kwana biyu kenan bata nan,ta tafi ainihin garinsu bikin dan qanwarta,yawanci idan zata da zahran take zuwa,hakanan wannan karon taqi binta don haka ta dauki amira da husna daga cikin jikokinta suka rakata.
Wayarta da bata dade da gama waya da nasir ba wadda ke aje saman kanta ta dauki tsuwwa,ta miqa hannu ta daukota tana duba lambar da aka kirata,ba suna alamun bata da ita cikin jerin ma’ajiyar lambobinta,saita daga ta kara a kunneta cikin sallama.
Ana amsa sallamar taji kamar tasan muryar,amma saita tambaya jin ba’a da niyyar yi mata bayani
“Dawa nake magana?”
“Nuraddeen ne….tsohon masoyinki,kuma wanda har a yanzu yake sonki” mamaki ya sanyata tashi ta zauna sosai,kodai da gaske ne shekaran jiya da sukaje gidan anty aliya yusra tace mata taga nuraddeen tsaye hana kallonsu?
“Waye kuma me wannan sunan?” Ta fada cikin gatse da basarwa,murmushi ya saka
“Na tsammaci jin sama da haka ma daga gareki….amma kiyi haquri ki bawa qwaqwalwarki dama ta tuna koni waye…don nazo da qoqon barata ne a karo na biyu a bani dama,damar kuma da zata kaimu har ga aure…..” Da sauri ta katseshi
“Kaga dakata…..ka riga daka barar da damarka tuntun tuni,abu daya zan gaya maka shine,daga yau sai yau,kada ka qara tunawa a ranka ka sanni,kada kuma ka sake gigin kirana harka koma va mahaliccinka” daga haka ta datse kiran ta aje wayar ta koma ta kwanta tana jan tsaki.
Kira ya shiga yi a jejjere,da taga zai takura mata saita dauki wayar ta danna masa block ta gyara kwanciyarta,daga qarshe ta sake jan tsaki ta miqe ta nufi kitchen,ta jawo salad din da bata yanka ba ta soma gyarashi tana cewa ilham ta kawo mata ruwa a roba,tana aikin cikin ranta tana mamakin qarfin hali da rainin hankali irin na nuraddeen,gami da zallar rashin kunya da yake tunanin yana da sauran dama,yana kuma da qwarin gwiwar da zai iya fuskantarta ido da ido ya gaya mata wata maganar.
Washegari sha biyu na rana kiran nasir ya shigo mata,tayi mamaki don basu fi awa biyu da gama waya ba,duk da cewa ta sani mayen kiranta ne shi a waya,baya gajiya,amma yadda tazo ta tadda tarin miscal ya bata mamaki,don lokacin bata kusa da wayar,ba bata lokaci tayi masa flashing ko daqiqa uku ba’a rufa ba ya kira.
Cikin zallar mamaki ta samu gefan katifarta ta zauna tana sauraren masifa da bala’in da nasir ke kwararawa cikin waya,wanda ta kasa fahimtar inda zancan ya dosa,ta gane dai akanta yake maganar,kuma duka zallar kishi ne,amma bata gama gane da waye yake ba,har sai daya qara mata haske ta hanyar cewa
“Wallahi saina nuna masa kurensa….ni zai rainawa hankali,harda dora hotonki saman dp?,to idan ma kuna tare ki gaya masa yayi saurin saukewa ya kuma fita daga harkarki tun ba’a ji kanmu ba”
“Wai waye don Allah….kayi haquri kamjn bayani mana”
“Nuraddeen yake ko waye….whatever ma ake kiransa dai ki gaya masa ke ba tashi bace” ita dariya ma zancan ga bata,tana mamakin yadda yake kishinta,ita sam ko wayar jiya ma ta manta sunyi ta dashi bare shi kansa nuraddeen din
“Ka kwantar da hankalinka mana” ta fadi sannan a hankali ta warware masa komai.
Ajiyar zuciya ya saki,cikin sanyin murya yace
“Ok…ok,pls pls fatima,don Allah ki riqemin amana,ki riqemin amanar kanki kinji don Allah,kada ki auri wani saini” idan da sabo ta saba dajin wannan kalmar daga bakinsa,itace kalmarsa ta qarshe duk sansa suka gama hira,idan akwai baquwa aciki itace kada ki auri wani saini
“In sha Allah” ta bashi amsa,saiya saki ajiyar zuciya sannan ya mata sallama yana aje wayar,itama ta aje tata tana jujjuya maganganu da sukayi cikin ranta.
*_ALฦIBLARSU_*๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ
Kwana biyu tsakanin wayarta da nasir din ta shirya zuwa gidan abban gwammaja zata dubashi ciwon qafa ya matsanta masa,ita da yusra suka shirya sai ilham,adaidaita sahu sauka dauka direct har can gwammajan,har qofar gida saboda mota tana iya shiga har qofar gidan.
Mai adaidaitan na saukesu salim na fitowa daga gidan,hannunsa riqe da ledar baqa,cikin raha dake nuna sabon dake tsakaninsu suka gaisa suka dan zolayi juna yadda suka saba sannan tace
“Da alama guduwa zakayi saboda kaga nazo”
“Haba yarinya….ma’aruf ke tsoronki,yanzu zanje na dawo,dinki zankai nan fage”
“Auto,saika dawo,ina jiranka”
“Kamar wani abun arziqi zaki bani baya ga ki karbe na hannun mutum”
“Ai raba arne da makami ibada wallahi” ta fada tana dariya gami da yin cikin gida abinta,shima ya wuce yana cewa yau kam sisi bazai kashe musu ba,basu da aiki saicin banza da wofi.
Ta taras da jikin abban da sauqi,harta zauna suka dan taba hira sannan ta wuce dakin umma suka dasa tasu hirar da hasina,ba jimawa suka shige kitchen suka dorawa umman abincin rana,har suka gama suka zuba suka zauna suka soma ci salim din bai dawo ba,sai da suka gama sun dan miqe suna hira suka jiyo sallamarsa.
Fuskarsa ba kamar dazun ba ya shigo falon,daya daga cikin kujerun falon ya samu ya zauna,daidai lokacin da umman itama ta shigo tana cewa
“A zuba maka abincin ne kafin ka wuce kasuwan?”
“A’ah umma,barshi kawai…..wani labari na samu yanzu mara dadin ji?” Itama guri ta samu ta zauna yayin da dukkaninsu sukayi sak,kowa ya bada hankalinsa kanshi
“Kamar yaya?,wanne irin labari ne haka?” umman ta fada idanunta yana kan salim din,yayin da hasina yusra da zahra suma suka zuba mishi idon suna son jin abinda zai fada………..
23/10/2021, 08:38 – ๐๐ป๐๐ป: 10
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
________________________________
“Yanzu a inda naje kai dinki wajen habibu….yakemin Allah ya sanya alkhairi,yace ashe biki zamuyi babu gayyata?,abun saiya bani mamaki,nace bakin wa?,yace bikin nasir mana!” Sosai maganar ta daki kunnen zahra,wanda ta dinga jin kamar sautin sakin bomb,saidai tayi namijin qoqari wajen tara nutsuwarta ta saurari qarshen zancan
“Ni dai ban iya cewa komai ba,a gabana ya kammala hada babbar rigar nasir din ta daurin aure,har na fito ban iya bashi amsa ba” salati sosai umma ta saka tana tafa hannu,yayin da zahra taji kamar daga zaunen da take ana shirin kada ita,don haka saita jingina da kujerar da take kai,tsahon wasu lokuta kafin umman tace
“Yanzu ta yaya zamu tabbatar da gaskiyar wannan labarin” nazari kadan salim din yayi sannan yace
“Bari na kira habibun,dama yace zai shigo anguwar yanzu wajen wani abokinsa” wayarsa ya ciro ya kirashin,anci sa’a kuwa yana gab da shigowa unguwar,ya roqeshi yanason ganinsa ya basji kwatancen gidan,yace zai iso yanzu in sha Allah.
Mintina ashirin habibu ya shigo har falon umma,a lokacin zahra na jingine kawai ba tare da wani magana ko motsi ba,tana jin yadda suketa tattauna batun a tsakaninsu.
Umma da kanta ta yiwa habibu bayanin komai,shima cikin nuna alhini da rashin jin dadi yace
“Indai ko haka ne tabbas nasiru bai kyauta ba,amma hausawa sunce waqa a bakin mai ita,bari kuji daga gareshi” daga haka ya saka hannunsa a aljihu,ya ciro wayarsa yayi kira sannan ya maidata handsfree.
Ringin uku aka daga,habibune ya soma magana
“Ango ango,ka sha qamshi”
“Chief tailor….yaya akayi?”
“An gama dinkin babbar rigar daurin auren fa”
“Kai amma naji dadi daka cika alqawari,don inason na kaita bugu ne”
“Yaushe to zaka shigo ka karba?”
“Zuwa anjima haka zanje gidansu amaryar,zankai mata invitation lokaci ya qure bata fara rabo da wuri ba,zan qaraso nan wajenka saina amsa din”
“Shikenan,a tahomin da nawa IV din,saura kwana nawa ne?”
“Rana ita yau in sha Allah”
“Ango ango,to Allah ya nuna mana”
“Amin amin,na gode” daga haka ya yanke wayar yana duban salim.
Tuni zahra ta dora hannayenta a fuskarta tana kiran sunan Allah,wai da gaske nasir shima ya yaudareta?,da gaske shima nasir aure zaiyi?,yarinyar da aka bashi zai aura ko wata daban,idan wadda aka bashi ce ai ba garin take ba,to amma yanzun cewa yake zaije gidansu amarya….me hakan ke nufi?,wai meke faruwa da ita ne?”saita miqe kawai ga nufi dakin hasina tana jin jiri yana dibanta,tana shiga ta maida qofar ta rufe don kada ma wani ya biyota,ta samu gefan gadon hasinan ta zauna,saita saki kuka a hankali hade da sheshsheqa.
Kamar wasa sai gashi a ranar kwanan gidan abban gwammaja ya kamasu saboda wani matsanancin ciwon kai daya saukar mata,umma ce ta dinga aikin bata maganganu,da kuma kwatanta mata cewa matar mutum kabarinsa,tayi addu’a idan har ya zalunceta Allah ya fidda mata haqqinta,tana jinsu sanda suke waya da umminta,sai kuma washegari bayan sallar magariba abubukar yayanta yazo da kanshi ya daukesu ya maidosu gida.
Saidai suna shiga bangaren umminta yace ta wuce,ta sameta a falo a zaune,suna hada idanu ta fahimci akwai damuwa qasan ran ummin da take boyewa,saita qarasa a hankali ta zauna gefanta tana gaidata,ta amsa sannan ta dora da cewa
“Ki tsananta addu’a,duk abinda kaso Allah kuma bai baka ba tabbas ba rabonka bane,qila ma ba alkhairi bane a rayuwarka,tashi ki tafi,Allah ya kiyaye”
“Na gode” tafada tana miqewa zuwa sassan hajjan.
Data shiga bata samu hajja ba,saita wuce dakinta,saboda yadda kanta yake sara mata,har yanzu kunnuwanta na jiye mata sanda habibu ya kira nasir din,yake gaya masa saura sati daya daurin aurensa,tana iya jiyo kamar wani sauti mai kama da zumudi zumudi cikin muryarsa,babu alamun bacin rai ko damuwa tattare da sautinsa,saidai bata jima ba hajjan ta shigo cikin jimami,inda ta takura mata sai data tattara ta zuwa dakinta,tace gwara su zauna tare har ta samu sassauci.
Saidai kuma abinda ya bata mamaki shine,a daren ranar saiga nasir ya kirata,kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga,don tunda abun ya faru tsakanin jiya da yau bai kira ba sai yanzun,tana son taji da wacce kalma shi kuma zaiyi amfani?,me zaya fada?,zai kare kanshi ne kamar yadda nuradden ya kare?,ko kuwa zai tabbatarwa da kansa laifinsa?.
A yanayin sallamarsa kawai ta fahimci baisan mai afkuwa ta afku ba,da irin salon daya saba yi mata magana yayi mata,sai daya gama sannan a hankali tace
“Ango” dif yayi na wasu sakanni sannan yace
“Wanne irin wasa ne wannan zahra?,waye kuma angon?” Wani bacin rai ne ya taso mata,wato ita zaya ninke a baibai kenan?ya shirya saidai kawai taji an daura aurensa?,saita miqe ta zauna tana tuna irin kalaman daya jima yana amfani dasu a kanta,tana tuna yadda yake nuna kaffa kaffa da zallar kishi a kanta,tana tuna yadda koda yaushe yana tafe da kyaututuka domin ta,wanda koda taqi amsa zai tilastata ta karba din,zaice tukuicin soyayya kenan kyauta,ashe babban tukuici yana tafe
“Nasir….bude kunnenka da kyau!,idan zaluntata kasoyi to ubangiji yamin kariya da katanga dakai saboda ya bayyana min gaskiyar abinda kake boyewa,ka zalunceni nasir!,kaso ka yadaureni kaje kayi aurenka ba tare da na sani ba?,to na godewa Allah daya bayyanamin shirinka” cikin wata rudewa da dirircewa yake cewa
“Calm down fatima….ki tsaya kiji mana,wallahi Allah ba haka bane,yarinyar nan auren hadi akayi mana da ita…..zabin hajiya da alhaji ce…..”
“Watanni nawa?,kwanaki nawa?,amma kullum nuna min kake bata da muhimmanci a wajenka?,hakanan maganar itama bamai muhimmanci bace?,ka gayamin cewa ka gamsar da hajiya ta aminta da naka zabin,amma abun mamaki saiga sauti farinciki daga maqogwaronka kana sanarwa da duniya daurin aurenka,a hakan zakace baka ita akayi?,ahaka kakeso na yarda dakai,bayan an ganemin babu wani damuwa ko kadan tattare dakai?”
“To naji,amma fatima….ina sonki ki yarda dani…..kuma in sha Allah zan aureki a matsayin matata ta biy…..”
“Allah ya tsareni da hada hanya da mayaudari….har abada ni dakai nasir na barka kenan,kaje….ina roqon ubangiji yayimin sakayyar abinda kayimin,Allah ya isarmin” daga haka ta kife layin ta sake sakin kuka.
Kuka tayi mai yawan gaske,wanda kafin tayi controlling kanta fa sassauta kukan nasir ya hada mata massages da kiraye kiraye babu adadi har ta kasa irga yawansu,sai kawai ta kashe wayar baki daya ta cusata qasan filo.
A ranar ta balla layin shima kamar yadda ta yiwa nuraddeen,hakanan ta kawar da duk wani abu da tasan zai tuna mata dashi,ta baiwa kanta qwarin gwiwar ci gaba da rayuwa,da kuma fuskantarta,tana mai burin haduwa da kyawawan sakamako a nan gaba
_saidai ina!,kowanne babi na rayuwa tafe yake da qaddararsa,saidai kuma DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUQI!_
Duk da ta cinyewa ranta komai amma hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba,saboda ita damuwa tana da tasirin bayyana gangar jiki koda an danneta a ruhi,hakan yasa ta faษa sosai kafin komawarta makaranta.
Wannan karon hajja da kanta tayi mata tayin zama a gida ta qara koda sati daya ne ta qara murmurewa kafin sannan amma tace a’ah,saboda jarabawar qarshe ta wa’ec da neco da suka fara jiyo qamshinta,gwra ta tattara hankalinta ta samu sakamako me kyau,don yadda qaddararta ta fara zuwa mata a hagunce ya sanyaya mata jiki.
Da yammacin ranar ana ya gobe zasu tafin haidar ya iso gidan,tana falon hajja tana goge sauran kayanta da zata wuce dasu yayi sallama falon ya shigo.
Kai ta daga ta dubeshi na sakan daya kana ta amsa tana maida kanya ga gugar,har yanzu yana nan da gayunshi kwarjini izza da isa,saima cika da ‘yar qiba da kuma murjewa daya sakeyi,hakan ya qara masa kyau sosai,kusan watansa biyu baya nan,sai yau ya dawo.
A sanyaye ta gaidashi,sannan ta tattare gugarta ta wuce ciki tabar falon,duk da haka sai data fara biyawa ta dakin hajja ta gaya mata isowarshi sannan ta fito ta koma dakinta ta barta tana ta murna da zumudin dawowar jikan nata,wanda babu yashi cikin jikokin nata,kasancewarsa jika na farko a wajenta,mai kuma yawan kula da ita da damuwarta,tamkar shita haifa ba mahaifinsa ba.
Wannan karon ma ta fito zata sha ruwa a kitchen taji hajjan na gaya masa abinda ya faru da ita,itakam bataso harga Allah hajjan na gaya masa
“Allah ya sawwaqe” kawai taji yace,qwafa taja a ranta tana cewa maganin hajjan da take gaya masan,aiba matsalar data shafeshi bace dama.
Basu jima da komawa ba lokacin visiting yayi,wanda su shine na qarshe d za’a musu saboda jarrabawa da zasu fara gab da lokacin ziyarar ko kuma bayan lokacin,sun wuni cikin farinciki,kamar yadda aka sani cewa rana ce ta farinciki ga kowanne dan makarantar kwana,wannan karon ‘yan gidansu da iyalan abban gwammaja da wuri suka koma,don haka ta dawo hostel abinta.
Gab da zata isa gadonta ta hangi ladifa hamza zaune riqe da takarda cikin hannunta,gefanta kuma maryam mustapha ce riqe da hannun ladifar dake digar hawaye.
Ba laifi suna zaman mutunci sosai dasu,kasancewar zahran mai faran faran da jama’a yasa take da yawan jama’a,banda yanzun da walwalarta taja baya ba kamar da ba,don ko da take shugabar dalibai kusan iya mu’amalarta yasa dalibai ke sonta,musamman juniors da bata yadda a zaluncesu ba don suna qasa dasu,hakanan suma basu isa su raina na sama dasu ba dole su basu girma.
“Allah dai yasa lafiya ladifa”
Maryam ce ta buda hannun ladifan ta ciro takardar ta miqawa zahra,ba bata lokaci zahran ta bude ta soma karantawa.
A hankali ta koma gefansu itama ta zauna tana fidda murmushi mai ciwo,wanda iyakarsa saman labbanta,ta ninke takardar sannan tace
“Ashe bani kadai bace ba?,bani daya keda irin wannan matsalar ba,gayamin ya kuke dashi” muryarta da sautin kuka take bata labarin yadda yake nuna mata soyayya,amma sai gashi tashi guda ya yaudareta,yayi aurensa ba tare ma data sani ba,sannan kuma saboda tsabar qwarewa yaci gaba da soyayya da ita,sai a yanzu data kusa tonashi ya bayyana mata yayi aure a sanda suke tare,ya tsallaketa ya auri wata,bayan ta kori kowa a kansa,bata sauraron kowa saishi,wannan wanne irin yaudara ce?,wanne irin cin amana ce?.
Kai zahra ke gyadawa sannan ta basu nata labarin,shuru koqacce tayi,a hankali maryam tace
“Bansan me samarin yanzu suka koma ba,sam.basu da wata ALฦIBLA ko manufa a rayuwarsu,ya kamata muma ‘yammata muyi karatun ta nutsu,mu daina basu yarda amanna da dukka soyayyarmu,da wahala ka tara yammata goma baka samu takwas a cikinsu suna da tabon yaudarar namiji ba,yaudara taban haushi,imma yaqi aurenki haka kawai saboda ranshi ya raya masa haka,ko kuma ya gujeki saboda ya nemi ki bashi kanki kinqi” kai zahra take gyadawa kawai,duk sanda ta tuna nuraddeen da nasir sai taji ranta ya sosu,abu daya data sani shine,a koda yaushe daka cuci mutum gwara shi ya cuceka,kuma sakayya yanzu tun a duniya Allah yake yinta.
*_IBRAHEEM_*
Bayan dawowarsu hutu babu jimawa suka zana jarrabawar fita daga makaranta,cikin iko da taimakon ubangiji,duk da irin qalubalen da suka dinga kawo mata tarnaqi amma hakan bai dakushe karsashi da karatunta ba.
Ranar da suka kammala aka kuma hada taro na yayewa da kuma sallamarsu,ranar ta zama ta musamman kuma me dimbin tarihi a wajen zahran.
Ranar da sai da tayi kuka na farinciki,saboda tarin kyaututtuka da kuma yabo data samu,kyaututtukan da wasu ma bata zacesu ba.
Kyauta ta qarshe data samu itace wadda daliban makarantar suka hada mata,saboda yadda sukaji dadin shugabancinta,da yadda ta tsaya tsayin daka akansu wajen kwatanta adalci da gaskiya.
Tana rungume da kyautar suka sake hada ido dashi,wannan shine kusan karo na biyar,duk sanda ta hau step din ta amsa kyauta tazo saukowa saita tsinci idanunshi a kanta,qaramin tsaki taja tana jin haushi har cikin ranta,ita sam ta tsani dabi’ar kallo,bama kuma kamar yanzun data yanke tsammani wa maza,tayi musu kudin goro.
Dukkaninsu suna tsaye gaban motocin gidansu,wanda kaso mafi yawa na ‘yan gidan nasu sunzo mata,ciki harda hajja,bata da wasu kaya masu yawa da zata koma dasu,don kusan duk ta kyautar dasu,kamar su katifarta botiki house wear dinta da sauran tarkacenta ciki harda jakar goyo ga wadanda basu da qarfi,yau jinta take kamar wadda aka ‘yanta daga kurkuku,kana kallon fuskarta zaka shaida hakan.
Cikin yaran da sukayi sabo dasu suke kuma mata kallon yayarsu ta qaraso tana cewa
“Anty fatima…..ance anason magana dake” ta fada tana nuno wata mota,daga kai tayi ta kalli motar,babu kowa kusa da ita,hakan yasa ta tambaya waye?
“Wai mamar qawarki ce”
“Mamar qawata?” Ta maimaita cikin mamaki,kafin tasan amsar da zata bada hajja tace
“Yi maza kije ki dawo kuzo mu wuce kada muyi rana a hanya” saita waiwaya ta cewa salma tazo ta rakata,suka jera tare har zuwa jikin motar.
Suna tsaiwa aka bude murfin motar aka fito,kallo daya tayi masa ta shaidashi,saurayin dazu ne,wanda yaketa faman binta da kallo,sanye cikin shadda dinkin zamani,kanshi babu hula,kallo daya zaka masa kasa cewa wayayyen mutum ne,wanda ilimin zamani ya rasashi,da murmushi yake dubanta
“Ayimin afuwa,nayi qarya da maman qawarki ko?,naga alamun idan ba hakan nayi ba babu lallai na samu ganinki,mai yiwuwa ma nayi asarar dama ta” itadai batace komai ba sai dubanshi da take,gami da son jin ba’asin kiranta,ganin kamar yana bata musu lokaci yasa ta tambayeshi kai tsaye
“Allah dai yasa lafiya,ko yarinyar tayi batan kan wadda kasa a kira ma?,don mi bansanka ba” murmushi ya saki yana dubanta
“Ni na sanki,tun ba yau ba,saidai kuma yau din idanuna suka fara ganinki” bata fahimci zancansa ba,kuma taga alamar kamar yana son maida zancan wasa ya kuma bata mata lokaci,don haka tace
“Zaifi kyau ka fadi saqonka,don na bar iyayena na jira” gyara tsaiwarsa yayi
“A’ah,aiko ba za’ayi haka ba,ya zamu barsu mama na jiranmu?,inaga kawai ki bani lambar wayarki sai muyi magana”
“Baka da abin cewa,don haka sai anjima” ta fada tana yin gaba.
Ga tsammaninta salma na biye da ita,amma tana waiwayawa saita taras acan ta barota,dan tsaiwa tayi har salman ta iskota,cikin hade rai tace
“Ki tabbatar da cewa ba number wayata kika bashi ba” dariya salman tayi
“To meye amfaninta idan ba’a bashi ba,kika san inda rana zata fadi?,kika sani ma ko shine mijin da kiketa jira Allah ya kawoshi yanzu,indai hakane ai kinga yazo a dai dai,za’ayi aurenmu kamar yadda aka tsara” baki zahran ta tabe
“Ke kuma daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi?,to ba girin girin ba tayi mai dai” dariya ta sakeyi
“Zatayi mai lunqui ma kuwa in sha Allah,don shi yace kinyi masa,hakan kuma da kikayi babu komai,don tun ganin farko daya miki yace yaga alamun me ajice dama” tsaki kawai zahran taja,don ita sam abun ya fara barin kanta,tana ga hutu take buqata da kuma samun space sosai da zata hutawa zuciya da qwaqwalwarta………
23/10/2021, 08:40 – ๐๐ป๐๐ป: 11
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
_____________________________
Tunda ta koma gida ibrahim ya samu nayi,kiran safe daban rana daban dare daban,har sai da duk wanda yake tare da ita yasan da xaman ibrahim din,tun tana sharewa itama har ta soma dagawa dole tana saurarensa.
Ibrahim din irin samarin nan ne ‘yan hira,ya iya labarai kala daban daban,sau tari koda ba zatayi magana ba zaice babu komai,yau shi zai mata hira,zata tsaya tana saurarensa yanata bata labarai kala kala,saidai kawai tayi murmushi idan wani abun ya bata dariya,haka zasu kwashe kusan awa guda,saidai tace ta gaji.
Ya gaya mata wasu daga cikin abubuwan da suka shafeshi,sunansa da aikinsa da unguwarsu,saidai ita din banda sunanta bata gaya masa komai a kanta ba,don gaba daya komai ya fice mata akai,bata jin wani karsashi akan lamarin sam,shima kuma saita lura bai fiya tambayarta personal abubuwan da suka shafi rayuwarta ba.
Cikin haka maganar auren yammatan ta taso,an soma da kawo kudin hafsat da yasira,naira dubu hamsin hamsin kowaccensu,aka saka rana kamar yadda aka tsara za’a tsaida rana guda daya.
A daren ranar su abba suka kirata,kira na farko tsakaninsu tunda aka fara zancan aurensun.
Tunda ta shiga falon taga zaki a ciki sai taji kamar ta koma,batason ana tattauna personal issues dinta a gabanshi ko kadan,harta shiga ta zauna ta gaida abba babban dashi bai daga kai ya dubeta ba,itama tafison hakan,da da hali ma fiddashi zatayi daga falon.
Cikin nuna kulawa abban yace
“Mamana….nayi magana da hajja,ta shaida min akwai wanda yanzu kuke tare dashi ibrahim ko?” Kai ta gyada idanunta suna kallon qasa
“Eh abba”
“To ma sha Allah,yanzu abinda za’ayi shine,ki shaida masa cewa muna son ganinsa,ya kamata kuma ya turo magabantansa,tunda maganar auren ‘yan uwanki ya taso,sai a hada gaba daya”kanta a qasa tace
“To abba”.
A hanya tana tafe tana tunani,hakanan sam maganar ibrahim bata kwanta mata a rai ba,amma babu yadda zatayi,ba zataso ace duka sa’anninta kowa babu shi ba saura ita kadai a gidan.
Tana shiga daki saiga kiranshi,ta dauka tana zaman gefan katifa suka fara magana,kafin takai ga gaya masa nata saqon yace
“Baby….ya kamata ace mun soma ganin juna fa,yin waya a iya waya kawai abun ya isa,ya kamata mu canza tsari….a ina zan ganki?”
“A gidanmu…..akwai maganar dama da nakeso muyi dakai” cikin ‘yar dariya dariya mai kama da murmushi yace
“Ah haba…..ai yanzu an daina wannan yayin,haduwa a gida kamar zamanin da,mudai samu wani waje haka,wanda zamu sake sosai,mu mori soyayyarmu da lokacinmu,inda babu abinda zai dinga razanamu” sosai mamaki ya kama zahra,amma saita danne mamakin nata tace
“Razana kuma kamar wasu marasa gaskiya?” Ta fada sound din muryarta yana sauyawa
“Eh mana,kinsan ita soyayya tana buqatar kebewa da nutsuwa” tsaf ta fahimta inda ya dosa,kuma bata taba tsammatar hakan daga gareshi ba,don haka ta kaurara muryarta sosai
“Ina jin baka shiryawa ganina na ba,a qa’idar gidanmu duk wanda keson ganinmu zai samemu cikin gidanmu ne,idan ka shirya zuwa saina gaya maka saqon gaba daya” daga haka ta katse wayar,ta koma da baya ta kwanta tana nazarin kalamansa,ba shakka ya bata mamaki,saidai kuma ba zata yanke masa hukunci haka da wuri ba,tunda wannan shine karon farko da hakan ta faru.
Ga mamakinta zancan ya wuce,sai gashi bai haqura dayi mata maganar inda zasu hadun ba,harda bata list na sunayen guraren shaqatawa yace ta zabi duk wanda takeso a ciki.
Yanzu ya daina bata mamaki saima tsoro,randa ta gaji da jin zancan ta buda baki cikin bacin rai tace masa
“Ibrahim,wannan maganar da kake yawan gayamin itace take tabbatar min da cewa ba sona kake ba!” Cikin dirircewa yace
“Hana baby….ki daina fadar haka,waye yace miki bana sonki,kinsan yadda nake jinki a zuciyata kuwa?”
“Ban gani a qasa ba,idan ka damu dani….idan har sona kake da gaskiya ka tako kazo ka riskeni gaban mahaifana mana,baka dinga neman kebewa dani a wani waje da babu idon naka ko nawa ba!” ta fada da zafinta
“Shikenan,is ok” shima ya fada cikin sanyin murya ganin yadda ta dauki zafi
“Allah ya baki haquri,yanzu ki gayamin saqon da kika ce tun rannan an baki”
“Ance na gaya maka cewa ka fito”
“Na fito ina?” Ya fada da wani irin sauti
“Aure mana” ta fada itama kai tsaye tana sauraren amsar da zata fito ta gaba daga bakinsa,don tuni ta gama hasashen amsarsa ta qarshe
“Ok…ok…am really sorry,sai yanzu na fahimta” sai kuma yayi cool da muryarsa sosai
“To ai baby shi yasa nakeson mudan hadun,mu fahimta juna kafin akai ga batun aure,tunda kinsan shi batun aure ba qaramar magana bace,zamane na dindindin,kinga dole saimun fahimci juna face to face tukunna” shuru tayi kawai,wani abu mai tauri yana tokare mata wuya,abun akwai zallar rainin hankali da ban mamaki,ada kullum shine bashi da zance saina aurensu,amma a yanzu tazo da batun yana neman noqewa.
Tun daga ranar saiya zamana bashi da zance saina gini yakeson ya fara,mota yakeson ya canza,yanzu kasuwa babu ciniki komai ya zamana sai a slow,gininsa ko linter baikai ba,ga hada lefe da sauransu,kullum cikin qorafin ya fada financial crisis iri iri.
Tuni tayi masa aji sukutum da guda ga ajjiyeshi,gefe guda kuma shirye shiryen biki ake a gidan haiqan,kowanne sashe suna nasu shirin,itama bata zauna ba,ta shiga anayin komai da ita,don ‘yan uwanta ne da bata da tamkarsu.
Wannan karon umminta da kanta ta kirata ta mata magana akan ibrahim,abinda bata taba yi ba akanta kenan
“Ki tayani da addu’a” shine amsar da zahran ta baiwa ummin nata,domin tasan abun babu dadi,koda itace kuwa,sun taso tare,karatu da komai tare,amma dukka sauran zasu tafi su bar diyarta?,duk da kasancewarta mutum mai yawan haquri da yarda da qadddara,tana da yawan ibada,abinda yasa take da wata nutsuwa ta musamman kenan
“Addu’a kullum cikinta muke,saidai aci gaba,ubangiji yayi zabi mafi alkhairi” abinda tace mata kenan ba tare data nuna damuwa ko a fuskarta ba.
*_ALฦIBLARSU |||_*๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ
Ana gab da sallar magariba suka dawo daga kai dinkunansu na biki,wanda ta hada dana hajja ummint ilham harda nata duka takai musu zoo road,kasancewar duka duka bikin sati biyar ya rage.
A gajiye libis take,saboda sun dan sha tafiya a qafa kafin su samu abin hawa,saboda yau ana wahalar abun hawa wanda batasan dalilin da ya kawo hakan ba.
Bandakin tsakar gidan hajja ta daura alwala ta shiga dakin hajjan ta tada salla,tana idarwa wayarta ta fara tsuwwa,ta shafa addu’ar da takeyi ta janyo wayar tana duba mai kiran.
Ibrahim ne,tsakanin jiya da yau sam basuyi waya ba ko sau daya,ita ta sha’afa ma dashi gaba daya,kara wayar tayi a kunnenta tana yin sallama,ya amsa mata,saidai sautin muryarsa batayi mata yadda suka saba magana ba.
Gaisawa kawai sukayi ta shigar masa da qorafin da taci alwashin gaya masa
“Ibrahim…..sam banga alfanu ko ma’anar ci gaba da tarayyarmu ba a haka…..aure shine ribar kowacce alaqa da dangantaka,ya kamata mu fuskanci reality,kayi abinda ya kamata” ajiyar zuciya ya sake cikin wani yanayi ya soma magana mai kama da ko in kula
“Abinda na kira na gaya miki dama kenan,don kada ki zargeni….kin ganni nan…..wallahi kakata ce wadda ta haifi ubana tayimin mata,ta kuma ce lallai lallai kona aureta kota tsinemin,ni kuma naga babu yadda zanyi ko don na farantawa babana,shi yasa na kiraki na baki haquri don dole nayi musu biyayya,Allah ya hada kowa da rabonsa” daga haka ya katse wayar.
Tamkar mutum mutumi haka tabar wayar a kunnen tana sauraren shuru,duk da cewa tasha qiyasta haka qarshen alaqarsu zata kasance,amma bata taba kawowa zatazo ta wannan sigar ba.
Sallamar salma ita ta taimaka ta dawo da ita hayyacinta harta samu nasarar cire wayar daga kunnenta,kallon fuskar zahran yasa salma ta fahimci akwai matsala,saita qaraso tana tambayar zahran lafiya?
“Mun rabu da ibrahim shima salma” ta amsa mata da yanayin data kasa tantance wanne ne?,baqinciki ne ko tashin hankali?”.
Duk abinda salman ke fada tana jinta ne kawai ba tare da tana fahimta ba,har tayi ta gama,saita zama kamar wata mutum mutumi,abu na qarshe data ji shine qwalla dake saukowa a idanunta masu dumi,wanda yayi dai dai da shigowar hajja.
Wannan karon itama hajjan hankalinta tashi yayi fiye da baya,ta dinga salati tana salallami,ita kanta salma hankalinta ya tashi,wannan wacce iriyar qaddarace haka daya bayan daya?.
Kusan duk wani makusancinta a wannan karon lamarin yafi shigarsa,babu abinda zahra ta rasa,kaf yaran gidan babu wanda keda kyau da sura irin tata,hakanan tarbiyya,abinda yayi su salma shi yayisu,asali da nasaba dukka daya,to amma tata qaddarar tazo daban da tasu,kuma babu wanda ya isa ya sauya mata,saidai addu’a nada qarfin ikon sauya komai da izinin Allah,wannan shine wasu daga cikin kalaman hajja data cika da damuwa matuqa gaske.
ฦarfe tara na dare ta isa sassan umminta bayan kiran datayi mata kwanaki uku da faruwar al’amarin.
A dakin gadonta ta sameta ita kadai zaune gefan gado,bayan ta baro qannenta a falo zaune,zata zauna qasa ummin ta nuna mata gefanta gami da cewa
“Zauna nan”babu musu ta zauna din tana duban mahaifiyartata
“Zahra’u….kalleni nan” ta fada tana dubanta,kanta ta daga tana duban ummin tata,ta hangi da gasken gasken zata gaya mata koma menene zai fito daga bakinta din,saboda ba kasafai take kiran sunanta haka kai tsaye ba,da wahala ta kirata haka da wannan sunan kai tsaye,don sunan hajja ne fatiman,sunan dake da daraja a idonta,don haka ta sake tattara mata hankalinta
“Zahra’u….inason ki gayamin,tsakaninki da mahaliccinki wanne abu kike aikatawa da dukka manemanki suke barinki haka bagatatan?” Take idanunta ya tara hawaye,muryarta tana rawa tace
“Ban sani ba ummi,bani da masaniya”
“Ki gayamin inna wuro….tun wuri ki shaida min,meke faruwa?”
“Ki yarda dani ummi,wallahi babu wani abu” shuru ne ya biyo baya na wani dan lokaci,sai sautin sheshsheqar kukan zahran tsahon wani lokaci sannan ummin ta sake cewa
“Inason ki sake dagewa da addu’a,bawai ki zauna haka ba,ki gayawa Allah matsalolinki da buqatarki,a shirye yake ya amsa miki buqatunki,ya kuma yaye miki matsalolinki” kai take gyadawa a hankali,sosai tausayin ‘yar tata ya kamata,sai tace
“Tashi kije…Allah ya shige mana gaba”.
***********
Sannu a hankali kwanaki suke shudewa,lokacin biki kuma yana qaratowa,harya zamana saura sati hudu kacal biki,shirye shirye suka kankama sosai,yayin da zahra ta maida kanta busy ta kuma shiga harkar bikin kamar yadda ya kamata ta kasance a ciki,ta kowanne bangare akwai hannunta a ciki.
*_ฦADDARA ta riga fata….._*
ฦarfe biyar da wasu mintuna na yammacin ranar alhamis ne,tsaye suke a farfajiyar gidan suna amsar wasu daga cikin dinkunansu da telarsu ta gama ta kawo musu suna dubawa,babu jimawa suka sallameta,kowa ya ninke nashi ya saka a leda,suka koma tattauna sauran abubuwan da basu kai ga aiwatarwa ba wanda ya shafi bikin.
A hankali a hankali suka soma jin sautin salatin daga sassan abba babba,sak dukkaninsu sukayi suka kasa kunne,tabbas daga can sautin salatin yake fitowa daya nabin daya a jejjere.
Zumbur hafsat ta miqe fuskarta dauke da tsoro da firgici tace
“Kamar muryar mama….mama ce….ina zuwa” cikin sauri ta durfafi sashen nasu,yasira ta rufa mata baya,sauran kuma suka tsaya cak,kowaccensu ta kasa motsawa cike da fargaba jin abinda ya faru,da kuma abinda zai biyo bayan salatin……
_kuyi manage da wannan,mu hadu gobe in sha Allah dan jin meke faruwa?……_
23/10/2021, 08:40 – ๐๐ป๐๐ป: 12
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
_____________________________
Minti biyu saiga hafsat ta fito tana hawaye hannayenta a ka,dukkansu suka nufeta cikin sauri kuma cikin tashin hankali,don dukkansu sun kasa shiga sashen har sai data fito
“Yaa zahra…..yaa zahra,ya zahra ta mutu” ta fada tana rushewa da kuka.
Sak kowaccensu tayi tana jin maganar tana shigarta,babu wadda ta kawo faruwar hakan cikin ranta a cikinsu,zahra ce tayi qarfin halin cewa
“Yaa zahran da take makaranta?,me ya sameta haka?,rashin lafiya tayi?”
“Maciji…..maciji ne ya sareta”
“Innalilahi wa inna ilaihi raji’un” kowaccensu ke maimaitawa.
Cikin ฦanฦanin lokaci duka matan gidan suka shirya suka fito saboda nuna kara ga mama,uwa uba kuma ga surukuta da take shirin shiga tsakani,gidan ya zamana babu kowa,daga ‘yammatan sai yara,su dinma zaman jugum jugum sukayi,kowanne a cikinsu yana tuna yaa zahran da irin kirkinta,haquri gami da sanyin hali.
Yasira ce taja doguwar ajiyar zuciya tana cewa
“Allah sarki yaa haidar,ko yaya zaiji?” Ta fadi maganar tana tuna yadda suke da zahran tashi,kusan kaf wanda yasan haidar bai taba ganinsa yana soyayya ba sai akan zahran,wata iriyar soyayya suke shida ita,ita tana girmamashi da girmama ra’ayinsa hadi da bashi kulawa,hakanan shima ya iya tattalinta da nashi salon na iya kula da ‘ya mace cikin sanyi,wanda ba kowa ne zai fahimta haka ba sai mai dogon nazari.
Sai washegari su suka je gidan makokin bayan sun girka abinci mai yawa sun tafi dashi kula kula,ko acan ma kusan baya ga mahaifan zahran haidar shine mutum.na gaba da aka tausayawa,kowa yaje ya masa gaisuwa ya dawo saiya fadi irin halin daya ganshi,wata mata dake matuqar kama dasu mama,wanda da alama danginsu ce tace
“Dole aliyyu ya shiga wani hali,a gabansa ajalin zahra ya risketa,kuma a gabansa ta mutu,ai dole,mutuwar masoyinka gaban idanunka aiba qaramin al’amari bane da zaiyi saurin barin zuciya da tunani nan da nan”.
Shuru inna wuro dake gefe tayi tana nazarin al’amarin,tabbas jikinta yayi sanyi sosai,komai saiya sake fice mata akai,musamman sanda ake dawo da kayan zahra daga hostel,yau ga komai na zahran amma babu ita,tana can duniyar da babu wanda ya isa ya dawo da ita,ta tafi kenan tafiya ta har abada saidai tarihi.
A hanyarsu ta dawowa hafsat ke sake basu labarin yadda abun ya faru,ashe a makaranta tsautsayin ya sameta,a sannan haidar din yaje wajenta,ta juya da niyar zuwa hostel ta dauko biro da takarda zata rubuta masa list na abubuwan da take buqata na biki,yaga gilmawar macijin…..kafin ya isa gareta yakai mata dauki harya sareta,rashin samun allurar akan kari shi ya kawo ajalinta,don suna hanyar wata barrack,duk da ba tasu bace amma yana da alfarma ako ina,wanda yake da tabbacin acan za’a samu allurar,ta mutu cikin motarsa,baima yarda ta mutun ba saida aka shigar da ita clinic din aka bincika aka shaida masa rai yayi halinsa.
Shuru kowa yayi yana jinjina al’amarin,tare da kadaita girman ubangiji,isa da buwayarsa,babu wanda ya taba kawowa zahra mutuwa koda ita karan kanta,ta mutu ta tafi a lokacin da masoyanta ke buqatarta,dangi keta shirin aurenta,ashe shirin zaman makokinta ake
(Allah kasa mu cika da imani,ka kyauta qarshenmu,kasa mu mutu alokacin da kake mai yarda da amincewa damu amin summa amin๐คฒ๐ฝ๐คฒ๐ฝ).
Rasuwar zahran yasa aka qara wata daya kan yadda aka tsara bikin,zuwa sannan ana saka ran zuciyoyi sun huce,an dan samu nutsuwa da dangana akan lamarin.
*_SAUYIN RAYUWA_*
Tun daga sanda abun ya faru gaba daya tamkar an sake canza haidar din daka wanda dacan suka sani zuwa wani na daban,ya sake zama miskili na qin qarawa,bai damu da zama ko rayuwa cikin mutane ba,magana saita zama dole ko ta shafi aikinsa,ya sake zama mutum mai zafi qwari da gaske fiye da baya,har kowa cikin gidan na shakka da dari dari na taboshi ko shiga cikin sabga ko huruminsa,bama su da suke qannensa mata ba,harda su ya musty kowa shiga taitayinsa yake idan ana maganar ya haidar,hakanan ya sake rungumar aikinsa,ya rabu da komai.
Hakan ya damu hajja qwarai,harta ringa qorafi,tana ganin ya sanyawa kansa damuwa mai yawa kan mutuwar zahra,ta fuskanci ma kamar yana dorawa kansa ne alhakin mutuwarta,da farko hakan hasashenta ne,amma data dameshi da qorafi da mita,da kuma son jin ta bakinsa saiya tabbatar mata da hakan
“Da banje gurinta ba a sannan,da ban fito da ita ba,da abinda ya sameta bai sameta ba,da tuni taba raye har yanzu” baki hajja ta sake tana kallonsa cike da mamaki,abun nasa ya zarce inda take tunani
“Ina hankalinka yake ne zaki?,ina imaninka da tauhidinka ya tafi?,shin ka manta kowacce rai bata tsallake ajalinta?,ka manta cewa kowacce rai saita dandani mutuwa?,ka manta kowacce rai na tare da qaddararta?”
“Duka nasan da hakan….kuma ina yawan gayawa kaina haka,saidai har yanzu na kasa cire tunanin cewa nine sila”.
Ganin abun bana qare bane yasa tace su sashi kawai a addu’a,ubangiji ya sanyaya masa zuciyarsa,ya cire masa wannan tunani daga qwaqwalwarsa.
Biki akayi gagarumi wanda yabar tarihi cikin zuri’arsu,baqi na kusa dana nesa duka sun hallara,ansha hidima sosai,a hakanma an rage wasu abubuwan saboda rasuwar da akayin,amma hakan bai hana wasu hidimomin ba,tunda yaran bana sashe daya bane ba.
Xahra tamkar zata raba kanta gida hudu,saboda kowacce idan ta tashi ita take nema,baga yasira ba,baga yusra ba,baga hafsat ba,hakanan ba ga salma ba,a qarshe dai bayan amare kowacce an miqa ta gidanta sai data kwanta zazzabi na kusan kwana biyar.
Gaba daya daga bikin xuwa daurin auren babu wanda haidar yazo,ya kira ya musu Allah ya sanya alkhairi,ya kuma ce aiki ne ya tsareshi bazai samu zuwa ba.
Abba babba shi da mama zasuyi fada hajja ta hana
“Akul!,kada naji kada na gani,ku qyaleshin tunda yace aiki ne,kudai naku kuci gaba da yi masa addu’a,tsanantawa ba naku bane,Allah yayi mata rahama,shi kuma ya bashi dangana”da haka suka haqura da qorafin da sukayi niyyar yi.
Duk wanda yaga zahran cikin hidimar bikin cewa yake
“Kema Allah ya fito miki da na gari” takanyi murmushi ta amsa cikin ranta,ba domin abin ya dameta ba ko ya ษaษata da qasa ba,yayin da ‘yan gaza gani,yan bani na iya,masu kokawa da qaddara da qarfin tuwo kance
“Ummm…..zahra kenan,ko kema kin bi sahun wasu yammatanne masu jiran mai kudi gida da mota,maka duk sati…kada dai kyau ya rudeki ki cuci kanki” suma takan bisu da dariya kawai,don a sannan bata da lokacin bata lokaci,hakanan bata da damuwa dasu tasan kuma ba hakan bane bare maganar ta dameta,yayin da wasunsu kance
“Uhmmm….zahra matar manya,da alama naki bikin na dabanne,saimun shirya sosai,dama irinku ai sai da babban kai” suma duka aji daya take saka su da masu magana ta biyu,dukkaninsu ba matsalarta bane su din,shi yasa basu da wata amsa daga gareta.
Kwana uku kacal da tafiyarsu sai kadaici da kewa ya soma damunta,dukka gidan taji ya daina mata dadi,bata taba tunani ko kawowa zata damu har haka da rashin ‘yan uwan nata ba sai yanzu,duk saita sake zama wata so silent,bata fiya yawan hira dariya da raha da aka santa da ita ba.
Hajja ce mutum ta farko data fara lura da hakan,duk itama sai taji babu dadi,tasan cewa kewa ce ke damunta na ‘yan uwanta da suka rayu tare suka taso tare,don haka tayi wani tunani,ta nemi abban gwammaja da babban danta abba babba ta zauna dasu,ta bada shawarar baiwa zahran damar ci gaba da karatu,idan yaso duk sanda Allah ya kawo mata manemi sai ta yanke tayi aurenta,don yafi wannan zaman da zatayi,domin zaman bashi da wani alfanu,hakanan babu abinda zai qara mata sai damuwa.
Dukkaninsu sunyi na’am,don result din zahran ba qaramin kyau yayi ba,don haka abban gwammaja ya nemi a bashi takardunta amma abba babba yace sam wannan karon shi zaiyi wannan aikin,hakanan abban gwammaja ya sallama din,tunda sun bashi damarmaki a baya sosai kan yarinyar,bai kamata a yanzu shima yaqi basu tasu damar ba.
Wani irin farinciki da bata taba tunanin zata jishi ba shi taji a sanda labarin ci gaba da karatunta ya risketa,duba da cewa ita sam bata da sha’awar ci gaba da karatu tun a baya,hafsat da yasira sun fita wannan kwadayin,tayi murna sosai,ta kuma tabbatar da qaunar da hajjanta ke mata ta daban ce,hakanan ‘yan uwan mahaifin nata mutanene da samun kamarsu a wannan zamanin sai an tona,wannan shine ya zamto silar ci gaba da karatun zahran,mace ta farko a tarihin gidan data taba tsallakewa zuwa makarantar gaba da secondry.
*_SABUWAR DUNIYA_*
Kamar kowacce daliba,ta shiga makarantar cike da baqunta da rashin sabo,komai nata idan ka gani irin na farin shiga ne,sannu a hankali har ta fara gogewa tana kuma gane kan abubuwa.
ฦawar farko data fara yi bayan zuwanta makarantar itace hindatu abubakar,babban abinda yaja hankalinta zuwa qawancesu shine qoqari irin na hindatun,duk da cewa sun fito ne daga mabanbantan gida masu mabanbantan dabi’u al’ada da kuma wadata,saboda hindatun iyayenta masu sukuni ne qwarai da gaske,don mota ta daban kuma ta musamman ake kawota makarantar kulli yaumin,a kuma dawo a dauketa,daga wayar hannunta zuwa suturu kawai zakasan ‘yar babban gida ce,Allah ga hada jininsu da hindatu da wani irin qawance daya gauraya da qaunar juna,qauna kuma ta fisabilillahi,don da farko zahra taso janye jikinta daga abota da hindatun,saboda tsari da matakin rayuwarsu ba daya bane,da jajircewar hindatun qawancen nasu ya daidaita,kowa kuma yake amfani da irin nashi life style din ba tare da ya takura dan uwanshi akan yanayin nashi tsarin rayuwar ba.
Iyayen hindatun ‘yan boko ne na gasken gaske,ba irin ‘yan bokon muna boko ba,kusan hatta kakan hindatun asalinsa dan boko ne,irin ‘yan bokon da turawan mulkin mallaka suka koyar tun duniya tana kwance,don haka idan ana gadar boko xa’a iya cewa sun gadon,don kuwa hatta da dabi’unsu da al’adunsu irin na nasara ne,akwai ‘yancin da zabar rayuwa cikin gidansu hindatun,hakan ya sanya kome zakiyi kina da right,babu me tauyeki ko hanaki,wannan yasa sau tari zahra kan xauna tayi ta mamakin rayuwarsu,domin ita nata ahalin don boko sunyishi,ba za’a gaya musu shi ba,amma basu yarda hakan ya janyesu daga kan tsari da al’ada ba,da kuma dabi’u na musulunci.
Sannu sannu sai qawayen hindatun suka soma zama na zahra,domin kusan ko yaushe kuma kullum suna tare,dakinsu guda saboda kwanan hostel takeyi,hindatu nada shaqiqan qawaye guda hudu da bata da kamarsu,dukkaninsu suna ‘ya’yan manya ne,kowaccensu tana ji da arziqin ubanta wayewa uwa uba kuma gayu,akwai batula,nadiya,farida da kuma jannah,wadanda kansu ya bude sosai,hakan idanuwansu kusan a bude yake.
Kusan duk makarantar an sansu a haka suke su biyar saiga zahra ta shidansu,suna da matuqar kirki faran faran da son mutane,suna da taimako ga me buqata,hakanan suna da sauqin kai,arziqin iyayensu bai sanyasu jin kai ko izza ba,duk wanda ya mu’amalancesu zasu mu’amalanceshi suna da kyakkyawar dabi’a,hakan shi ya boye kaso mafi yawa na halayensu marasa kyau,kamar tara samari kala kala daga mabanbantan yare,zuwa duk wani party ko dinner da zuwa guraren shaqatawa joint joint iri daban daban,da sanya dinkuna masu daukar hankali da kuma qananun kaya,duk da cewa qananun kayan ba masu muni ne da yawa ba,amma tunda sun saba da al’adarmu,sai suka zama abun qyama ne ga duk wani bahaushe,ko kuma wanda ya sarayar da nashi yaren da qabilar,ya koma bahaushe zam.
Hausawa sukace zama da madaukin kanwa,duk da cewa zahra bata dauki ko kwafi wata mummuna daga cikin dabi’u ko halayensu ba,hasalima idan sunyi abinda bai mata ba tana qoqari wajen ganin fta saitasu a hanya,wani taci nasara,wani kuma saidai ta haqura,ta koyi ayi da iya kwalliya daga garesu,idan tayi ado sai kace ita dinma ‘yar wani ce,dama can zahran maison ado ne,saita hadu da wadanda suka fita iyawa,suka kuma fita sanin kan abun,hakan ya sanya cikin qanqani lokaci zahran ta zama zahran ta gaske,ta murje ta qara zama cikakkiyar mace wadda hankali nutsuwa da cikar matantaka suka bayyana a gareta,ta murje ta zama ‘yar gayu ta gasken gaske.
Hatta dasu batula da suka fita komai na more rayuwa amma sukanyi sha’awa da burin inama ace sune zahran,inama ace sune suke da kyan diri da sura irin nata,inama ace sune keda farinji da kwarjininta,wani irin farinjini da babu inda zata shiga ta fita ba’a samu me son ba,saidai a wajenta ita dukkaninsu sun makaro,domin kuwa gaba daya soyayyar da suke nema a wajenta itace lissafinta na qarshe a rayuwa,kwata kwata bata cikin tsarintq,don bata hangi komai cikinta ba face wahala da bacin rai,zamanta a haka tana ganin yafi mata komai kwanciyar hankali,ta maida karatunta sama kuma gaba da komai,saidai kuma duk da baka idan qaddarar bawa bata qare masa ba,tofa la shakka babu tsumi kuma babu dabara saita riskeshi.
*_ABDUL_YASAR_*
Matashin saurayi mai shekaru a qalla talatin,mai matsakaicin kyau kuma ma’aikacin banki dake aiki jahar kanon mu ta dabo,dan kaduna kuma,a fuskarsa yana da suffar kamala da hankali,wanda ya shigo rayuwar zahran a daren wata alhamis,qarfe takwas na dare sanda take kan dawowa daga gidan dinki bayan takai dinkin atamfarta sharada kan titin yahaya gusau,wanda a yanzu kusan da wahala ta shafe watanni biyu batayi sabon dinki ba,hajjanta ta tsaya mata,haka ma abban gwammaja.
Tun asali bata fiya son fitar dare ba,kada ma ace wannan unguwar zatazo,domin titin indai dare yayi akan samu qarancin zirga zirgar ababen hawa musamman na haya,saboda manyan gine gine dake cike a unguwar yawanci saidai motocin gida dake wucewa ษai ษaiku.
Abinda ma yasa ta yanke taje din,ganin anyi gyaran titin na yahaya gusau din,hakan bazai bata matsalar dawowa gida ba,tunda tazarar dake tsakanin unguwarsu da unguwar bamai yawa bace,zata dawo da wuri.
Saidai kuma tunda ta fito titin adaidaitan data wuce basufi a qarga ba,su dinma akwai mutane ciki,haka ta soma takawa a hankali don rage tsayin tafiyar,gabanta na dan faduwa kasancewar titin akwai fitilun titi,amma basu da maraba da tirken awaki,tunda ba’a kunnasu bare su bada hasken da ake buqata,sai hasken gine gine jifa jifa dake bakin titin,da kuma hasken ababen hawan dake wulgawa.
Sai yanzu take jin hushin kanta me yasanya bata taho da dan rakiya ba cikin yaran gidansu?,tana tsaka da wannan tunanin wayarta ta dauki qara alamun kirane ya shigo,ta dago qwayar tana duba me kiran nata.
Hafsat ce,saita saki murmushi najin dadin ganin kiran ‘yar uwartata
“Aini nayi fushi wallahi,babu abinda zakice dani” hafsan ta fada zahra na daga wayar
“Wayyo Allah na,me kuma nayi?”
“Au baki ma sani ba?,to bari na gaya miki,kinga na farko tunda mukayi aure zuwanki gidajenmu baifi a qirga ba,kowa qorafi yakeyi,na biyu kuma bani da lafiya,kowa yazo ya dubani,wasu sun kirani amma keda ya haidar baku zo ba banga kiranku ba,to wai don Allah meye marabarki da ya aliyyun ma?”
“Na yarda na miki laifi,amma ki daina hadani da wannan dagen….sannan kimin uzuri,rashin zuwa na gidanku wallahi hafsat makaranta ce,kuma kin sani,sannan lalurarki ni dana dawo babu wanda ya gayamin baki da lafiya”
“Eh ai saboda ansan ma ba zuwa zakiyi ba” murmushi tayi mai sauti
“Kiyi haquri….haba hansatuwa,aiba haka tsakaninmu,in sha Allah gobe ko jibi zaki ganni,kuma wannan karon bazan koma ba saina jewa kowa na kashe mitarku,ke ina tunanin ma da qyar idan ba strike za’a tafi ba wani satin,kinga idan hakan ta faru kwana daya daya zanwa kowa”
“Heee….na dai jiki kawai,a samu kizo dinma”
“Waima meya sameki?” Zahran ta fada tana qunshe dariya cikin salon tsokana saita dora da
“Kodai an gamu ne?”
“An gamu dake ba….idan kinzo kya gani”……
Tana tsaka da wannan maganar idanunta sukayi arba dasu,matasa ne su uku tsaye a gabanta sun tare hanyarta,saita sauke wayar da sauri daga kunnenta ba tare data samu sukunin yin sallama da hafsat ba
“Bani wayata!” Daya daga cikinsu ya fada cikin gadara yana miqa mata hannu,kai ka rantse da Allah wayar tasa ce,mamaki da tsoro ya sanyata tsaiwa tana kallonsu,daya daga cikinsu ya daka mata tsawa yana daga rigarsa ya zaro wuqa daga qugunsa
“Zaki miqo ko sai na farke miki ciki anan!” Kalaman da suka sake kadata kenan,ta miqa hannu zata basu wayar,dai dai sanda hasken mota ya dallaresu,ba tare da sun tsaya bi takan wayar ba suka ranta ana kare.
Tana tsaye a nan sannu a hankali motar ta qaraso,babban mutum ne a ciki,don ya kusa haifarta
“Garin yaya suka tareki?,maza ki wuce kibar wajen nan”
“To baba na gode” ta fada a tsorace tana yin gaba,saidai ko taku goma batayi ba taji magana a bayanta.
Tana waiwayawa sukayi arba dashi
“Karki tsorata,muje na rakaki,ina daga can baya na hangi meya faru” matashin ya fada,saita danji nutsuwa,don haka tabi bayanshi har suka sake gangarowa bakin titi sosai
“Al’ummarmu ta lalace ta zama wata irin al’umma,tarbiyya tayi qaranci,daba sata fashi da makami,garkuwa da mutane fyade da sauran munanan ayyuka,gaba daya su suka cika al’ummarmu suke mana barazanar rushewarta,gaba daya matsalar an rasa makamarta,saidai abu daya ne,duk wannan matsalar tushenta da asalinta gidan aure ne” kai ta gyada cike da gamsuwa,kalamansa sun dace da mutum mai hankali irinsa,wannan dalili ya sanya taji tsoron da takeji ya sake raguwa,hankalinta ya dan kwanta,daidai lokacin da wata adaidaita ta nufosu babu kowa a ciki ya tsaidata,sannan ya waiwaya yana tambayar zahran ina ta nufa tace mishi gadon qaya,shi kuma ya shaidawa mai napep din.
Sai data shiga sannan yace
“Abokina nima bari na zauna gefanka,tunda duka hanyace,idan ka sauketa ka qarasa dani tal’udu”
“To ba damuwa master,shigo mana” ya fada yana dan gyara masa gefansa.
Tunda suka shiga kusan zancan yadda arewa kullum ke tabarbarewa yakeyi,wanda wannan yana daya daga cikin abinda ke ciwa zahra tuwo a qwarya,wanda takejin inama ita marubuciya ce?,inama ace zata iya rubutu,tabbas da alqalaminta zai sauka ne tsakiyar arewa,kuma kan ‘yan arewa,yadda muka share baki muna bacci har yaqi ya cimmana har saman gadajen baccinmu,yadda shugabanninmu da wakilanmu suka zama lusarai,’yan son kai da son zuciya,suka zama kamar aladu marasa kishin kansu ma bare na jama’ar da suke wakilta,indai zasu cika aljihunansu da kudi,indai ba zasu talauta ba,yadda muma muka zama masu matacciyar zuciya,muka saida mutunci qima daraja martaba da kwarjini irin na arewa da ‘ya’yanta,kuma har gobe baccin muke ci gaba dayi,mun kasa tunanin kanmu,anata tsere mana ana mana fintikau,an raina mu bayan mun wuce raini,munfi qarfin raini da dukkan wani qasqanci,muna kashe junanmu,muna talauta kanmu,muna dakushe tattalin arziqin yankinmu,bayan mune ZUCIYAR NIGERIA din ma gaba daya,wannan shine babban tunanin zahra akoda yaushe.
“Wanne layi zaki shiga?” Taji ya tambaya,saita nunawa mai napep din har suka qarasa qofar gidansu sannan ta sauka,tana niyyar biyan mai abun hawan yace
“A’ah hajjaju ki barshi,inason in samu ladan”
“Na gode” ta fada kawai ta fada gida,don har yanzu tsoron data shiga dazu bai saketa ba,batasan sanda suka bar qofar gidan ba.
Sanda ta shiga gida ta gayawa hajja sallallami ta saka
“To alhmdlh da ubangiji ya tsare,shi yasa fa ba’a son fitar daren nan,shi kuma daya kawoki har nan Allah ya saka masa da alkhairi…..oh ni fatima,wannan lalacewar tarbiyya ubangiji yayi mana magani,shekara kusan saba’in a duniya amma baka daina ganin abubuwa iri iri ba” dariya zahra tayi
“Wa zaice kin shekara saba’in din hajja?,don dai kawai kinqi aure ne,kin dage sai a lahira idan kin hadu da tsoho alu”
“Kyaci gidanku idan na miqe na sameki,saina gwada miki tsohon qashi” zahran na dariya ta wuce dakinta,cikin ranta tana godewa Allah daya kubutar da ita,sai kuma ta tuna da mutumin da suka sauketa yanzun qofar gida,lallai yana da tunani mai kyau
“Allah ka gyara mana yankinmu dama qasarmu baki daya” ta furta a sarari tana cire daurin dankwalinta zuwa kayanta ma gaba daya ta fada bandaki don ta watsa ruwa ko zata ji dadin jikinta,kafin kuma ga fita ta nemi abincin dare,don tasan tuni gaje ta gama.
23/10/2021, 08:40 – ๐๐ป๐๐ป: 13
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
_____________________________
Kusan ta mance da abdulyasar gaba daya,don a qalla an kusa sati da wani yammaci akace ana sallama da ita,tayi mamaki sosai don a yanzu tasan bata da appointment da wani kan zaizo nemanta,har ta aika yaron tace masa yaje yace bata nan hajja ta tsaidashi,tace
“kace masa tana zuwa” fuska tadan bata tana duban hajja
“Nifa wallahi hajja ban san waye ba,da kin barshi kawai ya tafi”
“A’ah,ai baza’ayi haka ba,idan kuma shine mijin auren fa kika koreshi?” Saita dan buga qafa kadan tana turo baki,sannan ta miqe ta nufi daki.
Ganin doguwar riga ce a jikinta mai dogon hannu,kuma budadde ne dinkin babu ta inda ya kama jikinta saita sanya qaramin mayafi tayi rolling dashi sannan ta fito.
Yana jikin katangar gidan a jingine tayi sallama,da murmushi a fuskarsa ya dago yana amsawa,sai a sannan ta gane waye,saita dan sake masa fuska kadan suka gaisawa.
“Hala baki gane waye ba” dan qaramin murmushi tayi
“Na gane mana,sunanka ne kawai ban sani ba”
“Nima haka,ai anmin rowar suna,har muka rabu banji sunan malamar ba,shi yasa yanzu nayo tattaki nazo naji daga bakinta….nidai sunana abdulyasar……” Daga nan yayi mata bayanin kansa,itama bataqi ba ta gaya mishi sunanta,sannan ya gabatar mata da abinda ya kawoshi,ya kuma dora da cewa
“Ni da gaske nazo,kuma da gaske nake,ina fatan babu wani a gabana,kuma babu wanda ya rigani?” Murmushi kawai tayi ba tare data bashi amsa ba,dai dai sanda motar haidar ta danno layin,ta kuma qaraso gaban gidan,yayi horn mai gadi ya bude masa ya shige,da alama yau ya dawo yazo hutune kamar yadda yakanyi kusan duk qarshen wata.
Tasan halin ya haidar din duk da bata ga alamun ya ganta ba,amma gudun faruwar wani abu yasa tayi masa sallama ta shige gida,bayan ya nace ya amshi lambarta.
Kafin ta qarasa sassansu wayarta dake hannunta tayi tsuwwa,hindatu ce ke kiranta,saita dakata da tafiyar ta tsaya amsa wayar
“Ya akayi ne qawa?”
“Lafiya wallahi…..ya gida yasu daddy?”
“Lafiya lau,duka na barosu a gida bama tare”
“Ina kika tafi kuma?” Zahran ta tuhumeta tana dan tsuke gira
“Ba wani waje bane me nisa,lagos ne,ana bikin wata qawata….so akwai wani event da za’ayi a nan din” gyara tsaiwa tayi
“Amma fisabilillahi hindu biki a kasa yinsa a garinsu amarya har sai an dauki wani event din an kaishi wani gari me nisa haka?”
“Wanne nisa tafiyar jirgi?,yan mintuna marasa yawa anje”
“A ina kuka sauka kenan?”
“Guest house mana,muna da wanda muka sani ne?” Dogon tsaki zahran taja
“Kunnen qashinki shi zai sa mu raba gari dake hindu,tunda bakya yarda da abinda nake gaya miki” dariya ta saki
“Ko kin raba gari dani ni bazan raba dake ba…..karki damu,idan akwai wani abu ba dai dai ba daddy ko mommy xasu yi magana,ni kiranki nayi ma na gaya miki….gobe fa za’a je strike din nan,kuma sai baba ta gani sunce” bata rai zahra tayi
“Wato a duniya shi dalibin nigeria bazai taba gama karatu ta dadin rai farinciki ko walwala ba?…..ai shikenan,sun yiwa kansu,muma mayi azuminmu a dadi,Allah yasa sai an sallace za’a koma” dariya hindatu ta saki
“Wallahi nima haka nace,kinsan hali dai,idan ina azumi ba kanta,bana ganewa kwata kwata” saita kauda wannan zancan ta dauko na farko
“Yanzu yaushe xaki dawo?”
“Gobe in sha Allah….”
“Kin tabbata?”
“Da gaske nake….jibi ma zanzo har gida ki tabbatar da kanki,saka ranki a inuwa” daga haka zahran ta katse wayar,Allah ya sani tana qaunar hindatun,kuma tana da halaye masu kyau na kirki da son jama’a,amma rayuwarta ita a wajenta da iyayenta ba komai bane saboda tsabar wayewa,dukkansu bata zarginsu da aikata alfasha da maza,amma saidai yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu wayewarsu tayi yawa,irin wayewar da dole zata iya janyo maka zargi ga idanun al’umma,kuma yana daga cikin cikar kamalar mutum ya guji dukkan wani abu da zai jefa zarginsa a zuciyar al’umma,da wannan tunanin ta isa sassan hajjan,saita tadda haidar dofane a hannun kujera yana latsa waya,jikinsa wata fara qal din shirt ce ta maza mai V neck short sleeve,sai wandon kaki dake jikinsa,da wani farin qal din booth da yakai masa har qauri,hajja na zaune daga gefansa,da alama wata maganar takeyi dashi,shi kuma yana sauraronta,yayi wani irin kwarjini musamman yau daya bar iya wandon ma kawai a jikinsa,hakanan fatarsa tayi fresh tamkar babu abinda ke damunsa,saidai kuma fuskarnan tana nan kamar kowanne lokaci babu rahama ko digon dariya tattare da ita,sai gashinsa daketa glowing wanda ya qara masa kyau da cikar mazantaka.
Kansa ya daga ya jefeta da wani irin kallo,murya a dake yace
“Ke….zonan” da baya ta dawo ta zauna jikin hajja kamar zata shige cikinta,ya cira kai da lumsassun idanunsa dake cike da kwarjini yace yana duban hajja
“Ya akayi ta fita da wannan shigar?,waye kuma a waje data tsaya dashi?” Duban zahra hajja tayi sannan ta dubeshi
“Me ya samu shigar tata?,sannan idan saurayi yayi sallama da budurwa dama binsu ake a tsaya tare dasu ko kuwa?” Sai daya lumshe idanunsaya budesu sannan yace
“Amma hajja kinfi kowa sanin tsarina a kansu tun sauran na gidan nan ko game da saka qananun mayafai ko?,sannan haka sama taka ba’asan mutum ba yazo ya kirata ta kada wadannan zoqala zoqalan qafafun nata ta fita?”.
Wayyo….ji zahra tayi kamar ya kwada mata mari,tunda take ba wanda ya taba aibanta surarta saishi,tasha ji a bakin maza daban daban yadda suke koda halittarta duk da ita ba burgeta hakan yake ba,ba kuma damuwa tayi dasu ba,shine yau shi don wulaqanci zai jefeta da wannan kalmar?.
Hajja kam baki ta kama sannan ta saki tana ruqo hannun zahran
“Karka sake gayawa jikata haka,a ciki ni banga abun laifi ba,indai ba daga bracck aka bata kama rai ba zaka zo ka juyeshi a nan ahto” qaramar ajiyar zuciya ya sauke
“Ke tashi ki bamu waje” ya fada cikin sigar bada umarni,saita miqe da hanzari,ta murguda baki bayan ta juya musu baya cikin ranta tana mita.
Sai da yaga shigewarta sannan ya dubi hajja dai
“Hajja….yarinyar nan,haka kawai kuka kaita universty,ke baki ganin sauyin dabi’u tattare da ita?” Hannu ta daga masa
“Haidar….haidar…me yasa haka ne?,ni babu wani abu da zahrata ta sauya dashi,kada na sake jin wani abu makamancin haka daga bakinka” wayarsa ya mayar aljihun unifoarm din sojojin dake jikinsa,sannan ya miqe a nutse
“Ina kuma zaka muna magana?” Cikin i don’t care manner yace
“Akwai kaya da nakeso a fito dasu kafin na shiga ciki,don bazan samu fitowa da wuri ba….idan na fito ma tattauna” daga haka ya soma takawa da wata irin tafiya mai cike da qasaita da nuna qarfi da ginuwar gangar jiki yabar falon.
Sai a sannan zahra dake labe ta fito da hanzari muryarta na rawa kamar zata sake kuka tace
“Kinji ko hajja….kinji sharrin da yakeson yimin,ni ba’ace komai a kanshi ba saboda zaman bariki ba saini don ina makaranta”
“Kinga dagani….na gaji da wannan iskancin naku keda zaki,yara kamar mayu?,kamar masu ganin hanjin juna?,to wallahi idan bakuyi wasa ba aure zan saka iyayenku su daura muku naga qaryar iskanci” wani irin tsalle zahra dake zaune a jikin hajja ga buga kamar wadda aka dorawa kunama a jiki,ita kanta hajjan saida tayi sak cikin tsoron tana duban zahra dake fadin
“A’uzu billahi minash shaidanir rajim,hajja….wacce irin masifa kike ambata da yammacin juma’ar nan?” Ta fada idanunta duka a waje,tafin hannu kawai hajja ta saka tana rufe bakinta dashi tana fadin
“La’ilaha ilallahu,muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam inna wuro?,kamar wadda tace miki tsohuwarki ta mutu?,wannan zancen ne masifa?,anya zahra?” Ganin yadda bacin ranta ya bayyana yasa ta sassauta nata,ta qarasa wajen hajjan ta zauna tana narke murya
“Kiyi haquri hajja,ba haka nake nufi ba,don Allah ki haquri,amma.in sha Allah na daina shiga huruminsa,dama ni ba shiga nake ba,shine haka nan ba gaira ba dalili ya matsantamin”
“Kema ai bajin magana kike ba,ko don kinga ina baki kariya?”kamar zatayi kuka tace
“kiyi haquri dai don Allah abar zancan,na daina in sha Allahu” shuru tayi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta sake ajiyar zuciya
“Ai shikenan….Allah ya kyauta” jin haka don kada ta sake jan wata maganar saita miqe kawai tayi dakinta,a ranta tana juya zancan
“Itama.hajjan nan wani lokacin wlh tuburarriya ce,haka kawai da yammacin ranar juma’a,dai dai sanda ake amsa addu’a ki fadi wannan mummunan kalamin kisa ‘yan amin su amsa?” Ita daya ta qaraci mitarta cikin daki harta haqura.
Da magariba zata gurin me gadi amsowa hajja goro da me gadi yace tazo ta amsa taga qofar gidan nasu cike da jama’a,kusan hakan ba sabon abu bane wajensu,duk randa aliyyu ya sauka a garin gidansun baya rabo da mutane,duk da cewa ko baya nan din ba’a rasa mabuqata jifa jifa masu neman taimako,amma kuma cikarsu bata kaiwa yadda take a yanzun.
A yanzun ma rabon kayan abincin azumi da alama yasa akeyi,don ga kwalayen kayan abinci nan kala kala da qananun buhun shinkafa,tabe baki tayi sanda taji wani yana zabga addu’a da koda layin duk da baya wajen,don baya zama a inda ake rabon,saidai ya wakilta ma’aikatan gidan
“Uban tausayi uban talakawan unguwar nan dama gundumar nan gaba daya,zuciyarka fara tas take hakama ayyukanka,ubangiji yasa kafi haka,ya qara arziqi da daukaka”
“Green snake….under green grass kenan” ta fada qasa qasa tana sake tabe baki,tana tsaye tana kallon yadda suke layi suna karba cikin farinciki,don mai gadin shima yana can,sai daya hangota sannan ya iso yana cewa
“Kiyi haquri uwar masu gida,banga zuwanki ba,saqon hajiya hajja ko?,ina can muna rabon aikin alkhairin haidar…..wannan yaro ya dace,ubangiji ya kareshi yasa yafi haka,yana faranta ran talakawa” ya fada yana cusa kanshi dan dakinsa,ya dauko saqon ya miqa.mata ta karba ta juya,tana sake jiyo kalaman yabo daga bakin mutane.
Ta sani cewa wani lokaci akan zo ma su hajja godiya kan wani abu da aliyyun yayi cikin unguwar,saidai su amsa don babu wanda yasan ma yayi din,kusan haka dabi’arsa take idan zaiyi wani abun alkhairin,itakam tana dauka kawai shashanci ne irin na mutane,don bataga alamu a yadda aliyyun yake da baqar zuciya,zai iya wani abun arziqin da zai farantawa wani rai ba.
*************
Kamar da wasa kuwa wata washegarin ta gama wankewa hajja qananun kayanta ta fito ta falo,tana tsaye gaban tv taji kamar muryar hindatu tana magana,da alama yaran gidansu ne da yau gaba dayan ‘yan mazan da matasan abba babba ya raba musu gyaran flowers da farfajiyar gidan,tunda an yiwa wanda yake musu wannan hidimar rasuwa,ya tafi qauye.
Aje remote din tayi tana tafa hannu cikin mamaki da jin dadi
“Na zaci zancanki ne kawai fa da kika ce zaki zo” itama tana murmushin tace
“Kin taba ganin na saba alaqawari” kai ta girgiza tace
“Ina sara miki ta wannan sashen ai”.
Sai data gabatar mata da ruwa da lemo sannan ta yiwa hajja magana ta fito suka gaisa,ba wannan bane zuwanta gidan na farko ba,ta taba zuwa sau daya,wannan ne na biyu,hindatun ta jima sosai suna hira,don a nan taci abincin rana ma,sannan ta kira jannah batula nadiya da farida suka hada kira na bai daya suka sha hira har zuwa sanda akayi sallar la’asar,ta shiga nan bandakin zahra din ta daura alwala.
Tana saman abun sallar zata tayar kenan ta waiwayo ta dubi zahra
“Yauma fa na sake ganin yayankunnan,ya hakimce saman kujera qafa daya saman daya yana karatun jarida,duka yaran kowa cikin hankalinsa yake aikinsa ba hayaniya da alama shike gadinsu,bakiga yadda tsare gidan da yayi yayi masa kyau ba”hindatu ta fada,kallonta zahra tayi
“Wanne fa?,ya musty ko ya shamsu?”
“A’ah fa….sojan nan….wallahi nikam idanuna basu taba ganin namijin da yamin kwarjini,ya kuma burgeni,na kuma ji na shirya aurensa ba irinsa….don Allah qawata ki shigemin gaba mana” ta fada cikin karyar da murya.
Tsaki zahra taja
“Don girman Allah ki tada sallarki ya fiye miki arziqi,wannan maganar taki ki nema abokin yinta amma ba zahra’u ba” saita sanya filo saman katifarta ta kwanta rub da ciki,hindatun dai bata haqura ba tace
“Saboda me kika ce haka?”
“Ki barni don Allah hindatu” da taga ta matsa da maganar,da zancan saita gaya mata dalili sai tace
“Ba ya haidar ba?,ai nan ne gidansu,kuma yana cikin gidan,kina iya gwada sa’arki,kije ki gabatar masa da kanki mana qawata”
“Au haka kika ce?,zakiga aiki kuwa da cikawa”ta fada tana kabbara sallarta
“Da dai yafi” itama ta amsa mata tana gyara kwanciyarta.
Tare suka fito don mata rakiya,zuwa sannan sun gama gyaran sai ganyayyakin da suke hadawa,ya mustapha na nuna musu inda zasu zuba za’azo a kwashe daga wajen kwashe shara.
Har yanzun haidar din na zaune inda yake,saidai wannan karon maimakon jarida wani littafine a hannunsa yana dubawa,mai kalar kakin soja,tabo zahra hindatu tayi,saita matsar da hannunta ba tare data dubi zahran ko inda haidar din yake ba,don ta fuskanci abinda take nufi,sai tayi gaba hindatun na biye da ita.
Bata ankara ba taji hindatun na gaida haidar cikin wani salo,saidai bai amsa ba sai data sake magana karo na biyu sannan ya amsa ciki ciki da qyar kamar wanda aka tilasta.
Suna qarasa ficewa qofar gidan zahra ta kwashe da dariya
“Wai me hakan?” Hindatu ta tambaye ta tana dubanta
“Ai gwara da kika ga halinshi da idanunki,idan da gaya miki nayi ba lallai ki yarda ba” tsaki hindatu taja
“To sai me?,ni wallahi burgeni ma ya sakeyi”
“Au Allah?”
“Qwarai kuwa”
“To Allah ya taimaka” zahra ta fada tana dariya harta raka hindatun bakin ‘yar qaramar motar da aka siya mata ta tasheta tabar layin,ita kuma ta koma ciki.
23/10/2021, 08:40 – ๐๐ป๐๐ป: 14
*OUM DUFAIL!!*
_GIDAN ADO ฦAWA DA KECE RAINI_๐๐
๐ฝ
_OUM DUFAIL ta tanadar muku dukkan nau’in kayayyakin gyaran fata gashi dama jiki gaba daya ZAHIRINKI DA BAฦININKI samfurin MAIDA TSOHUWA YARINYA_
*kayayyakinmu sune kamar haka*
FACE AND BODY SCRUB=2500(300ml)
Face and body mango butter=3k (250ml)
Face cream= 1800
Corretor oil/vitamin C oil=2k
Fairness skin lotion= 2500
Hot chocolate skin lotion 2500
Serum (for Nuckles )2k
Nuckles cream (stubborn)3500
Mix fruits Arabian black =soap 1800
Mix fruit glycerine soap =1900
Beetroot=1900
Coconut, milk,egg..face soap=1200
Lavender mix fruit soap =1800
Body wash =1500
cleanser=1600
Hair spray =700
Hair oil =1500
Hair relaxer =700
Hair butter 1700
Shampoo =1500
Breast=oil 2k powder 2k
Strech marks cream= 2k
Beetroot pink lips =700
Baby care soap glycerine=1k
Baby care butter =1500
Shea butter baby soap =700
Tsumin tula =2200
Tsumin zinariya =1200
Sliming tea =1500
Amarya set =25k
Liquid Arabian black soap =1900
Cleansing water =1500
*Ku dubamu a handle namu na Facebook da Instagram*
Ummu Dufail
*ko ta number wayarmu kamar haka*
07067943479
*_muna turawa kowacce jaha dake fadin nigeria da yardar Allah_*
*_INGANCI DA RAHUSA SHINE TAKENMU_*๐ค๐พ๐ค๐พ๐ค๐พ
_____________________________
Za’a iya cewa abdulyasar ya samu shiga wajen zahra saboda halayen daya nuna,wadanda suka sanya tun tana dari dari dashi harta saki jikinta,saidai shi kansa yadan dauki lokaci kafin ya samu ta sake dashi,saboda tana ganin kamar za’a koma ‘yar gidan jiya ne,saidai yadda yake kaffa kaffa da ita,da yadda yake nuna tsananin kishinsa a kanta,da kuma yanda yake yawan jan hankalinta kan rayuwa kamewa da kula da mutuncin kai yasa ya sake samun fada a wajenta.
Sau tari idan yaga wata halayya ta wasu yammatan yakan qalubalancesu,don hatta su hindatu sai daya so ya rabata dasu,saidai data zauna tayi masa bayani da kuma alfanun zamansu tare ta yadda zata ci gaba da nusashshesu yasa ya fahimta ya kuma haqura.
Ta nata fannin sosai take qoqari wajen ganin ta kyautata masa shima,saboda yadda ya damu da dukkan lamuranta,ta lura mutum ne maison cima mai dadi,saidai ba kowacce iri ba,hakan ya sanya duk sanda zaizo wajenta girki na musamman take masa,koda bazaizo bama,sau tari idan akwai kudi hannunta zata kirashi ranar taji abinda yafi sha’awar ci,shi zata dafa masa ya aiko a karba masa,ko yazo da kansa,yawanci yafison cimar gargajiya,kamar dambu,danwake,alala,wainar fulawa da sauransu wani lokaci harda dan malele,to koda su din zata masa,zata kashe kudi sosai ta qawata masa su,misali alala,na ‘gwangwani baifi uku ba,zata zuba masa qwai wadatacce,hakanan wainar fulawa zata cika mata qwai,harka dinga jin kamar wainar qwai qwai,fulawa fulawa,kirkinsa da yadda ya samu fada wajen hajja saboda dabi’unsa yasa koda batayi niyyar yi ba hajja da kanta zatace tayi masa,da kudinta kuma,takance
“Abudulyassar akwai kirki akwai hankali,ai babu abinda ba za’a yiwa yaron nan ba,yana da nutsuwa da sanin ya kamata,ni ba abinda yake burgeni irin yadda yake tsaronki,kamar yadda yayanku haidar yakeyi”.
Hatta fita siyan katin waya idan yaji tayi ranar babu zaman lafiya,ya dinga fushi kenan da ita,bare kuma ya kira sama da sau biyu yaji busy,alamun tana waya kenan,ya dinga mita da qorafi da binbini,tun bata saba ba har halayyarsa ta zama ba baquwa bace wajenta,abokai da na kusa da ita kance
“ki gode Allah,mai yiwuwa sauyi alkhairi ubangiji zai miki,shi yasa dama ya kore dukka wadancan ya kawo miki wannan”.
Na biyu tana jin dadin aduk sanda tayi girkin ya tafi dashi gida yake cewa mama(mahaifiyarsa)taji dadinsa,harma wani lokaci yakan kirata ya bata maman su gaisa ta kuma yi mata godiya
(A baya nasa abdulyasar dan kaduna ne,afwan zamu canza mu barshi a dan kano ne saboda wasu dalilai da anan gaba zan fadesu).
Bata mantawa akwai wani lokaci da wasu ‘yammata suka zo suka wucesu,sosai sunyiwa fuskarsu bleeching wanda koda yaro qarami yana kallonsu zai gane,tasan halinsa,don haka tayi sha’awar tsokanarsa
“Nima man nan xan fara shafawa fa…..dama duk cikinmu da muka tashi na fisu duhun fata,kaga nima saina fito washar abuna” fuska ya tamke sosai yana dubanta
“Zahra’u,kice min kawai lokacin rabuwarmu ne yayi” idanu ta fiddo tana boye dariyarta
“Kamar yaya?”
“Eh mana….,ai daga randa naga kalar fatarki ta canza,ko naga qibarki tafi yadda kike a yanzu,hakan na tabbatar min kina amfani da wasu magunguna kenan,todaga ranar bana jin alaqarmu zata ci gaba da wanzuwa” dariyarta ta sake,tana sake jinjinawa tsantseni irin na abdul yassar din,da kuma yadda yake kiyaye doka da qa’ida,da qoqarinsa na azata bisa turba kowanne lokaci
“Ka kwantar da hankalinka,nima duka irin wadan nan ababen basa birgeni sam,saboda dukka alqawari ne da shaidan yayi kan saiya batar da ‘yan adam,ya sanyasu sun aikata hakan,Allah ya bamu labarin hakan cikin suratun nisa’i wato surar mata kenan,saboda ubangiji yasani cewa mu mukafi kowa saurin dulmiya daga kaidin shaidan,suratun nisa’i,aya ta dari da sha tara.
“Allahu akhbar”ya fada yana lumshe ido
“Shi yasa kowanne lokaci nake godewa Allah da ya bani ke,na dade daji a jikina tun sanda na soma ganinki nayi matar aure,kuma irin macen da kowanne namiji zaiyi burin mallaka” kafin ya sake cewa wani abu wayarsa ta dauki tsuwwa,ya ciro ya duba
“Eh ina wajenta….ok to” ya fada yana murmushi,ya maida wayar aljihunsa
“Auwal ne”
“Ayyah….dama kwana biyu baiyo rakiya ba”
“Wallahi….wasu ‘yan sabgogi ne suka sanyashi gaba,kinsan mu talakawa saida nema” murmushi kawai tayi sukaci gaba da hira,auwal abokinsa ne sosai,wanda yawancin lokutta yana daukoshi suna zuwa tare.
Ba’a rufa minti ashirin ba auwal ya iso saman babur dinsa lifan
“Na fatima zahra,bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi” ya fada yana dariya kana ya bashi hannu suka cafke,kana ya maida dubansa ga zahra
“Dama ai nasani,bazai wuce nan din ba….gaskiya fatima kin dace da masoyi na gaske,kowa yasan abdulyasar yasan ki,ba wanda baida labarinki,ya dagawa kowacce mace red card saboda ke,wai don Allah meye sirrin?” Murmushi tayi tana cewa
“Um um auwal banda ziga,irin wannan koda abokinka haka?,kada fa naga ba haka ba” dukka hannayensa ya daga sama
“A’ah….aini bana shakka….bana shakka kan maganata,ke kike shakka saboda bakiga yadda ya damu dake ba ya kuma damu da zancanki ba….amma lokaci yana nan zuwa da zaki yarda”
“To Allah ya nuna mana”. Baifi minti goma suka qara ba auwal din ya daukeshi suka wuce.
Cikin haka watan azumi ya sake kamawa,shima yazo musu a sanda ASUU suke halin nasu,don haka wannan karon ma a gida sukeyin azumin.
Rana ta farko misalin qarfe biyu na rana,bayan zahran ta idar da sallar azahar,kusan tana idar da sallar azahar take fara girke girken shan ruwa ita da baba gaje,wanda ita baba gaje da haidar suke shan ruwa a nan,sai kuma su abba babba da duk ranar satin qarshe suma suke shan ruwa tare da mahaifiyarsu,ma’ana duk bayan kwana bakwai,to tare dasu ranar za’ayi girki,to yanzun ma da haidar din bai dawo gida ba iya su ukune girkin,amma hajjan takam fidda sadakar abincin mutum uku haka zuwa maqota ko biyr wadatacce da zai isheshi mutu yaci harma ya rage,bayan wanda akanyi a raba sadaka,ta nade abun sallarta ta fito falo,dai dai sanda taji hajjan na cewa gaje
“Tunda haidar bai dawo ba,lokaci lokaci a dinga saka sanwa da yaron nan abdulyasar” murmushi baba gaje tayi
“Hajja kina ji dai da yaron nan”
“To gaje….ai duk wanda zaiso naka ya gama maka komai”
“Gaskiya ne….wannan haka yake” ta amsa tana komawa zuwa kitchen,zahra kuma ta qaraso wajen hajjan
“Hajja,da kawai an qyaleshi,tunda kusa da gida yake,inda ace nesa ne shine”
“Kijimin ‘ya da rashin son alkhairi,to banda ma lalacewa ta zamani,mu a yadda muka tashi mukaga iyayenmu da kakanninmu nayi,koda wucewa mutum yazo yi ya dan zauna ya huta a qofar gidansu yana da kwano ranar a cikin gidan,ko kwana nawa zaiyi a wajen,bare kuma surukin gida guda” jin zata mata tarere saita barta,tabi bayan baba gaje zuwa kitchen.
Sosai abdulyassar kuwa yake nuna yabawa da dawainiyar abincin,a haka har aka sallace azumin gaba daya,saidai ita abinda yake bata mamaki,duk da ba damuwa tayi da komai nasa ba,abdulyasar din ba gwanin kyauta bane,amma da sukayi maganar da salma sai tace
“Kada ki damu,wani haka yake,saikin shiga gidansa sannan zaki gane ba rowa bace,gwaji ne” da wannan ta share zancan.
Biyu ga salla gidansu ya cika da baqi,jikoki da yaran da aka aurar,cikinsu harda su salma yasira yusra hafsat,sai manyan yayyensu da suka dan jima da aure,anty alawiyya anty fiddausi da anty nusaiba,wadanda kowaccensu daga me yara hudu saimai biyar,dukkansu qannen ya haidar ne,anty nusaiba ce kawai ta bashi shekara daya da wata uku,mama tayi kwainika a tsakaninsu(gwarne inji wasu hausawan ko?๐),hakan ya sanya koda ka gansu ma ba zaka zaci ta girmeshi ba,duka saiya zama yayan kowa.
Itakam zahra ranta a bace yake,don gaba daya dinkunanta babu wanda telor dinta yayi mata,saboda rainin wayo ma data matsa sai yaran shagon sukace ya tafi ittikafi lagos,badon takai zuciyarta nesa ba a ranar su kansu yaran da sun sha ruwan zagi,Allah yasa tana da wasu kala hudu da maman hindatu ta dinka musu iri daya da hindatu ,dasu ta dinga amfani,amma ana ya gobe ‘yan gidan nasu suzo,saboda wani dan qaramin taro suke ranar kowa zaizo,ta daga hankalinta,saboda akwai kayan da takeso sakawa a ciki,don haka ta shirya da safe da wuri ta iske hajja a falo.
Ita da haidar ne zaune,sai umaima ‘yar abban tsakiya da nuratu dake gefe gaban tv suna goge kayansu,da alama suma su zasu saka yau ko goben da kowa zai hallara
“Ummm…..kaga ‘yammatan gidan nan,wadan nan kayan na yaushe ne?” Da ido umaima ta mata nuni da sashen da haidar din ke zaune,don ita bata lura dashi ba,daga kai tayi ta dubi wajen,magana suke da hajja,hannunsa riqe da kudade,yayin da hajjan ke riqe da wata takarda wadda kamar list din sunayen mutane ne a jiki,ta kuma tabbatar da hakan sanda hajjan ke fadin sunayen yana irgo kudin yana miqa mata tana ninkesu,da alama su za’a baiwa kenan,saita yatsina fuska ta dawo da dubanta kan yaran,wato kowa indai da haidar a wajen baida sukuni?,for god sake zai dami kowa ne ahaan….
“Waye zai rakani amso dinki?” Duk sai sukayi matsa gefe
“Anya ko yaya zahra zaki samu dan rakiya yau,wallahi ya musty ne yace kowa ya shirya zai kaimu shoprite mu zabi abinda mukeso,daga nan mu wuce minjibir park” ta fada qasa qasa don kada haidar din yaji saita kama baki
“Yau ni ake qin rakawa?….to ai gobe ma rana ce” suna ‘yar dariya suke cewa
“Ki haquri yaa zahra…Allah yace duk wanda yaje wani gun bazai jirashi ba” batace komai ba ta qarasa wajen hajja,a sannan har haidar din ya miqe,hannunsa empty,da alama ya rabar da kudinne gaba daya.
Fuskarta ba walwala ta gaidashi harda dan rusunawa kadan saboda idanun hajja,don ta fuskanci tun dag wancan lokacin ta sanya musu idanu,shi yasa take iya bakin qoqarinta na nuna mata cewa ta daina din kamar yadda tace,ya amsa a dake kamar yadda dabi’arsa take,bata damu ba ta dubi hajja
“Hajja…zanje na karbo dinkin nan,na samu guda daya”
“To…ba matsala….amma haidar ya saukemin ke,naga fita zakayi ko?” Tayi maganar tana dubanshi,ya amsa da eh ba tare daya daga kanshi daga matsa wayar da yakeyi ba
“Yauwa,ka sauketa da Allah,inaso ta dawo da wuri ta kitsemin kan nan nawa” ta fada masa sanda yake takawa yana barin falon,wani irin sak zahran tayi,ta buda baki zatayi magana yadda hajja ke kallonta yasa ta wayance
“Hajja santsin gashinki fa yasa kitso bai zama fa”
“Hakanan za’amin,bana son zama da tsefaffan kai”
Kai ta gyada kawai sannan tabi bayansa itama ta fice,hajja ta samu waje ta zauna,cikin ranta tana raya cewa yawan samun kusancinsu kamar haka me yiwuwa *SABANIN ALKIBLA* da rashin fahimtar dake tsakaninsu zai ragu ko yaya.
Sanda ta iskeshi a ma’ajiyar motoci har ya kunna motar,ta bude gidan baya ta zauna,a nutse ya waiwayo ya mata wani kallo daya sanyata tilas ta fito daga bayan ta dawo gaba,don ga fahimci manufar kallon nasa sarai.
Luff tayi cikin motar,wani irin qamshi mai taushi da sanyawa zukata nutsuwa ke tashi cikin motar,ga sanyin ac daya karade motar,shi kansa wani qamshi yake busowa kamar an zuba iskar wani abu,yayin da wani slow music ke tashi qasa qasa yadda bazai takura me sauraro ba.
Basuyi nisa ba wayarshi ta kama ringing,cikin wani sauti mai dadi,wayar ya janyo ya kara a kunnensa da hannu daya,yayin da daya hannun yaci gaba da tuqi dashi
“Ya akayi?” Ya fada da sauti mara amo
“Ok….ba damuwa….ganinan” ya fada yana aje wayar ba tare daya damu da kasheta ba,sannan ya sanya signal ya fada wani titin.
Da sauri zahra ta dubeshi,don ba titin da zatayi ba kenan,kwata kwata sun kauce hanya
“Ya haidar b…..” Hannunsa ya daga mata alamun ta dakata ba tare daya waiwayo ya dubeta,a hankali ya gangara gefan titin,sannan yace
“Sauka” still idanunsa na kallon gaban motar,da mamaki ta kalleshi,ta kalli titin da suke kai,indai tace anan zata samu abun hawa zataci wahala koda kuwa ace ba bikin sallah ake ba,saboda titin ya baude sosai da hanyarta,saita kau da kanta daga duban data masa,shuru ya ratsa motar na sakan goma,sannan ya tasheta yaci gaba da tafiyarsa hankali kwance.
Basuyi nisa ba suka tsaya qofar wani gini,wanda baiyi kama da gida ba,yafi kama da qawatacciyar ma’aikata,parking yayi da kyau,sannan ya buda murfin motar yayi ficewarsa,ta bishi da kallo har aka bude masa qofar ya shiga.
Ajiyar zuciya ta saki ranta na baci sanda ta kalli agogon hannunta taga ta kwashi minti talatin zaune a motar babu shi babu dalilinsa,Saita fara neman abinda zata rage zaman kadaicin dashi,tunda ta baro wayarta a gida,a tunanin yanzu yanzu zataje ta dawo.
Aljihun gabar motarsa ta bude,duk da zuciyarta na gargadarta da aikata hakan,tana budewa wani dan qaramin littafi mai adon zaiba ya fado,yana da ษan nauyi kadan,saita daukeshi daga qasa,har zata maida sai taji ya dauki hankalinta,don haka ta tsaya ta bude.
Shafin farko ne kawai ke dauke da wasu kyawawan rubutu,wanda ajiki akayi magana mara tsaho kamar haka
_Abune mai matuqar ciwo ne a rayuwa rashin masoyi ko kuma wanda yake qaunarka,zaka yita tunawa cewa yayi maka nisa,kullum idan rana ta fito ta fadi ya maka nisan da babu masaniyar ranar da zaka taddoshi,sannu a hankali saika soma manta yanayin murya dariya ko murmushinsa,kome yawan damuwarka ba zata taba dawo maka da shi ba,amma sai zuciyarka ta kasa gasgata hakan,kayita hasashe da fatan zai dawo gareka_
Yaa zahra ce ta fado mata a rai,tasan tabbas kalamanta ne,da ita yake,hakanan sai taji jikinta yayi sanyi,kalamai ne marasa yawa amma masu ratsa zuciya,saita samu kanta da sake maimaita rubutun.
Tana tsaka da maimaita rubutun taji tsaiwar mutum a kanta saitin window din da take,aliyyu ne tsaye,harde da hannayensa a qirji yana dubanta,kwarjininsa da tsoro yasa ta diririce,ta soma qoqarin maida littafin inda yake,sai taga kawai ya miqo mata hannu,ba musu ta sanya masa littafin a hannun nasa a sanyaye,sai kuma taga ya bude murfin sit dinta,da idanu ya mata alamun ta fito,a sanyaye ta fito cike da tsoron me zai mata,tana tsaye ya zagaya ya shiga nashi sit din,ya sanya hannu ya rufe daya murfin bayan ya rufe nasa,sannan ya kunna motar yaja yana barin wajen,zahran ta bishi da kallon mamaki har sai daya fice daga layin.
Ginin daya fito daga ciki tabi da kallo,haushi da takaici na cikata,koma me ya mata hajjan ce ta jawo mata,inda ta qyaleta ina ruwan biri da gada?,ta hau napep asirinta a rufe ya kaita ya dawo da ita,yanzu gashi nan ya jawo mata bankada tana zaman zamanta,haka ta dinga takawa da qafafunta har ta isa titi,saidai acan ma sai data dan sha wuya kafin ta samu abun hawa,kasancewar garin kano kan cika ya tumbatsa da baqi a duk yayin da ake shagulgulan bikin sallah,hakan yakan sabbaba cinkoso da rashin samun abun hawa akan kari.
Ranta a bace ta isa shagon,abinda yadan sanyaya mata raima taje ta taras ya gama mata duka dinkunan,tana amsa tayo gida,saidai batayi niyyar gayawa hajja ba sam bare tace wani abu da zai sake dagula mata lissafi.
*********** **** ********
*_BANKAฦA_*
_abun ษoye!_
A hankali take takowa daga cikin gidan zuwa qofar gida sanye da doguwar riga marron mai sulbi,duk da ba kwalliya tayi ba amma tayi mata kyau sosai,hakanan jikinta na fidda wani qamshi mai aji da tsayawa a rai.
Abdulrashid ke kiranta,wanda tasan da zuwansa dama,tunda jiyo yazo harta zuba mishi bincin salla da sukeyi,wanda a tsarin gidan kwana uku akeyi ana abincin sallah,ran salla washegari da wata washegarin,ya shaida mata gobe zaiyi tafiya,an kirashi wani aiki me muhimmanci,amma kafin ya wuce zai biyo suyi sallama.
A tsaye ta sameshi ya bata baya,goye da jakar matafiya,ya waiwayo fuskarsa fadade da fara’a yana amsa sallamarta
“Wai har ka gama shirin?” Agogonsa ya duba
“Wallahi,ni suke ma jira abokan tafiyar fa,bazan iya tafiya bane saina zo na ganki”.
Murmushi tayi,sosai takejin dadin yadda yake bata kulawa
“To ai gani” ta amsa masa tana murmushi,kafin ya bata amsa wayarsa ta sake tsuwwa,ya cirota daga aljihunsa ya daga
“Ok….gani,ganinan ai nace” maida wayar yayi yana cewa
“Fatima,tafiya zanyi saina dawo,banajin zan wuce sati daya kacal”
“To Allah ya tsare hanya….am na manta,bari na shiga na dauko ma saqo minti daya” tuni ya soma tattakawa
“Jirana ake fatima afwan….amma da mun dauki hanya zan kiraki in sha Allah,daga nan har zuwa 12 na dare ki jirani” kai ta gyada
“To shikenan,Allah ya tsare hanya,ya dawo daku lafiya”
“Amin na gode” ya fada yana takawa da sassarfa,ita kuma ta juya zuwa cikin gida…..
Masu karatu
*ALฦIBLARSU!*๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ
23/10/2021, 08:40 – ๐๐ป๐๐ป: 15
*_ina ‘yan uwa musulmai masu kishin addinin islama???_*
*_maza ku matso ga wani aikin lada ya samu_*
*_ฦanku kuma dan uwanku kuma qaninku wato ABDURRAHMAN,yaro mai hazaqa gami da kwadayin haddace littafin Allah mai tsarki,ya bude YOUTUBE CHANNEL nashi na qashin kansa,ku tallafa masa ta hanyar shiga wannan shudin rubutun ku danna masa subscribe,ba abunda xai rageku dashi saima samun dimbin lada dalilin KARFAFA MASA GWIWA,MUN GODE ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ_*
๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ
Tana komawa cikin gida shirin kwanciya tayi saboda a gajiye take yau din,duk da tana son zuwa susha hira da hafsat wadda tazo dazun,zata kuma kwana har uku,saboda me gidan nata wata tafiya ta kamashi,da qyar kuwa ya haidar ya barta saida yaji daga bakin mijin nata,sun yiyyi baqi yau din sosai,bata zauna ba hakan yasa ta gaji da yawa.
Sai data kwanta sannan ta kira hafsat tace karta jirata,tayi kwanciyarta gobe da sassafe zata shigo ta tasheta
“Ba komai wuron hajja,Allah ya kaimu”
“Aha” tace tana datse kiran.
Tana sane da maganar da sukayi da abdulyassar din kan ta jirashi zai kirata,tasan kuma tsaf bacci zai iya daukarta,don haka sai kawai taja laptop dinta ‘yar qarama da abban gwammaja ya siya mata ta kunna,ta zabo daya daga cikin fina finan ciki ta kunna ta soma kalla.
Tun tana cijewa tana kallon har idanunta sukayi nauyi,batasan sadda bacci ya dauketa ba.
Sanda ta farka da sauri ta jawo waya tana dubawa,a zatonta zata samu miscal din abdulyasar din,babu miscal babu kuma saqo,ta kalli agogo,sha biyu na dare har da rabi,kenan ya saba lokacin da yace zaiyi kiran nata?,hakanan sai taji idanunta ya bushe,baccin yayi nasa guri,saita miqe ta shiga bandaki ta daura alwala,ta dawo ta tada salla.
Ta kusa kaiwa qarfe biyu saura na dare tana zaune saman abun sallahn,har bacci ya sake dibanta taji qarar wayartata,saita miqa hannu ta dauko wayar,idanunta ya sauka kan agogon qarfe biyu da rabi na dare,ga mamakinta lawal ne abokin abdulyassar yake kiran,sosai hakan ya bata mamaki,wata mummunar faduwar gaba ta ziyarceta har batasan sanda ta daga wayar ba.
Muryar lawal dince ta bayyana cikin tsantsar tashin hankali yake fadin
“Zahra….abdul ya mutu,abdul ya rasu,qarfe sha biyu na dare yayi hatsari a hanyarsa ta tafiya,Allah yayi masa cikawa a take” dif wuta ta dauke mata,saita daina jin abinda lawal din yake fada,sai wata qara dake ratsa kunnenta kamar an buga qarfe da qarfe,ita dai batasan mintinan data shafe a haka ba,batasan kuma sanda lawal ya katse nashi kiran ba,batasan yadda akai ta kai kanta dakin hajja ba,sai ganinta tayi ta fada saman hajjan tana wani irin numfashi.
A matuqar firgice hajjan ta miqe ta zauna,don dama bata jima da gama sallar dare ba ta koma ta kwanta
“Zahra’u….zahra’u!….mene ne?,innalillahi wa inna ilaihi raji’un,yi kuka….kiyi kuka zahra’u,barshi ya fito” ta fada taba danne mata qirji,ganin yadda yake sama da qasa numfashinta kuma na wahalar shaqa,cikin ikon Allah ta fusgo numfashin da qarfi sai kuma ta saki wani qaqqarfan kuka ta fada jikin hajja gaba daya ta qanqameta
“Innalillahi” hajja keta maimaitawa,cikin ikon Allah itama zahran saita kama,tsayin wasu mintuna masu tsaho sannan ta iya magana cikin sheshsheqar kuka
“Hajja…..abudul….yassar ya…..mutu,yayi hatsari baya…..n nyabar wajena,ya rasu hajja!” Ta qarashe cikin gunjin kuka.
Sosai hankalin hajjan ya tashi,ta sake qara qarfin salatinta tana kuma maimatawa,wannan dare ya zamewa zahra dare mai tsaho duhu da kuma qunci,haka suka zauna ita kuka hajja lallashi,kafin gari yakai ga wayewa tuni idanunta suka suntuma suka kumbure,qwayar idanunta dukka sun shige ciki.
Suna idar da sallar asuba hajjan ta daga waya ta kira abba yusuf,saboda abba babba baya gari,cikin lokaci qanqani ya iso,bayan su gaisa ta shaida masa zancan rasuwar
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” shima ya dinga maimaitawa
“Yanzu abinda za’ayi….inaga idan gari ya sake shaaa,ka bawa mustapha ko shamsu muqulli sukaita gidansu yaron,don hankalinta bazai taba kwanciya ba,ba zata zauna ba,in yaso idan ya dawo daga kaitan zuwa lokacin mu mun kintsa saiya miqa mu,idan mukaje saimu duka mu dawo tare,ku kuma ko zuwa yamma haka zuwa dare kwa leqa ku yiwa iyayensa maza ta’aziyya”
“To shikenan,Allah yayi masa rahama,yasa ya huta”.
Da qyar hajja ta sanyata tayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga da hijabi,duk wanda ya ganta saiya tausaya mata,saboda yadda gaba daya fuskarta ta sauya saboda kuka,ga wani irin ciwon kai daya saukar mata lokaci daya,har dan zazzabi zazzabi takeji.
Kafin su tafi saiga hafsat ta fito itama a shirye,hajja zatayi qorafin ta koma tace da ita
“Ba za’a barta ta tafi daga ita saisu umaima yara ba,na kirashi na gaya masa mutuwar,nace zan rakata yace babu damuwa”
“Khalas….shikenan” hajja ta fada sanda hafsat din ta shige motar,shamsu ya tayar da motar suka fice.
Ko a cikin motar ma dai kukan take yaqi tsaya mata,ta dora kanta saman kafadar hafsat tana shashsheqa
“Kiyi haquri zahra ki masa addu’a,a yanzu ita yafi buqata”
“Shikenan hafsa…shima ya tafi ya barni,hafsat nice mutum ta qarshe da yazo wajenta,nice mutum ta qarshe daya kira da wayarsa,ashe da yazo bankwana yazo yimin?,ashe ya tafi kenan?” Sosai ta karyarwa da hafsat zuciya,haka taci gaba da lallashinta har suka isa qofar gidan su abdulyasar da taimakon kwatance da lawal ya dinga musu.
Babu kowa qofar gidan sai daidaikin mutane,da alama an tafi kaishi makwancinsa na gaskiya,hafsat din ita ta riqe zahra har zuwa cikin gidan.
Cike gidan yake da mutane,wasu kuka wasu tagumi,hafsat ce mai qarfin halin gaidasu,sannan ta tambayi inda hajiyan abdulyassar din take,aka nuna musu wani falo dake cike da jama’a suka nufi can.
Kana kallonta zaka gane mamansa ce saboda suna kama,tana zaune saman kujera,sanye da ash din hijabi da carbi a hannunta tana ja.
Gabanta suka samu suka isa,zahran ta zube a gabanta hafsa ta zauna gefanta,hafsat ce ta fara yi mata ta’a ziyya sannan zahra cikin shaqewar murya,daga bisani hafsa tace
“Zahra ce hajiya” hafsan ta zaci zataga wani alamu na nuna kulawa ko sanayyar sanin sunan,babu wani alamu na ta gane abinda hafsan ke fada,tadai ce
“Allah sarki,mun gode Allah ya bada lada”.
Zaman shuru ne yaci gaba da wanzuwa a falon,zahra na cikin hijabinta tana kuka,ganin yadda falon ke sake cika yasa hafsan ta sama musu wajen zama daga waje,abinda ta lura dashi har suka tashi hajiyan ma bata lura da tashin nasu ba,zataso tambayar zahran cewa anya sunsanta kuwa?,to amma yanayin da a yanzu take ciki ba lokaci bane na mata wannan tambayar ba.
Awa kusan guda kenan da zamansu a wajen zahra ga dubi hafsa
“Hafsa qishirwa nakeji,bazan kuma iya shan komaj cikin gidan nan ba”
“To muje waje mana mu samu wani shop ko lemo kisha” kai ta kada
“Ruwanma ya wadatar” ta fada tana miqewa da qyar
“Wash kaina” ta fada sanda ta miqe din
“Lafiya?” Hafsa ta tambayeta,saita dan ya mutsa fuska
“Mtsweww,kaina ke ciwo”
“Dole ai,wannan kukan da kikayi ai ba kadan bane”da haka suka taka zuwa wajen gidan.
A yanzun layin a dinke yake da jama’a,da alama har sun dawo kenan,haka yasa sabuwar qwalla suka zirarowa zahra,yanzu haka abdul nacan kwance,nacan kwance qasan qasa,babu kowa saishi kadai,babu kowa sai halayyarsa da ayyukansa.
“Zahra duka shagunan layin nan a rufe suke” taji hafsat na fada,kai ta gyada tana share hawayen fuskarta
“Eh na gani,amma layin nan kamar layin gidansu rabi’ah ishaq ko?,da kika tana rakoni?”
“Eh tabbas,aiga gidan nasu can ma qarshen layi”
“Yauwa,mu qarasa nasha ruwan a can kawai”
“Ok” hafsat ta fada,kai tsaye suka miqe zuwa gaba,wanda gidan ke jerin gidajen dake jikin gidansi abdulyasar din,tsakaninsu da gidansu abdulyasar din gida biyar ne kacal.
Da sallama suka shiga gidan,wata mace dake duqe bakin fanfo tana wanki ta daga kai tana amsa musu sallamar
“Ku qaraso mana” ta fada tana dagowa daga duqen da tayi.
Gaidata sukayi sannan suka shaida mata su din qawayen rabi’ah ne
“Ayyah,kuma gashi bata dade ta fita ba wallahi”murmushin qarfin hali zahra tayi
“Babu komai,dama ruwa muka shigo zamu sha_ta qarashe maganar ta duqawa kamar wadda zatayi ruku’u saboda yadda kanta keci gaba da sara mata
“To babu damuwa,bari A kawo muku” saita yi gaba daga can qarshen tsakar gidan,ta bude wani fridge dan qarami dake qasan rumfa tana cewa
“Hala daga gidan rasuwar gidan su abdul kuke?” Hafsat ce ta amsa mata
“Eh wallahi” cikin nuna jimami da alhini ta sake cewa sanda take ciro ruwan
“Ai mun tashi da tashin hankali yau,mutuwar matashi yaro,babban abun tausayin ma,yau satinsa biyu cif da kai kudin aure…..” Kalma mafi girma da muni data daki zuciya da kunnuwan zahra,kalmar da taji kamar a wani mugun mafarki aka furtata,kafin ta dawo hayyacinta sautin muryar hafsat cike da zallar mamaki ta furta
“Sati biyu da kai kudin aurensa?”amsa musu tayi sanda take rufe fridge din tana dawowa zuwa garesu
“Wallahi Allah,bari kawai….daxun yarinyar da ya kaiwa kudin tazo,abun gwanin ban tausayi,bakiga kukan da take ba,tana faduwa ana dagata,dukkanmu sai data sanyamu qwalla,sai data sake saka hajiyarsa kuka sosai,qarshe kasa zama tayi sai gida aka maidata,kinga keyholder din kai kudin akan window na ma,ni ko amfani da ita bankai ga yi ba” qarashen maganar yazo dai dai da zamewar zahra daga durquson da tayi zuwa zama dabas a qasa
“La haula wala quwwata illa billah” kawai zahran ke fada cikin zuciyarta,bakinta zuwa maqogaronta ya sake bushewa raqayau kamar bata taba kurbar maqwarwa daya ta ruwa ba tunda Allah ya halicceta,tana jin sanda matar ke miqo ruwan amma saita kasa amsa,maimakon karba ma saita miqe tsaye kawai ta nufi qofa,bataga wani sauran amfanin zamanta ba kuma,tana jiyo hafsa na mata godiya gami da sallama.
Tuni ta miqi hanya ba tare dako waiwaye ba,ita kanta hafsat din sai cimmata tayi a hanyar
“Zahra….da kin tsaya ya shamsu ya dawo ya maidamu” kaita girgixa idanunta na sauka kan gungun abokan abdulyasar dake zaune qasan wata rumfa,can ta hango auwal a tsakiyarsu,wani abu ya caki zuciyarta,tsanar auwal din ta kamata,tabbas babu shakka yasan komai,yasan duk abinda ke wakana tunda amininsa ne,dashi aka hada baki,dashi aka rufeta
“Muje kawai hafsa,ma hadu a hanya” a yanayin data ga ta shiga,tasan cewa koda bayani tayi mata babu lallai ta fahinta,don haka taci gaba da binta a baya suna tafe zafin rana na dukansu.
Basuyi nisa ba suka soma jin hirar wasu mata biyu a bayansu
“Kai mutuwa….mutuwa masu gari,babu ruwanta da babba ko yaro,tsoho ko tsohuwa kawai dauka take”
“Hmmm….kedai Allah yasa mu dace,mutuwa ma irin wannan ta abdul ai tafi ratsa jiki da daga hankali,mutuwar saurayi?,sati biyu kacal da kai kudin aure ashe ba za’ayi auren ba,babu ma abu mafi tausayi irin yarinyar daya kaiwa kudin,kamar zata shide wallahi abun tausayi”
“Ai da tausayi,Allah yasa mu cika da imani”.
Cak zahran da hafsan duka suka tsaya,a sace zahra ya waiwaya ta dubesu,dukkansu babu wanda tasan fuskarsa a cikinsu,suna tsaye sukazo suka giftasu,da alama ma basu ankara da tsaiwarsu ba,sukayi gaba suna ci gaba da hirarsu.
A zafafe zahra ta soma takawa tana koma zuwa layin da suka baro,hafsa ta cafki hannunta
“Ina zaki?”
“Zanyi magana da auwal” daga haka ta zame hannunta ta koma.
Suna nan inda ta barsu,harda qarin wasu abokan nashi wadanda yakanje dasu lokaci zuwa lokaci,dukkansu tasan fuskarsu sunsan fuskarta.
Auwal din ne ya soma ganinta,saiya miqe,kafin ya tarbota harta iso wajen,cikin tsananin nuna jimami yace
“Sannu zahra….ashe kin iso,ya mukaji da wannan abu daya samemu?” Dukka sauran abokan sai suka soma yunqurin yi mata gaisuwa,a qalla sunkusa su biyar,hankalinta ta maida kan auwal
“Zuwa nayi na maka godiya kan zalunci da munafuntata da kukayi,na gode sosai,ubangiji ya saka da alkhairi” cikin yanayi na rudewa ya soma magana
“Munafuntata kamar ya?” Tana ji a ranta baqincikin da datake ji ba zata iya rufeshi ba
“Da kun gayamin kai da abdulyassar ban dace dashi ba,da kun gayamin yakai kudin aure…dana fahinceku na kuma rabu dashi ta sauqi bawai ta irin wannan hanyar ba”.
Sai auwal din ya dora hannu saman ka yana cewa
“Kai innalillahi,Allah ya tsinewa munafuki…..wai mutum ma na qarqashin qasa,ko awanni biyu bai cika ba amma ba zasu bar gawarshi ta huta ba….to duk wanda ma ya gaya miki qarya yake,kawai ‘yan hada husuma ne wadanda basaso a zauna lafiya,masu zuwa lahira da qoqon dambu….ko ba haka bane mansir?” Ya fada yana maida dubansa ga daya abokin nasa wanda daga auwal din sai shi a wadanda abdulyassar din yafi zuwa dasu
“Haka yake….hakane auwal”
“Baya ga key holder din dana gani!” Ta fada a zafafe
“Au….wannan fa friends ne suka hada suna tsokanarsa saboda yadda sukaga ya tsani yarinyar….just for fun akayishi,shine mutane suka sauya zancan?”
“Dakata!” Ta fada da sauri tana daga masa hannu ganin yanason raina mata hankali
“Dukkan abinda bawa ya shuka shi zai girba,kaje….na barku da Allah” da haka ta juya ta soma barin wajen,tana ji abokan nasa na qwala mata kira hankali tashe,saidai babu wanda ta waiwaya ta kalla bare ta koma,saima ta tsaida musu napep ta haye hafsat tabi bayanta.
Wani yawu mai tauri take hadewa cikin motar,gaba daya ji take zuciyarta ta bushe ta qeqashe,lamarin maza ya fice mata fit a ka,me yasa ne basu da *ALฦIBLA?* me yasa kowanne da kalar zaluncinsa ga ‘ya mace?,saboda muna da rauni?,saboda ba zamu iya aurar da kanmu ba saidai a auremu?,me yasa mazan zamanin nan suka zama fitina ga rayuwar ‘ya’ya mata?,me yasa duk wani bala’i,shiga ha’ula’i da tashin hankalin mace mafi akasari kan ษa namiji ne?,baki auren ba baki huta ba,kinyi auren baki huta ba,sai yaushe diya mace zata hutama ranta?,ba a iya kanta ba,akan mata ‘yan uwanta da yawa taga irin hakan,me yasa suka maidashi kamar anko ko gasa,sun maidashi abun kwalliya,YAUDARA!….shin basa tunani ne?,basa tunanin cewa suna wataran iyayen wasu ne?,basa tsoro da fargabar kada abinda sukayi a fanshe kan diyoyinsu wadanda basuji ba basu gani ba?,inda ta godewa Allah….babu wanda ta saidawa mutuncinta,babu wanda yayi nasarar tarwatsa mutuncinta,yau inda acw ta aikata hakan ta tabbatar nadama da dana sanin da take ciki ta zarta ta yanzu,sai Allah yasa bata watsar da tarbiyyarta ba,bata bari rudi da zaqin soyayya ya jata ta aikata babban kuskure mai tarwatsa rayuwa ba,kuskuren da bashi gyaruwa har abada, yanzu kam takai qarshe…..takai maqura,enought is enough….ta dauki iya abinda zata iya dauka,ya isa haka!,ya isa!……
Ire iren wadan nan tunane tunane su ta dinga yi har suka qaraso gida,wanda ko tsaiwa a biya mai napep din kudinsa batayi ba,batasan ya suka qarke da hafsat ba.
A falo ta tadda hajja tana karyawa,bata bi ta kanta ba ta wuce dakinta da wani irin sassarfa,gaban mudubi ta tsaya,ta cire hijabi ta kuma cire doguwar rigar jikinta,daga ita sai vest da under wear,kanta take qarewa kallo lungu da saqo,sai a sannan kukan ya qwace mata,da gudunsa kuwa kukan yazo,kukan da zaka tabbatar da cewa yana fita ne daga tsakiyar zuciya,yana kuma tafe da wani irin qunci da baqinciki
“Me na rasa?,meye bani dashi?,meye illata!,ku gayamin!” Ta fada a fili hawaye na gudu tana kuma tambayar kanta da kanta.
Ji tayi an rungumeta,hajjanta ce
“Me haka zahra’u?,ki nutsu mana,kita maimaita Allahumma ajirni fi musibaty,wa akhlifni kairan min ha” da muryar kuka ta kama addu’ar tana ta maimaitawa har ta soma samun nutsuwa,don haka hajjan ta zaunar da ita gefan gadon tana shafa bayanta kadan kadan tana tayata nanata addu’ar.
*_wajen daya kamata a tsaya mu fafata kan wanda yafi iya yaudara cikin samarin nan uku yayi,da kuma matakin daya kamata budurwa ta dauka idan ta samu kanta cikin irin wannan situation din,idan kuna da buqata ku sanar min domin bude grp musamman saboda haka,karku manta,dama munce akwai fafatawa da tattaunawa kan mai zafi kan kowanne littafi,ma’assalam_*
23/10/2021, 08:41 – ๐๐ป๐๐ป: 16
*KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พโ๐พ,kada ki dauka ko kiyi amfani da kayan da ba naki bane,ba kuma mallakinki bane!*
A hankali aka turo qofar dakin,hafsat ce jiki a matuqar sanyaye,idanunta kan zahran,zuwa sannan kukan da takeyi ya ragu sai ajiyar zuciya
“Zahra…..sawwama nason magana dake,tana falo”
“Sawwama?” Ta tambaya tana kallon hafsat
“Eh sawwama ta layin shago tara” ta ganeta,duk da babu alaqa tsakaninsu,saidai gaisuwar mutuci saboda babu tazara sosai tsakanin unguwanninsu
“Lafiya?” Zahran ta tambayi hafsan tana kallon yadda yanayin fuskarta ta sauya fiye da dazu
“Daga gaisuwar gidansu abdulyassar take” shuru tayi yana juya maganar,to meye ya faru?,saita miqe kawai kai tsaye ta fice zuwa falon.
Kallo daya ta yiwa sawwaman tasan cewa lallai tasha kuka itama ba na wasa ba,gaba daya idanunta sun tasa har lebunanta,zahran ta qarasa a hankali ta zauna gefan sawwaman
“Ashe kema kinsan abdulyasar?” Kai ta iya jinjinawa kawai ba tare da tace komai ba,saboda wano ciwo dake taso mata a qirji
“Ashe bani kadai bace?….bani kadai ya yiwa haka ba?” Maganar da taja hankalin zahra kenan da ta daga kai ta dubi sawwaman,kallon da take mata yake nuna tana da buqatar qarin bayani
“Abdul yayimin alqawarin aure….infact ma yau sati daya da tura magabatansa gidanmu,amma abun mamaki sai nakejin yau sati biyu dakai kudinsa wajen wata walida….baya ga haka ashe kema….” Hannu ta dagawa sawwama murmushin takaici na fita daga fuskar zahran,a take wasu kalamai da abdul din yake yawan gaya mata suka dinga dawo mata aka tar kamar a sannan yake furta mata su
“Duk duniya akwai wata bayan ke?,duk duniya akwai wata diya mace data isa ta rabani dake?,me kike fargaba a kaina?,akwai wata mace data isa na bata lokacina akanta na tafi zance wajenta idan bake ba…..zahra duk kyan mace….duk ajinta….duk gayunta saidai tabi bayanki”
“Duk abinda kika fada haka ne….hakane sawwama” kuka sawwaman ta fashe dashi,wanda da alama zallar baqinciki da bacin rai yake cin zuciyarta
“Abdul ya cuceni,ya zalunceni…abdul…” Da sauri hajja data fito tace
“Kiy shuru karki sake cewa komai,kuyi haquri ku masa addu’ar Allah ya yafe masa kuskuren daya tafka” miqewa zahra tayi ta koma daki don ba zata iya ci gaba da tattauna wannan maganar ba,hajja da hafsat sune suka sallami sawwama.
A ranar ko kusa ko alama bacci bai gitta ta ba bare ya samu nasarar daukarta ba,duk juyin da zatayin abdul din take tunawa,kalamansa da salon yadda yaso sabuleta daga rayuwarta ta wata siga mai masifar ciwo,shima so yayi yayi mata irin yadda nasir da nuraddeen sukayi mata?,so yayi ya karya mata zuciya?,yayi gutsi gutsi da ita?,don ta tabbatar a yadda ta bawa soyayyar abdulyasar amanna da Allah ya barshi da ransa hakan ya faru babu tantama zata iya rasa lafiyar zuciya,saita goge hawayenta ta miqe ta zauna tana gayawa kanta,wala’alla Allah ne ya sota da rahama ya daukeshi,ubangiji baiyi zataga wannan baqinciki da bacin ran da tashin hankalin ba,amma lallai ta yanke tsammani,hakanan ta debe haso daga dukkan lamarin maza,abun ba qarami bane,sha’aninsu ya wuce tunaninta.
Kwanyarta tana iya tuna mata sanda abdulyasar din yake musanyan waya da ita,ya aje mata wayarsa yacw ta bashi tata aga wanda yafi gaskiya a cikinsu,aga wanda saurayi ko budurwa zasu kira,ashe a sannan wala’alla sabon layi kenan yake sakawa?,ko layin da ba’a sanshi dashi ba?.
Sannan tana iya tuna sanda yakan rufeta da masifa cikin zallar kishi,yana cin alwashin duk randa yaga wani ya kulata ko ta tsaya dashi,ba shakka saiya masa diban karen mahaukaciya ya sadashi da qasa ya take wuyansa,kome zai faru indai a kanta ne saidai ya faru,tana iya tuna sanda yake tsaidata ya rakata makaranta ko wani guri da kansa,tana iya tuna sanda fafur ya hanata shiga kasuwa,ashe duk bogi ce?,qarya ce?,ashe bayan ita hadda sawwama wadda yakai magabatansa?,anya ko magabatan gaske ne bana haya bane?,anya kuwa bana bogi bane?,saboda babu iyayen arziqin da zasuje maka maganar aure wannan satin,wani satin kuma suje maka gidan su wata da saninsu,to bayan ita da sawwama mata nawa ya yaudara?,wannan Allah ne kawai masani.
Cikin daren ta yiwa kanta da kanta fada,ta gayawa kanta cewa da batasan abdulyasar ba,kafinshi kuma wasu sun yaudareta,ta kuma ci gaba da rayuwarta ba tare da komai ya sameta koya sauya ba,hakanan a yanzun ma zataci gaba da rayuwa babu shi,zata dora daga inda ta tsaya,ba zata bari damuwar wanda baisan da damuwarta ta dameta ba,damuwar wanda baya doron duniyar ma gaba daya,kai koda yana raye…..dukkan namijin da zai miki haka bai cancanci ki damu kanki saboda shi ba,saboda ya nunawa duniya cewa u r a zero behind decimal point,baki da wani amfani a tare dashi,keda babu duka daya,don me zaki damu da irin wadan nan?,me yasa irin wannan namijin zaki dora damuwarki a kanshi?,a daren,a kuma sannan ta yiwa kanta alaqawarin cire dukkan damuwar wani abun banza namijin daya yaudareta,ta kuma dasawa kanta takunkumin tserewa soyayya da kuma nisantarta bakin iyawarta,har sai taga abinda ya turewa buzu nadi,ko kuma abinda alqalamin qaddararta ya rubuta ya tabbata.
Sosai hajja tayi mamaki washegari da taga sakewa a tare da zahran,wanda sam batayi tsammamin ganin hakan tattare da ita ba,bata tanka mata ba sai taci gaba da biye mata,can qasan ranta tausayin zahran yana ratsata,duk inda ta gifta sai ta bita da kallo,haqiqa ta hadu da jarrabawa mai tsauri da wahala,amma kullum fatanta ya zama nasara ce a rayuwarta.
A irin hakan zahran ta lura da kallon da hajjan ke mata,ta fahimceta sarai,amma sai tayi murmushi
“Wai ya kiketa kallona tsohuwa?,kodai na miki kyau ne?” Kai hajjan ta gyada sannan tace
“Ina miki fata da addu’ar wannan ya zama karonki na qarshe da zaki sake fuskantar qalubale irin wannan kaf rayuwarki” saita rausayar dakai kawai,cikin zuciyarta tana amsa da amin.
Wannan karon ma umminta kasa jurewa tayi sai data titsiyeta
“Innawuro…..ki gayamin gaskiya idan akwai wani abu a qasa….”
“Wallahi ummi bansan komai ba,bansan meke faruwa ba” shuru ummin ta danyi na wasu mintina,sannan a sanyaye tace
“Kin tabbatar ba saida musu mutuncinki kike ba?” Sosai maganar tayi ma ummin kanta nauyi da zahran,saidai ya zamana dole ta yiwa zahran wannan tambayar,saboda uwa bai kamata a muhallin irin wannan da kike bincike da qwaqwwafi ba ki dinga boye wasu maganganun,wai don kawai kunya da nauyinsu,kan zahran a qasa tana fitar da qwalla tace
“Allah ya tsareni ummi,ubangiji ya tsare miki ni,kuma har abada bana fatan ya bani ikon ko damar da zata sanya nayi fatali da tarbiyyar da kuka gine ni a kanta,wallahi wallahi koda tunanin aikata hakan bai taba zuwa kaina ba bare na aikata ummi,ki yarda da ‘yarki” nannauyar ajiyar zuciya ta sauke
“Na yarda dake…..ba kuma wai ina zarginki bane,amma ya zama dole nayi aikina na uwa na bincika da kyau,na tabbatar addu’ar da kullum ba dare ba rana da nake miki keda ‘yar uwarki dama sauran dukkan yaran dake gidan nan ba zata fadi qasa banza ba,na yarda jarabtace kamar yadda take rubuce a rayuwar kowanne musulmi…..kici gaba da addu’a,kada dimuwa ko zafin jarrabawa yasa ki kasa cin ribar haqurinki….karbi wannan” ta fada taba miqa mata wata doguwar takarda,addu’o’ine a rubuce a cikinta,addu’o’i ingantattu masu ma’ana,wanda suke dauke da kalmomi masu girma da tsarki gami da kambama ubangiji,wadanda su kadai sun isa sanya nutsuwa a zuciyar bawa da samun biyan buqata daga wajen ubangijin talikai.
Godiya ta yiwa ummin sannan ta baro sashen,tun a ranar sata soma addu’o’in ta dinga jin sukuni da nutsuwa yana ratsata,ta sake jin zuciyarta wasai kuma fes,haqiqa ubangiji yayi gaskiya da yace ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata suke samun nutsuwa,lallai babu abinda yakai ambaton ubangiji sanya nutsuwa a zuciyar mai damuwa.
Cikin satin ta hada kayanta ta koma bakin karatunta,tunda komai ya daidaita an koma makaranta,ta kuma fuskanci karatunta da kyau,ta watsar da duk wani damuwa da hayaniyar soyayya,babu wani da namiji da take tsaiwa ta kalla sau biyu ma bare ta saurari kalaman bakinsa,duk ta musu kudin goro gaba dayansu.
*_BAYAN WANI LOKACI_*
Zaune take cikin dakin kwanan dalibai wanda ya zama mallakinsu ita da hindatu batula da jannah,yayin da nadiya da farida suke daki daya daura da nasu suda wasu mutum biyun,to amma idan baka sani ba zaka zaci dukkansu daki guda suke,saboda kusan komai a nan dakinsu zahran sukeyi,hatta da abinci daya sukeyi,duk da basi fiya ma girma abinci ba,saidai suyo takeaway,idan kaga girkakken abinci to aikin zahra ne,sau tari sukan mata qorafin tana walahar da kanta da wani girki,ta bari kawai suyo takeaway suci,takan ce
“Ni ban saba bafa,abincin da zaka girka da kanka yafi albarka,sannan kayan anincin da nazo dasu daga gida saina jibgesu su lalace?,ko kuma na maidasu gida idan an tambayeni nace qawaye suna siya min ina ci?” To su dinma idan ta dafa kowa dafifi yake wajen ci,saboda ita din ba baya bace wajen iya girki.
Kamar yau dinma dakin nasu cike yake da hayaniyar ‘yammata,kasancewar suna cikin ranakun qarshen mako ne,kuma wannan karon kusan dukkaninsu basuje gida weekend ba,ita zahra saboda CA da zasu fara,kuma a satin zasuyi kusan gudan hudu,shi yasa taga gwara ta zauna waje guda tayi karatu sosai.
Yau dinma ita ta dafa musu abincin,kowa yaci ya qoshi,da suka kammala saita taja takardunta da system dinta saman gadonta ta barsu nan tsakar dakin kan carfet din da suka malale dakin dashi
“Yar allazi boko” taji su suna tsokanarta,bata kulasu ba sai murmushi kawai datayi taci gaba da karatunta,batason ta tsaya tankasu su dauke mata hankalinta,suma sukanyi karatun,amma saidai baiko kai nata ba,sukance sun gaji basu iyawa,da sun taba iya yadda zasu iya suke ajewa su shiga sabgarsu.
Yanzun ma hira suke masu charting nayi,harda qawayen su batula daga wani dakin,ana tsaka da haka taji mardiyya qawae farida ta luqa ashar
“Ferry….zoki gani….maza maza zo kiga” da sauri farida ta aje tata wayar ta matso kusa da mardiyya,saita zare glass din fuskarta,da qarfi ta furta
“What…..muhsin ne fa,wata fa naga ya dora yana furta kalaman soyayya a qasan pic dinta,kan bala’i” saita fada tana dauko wayarta da sauri tana duba wajen status dinta
“Zo kiga,ni bai nuna ajerin nawa status din ba,babu status dinsa” dariya wata rabi’ah dake zaune kusa dasu tayi,ta tashi ta zauna tana cewa
“Wai baku gane meke faruwa bane,ai na taba gaya miki farida tun kwanaki kika qi yarda,kinzo kina wani jin kin isa kinkai,wai waye ya gaya miki ma cewa a yanzu ana cika baki kan namiji?,ai wannan lokacin ya wuce,lokacin cika baki da alfahari,da basu amanna dari bisa dari…..everybody listen to me” ta fada tana gyara zamanta sosai a tsakiyarsu tare da miqe qafafunta,hakanan maganar da rabi’ah din ta soma fada ta dauki hankalin zahra,bata sauke littafin hannunta ba amma hankalinta na kanta
“Luggar mazan yanzu…..zasu iya yin budurwa dari ko dubu ta watsapp….kuma zasu iya dora hotonta a status…amma kuma,duk sanda zasu dora hoton daya,tofa zasu cire dukkan sauran su sanyasu a jerin wadanda a ranar ba zasuga status dinsu ba,ba zasu ciresu ba har sai hoton yayi disappering,ko kuma ranar naki pic din zasu saka,saisu cilla waccar cikin inda suka ciroki ke kuma a fito dake,donki gani,kiji dadi,ki kuma qara amanna dasu…so dukka abun bugene,duk ta yadda suka biyo miki ki bi musu ta haka,kada ku saurara kunji….kuyita musu yadda suke muku kawai,dakun samu na dauka ku dauka ku watsar dasu” ta qarasa fada tana sheqewa da dariya.
Maganar status din ta baiwa zahra mamaki,wato kullum sabon salo suke fiddawa?,saidai fatan samun shiriya,amma kuma zancan gogayya da samari barkatai sam shawarar batayi mata ba,saita tabe bakinta kawai taci gaba da karatunta,gefe guda hayaniyarsu tana cika mata kunne,da Allah ya taimaketa zuwa wani lokaci suka fara raguwa da kadan kadan,har dakin ya rage daga ita sai hindatu wadda ta haye gado ta kwanta zata dan rage bacci a cewarta kafin ta tashi tayi karatu.
Turo qofar dakin da aka sakeyi da qarfi yasa zahra dagowa tana fatan ba sune suka sake dawowa ba,basu din bane yanzun jannah ce,sanye da straight gown da hill shoes,sai qaramar hand bag da qaramin mayafi data nade wuyanta dashi,kusan shigarta kenan wanda kusan kullum sai sunyi rigima da zahra akan haka.
Yau din fuskarta sam babu alamun walwala,gefan gadonta ta samu ta zube tana zare mayafin kanta cikin masifa take magana
“Ni hisham zaiwa haka?,ni zaiwa wannan akuyancin?” Hindatu dake kwance bacci ya fara dibarta ta daga kai tana dubanta
“Ke kuma meya hadaki da hisham din naki yau?” Iska ta furzar daga bakinta sannan ta zame ‘yar hular dake kanta ta sabule takalminta ta zauna sosai saman gadon tana harde hannayenta
“Yau ni hisham zai fito qarara yacemin nayi haquri da maganar aurenmu….shi matarsa ta gida ta isheshi” sosai hindatun ta tashi ta zauna
“Hisham din da kansa da bakinsa?” Kai ta jinjina cikin tsananin jin zafi
“Shi din fa….shi yasa ya kasa zuwa ya gaida dad,ko mami ma danace yaje cewa yayi wasu shirye shirye yakeson ya kammala tukunna….”dauke kanta hindatu tayi zuwa sashen da zahra ke zaune
“Kinji fa zahra?” Saita ture littafinta gefe
“Naji” ta fada tana saukowa daga saman gadonta,ta daura dankwali sannan ta fita zuwa toilet,mintina kadan ta dawo ta samesu suna tattaunawa,ta koma bakin gadonta ta zauna sannan ta dubi jannah.
“A inda kullum muke fada dake kenan fadan gaskiya….ita kuma gaskiya daci gareta,hakanan fure take bata ‘ya’ya,ita kuma rayuwa duk abinda ka shuka shi zaka girba,ba zaka taba shuka qaya ba kace inibi kakeson cira,jannah…..na dade ina miki nuni da waye hisham,illa da dafin dake tattare dashi,hisham yayi amfani da son da kike masa yayi fooling naki,ya kuma yi amfani da damarsa a kanki,a yanzu ya gaji dake ne shi yasa ya fito miki ta wannan hanyar kai tsaye,don ya ajjiyeki ya kuma lalubi wata mai tsautsayin me qaramin tunanin….kiyi haquri da harsh word da nake amfani dasu a kanki,kawai ni duk inda gaskiya irin wannan tazo gittawa ta gabana saina fadeta,abinda yasa na kira dame qaramin tunani shine….babu ta yadda wanda yakeson ya aureki ki zame masa uwar yaransa kuma mace ta gari abar alfahari ya daukeki cikin motarsa yana yawo dake,ya daukeki ba cikin gidanku ba,ba gaban iyayenki ba,ku hadu a wani waje ya saki gaban mota kuna yawo,yaje ya killace ‘yarsa,yaje ya killace matarsa,yaje ya killace mamarsa….amma kefa?,saboda baki da wani daraja,baki da wani matsayi da za’a baki,shi yasa bai dauki hakan a bakin komai ba,daga sanda wanda yace miki yana son aurenki yazo miki da magana kan matarsa qazama ce,matarsa bata iya soyayya ba,matarsa yar qauye ce,kece kika iya komai,matarsa ta gaza ta kowanne fanni,amma kuma ko yaushe yana nanuqe dake,yana fasa miki kai,ta wani sashen kuma a dabarance yana qoqarin ku dinga hulda ta hada jiki romance da kissess amma kuma ko sau daya bai taba tunanin kiyi aure ba,ke koda ya taba tunanin hakan ko furtawa toba shakka na yaudara ne,daga sannan kuma kin samu babbar matsala,a haka da kike yawo dashi janna,cikin irin wannan shigar da wannan rayuwar kike tunanin zaya daukeki yakai gidansa a matsayin matar aure?,me zaya killace?,me zai burgeshi har yakai ga aikata hakan?,bakayi haka bama da sautayi a wannan zamanin ya kuka qarke dashi bare ace kinyi?,ni na isheki manuniya da ishara,kafin kice hisham ya yaudareki ya kamata ki fara cewa kin yaudari kanki,idan maganata ta miki zafi jannah kiyi haquri”sosai taga yadda jikinta yayi masifar sanyi,saita kasa cewa komai,sai dogon nazari da tunani data fada,bama ita kadai ba har hindatu dake kwance.
********** ******** ********
*_ฦADDARA….ta riga fata_*
Cikin sati sunyi CA sa yawa kamar yadda ta zata tun wancan satin,to satin gaba ma kusan akwai sauran tarin karatuttuka,hakan ya sanya kowacce ta sake haqura da zuwa gida weekend,saidai kuma sun shirya zuwa daya daga cikin masaukan baqi hotel don su huta a can a cewarsu.
Sanda suke shirya tafiyar zahra na zaune tana jinsu bata tanka ba,tadai yanke idan sun tafin gida zata wuce ko kwana guda ne ta rage ta dawo.
Saida suka gama hayaniyar yadda zasu gudanar da ranakun qarshen makon sannan suka soma raguwa sannan hindatu ta iso kusa da zahra ta zauna
“Amini….ko sau daya baki taba karar binmu bafa” kallonta tayi
“Ko sha’awa wajen banayi,me zai kaini nikam,kuma ina mamakin yadda kuka maida wajen kamar ba’a bakin komai ba zuwanshi” dariya sosai hindatu tayi
“Kinga,mufa mutanenmu ne suka yiwa wajen mummunan fassara,amma a qa’ida wajene da iyali ma suke iya zuwa su kama daki suyi dukka iya kwanakin da sukeso,su huta daga hayaniyar gida data jama’a,ni kusan duk qarshen wata bazan manta ba kafin nakai haka,sannan abubuwa basu yiwa daddy yawa ba muna zuwa muyi kwana biyu haka ko uku,ba wani abu bane me muni,saidai idan mutum dama da mummunar niyyarsa yaje,don Allah kizo muje wannan karon,sau daya dai tak” kai zahran ta girgiza
“Naji bayananki,amma am sorry bazan iya zuwa ba hindatu saikun dawo” ranta ta bata da alamun bataji dadi ba
“Shikenan….tunda baki yarda dani ba,komai kika fadamin ina qoqarin yi dabi,bana tsallakewa shawararki saboda nina aminta dake….na gode,dama sunatamin dariyar cewa ni kadai na damu dake,yau na gasgata hakan” saita sauka daga gefan gadon ta koma nata tana hada kayan da zasu je dasu.
Ganin yadda harta gama hada kayan bata kalleta ba dakin shuru yasa taji duk babu dadi,ba kaifi hindatun tana daukar duka shawarin zahran da qoqarin ganin tayi abinda zahran keso,da gaske taji haushinta kenan sosai,har ta isa bakin qofa zata fita zahran ta kira sunanta
“Haushi kikaji kenan?” Kafada ta daga
“Saboda me?,bayan baki yarda dani ba?,akanme zan takuraki kiyi abinda baki niyya ba” kaita kada tana murmushi
“Zanje….shikenan ko?” Cikin murna ta dawo
“Na gode sosai….ina mai tabbatar miki zakiji dadin tafiyar da zamuyi,gobe da kanki zaki ce muje” murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.
23/10/2021, 08:41 – ๐๐ป๐๐ป: 17
*KIJI TSORON ALLAH โ๐พโ๐พโ๐พ,karki taba kayan da ba naki ba ba kuma mallakinki bane*
ฦarfe hudu na yammacin ranar suka dunguma su shidda cikin motar gidansu hindatun suka tafi.
ฦaya daga cikin tsadaddu kuma qawatattun hotel sukayi masauki,suka kama daki guda babba wanda zai ishesu a wadace,itakam tana zaune daga gefe tana kallonsu yadda suka sake tamkar suna cikin gida ko cikin makaranta,ita kam har cikin ranta bata jin wani walwala ko karsashi ko kuma wani jin dadin zuwa wajen,sai take ji acikin zuciyarta duka wani irin babu dadi,sai takejin kamar ta aikata wani mummunan abu mara kyau,haka kawai takejin babu dadi har qasan ranta,har sai da farida ta ankara da haka
“Ki sake mana haba zahra,mu kadai ne fa a dakin,babu wanda yake shigo mana ko ya isa ya shigo” murmushi kawai ta musu,sai tabi lafiyar lafiyayyen gadon dake dakin tayi kwanciyarta akai,don kafin su fito tasha karatu sosai,tana son ta huta kafin ta sake dora wani,don ta taho da dukka litattafanta,har suna tsokanarta cewa ba hutawa zataje yi ba kenan,tunda ba zata bar qwaqwalwarta ta huta ba.
Suna ta hayaniya da walwalarsu har zuwa sanda akayi knocking qofar aka kawo musu abincin dare,kowa ya fara diban nasa duk da cewa akwai sauran lokaci kafin ma ayi sallar magariba din,hindatu ce ta dubi zahran
“Zahra….ga abinci,ki sauko kowa nacin nasa” kaita kada tana hamma
“Kai a’ah,sai an idar da sallah” daga haka ta sake gyara kwanciyarta,tun tana jin hirarrakinsu sama sama har ta fara daina jiyosu,babu jimawa kuwa bacci mai nauyi ya debeta.
Sanda ta farka hindatu ce kawai tayi saura a dakin,tana niyyar saukowa daga gadon tana duba agogo,qarfe bakwai da ashirin na dare,inda Allah ya taimaketa tana hutun sallah
“Duka ina suka shiga?” Ta jefawa hindatun tambayar wadda ke tsaye gaban madubi tana gyara sumarta da mayukan gyaran kai
“Duk sun fice,amma sun kusa dawowa”
“Fita kuma?,nan duka bai ishesu yawo ba?” Ta sake tambayar hindatun
“Nan kusa da inda muke nefa,aka bude wani sabon wajen cin abinci daxun,to na wani abokin farida ne,shine ya gayyacesu” baki kawai ta tabe,ba shakka duk inda wayewa tayi yawa matsala ce,su a wajensun wannan normal ne,ba wani abu bane,amma a asalin tarbiyyar malam bahaushe wannan din mummunar illa ce,saita miqe ta shiga toilet ta canza pad ta kuma daura alwala ta dawo ta zauna bakin gadon tana karanto azkar dinta na maraice da bata samu damar karantowa ba,tana yi tana duban hindatu daketa shiri da alama fita zatayi,batace mata komai ba har sai data ga ta daga waya tayi magana na ‘yan mintuna ta aje,ta dauki mayafinta tana yafawa
“Ina kuma zaki kema?” Waiwaya tayi tana duban zahran
“Waya zamuje siya nida mudassir a glass show,minti talatin ta isa munje mun dawo” sosai zahran ta hade fuska
“Yanzu kina ganin kamata ce ki fita da saurayi takwas saura na dare siyan waya?,cikin motarsa daga ke saishi?”
“Babu komai qawata kada ki damu,ko a gida dana sanarwa mommy muke tafiya” maganar ta ratsata,batasan illar boko xallah ba sai yanxu,gaba daya duk wani abu daya kamata a kalleshi amatsayin abun qyama suba hakan bane a wajensu saboda rashin tasirin ilimin addini,saita miqe ta isa inda hindatun ke tsaye.
“Hindatu,a koda yaushe inason ki dinga tuna cewa kina rayuwa ne a qasar hausa,ina son ki dinga tuna cewa qa’ida da kwaikwayo kan tafarkin addini shine gaba da komai,na miki uzurin rashin tashi kan irin nawa bigiren,wala’alla har a zuciyarki ba komai bane hakan,amma idan baki sani ba bari na gaya miki illar…..akwai babbar illa a wajen ‘ya mace ko ince ganganci wajen shiga motar wani da namiji,nasha maimaita miki wannan maganar….abinda yasa na nace mata shine,shiga motar da namiji ki yadda ya tuqaki shine mafarin komai,shine sila da dalili na faruwar komai,komai zai iya faruwa,idan nace komai ciki harda rasa budurcinki gaba daya…..” Idanu hindatun ta qwalalo
“Ki yarda dani qawa…..wallahi ban taba zina ba,ban taba bada kaina ba” murmushi zahra tayi ta dafa kafadarta
“Haba hindatu….ta yaya zan miki wannan mummunan qazafin,amma idan kin kubuta daga zargina sauran mutane fa,kin isa ki wanke kanki?,akwai abubuwan da zaka dinga aikatawa da zasu iya ja maka mummunan zargi da zato daga mutane,zargi mai wuyar wanke kai,irin wannan rayuwar,ku kunsan bakwa wani mummunan aikin,amma shaidar da mutane zasu muku itace ku bana gari bane,idan kin shiga motarsa komai bai faru ba zaki iya kubuta daga riqe miki hannu da zaiyi?,zaki iya kare kanki daga yunqurin miki kiss ko runguma?,idan yaso cutar dake kin isa ki bawa kanki kariya?,sannan kome ya miki baki da hujja,laifinki ne,ke kika kai kanki hindatu” sosai jikinta yayi sanyi,ta daga kai tana duban zahran
“Gaskiya kika gayamin qawata,na kuma fahimta maganarki,sannan na gode miki qwarai da gaske,ban dauki hakan a wata babbar tawaya ba sai da kika nusashsheni,in sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba” ta qarashe maganar tana cire mayafinta,sannan ta dauki wayarta ta tura masa tex ta koma ta zauna.
Daya daga cikin halayen hindatun da suke burge zahra kenan,sauqin kai da kuma saurin daukan shawara.
Tana zama saiga sauran suna shigowa,kafin kace me sun sake hautsina dakin
“Kai….kai jama’a,ku bakwa gajiya dan Allah da hayaniya?” Inji zahra da suka hana kunnuwanta sakat,dariya suka saka gaba daya jannah tace
“Kamar yadda baki gajiya da karatu ba” saita saki murmushi kawai tana gyada kai,tasan me hali dai bazai fasa halinsa ba.
***** ***** ****** *****
Washegari a daki dukka suka yini a tare,saidai da yammaci lis suka shirya dukkansu domin zuwa siyayyan kayayyakin amfani da kuma kallon wani sabon hausa film da za’a haska a film house cinema dake ado bayero mall.
Fir tace ba zata bisu ba,hakanan idan suka jima basu dawo ba saidai suzo suga ta tafi,basu ji dadi ba,saboda sunce ba jimawa zasuyi ba,hakanan bai kyautu su barta ita kadai ba,amma tace sam itadai sai sun dawo,hasalima akwai sauran karatunta da bata qarashe ba,haka suka shirya suke fice a motar jannah.
Karatunta taci gaba dayi,lokaci lokaci tana kallon tv dake aiki,saidai ba’a jima ba taji zaman ya gundireta,shuru hakanan babu kowa ba motsin kowa,don haka ta aje littafin tana duba agogo,dab ake da kiran sallar magariba,koda ta fita bata da matsala,tunda tana fashin sallah,don haka ta dauki mayafin doguwar rigarta ta yane kanta,sannan ta zira plate din takalminta daya dace da kayan jikinta,ta buda dakin ta fito.
A sama suke,saidai akwai qawatacciya kuma doguwar baranda ta bayan dakunan wadda zaka iya hangen farfajiyar hotel din idan ka tsaya ta jikinta,hakanan wanda yake qasa shima zai iya ganinka idan kaso,anan din ta tsaya,tana kallon yadda mutane ke kai kawo cikin hotel din kowa na sabgar gabansa,wanda yawanci duk wanda zai shigo ko ya fita cikin mota yake,da kadan da kadan take kallon wajen tana kuma karantar wasu abubuwa masu tarin yawa.
A qalla ta shafe kusan minti ashirin tsaye a haka har duhu yadan fara yi sannan taji tsaiwar ta soma isarta,saita janye idanunta da niyyar juyawa tabar wajen,saidai caraf idanun nata suka fada kansa.
Matashin saurayine fari sol,ma’abocin tsaho hakanan baida jiki,mai yalwar baqar sumar kai da kuma qasumba,sanyw da qananun kaya yana kuma tsaye jikin motarsa idanunsa fes bisa kanta,tsaki taja mai qarfi data lura da irin kallon qurilla da yake mata,ranta yana quna,tana fadi a ranta,wama yasan adadin lokacin da ya shafe yana kallonta bata sani ba.
Koda ta koma daki bandaki ta shiga ta sauya audugar jikinta,sannan ta dawo ta fesawa hannuwanta da jikinta turare ta koma kan karatunta,tanayi tana duba lokaci,saidai har yanzu babu su hindatun babu alamarsu,ranta ya soma baci,ta soma jin haushin kanta kan me yasa ta biyosu?,bayan gaba daya tsarin rayuwarsu ma ba daya bane?,yanzu meye amfanin zamanta a nan?,saita dauki wayarta ta soma kira.
Saidai duk wadda ta kira din tana shiga tana kuma ringing amma ba’a dagawa,babu kuma amsa,haka ta qaraci kiransu gaba dayansu babu wanda ya daga,zuwa sannan tara da rabi na dare agogo ke nuna mata,ga yunwa tana ji,duk da sun gaya mata taje tayi order din abinci a reception idan tana da buqata kowanne iri ne,to batason fita shi yasa bata karbo ba,ga wayar dakinsun daxu ta samu matsala bare ta kira daga daki a kawo mata,zuwa yanzu kuma yunwa takeji bata wasa ba,hakan yasa ya zame mata tilas ta fita ta karbo din kenan,saita sake tashi ta gyara yafenta ta kuma fito daga dakin.
Cikin tuqi mai cike da nutsuwa ya sako kai farfajiyar hotel din,hannunsa daya yana tuqin dashi,yayin da daya hannun yake amsa wayar cikin nuna girmamawa ga ubangidansa da gazo gani cikin hotel din,wanda ganawa ce ta sirri da zasuyi dashi gabanin taron qasa sa za’a gabatar na dukka ma’aikatan tsaro na qasa,kama daga sojojin sama dana qasa dana ruwa gaba daya,yanzun yana amsar direction ne na daki da inda zai ganshi,har ya qaraso wurin ajiyar motoci sannan ya ida wayar yana mai cewa
“Yes sir!” Sannan ya sauke wayar daga kunnenshi ya kasheta gaba daya,ya janyo aljihun motar ya zurata,sannan ya zauna na wasu mintuna yana karantar yanayin wajen a matsayinsa na qwararren jami’in tsaro,sai daya tabbatar komai na wajen yayi masa sannan ya bude murfin motar ya fito.
Duk wanda ya kalleshi saiya kuma,duk da cewa babu wata alama da zata nuna maka yanayin aikinsa,amma shigar da yayi da wasu shegun qananun kaya masu kyau da aji sun amsheshi,takawa yake zuwa reception cikin wata tafiya me cike da kuzari mazantaka da kuma karsashi,hannunsa daya riqe da key din motarsa,daya hannun kuma wata ‘yar mitsitsiyar waya ce da yake iya rumtseta a tafin hannunsa guda daya.
Yana magana da daya daga cikin receptionist din sanda ta qarasa saukowa,a nutse itama ta tsaya saitin daya ma’aikacin wajen tana gaya masa abinda ya sauko da ita.
Cak ya tsaya da maganar da yakeyi,a hankali ya juya kanshi zuwa sashen da yakejin muryar na fitowa,daidai sanda itama qamshin turaren da take tsammanin ta sanshi,a kuma cikin gidansu ya soma shiga hancinta,har kuma yaja hankalinta zuwa ga kallon gefanta.
Ido hudu sukayi,cikin matuqar tsoro da razani taja baya tana kallon cikin idanunsa,yayin da shima ya kafeta da idanun yana mata wani kallo daya sanya taji kamar an maida qafafunta sama ne kanta kuma a qasa,tashin hankali da gigita suka bayyana tun daga zuciyarta zuwa saman fuskarta.
*_kuyi manage don Allah,yau nayi busy_*
23/10/2021, 08:41 – ๐๐ป๐๐ป: 18
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโi yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koโina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โdai_
_______________________________
Da wani irin zafi ya soma takawa inda take tsayen,tamkar ma ya manta da cewa gap din dake tsakaninsu ba wani me yawa bane,itama sai tayi yunqurin ja da baya,wanda hakan yasa yakai mata cafka da zafinsa,ya samu nasarar riqe singalalin hannunta,abinda ya sake rudata kenan ta sake daburcewa,tsoro ya kuma cikata,yayin daya bude baki cikin wata tsawa
“Me ya kawoki nan!” Ya fada da dakakkiyar murya mai qarfin amo da sauti,irin ta sojan daya saba karba da bada umarni a fagen daga.
Yadda dai daikun mutane suka juyo suna kallonsu ya ankarar dashi,saiya sake mata hannun nata da sauri,fuskarsa na gauraye da wani irin bacin rai,ya zare muqullim motar daya maida aljihunsa ya cilla mata,ya kuwa sauka saman qafafunta,duk da taji zafin amma ba shine a gabanta ba,tashin hankalin dake a gaba take hararowa,tasan cewa abinda zai biyo baha din ba dan qarami bane,ta kuma fahimta me yake nufi,don haka ga duqa ta dauki key din ta fara takawa tana ficewa daga wajen kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki.
Sai data fice sannan yabi bayanta ba tare daya tsaya amsar number dakin da yake nema din ba,tana gaba yana bayanta amma ba zaka zaci tare suke ba har ta isa bakin motar,daidai lokacin matashin da tun dazun yake dawafi cikin hotel din yana nemanta tare da burin sake ganinta ya hangeta,don haka da sauri sauri ya sauko a nufosu idanunshi a kansu,yana ganin sanda haidar ya fisge muqullin ya buda motar ta shiga baya ta zauna.
Sai daya tabbatar ta shiga sannan ya sanyawa motar lock,duk da ya dage dukkan gilasan motar bakan baisa yayi tunanin kunna mata ac koya rage wani glass din ba don iska ta shigo mata.
Yana zare key din yaji an dafe hannunsa,ya daga kai a nutse don ganin waye
“Me haka kake?,zaka kama yarinya ka rufe cikin mota saboda me?” Wani banzan kallo haidar din ya kafeshi dashi,cikin ransa yana tambayar kansa da kansa shi din waye?,sosai ransa ke tafasa baiso ya huce masa laifin da bashi ya aikata ba,amma kuma yanajin wani sabon bacin ran na taso masa dangane da rainin hankalin da yakeson zuwar masa dashi,shi waye nata da zai qalubalanceshi kan hakan?,ya santa ne?,shi ya kawota?,ko tare suka zo?.
Zare key din yayi ba tare daya sake bi ta kansa koya dubeshi ba,ya juya ya soma takawa zaibar wajen saurayin ya mara masa baya yana ci gaba da cewa
“Malam ka budeta nace tun kafin ka gano kuskurenka…..bakasan waye ni ba ko?” Ya fada cikin zafi dason nuna nashi qarfin qwanjin.
Wani irin juyowa haidar din yayi a zafafe har hana take masa rabin qafa da ingarman takalminsa
“Idan kaci gaba da bina kana min wannan ษaษatun sai na saka kayi nadama kai da banzan matsayinka,kuma zaka gane kuskuren aikatamin hakan kafin ni na gane nawa kuskuren,stay awa frm me tun ban rugurguza kwanyarka” tabbas ya hangi wani strong abu cikin idanunsa,ya kuma hangi yadda yake furta maganar bilhaqqi,ya kuma tabbatar ba’a banza yake magana kan yarinyar with confidence haka ba,amma a amtsayin da mahaifinsa keda shi a nigeria yafi qarfin wani da baisan ma ko waye ba ya gaya masa magana irin haka ya qyale ba,don haka zai jira yaga yadda za’ayi ya fita daga hotel din ya kulle ‘yar mutane cikin mota
“Zan gani ta yadda zaka fita daga wannan ginin” ya furta sanda haidar ke komawa zuwa ciki,sai daya sake bi ta reception aka gaya masa dakin sannan ya wuce.
A nutse ya bude dakin da sallama a bakinsa,mutumin wanda a qalla ya kusa shekara hamsin da biyar ya amsa mishi,yana zaune saman kujera riqe da jarida yana dubawa,koda ba’a gaya maka ba shima kasan cewa soja ne,irin wanda ya jima cikin harkar bautawa qasa da bawa rayukan al’umma tsaro.
Fuskarsa dauke murmushi dake nuna kulawa da qauna yace
“Barka da zuwa aliyyu” qyam ya tsaya ya sara mishi kamar yadda sojoji keyi don nuna girmamawa ga manyansu,ya karba gaisuwar yana nuna mishi wajen zama.
Da kansa ya tashi ya nufi fridge na dakin ya daukowa zaki abun sha,yana mitar
“Bansan ina haisam ya shiga ba….almost one hour daga zaiyi waya” ya qarashe maganar yana miqa haidar drinks din,wanda ya miqe yasa hannnu ya amsa yana cewa
“Thank you sir”
“U r welcome” ya amsa mishi yana murmushi,suka zauna a tare.
Saida Aliyyun ya soma shan lemon sannan suka soma maganar daya sanya ya kirashin,general hamza adamu gusau kenan,mutum mai kirki qwarai da tausayin na qasa dashi,kusan shi ya zama kamar role model na aliyyu,saboda yadda yake da hazaqa da gaskiya riqon amana da aiki tuquru,yana son aliyyu sosai,hakanan yana mu’amalantarsa kamar dan cikinsa,saboda yadda Aliyyun keda jajircewa sadaukantaka gaskiya riqon amana da rashin tsoro,duk wani abu na ci gaba yakanyi qoqarin kawo aliyyun ya sakashi agaba,tun matsayinsa baikai wajen bama,hakan ya sanya cikin qaramin lokaci ya dinga samun qarin girma har zuwa matsayin da aliyyun yake kai a yanzun,yana samun kulawa da horaswa ta musamman daga wajen general hamza din,hakan yasa Aliyyun ya zama gagara badau,kuma qwararren soja daya iya aikinsa ya kuma san me yakeyi,dalili kenan da yasa su kansu sukeji dashi,domin kamar sun horeshi ne yazo ya kuma fisu qwarewa da sanin dabarun aiki kala daban daban,don haka ko ame akace akwai haidar din a ciki basa haufi.
Sunyi nisa da tattaunawar da sukeyi akayi kncoking,general ya bada umarni sannan aka turo aka shigo.
Daga kai aliyyu yayi daga duba wani map da daddy ya bashi kamar yadda yake kiransa yana amsa sallamar,idanunsa ya sauka kan saurayin,sun gane juna fes,sai kowanne ya daure fuskarsa,aliyyun yaci gaba da duba map din saurayin kuma ya qaraso ciki lokacin da daddy hamza ke cewa
“Daga ina haka?,kusan awanni biyu?” Shafo kansa yayi yana cewa
“Am sorry dad….wani abune ya tsaidani,but am back ai” kai ya jinjina yana nuna masa haidar
“Da daya yarona nan,Aliyyu mas’ood dabo” da sauri ya cira kai yana duban aliyyun,saboda koda fuskarshi boyayya ce to sunansa sananne ne a kunnuwa mutane ciki harda shi,bare ya jima yana jin sunan a bakin baban nasa,da kuma yadda yake ji da haidar din
“Ku gaisa mana haisam” yayi maganar yana maida kallonsa ga aliyyun,wanda ya aje takardar hannunsa saboda girmamawa ga daddyn ya miqe tsaye,yayin da haisam din shima ya tako inda aliyyun yake ya miqa masa hannu,shima miqa masa yayi sukayi musabaha,murya can qasa haisam din yace
“Nice to meet you!” Kai kawai haidar din ya kada masa yana zame hannunsa daga na haisam din ya koma ya zauna.
“Ka ganshi nan,yaqi aikin soja,yafison kasuwanci” inji daddy yana nuna haisam da baki,fuskar aliyyu ce kawai tadan motsa alamun murmushi yayi,sam hankalinsa shi bai wajen,Ya qagauta ma su gama maganar da zasuyin yabar wajen.
Sai daya qara kusan wata awa dayan sannan general ya sallameshi,ya miqe ya sara mishi ya qame sannan yamiqa masa hannu sukayi musabaha,ya dubi haisam
“Ka raka dan uwanka haisam zuwa mota,kwayi musayar lambobin waya ko?”general ya fada bayan sun gama sallama da aliyyu
“Ok daddy”ya fada yana miqewa,ya gyara zaman shirt din jikinsa yana bin bayan aliyyu.
Yadan masa rata amma ya dage ya cimmasa,ya tsaya daga gefan kadarsa,saidai duk da tsahonsa ashe aliyyun ya zartashi a tsaho,duk da yayi masa kallon nashi tsahon yafi nasa,ashe cika da murjewar jiki da haidar din ya fishi yasa yayi tunanin ya zarta tsahonsa
“Yaronmu kake ashe?,sai kabi a hankali ko?” Haisam ya fada yana duban haidar ta gefan ido.
Cak haidar din ya tsaya,ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana dan fidda wani murmushi na gefan baki,tsahon sakan biyar sannan ya waiwayo sosai yana duban haisam din,sai daya nuna hanyar da suka baro da hannu sannan yace
“Wancan da muka baro….girmansa nada yawa a dunun haidar….banda haka daka fahimci cewa ko jimina ta saka kanta a tabo…ba za’a kira kaza ba,amma duk da hakan zan gaya maka wani abu guda daya wataqila yayi maka amfani…..yaro tashi ka nemi suna….karka raba kanka da kowa,zaifi maka kyau da cikakken alfahari ka shaidawa duniya kai tsaye cewa kaine wane wane kamar yadda kullum nake alfahari da cewa nine Aliyyu mas’ud dabo….bawai ka cewa duniya kaine ษan general hamza tahir ba” saiya murza yatsunsa saman fuskar haisam sannan ya qara da cewa
“Ka kiyayi shiga gonar haidar ta irin wannan sigar…..i repeat my self….ka kiyayi shiga gonar haidar” daga haka ya juya yaci gaba da tafiya ya barshi nan a tsaye.
Maganganun haidar din sun masa ciwo sosai,yana son ya nuna masa nasu qarfin ikon amma abu daya ke masa shamaki,yarinyar daya sanya cikin mota ya kulle,wanda tunda ya ganta yaji nan duniya ya samu matar aure,baisan alaqar dake tsakaninsu da ita ba,yana tsoron kada yaje ya bata rawarshi da tsalle,don dai yasan tabbas ba shakka baya ga macen bariki,babu wanda zaiwa macen da bai isa da ita haka ba ta bishi ta kuma yi biyayya,amma koma meye zaibi a sannu ya bincika,saboda haka ya nufi tashi.motar da sassarfa ya bude ya shiga,yayi ready yana jiran yaga tashin motar aliyyun don ya mara masa baya.
Duk da rashin mashiga da mafitar iska cikin motar amma a cure take waje daya,duk da gumin daya gama jiqeta saboda tsabar tunanin data fada yasa sam batajin jiqewar,tunanin mafita da makomarta take,harta hango kanta a gabansu abba tsakiyarsu suna tuhumarta meya kaita hotel,da wanne baki zata kare kanta?,wanne irin wawanci da dolanci haka ta aikata?,me yasa?,me yasa?,haka take tuhumar kanta,hankalinta a wani matuqar tashe.
Sanda taji yana bude qofar sai da hantar cikinta ta kada,wani matsanancin tsoronsa da bata taba jin irinsa ba ya rufar mata,tana nan a yadda take har zuwa sanda ya bude motar ya shiga,ya maidata ya rufe sannan ya tada ita ba tare da yace mata kanzil ba,abinda bata taba tsammata ba,tana jiran taji hukunci ko wata magana daga bakinsa amma saidai tunda suka fara tafiya har suka isa gidan babu abinda yace da ita.
“Fita!” Ya fada cikin daka tsawa data sanyata kama murfin motar ta fito da hanzari,cikin gudu gudu sauri sauri tayi sassan hajja,saidai tana gab da shiga sukayi karo da anty uwani,taja da baya da sauri,haka itama anty uwanin,mace guda daya tilo da halayyarta kan zahran ta bayyana,tana matuqar adawa da yadda hajjan kewa zahran,kulawa qauna da soyayya da take nuna mata,ko dama can macace mai fada,masifaffiya ce ita din,ita ‘yace ga qanwar hajjan,tayi aure tana da yara hudu,uku maza sai mace guda daya autarta suwaiba,wanda itama ta dauki son duniya ta dorawa suwaiban,ji take sosai da ita,mijin nata ya rasu,koda kuma bayan rasuwar tasa bata sake wani auren ba.
“Me haka ke kuma kamar wadda aka biyo?” Ta fada cikin masifa tana qare mata kallo
“Ina kwana yakumbo” ta fada kamar yadda suka saba gaya mata,ko amsarta bata tsaya ji ba ta qara wuta zuwa ciki,sai anty uwanin ta bita da kallo ta kuma fara masifa
“Eyeee….ni zaki gaisar a haka?,lallai yarinyar nan iskancinki kullum qara gaba yake,koda yake kina da daurn gindi ne shibyasa,amma zamu hadu dake bari naje na dawo” ta fada tana buga cinya gami da yin gaba.
Sam bata kula da umminta dake falon hajjan ba sai data isa gaban hajja,saboda abune baqo a wajenta,ba kasafai ta saba ganinta din ba
“Lafiya?” Hajjan ta jefa mata tambayar tana duban qwayar idanunta,saboda yadda ta ganta kamar a birkice,yayin da ummin tata itama hankalinta gaba daya yake kan zahran a fakaice,don a zahiri ba zaka ce hankalin nata yana kanta ba.
Ko kafin tace komai haidar yayi sallama,a nutse yake takowa zuwa cikin falon,yana qoqarin rage zafi da radadi da yake ji daga cikin qirjinsa zuwa maqoshinsa,kallo daya ummin ta yiwa fuskarsa tasan ba lafiya ba,don idanunsa nakan hajjan da zahran,hakan ya sanya ta miqe don basu waje,duk da can qasan zuciyarta hakanan ya cika da zulumi da fargaba,sai taji batason tafiya,amma saita tanqwara zuciyarta ta duqa ta dauki carbinta ta fice ba tare da sun ankara bama.
Tana barin cikin falon taji ta kasa sake daga qafarta,abinda bata taba yiba kaf tsahon rayuwarta ta tsaya sauraren zancan wasu koda kuwa ya shafeta,amma a yau din sai taji tabbas tana son jin me ya faru?,wanda jikinta ya bata kan zahra ne,don ba haka ta saba zuwa gida weekend ba.
“Kai zaki…..lafiya?” Hajja ta jefa masa tambayar ganin yadda idanunsa suka sauya launi,ya kafeta da ido ya kuma kasa cewa komai
“Gata nan hajja,a hotel na daukota” idanu hajjan ta zaro sosai,hannunta dafe a qirjinta
“Kai haidar,banason shirmen banza da wofi,kasan kuwa me kake fada?,otel fa kace!” Kai kawai ya jinjina mata alamun tabbatarwa
“Kai!,haidar…..na gaya maka banason sakarci ko?,ka gayan gaskiya” wannan karon sai yaqi tanka mata,illa lumshe idanunsa da yayi kawai bai sake furta komai ba,sai hajjan ta waiwaya inda zahra ke tsaye,tana jin kamar zata saki fitsari
“Innawuro….abinda ya fadi gaskiya ne?”kamar ta dora mata dala da gauron dutse haka taji
“Eh hajja….amma….” Salatin hajjan shi ya katse sauran magana da bayanin da tayi niyyar yi mata,yayin da umminta dake tsaye daga can bakin qofa ta soma maimaita
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil,Allahumma ajirni fi musibaty,wa’akhlifni khairan min ha” daga haka ta ja qafafunta da take jin sun mata nauyi ta soma barin wajen cikin matsanancin tashin hankali,wani hazo hazo take gani a idanunta,a haka takai kanta bangarenta cikin mawuyacin hali.
“Zahra’u….hotel fa zahra’u,hotel aka ce fa?” Ta fada tana duban zahra wadda takejin inama ana iya maida hannun agogo baya ta maida ta goge dukkan wani kuskure data aikata nabin su hindatun da tayi
“Hajja….ki tsaya na miki bayani,wallahi ba abinda kuke zato bane,ba abinda kuke tunani bane….na rantse d….”
“Rufemin baki….zahra’u ai yau ni kika kunyata,ni kika baiwa kunya wallahi,oh ni fadimatu” hajjan ta fada cikin matsancin firgici tsoro da kuma tashin hankali
“Matsa daga kusa dani,tashi ki ban waje nace” karon farko da hajjan ta taba korarta daga inda take tunda suke a rayuwarsu,hakan yasa taji wani sabon tashun hankalin ya rufto mata,saita kasa jurewa ta kwasa da gudu tayi daki.
Shikam haidar na tsaye,sai a sannan ya bude idanun nasa,ya juya ya soma takawa zaya bar falon
“Haidar….zo nan” hajjan tayi kiran sunansa tana qoqarin binne tashin hankalinta,baice komai ba ya dawo ya tsaya daura da ita,ta masa kallo na tsaf,ta karanci yadda ranshi yake masifar bace
“Bana son naji maganar nan a bakin kowa haidar….banaso” idanunsa ya bude sosai yana kallon hajjan,kamar ba zaya tanka sai kuma ya bude bakinsa
“Me yasa zakice haka hajja?,sai yaushe xaki daina bata kariya kan dukkan laifin data aikata koda kuwa muninsa yakai wannan?,wannan kariyar ita ta zame mata rigar da take iya shiga ta buya a ciki,taci gaba da aikata abinda ranta yaso a sanda taso ba tare data samu wata tirjiye ko kuma shamaki da zai hanata kaiwa ga ci gaba da aikata mara kyau ba….don Allah hajja wannan karon….ki cire soyayya ko qauna,ki kuma kauda kai,ki bari ayi hukuncin dashi yafi dacewa”
“Haidara” hajjan ta sake kiransa karo na biyu
“Nasan zahra’u ciki da bai,na santa sanin dako mahaifiyarta bata sani ba,ni ina ji a jikina,ina jin cewa zuwanta ko ganinta a wajen baya nufin ta aikata ko tana aikata wani mummunan abu ne,kuma nasan bayanin da taketa qoqarin yimin kenan,saidai naqi bata dama da wuri tayi bayanin,har sai rashin bata damar ya zama wani hukunci mai zaman kansa a gareta,nayi imanin jinina bazai taba aikata wata mummunan alfasha har kamar haka ba,addu’a ba qarya bace” shuru yayi ransa yana baci,yana ganin hajjan tana bata kariya ne kawai saboda kada ta fuskanci hukunci,wanda hakan ya jima yana bata masa rai,shin ita hajja bata ganin sauyi qarara tattare da yarinyar ne?,har sai yaushe sannan zata ankara su yiwa tufkar hanci?,duk wasu doka da qa’idoji na gidan hajjan da karan kanta tasha karyasu indai akan yarinyar ne,wannan shine dalilin da yasa sam yarinyar bai hada idanuwa da ita,saboda yana da yaqinin duk sanda ta masa wani abu mai kama da sangarta ko rashin kunya zai iya ษaษษalata ya zubar.
Saiya juya kawai yaci gaba da takawar,hajjan nada wani irin girma da qima a idanunsa,amma yana jin sam hukuncin bai kwanta masa a rai ba,saidai kodon saboda girmanta da matsayinta bazai iya tsayawa yayi ja’inja da ita ba,a haka ya fice ba tare daya sake cewa komai ba.
************
Kwana uku da dawowartata amma sam hajja taqi tsaiwa ta saurareta ko taji bayaninta,wanda hakan yayi mugun daga mata hankali,don hajjan itace last chance dinta,tana da yaqinin koda kowa yaqi saurarenta,koda kowa yaqi yarda da ita zata samu dukkan wadan nan abubuwa daga wajen hajjan tata.
Cikin kwana ukun ta rame ta fada saboda fargaba,sai a rana ta ukun hajjan ta tsaya da qyar ta saurari bayaninta,ta yarda da ita ta kuma gamsu,saidai tasha fada da masifa daga wajen hajjan irin wadda bata taba yi mata irinsa ba,duka bai damu zahra ba,tunda ta samu abinda takeso,sai data gama fadanta tsaf ta miqe sannan tace cikin dari dari da tsoron amsar da zata bata
“To hajja makaranta,anata CA bana nan” wani kallo mai kama da harara tayi mata
“Saiki jira kiji abinda yayanku zaice,don shurun da yayi kan zancan bazan sake tilastashi kan makomar makarantarki ba”
“Sai kace shine uban kowa cikin gidan nan?,koshi ya haifi kowa?” Abinda zahra keson fada kenan,amma tasan fadin hakan shi zai sake dagula komai,bata ma isa tace din ba,haka taja bakinta tasa masa zip ta zuge ta zubawa sarautar Allah ido,cike da fargaba kada ta rasa abubuwa masu muhimmanci acan makaranta.
Har hajjan takai bakin qofa ta waiwayo
“Waye haisam?” Tambayar data daurema zahra kai
“Haisam kuma?” Zahran itama ta maimaita sunan ta sigar tambaya wa hajjan
“Eh shi” nazari kadan zahra ta fada,tafi kowa sanin cewa ta jima da yiwa kanta shamaki da duk wani da namiji bare tace ko yana da alaqa ne da rayuwarta,don haka ta girgiza kai
“Bansanshi ba hajja” kai ta jinjina
“Bari yayankun ya dawo” bin hajjan kawai tayi da kallo saboda ta kulle mata kai,waye haisam din?,kuma meya hadinsa da yaa haidar?,data kasa canka saita tattara tunanin duka ta watsar,koma waye kuma koma.meye matsalarsu ce,itakam ta jima sa cire sabga ko sha’anin maza daga tsarin rayuwarta,hakanan ta dade da ciresu daga cikin jerin matsalolinta da zasu dameta.
Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.
Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.
*_ABINDA KA SHUKA_*
A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun sosai.
Na tsugunnen abdulyassar ne,na tsayen kuma auwal ne,sam babu alamu na walwala ko farinciki kan fuskar abdulyassar din,face ma uban gumi da yake hadawa,fuskarshi amurtuke sosai.
Kai ta dauke zata gotasu taji an riqe hijabinta,saita juyo da sauri,auwal ne,ya soma magana cikin zallar damuwa kamar zaiyi kuka
“Haba zahra….yanzu kina ganin abdulyassar haka zaki wuceshi ba zaki kulashi ba?,don Allah ki dawo ki tambayeshi me yake damunsa?,wallahi kinga munyi munyi ni da hajiyarsa ya gaya mana abinda yake damunsa yaqi cewa komai tun daxu,babu yadda bamuyi dashi ba,munyi munyi ma ya tashi daga nan amma yaqi” hijabinta ta fincike daga hannun auwal din tayi gaba abinta,tana jin auwal din na kiranta,tana kuma hangen yadda abdulyasar din yaci gaba da zama awajen…….
(Exactly haka yarinyar tayi mafarkinsa kwana biyar da rasuwarshin,na manta ban kawoshi tun a sannan ba saboda ajizanci na mantuwa).
Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta soma baiwa labari.
“Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki yafe masa ba” baki zahran ta tabe
“Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa”.
Tana kammalawa tace bari taje wajen umminta,don tunda tazo bata je wajenta din ba,saidai yanayin yaddata amsheta,da yadda ta amsa gaisuwarta ta ya daga mata hankali ya bata mamaki,ta kuma shiga wasu wasin anya kuwa ba wani abu taji kan case din daya dawo da ita gida ba?,tunda haidar din mutuminta ne,to amma ita kanta tun ranar bata sake ganin haidar din ba,asalima kamar taji suna waya da hajja na masa fatan alkhairi kamar ma tafiya yayi wani waje,wannan abun saiya sake sanyata a rudanin data fita,ko sansa ta koma sassan hajjan saita kasa sukuni.
*_BA ZATA!_*
_baya da ฦura_
Masu karatu muje zuwa
_Da gaske iya qarshen matsalar kenan wa zahra???_ ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ๐ถ๐พโโ๏ธ
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:42 – ๐๐ป๐๐ป: 19
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
_____________________________
*_BA ZATA!_*
_Baya da qura_
Tana tsaka da sallah sau biyu inna gaje na leqowa dakin da zummae ganin ta idar din?,a zuwa na uku ne ta sameta tana zaman tahiya,saita tsaya tana dakon zahran har zuwa sanda ta kammala ta kuma yi sallama.
“Uwar masu gida anason ganinki a falo” inna gajen ta fada tana duban zahra,saita saki addu’ar da takeyi tadan ja tsaki
“Anty uwani ko?,ni sam banison zuwanta gidan nan wallahi,haka kawai baka taka mata ba baka zubar mata ba ta saka maka idanu” kai inna gaje ta kada
“Ba ita bace,hajja ce….da alhaji babba” haka kawai taji wani faduwar gaba da batasan meye dalilinta ba,haka nan sai jikinta yayi sanyi
“Tom,ina zuwa” ta fada tana qarasa addu’o’inta ta shafa sannan ta miqe.
Tun kafin ta qaraso gabanta ke dukan uku uku saboda fuskokin data hanga cikin falon,abba babba abba yusuf,abban tsakiya haidar da kuma hajja,sai umminta daga gefe
“La haula wala quwwata illa billah” shine abinda take maimaitawa,take dukka qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,hakan yasanya tafiyarta ta koma slow harta qaraso cikin falon.
Cikin girmamawa kamar kowanne lokaci ta gaidasu,suka amsa mata fuskar kowannne babu komai a samanta,ko kuma ace ba zaka karanto wani sauyin yanayi tattare da ita ba.
Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni,sa’annan abba babba ya soma magana
“Zahra’u…”
“Na’am abba” ta amsa cikin sanyi da raunin murya
“Mahaifiyarki tazomin da wani al’amari wanda yake da girma a wajenmu,bayan na saurari dukka bayananta da kuma hukunci da matakin da take buqatar a dauka…..nayi magana da aliyyu gashinan,na kuma ji duk abinda ya sani daga bakinsa,saina samu hajja na kuma tuntubeta game da lamarin….tayi mana bayanin komai itama,da kuma yadda kika gaya mata,saidai duk da haka mun nemi ta bamu damar yin magana dake,duk da cewa da farko taqi hakan,to a yanzu gamu gaki inna wuro,ina son ki dubi girman Allah ki gaya mana cewa shin da gaske a hotel haidar ya ganki?” Qas tayi da kanta,qwalla na taruwa cikin idanunta,kunyar kalmar takeji kamar qasa ta tsage ta shige,dana sani da nadama na sake cika zuciyarta,ta kasa cewa komai har sai da abba babba ya maimaita tambayarshi,cikin muryar kuka tace
“Eh haka ne abba…..amma wallahi wallahi abba,na rantse da wanda raina yake hannunsa abba ba wani mummunan abu bane ya kaini,munje ne yin karatu nida sauran qawaye na saboda test da muke dasu da yawa a satin….ko sanda ya haidar ya ganni amsar abinci ya fito dani….”
“Ya isa haka,yarinya aita gama magana….idan dukkaninku baku yarda da ita ba,bakuma yarda da abinda tace din ba ni na yarda da hakan,dukkanku na fiku sanin wacece zahra’u….bama ita kadai ba,addu’ar da nake na dare ba rana ina da tabbacin ubangiji bazai wofantar da ita ba,babu wani cikin zuri’ata da xai aikata alfasha da iznin ubangiji”hajja tayi maganar da alamun ranta ya fara baci,ajiyar zuciya abba babba ya sauke,duk da dama zuciyarsu bata taba basu zahra’un zata aikata wata alfasha ba,amma yanayin yadda take magana ya isa ya shaida maka gaskiyar abinda take fada din,hakanan kuma bayanin nata ya sake sanya musu nutsuwa a ransu,saidai dukka ba zasu nuna haka tashin farko ba,dole ne su tauna tsakuwa don aya taji tsoro,don haka abba yusuf ya soma fada sosai kan zuwan da tayi,wanda yace sam bata da wata hujja ta zuwa din,tunda ba tarbiyyar gidan bace,hakanan duk wanda ya ganta akwai kallon da zai mata da kuma yadda zai fassara ta,haka ya dinga fada sosai,saboda kusan duka ya fisu zafi,yayin da kanta ke qasa hawaye wasu nabin wasu.
Itama ummin nata nata kan yana qasa,bata zargin diyarta ko daya,saidai tana da tarin fargaba,tana tsoron zamani,tana tsoron qawaye,tana tsoron gurbacewar muhalli,tana sane da cewa a yanzun tarbiyya ta zama wani abu mai tsananin tsada wanda sai wajen wane da wane ake samunta,tsadar tata taki jallin da hirar wanda ya rabauta da samunta ake,farautar masu ita ake,tsada suke da kuma wuyar samu,tattalinta kuma abune mai hatsarin gaske,wanda idan ka tsira da ita ba tare da wani yayi nasarar fauce maka ita ba to abun ayi maka sambarka ne,tana fargabar yadda diyarta ta kafa tarihin soma karatun gaba da secondry cikin gidan ya zamana ta kafa wani tarihin na daban,tarihin da bata fata ko burin samuwarsa,a kullum kwanan duniya dama takan kwana da tashi cikin fargaba,koda yaushe burinta shine diyarta ya zamana tana gidan nata mijin kamar yadda aka tsara ko kuma aka gina gidan akan hakan,wannan zai fiye mata kwanciyar hankali fiye da ace tana can tana karatu,tunda jarrabawa ta soma samun diyartata bata taba samun nutsuwa ko sukuni na sakan ba,idanunta basa barci,zuciyarta bata hutawa,bakinta baya gajiya da yi mata addu’a ako da yaushe,a kullum takan wayi gari cike da buri da kuma fatan Allah ya fiddo mata da miji na gari,koda kuwa zai zama silar datsewar karatunta,a yanzu kam a wannan bigiren….tana jin ya kamata ta motsa,tana jin ya kamata ta magantu,tana jin ya kamata tayi wani abu da zai sama mata nutsuwa ko yaya ne.
Sai da suka gama fadan sannan sukayi mata jan kunne da gargadi mai qarfi,saida suka gama gaba daya sa’annan umminta da tunda aka fara batace komai ba tayi magana
“Hajja…..yaya(haka suke kiran abba babba tun tale tale,dukka matan qannen nasa
“Na’am halima muna saurarenki”
“Yaya dukkan fada da qoqarin da kukeyi akan zahra’u duk da cewa diyarku ce…..amma ya zama dole ga duk wanda ya gani ya yaba muku…idanma har akwai abinda yafi yabo din kun cancanci samunsa,a yau sau daya tak ina neman wata alfarma….alfarma guda daya da nake fata da kuma burin xan sameta daga gareku” shuru ya dan ratsa kafin abba babban ya bude baki yace
Fadeta halima….in sha Allah ba zata gagara ba”yayi furucin tare da yaqinin haka yake cikin zuciyar mahaifiyarsa hajja,domin halima takai mace,duk inda mutum mai tsananin kawaici kan diyoyin cikinsa da sanin ya kamata yakai takai,suna da tabbacin tunda har yau ta iya buda baki tayi magana to ba shakka lamarin ba qarami bane a zuciyarta.
“Inason a dakatar da zuwan inna wuro makaranta….ma’ana a dakatar da karatunta” sosai zancan ya daki zahra,don bata taba kawowa umminta da bakinta zata nema hakan ba,fitar furucin daga bakin ummin nata ba qaramin razani da gigita ya sanyata ba,domin tana qaunar karatunta a yanzu,qaunar da a baya batayi masa ba,ta damu dashi damuwar da abaya batayi masa ba
“Ba wanda zai dakatar da ita daga karatunta bayan bamu tabbatar da laifinta a kanta ba”
“Don Allah hajja na roqeki to kimin alfarma ta biyu….taci gaba da karatunta,amma da sharadin zata koma bakin karatun nata ne da igiyar aurenta a kanta…..” Dif dakin yayi tamkae anyi ruwa an dauke,ga zahra kuwa rudanin data shiga yanzu ya zarta na baya
“Don Allah hajja….kiyimin wannan alfarmar” muryar ummin tata ta sake ratsa shurun.
Dukka wata laka ta jikin hajjan tamkar an zareta,wani irin nauyi da tausayin halimatun ya shigeta sanda take zaune gabanta tana roqon ayi mata alfarma kan diyar cikinta,ayi mata alfarma kan diyar data haifa da kanta,diyat da duk duniya tafi kowa iko da isa da ita,tabbas! Halimatu mutum ce,cikakkiyar mace mai cikakken kunya da kuma tarin kawaici,kawaicin da bata jin baya ga halimatu sai khadijatu mahaifiyar haidar ce kawai za’a samu da irinta tattare dasu,bata taba ba!,koda wasa bata taba nema ko maida hukuncin hajja baya ba a kan zahran,kulkum abinda hajja ta aiwatar ko ta zartar dai dai ne akan zahran,halimatun bata da wani zabi ko nuni dangane da duk wani lamari da ya shafi rayuwarta,lallai a yau din ya kamata….ya cancanta ayi mata itama abinda takeso!,saidai kuma hakan na nufin yiwuwar rugurgujewar ko samun tasgaro ga karatun zahra’un tata,karatun da take da tabbacin a yanzun shine komai na zahra’un,kai…..bata tunanin wannan ra’ayi ko hukuncin halimatu ne,tafi zato da zargin aliyyu shine ya shirya komai ta bakin ummin,ya kuma ja bakinsa yayi shuru,bayan taja kunnensa,ta kuma jaddada da masa buqatarta,lallai itama zata nuna nata qarfin qwanjin,zata nuna nata ikon,kai lokacima yayi da zata cika mafarkin data dauki shekara da shekaru tanayi,lokaci yayi da zata cika burinta,lokaci yayi da baraka guda daya data rage zata dinketa tsaf!,koda hakan na nufin rikici da tashin hankali daga kowanne gefen.
Cikin wani irin amo da salo daya tabbatarwa da duk wanda ke dakin da gaske hajja ke magana,da gaske hukunci take zartawa mai zubin KAIFI DAYA!,MAGANA DAYA!,cikin salo na umarni kai tsaye tace
“Kin wuce ki nema alfarma akan diyarki halimatu,baki ma taba nema ba sai yau,kuma zaki samu da izinin Allah,zahra ba zata koma makaranta ba saida igiyar aurenta akanta….zahra zata koma makaranta cikin satin nan a matsayin matar aure….a matsayin matar Aliyyu,rana ita yau nakeson inga zahra’u a matsayin matar aliyyu!” Takai qarshen zancan tana sauke idanunta kan abba babba,wanda hakan ke nufin cewa tana da buqatar ya zartar da umarnin data bayar kenan.
Da wani irin sauri aliyyu ya dago da kanshi,wanda tunda aka fara dambarwar wayarsa ke hannunsa yana sarrafata cikin qwarewa,kanzil baice ba sai a yanzu da yaji fitar furuci mai nauyi daga bakin hajjan,furucin da ko cikin duniyar mafarki bai taba hakaito kwatankwacinsa ba,sai yaji sam hukuncin ma bai samu zama a kwanyarsa ba,lafazin nata kamar wani wasa ne ko raha a kunnuwansa,haka yaci gaba da gayawa zuciyarsa,saboda haka saiya sake rusunar da kansa yana ci gaba da danne dannen wayarsa abinsa,saidai kuma wannan karon sam zuciyarsa taqi yarda ta bashi hadin kai yaci gaba da abinda yakeyi din,gaba daya ta karkata ga sauraron abinda ke gudana a falon.
Ta fannin zahra kuwa numfashinta ne yayi qaura daga gangar jikinta na wucin gadi,tana son kiran sunan hajja ta kasa,tana son roqon hajja alfarma amma ta kasa,tana son tace a’ah amma dukka ta gaza aikata hakan,har zuwa sanda hajja tace
“Kai ka bata zaki….kuma kaine zaka gyara….dolenka” furucinta na biyu daya sanyashi shiga taitayinsa,ya kuma sake alamta masa hajjan fa da gaske take,abinda take fada da gaske takeyi,saiya aje wayarsa gefansa,karon farko shima da yace
“Me na bata hajja?,me nayi ni din?”
“Duukkan abinda ke faruwa anan kaika bazashi har ya kawomu ga zama a nan….”
“Bashi bane hajja…..kada ki masa hukunci ba bisa laifinsa ba,haidar bai gaya min komai ba,kuma ya bani mamaki daya boyemin…tunda ba don kunnuwana sun jiye min ba haka zai rufeni?,bayan shine mutum daya tilo cikin matasan gidan nan da yake da dabi’ar tsawatarwa da tsaiwa tsayin daka kan halayyar qannensa,don me zai watsar akan zahra’u?…..na roqeki hajja ki soke qudurinki…..kiyi haquri,amma zan iya cewa ba’a kyautata masa ba matuqar akace shine wanda zai aureta”
“Halimatu…..indai na isa a gidan nan,indai nina tsugunna na haifeku(ta fada tana nuna su abba yusuf)to rana ita yau inna wuro zata zama mata ga zaki….ku riqe wannan”
“Hajjaaaaa!” Zahra da wannan karon ta samu nasarar fisgo kalaman bakinta ta furta cikin wani irin rauni,hawaye na sauka saman kuncinta
“Don Allah hajja…..don Allah kiyimin kowanne irin hukunci amma banda wannan….wannan din ba gata bane hajja……shine hukunci mafi tsanani da tsauri da zaki yankema rayuwata a karo na farko!” Ta qarasa maganar kuka na qace mata,tsam ummin ta miqe a nutse ta fita daga falon ba tare data tsaya sake jin komai ko sake cewa komai ba,mutum na biyu da ya sake miqewa zai rufawa ummin baya haidar ne,don shi maganar hajjan jinta yake kaman tatsuniyar gizo da qoqi,don baiga dalili ko abinda zai saka wannan kwamacalar yiwuwa ba,kawai saboda ana son hukunta yarinya sai an jingina da tashi rayuwar?
“Kai aliyyu….dakata” abba babba mahaifinsa ya dakatar dashi,saiya koma hannun kujerar daya tashi cikin girmamawa ya zauna
“Gani abba” ya fada wata irin murya mai kauri
“Dukkaninmu nan daka ganmu(ya fada yana nuna junansu da yatsa)albarkarta muke nema….dukkanmu aljannarmu tana qarqashin qafarta,sa’annan babu wani abu da zata nema nan gidan duniya mu kasa yi mata shi,koda fansar ranmu ne zamu bada,ina fatan ka fahimci abinda nakeson fada?” A wannan karon zuciyarsa sake gaya masa take abun babba ne,saidai har yanzu zuciyar ‘yan mazan a dake take,har yanzu baiji wani darrr ba,don haka ya gyada masa kai kawai ya dora da fadin
“Eh abba….”
“Amma yaaaya…..hajja ina ganin kamar wannan hukuncin baiyi tsauri ba?,ya kamata a zauna a sake duba abinda zai yiwu ko?” Cewar abban tsakiya wanda kukan zahran bai masa dadi a ransa kamar yadda baiwa sauran
“Kai muftahu…..” Hajja ta fada da salon son dakatar dashi,dai dai nan haidar ya miqe tsam abinsa ya fice daga falon.
Da wani irin sauri itama zahran ta miqe tayi dakinta saboda ji da tayi ta kasa zaman falon,kamar idan ta tashi tabar musu falon ta tserewa wannan mummunan hukunci na hajjan,amma data shiga dakin saita kasa zaune ta kasa tsaye,kamar wata zararriya haka ta dinga jin kwanyarta na yamutsawa,ta dinga leqensu abban tana so suyi subar falon,tana da tabbacin barazana ce kawai hajjan keyi amma zata janye,tasan cewa da taje ta kwantar da kai ta lallabata shikenan za’a wuce wajen,duk da tafi kowa sanin halin hajjan tunda tafi sauran zama da ita,sau tari tana da kafiya da zafi kan wasu abubuwan,wanda idan ta juye maka zaka tsammaci ba ita bace.
Kansa yake gayawa cewa babu wani abu da zai faru sansa yake dosar nahiyar da dakunansu suke,dukkan abinda hajjan ta fada barazana ce kawai saboda tana tunanin ya qetare abinda ta gaya masa,tana so ne ta kaษashi kawai saboda haka,saidai can can qasan ranshi ya kasa samun nutsuwar da yakeson samawa kansa,ya kasa gamsuwa da dukka kalaman kwantar da hankali da zuciyarsa ke jero masa,ya kasa daukar kowanne daga ciki,indai har kuwa hajja na nufin abinda ta fada da gaskene har cikin zuciyarta….to a karon farko wani mummunan al’amari zai iya faruwa wanda shi kansa bai sanshi ba,bai kuma san qarshensa ba.
Har ya saka key zai bude gefen nashi wayarsa ta dauki tsuwwa,tun kafin ya ciro ya saki tsaki,don sai yaji qarar wayar kamar wani qarin damuwa ce cikin kwanyarsa,ya zaro yana duba mai kiran,general hamza ne,babu uzuri matuqar kira daga wajen irinsu ne,don haka ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa kamar yadda ya saba
“Abu biyu yasa nayi kiranka aliyyu…..na farko akwai wani gagarumin al’amari daya tunkaroka,wanda kyanta idan ka samu dama ka sameni saboda kaji kai tsaye daga bakina…..na biyu kuma batu ne na auratayya” saiya dan saki murmushi
“Ina farincikin shaida maka cewa ina saka ran nan gaba kadan xamu hada zuri’a,zamu hada jini da familynka….,duka dai idan ka samu dama kazo na ganka” kusan bai fahimci dukka maganganunsa ba,ya sani kuma a yanzun yadda yake jinsa ba fahimtar zaiyi ba,don haka kawai yace
“Sir…in sha Allah zan shigo gobe da safe” godiya general ya yiwa aliyyun kamar ba shine samansa ba,sannan ya katse wayar……
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโi yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koโina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โdai_
23/10/2021, 08:42 – ๐๐ป๐๐ป: 20
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโi yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koโina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โdai_
___________________________
Ko gama fita su abba babba basuyi daga falon ba zahra ta fito da sassarfarta,kai tsaye ta fada jikin hajjan gami da riqe hannayenta
“Hajja….don Allah kibar wannan zancan,ki haqura dashi…..” Sosai ta dinke fuskarta,wanda kusan hakan baqo ne ga zahra
“Ke zahra’u,ki bude kunnenki ki jini da kyau,babu fashi a maganata,saboda haka bana son ki sake cewa komai” kuka ta barke dashi tana sakin hannayen hajjan
“Toni hajja na haqura….na haqura da karatun wallahi indai sai an aiwatar da wannan sharadin”
“Ko kin fasa karatu fa aure babu fashi….idanma zaki sanyawa ranki dangana ki sawa ranki ahto,don dukkaninku na gaji da ganinku daga ke har shi kuna yawo haka tsigai tsigai dukka shekarunku sunkai,sannan wannan shegen takun saqar naku ma gwara a kawo qarshensa” sosai ta saki sautin kukanta tana cewa
“Wallahi hajja yanzu bama fada,don Allah yaushe ma rabon da kiga na kulasa,ki janye hajja don Allah” miqewarta ma hajjan tayi tana cewa
“Saikuma kiyi tayi idan jajen farar kaza halak ne” kafin ma hajja tayi nata dakin zahran ta rigata miqewa da gudu ta nufi dakinta tana fadin
“Wallahi bakya sona hajja…..bansan haka ba sai yau” baki ta tabe kawai ta bita da kallo harta shige dakin ta kulla qofa.
Qaramin murmushi hajjan ta saki tana girgiza kai gami da sakin ajiyar zuciya
“Duka kwayi ku gama ‘yan nema,duk tsiya mutum ai bayaqi jininsa haka ba” tayi maganar a fili amma qasa qasa,cikin ranta tana jin sakayau,wani irin dadi da karsashi takeji,ji take kamar ma ta janyo rana ita yau din ayi komai a wuce wajen,don daurin auren yanzu ita shine a gabanta,koma meye ya biyo baya.
Tsaye yake a tsakiyar yalwataccen bedroom din nasa daure da towel yana sharce ruwan wankan dake diga daga kansa zuwa sassan jikinsa dake cike da gargasa,wata iriyar kasala yakeji sosai,banda haka tun sassafe yaso zuwa wajen general yaji neman da yake masa,amma gashi har kusan sha daya da rabi na safe yau din bai fita ko ina ba,duk da tarin abubuwan yi da ya shirya zaiyi a yau din.
Sai daya shafe kusan minti talatin yana shiryawa,cikin qanqanin lokaci ya fito fes cikin wasu qananun kaya da sukayi masifar amsarsa,saidai fuskar nan a dinke take tsaf,yakanji yanayi na bacin rai ya mamayeshi a duk sanda ya tuna zantukan hajja na jiya,duk da cewa yana sake gayawa kansa wasa ne,kuma bazai taba yarda ko lamuntar hajjan taci gaba da irin wannan wasan gaban yarinyar ba har yaja masa raini a nan gaba,don bazai dauki raini ba,wayarsa da key din mota kawai ya dauka ya fice a dakin.
Sassansu ya fara shiga ya gaida mahaifiyarsa da momy abokiyar zamanta,a can ya samu anty uwani ta dubeshi bayan ya gaidata
“Kana nan dai zaune kana sake cinye shekarunka a gida,tun mutuwar yarinyar can zahra’u,banda abinka ai dole haka zaka haqura,ka sake zabar wata cikin dangin mahaifinka kuma tunda an gwada na mahaifiya,ko ‘yar uwarka ma suwaiba ai baqi zatayi ba aliyyu sai a jarraba ko?” Kallo daya ya mata ya kauda kai,tamkar ma badashi take ba,shi dama ko can ba wani shiri suke sosai ba,don bai sakar mata fuska,ita kuma shakkarsa take,bare kuma ‘yarta da ko kallo bata isheshi ba,yana shirin fita mama tace masa
“Idan ka dawo kazo ina son magana da kai”
“To” ya amsa mata ba tare daya kula da a dawo lafiyar da anty uwanin ke masa ba.
Yana taka sassan hajjan amma ji yake kamar ya koma kada ya shiga,saidai bazai iya ba matuqar yana garin,da haka ya iske babban falon tsohuwar,babu kowa ciki amma yana jiyo motsi daga kitchen,saiga jidda jikarta na fitowa hannunta riqe da wasu farantai.
Cikin girmamawa ta rusuna ta gaidashi,ya amsa zai tambayeta tsohuwar kenan sai gata ta fito daga dakin zahra,wadda ta kulle kanta tun jiya,ko abincin dare bata ci ba,ga na safiya ma da taqi budewa bare taci,sai da qyar hajjan ta samu ta bude qofar ta ritsata da tea tana qwalla tana roqarta ta janye zancan tayi kurba hudu.
Daga tsaye yake gaidata saidai ya dan ranqwafa,fuskarsa babu walwala ko fara’a,ta amsa masa tana zama gami da cewa
“Tun dazu nasa aka kaimaka abun karin,anje anyi bugu anyi bugu baka bude ba”
“Eh….bacci nake lokacin” baki tadan tabe kadan sannan ta dan daga murya tana qwallawa husna dake kitchen kira kan ta hado abun karyawa ta kawo masa
“Barshi kawai….sauri nake zan fita” ya fada yana dakatar da bayanin da takewa husnar
“Madalla….idan ka dawo kazo zanyi magana dakai”
***********Kai tsaye a yau din aka masa iso cikin katafaren falon general hamza,wanda ya tsaru qwarai,ga hotunan iyalinsa nan manne a kowanne bango na falon nashi,wanda ya wadatu da iskar ac mai ratsa jiki.
Zaune suke su biyu tak cikin falon daga haidar din sai general,gaban aliyyun cike yake da kayan ciye ciye iri daban daban,saidai yadda yakejin zuciyarsa babu sukuni baijin sha’awar cin komai
“Kaci wani abu mana haidar” general ya fada yana murmushi
“Alhmdlh daddy….a qoshe nake”
“To shikenan….ba laifi” ya fada yana zaro takarda daga cikin takardun dake gefansa,wadda akayi sealing nata cikin envalope ya miqa masa
“Wannan…..kada ka bude sai bayan kaje gida ka nutsu tukunna….yanzu magana ta biyu zamuyi dakai” kai ya gyada bayan ya amsa takardar ya aje saman cinyarsa
“Nasan kasan haisam zuwa yanzu,don na gabatar maka dashi” kai aliyyun ya sake gyadawa yatsunsa soke cikin na juna yana duban general gami da saurarensa
“To haisam dai ya sameni da zancan yaga wata yarinya yana sonta….ya kuma tabbatar min da ‘yar gidanku ce,duk da bansan ya akayi suka hadu kuma yasan yar gidan naku bace,amma dai yacemin sunanta zahra” ya qarasa fada yana duban haidar.
Baiyi wani mamaki sosai ba najin zancan musamman idan ya tuna da abinda ya faru ranar daya taso zahran zuwa gida daga hotel,saiya gyadawa general kai
“Eh….qanwata ce”murmushin farinciki general ya saki
“Ma sha Allah….muna da uwa a bakin murhu…..yanzu dai ni hamza ina nemawa yarona auren zahra’u….duk da ban gaya maka ba….haisam ba dan cikina bane,amma baida maraba da dana dana haifa,saboda dan qanwata ne data rasu awa daya tak bayan ta haifeshi,so a wajen iyalina ya taso,baisan wani uba ba bayan ni,bai kuma san wata uwa ba bayan mai dakina” kai haidar ya kada cike da gamsuwa,ta wani gefen kuma sai yaji kamar an rage masa nauyin dake cikin zuciyarsa,saboda hango mafita da yayi ta hanya mai sauqi kan zancan aurensa da zahra,indai har nema mata mijin ci gaba da zuwa makaranta ne zaisa su laqa masa auren da bai shirya ba,auren da baiji ba bai gani ba,to ga miji nan ta samu,saisu sake masa mara yayi fitsari,duk da yaron bai wani kwanta masa ba tun a wancan ranar da sukaso samun matsala da juna,don haka da karsashinsa yace
“Indai ni zan aurar da ita….to na bashi,saidai bazanyi saurin fadin hakan kai tsaye ba,zan isar da saqonka zuwa garesu,kuma ina da fatan cewa za’a dace”
“Ma sha Allah,ma sha Allah” general keta fada cikin nuna farinciki,sun taba hira da haidar din kan abinda ya shafi aikinsu,sannan haidar din ya masa sallama ya fito.
A farfajiyar gidan sukayi kacibus da haisam,a wannan karon fuskar haisam a washe bakinsa a bude ya nufi aliyyu da dan hanzarinsa yana miqa masa hannu gami da cewa
“Barka da warhaka” wani kallo aliyyun ya masa yayi gaba abunsa ba tare daya bashi hannun sun gaisa ba,ya qarasa motarsa ya bude ya shiga ya tasheta ya fice daga gidan.
Iska haisam ya kaiwa naushi,me ya yiwa guy din nan tun karon farko ne haka suke samun sabani?,amma koma meye zai lallaba su bashi auren zahra,kome zaiyi masa zai iya shanyewa indai zasu bashi zahran,saboda ta gama yi masa a rayuwa,bai taba ganin macen data masa dari bisa dari ba irin zahra’un.
A hankali yake tuqin kamar wanda baida lafiyayyen injin mota,da hannu daya yake murza sitiyarin motar,daya hannun kuma ya aza yatsunsa saman labbansa yana dan shafasu a hankali,yayi nisa cikin tunani da kuma lissafin yadda abubuwa zasu kasance da yadda zai tunkari su abba da maganar haisam,shi a karan kansa cikin idanunsu yaga gasken gasken son qulla lamarin daga garesu,amma kuma ta wani fannin yana da hope na cewa zasu karbi zancan haisam din.
Shawara ta qarshe da zuciyarsa ta bashi itace,ya tunkari yarinyar kai tsaye yayi mata tayin amsar haisam din koda baiyi mata ba matuqar dukkansu suna son zame kansu daga al’amarin,idan yaso daga baya sayi dukkan mai yiwuwa su warware zancan haisam din,da wannan shawarar ya qara gudun motarsa,tafiya kadan ya sanya signal yahau club road bayan ya baro titin gidan general.
Bai dawo gida ba sai bayan sallar isha’i,sai daya fara sauke abu sufyan da suka wuni tare a gida sannan yayo gida.
Kai tsaye sassansa ya nufa,yana shiga ya zaro wayarsa ya kira musty yace ya sameshi daki,babu jimawa ya iso,order din abinda zaici ya bashi yayo masa a wani gidan cin abinci dake kusa da tasu unguwar ya hada masa da key din motarsa,yana murna ya fice kuwa da sauri,don yana masifar son aiken ya haidar din,ko banza akwai qaruwa,baya amsar canji da sauransu.
Kayan jikinsa ya fara cirewa ya zubasu a ma’ajiyar kayan datti,duk yadda wasu mazan keda aqidar watsa daki sam haidar din ba haka yake ba,da wahala ki samu dakinsa a wargaje da kaya,komai nashi tsaf tsf kamar wata mace,yana fitowa musty na dawowa,yace ya jirashi zai fito yanzu,saiya zira jallabiya golden colour mai gajeran hannu,bayan ya feshe jikinsa da turarukansa masu sanyin qamshin sai ya dawo falon.
Sai daya zauna gaban ledan da mustaphan ya aje sannan yace
“Idan ka fita….ka turomin yarinyar nan” dubanshi mustapha yayi
“Wace yaya?” Tsaki ya danja yana bude ledar
“Fatima”
“Ohk to” ya fada yana miqewa da sauri gamida aje masa muqullin ya fice.
Wani tunani da yayi shi ya sanyashi daukan wayarsa dake ajiye ya kira mustaphan
“Ka kiratanne?”
“No yaya….yanzu dai zan shiga”
“Manta kawai,bar kiran”
“Ok to” saiya datse kiran ya ajiye wayar ya jawo tarkacen takeaway din ya soma ci,saidai sam abincin bai masa test a baki,saboda ba sabonshi bane cin abincin waje matuqar yana gida,don haka cin abincin bai wani nisa ba ya aje ya wanke hannunsa ya sake daukar wayarsa ya fice zuwa sassan mahaifiyarsa.
Yana tafe zuwa sassan hajja bayan ya baro sashen mahaifiyarsa yana tuna maganganun da suka kusa kwashe awa guda sunayi da ita,wai da gasken kenan hajja take?,har maganar takai kunnen mamanshi?,har tana jaddada masa matsayi da girman hajjan a idanunsu?,da cewa hukuncinta dai dai yake da hukuncinta kona mahaifinsa?,da ire iren wannan tunanin ya isa sassan hajjan.
Sai daya jirata ta fito daga daki yana zaune yana kallon labarai a gidan tv,fuskarta babu yabo ba fallasa ta zauna daura dashi,shima saiya bar dukkan abinda yakeyi din ya tattara hankalinsa kanta
“Kince kina nema na,gani….amma kafin naji abinda zakice,bari na sauke nauyin saqo da alqawarin dana dauka” ya fada yana gyara zamansa sosai cikin kujerar yana duban hajja
“Nasan kinsan boss general hamza ko?” Kai ta gyada a nutse,idanunta kyam akan aliyyun,saiya lumshe ido ganin ta fahimta da wuri
“Yaronsa ko ince dansa….yaga fatima yana so….dazun naje wajen mahaifin nasa,yace na roqa masa alfarma wajenku kan a bawa dan nashi dama” daga haka ya tsagaita yana kallon hajjan.
Ga mamakinsa saita saki wani dan qaramin murmushi
“Wannan wasan kwaikwayon kuma ka shiryo?….kana tsammanin saboda ka sanya sunan general a ciki na kasa aiwatar da abinda nayi niyya na bawa dansa?” Kai ya kada
“Bazan miki qarya ba hajja….kinfi kowa sanin waye ni” kai ta gyada
“To naji….shikenan,aje a haka….baka shaida masa cewa mun mata miji ba,kuma kaine mijin?,gida bata qoshi ba ai bazamu baiwa dawa ba ko?,ba zamu zaka kyandir ba….mu haska wasu mu qona kanmu” sosai yake kallonta yana jin rudani nason lullubeshi,ya tabbata dai da gasken tsohuwar nan take,tanason hautsina masa dukkan lissafinsa da wani zaman lafiyarsa
“Amma hajja….for god sake yarinya tayi laifi ita kadai za’a hada harda ni cikin hukuncin?….me nawa ni a ciki?,hukunci ma irin wannan na aure?….kiyi haquri hajja,amma gaskiya bazan iya karbar wannan tsarin ba,babban kuskure ne ka yankewa kanka hukuncin amsar wani abu da bai dace da tsarin rayuwarka ba saboda wani matsantawa daga familynka,saboda zaka rayu ne tare da sakamakon wannan hukuncin daka yanke….bawai tare da familyn naka ba….,idan ma kin yanke hukuncin nan ne saboda ki faranta ran wasu….babu wani dalili da zai sanya ace saikin gamsar da kowa kin farantawa kowa rai cikin lokaci qanqani….azo kuma a rasa manufar abinda aka yanke hukuncin a kansa rasa manufa ta har abada….”.
” ka gama soki burutsun naka?”ta tambayi haidar kai tsaye tana duban tsakiyar idanunsa,shuru yayi yana dubanta shima ba tare da yace komai ba,yana karantar yadda al’amarin keda qarfi da girma a zuciyarta
“Ni fatima dabo…..na isa na sanya ubanka ma ya auri duk wadda naga dama ba tare d wani dalili ba bare kai,saboda haka ka fita daga idanuna….ka kiyaye ni haidar,zaka hadu da fushina irin wanda baka taba ganin irinsa ba,aure ne babu fashi,ruwanku kaida ita ku shirya,ruwanku kada ku shirya,dani da ku shege ka fasa!” Ta fada da qarfin murya.
Kusan tare suka runtse idanu shi da zahra dake tsaye bayan labulen daya raba dakunansu da falon
“Ya salam!” Ya furta yana jin wani ciwo a qirjinsa,ko kusa ko alama babu wani abu da ya taba hadashi da hajja makamancin hakan,sai kawai ya miqe ya nufo qofar fita,yayin da xahra take daki itama ta zube a qasa tana sakin sabon kuka.
Da kallo anty uwani tabi haidar sanda ya fice daga sashen hajjan,saita saka kai ita kuma,tana ji a jikinta akwai wani abu da yake faruwa,kuma koma meye saita jishi.
Sanda ta shiga hajjan na waya da wani dan uwanta daga can garinsu,saita samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana jiran hajjan ta gama
“Eh saura kwana bakwai daurin auren haidar da zahra ne……wallahi abunne ya taso bagatatan,don Allah ashaida musu…..daurin aure ne kawai….biki sai daga baya idan sun gama shirinsu za’ayi,don haka karsu damu,da lokacin bikin yayi za’a sanar saiku shaida musu”.
Idanu dukka anty uwani ta fidda tana zare ido,da tasan wannan mummunan labarin zataji da babu abinda zai shigo ma da ita sassan,ai bata bari hajja dake qoqarin kashe wayar ta kashe ba ta jefa mata tambaya
“Hajja….wai da gaske ne abinda naji yanzu kina gayawa su kawu inusa?”ajiyar zuciya ta saki
“Wallahi uwani….na gaji da ganinsu suna yawo a gabanmu,shi babu sa’ansa….ita babu sa’anta,naga gwara kawai ayi me gaba daya haihuwa da hanji”wani bacin rai ne ya tasowa uwanin,da gaske dai halima ita da diyoyinta masu gata da babbar fada ce a wajen hajja da babu wanda ke kaiwa matsayinsu?,daure ranta tayi sannan ta sake cewa
“Hakan yayi kyau….amma hajja suna son junansu kuwa?,kinsan zamanin nan…..ba’a tilastawa yara auren da babu son ransu,suna soma ya aka kaya bare basaso” isashen murmushin hajja ta saki tana miqe qafarta dake damunta da ciwo yau kusan kwanaki uku kenan,bata gayawa kowa bama bare su dameta da batun zuwa asibiti a hadata da tarin qwayoyi
“Uwani kenan…..har yanzun suna dana gaba dasu aiko?,kuma idan kasan irin tarbiyyar daka bawa naka baka shakkar komai” kai kawai take gyadawa tana kallon center carfet din da take kai.
Suwaiba keson haidar tamkar tayi me,hakan ya sanya anty uwani shigewa mama sosai tsahon lokaci donta sama musu fada ta yadda komai zaizo da sauqi,tunda shi din me son iyaye ne da qoqarin kyautata musu,sai gashi hajja ta yanke musu hanzari,inda tasan hakan zata faru takan hajjan zata fara neman fadar,shaf ta mance da cewa iyalin na matuqar qaunar tsohuwar,kuma suna a shirye kowanne lokaci domin bin umarninta kamar yadda take iyakar qoqarinta itama ko yaushe don ganin farincikin iyalin nata,tabbas ba zata bari,zata qoqarta,mai rai ai baya rasa motsi,don haka tace
“To Allah yasa ayi damu”
“Amin amin uwani” yunqurin miqewa ta soma yi hajjan ta dubeta
“A’ah,ina kuma zaki,ki shiga ki debi abinci kici mana”
“Ina zuwa hajja,nayi mantuwa me sashen babban yaya,zan dawo yanzu naci”
“Au to….idan kin shiga kicewa hadiza(maman haidar)ta baki saqon ki kawomin”
“Toh…toh” ta fada tana ficewa daga falon da sauri.
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:43 – ๐๐ป๐๐ป: 21
๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ
*_ALBISHIRINKU MATAN AFRICA DA KEWAYE , SHAHARARRAR KUMA KASAITACCIYAR MAI SAIDA KAYAN MATAN NAN WADDA KUKAFI SANI MAMAN YUSUF YAR SOKOTO TANA YI MAKU ALBISHIR DA CEWA ZAKU IYA SAMUN KAYANTA ADUK INDA KUKE CIKIN FADIN NIGERIA DA NIGER KARKU MANTA MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_* ๐๐๐๐๐๐๐ 07069711327
_Akwai zafafan kayan Mata masu kyau da arha cikin sauki da rahusa Kuma duk inda kike zamu aika maki kayanki cikin aminci da yardar Allah ba cuta ba cutarwa don a Dade anayi sai gaskiya uwargida da amarya ku garzayo Kar abaku labari_
Munada kalolin Kaya kamar haka๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐ซ๐๐ป๐๐ป
Maganin sanyi sahihi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata
Maganin gyaran nono domin dawo da martaban nononki hadin gargajiya da bashida illah ajiki
Maganin hips Mai tado da hips cikin kankanin lokaci
Maganin kiba Wanda zaisa ki ciko dai dai misali kiyi kyau kema ki shigo cikin jerin Mata masu aji
Maganin rage kiba da tumbi Wanda zaisa ki sace ki koma Yar dai dai abin alfaharin kowane namiji,
Akwai kalolin gumbuna masu kyau da saukar da ni’ima
Maganin matsi masu ciko da gaba da matseki Kamar Yar budurwa uwa uba zasu Baki dandano Mai gamasar da maigida
Kalolin garrika masu bawa mace niima da jimawa ajiki
Kalolin tsumi Sha yanzu magani yanzu dasa Mai gida ihun Dadi
Zumar mallaka
Zumar goron Tula
Zumar ridi
Zumar Mai rubutu
Hadin mallaka
Turaren mallaka
Shu’umar humra
Turaren AL’AJABI
Matan gaske
Ak 49
Sirrin tafin k’afa
Turaren fuska
Hatsabibin turare
Kwallin mallaka
Zoben mallaka
Jigidar maida tsohuwa yarinya
Maltinar Mata
Karya gado
Yajin Mata (yajin Mai ciko da mace)
Yajin maza (domin Karin k’arfi)
Muna dahuwar Kaya kamar haka๐ซ๐ฅ๐ซ๐ฅ๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป๐๐ป
Dahuwar zabo (mallaka)
Kazar Yar gata
Yan shila
Ciccibi
Dambu
Zuciya
Yan ciki
Kwai ukku
Tsoka Tara
Kifi
Da sauransu
Akwai sirrika sosai da muke hadawa ga wacce kishiya ta addabeta ko wadda take fama da butsarin namiji ko mafadacin namiji ko namiji Mai yawon dare ko Wanda yake bin Mata insha Allah duk zaku samesu Kuma da yardar Allah za’asamu biyan bukata
Muna bada magani ga yarinyar da tsautsayi ya fad’a Mata ta rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar da namiji Kuma insha Allah zaadace da yardar Allah
Abubuwan da yawa gsky Wanda in nace Zan lissafasu sai nakwashi tsawon lokaci maiso tabini PC don ganin kalolin kayan da muke dasu ,
Karku manta mace Mai gyara kanta Bata boranci taku ce maman yusuf Yar mutan sokoto 07069711327
.
Don Allah wadda Bata shirya ba tabari sai ta shirya sannan tayimun magana๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผngd
07069711327
_____________________________
Sanda ya koma daki ma kasa zama yayi,yakai ya kawo tamkar wanda ake kadawa kugen yaqi,cikin qanqanin lokaci idanunsa suka kada suka sauya launi.
Da sauri da sauri ya dinga sauke numfashi,har ya soma jin a hankali zafin da zuciyarsa ke masa yana raguwa,saidai gaba daya jikinsa babu qwari,daya laluba da kyau sai ya fahimci yunwa ce yakeji,bazai iya kuma cin abincin da ya siyo din ba,don haka ya yanke zuwa wajen ummi,don ita bata rabo da irin abincin da yakeso din,musamman ma yawancin lokuta takan aje fridge saboda shi idan yana gari,duk sanda ya buqata koda darene zata dumama masa shi ya koma kamar sabo ta bashi yaci abinsa hankalinsa kwance.
A gaggauce ta koma sashen abban babban,ta dubi nasma dake falo yin wani assigment da aka basu,gefanta mommy ce zaune tana duba wani dan qaramin english novel da yake meson karance karance ce,duk da shekaru sun dan tura
“Ke ina tsohuwarki?” Ta tambayeta,saita daga kai ta dubeta da mamaki,tunda tasan bata jima da fita daga sassan ba
“Tana dakinta” sai kawai ta wuce zuwa ciki,mummy tadan bita da kallo sannan ta dauke kanta ta maida ga abinda take.
Tana shiga maman na fitowa daga wanka,gefe daya kuma tana sauraren wata lacture ta dr malam umar sani fagge,gefan gadon maman ta zauna tana cewa
“Lallai hadiza,ke har kina da lokacin sauraron karatu ma ruwa yana shirin cimmaki kina zaune dafa’an” da mamaki maman ta dubeta
“Ruwa kuma uwani?,wanne irin ruwa?”ta fada tana dakatawa daga goge jikinta da take wanda takeson ya bushe ta shafa mai
“Hmmm…..wai dan Allah da saninki koda amincewarki za’a bawa danki auren sangartattar yarinyar can zahra’u?”murmushi ne ya subucewa mama
“Ni wallahi tsoro kika bani ma uwani…..na sani,zahra’u ai diyata ce itama kamar yadda yake dana,sannan kuma gwara hakan,ai ina ganin hakan shine kawai maganinsa tunda bashi da niyyar yin aure” matsowa anty uwani tayi kamar wani na kusa dasu zai iya jin abinda zata fada
“Amma dai hadiza don Allah banda abinki…..kaf ‘yammatan dake cikin dangi tsala tsala,dama wadanda ke yawo a gari,a rasa wadda za’a bashi sai yarinyar da kowa yazo guduwa yake ya barta yaqi aurenta,ke ko kishin kanki dana danki bakyayi?,kin taba tunanin meye ya hanata auruwa ma tukunna?,tunda dai banza bata kai zomo kasuwa,haka nan ruwa baya tsami banza,sannan bakiyi tunanin idan ma hadasun akeson yi saboda Allah da ma’aiki ba….me ya kawo wannan gaggawar?,daura aure nan da kwanaki bakwai kamar wadda ta aikata wani abun kunya da ba’a so ya fito?,haba hadiza,kiyi tunani mana,ga yara nan masu sonshi wadanda babu wani kokwanto a kansu?,ko suwaiba wannan tawa bakiga yadda take son yaron nan ba,kwanaki har jiyya ta kwanta,tsabar kamun kai da kunya ne yasa ta kasa bayyanawa”.
Kai mama ta girgiza
“Toh…koma meye Allah ne masanin gaibu,amma abinda na sani shine,hajja ba zata taba yin abinda zai cutar da yaran nan ba,kuma dukkanmu ta isa damu,saboda haka duk abinda ta fada dai dai ne,duk hukuncin data yanke kuma yayi dai dai” baki anty uwani ta kama tana duban mama
“To ai dama ita zatayi ne da kyakkyawar niyya,amma da za’a zurfafa bincike za’a gane akwai matsala”
“Ni bani da iko dashi tunda bani kadai na haifeshi ba,ikonsa naga mahaifinsa uwani,kullum addu’a muke Allah ya yiwa rayuwarmu zabi mafi alkhairi,kuma shi zamu ci gaba da yi,kema ki tayamu” daga haka ta juya tana ci gaba da shiryawa,gami da kokawar kauda dafi da mugun tunanin da uwani keson cusawa cikin zuciyarta haka siddan,ba gaira ba dalili.
“ฦnnnn,ai shikenan,wanda ke sonka dai shi zai hango abun cutarwa ya gaya maka tun baikai ga cutar dakai din ba,idan kinji haushina kiyi haquri”
“A’ah wallahi,ba wani haushi uwani,haba aliyyun da inna wuron ai duka yaranki ne kema” jin haka bata sake cewa komai ba sai kai data sanya ta fice.
Ajjiye man hannuta maman tayi ta koma ta zauna shuru na wami lokaci tana tunani,kafin ta miqe tana fada a sarari
“Dukkan alkhiairi ubangiji ya tabbatar dashi,ya kade dukkan wani sharri,yayi mana jagora” sai taci gaba da shiryawa abunta.
Da sallama ya shiga falon ummin,ta amsa masa tana daga zaune saman kujera,sanye da hijabi hannunta kuma riqe da carbi tasbih counter,wanda bata rabo dashi.
Yana gaidata su ilham suna gaidashi,ya amsa yana riqe da hannun sulaiman
“Ummi nace don Allah zan samu wani abu haka da zan iya ci?” Dan murmushi ta fitar
“Ai kuwa mutuminka muka dafa….ilham….tashi maza ki hadowa yayanku abinci”
“To” ta fada tana aje littafinta ta miqe ta mufi kitchen.
A dabarance haidar ke satar kallon ummin,duk yadda takai ga boye damuwar dake shimfide saman fuskarta amma hakan yaci tura,matuqar ka qware wajen karantar halayyar mutum kuma kayi mata farin sani zakasan cewa akwai damuwa tattare da ita da taketa yunqurin boyeta,saiya saukar da idanunsa wani sashen daban yana son boye nashi qwayar idanun kada ta karanto nashi yanayin.
Ba jimawa ilham ta dawo da komai a shirye,sai ummin tace
“Ajjiye masa yaci a nan basai yasha wahalar fita dashi ba” yasan ummin farin sani,zai iya cewa tun quruciyarsa suke tare,yadda yake iya karantarta haka itama take saurin karantarsa,a nan gabansa ilham ta duqa ta aje,ta duqa kuma ta zuba masa komai,sannan ta miqe ta kwashe litattafanta ita da sulaiman suka bar falon,kamar sunsan hakan ummin keda buqata.
Sai daya nutsa sosai a cin abincinsa sannan ummin tace cikin yanayi na nutsuwar nan tata
“Haidar…..dama inatason na aika ayimin kiranka” kanshi yadan daga kamar zai dubeta saiya fasa,shima anutsen yace
“Ba wata matsala bane ko ummi?” Kaita girgiza
“Matsala ce….kuma wadda na jawo maka,inason na baka haquri ne bisa matsalar dana ja maka,wanda inda nasan alfarmar dana nema wajen hajja sakamakon zai juye ne a wuyanka da ban nema ba,gaba daya maganar ma da nasan zata ja maka zargi wajen hajja da ban tadata ba…..”
“Ummi….don Allah karki sake cewa komai” ya fada cikin matuqar jin nauyinta,anya kuwa bata karanci duk abinda ke cikin zuciyarsa ba?,anya bataji maganarsu da hajja ba,wani irin nauyinta ya dabaibayeshi,yana iya tuna tun daga zuwanta gidan a lokacin da take amarya,yana iya tuna yadda ta riqeshi da,ษan data tsugunna ta haifeshi,ta nuna masa qauna sosai,irin qaunar da sai daya baro dakin mamanshi ya dawo sassanta,bai bar sassan nata ba har sai daya kai munzali sannan ya koma sashen da aka tanada saboda yara maza na gidan,duk da cewa a sannan shine da namiji na farko a gidan,bayan kuma ta samu tata haihuwar babu abinda ya canza,qauna da kulawar da take nuna masan bata ragu ba,kuma har kwanan gobe hakane….bayajin ya kamata ko sau daya tayi wannan furuci na ban haquri agareshi komai bata masan da tayi,bare ma babu wani laifi nata guda daya da ya gani kan lamarin gaba daya.
“Kina sani jin nauyi da jin cewa kamar kinga wani abu tattare dani dake sakaki tantamar baki isa….komai daya faru rubutacce ne kuma ya riga ya wuce” kai ta kada
“Nasan na isa haidar….amma lamarin aure ba qarami bane da za’a ce an yankeshi haka katsam babu nutsuwa ko yardar zukata….”
“Ummi….don Allah kiyi shuru kada ki sake cewa komai,kiyi mana addu’a”kai ya rausayar
“Shikenan…..ubangiji ya shiga lamarin” abu na qarshe data fada kenan.
Sanda ya koma daki sake shiga rudani yayi,sai yanzu yake hango girman dabaibayin da hajja tayi masa,tako ta ina shidin a qulle yake bashi da wata mafita,ya jima gaban window din daya fita waje daga dakinsa yana kaiwa hunhunsa sassanyar iskar dake kai kawo cikin fadin duniya,kafin ya samu nasarar waftar qanqanuwa daga yankin nutsuwa,sannan ya dawo cikin ainihin dakin.
Sai a sannan idanunsa suka sauka ga envalope din da general ya bashin,sam ya manta da batunta,don tunda ya shigo da ita ya aje bai kuma bi ta kanta ba.
Yakai hannu zai dauka idanunsa suka sauka kan dan qaramin hoton marigayiya zahra dake cikin wani qawataccen frame ruwan gold,saiya fasa daukan envalope din,ya soma kai hannunsa ya shafi fuskar hoton dake dauke da fuskar zahran,sannan qasa qasa ya furta
“Rest in peace” ya miqa hannu ya dauki takardar ya koma saman kujera guda daya dake dakin ya zauna ya farketa ya zaro takardar dake ciki.
Girman saqon da takardar ke dauke dashi ne ya sanyashi miqewa tsaye qyam cikin mamaki,gefe daya kuma wani farinciki na son kunnuwa tsakiyar bacin ran da yake ciki ya kuma shafeshi cikin mintuna qalilan.
Takarda ce ta qarin girma,wanda sam bai taba kawo hakan ba a ranshi,saboda shekarunshi da shekarun daya dauka yana aikin basu isa bashi wannan matsayin ba,a qalla saiya shekara ashirin da hudu sannan zai taka wannan matakin,amma sai gashi lokaci daya!,dare daya ya samu wannan matsayin.
Har ya nufi qofa da niyyara isa ga hajja da wannan albishir din sai yaja ya tsaya saboda tuna abinda ke wakana,rasa wanda zai raba labarin dashi yayi,don haka ya zauna ya lalubo wayarsa yana neman su abu sufyan,yana da yaqinin labarin bai fasu ba tsakanin manya da qananun sojoji da tuni sun kirashi.
Ya dan jima suna waya dasu,kafin wani lokaci kuma sai wayoyin mutane suka soma turereniyar shigo masa,da alama labari ya fasu,dole ya katse duk wani kira,ya shiga cikin gida ya shaidawa mama da abba babba,amma saiya share ‘yar tsohuwar bai shiga ya gaya mata ba.
Kafin ya kwanta sai daya kira general yayi masa godiya sosai bayan ya hadashi dasu abba sun masa tasu godiyar,jin bai tada masa batun su haisam ba yasa ya share shima baici komai ba,saidai ya gaya masa ana buqatarsa a office saboda wasu akwai shirye shirye na amsar office da kuma bikin qarin girman,shi a gobe zai koma wajen aiki,ya amsa masa da yana tafe da yardar Allah.
*********washegari***********
Gaba daya fuskarta ta kode ta jeme kai kace zaman takaba takeyi,saidai abinda ta fuskanta shine babu wanda ma ya damu da damuwarta,tun bayan da zancan ya soma zaga gidan duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi a sake take da walwala,bugu da qari kuma saiga kira daga hafsat yusra yasira da salma,duk wadda ta kira tana kiranta ne da ihun murna gami da tambayarta ya akayi haka ta faru?,baqinciki bai iya barinta cewa komai,saidai ta datse kiran,kuma ba zata sake daga kiran su ba,saidai suyita kira su gaji,daga qarshe saidai ta jisu suna waya da hajja daga falo,daga nan babu me sake kiranta,da alama ta gaya musu yadda aka qulla abunne ba bisa son ran kowannensu ba.
A kullum idan gari ya waye dama bata da wani aiki zaman daki tun daga wancan lokacin,saidai wanka sallah da kwanciya,abinci kuwa sai taji kamar cikinta zai hade da bayanta sannan zata dan tsakura ta koma ta kwanta.
Yauma kamar kullum,tana nan zaune gefan katifarta bayan ta gama wanka ta saka riga da zani na atamfa hajja ta turo qofar dakin ta shigo dauke da kwanukan abinci,wanda kullum ita da kanta ke kawo mata koda ba zata kulata ba,zata kawo mata ta ajjiye ta juya ta fita abinta ta barta.
Yau din data dora abincin saman inda take ajjiye mata saita qaraso inda zahran ke zaune ta zauna gefanta
“Ki zauna dai kiyita sanyawa ranki damuwa….ki hadu da wani ciwon tunda qananun shekarunki” karon farko tun bayan zancan da hajjan tabi ta kanta harma ta tanka ta,sai qwalla ta cika mata idanu,ta zumbura baki murya a dasashe tace
“Idan ma ciwon ya kamani aiba damuwa kikayi dani ba,kinga saina mutu kowa ma ya huta” murmushi ne ya kunbcewa hajjan
“Au Allah….saboda na miki gata na baki dandasheshen jikana….shine zaki ce haka?,au ashe?,sakayyar ma da zakimin kenan,maimakon ki bani danqwalelen goron albishir?”
“Ni so nake…..haka kawai ina zamana….saboda Allah bai kawomin miji ba shine za’ayi sadakata” ta fada tana fashewa da kuka,jikin hajjan sai yayi sanyi,saita koma cikin seriouse dinta bayan ta dafa bayan zahran
“Zahra’u,ki tsaya ki nutsu kiji abinda zan gaya miki,na tabbatar dama da farko zakiji babu dadi,zakiji na takuraki,zakiji ban miki adalci ba,saboda kaf cikin ‘ya’yana ko jikokina babu wanda na taba yiwa irin hukuncin dana miki….amma abinda nakeso ki sani shine,soyayya da qauna ce tasa nayi miki hakan,na tabbatar ko ba dade ko bajima zakimin godiya,zakiji kuma dadin wannan abun dana miki,alfarma daya nake nema a wajenki idan har na isa,idan har ina da kima da mutunci a idanunki” shuru hajja tayi tana kallon zahra da kukanta ya tsagaita,saita dora
“Na sani cewa a yanzu baki da wani daya shiga zuciyarki bare kice na miki karan tsaye….da wannan nake neman alfarma daga wajenki daki sassauta zuciyarki,ki cire wannan quncin takura da takunkumin da kika sanyawa ranki,ki yi juriyar maida komai ba komai ba….ki bawa aliyyu dama….na miki alqawarin cikin shekara daya indai ya kasa shiga zuciyarki da kaina zan amsar miki takardarki kije ki auri dukkan wanda yayi miki,kuma babu wanda zai tada hukuncina….abinda nakeso shine kawai ki kwantar da hankalinki” shuru tayi tana nazarin maganar hajjan tare da kokwanto,saidai cikin hikima da dabara irin tata ta tsofaffi ta samu tadan sauketa kadan,aka samu canji duk da ba wani me yawa bane.
_hello assalamu alaikum zafafa fans,kuyi haquri da jina shuru jiya,bana jin dadine,yauma da qyar na hada wannan,so idan kun jini shuru gobe kuyimin uzuri,amma in sha Allah ma zan qoqarta,kuci gaba dai dayi mana uzuri kamar yadda kuka saba,mu din ‘yan adam ne kamar kowa,mun gode da yadda kuke fahimtar damuwoyinmu_๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐ฅฐ๐ฅฐ๐ฅฐ
23/10/2021, 08:43 – ๐๐ป๐๐ป: 22
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO…! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*
_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA โYAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*
_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*
_*ZAโA FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*
_*GIRKE GIRKE GUDA 30๐ซ๐จAKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI๐ฅWATA DAYA CHAS ZAโAYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*
_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN๐๐พRIGIJI GABJI_*
_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*
_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*
_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_*
________________________________
Cikin kwanakin ikon Allah kawai zahra take kallo,yadda aka tada shirye shiryen daurin aure gadan gadan,saiga dinkuna hajjan tayi mata na shaddodi da atamfofi,ko kallon inda suke ita dai batayi ba,saboda ta fuskanci kamar ma kowa goyon bayan abun yakeyi.
Ta fannin aliyyu kuwa shiryen shiryen qarin girma da za’a masa ya janye hankalinsa sosai,don har wani lokacima yakan sha’afa da batun idan ba wani bane daga gida ya tada masa zancan,baya ma samun zama sosai,wani lokacima ba’a gidan ko a garin yake kwana ba.
Ana ya gobe daurin aure saiga baqi sun fara cika gidan,tun zahra na daukar abun me sauqi harta fahimci babba ne,saiga su yusra ma duka sun hallara,salma ta soma mata zancan itako ko qunshi da gyaran kai mana ayi mata a ranar dai.
Yadda ta rufe ido tayi ma salman tas da duk wanda ya goyi bayan zancan salman ya tabbatar musu da cewa lallai a wuya zahran take,ta dinga balbala masifa da bala’i har sai da kowa ya dare ya barta,ta buga tsaki ta sakawa dakinta key tayi kwanciyarta,bata sake bude dakin ba har zuwa washegari da safe,data tashi tana jin yunwa,sassan hajjan kuma akwai baqi,sa’annan haushin kowa takeji,batason yiwa kowa magana bare ta buqaci abinci a wajensa,don haka ta zurma hijabinta babu wanka ko kwalliya tattare da ita,kamar ba ita ake shirin daurawa aure ba tayi sassan umminta.
Abinda ya sake daure mata kai haushi ya cikata shine samun ummin nata da tayi tayi wanka abinta ta shirya cikin dinkin shadda sabuwa gal,daga ita har ilham da yusuf da sulaiman dukka iri daya.
Can dinma akwai baqi,duk da baikai cikar sassan hajja ba,saita gaisa dasu suna kiran amarya amarya,ba wanda ta tankawa,abincinma ji tayi ya fice mata a ka,don haka ta koma da baya zuwa sassan hajjan.
Mutane ta tarar yanxun a dakin nata ciki harda suwaiba,koma bayan dazu data fita babu kowa a ciki,hasina dake zaune gefan katifarta ce tace
“Ah,hala sabani mukayi,ummi tacemin kina nan,na shigo kuma ban tadda ki ba”
“Eh” ta amsa a taqaice tana isa bakin madubi ta dauki brush da maclien tayi bandaki,da hanzari hasina ta miqe tabi bayanta cikin bandakin.
Ta sameta harta soma brush din,saita jingina da qofa tace
“Wai zahra me kike yine haka?,nida salma ta bani labari na zaci iskancinki ne kawai,ai koda za’a miki auren da bakiso yanzun ai an daina wannan duhun kan,da iliminki fa?,barema miji irin Aliyyu….hmmm wallahi kukan dadi ma kike,hadadden mutum gentle man irinsa?,tsada fa irinsu suke wallahi” kamar jiran hasinan itama zahran take,saita hau kuskure bakinta sannan ta waiwayo ta dubeta
“Tunda ya miki me yasa baki magantu ba tun wuri ke an baki shi ba?”dariya hasinan ta saki tana daga hannayenta sama alamun surrender
“Kai ina….babban goro ai sai magogin qarfe,wallahi yafi qarfina tako ta ina,ya haidar ai sai irinku….yanzu dai ki maida wuqar….don Allah zahra,kodon ki farantawa umminki rai ki saki ranki kiyi abinda ya kamata,wallahi wallahi tun shigowata gidan nan na fara ganin fuskokin ‘yan baqinciki muraran,ko a dakinkin nan ma yanzu akwai yan baqinciki da yan saka idanu zaune suna aikinsu,don Allah karki fito sai kinyi wanka….na roqeki” ta fada tana hada hannayenta waje guda,harara zahran ta jefa mata sannan tace
“Naji….ki bani waje,ko kuma a gabanki zanyi wankan” dariya ta saki tana girgiza kai,haka kawai ta zama wata rigimammiya ta gaske,fita tayi gami da ja mata qofa.
Tana zama saiga anty alawiyya ta shigo itama dauke da qaramin yaronta
“Ina amaryar?” Ta tambaya suwaiba,saita yatsina fuska ba tare data amsa ba,hasina dake danna waya ta dago kai
“Tana wanka anty alawiyya”
“Toh….bari ina zuwa” ta fadi tana fita.
Kusan minti ashirin sannan zahran ta fito,wanda yayi dai dai da dawowar anty alawiyya,ta nema duka mutanen dakin su bata waje,sai hasina ce kawai ta rage.
Fada ta soma yiwa zahran sosai kan yadda ta maida kanta,ta kuma tilasta mata ta shirya,hakanan tana baqin rai da dacin rai ta shirya din,abinda yadan rage mata baqincikin shine zuwan hindatu,wanda bata tsammaci zuwan nata ba,tana bata labarin yadda suke kula da komai nata na makaranta,harda su CA da suke mata,wanda taji dadin hakan,saidai hindatun ta tambayeta dama zahran tasan aure zatayi shi yasa bata kula kowanne namiji,amma kuma koda wasa bata taba gayawa wani ko bashi labarin auren nata ba,harda ita karan kanta,duk da yadda suke?
“Uhmmm” kawai ta iya cewa hindatun ba tare data bata amsa ba.
Su ukune rak cikin katafaren dakin hotel din da suka sauka a daren jiya,haidar dake kwance rigingine hannunsa riqe da waya yana dannawa,sai Fahad dake zaune a gefansa yana latsa system din dake gabanshi.
Turo qofar akayi aka shigo,saif ne dauke da wata baqar leda dake dauke da tambarin wani kamfanin dinke dinke daya shahara a nigeria,inda suke saida kaya ready made kowanne iri.
Fahad ne ya amsa sallamar,ya qaraso ya cilla ledar gefan haidar yana dubanshi
“Ga kaya nan ka tashi ka shirya” ya fada yana zare sau cikin qafarsa,tsaki haidar din yayi yana sake dora qafarshi daya kan daya
“Ka qyaleni haka saif please,already na gaya musu ban shigo kano ba,ba lallai na samu zuwa daurin auren ba”
“Idan baka je ba kuma kayi yaya da sauran abokananmu da su zasu halarta” wani irin zabura yayi ya miqe ya zauna sosai saman gadon,da qarfi ya furta
“What!….waye ya gayyacesu?,waya gaya musu?” Ba tare daya ce masa komai ba ya nuna masa fahad da yatsa wanda keta latse latsensa ba tare daya tankasu ba.
Wani mugun kallo ya jefa masa sannan yace
“Waya saka?,waya aikeka?” Sai sannan fahad ya kalleshi
“Ra’ayi da radin kaina….waikai malam ma tsaya,duk fa wannan botsare botsaren da kake na banza ne da banga amfaninsu ba….qarya ma kake kace tun da can baka son yarinyar nan,in kuma kasan hakane me ya hana ka bamu dama mu da muke muradi?,da munyi magana sai kace mu kama girmanmu kai bakason raini,to yanzu ga qarshen tika tika nan,idan zaka tashi ka shirya kawai ka shirya bamason gulma da pretending”sosai saif keta qoqarin danne dariyarsa saboda ganin yadda haidar din ya zuciyo,ai kuwa basu ankara ba ya kaiwa bayan fahad harbi da qafarsa,Allah ya taimakesa ya goce yana dariya.
Ganin fahad xai jiqa musu aiki yasa saif ya koreshi waje
“Ka bamu waje da Allah malam” ya fada yana hade rai,saiya tattara tarkacensa ya fita yana fadin
“Ana so ana kaiwa kasuwa”
“Ka gaya masa….ni ba abokin wasansa bane wallahi ya shiga hankalinsa….if not zai raina kansa”
“Calm down mana aboki”cewar saif yana zama kusa dashi
“Ni ina mamakin wannan abun da kakeyi….banda abunka ai an wuce wannan qarnin,kada fa ka manta koda baka so kana da right na qara auren wadda kakeso,a yanzu bayan ita akwai uku a gaba ba zata tare maka komai ba,sannan kome zakayi kada ka duba hajja mana,ka duba iyayenka da aljannarka ke qafarsu,kada kayi abinda zaka watsa musu qasa a ido,wannan nasarar qarin girma daka samu duka sirrinta shine yadda kake kyautata musu da binsu,kada ka watsa albarkarka akan wannan minor issue din mana…and mamar zahran,ko yaya uwa uwace,haka ษa ษa ne,ko yaya tana son diyarta,ko yaya wani abu mara dadi ya bullo akan diyarta koda ta boye a fuskarta lallai tana jin ciwo a zuciyarta,da kanka ka gayamin matar she mean alort to you…..”
“Ya isa” ya dakatar da saif,tsahon mintuna biyar sannan ya aje wayar hannunsa ya miqe kana ya wuce bandaki kai tsaye.
****** *BAYAN WASU WANNI**********
Shudewar wasu qididdgaggun awanni da basu da tsaho unguwar tayi wani irin cikar kwari na ban mamaki,dimbin jama’a masu tarin yawa suka shaida daurin auren ALIYYU MAS’OD DABO da FATIMA SA’ID DABO bisa sadaki naira dubu dari,wanda abban tsakiya shi ya biya lakadan.
Dashi da zahra dake cikin gida dukkansu jin sanarwar daurin auren suke kamar a labarin tatsuniyoyi,kamar wani mafarki suke da babu dadewa zasu farka suga ba gaske bane,don haka shi haidar dinma ana gama dauraws maimakon ya shiga cikin gidan saiya shiga mota kawai,ya umarci drivern daya fara yawo dashi ya kaishi wani masaukin baqi na musamman ya kama daki na kwana biyu,babu irin nema da duban da ba’ayi masa ba babu shi babu dalilinsa,koda aka gayawa hajja cewa tayi
“Da ita data kwanta ciwo,dashi daya gudu duk ku qyale ‘yan kan uba,duk zasuyi su ware,ฦดaฦดan yau ne fa?,muna nan daku zasu baku mamaki,munafukan banza” haka suka gaji suka haqura da neman nasa,tunda sunsan koma ina yaje yana sane ya tafi din kamar yadda hajjan tace.
***** *_BAYAN KWANA BIYU_*********
Tuni gidan ya zamana babu kowa sai mutanen gidan,kai kace ba’ayi wani taro bama daya danganci biki,ta bangaren zahra tuni ta tattara auren da aka daura mata ta aje lamarinsa gefe,ta auna ta auno bata ga ta inda zai takura ta koya zame mata matsala ba,saidai dama da zai bata ko kuma ya zame mata tsani ko matattakala da zata taka ta cimma burinta na qarasa karatunta da take kan gaba,baya ga haka kuma sasan yadda zasuyi da sauran matsalolin,don dai bata manta da maganar hajja wadda ta sake sanya mata relief a rai ba,indai har haidar din ya kasa shiga zuciyarta to ta mata alqawarin amsar mata takardarta,maganar ma dariya take bata,don bataga ta wata hanya da haidar din zai shiga zuciyarta ba,ta yaya ma?,yadda yake jin kanshin nan,saidai kuma an samu arashin yadda yakeji da kansa itama dai dai take dashi,da ire iren wadan nan tunanukan yasanya ta sawa auren nata suna MATACCE,ta kuma fara tsara yadda zata koma makaranta abinta ba tare da wata damuwa ba.
******************
Kimanin qarfe takwas da wasu mintuna na dare,ita da hajja zaune a falon hajjan suna taba jira,ta tanqwashe qafafunta saman kujera tana yankan farcenta da nail cutter,ilham da husna na zaune daga gefe sun bada himma a kallo.
Kadan kadan kuma kamar daga dan nesa kadan da qofar shigowa sassan hajjan take jiyo muryarsa,tayi tsam da ranta,tabbas shine,don haka ba tare da kowa ya lura da abinda ta jiyo din ba ta miqe ta nufi dakinta,hajja da batasan wainar da ake toyawa ba ta dubeta
“Ke kuma meye haka?,wanne irin tashine haka kamar wadda ake kira?”
“Ina zuwa hajja” ta bata amsa tana shigewa dakin gami da turo qofar.
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu waje tana zama,ita sam bataso ma su hadu,saboda idan ta tuna cewa yana amsa sunan miji ne a gareta ita kadai tasan me takeji,ta kuma sha jan kunne wajen umminta kan kada ta qara yarda tayi wani abu akan haidar din da zai sosa ran hajjan,shi yasa tayi gaggawar barin wajen ma tun kan hajjan ta ankara da dalilin da yasata barin falon.
Ko minti uku batayi ba kuwa ta jiyo muryar nan tasa yana sallama cikin falon,a dake muryar take wanda hakan zai alamta maka fuskarsa na nan yadda kowa ya santa koma fiye da haka,babu digon fara’a ko walwala kenan,saita lumshe idanunta tana sakin tsaki,ta koma ta kwanta rigingine tana jin yadda zuciyarta ke daka.
Yana shirin xama su husna na gaidashi,ya amsa musu,duk sai suka miqe suna barin falon,sai ya zamana daga shi sai hajjan a falo,muryarshi a dake ya soma gaidata
“Barka da dare hajja….an yini lpy”
“Qalau muke” ta amsa masa a kaikaice
“Ka gama guje gujen naka?” Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,dubanta yayi kafin ya amsa mata
“Gudun me fa?…ba inda naje,kawai shiryen shiryen bikin qarin matsayin nan ne ya sanyani gaba,yazo kuma ya hade da wannan”
“Kai ka sani,nidai ina sake jadda da maka wallahi ka fita idanuna….ka kuma kiyaye ni,idan ba haka ba…bakai kawai ba,har tsohonka bazai ji da dadi ba” ta furta maganar tana kanne ido gami da nunashi da yatsa,sumeshi ya shafa yana furzar da iska
“Ya salam….to nikam hajja bansan me kikeso ba dani kuma,duk abinda kika tsara anyishi,saura me kuma?,me ya rage?” Zamanta ta gyara sosai tana kallonshi
“Ai kafi kowa sani,tunda dai kasan cewa cikin satin nan matarka zata koma makaranta ko?”
“Matata?” Ya tambaya yana jin kalmar wata banbarakwai,da confidence dinta ta gyada kai
“Eh,matarka zahra’u…..kana nufin mu ko dangin uwarta ne zamu ci gaba da dawainiya da ita?,ko bakasan haqqoqin mata akan mijinta ba na kira malami su karanta maka?” Ta qarashe da tambaya gami da zuba mishi idanu,idanunsa kawai ya dauke daga kanta ba tare da yace komai ba,kamar bazai magana ba sai kuma ya amsata
“Nima cikin satin nan zan koma,saboda ‘yan kwanaki ya rage na karba sabon matsayina” kafada hajjan ta daga
“Oho maka….kaika jiyo,ka fara sallamarta tukunna da dukkan abinda ya dace,idan yaso kafi ruwa ma gudu”
“Hajja hajja” ya kira sunan nata har sau biyu,tsohuwar tana son takai masa iya wuya,itama sai tace
“Ali…ina jinka,da magana ne?” Kai ya kada yana miqewa
“A bani abinci idan akwai”
“Zakaci iya na kwanakin dana diba maka ne kawai wlh,don bazanci gaba da aikin baban giwa ba” ta fada kamar me qunquni,yaji me ta fada amma sai yace
“Magana kike hajja?”harara ta dalla masa,saboda ta fuskancin yanzun so yake ya tsiro da wasan jika da kaka tsakaninsu
“ban sani ba,nace ka quce dakinka za’a kawo maka”
“Godiya nake” ya fada yana ciro wani turare daga aljihunsa ya aje gabanta,tabi turaren da kallo kana ta raka aliyyun da ido.
Turarenta ne da take amfani dashi,take kuma matuqar so,aliyyun yasan lagonta lokutta da dama,ba banza ba take sonshi duk cikin jikokinta,koda tayi fushi ta ruwan sanyi yake sauketa,sai tasa hannu ta dauka turaren,tana qwalawa inna gaje kira.
Cikin sakanni ta bayyana
“Gani hajiya”
“Shiryawa Aliyyu abinci maza gaje”
“Toh…toh,yanzu za’a kai masa?” Kai ta girgixa
“A’ah….ki hada kawai,matarsa ce zata kai masa”
“To toh,hakan yayi kyau” ta fada tana juyawa zuwa cikin kitchen din tana murmushi,ko ita abun yayi mata sosai,ta jima a ranta tana qiyasta auren aliyyu da xahra,ta dade tana sha’awar haka,amma bata taba furtawa ba,sai gashi Allah ya haskawa hajja,don haka cikin kuzari ta shirya komai cikin wani foldable basket mai kyau,sannan ta dawo ya shaidawa hajjan ta hada,ta amsa mata sannan ta turata ta shiga daki ta kira mata zahra,sai a sannan ma abunda ya faru dazu ya dawo mata kai,wato bisa dukkan alamu tajiyo maganarsa ne tun kafin ya shigo shi yasa tabar falon?,saita saki murmushi kawai cikin ranta tana addu’ar Allah ya shiryesu,ya kuma hada kansu.
Tare da inna gajen suka fito,tana dan rarraba idanu a falon ga zatonta yana nan saboda qamshinsa daya barwa falon,sai data tabbatar baya nan sannan ta qaraso tana sakin jikinta.
“Dauki abincin nan ki kaiwa yayanku” tace da ita tana murtuke fuska don kada ma ta kawo qabli da ba’adi,ido tadan fiddo
“Waiya musty ko ya abubakar?”
“Zaki” hajjan ta amsa mata a taqaice,ba shiri ta nemi wajen zama gefan kujera saboda yadda maganar taxo mata ba zata,wanne irin masifa hajja keson janyo mata tana zaman zamanta ne?,meye hadinta da kaiwa ya aliyyu abinci?,ita kaf rayuwarta ma zata iya tuna sau nawa ta shiga sashensa,shigarta ta qarshe ma kusa shekara goma,don duk abinda zai kaita dakinsa bata yarda ya hada da ita,iyakarta dakinsu ya musty,ko su dinma ba’a barinsu suje saida dalili,
“Amma hajja da kin baiwa su ilha…”
“Ban isa na aikeki ba kenan?” Ta jefa mata tambayar tana kallonta,xancan umminta ya dawo mata,saita saita fuskarta tana girgixa kai
“A’ah ba haka nake nufi ba,bari na dauko mayafina” ta fada tana miqewa,hajjan tabi bayanta da kallo cikin ranta tana dariya gami da cewa
“Kyayi kya gama”.
Ta jima a dakin tana jan innalillahi,gaba daya hajjan ta sakota gaba,meye na aikenta wajensa bayan tasan yadda suke dashi?,sai data gama dibi dibinta sannan ta zari zumbulelen hijabinta da baka ganin komai sai hannayenta da saman qafarta ta zura ta dawo falon ta dauki kwandon ta fice.
A hanya ta hangi aslam dan abban tsakiya,ta miqa masa kwandon
“Yauwa mutumina,don Allah kaiwa ya haidar yana dakinsa kazo na baka lada” baya yadanja yana dubanta
“Wa?,ni?,ba ruwana inna wuro,kinga,mommy ce ma ta aikeni zan karbo mata gugar kayanta zasu fita yanzu da abba”.
Yaran gidan kusan hudu ta hadu dasu kafin takai,saidai kowa ta nemi yakai abincin sai taga yaja baya,abun saita lura kamar hadin baki,ko suna tsoron wani abu,tunda dai tasan yaran gidan kaf da tsananin bin na gaba dasu,koda kuwa ba wasu shekaru masu yawa ka basu ba,hakanan basu da qiwa sam koda ga jama’ar waje bare na cikin gidan,da haka da haka tana haduwa dasu kowa na bata uzurinshi har ta isa kofar dakin nashi.
23/10/2021, 08:44 – ๐๐ป๐๐ป: 23
*Assalamualaikum warahamatullah taala wabarakatuhu*
08121491609
*Aisha s bayero traditional medicine and herbal reaserch center*
08121491609
*_MUN TANADAR MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BABU NA BIYUNSU KAMAR HAKA_*
*Step 1*
1_maganin sanyi
2_maganin niima set
3_maganin nankarwa
4_maganin kiba babba 8kkkarami
5_maganin hips
6_maganin gyaran nono
7_maganin rage kiba
8_maganin saka feeling
9_maganin cida kwai
10_zuma yar asali
11_maganin basir kowanne iri
12_hodar niiama
13_maganin mallaka
14_gumbar nonon rakumi 10k boket๐จ
15_gumbar madara 10k boket๐จ
16_turaren farin jini
17_kaza Mara kwai
18-turaren mallaka 3step
19_hadin matar minister
20_ kaza me kwai
*Step 2*
1.Turaren mallaka me kwalba
2. Me kunama Dan matsi 3k
3.tuaren goshi
4.turaren girji
5.tauwadar Mata
6.memory
7.kahon mallaka 8.yajin maza tea din maza
9. Dambun matsi
10. Man ayu 11.man damo pure daga zuwa sama
12. Kwallin idonka idona
13 garin Sha daka me kyau
14. Kubewar Mata gasunan dai da yawa bazan iya lisaafawaba harda na kyakkayin cinyoyin da matse matsi kina shafawa zakiji wasai
08121491609
dadai sauransu serious buyer yabiyoni private
me shawara ta bari saita gama karki batamun lokaci please
*_ku tuntubeni ta wannan number wayar_*๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ
08121491609
Tana tura qofar dakin wani bala’e’en sanyin Ac da qamshin freshner ya mata sallama tun kafin takai ga shiga,ashe da gaske ne ranannan data ji su hafsat na gulmarsa kan yadda yake babbakawa kansa ac,saita maida hannayenta cikin hijabi saboda sanyi,sannan ta sake tura qofar ta shiga sosai bakinta dauke da sallama qasan maqoshinta.
Tsaf dakin yake,hakanan babu wani tarkacen kaya duk da girmansa,babban gadone lafiyayye guda daya,sai kujera one sitter da two sitter da tv plasma daga gabansu kadan zaune saman wata tv stand ta zamani me tsari da yawan lockers,wanda ta tabbatar anan ya boye tarin takardunsa masu muhimmanci,bayan dan qaramin study room dinsa dake manne da dakin.
Haidar dake zaune saman daya daga cikin kujerun ya daga kanshi ya amsa sallamar,suka hada idanu saiya maida kan nasa qasa yana ci gaba da duba takardun daya barbaje a gabansa.
Yau daya sai taji ya mata wani irin kwarjini daya ratsa har cikin qasusuwanta,duk da cewa ba yaune karon farko data saba ganinsa ya hade girarsa haka ba,a’ah….dama dabi’arsa ce hakan.
A nutse ta qaraso gabansa ta aje kwandon,so tayi ta tafi amma suna hada ido sanda take shirin tashi saita koma ta zauna,kaf gidan sunsan tsarinsa baya sarving abinci da kansa,tuntuni sun saba al’adarsa haka,yana da wata izza da jin sarauta a jininsa.
Tana kammale kwanukan taji ya magantu cikin qasaitar nan tasa,takarda da biro ne ya aje gabanta
“Ki rubuta duk wani da kike buqata na komawa school”,daga haka ya dauki bowl din dake daukw da farfesun danyan kifi ya saka spoon ya fara shan romon a nutse bayan ya harde qafarsa cikij ta juna,yayin daya maida kallonsa ga tv dake aiki kan qaramin sauti da bazai damu mutum ba.
Ta gefan idanu ta kalli takardar sannan taja tsaki cikin ranta
“An gaya masa na damu ne da wani kayan hannunsa,koda can shi yakemin” tana kaiwa nan ta miqe abunta ta soma takawa zata bar dakin.
Taku biyu rak tayi ta tsinci dakakkiyar muryarsa yana cewa
“In kika sake kika fita saina biyoki har gaban hajjan na kakkarya wadan nan sili silin qafafun” yadda yayi maganar ya tabbatar mata bada wasa yake ba,duk da taji haushin ba’ar da yayi mata haka ta shanye,ta juyo tana zumbure zumbure,ta dawo ta samu can gefe ta zauna bayan ta dauko takardar.
Abu uku kawai ta rubuta taje gabansa ta ajjiye,da idanu ya kalli rubutun,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanun nasa ba tare da yace komai ba,hakan ya bata damar ficewa tana gunguni cikin zuciyarta.
Koda ta koma da kallo hajja ta bita,saboda bata tsammaci dawowarta da wurwuri haka ba,amma saita shanye,bata ce da ita komai ba.
Washegari tana kwance hajjan ta shigo
“Tashi kije ki gyara dakin mijinki” batasan sanda ta dawo rigingine daga kwanciyar rub da cikin da take ba fuskarta a hade tana duban hajja
“Waye kuma mijina?” Daquwa ta watsa mata
“Ungo nan….nace ungo nan,zaki tashi ko sai na radeki?” Ta fada tana kai mata dundu,tuni ta hantsilo daga gadon tana sosa bayan kamar ma ta sameta tana kuma duban hajjan
“Abun har yakai haka hajja?” Ta tambayeta kamar zata saki kuka
“Yama fi haka,indai zaki dinga min musu da shegen taurin kai….kuma indai kika ci gaba da yimin haka naga wanda ya isa ya karba miki takardar taki duk duniya” da haka ta juya ta fice daga dakin.
Tsoron furucin da tayi ne ya sanyata zarar mayafin doguwar rigar jikinta ta yafa tana ta mita a haka ta fice.
Har zata wuce hajjan ta kirata ta miqa mata key din,wanda dama can hajjan nada shi,daya a wajensa daya a wajenta,daya kuma a wajen mamarshi,ta amsa ta wuce tana fadi qasa qasa
“Kya ci gaba da share masa idan na komawata makaranta”
“Idan na barkin kin koma ba” hajjan ta bata amsa,sai tayi turus ta dakata da tafiyar da take tana dubanta kamar zata saki kuka
“Haba hajja,bafa haka mukayi dake ba”
“Zaki wuce ko saina iskeki?” Kamar zata dora hannu aka haka ta juya ta fice.
Kamar waccar ranar dakin ba wani dauda yayi ba,sai squeezing da beadsheet din yayi alamun an kwanta akai ne,mayafin ta daura saman kanta sannan ta fara kauda kayayyakin da suke ba’a muhallinsu ba.
Ta isa gefan gadon bayan ta gama gyara qasan,tasa hannu tana janye zanin gadon wasu frames masu kyau suka fado,cikin fargaba ta zagaya inda suka fadin,tana addu ar Allah yasa basu fashe ba,ta tsugunna ta soma daukesu.
Hotunan yaa zahra ne dukka guda ukun,kowanne sanye da hijabi take,fuskarta dauke da murmushi,kamar idan ka kirata zata amsa maka
“Margayiya” ta fada cikin zuciyarta,dan tsurawa hoton idanu tayi,sai kuma ta miqe tana jan tsaki data tuna daga inda hoton ya fado
“Aikin banza….har wani kwana da hoto yake waishi baban soyayya,aisai ka bita can shine ka burge,inda wani ne da yaji magana a wajenka” ta fada tana tuna yadda ya dinga treating din issue dinta dasu nuraddeen,locker din gefan gadon ta jawo ta watsa frames din,duk da tana iya hangen wasu pics din wanda da alama na yaa zahran ne,saita koma gadon taci gaba da gyarawa,kafin ta gama ta shiga toilet dinsa don wankewa.
Sai data kalli bandakin ta tabbatar komai ya fita fes sannan ta murda qofar ta fito.
Bata tsammaci ganinsa ko dawowarsa ba a sannan,bayanshi kawai ta hanga yana tsaye gaban gadonsa ya baje wasu takardu yana zaba,da alama daukarsu ne ya dawo dashi.
Jin taku ya sanyashi juyawa a hankali,sai suka hada ido na sakanni kafin ya dauke idanunsa ya maida ga abinda yakeyi ba tare daya ce komai ba,sai tabi ta bayansa itama ta fice daga dakin.
Batafi minti biyu da fita ba ya shiga wajen hajjan yana hadiye zuciya riqe da envalope a hannunsa
“Hajja….me yarinyar can kemin cikin daki bayan bana nan?”
“Sata ubana” ta amsa masa itama tana tsareshi da idanu,saiya lumshe idanunsa,tsohuwar tana bashi ciwon kai yadda ya kamata,ita kadai duk duniya ta isa tayi masa karen tsayen da take masa,saiya juya kawai ba tare daya sake cewa komai ba ya fice daga sashen
“Zanyi maganinku” ta fada a ranta,tana dauke idanunta saiga zahra
“Wai hajja ma tuhumata yake da shigar masa daki?,nidai wallahi hajja kina jamin ina zaman zamana” ta fada kamar zata saki kuka
“Yanzu ma na fara jaza miki” tuni ta tara qwalla a idanunta
“Bazan sake masa shara ba Allah,ayiwa mutum aiki sannan ya rasa me zai sakamin dashi?,to dakin nasa dakin wa yafi cikin gidan nan?”
“Idan bakije kinyi ba nida kaina kuwa zan dauki tsintsiya naje na share masa,idan kuma banje ba zansa daya daga cikin iyayenki yayi”saroro zahra tayi kafin ta juya zuwa cikin dakinta da sauri.
Mita take ita daya kamar zataci kanta,tana qissima sauran kwanakin daya rage tayi tafiyarta makaranta,ita gobe ma gidan salma ko hafsat zata,sai kuma ta tuna idan tace zata din sai hajjan nan tace saita tambaya,ita kuwa data tambaya gwara haqura da zuwan.
*BAYAN KWANA BIYU*
Ana ya gobe zata koma makarantarta,tana falo tana sake goge wasu kayan da zata tafi dasu atamfofinta,musaddiq jikan gidan yayi sallama shi da nurain,hannunsu dauke da leda suka zubw gaban hajja
“Gashi inji yaa zaki,na yaya zahra ne”
“Shi yana ina?” Hajja ta tambaya
“Yana waje yana sallamar wasu baqi ne” inji nurain yana hayewa saman kujera
“Jeka kace min idan ya gama yazo ina son magana dashi”.
Jin haka ya sanya zahra a gurguje ta gama goge kayan nata ta miqe zata shige daki
“Ke….dawo ki kwashe wadan nan kayan daga gabana” tana zumbura baki tana fushinta haka ta dawo ta kwashe ledojin ta jasu har cikin daki,ta musu waje ta jibge ta shiga sabgarta.
A gurguje ya leqo saboda kiran da hajjan tace tana masa,bayan sun gama gaisawa tace dashi
“Qarfe nawa zaka miqata makarantar a gobe?,don inason na qarasa hada mata abinda yayi shaura” kansa ya daga ya kalli hajjan
“Oh….ai dama bani ke kaita ba ko?”
“A sanda take babu igiyar kowa a kanta kuma ba matar wani bace ba ba…banason dogon magana,ka shirya gobe da wuri ka maidata makaranta” yasani cewa koda ya fada wani abun ma babu abinda zai janyo masa sai bala’en hajjan,wanda ya lura da cewa yanzun wani bala’i ta koya,motsi kadan zata ce anemo mata tsoho da tsohuwarshi.
******* *WASHEGARI********
K’arfe takwas da wasu mintuna ta gama shirinta tsaf,ta shiga tayi sallama da umminta sannan ta shiga sashen abba babba shima tayi masa sallama,sannan ta wuce dakin mama,maman haidar ta mata sallama
“Allah ya kiyaye hanya,ya bada ilimi me amfani” ta miqa mata wata baqar leda da batasan meye a ciki ba,hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya sannan ta fito.
Tana takowa zuwa bakin motar tana kallon yadda ake sanya mata kayanta bayan motar tashi,shi yana zaune daga ciki ba tare da ya ko motsa ba,tana tsaye har aka gama sanyawa sannan ta matsa ta bude gaban motar ta shiga a hankali.
“Ina kwana” ta furta domin bin umarnin umminta,bata ji ya amsa ba duk da taji alamun motsin fitar sauti,dama kuma ba damuwarta bace ya amsa din ko kada ya amsa,illa iyaka tasan cewa ta fita haqqi,ta kuma cikasa nasiha.
A hankali ya tada motar kana ya saitata ya fice daga gidan,kafin subar layin ya sanya hannunshi gaban motar ya dauko wayarsa yayi kira ya sata handsfree ya aje,bugu biyu aka daga
“Ka sameni a nasarawa sardauna cresent” daga haka ya katse kiran ba tare daya jira amsar da za’a bashi ba.
Tafiyar kurame da takura daga wajen zahra ta mintuna ba dasu gaza ashirin ba ya tsaya qofar wani gini wanda ake gab da kammalashi,kashe motar yayi ya zare key din ya fita daga cikinta y kulle sannan ya jingina da murfin,ita dai batace komai ba tana kalloshi ta cikin glass din har zuwa sanda ta hangi shigowar ya musty a napep na haya,bataji me suka tattauna ba,saidai taga ya miqa masa.key din,kana ya matsa daga jikin motar zuwa ginin gidan dake gabansu,shi kuma mustapha ya bude motar ya shigo.
Sai daya rufe sannan yace da ita cikin tsokana
“Sai matar babban yaya….Allah dai ya biya,matar soja marmari daga nesa” harara ta watsa masa
“Kaga ya musty bama haka dakai,dadai ya shamsu ne nasan zaiyi abinda yafi haka,don Allah ja muje,ni hakan ma yafimin dai dai” ta fada tana yatsina,yayin da mustapha ya qyalqyale da dariya.
Ko kadan hakan bai bata haushi ba,saboda tasan cewa inda shine zai kaita babu komai cikin tafiyar face zallar takura har su isa,wala’alla ma sai yayi ko ya gaya mata abinda ranta zai baci a banza.
Sanda ta shiga dakinsu kamar hadin baki duka roommate din nata suna nan,har da sauran ma,ihu suka saka suna kiran ga amarya ga amarya,bata tanka su ba saima harara data watsa musu
“Duk ku iya bakinku wallahi” don har ga Allah har cikin zuciyarta tana jin sune sila,su suka jaza mata komai,saidai ko kadan basuji gargadin nata ba,saima ci gaba da zolayarta da suke,hindu tace
“Erhmmm….erhmmm…ashe ashe dai….yayan dai da aketa nunamin sam baida kirki…..ashe dai kece zaki wufffff da abinki akemin hannunka me sanda” kicin kicin zahra tayi da ranta sanda take aje jakankunanta saman katifarta
“Kinga hindatu….idan baso kike aji kanmu ba ki aje wannan maganar….am seriouse bana sonta” saida suka gama kidansu da rawarsu sannan suka qyaleta.
Zuwa washegari ta gama gyara komai nata,batayi qasa a gwiwa ba ta koma lactures cike da hazaqa karsashi da qwarin gwiwa,saidai haka nan ta samu kanta da takatsantsan da mu’amalarta da mazan ajinsu,duk da cewa dama can duk wanda ya sa ta yasan tana da wannan zarrar,amma a yanzun takatsantsan da kamewan ya qaru,tunda ada issue din karatu yakan hadasu,amma a yanzun mawuyacine idan ba ya zama dolen dole ba.
23/10/2021, 08:45 – ๐๐ป๐๐ป: 24
*_Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg’s skincare is the best plug for you๐ค_*
*_Do you wish to have that flawless skin that’s free of all skin prblm_*
*_Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go๐_*
*_Try mg’s product nd I assure you you’ll never use any other product except mg’s productโ
_*
*_Mg’s will gv you the best out of all_*
*_With mg’s product ur skin is ๐ฏ clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day๐_*
*_We have herbal whitening black soap now nd beauty set available_*
*_Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it๐ค_*
*_Just gv it a try now nd see wondersโ
_*
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
*_Nd guess wht๐ฆป_*
*Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set๐so what are you guys waiting for hurry nd grab urs๐ now is the time to glow๐งโโ๏ธ*
*Pamper ur skin๐ฆต*
*Shine like a bride ๐ฐ*
*be part of the glow* *team karkubari abaku lbr*
Just chat 08062991549 to plc ur orders๐
Do not forget to follow us๐
Like nd comment pls dearies๐
Patronize us๐
mg’s always serve you the bestโ
โค๏ธ
______________________________
*_BAYAN SATI BIYU_*
karfe biyu na rana suka fito daga aji,sauri take tana Allah Allah ta isa daki ta cire kayan jikinta ta samu ta watsa ruwa saboda zafi da rana,tuni ruwan sama ya fara samuwa a wasu garuruwan kamar legos abuja da sauransu,ya zuwa sannan kano da kaduna suma suna saka ran samun nasu ruwan saman na farko.
Tana tafe tana qiyastawa a ranta,a qalla wannan satin tanason taje gida weakend,don tunda ta dawo bataje din ba,saboda kuma raguwar karatu da fara shirye shiryen jarabawa tana tunanin zata dauki kwana goma kafin ta dawo,don yanzu sam ba kasafai take jin dadin zama tare dasu hindatu ba,takatsantsan take,batason wata matsalar ta sake kunno kai,saidai duk da haka bata fasa gaya musu gaskiya ba,kuma alhmdlh tana ganin hasken hakan,don da yawa daga dabi’un da basu daukesu a bakin komai ba a baya zuwa yanzu babu mafi yawa daga cikinsu.
Tana gab da shiga dakinsun wayarta da bata jima da kunnata ba ta dauki tsuwwa,saita dauko tana duba me kiran,ya shamsu ne,tadan ja tsaki tana murmushi,tana rayawa a ranta wala’alla ya kirata ne kawai ya tsokaneta ya kuma cakar da ita
“Sai matar yaya” ya fada yana dariya,shida musty kusan sun soma sauya mata suna,tun tana bala’i harta gane ma zugasu takeyi
“Cima zaune….ya akayi?”
“Hajja….ita tasa na kiraki,kuma sai an biyani kudin katin dana qona”
“Karka damu,an gaya maka mu fuqara’u ne irinka?”
“Ni nasan kun girmi wajen….matar aliyyu dabo ce fa…..muma aci gaba da yi mana addu’a….ya haidar ya mana alqawari,upper dinmu tana nan zuwa hannu”
“Kaga…ka gayan saqon hajja ya shamsu koka qona katinka a bati wallahi”
“Naga alama kin soma rainamu nida musty tunda aka daura miki igiyar auren ya zaki….to hajja tace ta kasa samunki,ki shirya nan da minti ashirin ina hanya,zan daukeki nakai mata ke airport”
“Airport kuma?….me hajja keyi a can?”
“Kinga idan kinje kyaji,nidai aikina zanyi”
“Shikenan….saika qaraso” ta fada tana kashe kiran,sannan ta tura qofar dakin nasu ta shiga.
Hindatu ta samu ta zaune gefan gado riqe da plate tana cin abinci,daga ita sai vest da zanin atampha,da alama itama bata jima sa shigowa ba,zafi ya haukatata,sai jannat dake zaune a qasa ita kuma tana shan lemo.
Tana aje jakarta tana musu sannu gami da zare mayafinta,sannan ta soma qoqarin canza kayan jikinta zuwa na wanka,hindatu ta dubeta
“Ga abincinki fa…”
“Ai hindu inajin saina dawo zanci,yanzu ya shamsu yakirani hajja ke nemana wai kuma a airport…ko lafiya” hindun nakai lomar abinci bakinta ta amsa masa
“Lafiya mana,dadai asibiti akace shine zaki tsammaci ba qalau ba”
“Hakane” ta fadi tana sanya hijabinta gami da daukar shower gel dinta ta nufi bandaki.
A gurguje ta shirya cikin atamfa riga da skert da sukayi matuqar yi mata kyau da amsar jikinta,tana fesa turare kiran shamsu ya shigo
“Ki sauri don Allah,hajja nata azalzalata fa”
“Am coming” ta fada tana jefa wayar a jakarta gami da qarasa daura agogon hannunta,ta zura takalminta tana rataya jakarta hindatu tace
“Wannan kwalliyar kyanta zakin maza aka yiwa ita,bakiga yadda kwalliyar ta amsheki ba,sai yaushe kenan?”harara ta jefa mata tana gyara eye glasses dinta wanda ta soma amfani dashi kwanan nan
“To bashi aka yiwa ba sai yaya?,Idan na dade awa uku,shi daya kaini shi zai dawo dani,saboda jibi zan wuce gida,ban kuma gama shirya kayana ba,zanje dasu gida na canza wasu”dariya tayi
“Ai shikenan,Allah ya hadaku a hanya ya dauke abarsa inga ta tsiya,any way…….saikin dawo” inji jannat
“Ki gaida hajja” hindatu ta fada ita kuma tana dariyar maganar jannat wadda zahra keta aikawa saqon harara
“To zataji” ta fada tana fita da dan hanzari,don tasan halin ya shamsun da shegen qorafi.
Suna tafe a mota suna taba hira,duk da yawanci duk tsokana ce yake mata kamar yadda ya saba,kusan haka halinsa yake saidai idan ba’a hadu ba,ba yadda batayi dashi ya gaya mata meke faruwa ba yace shima bai sani ba,yana gida aka bashi wannan umarni,idan taje ta gani,sai tayi shuru kawai tana dan nazari a zuciyarta.
Babu jimawa suka iso filin sauka da tashin jiragen sama dake garin namu na kanon dabo,kai tsaye ya mata jagora tana biye dashi har zuwa inda yace mata hajjan nacan a zaune.
Tun daga nesa ta hangi hajjan,gefanta mama ce da umma matar abba yusuf,daga daya side din kuma abba babba ne da abban tsakiya,gabanta ne yadan fadi kadan,ta ambaci sunan Allah a ranta,sannan ta qarfafawa kanta gwiwa ta isa inda suke.
A ladabce ta gaida kowa idanunta na karantar fuskarsu,babu alamun tashin hankali tattare dasu,saima farinciki data karanto kan fuskar kowannensu,da alamu kuwa tafiya ce ta kamasu,don akwai travelling bag tare dasu,ta kasa tambayar kowa har sai data zauna kusa da hajjan tata
“Hajja….sai ina kuma haka?,ko bana anyi kira?,Allah yayi za’a koma umra?” Ta fada cikin sigar tsokana,baki tadan tabe
“A’ah fa….duk da itama umarar muna saka rai nan ba da dadewa in sha Allahu….amma yanzu dai yayanku ne bikin qarin girmansu ya tashi…..shine ya aiko mana da tikiti zamu sameshi can abujan” ta gane sarai kan wa take magana,saita dan dauke kai cikin sigar bagarar da zancan tace
“Shine takanas kikasa aka dauko miki ni,yanzu hajja ba zamu iya yin sallama ta waya ba?”
“Sallama dawa?,ai dake za’a tafi,kema na siya miki naki tikitin,tafiya kawai ta rage miki” da sauri ta dawo da dubanta ga hajjan
“Tafiya kuma ina?”
“Au….bakiji duka bayanan dana miki ba dazu….to can abuja inda za’ayi bikin”.
Wani gumi ne ya yanko mata ta tsakiyar bayanta,wai me yasa hajja keson ta dinga yarfata ne,banda yarfawa tsakani da Allah kawai sai ta jata gayyar sodi haka akeyi?,yanzu tana magana kuma sai cibi ya zama qari,gashi basu kadai bane a wajen,akwai mama,wanda tsakani da Allah tana jin nauyinta,don tsaf hajjan zata iya mata tarere ta barta da kunya,amma saita yanke bari ta gwada tata dabarar
“Banda abun hajja….haka ake tafiya gaba gadi babu shiri babu sanarwa?” Sheqeqe hajjan ta kalleta,da alamu babu nasara a zancan zahran
“Wanne shiri kuma?,duk wani shiri kwa yishi tare da mijinki….idan kuma ta kayan sawa ne gasu nan,takanas na kira ilhama ta hada miki duk abinda tasan ya kamata,sai kuma me?” Shuru zahra tayi tana duban ‘yar trolly dinta qaramar wadda takan dauka lokaci zuwa lokaci,cikin ranta tana furta innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,daga sannan bata sake magana ba,sai kawai taja bakinta ta tsuke,illa wayarta data ciro ta turawa hindu text na cewa ba zata dawo a yau ba,ta kula mata da lamarinta koda wani abun zai taso daga gobe zuwa jibi ta shaida mata,daga haka ma saita kashe wayar gaba daya ta zubawa sarautar Allah idanu,gami da hasashen yadda komai zai wakana,itadai tasan basa hada inuwa daya da haidar,amma ta qarfi da yaji alo tsiya alo danja hajja ta kafe sai sun jiqa kanwa guda dashi,ita sam bata qaunar wannan girman kan nashi da ji da kan nasa kamar wani mace,macen ma saraki.
‘Yar kallo kawai zahra ta koma tun daga shigarsu jirgi zuwa saukarsu,tsoron ma da akace akanji a hawa jirgi karon farko ita bai wani dameta ba,saboda inda zatan yafi komai damunta a ranta,ji take kamar ta rufe ido ta bude ta ganta a makaranta.
Suna sauka tun cikin airport din abujan aka taresu,wani matashi sanye da kakin soja ya musu jagora zuwa wata galleliyar sabuwar mota,wanda kallo daya zaka mata kasan cewa sabuwa ce da gaske,shi ya bude musu dukka suka shiga ya shigar da kayansu booth sannan shima ya shiga.
Gaishesu ya soma yi da tattaciyar hausarsa pure bisa dukka alamu dan arewa ne bahaushe,yanayin girmamawarsa garesu ke nuna yasan kosu din su waye a wajen aliyyun,saida suka gama gaisawa sannan ta yada motar suka fice,yayin da kunnuwan zahra ke biye dasu,tana jin yadda suke hirarsu,abba babba na nuna musu wasu guraren da ya sani cikin abujar idan sunzo wucewa ta wajen.
Tafiyar wajen minti talatin da uku ta sadasu da unguwar da suka nufa,unguwa ce dake cike da tsari da gine gine masu ban sha’awa,a hankali driver din yace
“Oga ya bada umarnin a saukeku a sabon gidansa,akwai duk abunda kuke da buqata,wani uzuri ya riqeshi amma nan bada jimawa ba zai iso ya riskeku a gidan”
“To ba matsala,ya kirani bayan mun sauka ai,munyi magana dashi” cewar abban tsakiya,kai matashin ke gyadawa sanda yake yunqurin tura motar tasu cikin wani madaidaicin gida dake dauke da matsakaicin qawataccen gate bayan mai tsaron gate din shima dake sanye da kaki ya bude musu gate din.
Wata madaidaiciyar rumfar adana motoci ya shiga ya faka motar kusa da wata mota dake a rufe ruf,da alama ita dinma sabuwace,zaka gane hakan kota iya tayoyinta.
“Ma sha Allah….ma sha Allah” kawai kowa ke fada,saboda yadda gidan ya tsaru ya kuma qawatu,duk da cewa ba wani qaton gida bane,saidai yana da yalwa dai dai misali,akwai haraba madaidaiciya wadda ke dauke da wata rumfa ta bunu da wasu irin kujeru qasanta da teburi saboda dora kofuna da lemuka,akwai balcony mai kyau da wasunirin kujeru guda hudu da wani irin qarfe da aka zube a cikinsa bayabga furanni wanda ta cikinsa balcony din zaka isa falon gidan,wanda ya dauki set din kujeru biyu sai dining area,daga daya bangaren akwai gajeran corridor wanda ke dauke da dakunan bacci guda biyu da bandaki a tsakiyarsu,duk da kowanne daki yana da bandaki,uwa uba kuma akwai wani spare dakin cikin falon.
Akwai ma’aikata maza guda biyu da suka tadda cikin gidan,daya shine kukun sa,daya kuma me gyara falon gidan da bandakuna,banda bedrooms dinsa.
Dakin dake cikin balcony din nan aka budewa su hajja,yayin dasu abba babba kuma aka bude musu na ainihin falon.
“Ma sha Allah….gaskiya ne,wannan gida saidai fatan alheri,Allah yasa an shiga a sa’a” umma ta fada tana kallon kowanne bango na dakin da aka qawata da wasu fitilu da fenti mai kyau,ga kuma qyallin sabunta na haska dakin ya qara masa wani haske me kyau.
Tunda ta samu gefan qatuwar katifar dake yashe a dakin bata ce uffan ba,duk hirar da suke tayi a tsakaninsu nata idanu,abu daya tayi shine ta shiga tayi alwala bayan sunyi tasu,hajja kuma ta hada da watsa ruwa,don ita jin zafi gareta.
Duban zahra tayi sanda take fitowa daga bandakin,tana ware mayafinta zata lullube jikinta don yin sallah
“Banga alamun wanka a tare dake ba,ko kina nufin yadda muka taho a haka zauna” sosai hajjan ta bata kunya,ta saci kallon umma dake sallah kana ta maida dubanta ga hajjan tana kyabe fuska qasa qasa tana mata qorafi
“Au….yoni Allah na tuba hadiza baquwata ce?,ki koma kiyi wanka kinjiko?”sauri tayi kawai ta tada sallah,don tasan idan ba hakan tayi ba hajjan ba zata qyaleta ba.
Kafin ta gama sallar umma tuni ta gama,saita tattara abun sallar ta fita daga dakin,da alama itama nauyi takeji,hakan ya baiwa hajjan damar tsigale zahra tasss,saidai tayi kunnen uwar shegu da hajjan,charting dinta ma take abunta,harta gaji ta haqura.
Kafin sauran suyi wanka su huta tuni an cika teburin gidan da nau’in abinci kala kala,cikin girmamawa da gurbatattar hausarsa yake shaida musu an gama komai,su abincin ke jira
“To….to sannu da qoqari yaro kaji” abba babba ya fada,sai yayi murmushi cikin girmamawa yace babu komai.
Ganin an kusa sallar la’asar sai suka yanke suyi sallah dukkansu a jam’i sannan su zauna cin abincin,don basuga masallaci nan kusa ba,haka kuwa akayi,abban tsakiya ya jasu sallar,suka idar sannan suka hallara kan dining din,ita dai hajja mita ta soma kan ba zataci abinci kan teburi ba,don haka zahra ta diba mata nata ta shimfida mata ledar cin abinci a qasa sannan ta aje mata
“Yauwa,yanzu naji batu….ke ya kika samu waje kika zauna?” Tace da zahra wadda ta koma saman kujera ta zauna maimakon ta koma wajen cin abincin
“Na qoshi” ta amsa mata ciki ciki
“Ungo nan” ta fada tana watsa mata daquwa
“Sauko kici tun banci mutuncinki ba” soma saukowa tayi dai dai sanda qarar bude gate din gidan ta riskesu,ba jimawa saiga biyu cikin yaran gidan suna shigowa da kayayyakin amfani na gida suna jibgewa,suna kammalawa muryar sallamarshi ta cika falon,hakan ya sanya zahra janye yatsunta daga abincin da take ci din,saboda ji take kamar zai mata kallon makwadaiciya,saboda zuwa gayyar sodin da hajja ta jawo mata,bugu da qari ta tilasta mata cin abincin gidansa,wanda ita sam bataso hakan ba.
Saidai yadda suka gaisa a tsaitsaye ma ya nuna akan uzuri yake,don ko nuna ya ganta cikin falon bata ga alamunsa ba akan fuskarsa,ya tambayesu zai koma sai wajen dare zai sake shigowa,yanzu ma ya tsaida wasu abubuwanne yazo yaga isowarsu lafiya,idan da abunda suke buqata suyi magana,addu’a sukayi masa da fatan alkhairi ya miqe yana musu sallama cikin kuzari da hanzari irin na namijin soja,taku bibbiyu ya juya ya fice daga falon.
Zahra ita ta gyara komai da suka bata,su abba babba suka buqaci fita gari wajen wasu daga cikin mutanensu da suke harka dasu,saiga driver ya taso da hanzari,motar da aka kawosu cikin gidan ya bude musu yace su shiga,oga yace duk inda zasu ya kaisu,hakan ya musu dadi da kuma sauqi.
Cikin gida suma hirarsu suke abunsu,zahra ce kawai ta shiga daki ta kwanta saboda gajiyar da takeji a jikinta,bata farka ba sai ana gab da sallar magariba,koda ta leqa falo duka suna can sun daura alwalar salla,da alama su abban ma sun dawo,ga mamakinta sai taga ya musty,idanu ta fiddo
“Kai,yaushe kazo?”
“Sanda kikayi nisa a duniyar bacci,yarinya taji hadadden gida” ya amsa yana dariya gami da sauke hannun rigarsa dake tattare,shima da alama alwala ya daura,da idanu ta masa nuni da mama dake wajen,dariyarsa ya gumtse yadan matso inda take
“Yaushe aka fara kunyar mama wai haka?,anya kuwa?,ba’a fara yi da danta ba?” Tabbas da zata iya duka zata kai masa,to amma saboda ba halin hakan saita bishi da harara shi kuma ya fice yana dariya,yayin data koma ciki itama ta soma haramar sallar.
Sai bayan sallar isha’i sannan ta shiga tayi wanka,ta dawo ta jawo jakar kayanta ta buda.
Da ษaya da ษaya take duba kayan da ilham ta hada mata,gaba daya haushin duniya ya cikata,tabbas da ilham na kusa saita mammaketa,gaba daya riga da skert dinta wanda bata sakasu saita dora after dress akai,sannan babu bra ko pant a ciki sai qwara daya,gefe daya taje ta debo mata kayan bacci cikin wadanda ta fara tarawa a baya,sanda take saka ran aurenta tare da ‘yan uwanta
“Lallai yarinyar nan ta rainani….Allah saita raina kanta,bari muje gida” ta fada tana cire daya daga cikin kayan baccin doguwar riga ce wadda kadan ya rage ta isa idon sahunta,ita kadaice me dama dama,saita dauki aron hijabi daya cikin hijaban hajja ta zumbula bayan ta shafe jikinta da turaruka kamar yadda ta saba duk sanda zatayi shirin bacci.
Falo ta dawo ta iskesu suna hira,mama da umma su suka fara tashi,dama tuni abba babba suna waje,da suka shigo kuma sai suka musu sallama,don abba babba yace ya kama musu masauki acan zasu kwana,ya rage a falon daga hajja sai zahra sai musty,sai a sannan zahran ta samu sukunin zubo abinci ta zauna tanaci suna kwasar dariya,saboda wata drama da ake haskawa,hajja ta dage saita fahinta abinda akeyi,musty na fassara mata yana hadawa da yi mata tsiya suna kwasar dariya abunsu harta gama,ta maida farantin ta dawo sukaci gaba da hirarsu.
Qarfe goma na dare aka sake bude gate din mota ta shigo,zahra dake zaune daura hajja sai taji tasha jinin jikinta,dukkansu sunji shigowar motar,saboda haka babu damar tace zata waske ta tashi,tilas taci gaba da zama a wajen,har zuwa sanda muryarsa ta fara ratso falon yana amsa waya kafin isowar gangar jikinsa,hannunsa daya dafe da waya,dayar kuma baqar leda ce dauke da tambarin wani wajen saida abinciccika.
Musty ne ya miqe ya amsa ledar yana masa sannu da zuwa,da hannu ya amsa masa yana qarasowa,ya samu waje ya zauna yana yin sallama da wanda suke wayar ya kashe ya maidata aljuhun gefan wandonsa yana duban hajja bayan yadan sauke ajiyar zuciya,da alamu a gajiye yake sosai
“Sannu da gida….ya naji gidan shuru?”
“Duk sun kwanta saura mu,babanka kuma yaqi kwana,yaa kama musu masauki sun tafi can” goshinsa ya dafe
“Ya Allah….daya fadi hakan yakeso ai da nayi waya an basu daki”
“Wallahi….sun jima aida tafiya”.
“Ina wuni” ta furta idanunta na kallon qasa,don ta fuskanci hajja ta sanya musu idanu sosai,saiya waiwaya kadan ya dubi inda take ya dauke kai kana ya amsa tare da cewa mustapha ya bawa hajja ledar,wanda ke ido biyu suyi amfani dashi,karba tayi tana masa godiya,saiya miqe yana wucewa zuwa ciki
“Inajin sai da asuba zamu hadu,am very tired hajja….mustapha…..idan ka tashi da asuba ka nemi ni,don zan fita da wurwuri akwai kuma aikin da zan baka”
“To yaya” ya amsa masa.
Bai rufe minti goma da shiga ba hajja ta dubi zahra tana hade rai
“Ke inna wuro….hada abinci ki kai masa” kamar zata musa saita fasa,ta miqe tana jin kamar ta bace hajjan ta daina ganinta,ta isa bakin dining din ta hada komai saman wani qawataccen babban tray ta durfafi dakin.
A hankali kamar wadda ta shigo sata ta tura qofar dakin,tana saka qafarta cikin dakin ta lume cikin wani kallausan carfet daya rine da sanyi,baya ga qamshi na musamman daya ziyarci kafofin hancinta,zata iya cewa dakinsa nacan gida kango ne akan wannan,duk da bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa qarewa dakin kallo amma a kallo daya kawai idanunta sun kaiwa qwaqwalwarta saqo da dama game da kyau da tsaruwar dakin,qarar ruwa da takeji daga wata qofa dake hannun hagu na dakin ya tabbatar mata yana bandaki,kamar an mata rahama haka taji,don haka da dan sassarfa ta isa ga wani dunqulallen qawataccen table ta dora plate din,ta koma da baya tana ficewa daga dakin da sauri.
Sanda ta koma tana ankare da irin kallon da hajjan ta bita dashi,amma batace da ita komai ba,itama saita share kamar bata gani ba,hajjan bata jima ba ta tashi ta barsu ita da musty sukaci gaba da hirarsu,ba’a jima ba itana taji bacci ya soma daure mata idanu saita miqe tana masa sallama,shima kayan kallon ya nufa yana kashewa gami da cewa
“Nima kwanciyar zanyi,saboda gobe na tashi fresh,kinsan goben nan fa babu sauqi,zamu hadu da manyan mutane….Allah yasa nayi babban kamu nima….” Harararsa tayi
“Ai anan kuka fi kauri”
“Kinga laifina?” Saita saki dariya tana yin gaba,sau tari sai ta dinga ganun mustapha kamar ba cikinsu daya da haidar ba,saboda tsananin sauqin kansa.
Da sallama ta tura qofar,sai taga duhu,qwayayen dakin a kashe,lalube ta soma yi don kunna qwan,taji muryar hajja na fadin
“Waye anan?”
“Hajja nice fa” ta fada dai dai sanda tayi nasarar ganin makunnin ta kunna,haske ya gauraye dakin
“Me kikazo yi kuma?,salon ki hana jama’a bacci ku da baku gajiya da surutu” saita miqe ta zauna sosai tana kallon zahra,mamaki maganar hajjan ta bata,don haka tace
“Nima kwanciyar zanyi ai,bacci nakeji sosai wlh”
“A ina zaki kwanta din?,badai a nan dakin ba” saroro tayi tana duban hajja,murya qasa qasa saboda karsu tashi sauran tace
“To a ina hajja?,akwai wani dakinne bayan wannan?”
“Eh….dakin mijinki me yake?,ko ce miki nayi na daukoki ne kizo ki kwanta gotai gotai a gabana?,ko kuma kiji dadin jirgi ki koma?” Idanu ta zaro,wato hajja da manufarta kenan a ranta tasa aka daukota takanas daga makaranta?,kwanan dakin haidar dai dai yake da kwana kusa da maqabarta,ta inama zatace wai taje su kwana daki daya?,saita karyar da murya kamar zata saki kuka
“Haba hajja….haba hajja don Allah”
“Au ba zaki fita ki tafi ba dogon bayani kikeso kenan?,toni bari na baki nawa makwancin naje mu kwan tare dashi” ta fada tana qoqarin miqewa duk da ciwon qafar da take fama dashi.
Abun saiya girmami kan zahran,da mugun sauri ta juya ta fice daga dakin,don tasan indai hajjan ta miqe to taja mata jagwal,don sai ansha daga kafin a sha kanta.
23/10/2021, 08:45 – ๐๐ป๐๐ป: 25
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO…! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE..*_
_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA โYAYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.*._
_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61*_
_*ZAโA FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU*._
_*GIRKE GIRKE GUDA 30๐ซ๐จAKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI๐ฅWATA DAYA CHAS ZAโAYI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN.*_
_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN๐๐พRIGIJI GABJI*_
_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!*_
_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar*_
_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA*_
_____________________________
Tsayawa tayi a tsakanin dakunan da falo tana kalle kalle,tare da tunanin me ya kamata tayi,tabbas kome hajja zatayi mata saidai tayi mata amma ba zata taba yarda ta shiga dakinsa da sunan kwana ba,sai kace wadda ake neman kai da ita?,ko kuma itace mijin shine matar?,sam bazai yiwu ba,saita qarasa ficewa,ta isa wajen tvn da dazun musty ya kashe ta kunna,ta koma kan kujera ta zauna tana rungume pillow gami da sauya tasha.
Kusan a qalla awa daya ta kwashe a zauna,gidan ya dauki shuru,sai tsoro ya fara cikata,don haka ta kashe tvn ta miqe a hankali ta nufi dakin nasu.
Sadaf sadaf ta tura qofar dakin,yan nan da duhunsa da alama kashe qwan hajja ta sakeyi bayan fitarta,saita kunna fitilar wayarta ta haska a hankali ta isa bayan hajjan tayi kwanciyarta nesa kadan da ita,ta tofa addu’o’in baccinta ta rufe idanunta tana addu’ar kada Allah ya farkar da hajjan.
Washegari tana kallon yadda hajjan ke maka mata harara,saita maze ta kuma dauke kai kamar batasan abinda ke faruwa ba,tasan idan tayi fushinta ta gaji dole ta sauko,shirye shiryen tafiya wajen gabatar da taron ma saiya janye hankalinta zahran ta sake samun sukuni.
Fitowarta daga wanka sukaji ana kada qaraurawar qofar falon
“Kai wannan abu sam babu hikima a ciki,wai wannan iblishiyar abar ke gaya maka kayi baqo….ke zahra’u…jeki ki duba kiga waye” hijabinta ta zura saman zanin jikinta ta fita falon.
Samuel yaron gidan ne tsaye bakin qofar,gefansa wata matashiya ce wadda a qalla zasuyi sa’anni da zahran,saidai xata iya baiwa zahran shekara uku tazarar shekaru uku kenan a tsakaninsu,fara ce sol,hakanan a kallo daya zaka fahimci ‘yar gayu ce,asalin gayu kuwa,ganin farko xaka fadi halinta na yawan fara’a,donko a yaxun ma fuskarta a washe take da fara’a,har haqorin makan dake bakinta yana bayyana,tayi ado sosai da wani irin lace,takalmi da jaka masu aji gami da mayafi daya dace da shigarta,hannu da wuyanta duka kayan qawa ne na mata,da alama bata wasa da kwalliya
“Madam….matar abokin yallabai ce,yace ayi mata iso” samuel ya fada da gurbatattar hausarsa,saita saki fuska tana matsawa gefe gami da cewa
“Bismillah,ki shigo,su hajjan suna ciki”
“To na gode”ta ambata cikin fara’a tana shigowa,zahran tayi gaba tana biye da ita a baya
“Bismillah….zauna,bari nayi musu magana” ta fada tana nuna mata wajen zama,cikin fara’a ta soma zama tana cewa
“Ok to….amma ba kece amaryar oga haidar ba?” Rasa amsar da zata bata tayi,bai kyautu tayi mata qarya ba tunda batasan matsayinta da kuma zancan da sukayi ba,sa’annan kuma hannu guda bata son amsa sunan matarsa sam,saita gyada kai cikin murmushi
“Eh”
“Ma sha Allah….hala kai ya dauki chargy bai gaya miki zuwa na ba….nazo ne zamu wuce tare daku can wajen taron,tare da yallabai zamu tafi,so kuma an kirasu babu damar su dawo gida su shirya din mu wuce tare,sai yace kawai nazo mu wuce tare daku….ni matar abokinsa ce kuma abokin aikinsa da za’a qara musu girma tare,sunana dr nasreen” dole ta dawo ta zauna cikin fara’a,tunda da alama su din basusan komai kan aurenta da haidar ba,bai kamata kuma ta nuna komai din ba
“Ni sunana zahra…..ya gida ya yara” murmushi ta sakeyi
“Gida lafiya lau,yara kuma tukunna”itama sai tayi murmushi
“To Allah ya kawo masu albarka”
“Amin summa amin na gode” dole ta miqe ta nufi kitchen da kanta,abinda bata gwada ba ko sau daya tunda sukazo gidan.
Tayi mamakin ganin kitchen din,ya hada komai da komai na buqatar girki,ta bude fridge ta debo ruwa da lemo ta hado da tea da aka dafa tun dazun a flask da sauran farfesun kayan ciki ta aje mata,sannan ta wuce ciki kiransu hajja.
Ta fito da kayan akwatinta duka tana duba wadanda zata saka,ranta a bace kawai yake,banda zuwan nasreen da kuma idanun hajja itafa babu inda zata je.
Hayaniya ta fara ji daga falon ta dadu,da kuma muryoyi kamar na ‘yan gidansu,kafin tace wani abu hayaniyar taji ta doso dakin da take,hafsat ce kan gaba dauke da babynta,sai salma a bayanta itama da nata baby boy din da tuni ya soma tafiya sai yusra daga qarshe.
Rungume juna sukayi cike da murna,sosai taji dadin zuwansun,abinda yaso sasu su bata ma tsokanarta da suka fara yi,Allah ya yanke abun ta hanyar shigowar nasreen,wadda hajja tace taje wajensu sai tafi jin dadin zama.
Hira suka shiga yi inda ita kuma ta hau shiryawa cikin wani lace army green da yayi masifar haduwa,dinkin riga da skert daya zauna mata sosai a jiki,tana shiryawa tana sauraren hirar tasu,da alama itama dr nasreen ‘yar hira ce,hakanan bata da wahalar sabo,don kuwa idan ka ganta a lokacin saika tsammaci ta dade da saninsu,cikin qanqanin lokaci suka saba da ita.
Tana gama shiryawa dukka suka rude da zolayarta kan irin kyan data yi,haushi ya cikata ta kasa magana,bugu da qari kuma ma da idanun nasreen dake wajen,wadda ke zaune gefe tana ta murmushi tana kallonsu,yanayin zamantakewarsu da hadin kansu,yadda suke haba haba da juna,da alama akwai saboda shaquwa mai qarfi a tsakaninsu.
Motoci uku masu tsananin kyau da tsari ne suka debesu daga gidan aliyyu haidar zuwa inda za’a gabatar da taron a babbar headquater sojoji dake garin abuja.
Tun daga waje xaka fahimta lallai babban taro ake,abu nasu maganin a kwabesu,ko ina jami’aine dake bawa wajen tsaro da kariya,tako ina komai na tafiya kan tsari,duk abun mutun idan yaga tsari da yanayin wajen sai yaji sun masa kwarjini,lallai soja ba wasa bane,dole ya haidar ya dinga yi mana kwarjini tanaji su salma suna fadin hakan,ita dai nata idanu ba tare da tace komai ba.
Babban wajene budadde wanda aka tanada saboda taro irin wannan,kujeru ne bisa tsari,wajen baqi da manyan baqi daban,wajen zaman sojojin dama wadanda za’a qarawa girma daban.
Suzo akan lokaci ne,hakan ya sanya suka samu waje mai kyau da zasu iya hangen dukkan yadda abubuwan zasu wakana,wanda hafsat ce ta haura ta hango musu ta jasu wajen suka zauna
“Da kyau hafsat,gaskiya kin iya zaben wajen xama,xanga dear da kyau wallahi” cewa dr nasreen tana gyara zaman hand bag dinta tare da gyara zamanta da kyau,wanda zamansu babu wuya wajen ya soma cika da jama’a,aka kuma fara gabatar da ‘yan wasu abubuwan kafin a shiga muhimmin taron.
*_BAYAN SHUDEWAR WASU MINTUNA_*
Mai gabatarwa ne ya amsa abun magana ya tabbatar da wajen ya hau tsari bisa doka da yadda suke gabatar da tarukansu,take wajen ya dauki saiti,kowa ya bada hankalinsa kan abubuwan da aka soma gabatarwa.
An yiwa manyan baqi maraba da zuwa,sai parade na musamman ada aka shirya saboda su,sai da aka fara gudanar da parade din sannan zahra tadan dago daga danna wayar da takeyi ta dubi wajen.
Sai abun ya dauki hankalinta fiye da yadda ta zata,don wannan shine karo na farko da aka fara parade a gabanta,a nutse take binsu da ido,yadda suke komai a nutse sannan kuma a tare,duk wanda yake wajen sai abun ya bashi sha’awa ya kuma qawatar dashi,musamman idan shi din ba ahalin abun bane.
Suna kammalawa wadanda zasu karbi qarin girman suka soma shigowa da daya da daya,kusan inda ta zauna din yana kallon inda aka tanadar musu domin zama,sannan kuma daura da wajen qofa ce,hakan ya bata damar ganin duk wanda zai shigo din.
Mutum na shida ne ya shigo
“Oh god dear…..yau ka canza sosai” taji de nasreen na fada cikin wani irin exciting,tadan kalleta kadan sanda take daga yatsunta,saita maida hankalinta ga wanda ke shigowar,ga mamakinta ya hangi matar tasa,shima kuma yatsunsa yake daga mata a fakaice,sai taji ta aika masa da kisses ya kuma dawo mata da amsa sanda yake samun waje yana zama fuskarsa dauke da wani irin murmushi.
Murmushi tayi itama wanda ya tsaya iya cikin zuciyarta,ko ba’a fada mata ba tasan cewa dr nasreen da mijin nata narkakkun masoya ne,idanu kawai sun isa baka amsa,tana shirin dauke idanun nata daga wajen ta hangi shigowarsa,wanda shigowar tasa tayi dai dai da sakin wani take daya dauki hankalin jama’ar dake wajen.
Taso qaryata idanunta da suka nuna mata yadda shigar kakin dake jikinsa ta amsheshi fiye da duk wani wanda yake sanye da kaki dake wajen,hakanan taso qaryata kanta data hangi zallar kwarjini dake kwance saman daurarriyar fuskarsa da ayau tadan sassauta daga yadda aka santa zuwa matakin daurewa na qasa qasa,batasan kaki na yiwa mutum kyau ba sai a lokacin,saidai ta alaqanta hakan da cewa rashin taba ganinsa cikin shigar da bata taba yiba yasa dukka taga hakan,saita janye qwayar idanunta sanda shi kuma nashi idanun ya sauka a kanta ba tare daya shiryama hakan ba,ya lura da dr nasreen daketa aikawa lieutenant jafar kallo wanda a yanzu xai koma matsayin captain,saiya lumshe idanunsa gami da yin bismillah ya zauna a mazauninsa.
Yanayin yadda taron ke gudana kawai ya isa ya sanyawa mutum nutsuwa da sha’awar ganin dukkan abinda ake gudanarwa a wajen,hakan ya sanya ta jefa wayarta a jaka,ta tattara dukka hankalinta a kan abinda ke wakana.
Hakanan lokaci zuwa lokaci idanunta na sauka a kanshi,kusan tunda ta sanshi bata taba ganin fuskarsa a sake haka ba,duk da ba dariya ko murmushi yake ba,tana jin su salma na gulmarsa,itadai batace komai ba,ganin haka hafsat ta tabo ta
“Wai yau bakiga fuskar sojanki ta saki ba?” Harara ta watsa mata tana dauke idanunta,daidai sanda suka hada idanu,saiya dauke kansa gami da sake daure fuskarsa,yadan juya kadan yana yiwa lieutenant jafar magana qasa qasa.
Bayan gama gabatar da komai,abu na kusa da qarshe daya rage shine saka musu igiyoyi da stars daga commanders dinsu,hakan yasa wajen ya sake nutsuwa kowa ya sanya idanu yaga nashi wanda yazo dominsa.
Daki daki aka dinga bi ana saka musu alamun qarin girmansu,cike da ban sha’awa karramawa da kuma girmamawa kan yadda suka sadaukarwa da qasarsu rai da lafiyarsu.
Aliyyu mas’ud dabo shine mutum na biyar bisa layi,general hamza shine zai saka mishi nashi,ya matso kusa da haidar din,saidai tsahonsa bazai iya kaiwa ba ga haidar din ba,cikin barkwanci yayi maganar a nemo masa abunda zai taka wanda hakan ya baiwa mutane dariya,murmusawa aliyyun yayi ya duqa dai dai yadda hannun general zaikai ya saka masan sannan akaci gaba.
Duka sai da aka gama sanya musu da sauran jawabe jawabe,sannan akayi sanarwa ta musamman akwai mutum biyar a cikinsu da za’a karrama da wasu lambobi masu siffar kwabo da za’a rataya musu,saboda sadaukantaka gaskiya riqon amana da kuma qwazon aiki,bayan wajen ya nutsu aka fara kiran sunayensu,mutum na farko ya isa wajen,saiya nema alfarmar iyalinshi ce zata sanya masa,duk da cewa shekarunsa sun kusa arba’in da wani abu hakan ya burge mutane,cikin nutsuwa ta taso ta rataya masa sannan ta tsaya aka musu hoto ta wuce,hakan ya sanya aka maida rataya abun wuyan ga iyalan sauran,marasa matan aure a ciki kuma mahaifi ko mahaifiya,abun saiya dinga bada qawa da burgewa,saboda kowacce mata in a romantic way take sanyawa mijinta,tana jin yusra na cewa
“Gaskiya ne,ban sake yarda soja akwaishi da son matarshi ba sai yau….jiba don Allah abun sha’awa,sun sadaukar da farincikinsu ga qasarsu…ma sha Allah,Allah ya dafawa sojojinmu”.
Lieutenant jafar wanda a yanzu ya koma captain jafar aka kira,dr nasreen ta damqi hannun zahra cikin farinciki ba tare dama ta sani ba
“Ma sha Allah my happiness….lallai yau ranarmu ce” ta fada tana duban zahra,itama zahra dubanta tayi,tana mamaki cikin ranta wannan wacce irin soyayya ce?wadda bata boyuwa,saita sakarwa dr nasreen murmushi kawai na qarfafa gwiwa,ta gyada kai
“Thanks” ta cewa zahra tana miqewa a nutse ta sauka daga wajen zuwa inda yake tsaye yana jiranta.
Kafin ta qaraso tuni ya miqa mata hannunshi,tana murmushi itama ta isa ta dora hannunta cikin nashi,kamar sun manta da tarin jama’ar dake wajen,ta amsa abun wuyan,tadan rusuna kana ta miqe ta zira masa fuskokinsu dauke da murmushi ta juya tana maqale a kafadarsa aka musu nasu hoton,tana jin salma na fadin
“Wow….matar nan ta hadu wlh”
Sam zahra bata damu ba bata kuma kawo komai ba,don bata tsammaci zuwan sunan Aliyyu ba,sannan tunda daga mama har abba babba na wajen,sun kuma fita cancanta,saidai me?,cikin sakanni sunan aliyyu dabo ya karade abun maganar,wanda kamar qiftawa da bismillah duk sojan daya kasance junior dinsa dake wajen saida suka miqe,sukayi salute nashi sanda yake takowa zuwa inda kowa yake tsaiwa cikin nuna zallar girmamawa,da alama akwai akwai alaqa mai matuqar kyau a tsakaninsu
“Ma sha Allah” ‘yan uwa dake kusa taji suna furtawa,lumshe idanunta tayi tana duban wajen yadda suke tsaye,abun ya qayatar da duk wanda yake wajen
“Get up mrs aliyyu dabo” dr nasreen ta soma fadawa zahra cikin fara’a,yayin da dukka su salma suka waiwayo suka sanya mata ido,kai ta kadawa dr nasreen
“Mama tana nan….haka abba ma”
“Tashi kije inna wuro” ta jiyo muryar mama,wanda sam bata zaci taji ba,saita miqe a hankali tana jin wani nauyi na saukar mata,qafafunta sukayi sanyi kamar ba zata iya tafiya ba,wanda wannan ya qarawa tafiyar tata zama slow,hakan saiya qarawa yanayin takun nata ado,da wani salo na daban mai qayatarwa.
Tunda ta taho ya zuba mata idanu da wani salon kallo,wanda ba lallai kowa ya fahimta ba,saif dake tsaye daga gefansa ya soma masa magana qasa qasa
“Smiling please….,just once” banza yayi dashi,saidai idanunsa yana kanta sanda take ci gaba da takowa,taqi kallon koda saitin inda yake,saidai tana sauraren salma dake bayanta tada n tako mata tana mata magiyar karsu bada ‘yan uwansu.
Sai data fara amsar abun wuyan sannan ta juya zuwa direction din da yake tsaye,saif ne cikin zaquwa yace
“Please zaki….i beg you mana,kaga fuskarka?,don’t behave like…….” Qafarsa yasa ya take gefan qafar saif da qarfi,wanda hakan ya sanyashi yin shuru tare da runtse ido
“Mugu” ya fada yana cije lebe,dai dai lokacin da zahran ta qaraso gaban haidar din,sai a sannan idanunsu suka shiga cikin na juna,kowannensu na iya ganin qwayar idanun dan uwansa kai tsaye…..
23/10/2021, 08:45 – ๐๐ป๐๐ป: 26
Taku biyu ta sakeyi zuwa gabansa,wanda hakan ya qara adadin kusancin dake tsakaninsu,a hankali ta daga hannunta da niyyar zira masa abun,saidai kuma ina,tsahonta bazai taba kaiwa ba,don kanta a dai dai qirjinsa ya tsaya
“Madam kina buqatar qara motsawa kadan,don maigidan naki sadauki ne da gaske tako ina” dukka sai aka sanya dariya,taku daya ta qara ta mannu da jikinsa,qamshin turarukansu suka soma gauraya da juna,gaba daya numfashinta yaso daukewa,sosai bugun zuciyarta ya qaru,ta lumshe idanu tana daga hannunta zuwa saman kansa.
Hucin numfashi taji sosai na sauka saman fuskarta,hakan ya sanya ta bude idanunta,gaba qwayar idanunta ta shige cikin tasa saboda ranqwafowa da yayi da kansa yadda zata samu damar saka masan,saiya lumshe idanunsa gami da budesu lokaci guda still akan fuskarta sanda ta janye nata idanun daga kanshi,karo na farko da yaga abinda mutane suka sha fadi,wanda bai taba gasgatawa ba sai yau,qwayar idanunta irin tasa ce,mai wata irin zaiba da walqiya,har cikin jinin dake zagayawa a jikinsa yake jin yadda tsigar jikinsa na tashi saboda yadda ta mannu sosai da jikinsa sanda take sanya masa abun,saita soma janyewa baya a hankali tana qara tazarar dake tsakaninsu sanda ta gama sanya masa,saidai da baya da baya take takawa tana jin kamar ba zata iya juyawa ba saboda bugun zuciyarta
“Madam….kada dai ki koma,baki gama sakawa sadaukin naki ba,saboda lambobin yabon nashi da saura” taji mc yana fada,tare da qarasowa daura dasu,ta waiwaya tana duban wanda ke miqo mata wani abun shigen irin wancan,saidai bambancin rubutu,hannu biyu tasa ta karba,sannan ta juyo ta dubi haidar dake tsaye,hannunsa saman abunda ta saka masan yanzu,saita sake komawa zuwa inda yaken kamar mai sanda.
Tana isa gabanshi idanuwa suka mata yawa saita fara qoqarin durqushewa a gaban nasa,da hanzari yasa hannu ya dagota,wanda hakan ya sabbaba mata fadawa jikinsa gaba daya,so yake tayi ta gama ta sauka daga wajen,saboda yadda ya fuskanci sunyi calling attention din mutane da yawa,tsintsiyar hannayenta dake riqe da igiyar ya kama,yanajin yadda tsigar jikinsa ta zuba har gefan fuskarsa,saiya ranqwafo kaman dazu,wanda hakan yasa yayiwa fuskarta rumfa fiye da dazun,ya daga hannunta har zuwa wuyansa sannan ya barta ta zura.
Gaba daya jin jikinta take yana rawa,tayi baya kamar daxu zatabar wajen,sai qafafunta suka lanqwashe,ta tafi luu kaman zata fadi,da sauri yakai mata cafka,ya samu nasarar riqo qugunta,ya tsaidata ta tsaya sosai,idanunta a nashi tasa hannunta tadan zame hannunshi daga qugunta da taga kamar baya da niyyar sakinta,sannan ta juya ta soma sauka daga wajen,wanda tuni tafi ya karade wajen,ita kuwa ji take kamar tayi tsuntsuwa ta isa mazauninta,saboda yadda duk inda ta gifta ake binta da idanu,haka duk inda ta gifta sai taji anyi magana akansu qasa qasa
“Beautiful couples”
“Ma sha Allah perfect match”
“Wow ma sha Allah” da dai sauransu,bata iya waiwayawa bare taga wanda ya furta maganar,harta isa mazauninta ta zauna tana fidda ajiyar zuciya me qarfi,tana jin yadda jikinta tacan ciki ya jiqe da gumi
“See love don Allah…..no wonder mata ke macewa murus kan Aliyyu,madam kin musu zarra fa da kikayi wufff dashi,anan wajen naga fuskokin abokan adawa da yawa” caa din dasu salma suka juyo sukayi mata ma yasa bata samu amsa maganar dr nasreen ba,duk da tanajin bata da amsar da zata bata din,sai kawai ta miqe ta soma ratsawa tana fita daga wajen,saboda wani iri da takejin kanta yayi,har yanzu kuma mode dinta bataji ya koma dai dai ba.
Tafiya tayi kadan tabar wajen dake da hayaniyar,gurin akwai qarancin zirga zirga da hayaniyar jama’a sosai,saita samu bayan wata qaramar mota ta hau samanta ta zauna saboda bata da wani tudu sosai motar.
Idanunta ta rufe dukka,ta shaqi iska sosai takai har cikin huhunta sannan ta fesar,a hankali ta soma bita na abinda ya faru yanzu a wajen.
(Ba lallai haka suke gudanar da taron qarin girmansu ba,na tsarashi a hakkane saboda yafi dacewa da abinda zai qayatar dame karatu,ya kuma tafi da salon labarin,ya alaqantu da abinda zaizo a gaba,so pls idan akwai soja ko sojanniya ๐,ko matar soja sai ku karba a hakan๐๐ฝ)
Sam batasan lokaci yaja haka ba tana zaune a wajen,har aka tashi taron,sai a sannan ‘yan gida suka fara neman inda tayi,saidai har suka gaji da neman babu wanda ya ganta,ga kuma wayarta na wajen dr nasreen bare su kirata suji inda tayin,dole wadanda zasu koma a ranar sukayi gaba,su hajja ma daga baya suka bisu,akabar mustapha ya lalubota tunda haidar din ma bai tafi ba
Tare suka jero shida abokin aikin nasa,suna tafe a hankali da alama tattaunawa sukeyi,hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,ya zuwa yanzu babu hula a kanshi,da alama cireta yayi.
A hankali idanunsa ya sauka a kanta,saiya dan zuba mata idanu,yanason tabbatarwa itace,a haka abokin tafiyar tasa ya lura da inda yake kallon,shima sai yabi wajen da kallo
“Lafiya dabo?” Ya tambaya yana dubansa
“Ba komai” ya amsa masa yana dage kafadunsa
“Ina zuwa” ya sake fadi yana nufar inda take din.
Sam batasan da zuwanshi ba,kamar yadda bata tsammaci zuwan nashi ba,kallonta yayi na sakan biyu sannan ya hada yatsunsa ya murza suka bada ษas ษas.
Da sauri ta bude idanun nata,sai ta zubesu saman tashi fuskar,take suka hada ido,sai kowa ya janye tashi qwayar idanun,saita kuma ta soma yuqurin saukowa daga saman motar,a lokacin dashi kuma ya juya baya kamar wanda baison ganin saukowar tata ya zaro waya daga aljihunsa
“Kazo maza ina ta baya” ya fada kawai yana kashe wayar,sannan har ta soma takawa zata bar wajen
“Karki dara ko ina….don idan kika batan da gaske babu wanda zaki kuma wahalarwa” iya abinda ya fada kenan,saita waiwayo ta dubeshi ta watsa masa harara,saidai ta makara,don tuni ya sake juyawa ya bada baya,don haka ta dauke kanta ta samu wata motar daban ta jingina,yayin dashi kuma ya koma wajen abokin aikin nasa da suka taho tare,suka jera har zuwa bakin motar haidar din,ya budeta ya shiga ciki duk da qafafunsa na waje,da alama akwai abinda yake daukowa.
Zamansa ba dadewa ta hangi mustapha ya iso wajen,sai haidar din ya fito,ya miqawa drivernsa key,suka shiga shida mustapha,sannan suka taho da motar inda take tsaye.
Cikin salon barkwanci mustaphan yace
“Sojiya yallabiya…yallabai yace a kaiki gida” ko motsa fuskarta batayi ba bare tayi murmushi,ta taka ta isa gaban motar,ta bude murfin baya ta shiga.
Duk yadda mustapha ya qware wajen tuburata da zolayarta wannan karon baici nasara ba,don bata kulashi ba,wani iri takeji cikin jikinta,mutuwar jiki da muguwar kasala,gaba daya bata marmarin komai sai xaman kadaici,kana kuma ta zauna shuru ba tare da magana da kowa ba,a haka suka qarasa gidan.
Hanyar da motar tabi har yanzu idanunsa suna kai,saida major inusa ya taba kafadarshi sannan ya dauke idanunsa ya maida kansa
“U r lucky dabo….komai naka na zuwa cikin nasara da kyawun yanayi,ka godewa Allah,ka samu muqamin da an jima ba’a samu matashi kamarka daya riqeshi ba,ka fito daga babban family masu sonka da qaunarka,masu tarbiyya da kuma hadin kai,lastly ka auri princess charm,she captured all the people’s……” Kallon da haidar din ya masa yasa bai qarasa ba,saiya cike zantukan bakinsa da murmushi kawai ya waske zancan,shi kam baima san ya masa kallon ba,kawai abinda ya sani major din ya qware sosai wajen bin mata,abinda yasa sam basa shiri ko jituwa shida haidar din,duk da yadda haidar ke sonshi,saboda mutum ne shi da baya jituwa da duk wani wanda ya kaucewa hanya ko yake ba dai dai ba,matuqar bazai gaya masa gaskiya ya yarda ya dauka ba,idan ka gansu tare da major inusa to sabgar aiki ce,saiya soma takawa yabar major din tsaye a wajen yana bin aliyyun da kallo.
“Shegen yaro……kana ganinsa haka kullum idanunsa a qasa kamar bai kallon kowa,amma yasan takun kowa,the worst part dinma….matan da ake gani bai kallo kuma basa gabansa,yayita yarfasu su kuma da shegen nacin son mai kyau da aji suyita binsa,ashe yana qare musu kallo a fakaice,banda haka ina yaga wannan har yayi wuffff da ita….gaskiya yasha kwana yaron nan” major inusa yake fada shi kadai kamar wani zautacce.
A tsaye ta samesu a falo,tana sallama umminta ta fara gani,sam batasan tazo ba,bata kuma bawa ranta zatazo din ba,saboda batajin dadi ance mata kusan sati guda kenan,duk da ita bata gaya mata ba.
Qarasawa tayi ta gaidata,sannan ta dubi salma dake riqe da jakar hajja,tana ta zuba zance ita dasu yasira wadda itama yau tazo din,duk an fito da jakankunan kayansu maman,wani sanyi ya ratsa zuciyarta,itakam dama ta gaji,so take kawai ayi a gama su wuce ko ta samu sa’ida hajja ta sakar mata mara tayi fitsari.
Data wuwwulga idanunta bata ga jakarta ba,sai tabi bayan salma data koma dauko jakar hannun hajja,ta isketa tana neman jakar a inda hajjan tace mata tana nan
“Don wulaqanci a dauki jakar kowa amma banda tawa,saboda ni bani da gata da galihu?”
“Ai an debi kayan da za’a koma miki dasu,an kawo miki wasu” duban salman tayi sanda take zuge zip din jakar
“Kamar yaya?”girarta ta daga
“Eh to….bari na tsegunta miki,kamar naji hajja tana fadin anan ke za’a barki,zaku taho tare da ya haidar ko?”
“Kambun bala’i!…..ni!,wallahi bazan zauna ba,tabdijan,ai itama hajjan ba haka mukayi da ita ba” ta fada tana jin wani tashin hankali yana ratsata,dafata salma tayi tana boye dariyarta
“Easy mana zuhra.”
“Anqi easy din…..naga alama hajja wani abu daban takemin ba so ba,in banda haka ta yaya zata ce na zauna da wannan mutumin a cikin gidansa?,ya kasheni kenan akai musu gawata ko?,dama haka takeso”.
“eh haka nakeso don ฦaniyarki….indai wannan shine rashin son to bana qaunarki fadi ki qara fada,ke salma tsaiwar me kikeyi ke kuma daga daukomi jaka?,miqomin driver yazo,ko mu wuce mu barki anan ki tayata zama” wani zillo salma tayi sai gata kusa da hajjan tana cewa
“Rufamin asiri kada ya zaki ya cillani ta window nayi kwanan qofar gida,a jawa yarona da mijina asara” kuka zahra ta saki harda dora hannu aka
“To wallahi nima bazan zauna ba,kowa tsoronsa yake amma haka kawai ni an hadani dashi?,saboda niba mutum bace?,idan ma cinyeni zaiyi ya cinyeni?”
“Eh haka nake nufi don gidanku,ja’irar yarinya” hajja ta sake cewa tana qwalalowa zahra idanu gamida tamke fuskarta kaman bada xahra’un tata take magana ba
“Wuce muje” ta fada tana nunawa salma hanya,tuni salman tayi gaba,tana danne dariyar dake taso mata,ita ta tseguntawa hajja cewa gobe zasuyi liyafar cin abincin dare dukka wadanda aka qarawa girma,kuma kowa da matarsa yake zuwa,idan ma akwai yara harda su,nan take hajjan tace dole haidar dinta shima asan ya zama babban mutum,dama a wajen taga idanun wata qabila yana haka haka akan jikan nata,duk inda yayi tana binsa da wani kallon yaudara na banza da wofi,tota Allah ba tataba,ba qaramin dariya akaci a motar ba da wannan ruษu da hajjan ta hada ba,tuni itama hajja tabi bayanta,ai kuwa itama zahran saita kwashi jakarta ta rufawa hajjan baya.
Kacibus sukayi da umminta wadda ta sake shigowa ta rage mararta kada fitsari ya dameta a mota,duk sai suka ja baya,ta dubi ummin itama ummin ta dubeta,kallon da tayi mata shi ya sanyayar mata da jiki,saita tsugunna saman jakartata a wajen,ita kuma ummin ta wuce ciki abinta.
Batafi minti biyu ba ta fito,a lokacin zahran ta dawo bakin qofa ta tsuguna kamar me neman gafara ko taimako
“Kiyi duk yadda zakiyi,kiyi duk qoqarin da zakiyi ki nunawa duniya ban baki tarbiyya ba,ki nunawa duniya na sama dake basu isa dake ba,nayi imanin kaf fadin duniya idan na mutu kika laluba daga farko zuwa qarshe baki da masoyiya kamar hajja har abada,hakanan ko yanzu na mutu zan kwanta cikin kabarina hankalina kwance game da aurenki,don nasan ba zaki tozarta a hannun haidar ba,bazai taba wulaqantaki ba,ba hannun gama garin mutum kike ba,shi din na musamman ne wanda yasan da daraja da mutuncin dan adam,wanda ya kulaa ya kuma girmama rayuwar mahaifiyarki,ruwanki kiga girma da mutucinsa saboda haka,ruwanki kisa qafa ki shure…..zakiga kamar ba’a sonki,tako ina an matsa miki…..soyayya ta gaskiya itace ka tsaya tsayin daka wajen ganin naka ya gyaru kafin kowa,sannan matsalar zamantakewa a hausance sunan mace ke fara fitowa kafin na da namiji….baki da hurumin yankewa haidar hukunci sabida tsohon tunaninki na ba *ALฦIBLARKU* daya ba,akwai banbancin ra’ayi tsakaninku ko?,wannan rusashshiyar hujja ce…..a yanzu ina miki magana da harshen uwa zuwa ga diyarta……ki nutsu ki fara dora komai kan muhallinsa da saitinsa…..sai angwada ake sanin na qwarai” daga haka ummin tayi gaba abinta ba tare data waiwayo ba,ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta,ita kadai tasan wanne fata ke gareta,ita kadai tasan adadin sau nawa tana hana idanunta bacci don ingantar rayuwar yaranta.
Da qyar ta tashi daga wajen ba tare data dauke jakarta data janyo wajen ba,a hankali tana jin yadda hayaniya da surutunsu keyin nesa da gidan,da alamu ficewa sukeyi,da qyar takai kanta bakin katifar ta zube,duka zantukan ummin nata sun tsaye mata kamar qusa a qahon zuci,hakanan sun kashe mata duk wani qwari na jikinta.
23/10/2021, 08:46 – ๐๐ป๐๐ป: 27
Tsahon awa guda gidan ya dauki shuru,duk da lokaci zuwa lokaci tana dan jiyo motsi da maganganu sama sama daga falo zuwa kitchen,wanda ta tabbatar da ma’aikata ne.
Tun azahar take kwance bayan ta gama hawayenta son ranta ta godewa Allah,kota kan abinci bata biba,duk da karin safe ne kawai a cikinta,abu daya ke tada ita shine sallah,sai ruwa kawai data ke sha wanda shima cikin dakin yake jiya da dare suka shigo dashi basu shanye ba,haka ta dinga juyi ita kadai,har zuwa lokacin da duhun magarib ya sako kai,aka fara qwala kiran sallahr magariba,saita miqe tana jin yadda tsakiyar cikinta ya qulle,da alamu ulcer dinta tana son tashi kenan idan batayi wasa ba,hakan ya sanya sai data fara fitowa parlour ta bude fridge ta dauki fresh milk mai sanyi babban gora daya tana duban yadda falon ya koma fes,ko ina ษas ษas dashi yana fidda qamshi,kamar ba’a taba yin baqi ba,ba abinda ke fita sai wani samfurin qamshin freshner na musamman,ga abinci a jere a cikin tsari saman dining table,saita dauke kanta ta koma daki,ta zauna ta zuqe madarar tas sannan ta shiga bandaki,tana fitsari taji gefan mararta na qullewa
“Ya salam” ta fada,alamun period na iya zuwa anytime kenan,haka ta daura alwalarta ta dawo dakin ta tayar da sallar.
*Aliyyu Haidar*
Sosai yayi relax a bayan motar bayan ya aje hularsa a gefe yana furzar da iska daga bakinsa,yana jin yadda sanyin ac ke ratsashi tare da qara haifar masa da kasala da kuma tayar masa da gajiyarsa ta zirga zirgar wunin yau.
Zuciyarsa da qwaqwalwarsa tayi nisa wajen tuna abubuwan da suka faru yau wayarsa dake aje tare da hularsa ta dauki tsuwwa,dan qaramin tsaki yaja,ba kasafai ya fiya son kira ba,saidai yau yasha kiran har ya gode Allah,a hakama don yana kashewa ne baya amsa wani.
Ganin sunan me kiran yasa ba shiri yakai hannu ya dauka,labbansa suka motsa cikin ransa ya furta
“Rigimammiyar tsohuwa” saiya kara a kunnensa
“Badai har kunje gida ba?”
“Harma mun huta yanzu haka?”
“Ma sha Allah,sannunku da qoqari,Allah ya qara girma da nisan kwana me amfani”
“Amin ya rabbi…amin Aliyyu,Allah yayiwa rayuwa albarka”
“Amin hajja”
“Yauwa…..dama na kiraka ne na gaya maka,nabar amanar jikata a gidanka” fuska yadan yamutse yana son ya fahimci maganar tata,kamar kuwa tasan tunanin da yakeyi tace
“Matarka zahra….zaku taho tare idan ka gama abinda kake….”
“Amma hajja….bamuyi maganar ba….sannan ma kuma karatunta fa?”
“Kai da ita ku kukasan wani karatu…..,jan kunne na kiraka nayi maka,aronta na baka,bance kuma atabamin ita tun yanzu ba ehe” tun kafin takai ga kashe wayar shiya kashe,saiya jefata gefe yana dafe kansa,hajjan ta soma wuce tunaninsa,tunda harta fara masa manya manyan maganganu irin wannan,banda abinta ma shi da bashi ya nemi a barta ba su suka barta don raษin kansu har tazo da wannan maganar,shikam wannan sabgar gada dayanta akwai qwara a cikinta.
Da ire iren wannan tunanin daya ci gaba dayi har suka isa gidan,ya fita yabar drivern yana kulle motar,yayi cikin gida,ma’aikatan dake harabar gidan suna masa sannu da dawowa.
A yanayi na gajiya yake nufar dakinsa yana observing na falon,komai fes kamar yadda yakeso,don babu abinda yafi tsana irin qazanta kaf rayuwarshi,shi yasa har yanzu ba abincin kowa yake ci ba,hakanan ba kowa yake bawa wankinsa ba.
Bandaki kawai ya wuce direct ya kunna water heater,saida ruwan ya tafasa ta kashe kanta sannan ya daidaita na zafi dana sanyi yadda zai masa dai dai da wankansa,kana ya shiga qasan ruwan ya soma sauka tun daga kansa yana tafiya da gajiya da kasalar data ma jikinsa qawanya,saiya rufe idanunsa yana tuna irin tarin baiwa da Allah ya masa,musamman a yau din,a hankali can qasan maqoshinsa ya dinga furta
“Alhamdulillah…Alhamdulillah”.
Ya kusa minti talatin yana sakarwa jikinsa ruwan dumin sannan ya cuda sabulun wanka ya dauraye ya hada da alwala ya fito.
Sai daya tsane jikinsa da towel sannan ya nemi doguwar riga me gajeran hannu ya sakakkiya ya saka,ya feshe jikinsa da turaruka bayan ya taje kansa,sannan ya koma ya zauna saman kujerar dake dakin ya dauki wayarsa ya soma laluben ‘yan gidansu,yanason yi musu ban gajiya,don wayar yakeson ya kashe gaba daya,don idan ya kwanta ya tabbatar salla ce kawai zata tasheshi,saboda yadda yake jin jikinsa.
Abban tsakiya ya fara kira,sannan abba yusuf,abbansa ne daga qarshe sai ya kira ummi,tata number bata shiga ba,don haka ya kira umma sa’annan ya kira mamanshi.
Tana hannun nurain a sannan,da hanzari ya nufi dakin maman yakai mata,don yasan zaiji babu dadi idan yayi gigin daga kiran ya haidar din,tunda yasan bashi yake nema ba.
A ladabce ya gaidata ya mata sannu da hanya,ta amsa masa sannan addu’a ta biyo baya,cikin farincikin dake ratsawa har cikin zuciyarsa yake amsa mata,sai kuma tayi kiran sunanshi
“Don Allah ka kula musu da amanar yarinya da aka bar maka,kada kayi wani abu da xai zamana ka watsamin qasa a ido,ka kuma barar da tarbiyyar da muka baka,a qarshe kuma ka qaryata soyayyar da hajja ke maka”
“In sha Allah mama zan kula….in sha Allah” daga haka sukayi sallama ya aje wayar yana sakin ajiyar zuciya yana shafa kanshi da hannunsa guda.
Tsahon wasu mintuna yana a haka ba tare da yasan me yake tunani ba,saiya miqe ya zura slippers dinsa ya fito falon.
Dining ya isa,ya zauna ya fara zuba black tea ya dumana cikinsa,sannan ya duba abubuwan da aka dafa din,ya zuba iya yadda zai iyaci ya koma saman kujerun falo ya zauna acan ya fara ci yana yi yana duba saqonnin da suka shigo masa waya yana maida amsa tsahon wani lokaci.
Dai dai lokacin da yunwa sosai ta dinga sakadar zahran,ta dinga juyi tana jin yadda ulcer dinta ta fara motsawa harta fara sanya mata ciwo tsakiyar cikinta,saita koma rub da ciki ta kwanta qwalla na sauko mata,ita koma meye ya faru hajja ce sila,ita ta jawo mata komai.
Qarfe hudu na dare ya farka kamar yadda ya saba tashi duk dare,wansa baya komawa daga sannan kuma sai bayan sallar asuba,a nutse ya miqe ya shiga bandaki ya dauro alwala,saiya janyo wayarsa zai duba lokaci,saboda dakin ba’a sanya mishi agogo ba tukunna,don gaba daya cikin kwanaki biyu aka zuba dukka furniture din gidan qarqashin jagorancin wani kamfani,duk da ya kashe kudo sosai shi kansa ya sani,amma yadda suka tsaran gidan da kaya masu kyau da inganci kadai ya isa ya gaya maka sunsan aikinsu.
SMS ya gani wanda da alama tun daren jiya ya shigo,dannawa yayi ya bude saqon,daga ummi ne,saiya zauna saman abun sallar tashi sannan yabude saqon ya fara dubawa.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya,a rayuwa bayaga mahaifiyarsa da hajja itace mace ta uku da yake ganin kima da darajarta fiye da kowa,saiya sauke ajiyar zuciya yana tuna cewa akwai jininta cikin gidan,wanda karon farko sun kwana sun tashi qarqashin rufin gini guda,tana kuma amsa sunan matarsa.
Ko ba komai,ko yaya tana buqatar yayi mata kara a rayuwa,koda komai bazaije ko ina ba,koda komai taqaitacce ne,amma ta cancanci ya nuna mata wannan karar.
Maganganun mama ya tuna datayi masa su awanni kadan da suka shude,kowa muhimmanci yake bawa zancan,kowa kulawa yake bawa yarinyar why?,saiya aje wayar tasa ya tada sallarsa,yana sallamewa ana tayar da iqama,don haka ya dauki abun sallah a gurguje ya fice,duk da yaso tsaiwa ya tadata kafin ya wuce din.
Saboda ita bai jima a masallacin ba,ana idar da sallar yayi addu’o’insa da basu wuce minti goma ba yafita a masallacin.
Sai da ya tsaya ya kunna dukka fitilun falon sannan ya dinga takawa a hankali ya nufi inda dakunan baccin nasu yake.
A hankali ya dora hannunsa kan handle din qofar sannan ya tura ta a hankali,dunษum dakin yake babu haske,hakan ya sanya baka iya ganin komai a dakin,saiya sanya qafarsa ciki,ya miqa hannunsa side din da makunnin qwan lantarkin dakin yake ya kunna,take haske ya gauraye ko ina tarwai.
Tsakiyar katifar ya hangota cikin kwanciyar rub da ciki,gashin kanta mai tsayi da santsi na asalin fulani data gada daga wajen umminta yayi ษai ษai saman filon saboda ciwon qirjin daya matsata ta cire ribbom din data daure gashin.
A hankali ba tare daya shurya ba idanunsa suka sauka kan sumar tata da kallo,wanda duk da gida daya suka taso zai iya cewa bai taba ganinta ba sai yau,saboda tunda can zahran ma’abociyar zama da dankwali ce ko hula,cikin biyu baka rasata da daya,ummi ta riga data sabar mata da hakan,koda za’a kamata da kowanne laifi ayi mata hukunci banda na zama babu dankwali,baya ga haka ma duk sunsan halinsa,kada ki sake ya sameki babu dankwali akanki.
Doguwar rigar baccin jiya ce a jikinta,saisai ta tattare dukka qaurinta a waje yake,da yake armless ce kana iya ganin dantsen hannunta wanda hannun nata guda daya ta sanyashi qasan fuskarta,dayan kuma tayi baya dashi,ya lanqwashe sosai,duk yadda akayi bacci ya dauketa a hakanne bata shirya ba,saiya janye idanunsa da sauri,yayi one step back da niyyar ficewa,saidai ya a matsayinsa na soja ya tabbatar yadda ta kwanta din idan ta tashi xata iya wahala,don haka saiya sake turo qofar ya dawo cikin dakin,ya taka a hankali har zuwa bakin katifar.
Har yakai hannunsa zai tattare mata gashin kanta,saiya janye hannun da sauri ya maidasu baya kamar wanda aka sawa shocking,tsahon second biyar sannan ya sake kai hannunsa.
Cak ya dagata da niyyar ya juyata gaba daya ya canza mata position na kwanciya,ya manta cewa bacci take,cikin baccin taji kamar tana tashi sama,hakan ya sanyata razana ba kadan ba,take kuma baccin ya yanke,saidai kafin takai ga bude idanunta qwaqwalwarta ta aike mata da saqon dagata akayi,cikin tsananin razana ta dunqule cikin jikinsa gaba daya tana sakin qara,qarar data gigitashi,saboda bai taba kawowa ranshi zata iya farkawa ba,gigitashin da tayi da qarar data qwalla da yadda ta dinga qoqarin zillewa daga hannunsa,don har ga Allah ta manta a duniyar da take,bakuma ta gane waye ba yasa gaba daya suka zube saman katifar ita dashi,don idan ya saketa ta fadi ita kadai duk da saman katifa ne yasan dole taji zafi……
23/10/2021, 08:46 – ๐๐ป๐๐ป: 28
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
________________________________
Gaba daya ya danne fiye da rabin jikinta,da sauri cikin cool voice dinsa yake fadin
“Calm down….calm down” saidai ina kunnuwanta ma basu iya jin me yake fada ba,burinta kawai tama ture koma wanene,ganin ta kasa gane me yake fadi,saiya sa hannunsa guda daya ya kama habarta ya riqe,cikin daga murya ya sake fadin
“Wakeup mana…nine fa,ke….ke!” Sai a sannan ta dauki muryarsa,gabanta yayi wani mummunan faduwa,saita tsaya cak da ihun data soma,yayin daya tsaya shi kuma yana kallon fuskarta na wasu sakanni,ganin ta tsaya yasa ya zare jikinsa a hankali ya miqe tsaye,har yanzu bata bude idanun nata ba,saidai ta mirgina daya side din ta yadda zata juya masa baya,tana jin yadda bugun zuciyarta ya dadu,hakanan qirjinta ya qara riqewa,tana fidda numfashi a hankali
“Ki tashi kiyi sallah” ya furta yana ficewa daga dakin.
Sai data tabbatar ya fita sannan ta miqe a hankali ta zauna,jikinta tabi da kallo,wani haushi ya kamata,yanzu a haka ya shigo ya ganta?,mema ya kawoshi dakinta?,sai taja tsaki ta miqe a hankali saboda yadda ciwon qirjin nata ke dada qaruwa,a dudduqe ta nufi bandaki.
Hancinta ta ringa budawa tana jin yadda qamshin turarensa ya kama jikinta adan shigarsa dakin,babu niyyar wanka a tare da ita,amma tasan cewa dole ta rabu da rigar,idan ba haka ba ba zata daina jin qamshin turaren ba,hakan yasa ta fidda rigar ta hada ruwan wanka tashiga.
Yana fidda kayan jikinsa zuwa na motsa jiki yana jan tsaki kadan kadan,tunanin yaqi barin ransa,me yasa bai qyaleta ta fadin ba?,da ba zata qara irin wannan kwanciyar ba,me yasa ma ya damu saiya gyara mata kwanciyar?,haka nan ya gama shiryawa cikin riga armless da wando iya gwiwa,wanda hakan ya sake fidda qirar jikinsa ta qaqqarfan namiji,da sassarfa ya fita daga dakin,yabi ta falo ya bude wata qaramar qofa data sadashi da dakin motsa jikin.
Babban daki na gym wanda ya hada duk wani nau’in qarafa da na’urori,kai tsaye ya haye saman daya daga cikin kayan motsa jikin,yanayi yana sauraren labaran duniya daga babbar tv din dake manne a dakin,daga wancan channel din idan sun gama ya juya zuwa wata,a haka sai daya shafe kusan awa daya da rabi sannan ya sauko ya ciro daya daga cikin towel dake rataye a dakin ya soma goge gumin jikinsa yana zama kan wata cushion chair dake dakin,sai daya huce sosai sannan ya dauki ruwa ya soma sha,yana duba wayarsa da bai jima da kunnata ba.
Minti goma sha biyar a haka sannan ya fito daga dakin,zuwa sannan ya tadda falon fes dashi,daidai lokacin kukunsa dake dauke da warmers guda biyu a hannunsa da alamu girkin safe yake hadawa ya fito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa ya zube yana gaidashi,ya amsa mishi yana yin gaba,sai kuma ya dakata ya dawo da baya yana dan wani nazari,yana ganin ya kamata ya dakatar da williams da Andrew,ya cansu da mata,duk da cewa shi din yafi jin dadin aikin mazan
“Williams” ya kirashi
“Yes sir” ya fada da sauri yana aje kwanukan hannunsa saman table din,sannan ya garzayo da sauri ya zube a gaban haidar din
“Inason na dan baka hutu na wata daya,ba don ka yimin wani abu ba,bayan wata dayan zanyi magana dakai saika dawo,ka jirani na shirya idan na fito zan baka abinda zaka riqe na wata gudan kai da andrew” sosai hankalin William ya tashi,don kowa fadi yake yayi sa’ar gidan aiki,ya kuma yi sa’ar uban gida mai kyauta da tausayi
“Sir….ina fata dai ba wata matsala bace?” Hannunsa ya kada
“Eh….kada ka damu,zaka dawo bayan wani lokaci”
“To na gode mai gida” ya fada cikin nuna girmamawa,yanajin dadi daya kasance ba wani abu ya aikata ba da zai rabashi da gidan,daga haka aliyyun ya wuce shi kuma ya kama wajen dining din yaci gaba da gyarawa.
A hankali ta shirya cikin atamfa riga da skert da suka zauna sosai a jikinta,don bata da wata tufa data wuce atamfar,saboda tafi sonta sosai,gashinta ta gyara saita ware dankwalinta kawai ta yafa,tana jin yadda hanjin cikinta ke nade waje daya,dole tana buqatar abinci,sannan charging wayarta yayi low,tana da buqatar jona chargy,hakan ya sanyata dole fitowa falon.
Chargyn ta jona sannan ta nufi saman dining din,taja kujera daya ta zauna,ita kam gaba daya takaicin yadda namiji ke shiga kitchen godai godai da sunan kuku yayi girki take,namijin ma kafiri,dyk tsantsamin ya haidar din ya tashi a banza kenan take rayawa aranta,yanzun ma banda mahaukaciyar yunwar da take ji da kanta zata shiga kitchen din tadan dafa wani abu,sai ta janyo ruwan zafi ta hada tea kawai ta soma kurba,lokaci lokaci tana tunanin gida da abinda sukeyi yanzu,wani sashe na zuciyarta kuma tunanin makaranta takeyi.
Tunanin da take ne yasa bataji tahowarsa ba,sai qamshin turarensa daya cika mata hanci,hakanne ya ankarar da ita ta daga kanta,ashe tsaye yake a wajen yana buda kwanukan gami da duba abunda aka dafa din.
Sanye yake da wata fara qal din shirt cotton mai gajeran hannu,sai wando three quarter shima fari tas dashi,hakama slipper din qafarsa,duk wanda yasanshi ya sanshi dason farar tufa tun asali,saita ajjiye cup din hannunta tana fadin
“Ina kwana?” Ba yabo ba fallasa ya amsa,saidai bai dubeta ba,kana yaja kujera ya zauna ya fara kurban tea din shima.
Zata bar wajen yana duba uban saqonnin taya murna da suka cika mishi waya,yana amsa wasu wasu kuma ya wuce,don yawan saqonnin da ‘yammatan sukayi mishi ma yasa sa yaga alamun mace bai budewa saiya wuce gaba
“Ki zauna ki rubuta duk abunda zaki iya buqata” ya fada a taqaice,saita amsa tana yin gaba,ta qarasa wajen wayarta zata dauka,dai dai sannan Williams ya buda qofar kitchen din zai fito,haidar dake cin chips ya kalli qofar ya maida idanunsa ga farantinsa,sannan yace masa ya koma ya fita ta baya,ya jirashi a waje zai sameshi a can,a ladabce ya amsa ya maida qofar ya rufe din.
Tana cire wayar saiga kira ya shigo,dr nasreen ce wadda tun a jiya sukayi musayar numbers na juna,sai taji taji dadin kiran nata,don haka ta wuce da a hannunta zuwa daki.
Sai data shiga ta samu waje ta zauna sannan ta daga
“Mrs dabo….an tashi lpy” murmushi zahra tayi,yanayin faran faran dinta kamar na hindatu,saidai nata maturely yake kamar yadda take nutsatstsiya tun daga fuska
“Lafiya lau amaryar jafar” dariya tadan saki
“Amarci ai mun bar muku,muda muka kwan biyu” sosai suka gaisa a sake kamar wasu tsaffin qawaye,sai tace da ita
“Ya shirye shiryen anjima kuma?,kin ganni a wajen gyaran kai,kantin wata babbar makeup artist ce,nace ko a nan za’a mana makeup na anjima iyi mana booking?,sai su biyo su daukemu daga nan mu wuce ko?” Idanu zahran ta waro waje,danqari!…..yo ita aita manta ma da wani zancan dinner ta anjima,baya ga haka ma ina ita ina saka kanta inda Allah bai kaita ba,shi kansa uban gayyar bata ga fuska ko alama ba bare ma aje ga batun zuwa makeup,waya aiketa bare yaga ta dade?,Allah ya taimaketa take qaryan da zatayi ta qwaci kanta ba tare da dr nasreen din ta fuskanci komai ba yazo mata,saita karyar da murya
“Ayyah….zanso hakan,amma kinsan halinshi fa,banjin anjiman nan zai yarda naje”
“A’ah….ya zai min haka,amma da bai kyauta min ba oga haidar,kuma ai ya sani mr and mrs ne…..let me call jafar ya masa magana ya barki…” Tana qoqarin tsaidata tuni har ta katse wayar,saita bita da sauri saidai an shaida mata busy,hakan ya tabbatar mata harta kira din.
Wayar ta aje ta dora hannu saman ka
“Innalillahi” ta fada jimantawa kanta,saita damu gaba daya,ta kuma zauna zaman jiran jin abinda zai biyo baya.
Minti biyar minti goma ashirin talatin awa daya biyu uku shuru dr nasreen bata kira tace komai ba,hakan sai yasa hankalinta ya kwanta taci gaba da sabgarta cikin dakin.
Cikin awa ta hudu taji ana knocking a qofar falon,saita share saboda tana tsammanin yana cikin gidan,jin knocking din na sake daduwa saita aje wayarta ta miqe.
Shuru falon babu kowa,saman table dinma babu komai duka an kwashe,dauke idonta tayi ta isa qofar ta bude,macace a tsaye sanye da uniform na sojoji,fara ce ‘yar tsamurmura mai qaramin jiki,gefanta wata ce sanye da kayan gida,saidai ita waccan din tana da garin jiki,cikin fara’a suka soma gaidata,ta amsa musu fuska a sake sannan suka fara mata bayani
“Oga ne ya aikomu,za’a shigar da kaya,sannan kuma idan kin shirya zamu kaiki” matsawa tayi suka fara shiga da kayan abincine dasu lemuka da drinks,saidai kuma bata gane idan ta shirya ba,don haka ta jawo wayarta saiga kiran dr nasreen
“Dear yace zakizo….amma fa ki hanzarta,wata takewa,daga ita saimu”
“Ok to” ta fada badon ranta yaso ba,dondai kawai bataso tayi wani abu dazai fallasa abinda ke tsakaninsu ne da haidar din,sannan bugu da qari idan ta fitan ko banza taga gari,ta huta da wannan zaman kurkukun data wuni yi.
Daya daga cikinsu ce ta bude mata bayan lafiyayyar motar ta shiga,sannan suma suka shiga suka tada motar suka fice,mai gadi yaja qofar ya rufe.
Babban gurine wanda kana kallonsa kasan ya tattara mata masu aji da wayewa,tana shiga masu karbar custumers suka tareta,ta tambaya inda dr din take suka mata jagora.
“Oyoyo….kinyi sauri amma” dr nasreen din ta fada cikin fara’ar nan tata,sai zahran itama tayi murmushi tana zama inda ta matsa matan suka shiga hira kafin azo kansu.
Dr nasreen din tace a fara yiwa,tana ta addu’ar Allah yasa lokaci ya qure kafin azo a kanta,don har ga Allah bata so,saidai addu’ar tata bata ci ba,nan da nan aka gama yiwa dr din akazo kanta
“Lite makeup pls sis” ta fadawa me yi mata kwalliya
“Ok” tace tana gyada kai.
Cikin qalilan din mintuna saiga zahran kamar an sauyata da wata ne,bakin dr nasreen yaqi rufuwa,cewa take
“Kefa kada ki bada ‘yan maza yau,wallahi kada kisa oga haidar yayi abun kunya gaba mutane,kinganki kuwa?” Murmushi kawai tayi bayan ta kalli fuskar tata a mudubi itama,tana sake dubawa nasreen din ta aje mata wata leda gabanta
“Ga kayanmu da xamu saka…..tunda ba’a gayyacemu biki ba da dear yacemin sun hadu dasu hajja tace masa kinzo na tanadar mana don mu saka iri daya….”
“Kai kai,duka dai dr?”
“Haba babu komai,mu saka sai suyi mana dauri,don naga tex din dear yace suna hanya” tayi maganar tana ware zaninta.
Wani irin lace ne mai azabar kyau da daukar idanu butter colour,dinkin da aka masa yayi masifar dacewa dashi,hakanan zahran kamar don ita aka dinka shi,kamar yadda ya zaunawa dr nasreen din sosai itama,sai duka kallo ya koma kansu sanda aka gamawa nasreen dauri aka fara yiwa zahra nata.
23/10/2021, 08:46 – ๐๐ป๐๐ป: 29
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโi yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koโina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โdai_
_______________________________
Dai dai sanda aka gama kira ya shigo wayar dr nasreen,ta dauka da hanzari
“An gama dear….gamu nan” saita sauke wayar tana duban zahra
“Ke….oganki ya matsu….yanata mita,muje” duk yadda zahra taso dr nasreen ta barta ta biya kudin kwalliyar qememe taqiya,haka ta biya sannan suka dauka kayansu suka fito.
Yaja saki gami da kallon agogon hannunsa yafi a qirga,idan banda kada jafar yaga kamar ya watsa masa qasa a idanu baiga abinda xai dakatar dashi xaman jira ba,shi totally ma bai shirya zuwa wajen dinner din ba gaba daya,hakanan yakejin baison yadda matansu ke karakaina a tsakiyarsu,sai yakega sam hakan bai dace ba.
Karo na qarshe daya kalla agogonsa,ya yanke ma ransa indai basu fito ba zaiyi tafiyarsa ne,saidai shi jafar din da ya daurewa qaryar zuwan qarqashi ya daukosu,ya daga kai da niyyar duban bakin qofar,saiya hangi fitowarsu sun jero a tare,dauke idanusa yayi daga kan dr nasreen ya maida kanta,murmushi ne kwance saman fuskarta,har fararen haqoranta na bayyana,da alama wata magana dr nasreen din ta fada data bata dariya.
Janye idanunsa yayi ya maida daya side din,har cikin zuciyarsa yaji inda ya maida din baiyi masa ba,ya sake canza waje,nan ma yaji baiyi masa ba,saiya dauke idonsa ya kuma maidawa inda suke tahowar.
Zuwa yanzu sun iso dab da motocin,kana iya ganin fuskokinsu tarwai ta hasken fararen qawayen da suka haske wajen,haka kawai ya samu kansa da xubawa fuskarta idanu,wane sashe na ranshi yaji yana baci ba tare da yasan dalili ba,saiya dauke idanunsa daga wajen,yama rufesu gaba daya sanda take qoqarin bude gidan baya ta shigo.
A tunaninta yana gaba,sai data shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe sannan ta lura dashi,duba daya tayi masa ta kauda kai,kamar mai bacci,saidai kuma yanajin komai,fuskarsa kamar ko yaushe a hade dai,tabe baki tayi cikin ra ta tana mita,tana kallo motarsu dr nasreen ta wuce gaban tasu kadan,sai suma suka tsaya,dai dai sannan wayarsa dake aje tsakiyarsu ta dauki kuwwa.
Bai buda idanun nasa badai still ya laluba hannunsa ya dauka ya kara a kunne,murya can qasa taji yace
“Kuje kawai” sai kuma yayi shuru yana saurare na sakannin da basu wuce biyar ba sannan ya kuma magana
“Banjin zamu iya zuwa” still dai wayar tashi tana kunnensa na wasu sakanni,da alama akwai abinda ake gaya masa,saiya sauke wayar,ya bude idanunshin kana ya shiga ya rubuta gajeran sms ya tura sannan ya maida wayar inda take,shi kuma ya gyara zamanshi,kamar wanda dama can ya shiryawa zaman cikin motar ne.
A qalla sun kusa minti goma a tsaye anata kira yaqi dagawa,yayin da zaman ya ginshi zahra,ji take kamar ta fita a motar ta bashi waje,don batasan ma’anar zaman ba,shi bai bada umarni a tafi ba,shi bai maidasu gida ba,a haka ta hangi fitowar jafar ya doso motarsu.
Knocking din glass din side din haidar yayi,saiya sauke glass din yana dubansa,hannayensa ya hade waje daya yana murmushi
“Am sorry boss,we apologize you…..madam ma tace a baka haquri a madadinta” bakinsa ya bude zaiyi magana jafar din yayi saurin tararsa
“I know….i know…ka share kawai,yau ne fa,just some few hours an gama an wuce wajen” bai sake cewa komai din ba,saiya dage glass din kawai,jafar din ya koma motarshi,shi kuma ya bawa drivern umarnin jansu,zahra na gefe tana gulma ita da zuciyarta
“Me shegen baqar zuciya…kome akayi masa oho,ni dama ya fasa zuwan ai gaba ta kaini,mtsewewww” tsakinta na qarshe ya fito fili ba tare data sani ba,saiya waiwaya ya dubeta,suna hada ido kowa yayi saurin janye qwayar idanunsa,ta tsammaci zaice wani abu ko zai tanka,saidai babu abinda yace,haka suka ci gaba da zaman kurame har suka isa wajen taron.
Kowacce na fitowa daga mota ta nufi ‘yar uwarta,tun kafin ta qaraso taga nasreen na danne dariyarta,saida tazo gab da ita qasa qasa tace
“Allah ya somu,da tuni muna gida yanzun,ashe kishin ‘yan maza ne ya motsa,to da heavy makeup akayi miki kenan zuciya zai hadiya?,wannan kwalliyar da ba wani abu aka qara miki ba sosai,abar da aka yita sama sama,lallai sai yanzu na sake gane aliyyu,yana da abun ban mamaki” jin zancan zahra tayi wani banbarakwai,dama abinda ya tsaidasu kenan?,lallai nasreen batasan waye ya haidar din ba,ba wani kishi,kishi a ina?,zallar iya mugunta ce kawai irin tashi data motsa,amma a sarari sai kawai tabi dr da murmushi.
To tunda suka je mazan nasu basu wani zauna ba,sunata fama da jama’a,saidai duk da hakan zahra na ankare dashi,har yanzu ba wata dariya saman fuskarshi,sai wani murmushi mai kama da anyi masa dole,ta tabe baki yafi sau nawa duk sanda taga yana murmushin gefan baki
“Kai…Allah kayi mana magani” haka take fada cikin zuciyarta.
Cikin hakanne ta lura da wata qabila cikin kakin soja,da alama ita sojan ce,tana ta bibiyar aliyyun a gindi a gindi,duk inda ya sanya qafarsa,saidai babu alama ko daya data nuna yasan Allah yayi ruwanta a wajen,haka kawai ta dinga jin qunci da rashin dadin xaman wajen,har zuwa sanda dr tace
“Tabdi….wato dai tawa ba zata haqura ba…..zahra….see dis woman” ta fada tana nunata da yatsa,sanda aliyyun ke tsaye yana amsar wani award da qananun sojoji suka bashi da certificate of honour.
Murmushi zahran tayi,cikin salo na basaja
“Manta da ita dr…..ina da labarinta,ni dashi gaba daya mun rufe babinta”
“Good…..” Ta fada tana jinjina ma zahran ๐๐ผ.
Cikin lokaci kadan bayan an gama ciye ciye wajen ya soma hargitsewa,kowa na hoto da familynshi,walau matarsa kawai ko kuma da yaransu,wanda yara daya zuwa biyu dama aka bayar da damar zuwa dasu.
Dai dai sannan jafar yazo ya janye nasreen dinsa,saiya zamana inda take din ita kadai ce zaune,hakan ya bata damar nutsuwa tana bin kowanne abu dake faruwa a wajen da kallo a nutse,gefe daya tana jin yadda qirjinta keson ya dawo da ciwon da yake mata data samu dazun ya lafa,wala’alla kodon tun tea din safe bata sake kai komai bakinta bane.
“Excuse me pls,zan dauki wannan kujeran…..hope babu matsala?” Taji ana fada daga gabanta,saita daga kai ta dubeshi,matashin saurayi danye shakaf,wanda da alama ko talatin bai cika ba,kai ta gyada masa tana dauke kanta ta maida filin wajen,karo na uku kenan da yake attempting din yi mata magana tana basarwa.
“Bakaga mutuniyar bane?taawaa” Saif dake tsaye kusa da haidar ya rada masa a kunne dariya na taso masa,baice masa ci kanka ba,saidai yana sane da yadda take binsa din,ya tsani matar sosai,saidai ta rufe ido ta kasa fahimtar hakan,yakanji wani lokaci kamar yayi mata dukan tsiya,saidai ba dabi’arsa bace,hasalima yana kallon duk wani namiji da zai daki diya mace a tsayin wawa mara tunani kuma lusarin namiji,wanda ya kamata a kama ayita duka sai an jigatashi,yadan waiga suna magana da wani suka hada ido da ita,ya daure fuskarsa,bayason naci ko kadan a rayuwarsa,dama daya ce ta rage masa da xaiyi amfani da ita ya koreta kwata kwata daga dukkan sha’aninsa,yanzu kuwa zaiyi amfani da damar,saiya soma takawa yana lalubar inda take zaune da idanunsa,yayin da taawaa taci gaba da binsa a baya,tana tsammanin zai fita ne daga jama’a ta bisa ta fake da yi masa Allah ya sanya alkhairi wanda ta tura masa saqonni ta email dinsa sms da WhatsApp dinsa sunfi guda nawa amma bai amsa ko guda daya ba
Can ya hangota sanda saurayin ya sake dawowa yana tambayarta zai kuma daukar kujera daya kamar daga gidansu tazo da ita ta raya cikin ranta,saidai banza tayi masa bata ko kalleshi ba bare ta kulashi,ganin hakan yasa ya dauka yayi gaba,Aliyyu ya bishi da idanu yana bibiyar inda zai zauna,saidai tuni ya bace cikin mutanen dake kai kawo a wajen,wani abu ya hadiye har ya isa inda take zaune.
Hannu kawai taga an miqo mata,ta daga kai don ganin waye,sai tayi arba dashi da kuma tawakkalt dake tsaye daga bayansa,duk da fuskarsa a dinke take tsaf,saidai wadda ke bayan nasa bata iya hangen hakan,cikin second ta karanci komai,saita daga nata hannun ta sanya cikin tafin hannunsa da yake miqo matan,saiya maida hannun nasa ya rufe,ya runtse hannun nata tsakiyar nasa,wanda hakan ya sanya tsigar jikin kowannensu zubawa,dumin da tafin hannunta ke dashi ya ratsa duk wata jijiya ta jikinsa cikin sakanni,saiya dagota yana cewa
“Am sorry…..na barki ke daya ko?” Yanayin yadda ya dagotan gaba daya kamar wadda ya fusgo cikin salo yasa babu yadda zata iya tsaiwa da qafarta dole saidai ta fado gaba,shine kuma tsaye a gabanta,don haka jikinsa ta fada gaba daya,saiya sanya hannayensa ya riqe qugunta,a hankali cikin salo na rada yace mata
“Just a plan….karki zurfafa da yawa”.
Rasa abun cewa tayi saboda gaba daya a rude take,jikin ya Aliyyu?,ya haidar yau itace rungume cikinsa?,kuma unexpected?,sannan uwa uba yadda taga nan da nan idanun wasu sunyo kansu,da alamu dama tun dazun suna bibiyarsu ne
“Nasan da zaman kowanne….and i want expel them daga rayuwata”.
Cikin wani irin expression saman fuskarta ta daga kai ta kalleshi,qwayar idanunsu suka hadu waje guda,saiya dage mata gira daya,duk da har yanzu fuskarsa a dinke take
“Yes” canza mata wajen tsaiwa yayi daga gaba zuwa gefan kafadarsa,ya zagaya hannunsa a bayanta,ya riqe side din kafadarta daya da hannunsa daya,ya soma takawa a hankali tare da ita,dole gangar jikinta ta bishi suka soma ratsa wajen,yayi da taawa ta bisu da idanu,sai taji ba zata iya bari ba,don haka ta rufa musu baya dai still tana biye dasu,duk da tayi nesa nesa dasu ba kamar dazun ba.
Gaisaw yaci gaba dayi da mutanensa,kusan duk wanda ya gansu tare saiya tsaya,duk wani taku da zasuyi jikinsu na gogar na juna,hakan ya dinga weakening dinsu gaba daya ba tare da kowa ya sani ba,wanda kafin wani lokaci zahra ta rasa duk wani qwari daga jikinta,kusan riqon da yayi mata shike riqe da gangar jikinta,wannan shine karon farko data fara raba jikinta da wani da namiji,kamar yadda shima yake karin farko a rayuwarsa.
Hakan da yayi ba qaramin kada da yawa daga mutanen da yakeson kadawar yayi ba,a hankali yaga fuskokin suna canzawa,wasu kuma suna zamewa daga wajen,ciki harda taawa din data rasa inda zata tsoma ranta,ganin har a lokacin tana cikin jikinsa,hakanan duk inda zai zagaya tana tare dashi.
Da gaske yake bazai saketa a yanzun ba,riqonshi a gareta wani abune na daban da bata saba dashi ba,so take ya saketa ko zata rage wani abun,duk inda ya dora hannunsa a jikinta tana jin saqon saukar hannun har cikin qasusuwanta,kamar wanda keda wani abu na musamman cikin tafin hannunsa
“Cikina” yaji ta furta kalmar a hankali,saiya waiwaya ya dubeta kadan,suna hada idanu saita lumshesu,sam ya zuwa yanzu batason kallon qwayar idanunsa
“Ok” ya fada bayan ya dauke idanunsa daga ka ta na wasu sakanni,a hankali yayi niyyar zameta,saita tafi talau saboda yadda da gaske qirjinta ya riqe da ciwo,bai zaci haka ba cikin zafin nama ya riqota ta dawo jikinsa
“Are you serious?”kanta ta daga masa a hankali sanda take kwance a qirjinsa tana sauke numfashi,idanunta a runtse gam,hancinta na cika da qamshin turarensa,dumin jikinsa na ratsa fuskarta,tana iya juyo bugun zuciyarsa sosai
“Ok….ok” ya fada a hankali yana dan duban fuskarta dake cikin qirjinsa yana tunanin yadda zaiyi mata zuwa mota.
“Bani hannunki” ya fada calmly cikin qarfin hali,saita miqa masa hannun ya sake matseshi cikin nasa a hankali yana jin yadda tsigar jikinsa ke tashi tun daga qwaqwalwarsa zuwa gangar jikinsa,wanda sam baisan yaushe ya samo irin wannan feeling din ba,sai suka fara takawa a nutse har zuwa bakin motar.
Ga mamakinta da kanshi ya bude mata motar ta shiga ya rufe,saiya kunna ac na motar bayan ya dage dukka glasses din sama,sannan ya rufe ya juya yana barin wajen.
Idanunta ta bude tana kallonshi ta cikin glass din motar,karon farko da yayi wani abu da za’a bashi suna da tallafi a gareta kenan,bata sani ba,kona ganin idanun mutane ne?,saita rintse idanunta tana jin yadda ciwon ke sake motsa mata,ta sauke ajiyar zuciya tana kwanciya sosai cikin kujerar tana sauke numfashin wahala,wanda batayi cikakken minti ashirin ba taji saukar wani abu,ko data bude idanunta sai taga ruwan sama ke sauka,dai dai lokacin data hangi tahowarsa cikin sassarfa da qaramar lema a hannunsa,taci gaba da kallonsa tana riqe da saman cikinta har ya iso gab da motar,saita maida idanunta ta lumshe kamar me bacci,can qasan zuciyarta tana ambaton sunan Allah.
23/10/2021, 08:46 – ๐๐ป๐๐ป: 30
A nutse ya bude murfin motar ya shiga sannan ya rufe,yana shirin saka key ya kunna motar idanunsa suka kai kanta,ya dubi yadda ta cure waje daya,sai haka ya tuna masa da zahra….lokaci na qarshe a rayuwarta daya dauketa cikin motarsa,lokacin da take nemam agaji a sanda bashi da abinda zai iyayi mata,a haka a cure waje daya a sit din da wannan zahran ke kai,sai yaji wani abu ya tsarga masa tun daga kanshi har zuwa qafafunsa,sai daya furta can qasan maqoshinsa
“La haula wala quwwata illa billah” sannan ya bude idanun nasa ya tada motar suka fice daga wajen cikin tuqi a hankali saboda yadda ruwan saman yake qara qarfi.
Sannu a hankali suke tafiya bisa titin,haka kawai ya samu kansa da waiwayawa ya dubeta lokaci zuwa lokaci,time by time takan motsa ta kuma cije labbanta saboda ciwon da take jinsa har gadon bayanta.
A qalla sun shafe kusan minti talatin sannan suka qarasa unguwar tasu,yayi horn aka bude musu ya sanya motar tishi ciki ya ajeta a wajen adana motoci na gidan,saiya kashe motar,ya zubawa waje idanu ta cikin glass din motar yana kallon yadda ruwa ke gudu yana sauka da qarfinsa,a irin wannan yanayin da lokacin zuciyarsa na masa wani irin fes,tamkar ruwan na sauka ne saman zuciyarsa,saiya sanya hannunsa ya bude murfin motar ya fita,ya ware lemar hannunsa.
A kasalance itama ta bude murfin motar ta zura qafafunta tana rufe ido saboda yadda ruwan ya soma feso mata,duk da haka bata fasa fitowar ba,don babu abinda take buqata a yanzu irin ta samu waje ta kwanta sosai ko zata rage azabar da takeji.
Qanqame jikinta tayi waje daya ta soma nufar cikin gidan,saidai batayi taku biyar cikakke ba taji an lulluba mata abu saman kafadunta.
Kanta ta dago sanda yake dora mata lemar hannunsa tsakanin hannayenta,kafin takai ga kallon qwayar idanunsa tuni yayi gaba,cikin kuma ruwan saman dake saukowa yana dukan suit din jikinsa daya cire ‘yar saman ya rufa mata,mamaki ya tsaidata,sai kuma tasoma takawa itama zuwa cikin.
Kamar wanda ya tuna wani abun saiya kuma ya tsaya,sannu a hankali ta iskeshi harma ta wuceshi sannan ya rufe mata baya,tana gaba yana bayanta har suka isa qofar falon.
Zagayeta yayi ya matsa bakin qofar ya sanya key din ya bude,sai yaja baya ya tsaya,taja qafafunta ta shige,da qyar ta qarasa dakinta ta zube saman katifa tana juyi.
A qalla ta kusa minti talatin babu wani sauqi,kadaici da zama ita kadai ta qara ta’azzara mata ciwon,sai qwalla ta cika mata idanu,nan da nan suka fara gangarowa,tana rayawa a ranta inda yanzu ace tana gida babu shakka da tuni an sama mata magani,koda babu magani akwai kai kawon jama’a da zai dauke mata wani abu daga ciwon komai qanqantarsa.
A nutse yake takowa cikin falon bayan yayi wanka da ruwa me dumi sosai ya sanya kaya masu dan kauri saboda ruwan daya dakeshi daga gun ajiye mota zuwa cikin gidan,har yanzu ruwan ake tafkawa bai tsaya ba bai kuma sassauta ba,garin gaba daya ya fara daukar sanyi,saman dining ya qarasa ya samu abinci yaci,ya gama yana sauko ya nufi daki don sanyin daya soma busawar ya fara sashi jin takura,bargo kawai yake da buqatar shiga.
Har zai shige dakin nasa kuma saiya dakata
“Amanar Allah ce a hannunka” ya tuna zancan mamanshi,saiya sauya akalarshi zuwa dakin nata.
Yana shiga ya sanya hannu da sauri yana kashe fankar dake faman wulwulawa kamar babu sanyin ruwan sama,sannan ya dauki remote yayi controlling sanyin da acn ke bayarwa sa’annan ya waiwaya saman katifar dakin.
Can ya hangota cikin bargon tana mutsu mutsu,duk da baka iya ganin koda kanta
“Wayyo Allah na” daya kasa kunne yaji tana fada qasa qasa,saiya qarasa da sauri ya haura zuwa saman katifar ya tankwashe qafafunsa,sannan ya saka hannu yana yaye abun rufar dai dai sanda ta qaraso dab da ita yake zaune garin mirgin mirgin din da takeyi
“Ya Allah” ya fada a hankali yana duban yadda take riqe da qirjinta,tun asali shi mutum me mai tausayin mara lafiya,abu na farko dake daga masa hankali,lalura da kuma raunin ‘ya’ya mata.
Miqewa yayi tsaye da sauri yana ciro wayarsa daga aljihunsa,idan bai manta ba ya taba zuwa hutu gida lokacin bata da lafiya irin haka,yaji hajja tana cewa ulcer ce,da alama yanzun ma itace.
Kai tsaye number jafar ya kira,bugu uku ya daga
“How far oga?” Ya fada a sake
“Nasreen tana kusa?”
“Eh….Allah yasa lafiya”
“Lafiya…..amm….” Saiya rasa sunan da xai kira zahran dashi,daga qarshe yace
“Madam ce ba lafiya,ulcer dinta ta tashi….ko zata turamin medication da zata iya sha da zasu bata relief koda zuwa safiya ne?”
“Ok hold the phone” ya fada,sai yajishi yana magana duk da baijin me yake cewa,da alama tana kusa dashi ne,tsahon second talatin sannan yaji muryar jafar din,ya gaya masa magungunan da zata sha din,ya masa godiya sannan ya kashe kiran,ya sake kiran wata number sukayi magana,ya tura sunan magugunan sannan ya katse kiran nan ma yana maida dubanda dai a kanta,har yanzu babu wani canji da sanda ya shigo,yana tuna yadda ummi ke damuwa isan bashi da lafiya,ta miqa dukkan kulawarta akanshi,ya kamata shima ko yaya a yanzu ya kamanta akan jininta,saiya koma bakin katifar yadan tsugunna,yasan cewa bataci komai ba,yakan ji wani lokacin yadda suke daga da hajja idan bata da lafiya kan cin abinci,don haka yace, mata
“Tashi ki samu wani abun kici kafin a kawo magani” kaita girgiza masa alamun ba zataci ba,saiya dan xuba mata idanu na wasu sakanni,ba tare da yace da ita komai ba ya tashi ya fice.
Kusan minti talatin ya sake dawowa dakin,hannunsa dauke da wani irin mazubin abinci mai kyau,mai dauke da tambarin wani waje,ya qarasa ya janyo table din dake dakin ya dora akai,yana shirin miqewa wayarsa ta dauki ruri,ya daga yana amsa sallamar,wanda ya aika siyo magani ne ke shaida masa dukka pharmacies din a rufe suke
“Ok….thanks” ya fada a gajarce yana katse kiran
“Tashi kici abinci” ya kuma fada yana juyawa ya fice a dakin.
Bai wuce minti biyar ba ya dawo dauke da wata butar shayi me qananun kofuna,ya ajeta inda ya aje wancar ledar a hankali yana furxar da iska daga bakinsa,saiya dubeta still dai tana kwancen bata tashi ba,sake maimaita mata yayi ta tashin,saita girgiza masa kai alamun a’a
“Ki tashi nace….ina wasa dake ne!” Ya fada a dan tsawace,wanda hakan ya tilastata yaye bargon da take ciki,hawaye ne jage jage a idanunta,da gumi daya jiqe mata fuska,da alama zazzabin daya soma rufeta ne yake sauka,saita zauna sosai ba tare data miqe din ba.
A hankali yake takowa direction dinta,fuskarshi a dinke idanunsa a kanta,ya isa gabanta ya duqa a hankali ya riqo hannunta ya dagata cak ya miqar da ita tsaye,duk sai tajita wani irin a mugun takure,duk da ciwon da takeji,don babu mayafi a jikinta bare dankwali.
Taku biyu yayi ya hade tazarar dake tsakaninsu,kafin ta ankara ya jata zuwa qirjinsa kamar mai shirin rungumeta,ajiyar zuciya ta subuce masa a sirrance,ya dora hannunsa a hankali a bayanta yana lalubar zip din rigarta,saita sandare a tsaye tana raba idanu,jikinta ya dauki rawa gaba daya lokacin da taji ya kama zip din ya soma zugeshi zuwa qasa
“Zzzzzan….” Take fada bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yakeyi,ko harafi daya ya kasa fitowa daga bakinta,har sai da taji yakai zip din qasa,rigar ta rabe gida biyu,taji hannunsa saman kafadarta,yana nufin sabule mata rigar xaiyi?,ta tambayi kanta da kanta,ai batasan sanda ta cafe tsintsiyar hannunsa ba cikin hawaye tace
“Zanc…..zan cire da kaina” nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana zame hannunsa daga cikin nata,don dama yana tunanin ta yadda zai qarasa aikin da yake pretending din yin,saiya taka da baya da baya,sannan ya juya bayansa,ya tafi zuwa window din dakin ya yaye labulen ya bude glass din ya saka kanshi a ciki yana sake sauke ajiyar zuciya gami da fidda iska daga bakinsa zuwa hancinsa,yana jin wani irin yanayi cikin jikinsa.
Kamar wata sakarya ta riqe wuyan rigar gam,tana tsaye tana rawar sanyi,tana kuma satar kallon yadda ya juya mata baya,yana nufin yana dakin xata canza kaya kenan?,idanunta ne suka sauka kan qofar toilet,sai tayi sauri ta nufi bandakin itama tana sauke ajiyar zuciya.
Bata jimaba ta fito sanye da hijabi,kamar yaji takunta ya waiwayo a hankali,Ya qarasa inda ya aje kayan,sannan ya biya ta gaban mudubi ya dauko wiper da yakan ajjiye saboda goge busashen abu,sosai ya zauna a gabanta har gwiwarsa na gogar tata,ya ciro daya daga cikin wipes din ya kamo fuskarta tsakiyar hannunsa sannan ya fara dauke duka powdern dake fuskarta.
Idanunta ta rufe gam,sanyin wiper din na ratsa fatarta,numfashinsa dake fita anutse na dukan fuskarta,yayin da kuma takejin nauyin idanunsa dake yawo saman fuskarta.
Kowanne waje idan ya saka wiper ya goge saiya kalleshi,sosai yake ganin kamanninta wanda a baya ko za’a tsireshi baisan ya fuskarta take ba,manyan idanu dake qawace da gashin ido dogaye,daga samansu kwantacciyar gira ce mai yalwar suma itama wadda ta kusa hadewa da juna,a hankali harya gangaro kan lips dinta da suka jambaki,saiya sauya sabuwar wiper,ya saka dan yatsansa a cikinta ya dora saman lips dinta ya fara gogewa.
Jikinta ta qanqanme saboda ji take kamar yana mata tafiyar tsutsa,ta gefan aliyyu kuwa haka ya dinga goge jambakin ainihin kalar labbanta na fitowa,baisan cewa ya jima yana gogesu ba sai da zahra da har yanzu idanuna ke rufe tace
“Zafi”saiya janye hannunsa da sauri yana sake daure fuska,sai yaja tsaki qasa qasa sannan ya aje abincin gefanta,ya miqe ya fice yana yarfe hannu,gami da tuhumar kansa,me yasa bai bar mata kwalliyarta ta goge da kanta ba?,daga bisani ya aza hakan a matsayin kyautata zai gwada yi mata kamar yadda mahaifiyarta ta gwadawa tashi rayuwar.
A hankali take cin abincin kamar ta rusa kuka saboda yadda sam baya mata dadi a bakinta,ga numfashinta dake wani irin nauyi,bata ci da yawa ba ta ture kwanon ta koma rub da ciki,a yanzu duk yadda taso ta daure dauriyarta ta qare,ta soma raki a bayyane don ta kasa yin shurun.
Dai dai sanda ya sake dawowa dakin bayan ya gama shirin barcinsa yaga iya abincin data ci din,sauri yadan qara zuwa inda take kwancen,sai yaja da baya,ya zuba ruwan dumin daya tafasa ya barshi yadan sha iska cikin cup din daya dauko,ya sanyata ta sake zama tana sharar qwalla.
Kallo daya yayi mata ya dauke kanshi yana tuna zahra,lokacin da qwalla ke fita daga idanunta kamar haka,tana cewa ya yafe mata mutuwa zatayi,bai taba kawo mata mutuwar ba a sannan sai gashi ta tafin,wannan tunanin yaji ya motsa zuciyarsa,wannan tunanin yasa yaji baiso yabar dakin,hakanan ya di ga jin idan yabar dakin kamar wani mummunan abu zai biyo baya,saboda haka ya koma dakinsa ya dauko duk abinda yasan zaya iya buqata ciki harda sytem dinsa da wayoyinsa ya dawo dakin,a lokacin tayi rub da ciki cikin bargo,bata juye juye kamar daxu,saidai lokaci zuwa lokaci takan motsa,da alamu ta samu relief ne daga ciwon.
Saman kujerar dakin yayi zamanshi bayan ya maida dakin dim light,saiya bude system dinsa ya soma rage aiki,aikin yadda zai gudanar da office dinsa,da kuma bataliyar rundunar sojin dake qarqashin jagorancinsa,ya soma tsara komai bisa hikima,saidai baya daukar wasu mintuna masu tsaho bai daga kai ya dubeta ba.
A hankali ya zare gilashin idanunsa da yake amfani dashi idan zai dade saman screen na waya ko system,ya ajeshi gefe yana miqa,ya sake duban inda take kwance sau babu adadi,har yanzu dai ba alamar bacci ya dauketa,saiya tattare komai waje daya,ya taka a hankali har ya isa saman katifar,ya zauna sosai,saita rintse idanunta tana jin yadda ya zauna gefan nata kamar tayi kusanci da yawa,gabanta ya dinga faduwa,sanda ya dora hannunsa saman goshinta da wuyanta bayan ya yaye bargon data rufa numfashinta ya sake yi mata wahalar shaqa,hakan yasa yadan firgita,saiya dagota daga kwanciyar da tayin,ba tre da tunanin komai ba ya zira dukkanin hannunsa cikin rigarta ta baya,ya kama maballin bra dinta yana qoqarin balle mata wai ko zata samu damar shaqar numfashin sosai,kamar yadda yaga suna yiwa juna sometimes a gida ko a battlefield idan tsautsayi ya ritsa da dayansu numfashi ya fara masa wuyar shaqa,suna cire masa duk damarar dake jikinsa don a rage masa wahala.
Ji tayi kamar zuqa daya ya rage mata na iska a duniya sanda taji dumin hannunsa a bayanta,kawai saita tafi luu gaba daya zuwa jikinsa tana jin wuta na dauke mata,bai damu ba,hakan ma saiya rage masa aiki,ya balleta gaba daya ya saka hannu ya zareta ya wurgata gefe,sai kawai ya gyara mata kwanciya saman cikinsa ta rub da ciki yadda ya fuskanci tafi jin dadin kwanciyar,bata da wani zabi da ya wuce tayi likimo,babu qarfin zame kanta daga gareshi,sannan tsoro da tsananin mamakin jinta kwance tsakiyar qirjin mutumin da bata taba kawowa kanta hakan ba yasa batajin akwai wata kalma guda daya da zata iya fita daga bakinta.
Wani dumi ne ya dinga ratsata,duka sanyin da takeji yayi nasa waje,daddadan turaren aliyyu daya zama tambarinsa ya baibaye dukka kafar hancinta,lallausan gashin qirjinsa ya dinga gogar fatar fuskarta,ta dinga jan numfashinta da nauyi tana saukewa,ba tare da saninta ba sai hakan ya zamana kamar wani communication ne tsakanin jikinta da nashi,sai ya zamana kamar tana pushing jikinta da nashi.
“Subhanallah” ya fada cikin zuciyarsa yana qaryata kansa,take ya dinga jin tsigar jikinsa na zubawa,saiya dunqule kowane hannu nasa ya damqe tafin hannunsa sosai,sai a sannan ya lura ya kuma gane gangancin daya aikata,wanda shi sam bai kawo hakan ba,ya karkata tunaninsa da son ganin ta samu relief na ciwon da takeji.
Ga mamakinta kuma saita dinga jin komai yana daidaita,numfashinta ya fara zama dai dai,hakanan ciwon shima yana raguwa da kadan da kadan,sai kuma idanunta suka fara nauyi kamar an dora mata dutse,da alamu qaqqarfan bacci ne yakeson sureta,wanda ciki qanqanin lokaci ba tare data ankara ba yayi awon gaba da ita.
23/10/2021, 08:47 – ๐๐ป๐๐ป: 31
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
___________________________________
Yadda yaji numfashinta na sauka a hankali cikin nutsuwa ya tabbatar masa da tayi bacci,hannunsa yasa zai sauketa saita motsa,hakan yasa ya fasa ya maida hannunsa ya ajiye,tsahon minti biyar ya sake daga hannun nasa zai sauketa,hakanan wannan karon a karan kansa yaji ya kasa,saiya sake maida hannun nasa ya ajiye yana maida numfashi gami da runtse ido,wani irin yanayi yakeji cikin jikinsa,irin wanda tunda yake bai taba jinsa ba,wani nauyin jiki da kasala yakeji,minti daya biyu saiya kalli fuskarta,duk da baya iya ganinta sosai saboda fuskar na kife a saman wuyansa ne,gaba daya jikinta dake manne da nashi ya soma takurashi gami da rikita masa lissafi.
Yayi tsammanin zai jure amma saiya kasa,don haka tilas tasa ya zameta daga jikin nasa cikin dabara,ya koma gefe yan furzar da iska daga bakinsa,ya kuma kulle idanunsa,sannu a hankali jikinsa ya soma nauyi shima,bacci ya qara maaa rauni da kasala,saiga bacci ya fisgeshi ba tare daya sani ba.
Dukkansu babu wanda ya sake farkawa, saishi ne da akayi kiran sallah firgigit ya tashi,sam ya mance a inda yake sai daya nutsuwarsa ta dawo jikinsa,saiya miqe a hankali bayan ya gama addu’ar tashi daga bacci ya miqe a nutse ya nufi bandaki.
Alwala ya daura,ya dauki dadduma a nan dakin,sannan ya dubeta yana qarasa inda take,yasa hannunsa saman pillow din da take kwance ya bubbuga,ta bude idonta dake cike da bacci sai cikin nasa,tayi saurin mayarwa ta rufe,shi kuma ganin haka ya sanyashin yin gaba yana cewa
“Lokacin sallah yayi” yana qarasa ficewa daga dakin.
A nutse ta sauka daga gadon zuwa bandaki tana tuna abinda ya wakana daren jiyan,dukka jikinta babu abinda yake sai fidda qamshin turarensa duk motsin da zatayi,duk sai taji wani irin kunya da nauyinsa sun saukar mata wanda bata taba ji ba sanda ta tsaya gaba madubi ta tuna shi ya cire mata bra,ita kadai a bandakin amma sai ta dinga ji kamar yana kallonta,tasa hannu ta cukuikuye rigarta ta nufi gaban sink ta daura alwala sannan ta fito.
Tana fitowa daga bandakin sanda ta miqa hannunta ta baya tana rufe qofar toilet din shi kuma yana shigowa,kai tsaye idanunsa suka sauka a kanta,rigar jikinta ta kwanta sosai a fatarta,ta yadda duk wanda ya kalleta yasan babu brazier a jikinta,hakan ya baiwa albarkatun qirjinta damar tsayawa sosai kowanne a muhallinsa.
Kamar wanda aka sanyawa shocking haka yaji,ya dauke kansa da wani irin sauri yana qarasa shigowa ciki ya kuma nufi kan gado kai tsaye,yayin da ita kuma ta qame a tsaye cukuikuye da gaban rigarta,gabanta na wani irin faduwa saboda lura da tayi da inda yake kalla din.
Saman katifar ya haura,ya dage filo ya dauki wayarsa,da alama ita ya manta ya dawo dauka,saidai yana miqewa yaci tuntube da breezier dinta,saiya janye qafarsa a hankali ya sauko ya fice.
Da sauri ta qarasa ta sakawa qofar key tana sakin numfashi,wai wannan wane irin abun kunya ne haka,sai data kusan makara sannan ta samu tayi sallar bayan ta tattare katifar.
Har wajen sha daya saura na safe tana dakin bata fita,duk da tayi wanka,amma nauyin haduwa dashi yasa ta kasa fita,uwa uba kuma mararta daketa qulle mata,addu’a take Allah yasa kada period din yazo sai ta koma gida.
A hankali ta bude qofar sanda taji anyi knocking,saita labe daga bayan qofar ta yadda bazai iya hangota sosai ba,haka itama.
Muryarsa kawai taji da mayen qamshin turarensa yana cewa
“U know you r sick….ki fito ki samu wani abu kici”
“Okey” ta amsa masa tana sakin qofar,ta koma cikin dakin tana laluben me zata yafa,ta ciji yatsa tayi Alla wadarai da wadanda suka hada mata kaya,kaf kayan babu hijabi ko daya,sai sannan ta tuna yace mata ta rubuta list na abinda take buqata amma batayi hakan ba,saboda batason abinda zai ja ta dade bata koma gida ba,kodon jarabawarta data tabbatar duk abinda akw ciki ba zasu wuce two weeks basu fara ba,inda kuma ta rubuta din wala’alla ta hada harda shi,amma yanzun idan sun dawo dole ta rubuta abinda ba’a rasa ba,dole qanwar naqi ta dauki mayafi ta yafa.
Saman dining ta sameshi da waya a hannunsa yana dannawa,yana jin takunta ya dago kai,ga mamakinsa ba inda idanunsa ya sauka sai a qirjinta,yayi maza ya dauke kai yana jan tsaki can qasan ransa,mugun haushin kansa ya kamashi,meya kaishi ma daga kai koda fuskarta zai kalla bare wani sashe na jikinta,inda Allah ya taimakeshi bata kula da hakan ba harta qarasa,taja kujera ta zauna,ta gaidashi ya amsa yana ci gaba da danne danne a wayarsa,bata ma sani ba shi ko yayi breakfast din ko beyi ba,ta hada ruwan zafi ta fara kurba a hankali,tana jinta duk a takure saboda zamanshi a wajen.
Tayi rabin ruwan zafin taji ษul daga qasanta
“Innalillahi” ta fada cikin faduwar gaba,da alama period dinta ne yaxo,ita kadai ta dinga wara idanu tana tunanin ya zatayi,bata gama wannan tunanin ba ta tsinci muryarsa yana cewa
“Ki sauri ki gama ki sameni a mota”
“Toh” ta amsa a sanyaye,yayin da shi kuma yayi ficewarsa.
Haka taci gaba da raba idanu da tunanin me zatayi,tana jin kuma yadda jinin ke flowing a jikinta,har zuwa sanda ya aiko mai gadi ya tsaya daga qofar falo yace mata ta fito inji oga,saidai tashin ya gagara,don ta tabbatar ba jikinta kawai ba,har kujerar da take xaune a kai ta baci.
Zabura ta kusa yi sanda ta tsinci muryarsa daga bayanta,ta waiwaya a hankali ta dubeshi,qwayar idanun nashi ne masu nauyi samanta yana dubanta
“Karki batamin lokaci fa….” Abinda kawai ta iya ji kenan daga bakinsa,bata da wata sauran dabara kuma,don haka ta miqe kai tsaye kawai ta tsaya cak ba tare data iya ce masa komai ba.
A hankali idanunsa ya sauka a inda ta tashin,ya fahimta sarai,don ta danyi staining wajen,saiya dauke idon nasa kawai ya juya ya fice.
Ta tabbata ya ga abinda takeson nuna masan,don haka ta nufi dakinta a hankali,ta wuce bandakinta,ta gyara kanta ta sake wanka gaba daya.
Tana tsaye waje daya a tsakar dakin tana tunanin me zata saka ta tare?,ko dankwalinta zatayi amfani taji an turo qofar dakin,duk sai ta duburbuce,ta rasa inda zata boye kanta.
Shi dinma dai kamar dazun,inda idanunsa suka sauka daxu yanzu ma haka
“Ya salam” ya fada yana aje mata ledar gamida juyawa yabar dakin,annan wanne irin jarraba ce yakeson dorawa kanshi?,wani mugun haushin kansa ya kamashi,yaja wani dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa,ya shiga motar yana rufe murfin da qarfi kamar ita tayi masa,sumarshi yaje shafawa da hannu daya yana furzar da iska daga bakinsa,can cikin zuciyarsa kuma yana jawa kansa warning,tare da son gayawa kansa da zuciyarsa hakan bazai sake maimaituwa ba.
Sai daya fita taja ledar ta som duba abinda ke ciki,pad ce da pants masu yawa,wanda tasan sundi qarfin buqatarta na dan lokaci,sai ta cira wanda zatayi amfani dashi,ta dora ledar saman akwatinta sannan ta bareta ta saka,tayi mamakin yadda akayi size na pant din yayi mata dai dai.
A gurguje ta shirya sannan ta fito,tun kafin ta qaraso ya hade ranshi sosai,ya kuma dauke kansa daga direction dinta harta qaraso ta bude gidan gaba ta shiga.
Tafiyar kurame dai sukayi kamar kullum,har suka isa ginin da kallo daya tayi masa ya gaya mata asibiti ne,private asibiti,daga yanayin tsarinsa da gininsa kadai ya isa ya gaya maka kudin da ake lasa na marasa lafiya,saidai kulawar da suke baiwa mara lpy ya cancanci kudin da suke karba.
Da alama nan yake zuwa idan yana garin,duk da cewa akwai na sojoji,saidai wala’alla kayan aikinsu da ma’aikatan ne basuyi masa ba.
Tare suka shiga ganin likitan,yana tsaye ta gama bayani ya rubuta mata magani,da kansa ya tsaya a pharmacy na asibitin ya amshi maganin.
Ita kam komai yayi mamaki yake bata,tamkar ba ya haidar din data sani ba,bata taba kawowa ranta akwai ranar da zatazo ta samu koda kallon mutunci sau daya ba bare akai ga kula da lafiyarta.
Bayan sun baro asibitin saiya tsaya a wani babban kanti yayi musu siyayya bisa radin kansa,ya zaba abubuwan da yake tunanin zata iya buqata sannan ya dawo suka tafi.
*_washegari_*
Tun qarfe shida na safe ta kasa komawa bacci saboda yunwa da takeji,wani lokaci ulcer dinta tana yi mata haka,sai ta sanyata jin yunwa kamar hauka,uwa uba kuma zaman banza data gaji dashi,wanda daga kwanciya sai danne danne a waya,gaba daya zaman ya gama gundirarta,babu wani abu na debe kewa.
Parlour din shuru babu kowa,saita wuce kitchen din kai tsaye,wanda wannan shine shigarta ta biyu tunda tazo gidan,sai a sannan ta qare masa kallo,babu abinda babu a ciki,babun ce kawai babu,hakanan komai atsare yake,da alama kuma tun tafiyarsu hajja ba’ayi girki a ciki ba.
Da iya cikinta kawai tayi niyyar dafa abinda zata ci wanda bazai ja mata lokaci ba,amma saita tuna gida,daga umminta har hajja basa gaba yin girki iya cikinsu,dole sai sunyi da al’ummar annabi,da kuma wanda rabonsa ya tsaga zaici,data duba store da fridge din kuma saita tadda akwai duk wani kayan buqata na amfanin girki,zata iya dafa kowanne abinci,don haka ta diba duk abinda tasan zata buqata ta fara sarrafawa.
Gas din waje hudu ne dashi,saita kunna biyu yadda komai zaifi mata sauri ta dora,ganin bata da sauran abinda zatayi saita fara tattare kitchen din,duk da bawai datti yayi ba,amma akwai qura na rashin shiga kwana biyun,data gama taga har yanzu abunda ta dora baikai mata ta sauke ba,saita miqa falon.
Tas ta gyareshi,ta kuma gyara guraren da baiyi mata ba,dama wani aikin sai diya mace,nan da nan sai gashi ya sake tarwai kamar an qara masa kyau,zuwa sannan ta koma kitchen taga abunda ta dora yayin,saita dora da aikinta daga inda ta tsaya.
A gaggauce ya fito daga dakin yana sake kallon agogon da yake daurawa a hannunsa,cike da mamakin yadda lokaci ya kufce masa haka yanata aikin bacci,sam baisan lokaci yaja haka ba,sai daya soma jiyo qamshin girki a hancinsa,wanda da farko ya zaci a mafarki ne,sai daya farka yaji cikin gidan ne,bai kawo zata shiga kitchen ba,don haka ya barwa ransa daga maqota ne,abinda ya sanyashi gaggawar kuwa daya tuna babu abinda zataci cikin gidan,jiyan dama nasreen ce ta kawo musu shi.
Sanda ya fito falon,dai dai lokacin da zahran ke fitowa dauke da warmers guda biyu,tana ta sauri ta gama ta jera ta koma daki abinta,don batason ya ganta,tayi ne kawai don babu kyau mugunta,musamman ta yunwa.
Ido suka hada dashi,saita dauke qwayar idanunta da sauri gabanta na faduwa hakanan,sannan wani kyau taga ya mata a ido yanzun da yake sanye da wasu kaya,saita koma takawa a hankali tana wassafa yadda zata wuce ta gabanshi,saboda yana tsaye qyam ne,kuma dole ta giftashi,uwa uba ma kuma riga da skert din dake jikinta na roba ce mai rawa,ya zauna yabi kowanne lungu da tudu na jikinta,kanta ne kawai keda dankwali,shi kansa dan kwalin rabi ne,dukka sumarta ta baya da goshinta ana gani.
Sannu a hankali idanuwansa suka bar fuskarta data dan yi fayau saboda ciwon kwama biyun da tayi,sai suka zarce suka sauka a muhallin da tun daxun yake gargadarsu a kanshi,hannunsa ya damqe waje guda yana dauke idanun nasa daga kanta,saidai shi kansa baisan yadda akayi ba yaji qarar faduwar flask din hannunta a gabasa,gab da yatsunsa,saura kadan su sauka a qafarsas,sannan ta daki jikinsa ta zame zata kai qasa.
Cikin matuqar zafin nama ya tarota,gaggawar yin sarving dinta ta hanyar tarota yasa ya dora hannunsa saman qirjinta ba tare daya ankara ba,da sauri ya daga hannun nashi daga wajen,kamar yadda itama ta miqe da sauri ta tsaya da qafafunta,duka sai suka duqa kusan lokaci daya suna qoqarin daga flask din.
Allah yasa ya rufu sosai,babu abinda ya zuba sai dan abinda ba’a rasa ba ta gefen murfin,da sauri ta dauke ta nufi dining din qafafunta na rawa,ta dorasu akai,ta yagi tissue tana goge bakin nasu,da zimmar bata lokaci har yabar wajen,saidai duk yadda ta dinga laqai laqai din gamawa don ya tafi aikin banza tayi,don sai jinsa tayi ya hauro wajen,yaja kujera daya ya zauna abinsa,fuskarsa a dake kamar bada shi abun dazu din dazu ya faru ba.
Gaidashi tayi a gurguje tana bari wajen,saita fasa komawa kitchen ta dauki abincin,ta fada dakinta kai tsaye.
Gefan katifar ta zauna tana maida numfashi,har yanzu tana jin dumin hannunsa saman jikinta,sai takejin kamar bai dauke hannun ba,don haka ta koma rub da ciki ta kwanta tana rufe idanunta tana kuma sauke numfashi ษaya ษaya.
Hanyar data wuce yabi da kallo sai data wuce,shima saiya sauke numfashi me nauyi daga qirjinsa,baisan me yasa koda yaushe idan ta fito ko baiso saiya kalleta,kamar wanda ake jan idanunsa da magnet,abinda sam ba halayyarsa bace,hasalima yana daya daga cikin jinsan mutanen da suka tsani yawan kallo.
Qoqari yayi ya kauda tunanin gefe,ya janyo kwanukan abincin ya soma budewa,tuni qamshi ya sake game wajen,saiya soma zubawa,yana fatan Allah yasa ษanษanon a dace da bakinsa,duk da yasan cewa ba baya bace ita,tunda kaf cikin yaran gidan ita kadai yake cin girkinta,itama albarkacin hajja take ci.
Sosai ya lodi abincin,duk da dama shi din ba baya bane wajen baiwa cikinsa haqqinsa,to amma ya dade rabon daya zauna yaci abinci mai yawa irin haka,sanda ya kammala ya duba agogonsa,yayi dai dai da lokacin da zai fita din,saboda meeting na gaggawa da aka kirasu,ya miqe yana gyara tie din wuyansa yana dan duban qofar falon,kamar ya shiga kamar ya fice,to amma idan ya shiga din me zaya ce da ita?,don haka saiya doshi qofa kawai ya fice,ya samu drivernsa yayi ready shi yake jira,ba bata lokaci suka fice daga gidan,dai dai sanda zahran ta saki ajiyar zuciya,ta miqe zaune sannan ta tashi a kasalance zuwa kitchen don ta dauki nata abincin.
23/10/2021, 08:47 – ๐๐ป๐๐ป: 32
*M’S TREATS*
_BASU FITO BA SAI DA SUKA SHIRYA_
*_shin kuna da labarin m’s treats?_*
*_idan baki dashi to su ake kira da KOMAI DA RUWANKA_*
*Domin kuwa sun hade dukkan wani abu da rayuwarku ke buqata*
*su gyara muku JIKINKU sannan kuma su gyara muku CIKINKU*
*_sun tanadar muku abubuwa kamar haka_*
*KAYAN QAMSHI DANA GYARAN FATA*
Smal halut
Sandal coconut
Janal banal
Arabian oud sandal bakhuor
Special kajiji
Sandal falake
Vip hawi
Sudanes sandal rose
Humra
White humra
Black humra
Kulakcca
Dilka soap
Whitening soap
*KAYAN SPICES*
Curry powder
Corriander powder
Tumeric powder
Mix spices
Ginger powder
Black pepper
White pepper
*SNACKS*
Samosa
Spring rolls
Meatpie
Cupcake
Birthday cake
Doughnut
*MAZA GWADA NEMANSU TA WADAN NAN LAMBOBIN WAYAR*
07061106161 *KO*
08099990056
*_ZAKU IYA ZUWA KU SAMESU A bayan northwest university layin gidan ruwan dish KANO NIGERIA_*
*_MUNA MUKU ALBISHIRI DA INGANCI DA KUMA RAHUSA_*
*hausawa sukace SAI AM GWADA AKAN SAN NA QWARAI*
_________________________________
Da kanta ta sanya hijabi ta miqawa maigadi nasu abincin,wanda ya amsa cikin farinciki yanata mata godiya,don ba kadan ba yaji dadin hakan,sannan ta dawo ta zauna tana cin nata abincin,lokaci zuwa lokaci tana kallon inda abun ya faru,tana tuna fuskarshi a sannan,sai ta dinga jin wani banbarakwai,don haka ta cuccusa ta miqa kwanon kitchen,sannan ta dawo ta kunna kallo bayan ta tabbatar yabar gidan.
Da daddare ma ita tayi girkinta mai lafiya,ta jere komai ta wuce daki,saidai har wajen goma na dare bataji shigowarsa ba,sai goma da rabi sa’annan taji dirin motarsa.
Tana kwance a daki tana iya jiyo motsinsa a falo,har zuwa sanda ya bude dakinsa ya shige,saita saki ajiyar zuciya ta tashi ta dauko maganinta tasha ta kwanta.
Ta zaci zatayi bacci ne da wuri,tunda batayi baccin rana ba,saidai kuma ina,haka ta yita juyi,har kusan sha biyu saura minti goma sannan ta samu bacci awon gaba da ita.
Shi dinma bayan yayi wanka ya saka kayan baccinsa saiya haye gado,yanajin gajiya kadan kadan cikin jikinsa,don tunda ya fita bai zauna ba,bayan sun gama meeting da manyansu kuma ya nemi zama da Battalia da yake jagoranta suka tattauna,babba kuma muhimmin aiki ne yake tunkarosu kan tsaron qasarmu,wanda yakeji a jikinsa da wahala wannan karon bai aje girma ko muqaminsa ba ya shiga cikin aikin da kansa anyi dashi ba.
Neman bacci yayi ya rasa,saiya dinga kame kamen abinda zai debe masa kewa,irin wannan yanayin na rashin zuwan bacci baqo ne a rayuwarsa,ya saba a duk sanda yaji bacci,kawai daya kwanta zai daukeshi,sai gashi yau zancan yasha banban,saiya dauki system dinsa yahau duba saqonni,har zuwa sanda yaji baccin da gaske,ya kasheta yayi addu’o’insa ya kwanta.
Duk yadda yakai ga jin barcin sai yaji kwanciyar babu armashi,ya soma canza position daga dama zuwa hagu,yana tambayar kansa ya akayi jiya yayi barci lafiya lau?,yau kuma abun ya faskara?,saiya tuna abinda ya farun jiya,da sauri ya kauda tunanin,ya dinga maimaita hasbiyallahu la’ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim,sannu a hankali yaji yana samun dai daito,bai dade da yawa ba baccin ya sureshi shima.
*_ASUBA TA GARI ZAHRA DA HAIDAR DIN HAJJA_*_MAGA WA ZAICI WASAN?_๐๐
Washegari ma tayi breakfast din,ta kuma aje masa ta shige daki,saboda sam batason haduwarsu,kallon dra lura yana mata ne bataso,nauyi yake mata da yawa,tana tsoron tsirfarsa kada ya lauya mata wani laifin,koya kwaba mata magana,saidai a rashin saninta ranar tunda sassafe ya fita,meeting din dai suke ci gaba dayi har sai sun kamo bakin zaren,batasan bai nan ba sai data fito wajejen la’asar zata dora girkin dare sannan ta ganshi,sai fita tayi dashi ta baiwa maigadi ya bayar,na dare ma data gamanan ta jere masa,saidai shi duk da ya dawo a makare kuma a gajiye bai fasa ci ba,saboda taste din yana masa dadi sosai.
Sai da safe xata gyara gidan ta gani,tayi tsammanin yau din ma ya fita da wuri,don haka tea kawai ta hada,ta soya qwai guda biyu ta hada da bread taci,saita gyara gidan,ta hada kayanta data saka zata wanke,don haka ta sanya t.shirt me qaramin hannu ta daura plain zani,hakan datayi saiya tuna mata da makarantar boarding,saita saki murmushi,ta tsaya gaba mudubi ta dubi kanta,ta tuna lokacin da bata fiya son shigar ba,saboda zakaga kamar ta saka pushup bra ne kuma ba ita ta saka ba,idan ma tayi shigar saidai tana maqale da hijabi,saboda baiwar halitta da qirar jiki da Allah yayi mata,sai suyita tsokanarta,shi yasa take zama da hijabin.
Barin gaban madubin tayi ta tattara kayan ta fice dasu backyard na gidan,inda yake da famfo da wajen shanya ta zubesu ta fara wankewa,babu jimawa ta gama ta fara shanyansu daya bayan daya.
A nutse ya fito daga dakinsa yana rufe bakinsa saboda hammae data subuce masa,ya dubi kan dining yaga wayam babu komai,sai yasa hannu ya shafi cikinsa,don yunwa yakeji qwarai,gajiya ce ta hanashi fita yau da wuri yadda ya saba,ya yanke kawai ya kwanta yadan huta zuwa azahar ya fita din,ganin babu komai akan dining din saiya juya ya shige kitchen.
Can ma wayam,saiya taka a hankali ya bude qofar da zata sadaka da bayan gidan don ya samu fresh air kafin yayi tunanin abinda zaici.
Itace ta farko da idanunsa suka fara gani,tana ta shanyarta a nutse,gefe da gefen zaninta duka ya jiqe,hakan ya sanya yabi jikinta ya lafe,ya bayyana shatin santala santalan cinyoyinta,t.shirt din jikinta ta zauna mata itama ta fitar da duk wata sura tata.
A hankali yakai bayansa ya jingina da qofar daya bude din,yana goye hannayensa a qirjinsa,ba tare da yasan me yake aikatawa ba yaci gaba da binta da idanunsa duk inda ta motsa,wani irin abu me qarfi da baisan meye ba yana fusgarshi zuwa gareta.
ฦarar faduwar bucket daga hannunta shi ya taimaka masa ya dawo zuwa hayyacinsa,da sauri ya taka a hankali da baya ya koma cikin kitchen din,yana sauke ajiyar zuciya tare da jin dadi da bata ganshi ba,cak ya tsaya tsakiyar kitchen din,yama rasa wanne tunani yake,yasa hannunsa ya ranqwashi tsakiyar kansa,cikin zuciyarsa yana gayawa kansa me yake damunsa?,me yake aikatawa haka?,dogon tsaki yaja ya taka zuwa inda gas yake ya kunna ya dauki tukunya ya zuba ruwa,saidai kafin yakai ga zuba kayan hadin tea din ya lura da flask din tea dake wajen,yakai hannu ya daga sai yaji akwai a ciki,don haka ya dauki cup ya zuba ya jingina bayansa yana kurba a hankali.
A hankali ya dinga ganin motsinta na daxu cikin idanunsa,ba tare daya ankara ba zuciyarsa ta soma zayyano masa irin abubuwan da yake buqata tare da mace,kowanne tana haska masa shi cikin idanunsa,yana kaucewa da qarfin tsiya tare da qaryata kanshi da kanshi,ya dinga jan tsaki shi daya yana kokawa da tunanin.
Da hanzarinta batare da tsammanin akwai wani a kitchen din ba ta shigo,saita zabura zata koma da baya,daidai sanda suka hada idanu,saita tsaya cak na wasu sakanni,sanda taga ya dauke idanunsa ta fara shigowa ciki don ta wuce,zuciyarta na wani irin bugawa da yaqi daidaita.
Sake daga idanunsa yayi karo na biyu yana kallonta ta qasan idanu,kallon da idan duba daya kayi masa ba zaka zaci ita yake kallo ba,saika dauka a lumshe idanunsa suke,dab da zata giftashi tace
“Ina kwana” ya amsa qasan maqoshinsa.
Ji take kamar zata harde ta fadi,jikinta yana gaya mata akwai idanu a kanta,kamar ta zuqo qofar ficewa daga falon ta fice gaba daya,saidai kash!,dab da zata fita taji muryarsa a dake yana cewa
“Zo nan” haka kawai ya tsinci kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,sai yaji baiso ta fice ne kawai,kamar tace masa zata qarasa daki ta dauka hijabi,to amma batasan me zaya fassara hakan ba,don haka ta sake juyowa ta dawo zuwa inda yake,dukka idanunsa na kanta da salon kallon qasa qasa mai kama da me bacci
“Hadamin breakfast” ya furta yana sake kurbar tea din hannunsa,ta zaci fita zayayi ya bata waje,sai taga ya matsa gefe kawai abinsa yana ci gaba da shan tea dinsa,daga qarshe ma sai yaja kujera yayi zamansa cikin kitchen din,sannu sannu kansa tsaye yaci gaba da binta da kallo duk motsin da zatayi.
Gaba daya duk sai ta rude ta daburce,sabida wani irin tasiri da idanunsa ke mata cikin jikinta,jikinta duka rawa yake,gani take kaman ba ya zakinsu ba,tun da can idan ya tsareka da idanunsa saika gwammace ya dakeka akan kallonsa mai nauyi,wani irin kwarjini ne cikin idanunsa,batasan me yasa ya tsareta haka da kallo ba,don haka duk aikin da zatayi saita dinga yinsa kwan gaba kwan baya.
Ta bangaren haidar kuwa haka kawai ya samu kansa da nazarinta,tun daga halitta zuwa yanayin aiki,shi kansa baisan nazarin na meye ba,amma ya kasa dainawa ko hana kanshi,har zuwa lokacin data sanya hannu zata sauke prying pan,wanda sam ta manta da ya kamata tasa wani tsumma ko safar hannu ta kitchen dake rataye kafin ta sauke din,sai ta saka hannun nata kawai kai tsaye.
Cikin tsananin jin zafi ta saki prying pan din tana sakin qara,abinda ke ciki ya tarwatse,radadi da zugi ya soma ratsata,ta fara yarfe hannunta.
Cikin sauri ya iso wajen kamar qiftawar idanu,yasa qafarsa da sauri ya ture frying pan din wanda saura kadan ta sanya qafarta still,hannun nata ya kama da sauri yana dubawa,tuni qwalla ta fara cika mata idanu saboda zafi,tuni yatsun sunyi ja,sai yajata suka isa bakin famfo ya kunna ya tara hannun a qasan ruwan dake zuba,a hankali sanyin ruwan ya fara ratsata,radadin ya tafi,saita lumshe idanu tana sakin ajiyar zuciya,dai dai lokacin da yake kallon fuskarta da lamsassun idanunta ke a rufe har yanzu.
Abinda bata so yawan kusancinsu,duk sanda yayi kusa da ita sosai haka takanji wani nauyi daga gangar jikinta har zuciyarta,sai taji kamar ya cika wajen da kwarjininsa da haibarsa,bugun zuciyarta yakan dadu,jiki da zuciyarta yayi wani laushi,ba zata iya fayyace me takeji game dashi ba,saidai ta sani cewa ya rage jin haushi da tsanarsa tun ranar bikin qara musu girma,maimakon haushinsa sai bugun zuciya da jin nauyinsa daya maye gurbi,haka kawai taji wani rauni na mamayarta,hakan ya baiwa qwalla damar ratsowa ta gefen idanunta.
A lokacin yana tsaye yana qarewa fuskarta kallo,yaga wasu abubuwa sama fuskarta da suke kama da nashi,wanda ko qannensa da suka fito ciki daya basuyi tarayya wajen kamanceceniya a su ba,a baya sanda take qarama idan aka fadi akwai kamannin,yana kallon mai fadar ne a matsayin me matsalar gani da kyau,amma a yanzu a dai dai wannan lokacin ya yarda kai tsaye babu musu.
Yatsunsa biyu ya saka a hankali ya dauke qwallar dake fitowa din
“Raguwa….kuka kikewa ciwon?,haka kikewa hajja?” Yaji ba zato ya fada,ita kanta sai data bude idanunta da gashin idanun suka jiqe da hawaye ta dubeshi mamaki fal qasan ranta,suna hada idanu ya janye idonsa kamar bashi ne yayi maganar ba,saiya saka hannu ya kashe famfon,ya jawo hannun saitin bakinsa ya soma karanta mata fatiha babu adadi yana tofa mata,daga ita har shi babu wani me cewa komai,sai hada idanu da sukanyi lokaci zuwa lokaci.
23/10/2021, 08:47 – ๐๐ป๐๐ป: 33
Karo na qarshe da suka hada idanun saiya saki hannun nata,yaja mata kujera ya mata nuni da idanu kan ta zauna a kai,a sanyaye kuma a hankali ta zauna din,saiya juya ya tsugunna yana tsince barin da tayi,ya gyara komai,kawai sai tagq yaci gaba da girkin
“Ya rabb…” Ta fada tana lumshe idanunta cike da zallar mamakin ya haidar din,dama zai iya amsar mata girki saboda kawai ta qone?,sauqin kaine ko ganin dama?,saboda dai su sun riga da sunsan halinsa,mai fada da kaushin hali shine tambarinsa a wajensu,bata gushe ba tana binsa da kallon mamaki har sanda ya kammala,yana juyowa suka hada ido,karon farko data ji wani abu me kama da kunya ya kamata,saboda kamata da yayi tana kallonsa,sai ya basar kawai yana riqe da plate din ya miqa mata daya,sauran kuma yayi hanyar fita dasu.
A daske a wajen take bin farantin da kallo,ya hada komai perfectly,duk da dama ta kusa gama komai din,amma shima yayi qoqari sosai,ba yunwa take ji ba,amma sai taji tana sha’awar taste dinshi,don haka ta sanya hannu ta diba takai bakinta.
Komai yayi daidai,kamar ita ta zuba seasoning din,a hankali tana ci tana ci sai gashi taci da dan yawa,ta ajjiye plate din tana duba hannunta,bai tashi ba har yanzu saidai alamun quna,hakan yayi mata dadi,tasan kuma sirrin fatihar daya dinga karanta mata ce.
Da kanshi ya dinga gayawa kansa akwai matsala,yana jin tsoron faruwar wani abu,yana ga ya kamata ya maidata gida tun baiyi abun kunya ba,abun kunyar daya tabbatar da cewa hajja saita masa tareren kaf dangi da ‘yan uwa.
Bai taba yarda da zantukan abokansa ba sai yanzu,wani lokaci idan suna irin wadan nan hirarrakin da suka danganci aure,yana dauka shirmensu ne kawai da kuma batawa kai lokaci,har suna ganin ko lafiya ce baida ita?,saboda sun riga da sun saba,dai daiku ne cikin wanda zai zama soja,ya kuma kai mataki da matsayin da haidar din ke kai ba tare da yana mu’amala da mata ba ko kuma shaye shayen abubuwan maye,sai gashi shi din Allah ya tsarkake shi,ya kubutar dashi,ko sigari baya sha bare akai ga barasa da sauransu,game da mata kuwa bai ma tsaiwa ya musu wani dogon kallo,ko yayi dogon nazari a kansu da zaya dami rayuwarsa,hakan ya kawo masa sauqin al’amuransa sosai,ya kuma sake kauda masa duk wani abu game dasu,duk da yasha tsallake tarkunansu,saidai suma suna kama kansu saboda sunsan halinsa,bashi da sauqi sam.
Yana gama cin abincin yayi wanka ya fice,bai dawo ba sai gab da magariba,ganin an kusa kira saiya daura alwala kawai,da niyyar idan ya dawo yayi wanka,sannan ya leqa yaga hannun nata,ya kuma nema musu abinda zasuci,saidai yayi mamaki da yazo tafiya sallah yaga kwanuka kan dining,harta samu qarfin halin yin girki kenan.
Tana dakin taji dawowarsa,saidai bata sa sha’awar fitowa don ta gama duk abinda tasan zai maidata falon,ana kiran sallah ta shiga wanka,ta fito ta shirya cikin hight waisted skert ta shirt mai gajeran hannu wadda ta dace da skert din,ya fidda qugunta sosai tare da plate tummy dinta,gashinta ta taje sosai wanda ta tsefeshi saboda tana period,yawanci haka takeyi,saita tsefe idan zatayi wankan tsarki ta wankeshi sannan a maida mata kitso idan tana ra’ayi.
Kamar daga sama taji sallama a falonsu,saita aje comb din hannunta da take kwantar da gashin nata cikin sauri ta bude qofa ta nufi parlour din.
Dr nasreen ce a tsaye cikin ado kamar yadda take a dabi’ance,kowaccensu fuskarta qunshe da fara’a suka nufi juna cikin murna,don har zuciyarta zahra taji dadin zuwan dr nasreen din,ko banza ta debe mata kewa yau na wasu awanni.
Sai data cikata da kayan ciye ciye sannan ta dubeta cikin mamakin me yasa har yanzu bata zauna ba
“Zauna mana kinata tsaye haka?” Murmushi tayi ta girgiza kai
“Ai banga ta zama ba,dear tana waje fa a tsaye” ido zahra ta fitar
“Kai!,ya shigo mana,me yasa kuma zai tsaya a waje” kai ta girgiza tana qwalalo ido
“Ah wai….ai bazai shigo ba,yasan fa waye mai gidan nan,wannan boss din naki akwai ban tsoro,yasan halinsa sarai….,ki fara shaida masa dai yana da baqo ko?” Saita dan daburce,tana nufin ta shiga dakinsa kenan ta masa magana,tunda ta tabbatar yana dakin tunda ya dawo gidan,dakin da tunda tazo bata taba gigin shigarsa ba,batason tace wani abu da zata dago kome ke tsakaninsu,don haka cikin fara’ar yaqe tace
“Yanzu kuwa zan sanar mishi,ai ba’a bar masoyi a waje ba” tayi qarfin halin tsokanarta,sai ta sake fadada fara’arta tana cewa
“Kema kya fada,shi yasa na kasa zama ai”.
Inda zai yiwu zata faki idanun nasreen ne taje ta sanyo hijabi,to amma yin hakan zai sanya ta saka mata ayar tambaya,dole qanwar naqi tayi qundunbala takuma yi shahadar quda ta durfafi dakin.
Fitowarsa daga wanka kenan daure da towel iya qugunsa,yana tsaye gaban mudubi yana sharce ruwan jikinsa,duk da cewa daga wanka ya fito kuma a tube yake amma ac ke kwarara cikin dakin,kamar baya jin yawan da tayi.
A hankali ta bude qofar dakin ta saka kai,ta daga idanunta a hankali tana wulgasu cikin dakin,saiko suka sauka a kansa yana taje kansa da wani cumb,idanunsa cikin madubin yana kallota,ko kadan bata tsammaci samunshi a yanayin data ganshi ba,yanayin qira da duk wata siffa ta jikinsa ta fito muraren,mai tsayayyen jiki da siffa dake nuna qarfi da mazantaka,da kuma alamun ya horu sosai kan aikinsa,kana ganinsa kasan yana daga qarfe.
Sosai idanunta suka nuna razana muraran,da hanzari ta juya a sukwane ta durfafi qofa,taku uku qwarara ya cimmata,ya sanya hannu ya cafkota tare da birkitota gaba daya,sai gata tayi kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,damshin ruwan dake jikinsa ya ratsa fatar hannunta da wuyanta,tsigar jikinta ta zuba,saiya matseta yana fadin
“Nutsu mana,ina zaki koma a haka kamar wadda wani mugun abu ya biyo,ba baqi mukayi ba?” Ya fada a dake,kasa furta komai tayi sai jikinta dake rawa,saiya yasa hannu ya janyeta daga jikinsa yana ladabtar da ita da kaifaffan kallonshi.
A nutse yake qare mata kallo tun daga yatsun qafarta har zuwa kanta dake gyare cike da baqa qirin din suma,fuska a hade yake dubanta
“Uhummm….,me yasa ko yaushe kike firgita kanki?,tell me,meke baki tsoro a jikina?” Gam ta rintse idanunta,don har ga Allah ba zata iya kallonshi a yadda yake tsaye a gabanta ba,don ita a wajenta bashi da maraba da tsirara,gashi hanya takeso ta samu ta tsere,saiya kada yatsanshi saman fuskarta
“Niba dodo bane?….kinji ni?” Kai ta gyada,sotake kawai ya bata waje ta fita,amma a maimakon haka ma sai taji yana saka lock na jikin qofar yana rufe qofar,saita bude idanunta da sauri,sai kuma ta sake kauda kai,cikin rawar murya tace
“Pls….zanje wajenta….jira take” baiko bi ta kanta ba yayi gaba abinsa,ya bude ma’ajiyar kayansa ya dauko wanda ya dace da ra’ayinsa,ya dawo gaban mudubin yaci gaba da shiryawa,tilas taci gaba da tsaiwa tana jiran tsammani,saidai kuma ta bashi bayane tana duban qofa,hakan ya bashi damar qare mata kallo,lokaci lokaci,yana dubanta yana shiryawa.
Batasan ya gama ba duk da qamshin turarensa mai laushi daya addabeta,har sai data ji yana bude qofar sannan ta ware idanunta a hankali,sannan ta tako ta nufi qofar,dab da shi ta tsaya ganin shima yana tsaye bai fita ba,cikin husky voice dinshi yace
“Ko yaya iyayenka suka yanke maka hukunci,duk boren da zakayi kada ka yarda ka nunama duniya….aikata hakan kamar kana gayawa duniya ne how valueless they are”,sai ya fara takawa yana ficewa daga dakin.
Magana yayi mata me harshen damo,saidai ta fahimceshi sarai,don haka tabi bayansa itama tana gyara yanayin fuskarta.
Ta taras suna gaisawa da nasreen din,daga yanda suke gaisawa kawai ya isa ka gane tana ganin girmansa sosai,cikin ‘yar dariya kasancewarta mai yawan barkwanci tace
“Ai cewa dear nayi yazo muje dubiya….Allah yasa qaruwa muka samu” dan murmushin gefan baki kawai yayi,saidai ya maida dubansa ga zahra,sannan yace
“Wata qila,gatanan kya tambayeta” saiya miqe yana ficewa daga falon.
Dan tabota nasreen tayi
“Kai qawata daga zuwa kiransa yanzu fisabilillahi shine aka shanyani?” Murmushi tayi
“Ayimin afuwa….” Tun kafin ta qarasa tace
“Anyi miki….tun kafin boss yayi aure munsha yin gulmarsa nida dear…mun gode Allah ma da gidansa ke shiguwa,saboda irinsu ko…..basu iya qonewa a love ba,ki gansu a waje kamar gaske,amma a gida…uhmmm” dariya sosai ta baiwa zahra,lallai batasan ya haidar ba da bata fadi haka ba,batajin irinsu so na shagaltar dasu haka,amma saita share zancen kawai suka shiga wata firar.
Tunda ya isa farfajiyar gidan yaga tare suke da major ya sake tamke girarsa sosai,duk da cewa akwai saif a wajen
“Yallabai….irin wannan shanyamu haka?” Major ya fada yana washe baki,wani kallo haidar ya masa sanda yake bawa jafar hannu suna gaisawa,sai da yazo kansa sannan ya amsa mishi
“Da kasan kana da abubuwan yi da yawa ma da baka zo ba,incase nan gaba kaga irin haka ka dinga tafiyarka kawai” saif dai na danne dannen waya yana boye dariyarsa,shi yasan qarshen alewa qasa,don major ya dage ne kawai saiya biyosu,amma yasan haidar din bazaiyi maraba da zuwanshi ba,jin amsar daya bashin sai yayi shiru baice komai ba.
Daga nan inda suke tsaye haidar din ya qwalawa mai gadi kira,ya bashi umarnin bude guest room sannan suka dunguma zuwa ciki.
Zuwan dama ya shafi ayyukansu ne,tattaunawa zasuyi ta musamman,don haka kai tsaye haidar ya shiga abinda ya tarasu,don shi sam bai farinciki da zuwan major,shima daya lura da hakan suna gama maganar data tarasun ya musu sallama,yace yana da wani uzuri,akwai inda zashi.
Yana fita saif ya qyalqyale da dariya yana kallon yadda haidar din ya hada girar sama da qasa
“Mai master….wannan wai duka kishin ne haka?,lallai fatima ta ciri tuta…wannan so ba qarami bane” dashi da saif din duka sunsan magana yake gaya masa a fakaice,saiya masa wani irin kallo ya bude baki
“Sosai,ko laifi ne hakan?….akan me ma zaku daukomin wannan kwarton ku shigomin dashi gidana….kai J,haka ka hadoshi da matarka a mota daya kuka taho?” Ya jefawa jafar tambayar,bai amsa mishi ba shima illa danne dariyarsa da yakeyi,sai haidar din ya jijjiga kai
“Next time zan gaya mata,duk sanda zaka dauki wani qato a motarka to saika sama mata abun hawa,koka bata motar tayi driving ku kuje ku hau ta haya….kai kuma” ya nuna saif
“Ka kiyayi haduwarmu wallahi” saiya miqe yana ficewa don sawa a amso musu drinks.
Sun dan jima don basu tafi da wuri ba,sai daya sallamesu sannan ya koma cikin gidan.
Cikin sauri take kammale falon da kwashe kwanukan zuwa cikin kitchen,don bataso yazo ya risketa,nauyi yake sanyata ji haka kawai duk sanda suka hada wajen zama.
Kallo daya ya mata ya dauke kai ganin yadda ta zumbula uban hijabi
“Ki shirya jibi zamu wuce gida” ya fada sanda take qoqarin wucewa kitchen,daidai sannan wayarsa ta dauki ruri ya soma qoqarin cirota daga aljihu.
Ajiyar zuciya ta sauke tana jin dadin zancan komawarsu,tayi kewar ‘yan gidansu gaba daya,musamman yasira dake ranta,wadda sukayi sallama randa zasu koma haihuwa ko yau ko gobe,tana ta zuba idanu amma shuru bataji ance ta sauka ba,wayarta kuma ya rasa me matsalarta yau kwana uku taqi daukan layi,so take duka saita koma ta bayar a duba mata.
Sunan hajja daya gani saman wayar yasa ya samu waje ya zauna sannan ya daga wayar,a aladabce yayi sallama kana ya soma gaidata,saida suka gama gaisawa sannan tace
“Kai daga baka aron diyar mutane sai ka yiwa mutane dif?,an gaya maka haihuwar yasira yau kwana uku ba’a samunta a waya amma banji daga gareku ba,halama baka shaida mata ba…..to ka dawomin da jikata maza maza ayi taron suna da ita” ya soma gajiya da rigimar tsohuwar,yana ji cewa zai fara nuna mata shima dan yaune ko zata dinga shafa masa lafiya,don haka cikin dakakkiyar muryarsa yace
“Zamu dawo,amma ba yanzu ba”
“Me kace?,to baka isa ba,ai dama aro na baka,na taimaka wa wannam shegen baqin ran naka,wala’alla idan kanajin motsin dan adam kusa dakai ka rageshi”
“Nidai dawowa ba yanzu ba,matatace….kuma qarqashin ikona take” daga haka ya yanke wayar,saboda iya tsiya ma saiya kashe wayar gaba daya,yadda ko zata sake kira ba zata sameshi ba.
Yana sane yayi mata haka,kuma a niyyarsa a wasance ne,amma sai yaji zancan daya gaya matan ya zauna har cikin zuciyarsa,saiya tsinci kansa da yin mita shi daya
“Wai aro….kaman wani yaro” ya furta qasa qasa a fili,wannan karon shima sai yayi wasa da hankalin tsohuwar,zata ga dan zamani kuwa,da haka ya miqe ya dauki duk abinda yake buqata a falon ya wuce.
Har zai shige dakinsa saiya tuna hajjan ta gaya masa ba’a samun wayarta,don haka ya sauya akalarsa zuwa dakin nata.
Daga bakin qofar ya tsaya yayi knocking,ba’a jima ba aka bude qofar a hankali,fuskarta tarwai a hasken qwan dake corridor din,tayi rolling da wani pink mayafi saman doguwar rigar baccinta mai kauri da laushi data sauka har qasa,sosai mayafin ya haska fuskarta,qamshin turarenta na busowa tun daga cikin dakin da kuma wanda ke jikinta zuwa inda yake tsaye,saiya sauke boyayyar ajiyar zuciya,muryarsa tayi laushi qwarai qwayar idanunsa cikin nata yace
“Me ya sami wayarki?” Dan yamutsa fuska tayi wanda hakan ya qara mata kyau ba tare data sani ba
“Hakanan ta daina daukan layi”
“Me yasa baki gayamin ba?” Yayi mata tambayar dashi kansa yasan batayi ma’ana ba,qila hakanne ya sanyata yin shuru itama tana juya maganar,saiya waske da fadin
“Daukomin ita” juyawa tayi a nutse ta koma cikin dakin,yabi takunta da kallo.
Batayi koda minti guda ba ta qaraso da wayar,hannu biyun data sanya ta miqa masa yasa ya bita da kallo,garin hakan bai kula ba ya hada da hannunta,ta zame hannun nata da sauri sai wayar ta subuce zata fadi a qasa,cikin zafin nama ya tarota da hannu daya yana ambaton
“Bismillahi” dan ja baya tayi kadan,sai taga ya juya kawai yabar wajen ba tare da yace komai ba.
Maida qofar itama tayi ta rufe tana sauke numfashi,wanne irin taushi hannunsa keda shi haka?,take tambayar kanta,sai tasa yatsa ta dungure kanta da kanta tana fadin
“Shiga hankalinki”.
_ZAFAFA BIYAR_๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ๐ค๐ฝ
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโi yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa…_
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_kujerar tsugunno_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata ba, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koโina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko _Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โdai_
23/10/2021, 08:48 – ๐๐ป๐๐ป: 34
Bayan ya shiga daki saiya aje wayar a gefan bedside drower dinsa,ya shiga bandaki yayi shirya kansa,sannan ya dawo ya shimfida abun sallah ya tada sallah,yakanyi sallah raka’a biyu ko hudu duk sanda xai kwanta,musamman idan yana jin gajiya a jikinsa wadda yake saka ran zaiyi wuya ta barshi ya iya tashi cikin dare yayi sallah.
Ya dan jima yana addu’o’insa,wanda ya tabbatar da cewa sune makaminsa a rayuwa,su suka hana a cimma sa,banda hakan yasani cewa da tuni tarin maqiya abokan gaba da masu neman irin matsayinsa sun dade da kwantar dashi.
Sai daya sauya kayan bacci sannan ya isa gadonsa bayan ya kashe qwan dakin,yana shirin jan duvet dinsa ya rufa idanunsa suka sauka kan wayar tata,saiya saka hannu ya daukota ya kuma kunnata,ta daidaita sanda ya kwanta sosai saman gadon,yasa hannu ya budeta,don babu passoword ko security pattern.
Hotonta ne ya bayyana tarwai,ya mamaye fuskar wayartata,tayi matuqar kyau cikin riga da skert,tayi rolling saman kanta,fuskarta dauke da murmushi daya bayyana jerarrun haqoranta,tun daga sama har qasa aka dauki hoton,qafafun nata cikin high hill mai igiya,jan qunshin salatif dake qafarta ya fito sosai,haka na hannunta dake saman cinyarta.
A hankali ya dinga bin hoton da kallo kafin daga bisani ya sauka ya shiga gallery dinta kai tsaye.
Hotunanta ne birjik a ciki,wani ita kadai,wani da ‘yan gidansu,wani da qawayenta,sosai ya dinga bin hotunan yana musu kallon qurilla,irin kallon dashi kansa bai san ya iyashi ba,irin kallon da bai taba yiwa kowacce diya mace irinsa ba,duk abinda ya kalla tattare da ita hakanan sai yaji yayi masa,sai yaji nutsuwa da kwanciyar hankali,wani side na zuciyarsa na gaya masa kadan kadan
“Matarka ce”.
Ya jima kan wani hotonta da tayi da wata farar armless shirt,da straight skert,kayan sunyi masifar fidda qirar qirjinta da qugunta,kanta babu dankwali sai manyan kalba guda uku da tayi ta saukar da jelarsu,daya lura da kyau a falon hajja akayi mata,kuma da alama batasan an dauki hoton ba,haka kawai sai yaji ranshi nadan baci bayan ya gama kalla din daya tuna cewa gidan nasu akwai samari,kuma suna iya shiga sassan hajjan kowanne lokaci,sai yaja dogon tsaki ya dannawa hoton delete,kana ya kashe wayar ya aje a gefansa wata kasala.na saukar masa,ya soma saukar da ajiyar zuciya a jejjere kamar yaron goye da yaci kuka ya qoshi.
Ya jima yana juyi zuciyarsa na gaya masa abubuwa da dama,ciki kuwa harda zai rasa damarsa ne,ya kamata ya tabbatarwa da kansa da ita din kanta cewa matar tasa ce da gaske,tsahon lokaci a haka kafin ya samu bacci ya daukeshi.
Washegari bayan sallar isha,yana saman dining don cin abincin dare,dai dai sanda take miqewa ita kuma ganin ya zauna din,sai yasa hannunshi ya dauko qaramar leda mai dauke da tambarin wani babban shagon saida wayoyi ya miqa mata,duk da batasan meye a ciki ba tasa hannu biyu cikin mamaki ta karba
“Na gode” ta fadi tana sauka daga wajen da dan saurinta,saiya dan bita da kallo,yana ankare da ita daga safiyar yau zuwa daren nan kamar walwalarta ta qaru,yasan kuma qila hakan baya rasa nasaba da zancan tafiyarsu gida,saiya kauda wannan tunanin yaci gaba da cin abincinsa.
Tana shiga daki ta fada saman katifa gaba daya,sannan ta zazzage ledar tana duba abinda ke ciki.
Waya ce tsaleliya,mai azabar kyau,wayar data jima tana bata sha’awa,saidai bata da isassun kudi da zata siya,sunyi magana tun kwanaki da yaya sadiq,yace idan ya samu kudi zai siya mata,basu samu bane kudin yadda ya zata shi yasa taji shuru.
Tsalle ta buga ita kadai tare da dan qaramin ihu,sai kuma ta nutsu tana zare idanu da rufe baki don kada ya jiyota,take ta sanya layuka da memory dinta daya dawo mata dasu da safe,sannan ta jona mata chargy,ta dawo ta zauna tana jiran ta cika.
******* ***** ********
Shirin tafiya gida kawai take hankalinta kwance cikin zaquwa,musamman data kira taji cewar yasira ta haihu,randa kuma zasu koma gidan saura kwana biyu suna kenan,ta gama tsarawa sai washegarin suna da kwana daya ko biyu zata koma makarata,don tasan za’a hadu sosai da ‘yan uwa da aka jima ba’a hadu ba,tunda anan gidansu za’ayi taron.
Ana ya gobe ranar da yace zasu tafin ta cika haka ta wuni tana zumudi,fuskarta ta cika da walwala,ko falon ma bata fito ba,tana can daki tana charting da ‘yan gida.
Hakan ya sanya ranar shi kadai yahau dining cin abinci,sai yakejin banbarakwai yau din,ya dinga kallon hanyar dakin nata amma shuru babu ko motsinta,baisan me ya sanya yaji baijin dadin zaman ba,ya dinga jan tsaki,ya fahimta rawar kai da zumudin tafiyar takeyi,saiya sake jan wani tsakin kawai ya dauki sauran abincin da bai gama ci ba ya wuce daki dashi.
*_WASHEGARI_*
Tun bayan sallar asuba take zaune saman abun sallarta bata tashi ba,agogon dake dakin yana nuna mata qarfe shida ta miqe,ta soma gyara dakin tare da tattare da rufe duk abinda tasan zai iya qura bayan babu kowa a dakin,daga nan ta yiwo falo,tana yi tana duba hanyar dakinsa ko zataji motsinsa,alamun ya tashi ko kuma wani abu,saidai har ta gama gyara falon,ta wuce kitchen ta gyarashi shima,ta killace dukka kwanukan ta gogesu da kyau ta maidasu muhallinsu yadda ya dace,ganin cewa tafiya zasuyi yasa bata dau wani girki mai tsaho ba,chips kawai ta soya ta dafa tea,ta koma daki ta shiga wanka.
Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da skert,purple ce da adon yellow me haske,ba qaramin karbarta kayan sukayi ba,sai data gama sannan ta sake fitowa zuwa kitchen ta debi abincin tadan ci,duk da cewa dazun ta kasa ci saboda tana zaton zai iya cewa ya shirya ta fito.
A kitchen din ta tsaya ta gama ci,tanayi tana kasa kunne ko zataji motsinsa,saidai harta gama bata ji ba,zata gifta dakinsa nan ma ta kasa kunne amma shuru,haka ta wuce nata dakin,saita dauka wayarta tahau watsapp donta rage lokaci,tana saka ran kafin ta sauka ya fito.
Ta kuwa samu kusan dukansu a online,suka shiga hira tana gaya musu suna hanya,hirar tasu tasaka mata zaquwar su tafi din,batasan ta jima a zaune ba sai data duba agogo,sha daya har tayi,saita fidda idanu tana aje wayar,ta miqe ta bude qofar dakin ta fito falo,shawagi ta danyi har zuwa kitchen ko zataga alamun da zai nuna mata ya tashi,saidai babu wata alama,hakanan ta sake komawa daki tanajin kamar ta shiga dakin nasa taga meya riqeshi haka.
Sha biyu na rana takai maqura wajen qaguwa,kamar zata saki kuka haka ta dinga ji,ta dinga safa da marwa tsakanin dakin zuwa qofar nashi dakin,tayi attempting na shiga dakinsa yafi sau biyar,saidai data isa qofar dakin saita kasa shiga ta juyo ta koma.
Qarfe daya dai dai na rana haqurinta ya qare,ta tsaya qofar dakin nasa tana saisaita kanta,tare da baiwa kanta qwarin gwiwa,a hankali ta dora hannunta saman handle din ta murda qofar ta bude.
Dai dai lokacin yana kwance rub da ciki cikin lallausan bargonsa yana duba saqonni cikin wayarsa,ya lulluba har kusan kansa,wanda duk wanda ya shigo xai dauka ma duka har kan nashi ya rufa,duk da acn dake kadawa cikin dakin amma jikinsa babu riga,sai wani boxer dake a jikinsa.
Duka yau bashi da intention na fita,don ya gama da office gaba daya,sun sanya date ma na tafiyarsu,kowa an bashi damar zuwa ya shirya sosai,yasan kuma yau din ya soke tafiyarsu saboda hajja,don haka ya yanke shawarar yini a gida ya huta sosai.
Tsayawa yayi da replying massages din sanda yaji an turo qofar ba tare daya waiwayo ba,zuciyarta na wani irin bugawa ta dake tayi sallama,saiya juyo rigingine,wanda hakan ya basu damar ganin juna sosai.
Kowanne sai da yaji shock a jikinsa,yanayin data ganshi babu riga ya tsoratar da ita,wanda hakan ya bayyana ingarman qirjinsa,ya kuma bayyanar da tarin gashin daya lullubeshi,mai laushi kamar shima gyara yake masa,inda shi kuma kwalliyarta ta dauki hankalinsa,wanda tsabar zaquwar tazo ta sameshi su wuce yasa ta manta ko dankwali bata daura ba bare aje ga batun mayafi,idanunta ta rintse sannan tace
“Ina kwana….na shirya tun daxun” dan ture bargon yayi,ya kwanta rigingine sosai,saidai ya tallafe kansa da hannayensa guda biyu ta qeyarsa,yadda zai bashi damar kallonta sosai
“Me kika ce?” Ya fada da lallausar muryarsa data soma canzawa saboda wani yanayi daya tsinci kansa,sake maimaitawa tayi harda dan daga murya don yafi jinta sosai.
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace
“Na soke tafiyar yau” gaba daya ta bude idanunta gami da wara su a kanshi cikin yanayi na tsoro,wanda hakan ya haifar masa da wani abu cikin jikinsa,saiya lumshe idanu sannan ya bude sanda duka a kanta sanda take fada cikin rudewa
“Amma fa hajja ce tace”
“Hajja ke aurenki?” Ya jefa mata tambayar data sanyata yin shuru,sake maimaita tambayar yayi,a hankali tace
“Amma ita ta…..” Sai kuma ta kasa qarasawa,ta canza salon zancan da
“Aro na ta baka,kuma tace ka maidani,bai kamata daga aro ka riqe mata ni ba….” Zancan nata saiya bashi dariya,can qasan ransa ya dara,me yasa suke son maidashi wani sakarai,amma a saman fuskarsa babu alamun dariya,hakanan yaji cikin zuciyarsa yana son nuna mata gaskiyar magana,ya kamata ta fahimci gaskiya ya gayawa kansa,ko yaya ya kamata ta tsorata tasan kuma meye matsayinta,don haka yana daga cikin bargon yace
“Zo ki gani” saita zuba mishi idanu tana dubansa,yayin da shi kuma ya dauke kansa daga kanta,ya maida gefansa kamar mai kallon wani abu.
A hankali ta fara takawa zuwa inda yake kwancen,zuciyarta na gaya mata akwai abinda zai nuna matan,gefansa ta tsaya,tana niyyar cewa gani…..ba zato ba tsammani taji gaba daya an fincikota,kafin ta gane abinda ke faruwa sai gata kane kane saman qirjinsa,ya matseta gam,sautin muryarsa deep inside har ears taji yana fadin
“Daga ke har hajjan bansan a inda kuka gano ana baiwa mutum aron matarsa ba,idan ita ta manta ke bari na baki tambarin da zaki dinga tuna u r my property” kafin ta ankara ya soma aika mata da wasu hot kisses,tun daga cikin kunnenta zuwa wuyanta,saiya fara yamutsata son ranshi da dukka hannayensa biyu,tuni yakai hannunshi muhallin dake tsole masa idanu,abunda ya kusa tafiyar da numfashinsu duka su biyun,zahra tsananin tsoro da firgici,yayin da shi kuma tadda abun fiye da yadda idanu ke iya gani ne,cikin sakanni ya soma fita daga saitinsa.
Mataki bayan mataki ya dinga bi yana wucewa,duk sanda yaje wani mataki sai zuciyarsa da gangar jikinsa ta buqatu zuwa mataki na gaba,ta bangaren zahra gaba daya duniyarta ga gigita,saboda bijirowar abinda bata taba tsammata ko.kawoshi cikin tunaninta ba,koda a cikin mafarki kuwa,hakan ya sake razanata,ta dinga qoqarin tattara dukkan qarfinta daya rage tana yunqurin turashi daga rumfa da kuma babakeren da yayi mata,saidai ina,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,a banza wai man kaza.
Tsoro sosai ya shiga bata ganin yadda ya soma juye mata zakin sosai,ya fara fita daga hayyaci da kamanninsa,ya koma yin komai da zafi zafi kamar mayunwaciyar dabba,mazantakarsa da jarumtarsa kawai yake nunawa ba tare dashi kansa ya sani ba,tsoro sosai ya cikata da fargaba,dana sanin shigowarta dakin ya fara mamayeta.
Bata gane abun da gaske bane sai daya fara neman hanya ษoษar,ta tabbatar idan dabararta batayi aiki ba tana ji tana gani kome zai lalace mata,saita saki kuka sosai,wanda dama tun daxun take yinsa,saidai baiyi qarfi ba kamar yanzu da take neman agaji da gaske,kiran sunan hajja da umminta data fara yi shine ya karyashi,ya kuma dawo dashi hayyacinsa,a hankali saiya fara dawowa hayyacinsa,ya kuma soma tuna abinda yake shirin aikatawar,sai duk aka zare masa wata laka ta jikinsa,saiya zame gefe guda,ya kuma hanata tashi sanda take yunqurin tashi cikin kuka,sukaci gaba da kasancewa a haka har tsahon wani lokaci da kukan nata ya tafi gaba daya,sai dan zafi zafi da take ji daga can,duk da ba wani me yawa bane.
Idanunta ta lumshe sanda ya miqe ya sauka daga kan gadon,bandaki ya shiga yana jin wani abu kamar jiri jiri na dibanshi,hakanan yayi sakayau kamae iska zata kwasheshi,ruwa ya tara mata sosai mai dumi,don ya sani daga shi har ita wanka yahau kansu,bai jima ba ya fito
“Ki shiga toilet akwai ruwa a ciki” daga haka ya nufi qofa ya budeta ya fice.
A falo yaci burki,saiya samu daya daga cikin kujerun dining ya zauna akai,yasa gwiwar hannunsa saman cinyarsa yana dafe kansa da dukka tafukan hannayensa,wani iri ciwo kan nashi yaji yana masa,dukka jijiyoyin kansa sun tashi,idanunsa da suka sauya launi har yanzu basu daidata ba,duka kansa ya cushe ya kuma kulle,ya rasa wanne tunani zaiyi,miqewa yayi kawai ya koma dakinta,ya bude nata toilet din ya shiga ya hada nashi ruwan wankan.
A hankali ta sauka daga gadon tana karantar kowanne canji daga jikinta,ta soma takawa zuwa bandakin,yanayinta yadan sauya saidai ba sosai ba,hakan shi ya tabbatar mata bai gama cimma manufarsa ba,don haka data shiga din ma ruwan dumi kadan tayi amfani dashi tajita normal,sai tayi wanka bata jima ba ta maida kayan jikinta ta dawo cikin dakin.
Idanu ta dinga rabawa tana cike da fargabar fita,don batasan ta inda zasu hadu ba idan ta fitan,gaba daya ita wani irin tsoronsa takeji,sanda taji an turo qofar dakin sai taji kamar ta zura da gudu,sai kawai ta sulale ta durqushe a wajen.
_____________________________
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI….! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN โDAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234ย 803ย 081ย 1300/+234ย 808ย 540ย 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:48 – ๐๐ป๐๐ป: 35
Cikin wata nutsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan da yayi yake takowa zuwa cikin dakin,hannunsa dauke da babban mayafinta da kuma abun sallah,sai daya fara shimfida abun sallar sannan ya qarasa gareta
“Kinyi alwala?” Ya tambayeta,tana daga duqen tana hawaye ta gyada masa kai
“Ohk….getup,tashi muyi sallah” ya fada yana miqa mata hannusa,a hankali ta daga kai,maimakon ta bashi hannun yadda ya buqata saita fuske masa,ta miqe tsaye a hankali tana jin yadda cinyoyinta suke so su fara tsami,riqe dantsen hannunta yayi,ya tsaidata sosai,sannan ya ware hijabin hannunsa ya sanya mata,saita isa da kanta saman abun sallar ta tsaya,don ta fuskanci jam’i yakeso suyi,saboda guda biyu ya shimfida.
Jallabiya ya ciro ya sanya,sai qaramar hula wadda ke tsayawa iya kewayen tsakiyar ka,ya feshe jikinsa da turarensa na da’iman,sannan ya shiga gaba ya tayar musu da sallar.
Koda suka idar saita miqe da niyyar tafiya dakinta,cikin sassauqar murya ya bata umarnin ta hau gado ta kwanta ta huta,sai tayi kamar bata jishi ba,miqewa yayi yana tattare abun sallarshi,sannan ya cimmata tana dab da fita a dakin.
Cak ya dagata ya rabata da qasa,ya isa da ita saman gadon ya kwantar da ita yana dan nishi
“Ashe dan banzan nauyi ne dake?,ke kika jawo na kusa miki aika aika,sannan zaki fice ki qunshe kanki a daki,salon ciwo ya rufeki ki ja mani magana wajen waccar tsohuwar,tace naci amanarta ban kula da ita ba” rau rau idanunta sukayi suna tara qwalla,lallai ma ya haidar din nan,ya cita wasa da yawa,amma babu komai,saita rama,saiya saka dan yatsantsa saman labbansa yana duban qwayar idanun nata yace
“Shshshsh….keep silence please”lumshe idanunta kawai ta dinga yi a hankali har ta rufesu,don tasan bata da wani sauran abun fada,tana gama rufe idanun nata yaja mata bargo ya lullubeta,sannan ya miqe a hankali ya fice daga dakin.
Da kansa ya dauki mota ya fita nema musu abinci,haka ya dinga tuqi a titin a kasalance,ya sauke dukka glass din side dinsa iskar waje tana shigo masa,wadda ke cakude da sanyin tasowar hadari,don ko rana babu a garin sosai,sai daya gama shawaginsa sannan ya zaba wani gidan abinci ya musu takeaway,ya kuma biya na dare da zasu kawo mishi har gida,don bai saka ran zata iya girki ba,daga dan tabata kadan duk ta wani langabe,saiya saki murmushi shi kadai yana shafa sumarsa zuwa habarsa sanda abinda ya faru ya dawo masa,idanun hajja kawai yake hangowa a lokacin ace taga abinda yaso aikatawar,tabbas da kashinsa ya bushe,tijara kuwa yasan sai wadda bata tuna ba.
Sanda ya koma ma bata tashi ba,saiya zauna yaci nasa abincin shi kadai,ya zauna yana duba labarai daga ingantattun jaridun dake kawo labarai online,saboda ya sake samun information da haske kan aikin dake gabansu.
Ranar gaba daya wasan buya dashi takeyi,gudunsa take hakanan wani tsoronsa take ji,tunda ta samu ta fice daga dakin nashi bata sake bari sun hadu ba,iyaka idan yayi knocking xai gaya mata ga abinci nan ta fito taci,sai ta dai daici ya gama ci sannan zata fito ta diba ta koma daki.
Ta gefe guda gaba daya hankalinta ya karkata zuwa gida,saidai bata ga alamu ba,bata kuma sake jin ya tada maganar ba,gashi a yanzun bata jin zata iya tunkararsa bare tayi masa zancan.
Kwana na uku da faruwan abun,da wani yammaci yana zaune a falo shi kadai,yana dai xaune ne kawai,amma sam bayajin dadin zaman,wanda shi kansa bazaice ga dalili ba,lokaci lokaci yakan dubi sashen qofar dakinta,tun ranar gaba daya hankalinsa da tunaninsa yayi kanta,baisan me yasa ba,amma baya yin wani qwaqwqwaran awanni bai tunata ba,duk data yanke daga hulda dashi,shi kuma bai tsawwala ba,saboda baison ya fiya shiga rayuwarta da yawa ya zamana akwai takura.
Wayarsa ce ta dauki tsuwwa,saiya miqe ya cirota daga chargy yana dubawa,hajja ce dai,murmushi ya saka,yasan darun nata ta kira tayi masa,don haka tun kafin yakai wajen zamanshi ya daga wayar,ya soma gaidata ta dakatar dashi
“Ba gaisawa na kiraka muyi ba,nace maka ka dawomin da yarinya amma kayi kunnen uwar shegu dani ko?,wai shinma ni din sa’arka ce koko yaya aka soma?”murmushi yayi wanda ya tabbatar ta jiyoshi
“Haba tsohuwa….na gaya miki fa matata ce….ya za’ayi ace ni za’a baiwa aro,ai saidai ni na baku….idanma naga dama kenan”
“Qaniyarka,nace qaniyarka…..auren bani na hadashi ba kuna tsalle tsallen banza?….” Saiya datsi numfashinta
“To kuma yanzu tsalle tsallen qauna muke…..basai a barmu ba muyi rawar gaban hantsi ba,koda mun dawo ma dan wankan da nake samu tana min Allah idanu xaki saka mana ki hana ruwa gudu….” Dogon salatin data dauko shiya tsaida zancan da yake,dariya irin wadda ya jima baiyi ba ta taso masa,ya danneta sosai
“Hajja….dama kinyi shuru,kin kuma qyaleni,don kin ganta a kusa dani abinci ma zata bani….ki gaya mata ta rage bani abinci da yawa kada mu dawo ki kasa ganeni”
“Ke zahra’u….kinci qaniyarki….qaniyarki nace” katse wayar yayi yayi dariyarsa son ransa,sai yaji ransa fes,ya samu waje ya zauna yana murmushin tsiyar da ya yiwa hajja,ya tabbatar bashi yaci,ya kuma janyowa zahra jagwal.
Kamar ance ya daga kanshi saiya hangeta bakin qofar dakinta,da alama taji duk yadda sukayi da hajja,kanta ta dauke yayin dashi kuma ya sassauta murmushin fuskarsa,tun daxu take dakon jin fitarsa ta fito taci abincin rana daya ce mata taci amma taji shuru,ganin babu alamun zai tashi,ga yunwa zata hallakata shine kawai tayi shahada ta fito.
Baice mata uffan ba harta diba abincin zata wuce yace
“Zo nan” dan hade rai tayi kafin ta juyo ta maida fuskarta dai dai,saita qaraso,ya dubeta
“Zauna nan kici….daga yau duk sanda kika sake rufe kanki a daki….zan balle qofar na shiga,kuma abinda xai biyo baya bazai miki dadi ba,don banga abinda xaisa ki ringa kulle kanki ba anan” narke fuska tayi,yunwa takeji sosai,kuma bata jin xata iya cin abinci a gabansa,kamar ya karanceta sama taka taji yace
“Eheeennn….idan xaki ci abinci kici,kaman bake muke bawa abincin ba a baki muna share miki majina a hanci” da sauri ta daga kai ta dubeshi,sai suka hada idanu,ta sake kautarwa da sauri saboda yadda ta kafeta da idanunsa dake mata kaifi da yawa,kai ya gyada mata alamun tabbatarwa
“Yesss…..ba zaki iya tunawa ba,saboda a sannan kinyi qanqanta da yawa…..kukan kitso…kukan wanka duk kin iya,da kika girma kuma sai kika zama mai tsiwa da taurin kai….right?” Ya qarashe da tambayarta,sosai maganar ta mata nauyi ta kuma bata kunya,zata iya tuna wani abun,amma wani abun ba zata iya tunawa ba,hakanan taji tana son sake jin wani abu daga bakinsa,mutum ce dakeson labarin quruciyarta,tana son a dinga gaya mata abubuwan da tayi zamanin quruciya wanda ita batasan ta yisu ba,ya karanci hakan akan fuskarta,amma bai sake cewa komai ba,saidai ta sanya cokali ta soma diban abincin a hankali tana taunawa,yayin daya lafe jikin kujera kamar mai kallo a tv,saidai ita yake satar kallo time to time.
Da magariba yayi waya aka sama masa ticket na jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano qarfe biyu na rana,bai shaidawa zahran ba ita kanta sai washegari daya dawo daga sallar asuba,haka nan wannan karon sai taji bata wani daukin tafiyar sosai,haka ta sake abinda yake da buqatar a shirya din,zuwa sanda ya gaya mata xasu fita ta kammala komai,ta yafa mayafinta,ta janyo akwatinta tayo falon.
A tsaye ta sameshi tsakiyar falon yana amsa waya,ya baiwa qofar da zata fito din baya,tun kafin ta qaraso ta gama qare masa kallo,sanye yake da wani trouser da shirt,sai high top takalminsa daya dace da kayan jikinsa,tun bata ga fuskarsa ba amma ta tabbatar da cewa shigar ta amsheshi,ta qara masa kwarjini.
Ta gefansa ta raba zata wuceshi,sai taji an kama hannunta dake riqe da majanyin akwatin matafiyar da take ja,waiwayowa tayi sai suka hada idanu,ya mata alama data saki,don haka ta zame hannunta daga cikin nashi a hankali,ya taka ya biyo bayanta yana ci gaba da yin wayarsa.
Dukkansu a baya suka xauna,driver ne ya jasu,wanda idan ya kaisu airport zai dawo da motar ne gida.
Ko a cikin jirgi ma babu magana tsakaninsu,saidai lokaci zuwa lokaci kowa ya kama dan uwanshi yana satar kallonsa,daga bisani ne haidar ya tanka
“Idan na sake kamaki kina satar kallona saina tsole idanun nan naki” gefe tayi da kanta,ciki ciki tace
“Da wanne idon mutum yasan ina kallonshi” baice komai ba amma taji kamar sautin fitar murmushinsa.
Suna sauka a aminu kano airport driver ya daukesu sai gida,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,tafiyar kusan minti arba’in ita ta kawosu gida,wanda tun daga harabar gidan tasan tabbas taro ake,saboda jama’a da kuma rumfunan da aka kafa,indai lissafinta yayi dai dai yaune sunan yasira kenan,harga Alla ta fidda rai data ji bai sake tada zancan ba,shi yasa ta daina lissafin ma.
Zumudi fal ranta ta saka hannu xata bude murfin motar,sai taji an dafe hannun nata,ta waiwayo da sauri idanunshi na akanta,hakanan tana iya jiyo hucin numfashinsa sosai saman fuskarta saboda yadda yake dab da ita,da wata irin kwantacciyar murya taji yace
“Ki nutsu da kyau,kada ki manta ke din wacece,banason yawo jiki a bude da sunan kina cikin gida….ki kiyayemin mutuncin igiyata” gaba daya ita zancan nauyi ma yayi mata,saita maida kanta daya side din,daga nesa tana hango su salma suna kai kawo,da alama hidima ta dauki zafi
“Soja baya son kawo qorafi ko kawo uzuri,just be obedient to my commands” cikin ranta take mitar ance masa a bariki ake dazai soma lissafa mata wasu qa’idoji,bata gama wannan ba taji ya zame wayarta daga hannunta,yayi wasu danne danne ciki sannan ya miqa mata
“This is my number,just call me idan kina da wata matsala ko buqata,bance ki tambaya kowa komai ba,ummi ko hajja,nayi cancel duka,zaki iya tafiya” da sauri ta buda murfin motar ta fito,wanda fitowar tata yaja idanun mutane da yawa,donma aliyyun zamanshi yayi cikin mota,ya kuma nada umarnin a sake fita dashi daga gidan,batasan inda xaije badai,tadai san koda can baison hayaniya kwata kwata,indai ana wani taro a gidan bai zama,sanda bai kuma wani zama saurayi ba wuni yake cikin dakinsu ya kebe kanshi shi kadai,mama tayita faman fadan me yasa baya son shiga dangi ko ya fito su gaisa,tun tana mita da qorafi harta gaji ta qyale,tunda ta fuskanci halinsa ne hakan,
Nan da nan labarin dawowar tata ya zagaye gidan,aka fara cecekuce da zancan dawowarta,ta fara gaisawa da ‘yan uwa data samu harabar gidan,suna amsawa gami da tayata murnar qarin girman da aliyyun ya samu,ta sake fuska sosai tana amsa musu cikin walwala da nuna jin dadi,da yawa suka dinga binta da kallo wanda batasan na meye ba,da haka harta isa sassan abba babba,inda canne yafi cikowar yan suna da yawa,tunda anan mahaifiyar yasiran take wato mommy.
Ihun murna ‘yan uwan nata suka saka sanda sukayi arba,kowa yayo kanta,suka cika kunnuwanta da magana,kowa da abinda zaice,salma ce daga can tace
“Allah matar ya haidar ba haka muka taho muka barki ba,anya ya haidar bai cika aiki ba kuwa?” Ta qarashe fada qasa qasa,wani wawan dundu zahra takai mata,akayi sa’a kuwa ta sameta,fa gantsare saboda zafi,sauran suka sheqe da dariya,dai dai sanda mommy ta shigo
“Waiku kam bakusan kun girma ba don Allah,yanzu kalli yadda sahal yake kallonku,kin dirke masa uwa…..daga dawowarki kin biye musu,tashi ki qarasa gaisawa da jama’a ki qyale wadan nan shirmammun,kuna nan a waje ana nemanku kunata baqi”tana kaiwa nan ta fice ta barsu.
Tare suka fito da ita,ta soma lalubar mama don su gaisa,a kitchen na tsintota sunata rabon abinci da taimakon masu aikin gidan,wai yau sai ta tsinci kanta tana kunyar maman,tana kunyar hada idanu da ita,tana shirin tsugunnawa har qasa ta gaidata tace
“A’ah,tashi inna wuro kada ki bata kayanki,bakiga yadda kitchen din yake a kacame ba” saita lalubi kujera ta zauna akai saboda ji take kamar zata fadi ta gaida maman tayi mata barka
“Ki shiga wajen hajja,can ne naga da sauqin mutane” da to ta amsa mata,suka fito tare da hafsa.
Hafsan ce ta dubeta sanda suka fito ta qyalqyale da dariya
“Anya zahraty wannan kunyar nidai ban taba gani kina yiwa mama irinta ba kamar yanzu,lallai yayana ya cika aiki….to ku shirya wallahi kuda hajja,tana nan satin nan gaba daya kullum saita muku dan biki” harara ta watsawa hafsan,bata iya bata amsa ba suka qarasa sassan umminta.
Kusan a tsaitsaye suka gaisa saboda jama’a itama dake cike a sassan nata,sai kawai ta wuce sashen mutuniyar tata hajja.
A dakinta ta sameta ita kadai tana tsaye inna gaje na wanke mata bandaki,da alama wani ya shigar mata ne,haka take,duk sanda wani ya shigar mata bandaki indai baqo ne to sai an wanke mata,har mamakin tsafta irin na tsohuwar zahra keyi,wani lokaci kuma ta tsokaneta
“Waike da kika kusa gangarawa tsaftar nan duk ta meye?” Wanda idan wani ne ya gayawa hajjan haka sai inda qarfin zahran yake,takance
“Kaga tafiya lahira a kanka,hajjanmu ba yanzu ba”.
Wani kallo hajjan tabi zahran dashi kafin ta yamutsa fuska sanda take gaidata
“Munafukai….sai yau kuka ga damar tahowa?,aida kun sani kun dawwama a can” ta fada da biyu,sabida ta bigi cikin zahran taji me zata ce,hade rai zahra tayi tadan ja baya
“Zaki fara daga dawowata,ni inacan kamar nayi me saboda kewarki,amma irin marabar da zakimin kenan?”
“Na miki da arziqi ma ‘yar nan,ina daya ja’irin?” Baki ta turo ta haye gadon hajjan,wanda tayi kewarsa sosai
“Ki kirashi ki tambayeshi mana” ta fada tana kwanciyarta
“Toooo…da saura kenan” hajjan ta fada a ranta,don tayi tsammanin zata kareshi ne
“Muje zuwa mahaukaci yahau kura” ta kuma fada a ranta
“Duk na isheku riga da wando” ta fada tana shigewa bandaki.
Wunin ranar cikin walwala tayi abinta gaba daya cikin dangi,har zuwa dare sanda aka qare sunan,baqi suka tattafi saura ‘yan gidan da yaran gidan aurarru wadanda sukayi aure,suma a cikinsu wasu sun tafi,tawagar su zahra kuwa suna tattare a sassan hajjan sunata kwasar hira,kamar ba za’a rabu ba,don yasiran a nan sassan hajjan take zaune tunda tazo haihuwa.
Tana idar da sallar isha’i zahran ta koma wajen ummin nata,suka sake gaisawa sosai sannan suka taba hira,wanda ta lura kusan fiye da rabin hirar tata kan aurenta da aliyyu ne a fakaice,tana mata jirwaye mai kamar wanka a kansa,ta rasa wanne irin qauna ce a tsakaninsu
“Nasan zakiyi mamaki me yasa na damu da zancan aliyyu a kanki ko inna wuro?….nafi kowa sanin aliyyu mijine na kerewa sa’a,irin mijin da ake cewa mijin marainiya,mijin dana jima ina miki addu’ar samu,kici gaba da gyara mu’amalarku inna wuro,zaki fuskanci abinda nake gaya miki,mazan aure irin haidar a wannan zamanin wahala sukeyi,cikin dari guda daya ne tak,Allah ne ya amshi addu’ar dana jima ina muku ya kawo sanadi da kika zama matarsa” wannan shine magana kusan ta qarshe da sukayi da maman nata,wanda da ita ta dawo zuwa sassan hajja,wanda zuwa yanzu an sake yoyewa,inna gaje ta gyara falon fes,sai fidda qamshi yakeyi.
Dakinta ta shige,saita tadda yasira ta baje abinta ita da jaririnta,sai suwaiba da itama zata kwana,sai wata ‘yar uwarsu badi’a,itama ba aure ne da ita ba.
Tunda can dama ba wani shiri suke sosai da suwaiba ba,don haka da badi’a suka gaisa kawai,ta diba kayan wankanta ta shige bandakin tayi wanka,sannan ta fito ta dauki kayan da zata saka ta wuce dakin hajja donta shirya,saboda ta fuskanci kamar suwaiba ta sanyawa duk wani motsinta ido,batason ta fusata harta buda baki ta gaya mata magana,shi yasa tabar musu dakin da niyyar kwana dakin hajja.
Saman abun sallah ta tadda hajjan,da alama idarwarta kenan,ta dubi xahran,saidai batace komai ba,har zuwa sanda ta gama addu’o’inta,ita kuma zahran ta gama shirinta,tayi tsalle ta haye gadon hajjan,sai a sannan ta magantu
“Ke zahra’u….tashi kije ki amshi abinci wajen gaje ki kaiwa yayanku”
“Habba hajja,don Allah ki qyaleni mana na huta,ni wallahi bacci nakeji” ta fada tana tura baki,dakewa hajjan tayi
“Tashi ki fita ki bani waje….billahillazi idan na fito na ganki a sassan nan….ke bama sassana ba ko ina nema sai ranki ya baci,ki amshi abinci ki kai masa ya kirani yace a kawo masa,kuma babu uban da zaije kaiwa mijinki abinci….” Tana tura baki tana komai haka ta sauko ta daga saman gadon,har takai bakin qofa ta sake kiranta
“Ba abinci kawai nace ki kai masa ba,karki dawomin sai gobe,idan kinqi ji kuma ba kyaqi gani ba” ko waiwayawa ta dubi hajjan batayi ba tsabar takaici ta qara gaba,itakam gaskiya hajja tana son wuce mata gona da iri,idan batayi wasa ba ta tattara ta koma makaranta zasu jima kafin su ganta,kowa ma a gidan ta shafeshi.
23/10/2021, 08:48 – ๐๐ป๐๐ป: 36
*KIJI TSORON ALLAHโ๐พโ๐พโ๐พKADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
Tana tafe a hanya riqe da kwandon kayan abincin kamar ta sakesu ta sanya kuka saboda takaici,ji take gaba daya hajja ta gama takura rayuwarta tako ina,tana wannan qunci har takai qofar dakin nashi.
Turawa tayi hadi dayin sallama qasa qasa,alamun ranta na a bace ne,a lokacin yana zaune saman kujera,ya miqe qafafunsa lan center table dan qarami dake gabansa,system ce saman cinyarsa yana typing da mugun sauri,da alama wani muhimmin magana yakeyi,dakin a dan hargitse yake da kaya.
Sau daya ya daga kai ya kalleta ya amsa sallamar ya maida kansa ga system dinsa,saita qaraso a hankali ta aje kwandon gefanshi,tsaye tayi ta rasa meye abunda zatayi,tana tunanin ta koma idan yaso hajjan tayi kwadonta ta cinye,idan kuma ta zauna din kamar ta zubda kanta ne,zaiga ita ta kawo kanta ma kenan,kamar tadda yayi mata sharri a abuja.
Sake daga kai yayi ya dubeta,idanunta nacan wani sashen daban,don ta jima bata iya hada idanu dashi,tun lokacin da wancan abun ya faru,duk yadda yakai ga qwaqwqwafi da qwaqwar su hada idanun bata yarda
“Have a sit please…..bana son tsaiwa” ta jishin,saita samu waje tana zama din,cikin ranta tana mitar har a gayawa soja tsaiwa zaice wani baison tsaiwa,takaicinsa ya sake cikata,ta rasa me zata masa ta fanshe haushin da hajjan ke cusa mata a kanshi,don haka ta tsiri zuba mishi abinci,kowanne plate saita cikashi ta tura gabanshi,shi sam baisan ma me ake ba,harta gama zubawar,saita miqe ta nufi dan qaramin fridge dinsa dake dakin ta bude.
Jere yake da hadaddun zobo,wanda da alama jin zuwansa yasa umminta tayi masa,tunda dama itake masa,saboda din mutum ne da idan ba dole ba bai fiya son lemon kwali roba kona kwalba ba,yafi gabe gagajiya,zobo ginger ko kunun aya,su yafi sha indai yana gida.
Murmushin mugunta ta saki,babu abinda zai dace da tsarin ta irin zobon,ta ciroshi cikin wata kwalba me kyau da ummin ke aikawa can wani store ana siyo mata ita,tana yanayi da jug amma ba jug bane,dan tsukakken bakine da ita,sata hada da cup din data gani saman fridge din ta taka a hankali ta koma wajensa.
Sai data iso dab dashi ta soma tsiyaya zobon,taf ta cika kofi,sai kawai ta saki cup din ya sullube daga hannunta,ya kuwa fada saman cinyarsa,take ya masa wanka a fararen kayan dake jikinsa,ya kuma fantsame har screen na system din da yaketa faman latsawa.
Cikin ba zatar zubar abu mai sanyi daya ji a jikinsa ya daga kai yana dubanta,tana tsaye a kansa,saidai tayi narai narai da idanu alamun rashin gaskiya,baice mata komai ba sai qoqarin kashe system din da yake saboda karya shiga ciki.
Sai data fara shutting down sannan ta tsinci muryarsa
“Kin saba ai” tayi mamaki da taji iya abinda ya fada kenan,saboda ita da gaske fusatashi takeson yi,saidai batasan lamfo yayi mata ba,sai daya gama kashe system din,ya janye dukka takaddun da yaga zasu baci sannan ya miqe.
Idanu ta zura masa qirjinta na bugun uku uku sanda taga ya nufota,hannusa guda daya cikin aljihun wandonsa fari daya baci face face da zobo,wani taku yake slowly,saidai ya aza qwayar idanunsa cikin nata sosai,wanda hakan taji ya mata nauyi matuqa,ya kuma qara mata fargaba,duk da haka ta kasa dauke qafarta ta ษara daga inda take tsayen harya cimmata.
Wata iriyar tsaiwa gab da juna sosai,har yatsun qafarsa na dungurin nata,har yanzu kallon qwayar idanunta yake data kasa janyewa daga cikin tasa,hannayensa ya daga sama gaba daya,kamar wanda yayi laifi aka kamashi yayi surrender
“Farashin da zaki biya wannan gangancin da kika yimin shine,ki cire kayan jikina ki daurayemin jikina da kika batamin haka kawai ina zaman zamana…..na yafe miki wankin kayan…..don yanzu dana saki ma waccar tsohuwar zata isheni da kwarorota da terere” kamar ya dauko guduma ya kwada mata haka taji,tsoro da firgici suka cikata,saboda daga yanayin yadda yake maganar ya tabbatar mata cewa da gaske yake bada wasa ba,ta kalli hagu da damarta,ko ina ya tare babu wajen kubuta,amma zata gwada,don kome zai mata ba zata iya abinda yace din ba,gwara ya mata duka da bulalarshi yafi mata sauqi.
“Am so sorry” ta samu kanta da furtawa cikin rawar murya,sake hade rai yayi tamau
“A soron gidanku nake kwana?” Yayi maganar yana dage mata dukka girarshi,saita kada kai
“Kayi haquri….banfa sani ba” kanshi ya kautar yana sake hade rai
“Sanda aka raba haquri bacci nakeyi” saita ware idanunta duka,wai dama ya haidar din ya iya magana haka,harda su baqar magana duka?
“To ka cire kayan….ka bani Allah xan wanke”
“Banaso,nima ina da hannu,and bakisan ni qazami bane….daqyar nake iya yin wanka?,kinga shine xaifi bani wahala ba wanki ba” sake zare ido tayi,tasan dai zaginta kawai yake,mutumin da idan heater din sassansa ta samu matsala kowa a gidan ya banu da dafa ruwan wanka.
Ta gama fahimtar bazai haqura ba dai din,don haka ta faki idanunsa,tayi wuff da niyyar guduwa,saidai taku uku kacal tayi taji an danqi hannunta
“Baki isa ba,ki batan jiki,ki batan kaya ki batamin guri kuma sannan ki gudu?,selfish girl”.
Qafa ta soma bubbugawa tana tara qwalla ko zai tausaya mata,yadda dai takeqa hajja ta karya mata zuciya,saidai abinda bata sani ba,hakan da takeyi tsokano ‘yan maza takeyi,saboda ko ina na jikinta dake rawa,idanunsa ya lumshe ya dora yatsansa saman labbansa bayan ya bude idon yace
“Shshshsh……ni banyi kuka ba saike?,zan baki another option…..koki wankemin jiki,ko na wanke da kaina,amma fa yadda kika jiqani kema saikin jiqe” da sauri ta gyada kanta,a tunaninta wannan shine zaifi mata sauqi,saboda tayi zato zaya dauko zobon ne ya kwara mata shikenan an wuce wajen,saidai ina,kafin takai ga wani tunanin sai ji tayi kawai ya dauketa gaba daya yayi bandaki da ita.
Cikin kwamin wankan daya cikashi da ruwan dumi ya jefata,wanda a niyyarsa dama idan ya gama cin abinci yayi wanka ya samu ya kwanta,tuni idanunta suka raina fata sanda ya salube hijabin jikinta,tuni rigarta ta lafe sosai a jikinta,ta bayyana duk wata halitta ta jikinta,gashin kanta da yasha ruwa shima yabi wuyanta ya kwanta,tuni ta dunqule waje daya,saboda ta fuskanci babu wata mafaka ko matsera.
Shi kuwa baya ya juya mata,haka kawai murmushin yadda tayin ya subuce masa,yakai geji,yana jin ya kamata ko yaya shima ya dana.
Batayi aune ba saijin mutum tayi tsulum cikin ruwan,da sauri ta daga kai don yin qorafi,amma suna hada idanu ta maida kanta qasa,qirjinta na wani irin bugawa,zuciyarta kamar xata fito,bata raina kanta ba sai daya dauketa gaba daya yayi mata masauki a qirjinsa,cikin hanzari ya ware hannayensa ya soma yawo dasu ko wane sashe na jikinsa,duk wani waje da yasan yana tsole masa idanu.
Cikin lokaci qanqani ta gigice,tana tuna abinda ya faru kwanaki uku ko hudu baya kada ya sake maimaita kansa,shikam ko a jikinsa,sai da yaga dama a qashin kansa sannan ya saurara.
Wankansa yayi har a sannan bata iya kallonshi ba,sai daya gama ya daura babban towel a qugunsa,saiya bude rariyar ruwan ya fita ya tara mata wani
“Zaki iya wanka” daga haka ya taka ya fice.
Tana qananun qwalla tana wankan,a haka harta kammala,sai kuma ta rasa me zata sanya ta fito?,idan ma ta fito din wanne kayan zata sanya tunda wanda tazo dasu sun jiqe?,towel ta hanga don haka dole shi ta daura,Allah yasa ya cire mata hijabin bai jiqe ba,saita saka shi ta fito daga toilet din a hankali kamar wadda ta yiwa sarki qarya kanta a qasa.
Waje daya ta samu ta zauna sanda ta fito din,yayin da yake gaban mudubi yana shafa mai,wani wasai yakejin ranshi da gangar jikinsa,wani shauqi da baisan daga ina ya taso ba yana ratsashi,itadai batasan me ake ciki ba sai taji sautin muryarsa yana cewa
“Hello hajja…..a samu yaro ya kawo mata kayan sawarta” shuru ya danyi da alama silleshi hajjan take,don murmusawa yayi kadan sannan yace
“Gani nan….zanzo na dauka da kaina” da haka ya kife wayar,ya qarasa shiryawa a gurguje ya fice,saita bishi da kallo tana dora hannu saman ka,shikenan ya janyo mata,ta shiga uku wajen hajja,tasan wallahi watan yi mata tijara ne ya kama,yanzu duk wanda yaga yaje dauka mata kaya saiya dauka wani abunne ya faru,kawai sai taji hawaye yana sauko mata.
Ya kusa minti goma sannan ya dawo,ya zube mata kayan wajen kala uku,abun kunyar ma data daga harda undies dinta da bra,ji tayi kaman qasa ta tsage mata ta shige,sauqinta daya ma daya dan fita ya bata waje ta shirya,bayan ya dawo yana daga zaune yasa tayi serving nasa,saita samu waje ta zauna bayan ta gama,lokaci lokaci yana satar kallonta,murmushi na subuce masa,can qasan ransa ya furta
“Silly girl,zanyi maganin wannan tsiwar taki” yana kallonta tayi kwanciyarta saman kujera,baice da ita komai ba,saida baccinta yayi nisa kawai ta tsinci kanta saman gadonshi,ta motsa yace da ita
“Kina tashi akwai punishment,just sleep” saita maida kanta ta kwantar tana irga qarfin hali da iya qarfa qarfa na ya haidar din,ita gaba daya kwance mata kai yakeyi,dukka halayen da take gani yanzu tattare dashi mugun baqin halaye ne da babu wanda ya zaceshi dasu
(Ni kuwa nace matar mutum ai ba wasa ba,duk wanda ke cika baki akan mace ba’a biyo ta kansa bane),ta qasan ido take hango duk motsinsa,saboda bayan yaci abincin aikinsa yaci gaba dayi,saidai wannan karon rubuce rubuce ne yaketa yi wanda batasan na meye ba.
A hankali qamshinsa daya kama zanin gadon da abun rufarsa ke ratsa qafofin hancinta,wani tattausan qamshi data kasa banbance na meye da meye,tun da can kusan lambarsa kenan,dashi ake gane yana waje,har zuwa yanzu kuwa duk wanda ya sanshi ya sanshi da qamshi,sannu sannu take shaqar iska zuwa hunhunta har wani bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba da ita.
*_WASHEGARI_*
Tun bayan sallar asuba bacci ya sake daukarta me nauyi,ita da tayi niyyar zata gudu tunda duku duku,don ba zata iya hada idanu da jama’ar gidan ba,sai gashi bacci ya kwafsa mata,ba ita ta farka ba sai goma saura.
A rude ta sauka daga gadon,saita hau juye juye,babu kowa cikin dakin sai ita,don haka ta nufi qofa da hanzarinta tana addu’ar kar ya shigo har sai ta fice,don babu abinda taqi jini irin su hadu a yanzun,idan ta tuna abinda ya faru jiya ji take kamar qasa ta tsage mata ta shige.
Saidai ta makara,addu’arta bata ci ba,tana murda handle din shima yana murdawa,sai sukayi kacibus bakin qofa,yadda ya sako kai gaba daya yana tsareta da idanu ya sanyata ja baya ta bashi hanya ya shigo.
“Ina kwana” ta gaidashi tana kauda idanu,ya amsa mata da
“Kin tashi lafiya?” Saita kasa maida masa amsa,bai damu ba yace
“Muje….ciki nima zan shiga” da sauri tayi gaba,kamar wadda ake tsunkuli
“Easy mana” ya fada yana taddota,suka jera kafada shi da ita
“Ko sau daya mana,yau kawai hajja ta yaba mana” da xata iya juyawa zatayi ta maka masa harara,wanne yabon hajja ita takeso,bayan ta kaita ta barota,babu wani abu a jikinta a yanzu da baisan wajen zamansa da size dinsa ba,itakam ai sun gama da ita shida hajjan,bai sake cewa komai ba itama haka,haka suka ci gaba da takawa har zuwa cikin gidan.
Duk wanda suka gamu dashi sai taji kunya ta kamata kamar ta shige qarqashin qasa,musamman da sukaci karo da abba babba,cikin farinciki yake dubansu sanda suke gaidashi,harda yi musu addu’a sannan suka wuce.
“Muje ki fara gaida ummi” yace da ita yana tareta daga yin sassan hajja,saita bishi suka wuce sassan ummin tata.
Tana cikin yin breakfast suka shiga,saita ture kwanon,fuskarta itama cikeda jin dadin daya kasa boyuwa take amsa gaisuwarsu,haka taci gaba da binsu da kallo har suka fito daga sassan
“Kinsan girman ladan sanya farinciki a zuciyar iyaye?,muje ki gaida mama itama” ya fadi yana nuna mata hanya,bata ce masa uffan ba ta bishi suka isa sassan maman,ita dinma kamar sauran,farincikinta bai boyu ba,hatta da momy da suka gaisar,sai jikinta yayi sanyi,dukka wannan farincikin na meye?,na ganinsu ne tare da Aliyyun kawai?,da wannan tunanin suka wuce sassan mai gayya mai aiki hajja.
Dukkansu suna falo harda me jego,suwaiba da badi’a,saisu anty aliya da suka zo suyar nama,idanun da sukayo kansu gaba daya sai taji kamar zata zube a qasa,kunya kamar ta kasheta,saita dinga mammazewa,ta qarasa cikinsu ta gaidasu,hajja ce dai sai data tura mata qeya sannan ta amsa.
Bayan sun gaisa haidar din yadan zauna a cikinsu anty aliyan,abinda yakan jima baiyi ba kenan,ba kasafai suke samun damar zamansa cikinsu ayi hira sosai ba,sai lokaci lokaci,hakan ya sanya zahra barin falon ta shige dakin hajja,don nata dakin su suwaiba su shige ciki.
Tana nan kwance hajja ta shigo dakin yakai sau uku,a fakaice take mata habaici a waqe anaso ana kaiwa kasuwa,irin salon waqoqin mutan da din nan,dadai ta gaji da habaicin hajja saita miqe ta fice tabar mata dakin.
Har yanzu yana falon shida anty aliya da anty nusaiba,zata wuce kitchen ta samu abinda zataci taji suna masa godiya,da alama ya musu irin alkhairin daya saba ne.
Inna gaje ce kawai a kitchen din,sai tayi zamanta kawai a ciki,ta hada mata abincin ta soma ci suna hira,ita dinma zancan haidar din take mata
“Ai gaskiya uwar masu gida kin dace,kinyi dace da mijin qwarai mai hannun alkhairi,inda ace shidin wani hamshaqin attajiri ne Allah ne yasan mutum nawa me zasuyi kudi ta sanadinsa,ko a yanzun ma ya zama inuwa ga mutane da yawa,saidai addu’ar Allah ya qara arziqi” murmushi ta yiwa inna gajen kawai,ta can qasan ranta sai taji zuciyarta na amsawa da amin…………
23/10/2021, 08:48 – ๐๐ป๐๐ป: 37
*KIJI TSORON ALLAH,โ๐พโ๐พโ๐พKADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
Washegari kuwa qaryar ciwo ta yiwa hajja bayan ta gama hada kayan da xata koma makaranta dasu a washegari,tayi kwanciyarta da wuri,duk da baccin bai dauketa ba amma tasha chart dinta,har daga bisani baccin gaske yayi gaba da ita.
Tunda ilham ta kawo masa abincin yace ta ajiye a nan,tsahon wani lokaci yana zaune,shi baici abincin ba,bai kuma ce a fita dashi ba,haka kawai duk yaji baya cikin sukuni,abincin ma baya sha’awa ci,xuwa wani lokaci sai gashi ya miqe,ya saka hannu ya bude dakin,ya leqa farfajiyar waje kamar me neman wani abu,daga baya kuma ya rufe qofan ya dawo ciki yana jan tsaki.
Gaban kwanukan abincin ya dawo ya soma saving kanshi,abinda ya jima rabon da yayi,tsakula kawai yayi yaji cikinsa ya cushe,saiya tura abincin gefe ya miqe ya nufi bakin fridge don dauko abin sha.
******** ***** ********
Tsaye take dakin hajjan rataye da qaramar jakarta,tana tsayen amma sai faman duba agogo take,tana so ta isa akan lokaci ne,akwai lecturer din dake nemansu,kuma tasan halinsa sarai,mtuqar ta wuce lokacin tofa ba shakka ko dawa take yawo ba zai bari ta shiga ba.
“Don Allah hajja ki sauri….zan makara fa” ta fada a shagwabe,saita rufe akwatin data bude din,ta miqa mata baqar leda
“Gashinan,ki tabbtar komai dake ciki kin shanyeshi kafin dawowarki gidan nan,Allah ya tsare….ina shi haidar din?”
“Munyi sallama fa,bacci yake,mustapha zai kaini” idanu hajjan ta tsareta dashi,bata yarda da zancanta ba,don tun jiya taga tana aiken yara suna siyo mata abubuwan da bata dashi a kantin layinsu da ษai da ษai,ta mata shuru ne kawai tayi kamar bata gani ba
“Motarsa kam dama ai wajen mustapha ta kwana,don ya aikeshi gidan innarku da safe zaije yakai mata saqo” qafa ta bubbuga
“Wai hajja yarda ne bakiyi dani ba”
“Na yarda dake,Allah ya kiyaye hanya” ta fada tana tattare kayanta data fito dasu,sanadin daukowa zahran abinda ta batan,ta san sarai indai baisan da tafiyarta ba bazai qyale ba,don baya daukan irin wadan nan abubuwan.
Sai data shiga ta yiwa duk mutanen gidan sallama,bata tarda mama ba ta fita tun sassafe dubiya,umminta dubu biyu ta bata,sai taqi karba,duk da ta yiwa account dinta tas saboda siyayyar data yiwa kanta da kanta,don kada ta tambayi haidar din,wanda tunda take bata taba yiwa kan nata siyayya ba sai wannan karon.
Gaban motar ta shige sanda mustapha ke kunna motar,ya tasheta suka fice daga gidan.
Tun basuyi nisa ba suka soma hirarsu yadda suka saba,cikin raha da zolaya,gab da zasu shiga farawa wayar mustaphan tayi tsuwwa,sai zahran ta xolayeshi
“Tun daxu ake faman kiranka,hala wata mai rabon wahalarce” ta fada tana sheqe masa da dariya
“Allah kinga makwancina da yawa…..ki zuba ido,sai nafi mijinki kudi,kibar ganin aikinmu har yanzu baizo hannu ba,hausawa suka ce gayawa wanda ya tara ya kiyayi me nema…..kai shine ma ke kira” ya fada yana zaro ido,sai zahran ta qyalqyale da dariya
“Qaryar kawai,ashema cika bakin naka bai kai ba,tunda gashi daga ganin sunansa kawai ya saka fargaba” hannunsa daya ya daga
“Na yarda wallahi….ke….kinsan soja kuwa….hmmmm” daga haka ya daga wayar,ya sanyata a handsfree.
Husky voice dinsa ce ta cika wayar,kamar bai jima da tashi a barci ba
“Kai kana ina?” Ya tambayeshi a dake,cikin girmamawa yace
“Gamu a hanya zan maida inna wuro makaranta”
“Waye ya baka izini?” Ya jefa masa tambayar data saka mustapha ware idanu yana duban zahra,wadda itama shi take kallo,dukkansu gabansu na faduwa,bai iya amsa mishi ba ya tsintoshi yana cewa
“Duk inda kuke ku dawo yanzu yanzun nan” daga haka ษif ya katse wayar,saiya soma neman wajen tsayawa,ya gangara gefan titi zaiyi reverse.
Kallonsa zahran tayi
“Wai komawa zakayi?” Girarsa ya dage duka yana kallonta sannan yace
“Eh mana….au so kike nace masa a’ah,tab….wallahi bazan iya ba,ke da kike matarsa ma bakice komai ba saini”
“To gaskiya malam tsaya na fita,na tari wata ta kaini,saboda indai banyi attending class ba daganan zuwa lokacin da lecturer din yace ba da wuya bai zame min matsala ba” lock yayi sauri ya sanyawa qofofin sannan ya fara reverse yana cewa
“Kinsan Allah ba xaki jawomin ba,ai kiyi haquri kawai na miqa masa ke da motar sa”.
Kafin su isa gida kuwa mita da qorafi mustapha ya shata,kamar ma shine haidar din,shidai dariya yake sheqa mata
“Sai dana tambayeki ya san zan kaiki kika ce eh,to ashe ma ko sallama bakiyi masa ba,bayan kinsan halin guy din nan,ba’a canza masa ko take masa doka,nidai na kaiki lafiya shine kawai mafitata a wajensa” .
Suna shiga harabar gidan ya sake kiransa
“Ok” kawai taji yace,ya kashe wayar sanda xahra ke tambayarsa
“Me yace?”
“Yace nakai masa key din” haushi takaici da baqinciki ya cika,wato ita bata ga tsuntsu bata ga tarko,saita balle murfin motar ta shige sassan hajja.
A falo ta sameta zaune tana karyawa,ta dinga kumbure kumburenta da qunquni amma hajjan bata ce mata ci kanki ba,a haka har kusan awa daya,wanda tuni ta fara qwalla,sai ga husna ta shigo,tace wai ta fito inji ya haidar,jakarta ta figa tafita kamar jakarce tayi mata laifi,ko magana bata yiwa hajjan ba,ita kuwa hajja sam bata damu ba,murmushi kawai ta saka,saboda hango tarin nasarori daga wajen haidar,wanda ta tabbatar nasarar da zata samu akan haidar,ita zata kai har kan zahran.
Yana zaune gaban motar ya kamo sashen labari na bbc hausa yana sauraron labaransu na ranar,yayi masifar kyau cika da kwarjini cikin qananun kaya,idanunsa saye cikin wani sunglasses mai azabar kyau qirar wannan shekarar,wanda glass din ya qara masa kwarjini qwarai,jikinsa ba abinda yake fitarwa sai qamshi mai sanyi,wanda yacakuda da qamshin freshner na motar da sanyin ac dai wadda baya rabo da ita.
Tana shiga motar sanyin daya cikawa motar ya sanyata yin gulmarsa a ranta,taja murfin motar ta rufe,sannan ta waiwaya kadan tana gaisheshi,ko kallonta baiyi ba ya tada motar,ya jata da gudu suka fice daga gidan,saita lafe jikin murfin motar kawai,tana jin bugun zuciyarta yana sauyawa.
Shuru ne ya ratsa motar sanda yake tsala gudu dasu saman hanya,duk da suna cikin gari basu fita wajen gari ba,ta karanci shima gwanin gudu ne sosai a mota.
“Kin rainani ko?” Ta tsinci muryarsa yana fada a taqaice,dan waiwaya tayi ta dubeshi kafin ta dauke kai,kansa da idanunsa suka suna kallon titi ne,kasa amsawa tayi,sai tayi shuru tana murxa yatsunta kamar yadda shima yayi shurun,kamar bazaice komai ba kuma saiya bude bakinsa gently yace mata
“Ko auren uwaka ubaka mukayi dake auren tasha nidin mijinki ne,kinda da haqqi wuyana kamar yadda nima nake da haqqi wuyanki,bare ma aurenmu yafi gaban nan,koda bakiso bani so,koda babu shaquwa a tsakaninmu,tunda iyayenmu mutane mafi daraja a rayuwarmu su suka daurashi,fita babu izinin miji haramunne kuma ba dai dai bane….sannan komai niya kamata na zama a sahun gaba wajen sani kafin kowa…..so please…..please kada ki sake,idan ba haka ba saina daure qafafunki a inda ake daure qafafun marasa ji irinki” maganganunsa sunsa jikinta yayi sanyi,saita tsinci kanta da furta
“Kayi haquri” softly,wanda hakan ya bashi mamaki,sai kuma yaji dadi har cikin ransa,kamar yadda itama mamaki ya kamata,tayi tunanin zai balbaleta da fada ne har yayi ma kamar zaya daketa,kamar yadda yake musu acan baya idan sukayi laifi,ko kuma zai gaggaya mata magana,ko yace ta tafi a motar haya,a haya suke hangen halinsa,mutum mai kushin hali fushi da fada,kafiya da taurin kai,amma sai taga duka baiyi ko daya ba,ya gaya mata magana ce ta hankali,wanda duk me hankali ta isheshi ya fahimta cikin ruwan sanyi,basai an qara masa da wani abun daban ba.
Bata yanke daga wannan tunanin ba taga ya tsaya qofar wani babban kanti,wanda ya hada komai da komai,kusan komai.na buqatar yau da kullum da amfanin rayuwa suna saidashi
“Wait” kawai yace yana cre set belt din jikinsa ya bude motar ya fita ya nufi shagon,saita bi bayansa da kallo,yana yin yadda yake taku cike da nutsuwa qasaita da ginshira,sai daya shige sannan ta dauke idanunta a hankali tana sauke ajiyar zuciya,yaushe ya haidar ya sauya?,yaushe yayi laushi,to amma ita game da yadda yake mu’amalarsa da yaran gidansu bataga sauyi ba,donko ranar suna sai daya yiwa su salma fata fata kan sunkai dare,kuma mazansu sunzo daukarsu kowacce ta shanya mijinta,har kusan kuka sukayi.
Babu jimawa taji an bude set din baya,shine riqe da babbar leda ya sakata a bayan motar ya rufe,sannan ya dawo set dinsa ya shiga ya sake tada motar.
Basuyi nisa sosai saman titi ba taji ya sanya casset na karatun dr malam umar sani fage,kamar yasan xabinta kenan cikin dukka malamai,babu malamin da take bin karatunsa qafa da qafa kamarsa,take kuma nutsuwa da dukka fatawoyinsa kamar shi,zallar hikima da dora bawa bisa hanya,da doron shari’a hanyar da zaka samu lahira irin malamin,batajin a wannan qarnin akwai malami kamarsa,zaiyi wuya,duk da ba’a rasa bayin Allah,wadanda suke lunguna da saqon qasa da garinmu,kuma Allah baiyi ambatonsu ya bayyana ba a bakunan bayinsa,amma shi yasan da zaman kayansa.
Wannan karatun shiya jagorancesu,ya kuma rakasu har cikin makarantar.
Suna shiga ya rage gudu,ya dinga gangarawa a hankali har yakai iyakar inda motoci ke tsaiwa daga nan babu qari,ya kashe motar sannan yana qoqarin bude murfin motar yace mata
“Dawo set din baya” saiya fita,bude murfin tayi kamar yadda ya umarcetan.
Yana tsaye a wajen motar hannunsa a qirji yace mata
“Ki duba kayan idan sun miki,an siyo su late…..but remember,nidin bamai kudi bane” ya fada carelessly kamar ma bashi yayi maganar ba.
Ledar kawai ta buda ta rufe tace
“An gode,Allah ya saka da alkhairi” saita fito.
Yana tsaye jikin set din data zauna dazun,kuma tabar jakarta a wajen tana da buqatar dauka,murya qasa qasa sanda take tsaye a gabanshi nesa kadan dashi tana facing dinsa tace
“Jakata” saiya dauke idonsa daya tsareta dasu,ya bude motar ya dauko jakar,kudi ya ciro dubu ashirin daga aljihunsa ya bude jakar ya sanya mata yana cewa
“Ki riqe wannan saboda koda wata buqatar zata taso….zanyi tafiya ne,koda zasu yanke miki kafin na dawo,karki tambayi kowa,kiyi gayawa mustapha,zaiyi handling komai” saiya miqa mata jakar,ta sanya hannu zata ansa,sai daya tabbatar ta riqe saiya janye jakar,ta bada amannarta gaba daya,hakanan bata zata ba,don haka ta biyo jakar talau,sai gata taja birki a gabansa,dab dashi,don taqi kadanne tazarar dake tsakaninsu.
Qas tayi da kanta saboda kallon da taga yana mata,ta kuma kasa janyewa,saboda ko yaya ta motsa jikkunansu zasu hadu.
Jakar ya sake miqa mata,ta miqa hannu a sanyaye karo na biyu zata karba,sai yasa daya hannun masa caraf ya damqe tsintsiyar hannunta,a tausashe ya jata ya jinginata da jikin motar,a maimakon dazun da shine ke tsaye jikin motar,sannan a tausashe ya sanya qafarsa tsakanin nata qafafun,ya kuma dafe gwiwar hannunsa saman motar dab da kafadarta,idan daga nesa ka hangesu zakayi tunanin tana rungume cikin jikinsa saboda kusanci,kusancin da jikinta da zuciyarta suka kasa dauka,saboda duk wani fitar numfashinsa tana jin saukarsa saman fuskarta,hakanan qamshin turarensa daya danne nata,uwa uba idanunsa masu kaifi da suka sake yi mata nauyi,sai tayi hanzarin yin gefe da kanta,wanda kafin sakan daya yasa yatsun hannunsa ya kamo habarta,ya maido da fuskartata saitin tashi.
Bai barta ba sai daya lalubo qwayar idanunta ya saka tashi a ciki,cikin wani irin sauti dake fita da qyar,can qasa kamar wanda bacci yaci qarfi ya soma magana
“Zanyi tafiya me nisa…..waje mai hadari,zan iya dawowa,zan iya salwanta a can,duk da bai cikin aikina…..amma zan shiga da kaina saboda na sake sadaukarwa da qasata ruhina,inason in samawa wadanda suke cikin qunci salama da nutsuwar ruhi…..pls forgive me if i hurt you a tarayyarmu”wani irin rauni taji ya mamayeta irin wanda bata taba ji ba,saita daga idanunta da cikin qaramin lokaci suka hada qwalla taf ta dubeshi,bata wani abu mai nauyi na sauka saman zuciyarta cakude da wani yanayi da batasan wanne iri bane,idan kuma ya mutu fa a can kamar yadda yace zai iya salwanta?,wani sashe na zuciyarta ya raya mata,rayawar daya sanya qwallar data tara ta subuce mata,ta gangaro saman kuncinta zuwa habarta
“Oh….no,bafa kuka nace ba,banason kuka ko kadan” yatsunsa ya sanya guda biyu ya dinga dauke mata qwallar,sai daya gogesu tas,maimakon ya daukesu saiya zarto dasu saman qirjinta,tun daga wuyanta zuwa qasa ya fara mata tafiyar tsutsa dasu,ya kuma sanya idanunsa cikin nata,take jikinta ya dauki rawa
“Am gonna miss my……” Shuru yayi bai qarasa ba yana ci gaba da kallonta,cikin qarfin hali ta sanya lallausan hannunta tayi caraf ta riqe hannun nasa tana girgiza masa kai,murmushi ya saka yana sauke hannuwan nasa,sannan yace
“Matsoraciya……” Saiya saka tattausan labbansa a hankali,yayi kissing nata softly da wani irin sanyi saman labban nasa da suka ratsa har kwanyarta ya sakata lumshe ido,tana jin wani feeling na cika zuciyarta,wani yanayi na farinciki yana cikata kamar ana yawo da ita a duniyar gajimare.
A hankali take tafiya,duk da ta bashi baya amma tana jin tsaiwarsa a wajen cikin jikinta,saidai batasan meye ya tsaidashin ba,kafin wani lokaci kafin takai ga bacewa a wajen taji tashin motar tasa a hankali,saita dinga jin wani abu me kama da kewa yanason kamata,inda tayi qarfin hali ta tattara duk wani jarumtata tayi tayi fatali da wannan batun,ta kuma qaryata kanta da kanta.
23/10/2021, 08:48 – ๐๐ป๐๐ป: 38
Wani mugun shewa taji sanda ta shiga dakin kwanansu,dama tun cikin aji ta fuskanci suna gulmarta da ido,don dai da malami a ajin,babu damar suyi mata magana ne.
Da ido ta bisu ganin yadda suketa mata dariya
“Dalla malamai,banason iskanci,meye abun dariya a jikina?,koni mahaukaciya ce?” Sai sannan hindatu tace
“Mahaukaciya tuburan kuwa……ah,ya haidar din da bashi da mutunci,ya zakin da babu ruwanki dashi,aka hanani neman soyayyar dan bawan Allahn nan,ash kinsan cewa qarshe ne shi a soyayya,ya gama haduwa tako ina,sai gashi ya kasheki da soyayya agun ajiyar motoci,har jama’a suka wuceku ma baki sani ba…nidai gaskiya qawa kinmin yankan baya ba kadan ba” ta fada tana hade fuska,janna tace
“Nifa banga laifinta ba,tsakani da Allah fa,waje zaiga guy irin wannan yana da dama ya bari ya wuceshi,wallahi ko nice sai inda maina ya qaremin,idan kuwa ina zaune yazo ya taya,ai babu wani kwane kwane zanyi wuff da abina”.
Babi babi na tsiya suka bude suka dinga yi mata,ita dai ci kanku bata ce musu ba,hakanan ta samu kanta da kasa tanka musu,sai data tafi bandaki sannan suka saurara mata,data dawo kuma aka shiga hirar yaushe gamo,nan ma sai da suka tsokaneta
“Daga yanzu zanje na dawo qawa kuma sai mukaji dif” tsaki taja tana nade abun sallarta
“Wallahi hajja ce,ashe ta timer min” dariya duka suka saka,janna tace
“Allah dai ya biya hajja,wallahi ta kyauta min” harara ta jefa mata,hindatu ta cafke
“Ta taimakeki kuwa,don bakiga kyan da kika qara ba,Allah yasa anyi me gaba daya” ta fada suna tafawa,dadai ta fuskanci iskanci da tsiya suka tanadar mata buhu buhu,saita miqe tabar musu dakin,saidai zancan hindatu ya tuna mata da abinda ya faru a wancan ranar,ranar da yaso yayi mai gaba daya din,sai wani qaramin murmushi ya sube mata,ita kadai taja hijabinta zuwa qasan hancinta tana jin kunyar kanta da kanta.
Dawowarta ba jimawa aka soma jarrabawa,wanda daga ita din watanni kadan suka rage musu suyi jarabawar kammala makarantar,kamar kowanne lokaci dai bata daga qafa ba,ta bada himma wajen karatunta sosai,duk da cewa lokaci zuwa lokaci tunaninsa yakan fado mata a rai,har yakan tsaidata na wasu mintuna kafin ta dora,tun tana yaqin ture zuwan tunanin kwanyarta harta haqura ta bashi dama,saiya zame mata jiki,don kusan duk sanda tazo kwanciya bacci shine abu na qarshe da zatayi kafin baccin ya dauketa,kaf xamansu na abuja sai tayi bitarsa,ranar da zasuyi sallama na qarshe da sauran moments nasu.
Batasan me yasa a kwanakin take yawan duba wayarta ba,koda yaushe tana kan cheaking sms da watsapp massages fiye da yadda ta saba,batasan dalili ba,sai randa zuciyarta tayi mata wata tambaya,wanda a take ta girgiza kai alamar a’ah
“Kina tsammanin samun kira da gareshi ne?” Wannan itace tambayar data yiwa kanta,wanda ko sau daya bata taba yarda da hakan ba.
Jarabawar wannan karon suna samun intervals sosai,don haka duk sanda taga akwai interval mai yawa saita tafi gida,tafiya gidan yakan sa mata nutsuwa,kuma yakan sanya taji kamar tadan rage nisan dake tsakaninta da wani abu wanda ada yake nesa da ita.
Sannu a hankali ta tabbatarwa da kanta damuwa ce,damuwa ce ta rashin ganinsa ko rashin jin muryarsa na tsahon tagwayen sati,har ana neman shiga sati na uku,hatta a gida hajja ta fara qorafin shuru haidar,bai kira ba,koda an kira ba’a samunsa,to Allah yasa dai lafiya,addu’ar data sanya gaban zahran mugun faduwa,saboda tuna maganar daya gaya mata
_”zanyi tafiya me nisa…..waje me hadari,zan iya dawowa….zan iya salwanta a can…..ki yafemin idan na saba miki a tarayyarmu”_,kawai sai taji kuka ya subuce mata,ta danneshi har sai data kai daki sannan ta sakeshi.
Kuka tayi sosai wanda ta kasa yarda da dalilin kukan nata da zuciyarta keta bata,saidai ko ba komai ta danji nauyin dake qirjinta ya ragu,ranar sama sama tayi karatun jarrabawar da zata zana a jibi,washegari ta hada kayanta ta koma makaranta,wanda jarabawar kawaidai tasan saidai Allah ya tsallakar da ita,amma ita kanta bata gama tantance abinda take rubutawar haka yake ba,ko akwai kusakurai da gyararraki ba.
Hajja kuwa bin zahra tayi da kallo tun sanda taga tayi daki da sauri sanda take jajjabin kwanakin da haidar din ya shafe babu shi babu labarinsa,murmushi ta saki,duk da tana cikin fargaba,saita daga hannunta sama tana cewa
“Allah na gode maka,Allah na gode maka,ko yau na mutu ubangiji ka cikamin dukka burina,Allah ka qara hada kan zuria’ata da iyalina,Allah ka qarawa annabi muhammad S A W wasila da fadila” daga haka ta sauke hannun nata,zuciyarta na mata dadi,ba shakka komai yayi dai dai yadda takeso,tasan cewa da zarar ya dawo komai zai kammala dai daita.
Ranar da suka kammala jarrabawarsu suka samu hutu na wasu kwanaki ba masu yawa ba,saboda zasu dawo ne suyi maza su dora sabuwar semester ta qarshe,tana kwance a dakinsu kamar ba wadda ke shirin tahowa gida ba,tana kallon su hindatu sunata shiri.
Tun sanda ta dawo daga abuja ta lura da wani abu,dabi’un su hindatun su canza gaba daya,abubuwa da yawa sun daina yinsu yanayin shigarsu ya canza sosai,wanda hakan ya bata mamaki,saidai bata taba tambayarsu ba.
Hindatun ce ta qaraso ta taba zahran dake kwance rub da ciki,saita daga kai tana duban hindatu,hijabi ne dan madaidaici a jikinta wanda ta dorashi saman abayarta,wadda ta rufe jikinta ruf
“Tunanin me kike mrs haidar?” Murmushi ta saki,ta tashi ta zauna tana duban hindatun,fuskarta qunshe da murmushi
“Ina mamakin me ya canza qawayena haka tashi guda” murmushin itama hindatun tayi,ta zauna gefan zahra
“Tasirantuwa mukayi da qawar qwarai,hakan shiya canza mu,sannan kuma mukayi aiki da hankali da tunanin da Allah ya bamu,muka ga cewa
23/10/2021, 08:49 – ๐๐ป๐๐ป: 39
Da yammacine liqis,tana zaune a falon hajjanta,gidan yau kusan shuru yake saboda dukka yaran gidan suna islamiyya,saura kuma kowa yana wajen sabgarsa ta yau da kullum,kamar sassan nasu yau su biyu ne daga ita sai hajjan.
Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana jin dadin xaman sosai.
Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta dashi a tata wayar
“Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa’a gaya mata” shuru taji anyi,duk da cewa da alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
“Hello….ance hajjan bata kusa,idan ta fito za’a gaya mata” jin still dai an sake yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.
Tana shirin shiga wani grp nasu na ‘yan makarantar kachako unity girls,group ne na ‘yan set dinsu da suka gama makaranta a shekarar,saiga saqo daga saman watsapp dinta ya shigo da baquwar number,bata fasa shiga grp din ba,sai data shiga ta gama uzurinta ta fito sannan ta duba saqon,saqone da bai wuce layi daya ba,amma saiya tsaya mata a rai,ta dinga nanatashi ita kadai
*_KINYI NESA DA IDANUNA DA RAYUWATA,AMMA KINA KUSA DA RUHI DA ZUCIYATA_*
sake shiga profile din tayi ko zata ga suna,babu suna babu dp,ta bincike contact dinta tsaf babu me irin number,zargin da yazo kanta yasa tayi saurin daukar wayar hajja ta bude,ta loda numbers din ta danna dial ko zataga suna ya fito a number amma babu,tabbacin zarginta ba haka yake ba kenan,ba haidar bane,to waye?.
Jin takun tahowar hajjan yasa ta maida mata wayar ta ajjiye,don ta lura yanzu wani gani gani take mata akan wayarta,saidai ta ganta hajjan
“Me akemin da waya ne?,bana son fa satar lamba ahto….idan mutum naso yayimin magana da kaina na dauka na bashi” shuru zahra ta mata,sai da taga ba zatayi shuru ba sannan tace
“Ni ai duka wayarki hajja babu lambar da xan sata fa,babu,ni kawai ko bandakin zaki shiga ki dinga shiga da abarki ma huta” baki ta tabe
“Oho dai,banda rashin gaskiya daga jin tahowata sai a maida waya da sauri a aje,kinga kuwa ai babu gaskiya ne” ta qarasa maganar tana zama,sai kawai zahran tayi kwanciyarta ba tare data sake amsa mata ba,tana ci gaba da maimaita saqon,jikinta yana bata daga inda saqon ya fito,amma zuciyarta ta gaza gasgata hakan,har sai data gaji da kallon saqon,kamar shi xai bata amsar tambayarta,ta sauka daga watsapp dinma gaba daya,saita dora wayar saman qirjinta ta lumshe idanunta tana tuna wasu abubuwa da suka zame mata farilla kullum sai tayi bitarsu a kwanyarta,haka nan tunasu suke sanyata nishadi suke kuma debe mata kewa.
****** ****** *******
*_BAYAN WASU KWANAKI_*
Yamma ce lis,wanda tun safiyar ranar ake fama da hadowar hadari da kuma washewarsa,saidai zuwa yammacin hadarin ya hadu sosai a sama,yana bada iska mai sanyi hadi da qamshin qasa,wanda hakan ke alamta cewa ruwan sama na tafe kowanne lokaci daga sannan
Ita da umaima da ilham ne a falon hajjan,ilham na mata manyan kitso a kanta saboda wankeshi da tayi,ya kuma isheta hakanan babu kitso,tana mata kitson suna hira jefi jefi,suna kuma kallon tashar arewa 24,gidan yauma babu mutane sosai,duk sun tafi sunan faccalar hafsat data haihu,da yake macace me kirki,kusan kowa ya santa a gidan,sauran yaran kuwa kowa yana makaranta.
Suna daga zaune suka jiyo qarar shigowar mota harabar gidan,ilham ta kalli umaima
“Kai….yau wani cikinsu abba ya dawo gida da wuri,mun shigesu yau munyi fashin makaranta….wallahi mu nema wajen buya” harara zahra ta aike musu tana cewa
“Ko kun buya saina gaya musu,ba yadda banyi daku ba ai kuka qi ji,haka ma hajja,gwara ma ku xauna suxo su ganku yafi muku sauqi” tana rufe baki hancinta ya soma shaqar mata qamshinsa,saita saki ajiyar zuciya,tana mamakin yadda ta damu da lamarinsa haka da yawa,tasan cewa ba shi din bane,kawai kamar ta saka lamarin a ranta ne da yawa shi yasa take jin hakan,don haka tayi shuru tana duban bakin qofar dakin hajja tana kallon yadda iska ke daga labulen falon.
Kamar a mafarki taga tsaiwar mutum bakin qofar falon,gabanta yayi wani faduwa data jima bataji irinta ba,ta daga kanta a hankali daga kan takalman da idanunta ke iya gani zuwa sama fuskar mutumin dake tsaye.
Haidar ne,cikin unifoarm na sojoji da suka bayyana zallar kwarjini da kamalarshi,cikakken unifoarm ne a jikinsa,saidai babu hula a a kanshi,kamar yadda ta lura ba kasafai ya fiya son sanya hular ba.
Idanunsu ne suka sarqe cikin na juna,kowannensu ya shiga kallon dan uwanshi,zuciyoyinsu na wani irin rawa tamkar an kusanta mayen qarfe da qarfe,a hankali ya soma takowa cikin falon,idanunsa cikin nata,wani irin abu mai qarfi yana jansa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,tamkar me sanda haka yaci gaba da takowar har ya iso dab da su
“Ya haidar sannu da xuwa” muryoyin ilham da umaima suka karade kunnuwansu,saiya cira idanuwansa a hankali zuwa kan yaran,sam baigansu ba,bai kula dasu cikin falon ba sai yanzu,saiya gyada kai,muryarsa da wani irin laushi ya amsa da
“Yauwa,sannunku” ya qarashe zancan idanunsa na sauka kan lallausan gashin zahran da ilham takai kitso na qarshe ta kalmashe mata jelar,a hankali cikin wani irin sanyi da laushi zahran ta miqa hannu ta jawo dan kwalinta daya zame tunda aka fara kitson ta lullube kan nata,idanunta har yanzu suna qasa,ta gaza sake hado ido dashi,sai zuciyarta dake wani irin bugu,duk sai suka miqe,ilham ta dauke man kitson da comb suka nufi qofa ita da umaiman.
Kansu gama ficewa hajja ta fito,tayi turus cikin mamaki tana dubansa
“Kai kuma yaushe ka shigo?” Fuskarta na washewa da fara’a
“Yanzun nan,ko minti daya banyi ba” sakin labulen data riqe tayi,ta soma takowa ciki
“Lale marhabin,wannan irin tafiya haka babu sanarwa babu labari?,tun muna ta zuba idanun ganinka har mun haqura mun janye” dan qaramin murmushi ya saki na gefan baki yana gyara tsaiwarsa,har yanzu idanunsa yana kanta,ita ke daukar hankalinsa tunda ya sanya qafafunsa cikin falon,wani irin kyau da haske yaga ta qara masa,sai yake ganin kamar an canza masa ita,bai sani ba,tsabar kewar data addabi ruhinsa zuciyarsa dama gangar jikinsa ce,ko kuma dai hakane da gasken ta sauya,yaci gaba da dubanta ta gefan ido sanda take miqewa daga qasa zuwa kujera,saboda wani irin weak da jikinta yayi cikin qanqanin lokaci
“Barka da dawowa” ta fada kanta na kallon yatsunta data sawa lalle jiya da daddare,saboda ta gaji da yadda sukayi fari,har faratan hannunta.
Ko kadan ba tare da wani jin nauyi ba,kamar ma ya manta da hajja dake wajen ya zuba mata mayun idanunsa
“Barkanki……mun sameku lafiya?” Yadda ya amsa din ya tilastata daga idanuwanta ta kalleshi,taci sa’a kuwa sun hada ido,saiya jefa mata wani kallo data ji ya girma kanta,tayi saurin dauke qwayar idanunta,sai kuma tayi rashin sa’a suka fada kan hajja,ashe su take kallo,hajjan kuwa data gwanance wajen iya fuskewa dauke idanunta tayi kamar ba’ayi hakan ba,saita miqe ma data jiyo ringing din wayarta tana cewa
“Yauwa….ina zuwa,Allah yasa nusaiba ce”.
Fitarta sai falon ya zamana daga ita sai shi,gyaran murya yayi kamar wanda ya qware,ta fuskanci so yake ta sake kallon qwayar idanunsa,wanda ta karanci al’amura masu dama a ciki,bata jin xata iya bari cikin lokaci kadan ta fadi qasa warwas,kota bari ya gane lagonta,ita din ba yau ta fara soyayya ba,tuntuni ta gama karantar kanta tsaf,ta kuma karanci inda zuciyarta tasa gaba,saidai karatun ya bata tsoro qwarai,saboda banbance babancen soyayyarshi data mata wani irin kamu ta ruwan sanyi da sauran soyayyar data yiyyi a baya,wanda yawancinsu sun mata kamu ne ta farat daya,bata taba zata ko kawowa cewa soyayyar da zata dinga shiga jikinka tana dafa ka a hankali tafi illa fiye da wadda zata kamaka farat daya ba.
Batasan ya akayi ba,tana tsaka da wannan tunanin ta shaqi qamshinsa sosai,wanda hakan yake gaya mata mamallakin wannan qamshin yana dab da ita fa,saita daga kanta da hanzari,yana tsaye a kanta ya kafeta da ido dai kamar maye,ya ciro hannunsa guda daya amma sai yayi saurin dunquleshi ya kuma janyeshi baya saboda jin motsin fitowa hajja,sannu a hankali shima ya janye jikinsa
“Zan shiga na sanarwa mama dawowata” ya fadi yana juyawa a hankali,saidai fiye da rabin hankalinsa yana kanta,so yake yaji kalaman bakinta,hakanan bai gaji da ganinta ba,yana son yajita cikin jikinsa,yaji dumin lallausan jikinta da yayi kewarsa kamar yayi hauka,baisan haka aikin yake ba,baisan harda kanshi zai nanawa hauka ba,inda ya sani,da bai fara aikin ba bare ya tafi da tabonsa,ya hanashi sukuni,rashin sukunin da saura qiris ya janyo masa damuwa kan aikin da yaje yi din.
Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,ta manta da wanzuwar hajja sam a wajen,sai suka hada idanu da ita,sake fuskewa tayi kamar bata fahimta komai ba,saidai can qarqashin ranta tana jin wani farinciki yana mamayarta,lallai ba shakka Allah shine abun godiya,ta gama karantar komai,tafiyar haidar din aiki ya zame musu kamar wani haske,kuma mataimaki wajen cikar aikinta,ba shakka lokaci yayi,lokaci yayi da za’a kawo qarshen komai kowa ya huta,zatayi qoqari tayi dukkan abinda ya dace,amma zata bashi sati daya kacal taga shin xaiyi wani motsi daya dace shima?.
“Tashi kije ki sama masa wani abun da zaici kafin ya kintsa,tunda yau tazarce kukayi mana saboda tsabar ganda da qyuya,kinsan kuwa shi din ba ci xaiyi ba” karon farko…..lokaci na farko da taji ranta babu damuwa babu takura saboda hajja tace ta sama masa abinci….lokaci na farko da taji tana marmarin shiga kitchen,tun daga qasan ruhinta zuwa zuciyarta,taji a ranta cewa she’s ready a dai dai wannan lokacin tayi dukkan girkin daya dace,don haka ba bata lokaci ta yiwa kitchen din tsinke.
Haka kawai ta samu kanta da zurfafa tunaninta kadan ta maidashi can baya,tana tuna kalolin abincin da yafi muradin ci,wanda a wancan lokacin matuqar su sukayi ya dinga gwalewa da kushesa kenan,wataran ma yaqi ci,har sai mama tayi masa fada sannan,ta saki murmushi tana tsaka da aikin,sanda ta tuna wani lokaci da hajja tasa ta diba masa abincin data yiwa abdulyasar,ranar kamar zaiyi me saboda tsabar hade gira,hatta hajjan tasha muzurai,akaci sa’a tayi magana,dama neman mai tankashi yake,yahau fada sosai,har sai dasu hafsat suka dinga kwasarsa suna gulmarsa a boye
“Hmmm…hala yau allurar sojoji ce ta motsa?”
“Allah sarki….duniya labari” ta fada a sarari ita kadai.
Bata dauki wani lokaci mai tsaho ba,kasancewar abincin dai dai cikin daya zuwa mutum biyu tayishi,ta shirya komai bisa wani tsari me birgewa,tana gyara kitchen din hajja ta shigo,ta kalli yadda ta tsara komai saita kyabe baki
“Ashe dai ashe dai,yanzu dukka zakin aka yiwa wannan?” Waiwayowa zahran tayi tana duban kwanukan data shirya da hannunta,sam batasan ma tayi abunda hajjan ta gani din ba sai data magantu,komai a tsare,duk wanda ya kalla saiya burgeshi bare ya bude ciki,flask din hajja ne sababbi,wanda jikoki da ‘ya’yanta ke siyo mata da wanda ake bata kyautarsu dake ajiyewa bata amfani dasu suta dauko ta bare ta zuba masa abincin a ciki
“Ya gama ci kuyi lissafin kudin kwanukana,saikun bayani,ko naje har gida na fanshe a kitchen dinki” kunya taji ta kamata sosai,don bata kawo komai a kanta ba sai yanzu,sai ta yiwa hajjan tabarmar kunya,tahau zumbura baki tana cewa
“Wai komai mutum yayi shi bai iya ba,inafa zaman zamana kika ce sai na masa abinci….inda naqi tashi kuma nan ma qilu ta jawo bau,nayin kuma nan ma ban miki gwaninta ba….to inaga kawai a fasa kai abincin”
“Iyeee…..to uwata,ni meye nawa a ciki idan baicin bama,asarata ko taku keda shi?,ki tambaya kiji,mijina bai taba neman abinci ya rasa ba wajena har ya mutu,girki ma daya amsa sunansa ba irin nakun nan ba taba ka lashe….wanda kula da mijinma kamar an muku gori sai ance kuyi,yo ni meye nawa afasa kai masa…..kai….mustapha” tahau qwala kiran gangan da ganganci,don tasan mustapha baya falon,baya ma gidan gaba daya,tun safe abba yusuf ya aikeshi gyaran motarshi,ai kam a sukwane ta saki kwanon hannunta cikin sink ta isa gaban kwanukan
“Saiki bari na bayar da kaina nida nasha aiki,amma kya kira ya musty mai shegen ci da saiya kusa hadawa da flask din duka ya cinye ma?” Dariya sosai ta qwacewa hajja ba tare data shirya ba,sai kuma tadan maze bayan ta gama dariyarta
“Ya suke da mijinki wajen shegen ci,kijimin yarinya” itadai sai raba ido take,kada hajja tayi mata aika aika,bata sake tanka mata ba har ta gama abinda ya kawota kitchen din ta fice abinta ko a jikinta.
Gangar jikinsa ce kawai zaune waje daya da sunan hutu,amma gaba daya zuciyarsa da qwaqwalwarsa sun gaza samun hutun da yake buqata din,ga yunwa da yakeji amma ya kasa katabus,minti daya biyu saiya dubi qofar shigowa sashen nasa,haka kawai jikinsa ke bashi tana nan zuwa gareshi kowanne lokaci,saiya yunqura zai tashi ya aiwatar da abinda zuciyarsa ke gaya masa,sai kuma miskilanci ya maidashinya zaunar,yana sonne ya tabbatarwa kansa cewa aikinsa yayi kyau?,duk da ya fara ganin alamomi da suka sanya ya baiwa kansa mark,tare da shanshano qamshin nasara,mutum ne shi daya tashi kaf rayuwarsa cikin cimma nasara kan abunda yasa gaba,matuqar nasararsa ta kasance……to wannan shine mataki na qarshe da zai kawo qarshen komai.
Miqewa yayi a karo na qarshe,yana jin juriyarsa da haqurinsa sunkai qarshe,bazai iya ci gaba da zaman jira ba,saidai yana isa bakin qofa yaji an murda handle din an turo qofar,dai dai sanda wayarsa ta dauki ringing,saiya dakata daga bayan qofar,ya ciro wayar yana dubawa.
Daya daga cikin jami’ansu ne me suna Deborah,tana qarqashin jagorancinsa,saidai ita din likita ce,wadda sanda suka dawo yabar kulawar sojojin da suka dawo dasu marasa lafiya da masu rauni ana kula dasu a asibitinsu,itace kuma shugabar likitocin ya buqaci zamun duk wani bayani bayan ya tafi kan ci gaban da aka samu kan marasa lafiyan,babbar macace sosai,don tayi shekara a qalla arba’in da takwas,kaf cikin ma’aikatan mata ita kadai yakewa dariya,saboda yana ganin girmanta kamar yadda take ganin nashi.
Mummunar faduwar gaba hadi da bacin raine suka bijiro mata sanda taji ya ambaci sunan mace cikin wayarsa,hakanan yana wayar cikin sakin fuska,abinda ba zata iya tune yaushe ne lokaci na qarshe data jishi yana waya da wani koda namiji bane cikin walwala haka,wani abu ya taso ya tokare mata maqogaro,har yasa kunnuwanta suka toshe,ta daina ji ko gane maganar da yake,maganganun da hasashen da zuciyarta keta kawo mata su take fahimta,don haka tana dire kwandunan hannunta tayi hanyar fita ba tare data ko kalleshi ba.
Duk takunta daya idanunsa na biye da ita,sai hankalinsa ya rabu biyu,rabi naga wayar da yakeyi,rabi kuma na akanta,karon farko daya taba qarewa tafiyarta kallo,kamar wadda ke rangaji haka takunta suke a tsare,saidai yanayin halittarta ne hakan,batasan ma hakan na faruwa ba.
Ganin ta nufo qofar gadan gadan saiya taka a hankali ya qarasa rufe qofar,ya murza muqulli ya rufeta gaba daya,sannan ya jingina jikinsa da qofar,sai ya zaman shida ita suna fuskantar juna.
Zata iya cewa bataji ya yiwa wadda suke wayar sallama ba,yadai zame wayar daga kunnensa ya jefata gefanshi,tsintar kanta kawai tayi cikin jikinsa,ya mata wata kyakkyawar runguma da taso zabge duk wani baci da ranta yayi kan wayar da yayi yanzun.
Tuni jikinta ya soma mutuwa saboda qamshij da jikinsa ke fitarwa,da wani irin dumi dake fita daga jikinsa zuwa nata,amma duk da haka ta aje wannan gefe,ta soma turashi da yunqurin barin jikinsa,da sauri ya sake yi mata qawanya da hannayensa yana sake yi mata kyakkyawan mazauni cikin qirjinsa yana fadin
“Ke……relax mana,kada kiyi kishi….abokiyar aikina ce fa,nothing else” mamaki ne ya kamata sosai,ya akayi ya karanci haka daga idanuwanta kawai?,kamar me aiki da sihiri,ko kuma wanda ya karanci ilimin sanin halayyar dan adam.
Mintuna a qalla kusan biyar suna tsaye a haka,shuru ba tare da ya sake cewa komai ba,ita dinma haka,kowa na sauraren bugun zuciya da fitar numfashin dan uwansa,ita kanta batasan ke ya debeta taci gaba da zama cikin jikinsa ba,sai taga ya kamata tayi koda pretendin ne,kada ta zubda kanta
“Ka sakeni” ta fada tana tura hannayensa,da sauri ya hannunsa ya birkitota ta dawo tana fuskantarsa,a maimakon dazu data bashi baya,hannayensa duka biyun ya sanya ya kama qugunta ya ruqe yana qarewa fuskarta kallo,cikin wata murya mai laushi da sanyi,can qasan maqoshi wanda koda kana kusa dasu sai ka kasa kunnenka sannan zaka iya jin abinda suke fada yace
“Zahra….” Mamaki ya kusan kasheta a tsaye a wajen,dama yasan sunanta ne?,eh dole tace haka,saboda tsahon rayuwarsu cikin gidan bata taba jin ya ambaci sunanta ba ko a wasa,ji tayi duk duniya kamar yafi kowa iya ambaton sunanta,kamar ya fadi sunan nata ne da wani yaren daban ba hausa ba
“Ke kadai ce rayuwata bata da amfani cikin taki rayuwar ko?” Ji tayi tambayar ta mata nauyi sosai,bata kuma gama fahimtar abinda ya fada din
“Yes….kowa yayi kewata amma banda ke….kowa yana nemana amma banda ke,kyautawa kenan?” Lallai yau mamakin da haidar din yake bata ya wuce tunaninta,da zata iya zata so ta daga kanta ta kalli idanunshi da fuskarshi,don ta samu tabbacin daga bakinsa kalaman ke fita
“Kin kyauta….matsamin daga jiki” kamar me jira kuwa ta janye jikinta,haushi ya cikata taf,ita din ya nemeta?,sau nawa yana kiransu hajja tana wajen ba wanda ya taba bi ta kanta,kwanciyarta a asibiti saboda waye tayi?,ko don ba zata iya gaya masa bane.
Caraf aka riqe hannuta,ta waiwayo da sauri don har ta soma yin gaba,fuskarshi a hade kamar bashi ne yayi maganar da yayin dazun ba,saiya sakar mata hannun sanda take zamewa itama daga hannunsa,ta juya zuwa inda ta ajjiye abincin ya bita a baya,ya samu waje ya zauna.
Duk wani motsi da zatayi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wanda hakan ke sake narkar da ita,kamar zata saki kuka haka takejin zuciyarta na rauni,wani abu mai qarfi yana ratsata loko da saqo,daidai sanda ta kammala zuba mishi abincin wayarsa ta dauki tsuwwa,hajja ce saiya daga kanshi tsaye,ya kuma sanya handsfree
“Zaki…..maza ka turomin innawuro….hadari garin” shuru yayi yama kasa amsawa hajjan,shi abun nata ma mamaki yake bashi,haushi ya kuma cikashi sosai,da gaske wannan karon yaji haushi har ransa,don haka yace
“Gata nan,daga yau a dinga turo min mustapha shamsu ko ibrahim su dinga kawomin abincina” saiya katse wayar,tana jinsa bata waiwayo ba,saita qara wuta,dama neman hanyar tafiyarta cikin sauqi take,don ita kadai tasan yadda yake qara wa zuciyarta pressure,tana jin kamar ba zata iya dogon xama dashi ba.
Tana fita ruwa ya tsinke,saita tsaya cak tana kallon yadda ruwan ke sauka daga sama da gudunsa,shahada tayi ta saka qafarta ta fara takawa cikin ruwan,wata walqiya me azabar haske aka saki,take ta haska ko ina kai kace tsakiyar rana ce,cikin sakanni ta dauke,kafin ta gama mutstsika idanunta da walqiyar ta kashe tsawa mai qarfi ta biyo baya,ai batasan sanda ta juya da mugun gudu ba ta koma ciki.
“Subhanallazi yusabbihur ra’adu bi hamdihi,wal mala’ikatu min khifatihi” ya furta addu’ar tsawa sanda yaji tsawar,yana gama rufe bakinsa tana shigowa a rude,ta jiqe sosai sai diga takeyi,sunayin arba kuma saita daburce,ta karanci abinda ya tsoratatan,amma sai yayi kaman bai gane ba.
Qin zama tayi tana ta leqen ruwan,saidai ba alamar zai dauke,ga sanyin ac ya hadu da jiqewar da tayi yana kadata har cikin jikinta,shima ya lura da hakan,amma yana mamakin dakiya da taurin kai irin nata,ya gama karantar komai daga gareta ta cikin qwayar idanunta,amma taba qaryata kanta da kanta da ayyukanta.
A hankali taji sanyin yana raguwa,data lura ashe kashe acn yayi,ya maye gurbinta da room heater,saita dan samu nutsuwa kadan,ta sake saka kanta tana leqen ruwan.
Ta saman kanta taji an yafa mata wani abu me qamshi,ta daga kanta da sauri sai taga ya bude mata lema
“Muje” kawai ya fada,ta tsaya sosai ta fara takawa yana biye da ita riqe da lemar,hannunta riqe da abinda ya yafa matan,wanda ya kasance qaramin bargo ne mai laushi sosai,kuma yana da nauyin da zai kare maka sanyi.
Tayi mamakin yadda yake tafe cikin ruwan,yana riqe da lema yana kare mata ruwan,shi kuma ruwan yana dukansa kamar bai damu bama,hakanan taji ta kasa daurewa,kamar idan tayi shuru bata kyauta ba,cikin sanyin murya tace
“Da ka saka lemar kai a kanka….ni wannan bargon zai qarasa dani ba tare dana jiqe ba”
“Kada ki damu,an koya mana tsaiwa cikin ruwa da rana kona awanni nawan ne ba tare da mun gaji ba…..” Kai ta jinjina tana ci gaba da tafiya yana biye da ita.
Suna zuwa bakin sassan hajjan ya zuge lemarsa ya juya abinsa,saita tsinci kanta da cewa
“Na gode” juyowa yayi kawai ya kalleta sannan yayi gaba,sai dataga bacewarsa cikin ruwan dake sauka farfajiyar gidan sannan ta taka ta shige sassan hajjan.
A falo ta tadda tsohuwar tana shan kunun tsamiya,ta rasa qaunarta da kunun tsamiya,saita bita da kallo sanda take sauke bargon daga kanta,can cikin ranta taji tausayin haidar din,daga yadda ya amsata tasan yaji zafi ne,to amma koma meye tafison sai an aiwatar da komai daya kamata sannan,yadda hankalin kowa zaifi kwanciya,ta tar cikin gidansa,an rakata kamar kowacce mace,ko a baya ma data barsu tayi yaqinin ransu babu komai a ciki,babu wannan abun data gani yana yawo yanzu cikin idanuwansu a da din (hmmm to hajja,Allah yasa dai burin naki ya cika na miqa zahra’u dakinta).
Dakinta ta wuce ta canza kaya,ta dawo falo taci abinci,bata jima ba taji bacci na ziyartar idanunta don haka ta wuce dakinta abinta tabar hajja da husna da ilham,wanda suma wani lokaci nan wajenta suke kwana,abba babba ya tsara hakan,saboda yace zahra’un idan ta tafi xa’a bar hajjan ita kadai ne a sassan,kuma ko yanzun ma idan ta tafi makaranta wajen nata babu kowa,shi yasa suka yo qaura suka dawo,dama kuma sunfi son nan din.
*_BAYAN KWANAKI BIYU_*
Kwanaki biyu kenan da dawowarsa,qarfe sha daya saura na safe ya shigo sassan hajjan,a lokacin abba babba abba yusuf da abban tsakiya duka suna falon hajjan,zahra na kitchen tana wanke kwanukan data hada musu breakfast,don tun safe sukazo suna ta lissafi,na haqqin Allah da za’a fitar cikin kudin hajja da ake juya mata,lokacin fiddawa yayi.
Tunda ta gama ta zuba masa nasa a fulasan da ake zuba masa kamar koda yaushe,kwanaki biyu kenan tun randa ruwan saman ya tareta hajjan bata sake bari taje din ba,saidai ta bayar a kai masa kamar yadda ya fada,ita kam zahra nata idanu ne,saboda tasan halin hajjan,katafila ce sarkin aiki,takan kowa take bi idan aikinta ya tashi.
A ladace ya cire takalmansa ya qaraso gabansu ya tsugunna,daya bayan daya ya gaidasu,yaji dadin samunsu a tare,tunda yaje bai samesu a sassansu ba dama
“A kawo maka abincinne?” Hajja ta tambayeshi,tunda ta lura kwana biyu wani shareta yake,tun ranar nan,itakam ko a jikinta,tunda tasan koma meye qarshe shi zaifi kowa mora
“A’ah…zanyi magana idan za’a kawomin din….magaa nakeso muyi dama” abbansa ne ya daga kai ya dubeshi yana ninke takardar daya gama rubutu akai,abba yusuf ne ya amsa
“To Allah yasa lafiya” qasaitaccen murmushin nan nashi na gefan baki yayi sannan yace
“Lafiya lau abba…..cikin yarjewar ubangiji inason satin nan da zamu shiga in sha Allah mu wuce umara,nida hajja da abba na…..da kuma mama” Wani farinciki ne ya bayyana sosai saman fuskar hajja,burinta a duniya kenan ta koma qasa mai tsarki,duk da cewa taje har sau biyu,hajji daya umara daya,amma wajene da babu musulmin da bazaiso ya dawwama ma a can ba,lallai ba shakka haidar din wata kyautar Allah ce cikin iyalinta,soyayyar da yake mata mahaifi da mahaifiyarsa kai dama ahalinsa gaba daya abarso a sameta ce cikin zuciyar kowanne daga cikin dangi,don samun dorewar qaunar juna da danqon zumunta.
Kowanne a parlour din son barka yake gami da sanya masa albarka,tare da yaba wannan namijin qoqarin sa yayi
“naso ace na qara da abban tsakiya da abba yusuf,to amma kudin hannuna sun qare,ba zasu isa ayi komai na mutum biyu ba,amma in sha Allah sune a lissafina na gaba” nunawa sukayi babu komai,su da dan uwan nasu duka abu dayane,sannan suna da yaqinin da yardar Allah shi mai kai kowa ne cikin dangi idan da halin yiwuwar hakan.
Sun dan jima anan suna tattaunawa cike da farinciki,kafin daga bisani suyiwa hajja sallama kowa ya nufi wajen neman kudinsa,sai falon ya rage daga hajjan sai haidar din,sai kuma zahra dake kitcehn tana dora abincin rana kawai don idan ta zauna ta huta gaba daya,inna gaje ciwon qafa ya hanata zuwa aiki tun shekaran jiya.
Kira hajjan ta qwalawa zahra tace ta fito da abincin haidar,ta zata kai masa za’ayi,batayi tunanin yana falon ba don haka ta fito gaba gadi haka abunta,wata straight gown ce a jikinta,wadda tayi mata das a jikinta.
Da kallo ya bita bayan ta gaidashi ta aje masa abincin ta koma,suna hada ido da hajja ya hade rai tsam sannan yace
“Yanzun haka take yawo anan?”
“To uban mutane,sai akayi yaya?ni bama wannan ba,tafiyar nan da zahra’u ya dace ayita,don baka je dakin Allah haka ziqau ba,kabar kyautar da yayi maka a gida ba” kallonta yayi ya soma zuba abincin yau da kanshi ba tare daya nema wani ya zuba masa ba
“Yanzu dai babu kudi hannuna,saidai nan gaba idan Allah yayi” hade ranta tayi sosai
“Eh na sani ai ubana…..ni zan biya mata da kaina,saboda haka a sama mata komai da komai,idanma za’a dage tafiyar sai lokacin data samu to a dage din” baice mata komai ba,dama kuma tasan halinta ba zaya tanka ba,don haka taci gaba da sabgarta kawai,tana ta kiran ‘yan uwa daya kamata su sani tana gaya musu batun biya mata umarar,abun mamaki kuma don iya qarfa qarfa irin na hajja sai take hadawa da zahra kan harda ita za’a tafin,shidai yana zaune yana cin abinci yana kuma kallon ikon Allah,zahra kuwa na kitchen bata ma san wainar da ake toyawa ba.
Sai da ya gama cin abincinsa sannan ya miqe ya fice,dole zaiyi maganin hajja,zai kawo qarshen wannan mulkin mallakar nata,zata ga nasa qarfin ikon akan aurensa,don haka tun a motarsa driver na jansa ya kira anty alawiyya.
Bayan sun gama gaisawa tayi masa godiya da addu’ar qaruwar aziqi kan umarar da ya biyawa iyayensu saiyayi mata maganar da ita ta sanya ya kiratan
“Kaya nakeso a hadamin,irin wanda ake hadawa amare a akwati” dariya ce taso kubce mata amma ta danne,don kada tayi dariyar ta jama kanta jagwal,duk da cewa ita ke gaba dashi
“Ohkey…..lefe kenan….kaman na nawa?,kuma akwati nawa?”
“Akwati bakwai is okey,nayi hidima da kudaden hannuna….amma banison kaya low quality please,designers kumadd high quality”
“In sha Allah babu matsala”
“Please su zama ready kafin na dawo”
“To shikenan….babu damuwa” saiya yanke wayar ya aje gefa,ya maida idanunsa kan titunan da suke wucewa.
23/10/2021, 08:50 – ๐๐ป๐๐ป: 40
Wayar ya sake jawowa,wata number ya sake laluba,wanda suke masa aikin ginin filin da ya siya a nan,yadan jima da siyan filin,tun farkon fara aikinsa ya hada albashinsa ya siya,hakanan da kadan da kadan ake aikin gininsa,yadda zaifi masa sauqi bazai wahala ko ya kashe kudi masu yawa ba lokaci guda,zuwa yanzu ginin yayi nisa qwarai,don abinda ya rage ma sauran abubuwan da ba’a rasa bane,da farko yayi niyyar ma ya kammala gidan ya saida,amma da yayi tunani sai yaga,bashi da mazauni kenan duk sanda yazo ganin gida saidai a cikin gidansu,auren da aka daura masa da zahra yasa ya fasa saidashin kwata kwata,saboda koba zahra ba dama dole zaiyi aure,idan kuma yayi auren zai dawwama zuwa gidansu ya zauna?,dole yana buqatar muhalli.
Da kamfanin yayi magana,ya shaida musu abinda yake da buqata cikin gidan,suka gaya masa kudinsa da zaya bayar,yayi musu alqawarin turawa zuwa qarshen wata,a sannan suna can basu dawo ba kenan a yadda ya lissafa,yana saka ran kuma kafin su dawo din an kammala komai,saiya aje wayarsa yana ci gaba da lissafe lissafensa cikin ransa,zuciyarsa fes,yana jin wata nutsuwa da sukuni suna ratsashi.
******** **** ********
Bai sakewa hajja zancan tafiyar zahran ba,kamar yadda bai amshi kudinta ba,tayi tunanin waskewa yakeson yi,saita matsa da mita da qorafi,sai ranar daya sameta zaune ya miqa mata komai da komai na tafiyar zahran da aka kammala bayan an dage tasu tafiyar da sati daya.
Kwalla ce ta qwacewa hajjan,abinda bai taba zaton gani daga idanunta ba,duka shida zahra dake zaune a gefanta suka zuba mata ido,jikinsu duka yayi sanyi
“Allah yayi maka albarka,ubangiji yaci gaba da gin riqo da hannayenka,Allah ya kula maka da rayuwarka,yadda kake taimakon al’ummar annabi kake kula da iyayenka da ‘yan uwanka….Allah yayi maka kyakkyawan sakamako,haidar….kaida zahra Allah shine shaida….kaf cikin jikokina babu wadanda suka shiga raina kamar yaku,hakan ya sanya nan duniya tun kuna da qanana bani da burin daya wuce Allah ya hada kanku kuso juna ku zama miji da mata,sai wani al’amari me daure kai ya soma gudana a tsakaninku,amma hikima ta ubangiji da baya maida addu’ar bawansa,sai gashi ya kawo hadin aurenku ta fuskar dani kaina ban tsammata ba…..haidar….ga zahra nan,a yau zan baka amanarta…ka riqe amanar zahra,kai da ita duka nasan halayenku…hakan ya sanya nake da yaqinin dukkanku kun dace da junanku,zaku gasgata abinda nake fada din,zahra,haidar yayanki ne kuma mijinki,ki bishi ki masa biyayya,ki masa biyayya kamar yadda musulunci ya tanada,Allah ya albarkaci rayuwarku” cikin sanyin jiki dukkansu suka amsa da amin,saita miqawa zahra passport din hannunta
“Zaki tafi umara tare damu,mijinki ya biya miki” kamar a mafarki taji fitar furucin daga bakin hajjan,saita daskare a zaune tana jujjuya passport din,yau itace zata qasa me tsarki ta qarqashin ya haidar din?,mutumin da take masa kallon mara qaunarta,wanda bayason yaga suna farinciki da walwala?,mutumin da take kiranshi da mara ALKIBLA?,mai baudadden hali,wanda sam ALKIBLARSU bata zo daya ba,ashe ta sanadinsa zata je taga ma’aiki?sai qwalla ta cika mata idanu,ta sake matsawa kusa dasu muryarta na rawa saboda farinciki
“Na gode,Allah ya saka da alkhairi,ya qara budi,ubangiji ya biya da jannatulfirdaus” idanunsa ya lumshe yana jin dadin muryarta hade da dadin addu’ar data yi masa ya amsa da
“Amin”.
“Wannan kadanne daga alkhairinsa,alkhairin nasa kuma da zaya shiga rayuwarki matuqar kika ci gaba da bin maganar magabatanki,matuqar kika ci gaba da daukar zancansu da muhimmanci,na taba gaya miki,haidar ba irin sauran maza bane gama gari,tun a shekarun quruciya na gama karantar halayyarsa tsaf,tun kafin na haifeki nake sha’awa inama ina da diya da idan ya girma zan bashi ita?,yana da boyayyun nagartattun halaye da dabi’u,yana da sauqin kai da sanyin hali,yana da tausayin mace…..amma dukka ba kowa ke iya karanta da gane hakan ba,saboda matuqar zaka mu’amalanceshi daga nesa,to tabbas zaka masa fassarar mai ra’ayin riqau,mai kakkausan hali,mara tausayi ne,mai zafi da saurin fushi,eh aliyyu yana da ra’ayin riqau akan gaskiya,yana da kafiya kan abinda yasan shine dai dai,yana da fushi idan yasan an sabawa dai dai ko doka,yana da rashin tausayi akan azzalumin mutum mara imani,amma matuqar baka da irin wadan nan siffofin,zakaji dadin zama da haidar fiye da kowane dan adam…..zan baki tips na zama da haidar din,a matsayinki na diyata,ni kuma uwa a gareshi da tasan halayyarsa,ba don ki mallakeshi ba,sai don ki masa biyayya ku samu zaman lafiya da qauna me dorewa” wadan nan sune lafuzzan umminta a sanda take shaida mata batun tafiya da ita bayab ta miqa mata passport dinta ta sanya masa albarka,zama ummin tayi ta dinga zayyana mata abubuwa masu matuqar amfani a rayuwarsu,har zahran ta dinga mamaki da kunyar hakan,saidai ta lura ummin ko a jikinta,saboda ta sani tana gyara rayuwar diyarta ne,tana kuma inganta rayuwar haidar dinta,aikine da takejin ya wajaba a kanta a matsayinta na uwa
*_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO_*
Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don wucewa qasa me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama daya ta abba yusuf ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran biyunne na haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya suka koma gida da sauran yaran gidan da aka taho dasu.
Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana mamayarta,ko hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin magana bane,sau tari wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya wuce duba labarai,ko duba saqonni da suka shafi aikinsu.
Yana ankare da yadda ta kasa sakewa din,nutsuwar data sakeyi ta bashi mamaki,kusan tun tale tale yasan zahra cikin yaran gidan,tayi shuhura wajen aikata laifi da samun kariya daga wajen hajja da a wancan lokacin yake ganin daure mata qarqashi kawai takeyi,abinda ya janyo rashin jituwarsu kenan,yaci alwashin shi bazai bari ta buwayi kowa ba,duk da girma ya sake canzata qwarai,amma a yau din ta sake canzawa,wata kamala ta musamman ke kwaranya tun daga fuskarta zuwa jikinta.
Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba agogon hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a nutse yana daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.
Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna sau nawa ta taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar shadda gezner gray colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin annurin kyau yake fitarwa na musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba suna gani ba yadan ranqwafa ta gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
“Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki” saiya miqe ya barta daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran turarensa tana shaqa wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab dashi
“Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida” hajja ta fada,sai haidar din yace
“Akwai…..muje a duba mata” yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi gaba yabi bayanta.
Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu waiga kallon juna,kowanne saiya kama dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi haidar yana maida kansa gefe daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai amma dole saita ja masa aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma kunyarta,qaramar dariya ta kubce masa.
Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi saboda yadda ake binsu da kallo,abun haushinma yadda duk ‘yammatan da zasu gifta sai taga sun bishi da kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan matafiya kenan a ranar.
“Kai….nasma,kinga sojan nan,wanda ke zuwa gidan general hamza” daya daga cikin fararen ‘yammata uku sanye da baqar abaya ta fada qasa qasa tana tabo ta kusa da ita,wanda hakan ya faru a kunnen zahra wadda ke tsaye daga qofar provision din tana jiran fitowar haidar da ya tsaya biyan kudin ruwa da lemon da suka siya,wani abu ne ya takore wuyanta,ta juya a hankali tadan kallesu,dogaye ne don sun fita tsaho,hakanan farare ne ba kamar ita da take chocolate ba,hannun kowacce tsadaddar waya ce,wadda aka kira da nasma ta bada attention dinta inda haidar din yake tsaye,saita fidda ido
“Wow….wallahi shine,don Allah heedaya,yau ko ya za’ayi mu samu number dinsa please” daya ce ta zaro idanu
“Waye zai tunkari wannan?,ban taba gaya miki yadda muka taba yi dashi ba,tsinannen girman kai ne dashi,kulashi shine great mistake da zakuyi,ku nema number dinsa dai ta wata hanyar daban,koda cikin gidan general ne”
“Gidan general ba kowa sai matarsa,duka yaransa sunyi aure,ita kuwa ban tsammanin tana da number dinsa”
“Quiet sis….gashinan fitowa fa” dayar ta fada,duk sai sukayi shuru har zuwa sanda ya fito din,ya qaraso inda zahra take,wadda kishi ya cikawa qirji,ranta ya dinga suya.
Jerawa yayi da ita,kuma ta tabbatar yammatan nan sun bisu da kallo,a hankali ta saka hannunta ta lalubo nashi,saita hade tafukan hannunsu waje daya ta matse gam,taqi kuma duban fuskarsa.
Mamaki ya kamashi dajin faruwar hakan,saiya bi hannuwan nasu da kallo,laushi da dumin tafin hannunta yana ratsashi,ya dinga qoqarin lalubar qwayar idanunsa taqi bashi dama,har sai da sukaje kusa da inda su hajja suke sannan ta fara qoqarin zame hannunta,shi kuma yace baisan zance ba,hakan yasanya ta dakata da tafiyar da sukeyi,ta juyo tana dubansa,matsowa yayi gab da ita zai hade tazarar dake tsakaninsu,taja baya da sauri,cikin salon marairaicewa ta shagwabe masa tana masa inkiya dasu hajja da ido
“Idan kika sake lasa min zuma a baki ko?hmmmm…..” Saiya gyada kao ya zare hannun nasa a hankali,ya soma yarfar dashi,kamar wanda wani abu ya maqale masa.
Cikin jirgi ta kasa ta tsare,saboda ta lura ashe jirginsu daya da ‘yanmatan,number din set dinsu dama daga nashi sai nata,don haka harda qirqirar baccin qarya saman kafadarshi.
Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya sosai,shikam zuwan yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take kwance kafadar tasa yana tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta wuce gona da iri.
Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya hango masallaci,su shida harda wata ‘yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama umara ta kawota
“Daki daya mas’ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu zauna a daki daya” hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma haka suka amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji nutsuwa,yaji har ransa hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan tsiyar hajjan,don haka kowa shida kayanshi ya wuce dakinsu.
Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar jakar hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani lumshewa sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara
“Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki dinga kwana a bayanta?” Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa data dadu a idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke idanunshi,order din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.
Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka biyo baya,sun ziyarci gurare masu yawan gaske wadanda suke da alaqa da tarihin musulunci,manyan gurare da suke da tarihi da kuma alfarma.
Sosai imani qaunar Allah da manzansa suka sake shigarsu,a kwanakin ibada sukayi ba kadan ba,hakanan tsakanin haidar da zahra kowa ya tsinci kansa da yin addu’a cikin zuciyarsa kan katari da kyakkyawa kan tarayyarsa da dan uwansa,dukkaninsu babu wanda yasan dayansa yana addu’a dominsa.
A kwanakin da suke cikin ibadarsu duk da suna daki guda kowa yana kwancinsa,da sun dawo daga masallaci ko xiyara kowa zaiyi wanka ya samu wajen kwanciya,kusan duk kwanciyarsa a qasa yakeyi,yabar mata gadon,yayin data dinga jin nauyin hakan,duk sanda ta daga idanu ta ganshi kwance saman carfet sai taji kamar bata kyauta ba,a hankali ta tsinci kanta yana burgeta matuqa,baya ga soyayyarsa data shigeta ba tare data ankara ba,ta yi mata shigar burtu.
A wannan tafiyar ta sake gasgata zancan mahaifiyarta,duk abinda ta fada dangane da haidar din haka yake,yana lura da damuwar kowa cikinsu,baga mamanshi ba,baga hajja ba,baga abba babba ba,baga ita ba,kullum kwanan duniya saiya tabbatar babu me buqata ko matsala a cikinsu,bugu da qari ta fahimci yadda yasan addininsa yadda ya kamata,duk da ta sani cewa sam gidansu basa wasa da karatun addini,amma kuma bata tsammaci samun sani da fahimtar addini har haka daga wajen soja ba,ta manta cewa suna suka tara,iya zamansu bataga yayi fada ko fushi ko sau daya ba,kamar ma walwalarsa aka qara yawanta,ya qarfafesu dukkansu sun ribanci abunda suka je aiwatarwa,basu sake ba sai da suka gama ziyararsu kaf inda zasu iya zuwa,sannan suka soma kuma yawon ganin gari.
Ranar farko da suka dawo daga tafiyar ganin gari da sukayi,miqaqqiyat tafiya ya kaisu wani waje,a gajiya suka dawo,don a qafa yace zasu taho,yana yi yana kwasar hajja,don ma Allah yasa yana ganin idanun mamanshi da abbansa suna kwabarsa,haka ya sanyasu tafiyar qafa yace kowa ya wasa jininsa,hajja kam ta dinga masa mita,saiya dinga dariya yana cewa
“Cikin irin tafiyar da muke wannan ba komai bace,kamar kaje qofar gida ka dawo ne” sai suka hada ido da zahra,wadda ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah yau haidar din ke dariya?,saiya waske ya dauke fuska,wanda ta fuskanci kamar haka halayyarsa take,ya iya waskewa mutum.
A hanya suka ga wani kantin saida kayan qwalam da maqulashe,zaka iya siya ka tafi dashi,zaka iya kuma zama kaci a nan,hajja kam cewa tayi bata shiga,zasu tsaya a waje ita da mama,don dama shi abba babba tashi tafiyar daban,ya hadu da abokan kasuwancinsa a can tun zuwansu,don haka shi tare dasu yake,su hajja ne haidar din ke jagorantarsu,ganin haka yasa yace zahra ta biyoshi suje su siyo,su suka samu abun xama nan suka zauna su kuma suka wuce ciki.
Kamar kowanne lokaci ta gefan idanu suke satar kallon juna,jallabiyya ce a jikinsa irin ta maza harda hirami,ita kuma baqar abaya tayi rolling daya lullube mata fuskarta da rabin hancinta.
Ita ta dinga dauka musu abinda take ganin zasu iyaci,hannunta ya cika saita rasa inda zata sanya,tana waiwaya ta ganshi gefanta riqe da kwando,suka hada idanu saiya saki qaramin murmushi ya miqa mata kwandon,ta zuba a ciki,ga mamakinta binta kawai yaci gaba dayi tana zaba tana zubawa,kai kace yaro ne da uban gidansa har suka gama.
Wajen biyan kudin akwai dan layi,saiya duba daura dasu yace ta zauna anan kada ta gaji,idan ya biya zai mata magana ta taso su tafi,murmushi ya subuce saman fuskarta,mutum ne shi mai nuna kulawa qwarai,tana sane da yadda yakema mamanshi duk safiya,dama ba’a maganar hajja,duk wanda ke qarqashinsa yana samun kulawarsa yadda ya dace.
Dukka hankalinta na kansa a fakaice,yana tsaye kusa da wani balarabe suna hira,tana mamakin yadda yaji larabci har yake iya mayarwa yadda za’a fahimta tun zuwansu,kwatsam ta hangi wata matashiyar balarabiya ta iskosu,saita tsaya tsam,tun daga sanda ya waiwaya ya ganta,zuwa sanda taga alamun hira yakeyi da ita,fuskarshi da fadada da fara’a wadda ta qara masa kyau sosai.
ฦirjinta ne taji ya quntat sosai,saita miqe tana cire earpiece din kunnenta dai dai sanda yake juyowa shida yarinyar suna kallonta,yana kallo ta miqe daga gurin ta fice da hanzari,zuciyarta na mata zafi,tana hango yadda ya sake mata fuska sosai kamar ba haidar data sani ba.
“Ke lafiyarki kikema mutane tsaki?” Hajja ta tambayeta sanda ta isa inda suke,shaf ta manta data isa dab dasu,kishi kawai ke nuqurqusar zuciyarta
“Eh mun gama siya,na barshi a can zai biya kudin,wajenne akwai layi”
“Ai dama….su da basu rabo da siye siyen irin wadan nan abebaษen”.
Tunda ya fito har suka qarasa hotel a tsume take,taqi ma koda kallonsa bare ta nuna tasan da wanzuwarsa,cikin ransa hakan ke masa dadi gami da burgeshi,ko banza yasan ya gama kama zuciyarta TABBAS! baya ko shakka kan hakan.
Shima baice ba har zuwa sanda ya dawo daga dubasu mamansa,ya tabbatar basu buqatar komai kafin ya kwanta.
Sam bata tsammaci dawowarsa da wuri ba,saboda tasan yanayin awa daya a qalla idan yaje musu sallama kafin ya dawo,itama yau gajiyar da sukayi ne ya sanyata bata kuma fita ba,saita shige wanka ganin ya fita,donta samu ta shirya a nutse,tunda yawanci idan yana nan saidai ta shirya cikin hijabi,fitar tasa ne ya sakata fitowa daga wanka daga ita sai towel a daure a jikinta,ta kuma tsaya gaban mirrow tana shafa turarukan da take amfani dasu,sannan ta ware gashinta daya jiqe da shower tana son yadan sha iska kadan kafin ta maida ta kulle,dai dai lokacin daya turo qofar dakin kunnensa maqale da waya yana amsawa.
A badini ta tsorata,amma a zahirance saitaqi motsawa,saboda batason ta motsa ma ya dauka ta damu dashi,gwara ta nuna masa haushinsa takeji koda ba zaya fahimta ba,don haka taci gaba da tsaiwa gaban mudubin tayi kamar batasan ya shigo din ba.
Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki a jikinsa haka ya dinga ji,karon farko kaf rayuwarsu daya taba ganinta a haka cikin irin wannan shigar,take aka zare masa dukkan wani kuzarinsa da lakar jikinsa,saiya juya a hankali yana maida qofar tare da katse wayar da yakeyi,duk da bai gama isar da saqon da yake isarwar ba.
23/10/2021, 08:50 – ๐๐ป๐๐ป: 41
A hankali ya isa bayanta ya tsaya dab da ita,sai a sannan tsoro yadan darsu a ranta,amma ta dake taci gaba da tsaiwa,tsaiwarsa tasa har jikkunansu na gogar juna,ya daga tafin hannunsa ya dora saman kafadarta yana kallon fuskarta ta cikin madubin,saita motsa zata matsa,yayi hanzarin saka daya hannun nasa ya tsaidata tsam a wajen,sauko da hannun nasa yayi a hankali daga kafadarta zuwa dantsanta har yatsunta na hannu kamar me mata shafar mai,saiya hade yatsuntsu waje daya sannan ya saki qaramin murmushi
“Me yasa ko yaushe kike son nuna baki so,kuma baki damu ba,bayan nasan qaryane,kina so,kuma kin damu dani” idanu ta waro dukka yana kallonta ta cikin mudubi,duk da jikinta rawa yake saboda kusancinsu da tafiyar tsutsar da yake mata a hannayenta amma hakan bai hanata magantu ba
“Ni…..ni bana sonka,kuma ba damuwa nayi ba,koma meye kayi rayuwarka cefa”
“Kishi zalla”ya fada a sarari sannan ya birkitota ya zamana suna fuskantar juna,dukka hannayenta ya kama ya riqe cikin nasa,yana kuma kallon qwayar idanunta
“Rayuwar mu dai mrs pretender…..am tired….na gaji da wannan jan ran ranki ya dade,na gaji da jira,sai yaushe zaki yarda zuciyarki nason dan uwanki aliyyu kamar yadda ALIYYU KE SONKI!,sai yaushe zaki yarda kin damu da haidar kamar yadda HAIDAR YA DAMU DAKE?,sai yaushe zaki fuskanci ke dashi duka kun hau ALKIBLA DAYA ta soyayyar junanku?….idan ke kinqi fada,kina jamin aji ko?…..” Ya tambaya yana sakar mata wani murmushi da babu abinda yake qara mata face saukar mata da kasala,da kuma wani mugun sonshi
“Kin cancanci kija ajinki ZAHRATY…..amma yau kam haidar dukka wata jarumtarsa ta qare,duk dauriyarsa ta tafi,abinda ya jima yana boyewa,abinda ya jima yana binnewa,abinda ya jima yana tunanin ya mutu babu shi yau ya raya kansa da kansa…….” Saiya dora kansa saman kafadarta duk da cewa ya fita tsaho,yadan rusuna ya rage tsayinsa,ta yadda hakan zai bashi damar rungumeta sosai cikin jikinsa,laushin fatarta na ษai ษaita tunaninsa,yana jin kamar bakinsa bazai iya qarasa furta abinda yakeson fada ba saboda nauyi da yayi masa,kamae me rada,kamar wadda ake zanawa kalaman tun daga saman zuciyarta zuwa qwaqwalwarta haka ya dinga amsar kowanne furuci me cakude da harafi dake fita daga bakinsa
“Ina sonki….soyayyar da qauna ce tafi rinjaye da qarfi a cikinta,qaunar kuma da ba daga zuciya kawai take ba,ta ratsa jini qasusuwana da kuma tsokata…..qauna irin wadda ke cakude da numfashina da kuma raina,wadda babu yadda za’ayi ta fita daga jikina….saidai ta hada harda numfashina” kalaman da bata tsammaci samunsu daga wajensa ba,shi din daya kasance cikin sahun maza da dukkaninsu ta basu sunan MAYAUDARA kuma marasa ALKIBLA,cikin mazan kuma ya kasance mai baudadden hali,mara uzuri mai zafin zuciya da fada,yau shine rungume da ita kamar zai karya qasusuwanta yana gaya mata yana sonta?,shine rungume da ita kamar zai maidata cikinsa yake fasa mata sirrin zuciyarsa?,bata gama wannan tunanin ba taji numfashinsa na sauya yanayi
“Kina sona zahra?” Ya tambayeta kai tsaye sanda ya cusa kansa tsakanin wuyanta,saita kasa bashi amsa saboda yawo da yake da harshensa a wajen
“Uhmmmm…..ki amsa min mana” ba zata iya magana ba,saboda abinda yake aikata matan tuni ya sanya qafafunta sun fara rawa
“Ohkey…..bari na dasa miki sabon harsashin da zaki fara sona koda baki shirya ba” daga haka ta nemi haske a dakin ta rasa,yasa hannunsa tuni ya kashe dukkan qwan lantarkin dake dakin wanda yake kusa da madubin da suke tsaye,sai qaramar futilar gefan gado wadda me dim light,gaba daya ya dagata yayi mata masauki saman gadon dake dakin shima ya daga qafafunsa da yajisu kamar basu taba sanin meye qarfi ko kuzari ba ya haye saman gadon.
Saukar numfashinsa saitin kunnenta ya sanyata rintse idanu,bugun zuciyarta ya qaru sosai,qamshinsa ya cika mata hanci,jikinta yayi wani rauni lokacin daya fara aike mata da saqonni,ta rasa duk wani kuzari nata,ya saukar mata da kasala sosai,sai taji yasa hannunsa yana qoqarin zare towel na jikinta.
Da sauri ta damqe hannun nasa tana girgiza kai,duk daba cikin haske bane amma yana iya ganin motsawar kan nata,da wata irin raunanniyar murya yace
“Nooo……nooo zuhra….” Yana mirgina kansa hagu da dama shima,yadda ya soma komawa ne yake bata tsoro,tana tsoro sosai,don ba zata manta abinda yaso faruwa rannan ba,sake maidata jikinsa yayi tsam,saidai wannan karon cikin zafin nama yake ci gaba da aike mata da zafafan saqonni,masu rikita dukkan wani mai lafiya,da sanyashi cikin shauqi,saqonnin da suka kusa sanyata fita daga hayyacinta,cikin qaramin lokaci ya zautata,ya fidda duka wata zalama da qwarewa tasa,ya nuna hazaqa da fikirarsa,harya rabata da towel din ba tare da tasan anyi hakan ba,bata fara hawa saitinta ba sai da taji za’a maimaita irin na ranan nan,a sannan ne ta ankara da wayo kawai yayi mata,ta kuma lura da wautar data tafka,sai ido ya raina fata,ta razana sosai,taso ta sake bore,saidai inaaa…..ya hanata wannan damar,don koshi a sannan baijin yana da control na kansa da kansa bare ya yiwa kansa birki,bai sassauta ba,hakanan bai qyaleta ba har sai daya samu isa duniyar ma’aurata,duniyar dake maida biyu su zama daya,duniyar zahransa,duniyar data sanyashi a ranar sunansa da nata ya cika.
*_BAYAN WANI LOKACI_*
Kuka take sosai amma shi murmushi ne ke fita saman fuskarsa duk da yana jin kukan yana sukar zuciyarsa sosai,ya sani akaran kansa cewa bai raga mata ba ko dis,amma ya ya iya da ranshi,zai iya cewa ba laifinsa bane,tana maqale da ita kamar wanda aka ce masa za’a qwaceta,zallar sonta sabo fil yake kwarara cikin ranshi,kamar ya ciro zuciyar tasa gaba daya ya bata kyautarta,ba irin lallashin da baiyi mata ba,gashi har sha biyu da rabi na dare ta hanasu barci,shi da kansa ya gasata sosai,sannan ya barta tayi wankan,data gama shiya taimaka mata ta fito,amma wajen shiryawa fir taqi yarda,sai baya ya juya mata yana dariya ciki ciki yabarta ta shirya da kanta,ko a yanzunma da take kwance cikin jikinsa sai daya mata fin qarfi tukunna,baisan me zai sanyata tayi shuru ba,duk da ya lura irin shagwabar da takema hajja yau take sauke masa,shagwabar da abaya idan yaga tanayi yake aike mata da saqon harara ko tsawa,sai gashi yau yasa hannu bibbiyu ya amsa
“Kona kira miki hajjan?” Ya fada qasa qasa,da sauri ta maqale kafada,saita cusa kanta cikin qirjinsa tana sassauta kukan nata,ita kam waya aiketa da wata hajja?,tazo ta tijarasu kota titsiyesu da tambayoyi?.
Cikin salon qwarewa da dabara hannunsa saman sumar kanta ya dinga kashe mata jiki,har wani bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,wanda cikin baccin ajiyar zuciya ta dinga saki,sai daya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya sauketa a hankali,ya dora mata kanta saman pillow ya rufa mata duvet,sannan ya soma gyara mata sumar kanta yana kallon fuskarta,fuskar zahransa,murmushi ya subuce masa daya tuna tsiwa irin ta zahran,amma yau bakinta yayi laushi sosai,duk da cewa dama ta jima da canzawa,abubuwan da suka faru dazun suka dawo masa,rakin data dinga yi,magiyarta da ban hanqurin data dinga masa tana cewa ba zata qara ba,shi kuma yana tambayarta ba zata qara me ba,dukkansu shida ita ya tabbatar mahaukata suka zama tuburan,ita ciwo ya isheta,shi kuma duniyar data jefashi ne yasa ya kasa fahimtar komai.
Sallah ya sauka yayi yana miqa godiyarsa ga Allah,ya sani cewa ubangiji ya gama masa komai,sai kuma neman taimakonsa kan bauta masa da tsare haqqoqinsa,sannan ya kuma ya shiga lamarin xamantakewar aurensu,ya bashi ikon da zai riqeta bisa doron shari’a,kan gaskiya amana tausayi da kyautatawa.
Tana bude idanunta dashi ta soma tozali,ya sanyata a gaba yana qare mata kallo,saitayi rub da ciki da sauri tana boye fuskarta,yana murmushi shima ya haye bayanta,ya aza mata nauyinsa yana cewa
“Good morning zahraty amarya” sosai ya bata kunya bayan wadda takeji,nauyinsa takeji sosai,musamman idan ta tuna waye ya haidar a wajensu,amma gashi dare daya ya sauya komai a tsakaninsu,kamar bashi ba,kamar wani aka canza musu dashi,bata taba ganin fuskarsa a yanayin data ganta ba tsakanin jiya da yau.
Sai da yayi da gaske sannan ta miqe ta fuskanceshi,ya dinga tsokanarta,ya hanata sakat,ita kuma kunyarsa kamar qasa ta tsage ta shige ciki haka ta dinga ji,bai qyaleta ba yaci gaba da bibiyarta duk inda ta saka qafa cikin dakin,saidai bai fiya magana ba,amma ayyukansa na gaya mata komai,shi ya hada mata ruwa ta sake wanka,ya gyara dakin da kansa,don yace harsu tafi babu masu sharar da zasu sake shiga musu dakin,tayi mamakin yadda ya iya aiki da kansa,ashe dama a baya rashin ganin dama ne?,ko kuma sune basu fuskanceshi ba,itakam mamakin sauqin hali irin nasa take,komai nashi a sauqaqe yake yinsa,babu zafin nan,babu izzar nan da suke zatan masa ita.
Wayarsa ce tayi qara,ya qaraso ya daga,hajja ce take kira,bayan sun gaisa sai tace
“Lafiya na jiku shuru yau?”
“Eh…itace bata jin dadi sosai,ta sha magani ne,tana kwance” duk da ranta ya bata wani abu amma sai bata nuna ba,kawai tace
“Ayyah,qila tafiyar jiya ce da haka kawai ka kwasa mutane….ni dinma qafata ciwo take sai dana shafa magani,to Allah ua sawwaqe,ya bada lafiya”
“Amin amin” yana dubawa yaga harta kashe wayar ma,sai ya saki murmushi suka hada ido da zahra,itama murmushin kawai tayi,addu’a dama take kada Allah yasa asirinsu ya tonu wajen hajjan,sai gashi bata gane ba
“Ko zakije ku gaisa?” Ya fada yana kashe mata ido,kafada ta maqale,tasan bata isa taje ta fito ba hajja bata gano komai ba,don ko tafiyarta tasan ta sauya.
Wuni sukayi sur cikin dakin ba tare da shi ko ita sun fita ba,sai yayi amfani da wannan damar,ya dinga lura da ita tare da dasa mata sabuwar qaunarta cikin zuciyarta,bai yarda sunyi nisa da juna ko raba mazauni ba,ya sanya nata sabo dashi da saboda jikinsa,tun tana kakkaucewa harta sallama.
Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce…..da fatan alkhairi ta bisu sanda suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake qasan zuciyarta.
Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu ita ya zabarwa abubuwan da za’a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.
Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar kallonta ba,a hankali yace
“U r my first love” cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
“Yes u r”Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take dubanshi
“Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar ษa a wajen ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin gidan” yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
“Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan…nayi a hankali,kada kulawar da nake baki tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.
“Lokacin da kika fara girma a sannan na zama saurayi” saita kalleshi,murmushi ya subuce mata,saboda fadar hakan da yayi ya tuna mata da abubuwa masu yawa,ta kuma gane dai dai lokacin da yake nufi din,shima murmushin ya sake mata mai sanyi sannan yaci gaba
“A lokacin na fuskanci kaf cikin sa’anninki da tsararrakin kin fisu tsiwa…..kafiya…rashin tsoro da kuma taurin kai,kuma kamar hakan ya faru ne saboda kulawa da hajja ke nuna miki,kinsan dalilin da yasa na aje soyayyarki?,wanda ya zama musabbin da har yau babu wanda yasan ina sonki?” Kai ta girgiza a hankali cike da daukin son jin ci gaban labarin
“Abu na farko da ya sanya naji ya cancanci na ajeshi shine ummi….ummi na nuna miki qauna da soyayya qwarai,hakanan ta azani a matsayin yaya a gareki,wanda ya isa da duk lamuranki,ya isa ya yanke hukunci cikin rayuwarki fiye da sadiq…..sai nayi tunani a karan kaina,matuqar naci gaba da sonki har aka kai sanda zaki sani koki fahimta….to ya zamana babu me tsawata miki kenan kan kiyi koki bari?,idan har na aureki kenan babu sauran wanda zai dinga taka burki akan al’amuranki?,komai zakiyishi yadda kike so?,hakan zaiwa ummi dadi?,ko kuma zaifi mata dadi idan naci gaba da tsaiwa kan rayuwarki ne?…..hukuncin na aje din shi nafi ganin dacewarsa,saboda haka na ajjiye dukkan wata soyayyarki da nakeji a cikin raina,na shiga treating dinki kamar sauran,na kuma qara matsa lamba fiye da baya,abunda ya kuma sawa naji na gamsu da hukuncin da na yiwa kaina,sabon suna da suka miki inna wuro,uwar masu gida ko?,hakan na nufin kiyi abinda kikeso,sannan lokaci qalilan daga dan fara tasawarki samari suka yiwa rayuwarki caaaaaa…..naso hajja a lokacin ta yarda da tsarin da naso kafawa a kanki amma fur taqi,saboda tana ganin na fiya matsantawa,bana duba maraicinki…..kinsan wani abu?” Saita girgiza kai a hankali,labarin da yake batan yana mata dadi sosai
“A duk sanda wani yazo ya kuma yaudareki ya gudu…..na fiki jin ciwon faruwar wannan,nakan jima ina jin raina yana baci,duk da nakanji kishi,nakanji bacin rai duk sanda kike tsaye da wani da sunan saurayi,to amma sai zuciyata ta gayamin,tunda ka aje soyayyarta ka zabi bata kariya,dole zuciyarka taqi ji taqi gani,dole ka daure ka zama jajirtacce,ka fuskanci dukkan wani qalubale,na karbi wannan magana,na kuma sake jaddadawa kaina hakan,dalilin da yasa na karbi zahra takwararki kenan,na soma nazartarta da halayyarta…..”sai yadan tsaya yana aje numfashi idanunsa kan zahran yadda ta nutsu tana saurarensa tana kuma fahimtarsa
“Am sorry to say….tana da haquri….tana da sanyin hali,uwa uba nutsuwa da kamewa,sannan kuma sunanku daya,wadan nan dalilai sune kadai suka sanya na miqa mata wuyana,saboda nasan wadan nan halaye zasu dai dai da tawa dabi’ar da halayyar,zatona da hasashen saiya zama gaskiya,ta fahimceni fiye da yadda na zata,ta kuma banbance abinda nakeso da wanda bana so,a hankali sai zuciyata ta fara samun nutsuwa da sukuni,na kuma gamsu zahran ta dace dani,saidai duk da haka baki fita daga zuciyata ba….sau tari nakan tura mata saqo wanda a zahiri sanda nake rubutashi dake nake,saidai nasan cewa koda baki sani ba kai tsaye,kuna karbar wayarta,kuna kuma shiga inbox nata,idan akayi katari kika karanta to kamar na rage wani nauyi dake zuciyata,na kuma isar da saqona,don yawancin lokuta tana gayamin yadda kike nuna zallar mamaki idan kikaci karo da daya daga cikin saqonnin dana tura matan…..bazan boye miki ba….nayi missing zahra’u,na kuma shiga tashin hankali na haqiqa sanda na rasata,har nakejin ma kamar bani bane….kamar zan zauce….na jima….na jima ina dorawa kaina alhakin mutuwarta,saboda ta rasu ne a sanda naje makaranta ganinta,da wani yammaci,na dawo daga gwambe,na tsaya ta wudil ganinta,saboda munyi waya tun ina hanya.
“Sanda na shiga makarantar na sameta shuru,kamar irin anyi hutu dalibai sun kokkoma gida,to amma nasan ana tsaka da zangon karatu ne,ba lokacin hutu bane,waya na daga na kirata da zummar bata mamaki,don batasan da zuwa na ba,na gaya mata inda nake tsaye,cike da zumudi da mamaki tace gata nan fitowa,saina maida wayar aljihuna ina duban inda nake tsayen,wajene mai yalwar bishiyoyi dogaye da kuma tarin ciyayi mai tsaho,tunda nake zuwan mata makarantar lokaci zuwa lokaci bamu taba tsaiwa a wajen ba sai ranar,ina cikin karantar yanayin wajen naga bullowarta ta gefena,kamar kowanne lokaci cikin hijabinta,tana tafe tana murmushin ganina,saina bata dukka hankalina harta qaraso…..
“Me ya faru yau naga makarantar taku yau so silent” tambayar dana fara mata kenan
“Wallahi tun jiya da aka samu fitowar macizai ne,sai kowa ya tsorata ya lazimci zaman daki,don yau ko lactures ma ba’ayi ba” kai na jinjina sannan nace
“Amma da kin gayamin da bazan shigo ba bare na fiddoki daga daki” dariya tayi
“To na godewa Allah da ban gaya maka ba bare ka haramta min ganin fuskarka….komai muqaddarine ai daga ubangiji,koda ina daki duk abinda ya qaddara zai sameni saiya samenin”basai na gaya miki sauran abinda tace min ko nace mata ba…saboda tsaro ba don tsoro ba” ya fada yana murmushi,itama murmushin tayi tana girgiza kanta,idanunta a kanshi,ajiyar numfashi yayi
“Yau soyayya ta sani dogon magana…..a taimakamin da ruwa” hannunta ta sanya ta bude masa gorar ruwan sannan ta ajjiye masa,ya dauka a nutse ya soma sha,yana sha yana ajewa yashaqi numfashi har ya gama,ya aje robar yana sauke numfashi tsahon minti daya sannan ya dora.
“Bari na samo maka abun sha a wani kanti nan” ta fada ta soma takawa,da hanzari na tsaidata
“A’ah….ni ganinki kawai nazoyi,bana buqatar ci ko shan komai” kafada ta maqale
“Ban yarda ba….saboda nima irin karamcin nan naka nakeso na koya,saboda haka saina samu ladan baqona” daga haka ta soma takawa ta cikin ciyayin nan tayi gaba,a cikin zuciyata inason tsaidata amma kamar wanda aka daurewa baki na kasa,inasin ince kada tabi ta wannan ciyayin amma na kasa fada mata,inason ince mata ta tsaya na rakata amma dukka kamar wanda aka daurewa baki duk na kasa fada,ashe ajali ne,ajali ne ya kirata,don batayi wani nisa da idanuna ba naga gilmawar wani abu ta bayanta,na fuskanci maciji ne,idan nayi magana kuma zata iya rudewa,don haka na fara takawa da wani irin hanzari da zafin nama,dai dai sanda ta waiwayo tana kallona,sai fuskarta ta nuna mamakin ganina ina tahowa inda take da mugun gudu,bansan ya akayi ba saijin ihunta nayi ta durqushe cikin ciyayin.
Sanda na isa na sameta riqe da qafarta,ta hada gumi sharkaf tana juye juye,dana dauke hannunta saiga inda macijin ya sareta nan,na bata taimakon daya dace,na riqeta zuwa asibitinsu na cikin makaranta,saidai abun haushin abun takaici basu da allurar kashe gubarsa,raina ya baci sosai,amma ban tsaya biye musu ba,saboda kada bata lokaci ya jawo asarar ran da naketa gudu,na sanyata a mota kawai muka wuto zuwa kano.
“Irin gudun dana dinga tsalawa ni kaina nasan Allah ne kawai yayi motar ba itace ajalinmu ba nida ita gaba daya,tana cure waje daya set din gaba taba murqususun ciwo da azabar dafin daya zuba matan,hankalina rabi ga titi rabi a kanta,qarin abun haushin asibiti manya guda biyu mukaje suma basu da allurar a dai dai lokacin ta qare,sanda muka dauki hanya zuwa asibitin mu a sannan ta kalleni,launin idanunta yana canzawa
“Kayi haquri ya haidar….kayi haquri,kuma naga ranka ya baci,duk abinda Allah ya shiryawa bawa bai isa ya tsallake mishi ba” saita maida kanta ta kwantar,kalamanta suka dagan hankali,na tsaya gefan hanya sanda naga yanayin jikinta ya saki gaba daya.
Nasan a sannan ta mutu don zuciyata tana gaya min haka…..amma idanuna a rufe suke,saina tashi motata da mugun gudun da yafi na dazu na nufi asibitin,saidai abinda nake tsoro dai shi aka gayamin,zahra ta rasu,dafin yaci jikinta yakai inda ba’a so yakai……”saiya tsaya da bata labarin yana duban yadda hawaye ke zuba a idanunta,a wancan lokacin sam batasan yadda mutuwar zahra ta kasance ba,kawai dai tasan saran maciji ne,hakanan tana ganin haidar yaqi daukan qaddara ne kawai,amma data kwatanta mutuwar masoyi ko aboki gaban idanun abokinsa sai taga abun ba mai sauqi bane,dole ya shiga irin yanayin daya shiga din,kasa jurewa tayi,sai tayi qasa da kanta kuka na kubce mata.
23/10/2021, 08:50 – ๐๐ป๐๐ป: 42
Murmushi ya saki,sannan ya taso daga inda yake zaune,yaja kujera dab da ita ya zauna har gwiwarsa na gogar tata,hannunsa ya sanya ya dago fuskarta gaba daya,saiya girgiza mata kai alamun
“A’ah”yatsansa guda daya ya sanya ya dinga dauke mata hawayen,murmushi kwance saman fuskarsa,har sai daya goge duk wani hawaye da yayi saura,saiya hada goshinsa da nata suna musayar numfashi,qamshin turarensu na gauraya da juna
“A wancan lokacin kinyi fushi….kin nuna kishi saboda ganina da wata balarabiya…..wadda nake ganinta da muni sosai idan na hada da kyakkyawar fusakarki,da kuma yadda zuciyata ta rayu da sonki……ta samu dukka fara’ata ne da kulawa saboda yabonki da tazomin dashi,ta shaidamin tunda taga shigowarmu taji mun burgeta…..tana son qawance dake,dalilin da yasa ta biyoni kenan har kika ganmu tare….saidai kuma a yanzun gashi kina kuka saboda wata da na taba so na baki labarin mutuwarta…me yasa bakiyi kishin xahra ba?” Ta rasa amsar da zata bashi,amma dole duk me imani yaji a yadda zahra ta rasun ya tabashi,ta riga data wuce zahra ba zata taba dawowa ba,kishi da ita tamkar abun nan da hausawa ke kira da ihu bayan hari ne.
Murmushi ya saka yana cewa
“Na fahimta….amma har yau kinsan ban samu makwafin zahra ba?” Cikin mamaki ta zare fuskarta daga nashi tana duban idanunsa,saiya dage mata dukka girarsa
“Eh….ban sake samun wadda tacemin ALIYYU HAIDAR INA SONKA BA,ban sani ba ko baqinjini gareni?” Dariya sosai ya bata,yanayin yadda yayi maganar ma abun dariya ne,sai tasa hannu ta toshe bakinta,yayin daya harde hannayensa a qirji yana qare mata kallo,dariyarta kadai ta sanyashi farinciki shima,gami da saukar masa da nutsuwa
“Aikam saidai idan har shin haidar din ne baiso a gaya masa ba,a iya sanina akwai daruruwa ko ince dubban mata dake ta dakon randa xai basu dama su furta wannan kalma a gareshi…..” Tararta yayi ta hanyar watsa hannayensa,kamar zai saki kuka yace
“Ni dukkansu ban gansu ba,bansan da zamansu ba,zahran hajja kawai na sani,kuma ita kadai nake jira da dakon randa zata gaya min hakan…..” Itama bata barshi ya qarashe ba yaji saukar kalaman kamar ruwan sama saman zuciyarsa
“Ya haidar kadai nakeso….shi nake qauna har abada” idanunsa ya ware cikin mamaki yana dubanta
“Say it again please”๐๐ฝ,duk kunya saita cikata,ta maida kanta wani sashen tana murmushi,sai ganinshi tayi ya koma inda ta maida kan nata
“Please….inason na sake ji” wani qwarin gwiwa ya bata daga cikin idanunshi,saita kalleshi sosai
“Ina son ya haidar,ina sonka…ina sonka” gaba daya ya tattareta cikin jikinsa,ya manta ma suna waje ne,sai data ankarar dashi,ta tabbatar da a 9ja suke da tuni sun tara ‘yan kallo,da qyar yayi controlling kansa,ya komqa ya zauna dab da ita,muryarsa cike da wani irin softness ya kamo hannunta ya riqe tsam cikin nasa sannan yace
“Hakan yana nufin….kin mallakamin rayuwarki?,kin zama ni na zama ke?,zakici gaba kuma da kasancewa tawa har abada,munyi amanna wa juna zamu rayu da juna duk rintsi duk kin yarda da wannan?” A kunyace kan irin salon kalaman dake fita daga bakin yayan nata,da salon kallon da yake mata ta gyada masa kai,saiya girgiza kai
“Banison body language…..pls ki gayamin da bakinki”
“Amince…..na amince ya haidar” lightly yayi kissing saman hannunta,ya rasa da wacce kalma zai sake magana,kawai sai yaci gaba da riqon hannunta cikin nashi yana kallon kayarsa kamar za’a qwaceta,har sai da tayi waving hannunta saman fuskarsa
“Bansan me zance miki game dani ba,abu daya zuwa biyu kawai bakina zai iya gaya miki,da kanki zaki dinga bawa kanki amsar irin mijin da kikayi katari dashi,sannan ina miki albishir din cewa……zaki shiga sahun matan da sukafi dukkan mata sa’ar miji a duniya” daga haka ya miqe yana riqe da hannunta,itama saita miqe suka soma takawa cike da wani irin xallar farinciki dake yawo dasu a duniyarsu.
Kwan daya tak suka qara suka fara shirin dawowa,ya bata dama ta siya dukkan abinda take da buqata,siyayya me yawa da batasan me za’ayi dasu ba.
Kamar yadda suka tafi tare haka suka dawo,sun tadda ‘yan Tarbarsu danqam suna jiransu,family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,babu wani bambanci da xaka gani tsakaninsu.
Tun a airphort din ta ankare da yadda ‘yan gidan nasu keta gulmarta ita da ya zakin,saboda duk inda yayi yana maqale da abarsa,baya jin kunya ko nauyi sam,motsi kadan nata idanunsa da hankalinsa yana kanta.
Da zasu tafin bai bar kowa ya shiga tashi motar ba,zahran ta rasa dalili amma yayi fuska,ta sani dukkansu shakkarsa suke,saboda haka ba wadda ta iya tunkararsa,sai hafsat data rage bata samu waje ba,tayita zagaye tanason tace ya dauketa,amma ta kasa,sai zahran ce ta dubeshi
“Please ya haidar….maman khairat ce bata samu waje ba” ta fada cikin marairaicewa,wani kallo ya watsawa hafsat din ta window,ba shiri ta fara qoqarin juyawa tabar wajen,amma sai zahran ta yaficeta ganin baice komai ba.
Bai tanka musu ba har aka fara tafiya,basuyi nisa da airport din ba ya bawa driver umarnin ya tsaya,saiya fidda kudi tana ajema hafsat din fuska a tsuke
“Sauka ki tari napep ki hau…..” Kallonshi duka suyi cikin mamaki,saiya hade rai tsam,zahra ta dubeshi a shagwabe
“Yayaaaaa”
“Shshshshhh…ba gida muka nufa ba,so take muyita yawo da ita?” Mamaki ya kamata,toba gida suka nufa ba ina suka nufa kenan?,tana ji tana gani hafsat din ta sauka ta tari napep su kuma sukaja motarsu suka wuce,sai tayi kicin kicin ita ala dole fushi take dashi,bai tankata ba,data kalli fuskarsa ma sai taga walwalarsa yake abinsa.
Tanata zuba ido tana ganin yadda suka shiga unguwar,mamakin wajen wanda zasuje take,daga dawowarsu daga doguwar tafiya irin wannan.
Bata samu amsar tambayarta ba har sai da suka tsaya qofar gidan,mai gadin madaidaicin gate din ya bude musu suka shige madaidaiciyar harabar gidan da zata iya cin motoci uku zuwa hudu ba tare da sun takura ba,da kansa ya fita,ya zagaya inda take zaune ya bude mata motar,fuskarsa dauke da murmushi yace
“Bismillah” dubansa tayi tana maqale kafada tare d zumbura baki,Ranqwafowa yayi saman kanta yana murmushi
“Beautiful…..wannan bakin naki….” Sai ya saka yatsunsa biyu ya kama labban nata ba tare daya qarasa fadar abinda ke bakinsa ba,janye bakin tayi da sauri saboda yawon daya fara da yatsunsa saman labban nata
“Ranki ya dade…..ina miki barka da shigowa gidan aurenki” ya fada murya can qasa kamar meyin rada,da sauri ta daga ido tana kallonshi
“Ya haidar….kada kayi haka,shi yasa ka hana kowa shiga motar mu….hajja fa” yatsansa ya dora saman lips dinsa yace
“Shshsshhhhh….banason kiran sunan kowa ba,bansan kowa ba sai ke,nan din duniyarmu ce ni dake,kema kuma zaki manta da kowa da komai soon” ba tare data shirya ko ta ankara ba taji gaba daya ya sunkuceta,ta Maqaleshi sosai,saboda ji da take kamar zata fadi
“Karki damu,a hannun soja kike” ya fada yana murmushi,saita maida masa martani itama ta maida kanta qirjinsa ta kwantar,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri,sai ta daga kanta cikin mamaki ta dubeshi,murmushi ya sake sakar mata
“My heart beat ko?,kada ki damu,sonki ne da zumudin kasancewa tare dake” wani farinciki taji yana ratsa zuciyarta,tanajin alfahari da kasancewarsa mijinta yana mamaye ruhinta,qaunar hajja ta sake fadada a ranta,tabbas ita din ba qaramar masoyiya bace,me yasa kaf cikin jikoki da ‘ya’yan ‘yan uwa bata zabi kowa ba sai ita?,ita kadai ta dauka ta mallakawa mutum mai tsada da daraja irin aliyyu?,a hankali a hankali take fuskantar komai,kamar yadda ta taba gaya mata cewa zata gane,zata fahimci gatan datayi mata,bata da bakin gode mata,bata kuma da abinda zatace mata face addu’ar gamawarta da duniya lafiya.
Tana daga hannunsa take qarewa gidan kallo tun daga hanya har shigarsu falo,ba’a cika masa kayan alatu na qarya da barnar kudi ba,amma ya qayatar matuqa ya kuma bada ma’ana,parlour,two bedrooms with toilets a qasa,dining area,kitchen,store da wani toilet din a falo,saman benan gidan ma falo ne da bedroom biyu,kowanne shima da toilet,gaban kowanne daki akwai qawataccen corridor da zai baka damar ganin gaba da bayan gidan,akwai dakuna daga bayan ainihin ginin gidan guda biyu masu falo daya da bandaki,sai wajen ajiye motoci matsakaici ha matsakaiciyar haraba don shan iska.
Dubansa tayi sanda taga yana aje kayansu a dakin daya direta
“Ina nawa bedroom din?” Wani kallo ya mata mai kwantar da zuciyar masoyi,saidai fuskarsa a dan hade take,saiya zare rigar shaddar jikinsa,jinsa yake gaba daya a takure,don bazai iya tuna rabonshi da saka manyan kaya ba,banda wannan tafiyar da hajja ta tubure kan lallai bashi ba saka fingilallu kuma damammun kayan yahudu,bayan garin ma’aiki zashi.
Sai daya qaraso dab da ita ya dagata tsaye yana riqe da qugunta da hannu daya,daya hannun kuma yana warware rolling din doguwar rigar dake kanta
“Banason na raba komai da matata,nafison komai namu mu dinga sharing….bawai saboda babu wadata ko ikon siya ba,a’ah…..inason mu samu kusanci qauna da shaquwa matabbaciya…..irin wadda a tarihin masoya kaf na duniya babu masoyan da suka samu shaquwa da fahimtar juna irin tamu” yakai qarshen zancan sanda yake fidda mata doguwar rigar jikinta,saiya zamana daga ita sai under wear da vest,kaman maye haka ya bita da kallon qurilla,yadan ja baya kadan ta yadda zai samu damar kallonta da kyau,saiya miqa hannunsa i zuwa muhallin dako yaushe yake tsone masa idanu,ya kumayi tafiyar ruwa da nutsuwarsa,gocewa tayi tana dariya,a ‘yar tarayyarsu ta qididdigaggun kwanaki,ta gama fuskantar shi din mutum ne da yake qaunarsu,suka kuma matuqar tafiya da hankalinsa,cikin zafin nama ya bita zai cafko yana cewa
“Oh….no,don Allah,kada muyi haka dake pleasessssssss” dai dai nan ya samu nasarar kamotan,ya mannata da jikinsa yana sauke qatuwar ajiyar zuciya,tsayin minti guda kafin yace
“Duk sanda nake tare dake,nakan manta wanene ni….ashe dai da gaske kedin aljannar duniyata ce,don Allah….ki rayu dani,mu mutu tare” martani ta maida masa ta hanyar rungumeshi tsam itama,yadda takeji cikin zuciyarta bazai misaltu ba,a hankali take rada masa wasu kalamai cikin kunnuwansa,kalaman da suka sake rura wutar dake ruruwa cikin zuciyarsa,suka kuma sanya ya daina gane komai,cikin qaramin lokaci suka qwace dukka hankali da nutsuwarsa,wanda hankalin da nutsuwar basu dawo masa ba,har sai data kaishi wata duniya ta daban,duniyar da kullum yake bege da muradin tabbata a cikinta matuqar da zahran ne.
Kwance saman qirjinsa wanda tuni bacci yayi awon gaba da ita,yayin da shi kuma yayi nisa cikin duniyar tunaninta,duk da tana tare dashi amma baya gajiya da tunaninta,bai taba zaton cewa qaunarta a zuciyarsa tayi nisa har haka ba,bai taba tunanin zuciyarsa zatayi nisa da zurfi cikin soyayya har kamar haka ba,ashe ubangiji sonshi yake da rahama daya sanya matsaloli tsakaninta da manemanta a baya,ashe tanadinsa ce ubangiji yayi masa,shi yasa yake rusa dukkan wata alaqarta da wani.
Qarar da wayarsa tayi ita ta katse masa tunaninsa,sai daya miqa hannu sosai sannan ya iya lalubota,saboda fadawa da tayi gefan gado,yana duba sunan yaga hajja ce,saiya sauke zahran yaja mata bargo ya lullube mata jikinta,ya zura qafafunsa qasan gadon sannan ya amsa wayar
“Wai ina kuka tsaya ne haidar?,baka duba lokacine?,kusan awa uku?,hafsa tace a hanya kuka sauketa,kuna ina ne?” Ya bude baki zaiyi magana sai yaji muryar tasa a dakushe take,don haka ya danyi gyaran murya
“Banason qaniya….ka bude baki kayimin magana”
“Muna gidanmu…..,gobe ko jibi zamu shigo mu sake yi muku ban gajiya”
“Gidanku?,wanne gidan naku”
“Gida na na gaida gida dubu” salati hajja ta saki tana sallallami,jin haka sai kawai ya datse wayar,yama kasheta gaba daya,ya tashi ya lalubo wayar zahran itama ya kasheta,ya hadasu gaba daya ya watsa cikin sif sannan ya wuce bandaki yana murmushi qasan ransa,yasan za’asha daru da rigima,tana can qila ta tadawa kowa hankali,shikam bazai dauki wannan gantali da aure da hajjan keta yi musu ba,ana masa wasa da hankali kamar zahran bata gama zama mallakinsa ba.
Kamar kuwa yadda yace din,kwanansu uku cikin gidan su kadai,babu abinda suke banda morewa amarcinsu,gami da sake dasawa juna sabo da shaquwa mai qarfi a tsakaninsu,cikin kwanakin zahran tayi mugun sabo da soyayyarsa,wadda ya dinga koyar da ita salo salo cikin dabara da tsabar qwarewa,sau tari takan saki baki tana tambayar kanta
“Da gaske ya haidar ne wanann?” Duk inda ta motsa yana maqale da ita,tare suke komai,girki gyaran gidan,wanke wanke,kai hatta ma wanka bai bari ta shiga ita daya,idan ko ta sake tayi ita kadai to tayi aikin banza,don sai ta sake,suna aikin yana tsokanarta,wasan guje guje sam batasan a inda ya koya ba,ya qware a sosai a tsokana,idan mamaki ya cikata ta saki baki da ido tana kallonsa,saiya hure mata ido da iskar bakinsa,wani lokacin kuma saiya hade bakinsu waje guda,yace bari ya rage mata mamakin da takeyi,saiya tsotsi lips dinta iya son ranshi sannan ya saketa,ya dubeta yace
“Kairukum kairukum li ahlihi,wa’ana kairukum li ahly. ุฎูุฑูู
ุฎูุฑูู
ูุขููู ูุงูุง ุฎูุฑูู
ูุขููู,annabi yace mafi alkhairinku shine mafi alkhairinku ga iyalansa,sai annabi da kansa yace nine mafi alkhairinku ga iyalina,yana taya iyalansa dukka ayyukan gida da kika sani….ni din waye da bazanyi koyi da wanda akayi duniya da lahira saboda shi ba?” Maganganunsa sunyi matuqar burgeta ba kadan ba,da gaske ne duk wanda ya hukunta wani mutum bisa wai wai ko kuma kallonsa da yake daga nesa ba tare da ya mu’amalanceshi ba,zai aikata babban kuskure,ashe kalar abinda umminta keta mata kwadayi kenan?,lallai uwa uwa ce,a kowanne hali makomar rayuwar ahalinta na nan cikin ranta,komai runtsi komai wuya,Aliyyu miji ne ษaya da ษaya,mai tarin nagartar da kaso mafi yawa daga cikin mazan yanzu suka rasa irinta
(Idan baki samu ba,saiki roqi Allah ya gyara miki dabi’ar naki mijin,ya zama me koyi da sunnar ma’aiki,idan kuma kin samu,saiki godewa Allah,kuma kada kiyi wasa da damarki,koki wofantar da baiwar da Allah yayi miki,idan budurwa ce ke….kina da sauran dama,ki fidda so ko burgewar dukkan wani qyale qyalen duniya daga ranki,ki tsayawa sallar dare,kiyita gayawa ubangiji da roqarsa ya zaba miki miji na gari,ba mai arziqi ko kyau ba,miji na gari ya wuce dukkan wani irin nau’in miji daya mallaki dukiya kyau mulki ko sarauta,miji na gari shine abu mafi tsada da daraja cikin rayuwar diya mace kaf!!!,da zarar kin dace dashi,tofa matar du wani mai mulki kudi kyau ko sarauta saidai ta biyoki a baya,matuqar itama ba katari tayi da irin naki mijin ba,ubangiji ya wadata qannenmu ‘yan uwanmu da ‘ya’yanmu da nagartattun maza๐คฒ๐ฝ๐คฒ๐ฝ๐คฒ๐ฝ,dama daukacin matan musulmi gaba daya).
Cikon kwana na hudun suka shirya wajen sha biyu saura suka nufi gida,duk a kunyace take,saboda batasan da wacce fuska zata kalli jama’ar gidan nasu ba,musamman mama da umminta,har gwara hajja an saba gauraya.
Sai da suka shiga kowanne sashe suka gaidasu sannan suka wuce sassan hajja,ga mamakinta ba wanda ya tsokanesu ko ya tada maganar,bare ya nuna yasan me ya faru,suna sallama sukaci karo da akwatuna masu azabar kyau blueblack guda takwas cas,kowacce shaqe da kaya a cikinta,wasu daga cikin ‘yan uwan hajja ne suka gama kalla,da alama tafiya zasuyi ma,don har sun miqe.
Ango da amarya suka kirayi sunansu dashi,itadai ta murmusa ta gaidasu cikin kunya,yayin da aliyyu ya fuske cikin salon miskilancin nan nasa,sai zahran ta dinga satar kallonsa ta gefan ido,ya zama aliyyun nan sak dake basu tsoro cikin gidan,suna hada ido ya kashe mata idonsa daya,ya mata nuni data rage kallonsa,yana taba zuciyarsa,saita janye idanun nata tana sakin murmushi,dai dai nan suka hada ido da hajja wadda ta gama sallama da baqinta suka fice
“Sannunku marasa kunya feqaqqu….bari na fara da babban rasa kunya beran tankan…..kaga….hade girar gefe da gefanka ba zasu tsoratani ko su hanani cima mutunci ba…..da zaka daukemin yarinya ka kaita gidanka da kanka anyi biki ne?,ko ce maka akayi ma ciniki ya fada ne?,ance maka ta gama zama taka?,aro ne na shekara daya shine zaka zaqewa mutane…..” Tana tsaka da bambaminta ya miqe yana cusa wayarsa aljihun wandonsa
“Don Allah ki hutama ranki…..don ciniki ya dade da fadawa….ki godewa Allah da bata shigo tana miki amai bama….idan sadakinne ya miki kadan ki fadi dame kikeso a qara yawanshi” baki ta kama tana zare ido,yana ganin haka yasan ya soma maganin rigimar hajjan,saiya juya ya fara takawa zai fita daga falon,ba tare daya ma kalli kayan lefen da yasan shi ya bayar aka hadashi ba,duk da yaga akwati daya ta dadu akwai,har zai fita saiya waiwayo,xahra nata danne dariyarta,hajja na tsaye inda take tana binsa da kallo
“Kuma ga amanar matata nan….quda idan ya tabata saina ciki tara”
“Haidar….aliyyu,dani kake maganar” ta fada cikin daga murya sanda yake ficewa daga falon,cikin ransa tana qyaqyacewa da dariyar abinda ya yiwa hajja.
Guri ta samu tana zama tana hade ranta tsaf,duk da cewa zallar farinciki ne qasan ranta me tarin yawa,already sun riga sun gama magana dasu abba babba kan abarsu tunda har sun hada kansu sunma wuce gidansu,shi dama taron biki al’adace kawai,tunda an qulla auren yadda musulunci yace,kuma jama’a sun shaida shikenan
“Gafara kika tsareni da ido mara kunya….ja’ira kamar ba kece nan kamar zaki mutu ba saboda mun aura miki shi,ashe lambu lambu kikayi,qiris kike jira” wannan karon dariyarta kubcewa tayi,sai kuma tayi saurin mazewa
“To tunda nafi qarfina aina haqura na zauna ko?,badai za’a ce banyi biyayya ba” murmushi ne ya qwacewa hajjan itama,tasa hannu tana daga kayan,don ita duk yadda ake kallon lefan bata samu gani ba saboda gajiyar tafiya da take tare da ita,sai yanzu tadan samu ta warware.
Zahra dai bata sanya hannu ba har hajjan ta gama kalla tana daga gefe a zaune,har saida hajjan da kanta tace ta matso ta gani mana,saita girgiza kai alamun a’ah,hakan saiya burge hajjan,duk da cewa an riga da an zama daya,amma har yau akwai abubuwan da zahran ke kunyar yinsu,ba kamar ‘yammatan yanzun ba,da wata ma randa za’a kawo lefan tana gidansu,masu kawowa ko qofar gida basa gama kaiwa take tsallen albarka ta fito aci gaba da gani da ita,tana gani tana comment,tana hanawa a tattaba mata wasu abubuwan,Allah ya kyauta.
*_BAYAN KWANAKI BIYU_*
Walima gagaruma haidar din ya shirya a sabon gidan nasu,ranar walimar aka taho mata da akwatunan lefanta,saiya zamana kamar itace a madadin yinin biki,sosai aka ci aka sha,aka gabatar da wa’azi da nasihohi ga mata kan zamantakewar auratayya,wadda ta ratsa zukatan mata da dama,dangi sosai suka halatta,gidan yayi cikar kwari,saidai anyi taro lafiya an kuma watse lafiya.
Rayuwa suka ci gaba da gudanarwa mai cike da tsantsar soyayya da qauna ta kwatance,idanu ko wanxuwar wani a waje baya hanasu nunawa junansu zallar son da sukewa juna,mutane da dama na mamakin haidar din,saboda kowa ya sanshi da miskilancinsa ya sanshi,sai gashi lokaci daya zahra ta sukurkutashi.
Tako wanne fanni yana jin zahran ta cancanci ayi mata kowanne iri so,don dan xamansu da ‘yan satittika yasa ya gama fahimtar wacce irin macace ita,ta dauki dukka halayen umminta wajen biyayya wa miji da iya kula dashi,wani irin salo da yake da tabbacin wasunsu ta samosu ne daga wajen hajja,wanda sau tari akwai lokuttan da zai samesu suna hira da ita,tana bata labarin yadda mata ada ke biyayyawa miji ba irin matan yanzu ba.
8:30 pm
A nutse take kai kawo tsakanin kitchen da parlour tana shirya masa abinci,duk inda ta gifta idanunshi yana kanta,shigar da tayin ta dauki hankalinsa matuqa da gaske,duk sanda xata gifta saita bar masa qamshinta,bai taba zaton mata nada son turare haka ba sai da zahran ta kasance matarsa.
Plates ne na qarshe data ajjiye,sai itama ta samu waje tana niyyar xama,hannunsa ya miqa mata yana lumshe ido,ba bata lokaci ta saka hannu nata cikin nasa,hakan ya bashi damar jawota jikinsa,yayi mata mazauni saman cinyarsa,hannayensa ya sanya dukka yana yawo dasu saman jikinta,bata hanashi ba,saboda tasan abinda yafiso kenan,saima ta kwantar da kan nata saman kafadarshi,lungu da saqo na jikinta yake bi yana sansana,tsahon wani lokaci sannan ta kira sunanshe cikin wata lallausar murya
“Hubby na….”
“Makaranta fa….exam ta kusa” shuru ne ya biyo baya,har sai daya kammala abinda ya soma din,saiya dubeta da lumsassun idanunsa da suka jirkice suka qara qanqancewa
“Bana jin xan qyaleki ke kadai xahraty…..zamu tsara komai mu fuskanci komai tare,zamuyi karatun jarrabawa tare,zan kaiki ki dinga zanawa muna dawowa gida tare….nasararki nasara tace,amma da zarar kin kammala,zamu koma abuja,zan koma bakin aikina,yanzun hutun aikin da mukajeyi nake mora,sai kuma yazomin a daidai,Allah ya sanyawa hutun albarka….na mallaki xahrata a cikin sa,ta xama haidar….haidar ya zama zahransa” murmushi tayi,ta juyo gareshi,ta saka hannayenta duka biyun ta saqalo wuyansa,fuskarta dab da tashi
“Na gode sosai da wannan sadaukarwa daka yimin….ina fata ni da kai zamu dawwama a haka,na gode sosai” ta qarasa fada tana hade fuskarsu waje daya,sai kuwa ya sake kai mata cafka,cikin sauri ta zame tana cewa
“Abinci yallabai…..ayimin afuwa a fara cin abinci” ta fada tana saluting nashi kamar yadda sukewa manyansu,idanunsa ya lumshe a kanta sannan ya budesu yana fidda murmushi,yana so tana kuma burgeshi duk sanda ta tsaya gabanshi haka ta qame tayi saluting nashi,bai taba ganin kyau ko burgewa a irin wannan gaisuwar ba sai da zahranshi ta fara yi masa irinta,shima maida mata yayi yana murmushi,har ta zauna bai dauke idanunsa daga kanta ba.
Kamar yadda ya fada din kuwa tare suka tsara komai,kamar yadda yake kama mata aikin gida haka yake tayata karatun jarrabawar,bata taba tunanin haidar din gifted bane,mai matuqar ganewa tarin basira da kuma dabarun koyar da karatu,bata taba marmarin karatu ba,bata taba jin karatun jarrabawa me dadi ba,wanda babu ginsa ko qasawa a ciki ba sai wannan karon,yasan tarin abubuwa game da abinda ta karanta din,idan tace ta gaji yasan yadda zai mata ta samu relief su dora daga inda suka tsaya,su huta suyi bacci su tashi suci gaba,yace so yake ta fita da sakamako mai kyau wanda zata bar tarihin cikin makarantar,kamar yadda shima yabar tarihi cikin tashi makarantar daya gama.
*_BAYAN WASU KWANAKI_*
Yana tsaye daga saman dining yana hada musu tea shi da ita a cup biyu,yanayi yana duba agogo,a shirye yake tsaf cikin wata dakakkiyar shadda sabuwa fil ruwan zuma,wanda saida aka sha daru shida zahran tashi kafin ya yarda ya sanyata,shiri ne na tafiyarsu jarabawa a rana ta farko,ya sake daga kansa yana duban hanya,sai gata ta fito dauke da plate a hannunta,sanye take da wani lafiyayyen lace itama ruwan zuma,dinkin riga da plain zani,sabida yace bai yarda ta saka skert ba.
Duban fuskarta yake sosai,tana tahowa inda yake din tana yatsina fuska
“Yau wani laziness kikeji hubby,kodai exam dince tun kafin a fara take bugunki?,karki fa damu,ina da zato mai qarfi a kanki,kisa a ranki an gamata kawai” ajjiye plate din tayi a gabansa,ta hade hannayenta waje guda ๐๐ฝ
“Bani da haufi tsoro ko shakka indai sojana yana kusa….mutumin dake iya kula da qasarsa ma bare ni mutum daya?,….na yadda da kaifin basirarsa,hakanan inda malami ne shi xaiyi wuya a sami malami kamarsa kaf qarninsa kuwa,koda bayan mutuwarsa ne da shekara dari” wani kallo ya kafeta dashi,yana jin kamar ya hadiyeta,gwana ce wajen iya tsara kalaman da zasu tafi da hankalin dukkan mai hankali,ya rasa amsar da zai bata illa tukuicin lallausan murmushinsa,wanda ya jima yana shaida mata ya tanadeshi ne kawai saboda ita,ta kuma yarda da hakan dari bisa dari,don takanyi mamakin yadda yake komawa zakin gaske a gaban duk wata mace koma bayanta,hatta da qannensa shakkar nan tasa tana cikin zukatansu
“Kawai dai qwan nan ne,tunda na fara soyashi zuciyata ke tashi….” Ta amsa mishi tambayarsa ta farko sanda take daukar cup din tea din daya miqa mata,idanu ya kuma zura mata yana karantarta sanda take kurbar tea din,har sai data lura,saita dage masa girarta dukka biyun,alamun tambayar lafiya?
“Anya ko hubby….anya ban jefa qwallona a raga ba?” Ido ta fiddo tana aje cup din
“Bana tunanin haka…..haba watanmu nawa sojana….kawai ko a gida banson qarnin qwai,kuma ko xanci ma saina yanka wadatacciyar albasa akai nake ci” kafadunsa ya dage yana bude plate din chips da qwan data aje masa
“Ohkey….amma ko chips din ai kyaci ko?” Fuska ta kyabe cike da shagwaba tana maqale kafada
“Nifa qamshinsu ya gama cikamin ciki…..saidai ka taimaka ka siyamin meatpie a wannan gurinnnnn” dariya taso bashi,tunda ya taba siya mata meatpie din ta maqale masa,saiya maqale kafada shima
“Naqi wayon,saidai idan kin yarda nima…..” Qarshen zancan ya furta mata qasa qasa,sarai ta gane abinda yake fada,saita sakar masa kukan shagwaba,ta dauke hand bag dinta dake gabansa ta sauko daga dining din tana diddira qafa,dariya sosai yakeyi shima,ya aje abincin ya biyo bayanta.
Har suka je suka dawo yana tattalinta,suna gama exam din ta zagaya inda ya zauna zaman jiranta ta sameshi,bata yarda kowa ya biyota ba,ya gama ganeta amma tana togewa,kishinsa take hakan ya sanya bata hada kowa dashi.
Da taimakon Allah da kuma agazawar haidar din ta kammala jarrabawar cikin babbar nasara,babu qunci ko takura ko wahala mai yawa,wanda dalibi ke tsintar kansa a duk yayin jarrabawa,wanda tasan cewa sirrin hakan na tattare ne da dafawar haidar din.
Ta yadda da cewa samun masoyin gaskiya babban dace ne a rayuwa,hakanan rashin sa’a a soyayya kada ya sanya mace ta yanke tsammani da samun haske kuma mabudin yayewar dukkan matsalarta,abu daya ake buqata shine,ki sake hankalta a yayin da duk wata qaddara ta sameki ko kika aikata kuskure,kiyi qoqarin zama me kamewa,ki ninki zurfin dora abubuwanki saman sikeli da mizani fiye da ko yaushe,sannan ki zafafa da addu’a,babu ji babu gani,babu daga qafa babu hutu.
Imani da qaddararta da tayi,ta karbeta hannu bibbiyu,ta kuma tsarkake zuciyarta,ta riqe mutuncinta da mutuncin gidansu,ta kuma yi biyayya ga magabatanta shi yasa Allah ya dubeta yayi mata musaya mafi alkhairi,ba shakka yaudara nada zafi da ciwo,tana da qarfin da zatayi barazana ga rayuwar wanda aka yiwa ita,saidai kuma girman ubangiji ya shafe komai,qudirarsa da alkhairinsa kan bayinsa yawa ne dashi,koda yaushe ko godewa ubangiji bisa kowacce irin nau’in qaddarar daya tsagawa rayuwarka,tayi maka dadi ko bata yi maka ba,wannan shike nuni da cikar imanin bawa.
Randa sukayi paper din qarshe ta dinga jin jikinta sama sama,haka dai ta daure akayi sallama da qawaye da abokan karatu,ko cikin mota ma cikin seat ta lafewa haidar din,daya tambaya tace babu komai gajiya ce,bai gasgatata ba amma ya qyaleta,saboda ya lura kaman batason magana ne,zatonsa bai tabbata ba sai da suka bude falo zasu shiga,saita tafi luu zata fadi ya tarota,ya qarasar da ita saman kujera yana mata sannu,gaba daya ya rude cikin qanqanin lokaci,ruwa ya bata mai sanyi tasha,sai numfashinta ya koma normal
“Sannu”
“Lafiyata qalau” tayi qarfin halin fada,saboda zallar damuwar data hanga tattare dashi
“No hubby….baki da lafiya” don kada tayi masa musu kota bata masa lokacima yasa bai tsaya sauraren kalaman bakinta ba ya dauketa cak sai bandaki,ya ajjiyeta sannan ya tara mata ruwan wanka
“Ki wanka na baki minti goma,zan shirya na kaiki kiga likita” saiya fiddo mata towel soson wanka da sabulun wankan ya aje mata,sannan yaja mata qofar ya rufe,saiya wuce daya bandakin shima.
Idanu ya zuba mata sanda ta gama shirin ta fito,saiya riqe hannunta sosai
“Duk yadda kika kai ga boyemin baki da lafiya hubby bazai boyu ba,kin manta ne,ni dake ruhi daya ne yake rayuwa a gangar jiki guda biyu?” Murmushi ta sakar masa,saiya karata da jikinsa suna takawa a hankali yana sake gaya mata wasu kalaman da suka sanyata sakin ajiyar zuciya a jejjere.
A qalla ya kusa minti talatin zaune shida ita cikin motar riqe da hannayenta yana jero mata kalaman nuna zallar qauna da godiya a gareta,tun lokacin da likitan ya shaida masa tana dauke da juna biyu gaba daya yayi wani irin rudewa,ko a yanzun ma hawaye zahran ke futarwa,saboda kalaman da yake amfani dasu a kanta sun girmi kanta,kalamaine da take da cikakken yaqinin ba kowacce mace bace Allah yake mata baiwa da samun mijin da zai furta mata su ba
“Gobe as early as possible zamu wuce abuja…thank god kin gama abinda ya zaunar damu,kinji kuma yace kin da buqatar cikakken hutu,so zan buqaci hajja kawai ta bamu baba gaje mu wuce da ita….but…banda fadar dalili,don i sure tsaf hajja zata hanani tafiya dake” dariya sosai ya bata data tuna da hajjansu,hajiya hajja,ayi tsiya ayi dadi,tana sonsu tana tattalinsu,amma idan tsiyarta ta tashi har su saita dandana musu.
Kamar yadda ya tsara kuwa tun a daren ya gama hada musu abinda yasan suna da buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,tunda komai a kwai a can,ya kira hajja yace baba gaje ta shirya gobe zata rakasu abuja,ta fara masa tambayoyi yace ta bari idan yazo gobe zasuyi magana,ranar kusan kwanan zaune yayi,rabi bacci rabi idanunsa biyu,duk sadda ya farka saiya tuna cewa wai shima ya kusa zama uba?.
Qarfe bakwai a gidan tayi musu
“Wai tafiya abujan na meye haka saikun daukemin gaje kuma?” Zahra ce ta marairaice fuska
“Haba hajja,can dinfa babu dadi wallahi xaman shuru” waiwayawa tayi ta dubeta
“To ba sai ya barki nan ba,ya dinga zuwa?” Baki zahra ta tura
“Habba hajja…a’ah wallahi,ni mijina zanbi”
“Na shiga uku ni fatsima…..yau naga abinda yafi xare tsayi…..innawuro ni kike gayawa haka kanki tsaye.” Ilham da husna me zasuyi in banda dariya,baba gaje dake tsaye a gefe tana tayasu,shikam haidar dama bai shigo ba yana wajensu abba babba suna gaisawa,daga can ya tsaya wajen ummi don bincika me dame take da buqata,duk da bata rasa komai,amma bakan baisa ya daina hidima gareta ba,kwata kwacin yadda zaiyima gidansu.
Yana shigowa kuwa tace
“Kama hannun matarka ku ficemin,Allah ya kiyaye hanya,nikam yanzu kunfi qarfina,Allah rabamu qalau” yasan wata tsiyar aka tufka sai baice komai ba banda dariya da yake dannewa,amma ya godewa Allah da hajjan bata harbo jirginsu ba,haka suka fice bayan sunwa kowa sallama.
Shida ita a baya suka zauna,don bazai iya juriyar awanni suna waje daya amma ba ita a gefansa ba,baba gaje da driver suna gidan gaba,hakan ya baiwa zahra damar kwanciya sosai bisa jikinsa,don sam bata jin qwarin jikinta,shi kuma ya tattarota cikin jikin nasa sosai,ya gyara mata yadda zata fi jin dadin kwanciyar.
Tun basuyi nisa ba kiran hajja ya shigo wayarshi
“Anya lafiya zahra’u kuwa take?,ni sai da kuka wuce naga yanayinta baiyimin ba” cikin dakiyar nan tasa yace
“Lafiya take hajja….wani abu ya faru ne?”
“Um um….amma kawai sai nakega kamar me yaron ciki….koma meye ne ka kula da ita da kyau,sannan idan akwai wani abu da baku gane mishi ba kayi hanzarin dawomin da ita gida….kana jina?”
“In sha Allah hajja”
“Allah yayi muku albarka,ya albarkaci rayuwarku,ya tsare dukkan abunqi”
“Amin amin,Allah ya qara girma da shekaru masu albarka” ya fada cikin jin dadi,har kullum yana ganin girma da qimar tsohuwar,saboda zallar qauna da take nuna musu shi da soulmate dinsa.
Zuwansu da baba gajen ba qaramin ma’ana yayi ba,domin itama ta hangi abinda hajjan ta hanga,duk da basu gaya mata ba,don haka bata barin zahran tayi komai,komai na gidan ta dauke shi,ita kanta zahran ba qaramin dadin zama da baba gajen takeyi ba,tana debe mata kewa,hakanan duk randa ta tashi jikin babu dadi zata gaya mata wani abu da zatayi wanda zaisa taji sauqi da qwarin jikin nata.
Ta fannin haidar kuwa ta samu dukkan wata kulawa taimako da qwarin gwiwa a matsayinta na mace mai haihuwar fari wadda batasan yadda abun yake ba,shi kansa bai barinta tayi wani abu da zai wahalar da ita,ta kowanne fanni ta zama ‘yar lele ta gaske.
Hajja batasan da zaman cikin ba,sai sanda ya samu hutu na sati guda,yace su shirya suje kanon su roqi hajja tabar musu baba gaje,a lokacin cikin nata ya shiga wata na uku,kuma ga duk mutum mai saurin tsinkaye da daukar haske zai fahimci akwai ciki tare da zahran,tayi wani kyau,hakanan ta sake cika,fatarta ta qara haske,sau tari haidar kan sanyata gaba da tsokana,ya hanata sakat,bini bini yana shafa fatarta,idan tayi qorafi sai yace
“Ke dince ki qara wani kyau,fatarki kamar atafa,karfa nan gaba na soma kasa gane hanyar fita daga gida,ko naje nayi shirme gaban manya ki jawomin hukunci” saita tureshi tana tura baki,sabida ita gani take kamar tsokanarta yake,don rannan daya goyata ya zagaya da ita cewa yayi ta sauka,ta fara ninka nauyinta,sai data dinga masa kukan wasa sannan kuma ya lalace wajen lallashi da bata haquri,ire iren yanayin rayuwarsu kenan,idan ka ganshi a cikin gida saika rantse da Allah ba ALIYYU MAS’UD DABO bane,sojan nan daya kasance dodon ‘yan ta’adda da marasa gaskiya dake cikin qasar nan,idan ka ganshi a waje sanye da kaki ba zaka ce zaka sameshi a haka cikin gida ba.
*_BAYAN WATA TARA_*
Tsaye suke cikin dakin hajja,taja rungume cikin jikinsa saidai ya rungumeta ne ta bayanta saboda tsinin cikinta wanda ya dora dukka hannayensa biyu akai,yana jin yadda yaron cikinta ke motsawa,kai kace zai fasa cikin ne ya fito,bai dauke hannun ba har sai daya tsagaita da motsin,suka saki ajiyar zuciya shida ita a tare,sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna.
Tausayinya yakeji fiye da kima,koda can shi mutum ne mai tsananin tausayin mace,macen ma ace mai juna biyu,yau saiga abuj cikin gidansa,a jikin mace mafi soyuwa duk duniya a wajensa baya ga iyayensa
“Banda hajja ce hubby duk duniya babu wanda ya isa ya sanyani na wani kawoki wankan gida” murmushi ta saki,ta sanya hannunta tana shafan kwantaccen gashin fuskarsa da ko yaushe yake qara masa kyau da kwarjini
“Kasan dai hajja ta fimu damuwa da kwanunanmu….sannan tun ban dade da shiga third trimester dina ba tace ka dawo dani gida,yanzu idan baka kawoni ba zataga cewa kamar bata isa damu bane,bayan ina da tabbacin cewa tayi hakanne saboda amfanin kanmu” fuskarta ya riqe tsakiyar hannunsa,ya matso da ita dab da tashi,cikin softness yace
“Hubby….inason in zama mutum na farko da zaya dauki ‘yarshi” yatsanta ta dora saman lips dinsa tana cewa
“Shshshs…..point of correction…..soja nakeso na haifa,jarumi kamar kai….mai kuma kama dakai” dagowa yayi yana murmushi,ya kama hannayenta duka ya riqe cikin hannunsa
“Little zahra ni kuma nakeso…..kuma inaji a jikina itace”
“Ok….ok,ba anyi yarjejeniya ba akan a bari har sai ranan?,duk wanda yayi wining zai zaba abinda yakeso mutum ya bashi…”
“Yes hubby” ya fada yana lakace hancinta,saita jefa masa harara
“Ka takurawa hancin nan nawa” dariya sosai ya saki yana cewa
“Ya qara kyau ne,kamar na dauke kayana na tafi dashi” tasan cewa girma ya qara fiye dana da,amma ba zai taba fitowa ya gaya mata hakan ba,saidai kullum idan ya dameshi da cewa hancinta yayi qato ko yayi muni sai yace mata suyi musanye da nata,ko ta bashi kayanshi yana so shi a haka.
Rigima ta soma yi masa kan ta gane dariya yake mata saboda tayi muni,lallashin duniya taqi shuru saboda bai daina dariyar badai,har sai da hajja tazo ta tankada qeyarsa sannan aka samu salama.
Tana zama saqonsa yana shigowa wayar tata
_zan qara kwana daya ko Allah zaisa ina da rabon ganin baby na,but please kada ki sanarwa kowa_
Idanu ta zaro cike da mamakinsa,muhimmin taro suke dashi da mr president a jibi amma yace bazai tafi ba,saita koma daki ta kirashi tana son tayi convincing dinsa kan ya tafi saboda muhimmancin taron amma fur yaqi,dole ta rabu dashi,ya daddogara ta dawo falo saboda ciwon mara da baya da yaketa tsunkulinta.
A falon tayi kwanciyarta suna hira da hajja,jifa jifa tana cije lebe idan aka mintsineta,saita dinga mamaki,don bata taba ciwon mara haka mai naci ba kamar nayau,ana mintsinarta amma da tayi daya biyu uku a rana shikenan sai washegari,amma nayau din yaqi barinta batasan dalili ba.
Ciwon bayan da taji yana yawa saita koma daki da niyyar kwanciya ko zai ragu,saidai tana shiga kamar an dado ciwon ne,tayi tayi ta zauna ta kasa qafarta ta riqe gam,dole ta dinga qwalawa hajja kira,sai gata bagatatan ba shiri.
Tuni ta fahimci haihuwa ce,ta aika umaima ta kira mata mamarta matar abban tsakiya,ta sanya ilham kuma ta shiga tsohon dakin zahran ta dauko kayan da aka ware don tafiya asibiti.
Kafin ilham ta dauko kayan maman umaima ta qaraso ciwon ya ta’azzaran mata,ta kasa tafiya bare akai ga batun zuwa asibiti,don haka hajja tace adan dakata ko zai lafa mata sai a tafin,saidai ina,gaba kawai ciwon yakeyi,wanda harta kasa jure masa tana neman taimako,baba gaje da kuma hajjan su suka riqeta lokacin da suka fahimci haihuwar tazo gadan gadan,cikin ikon Allah da taimakon addu’a cikin mintunan da basu wuce uku ba kukan jariri ya karade sassan hajjan gaba daya.
Kusan tare suka saki ajiyar zuciya ita da hajjan,farinciki mara misaltuwa ya sauka a zukatansu gaba daya,hajjan ce da kanta,duk da tsufa ta dauke yaron daketa watsal watsal cikin qazantar da suka fito tare yana canyara kuka,ta kasa daurewa saidata rungumeshi cikin jikinta qwalla na gangarowa daga idanunta
“Alhamdulillah….alhamdulillah” shine kawai abinda yake fita daga bakinta,sannan ta qarasa dab da zahran ta dora mata yaron saman cikinta tana shafa sumar kanta
“Sannu takwarata,sannu da qoqari,barka da arziqi” saita lumshe idanunta cikin matuqar jin kunya,gefe guda na zuciyarta farinciki na mamayeta,idanunta kan fuskar yaron,fuskar da ko ba’a wanketa ba ta bayyana kamar ya Aliyyunta daya dauko,sak shi,kamar kaki yayi ya aje,take wata qauna irin wadda ubangiji S W T yake dasawa a zukatan bayinsa tsakanin uwa da ษa ta fara kwaranya a zuciyarta.
Kafin kace meye wannan labarin haihuwar ya zaga gidan,tuni aka soma gyaran zahran da jaririnta,cikin qasa da awa guda tayi wankanta da ruwan dumi,an goge yaron da kyau,an gyara mata dakin hajjan yadda zai dace da yanayin jaririn,hajjan tasa an dora mata kunu bayan ta soma da bata tea mai uban kauri da bournvita saboda ruwan nono.
Sau wajen biyar yana attempting bude gidan nasa ya shiga sai yaja tsaki ya fasa,yayi imanin koda ya shiga baqiqqirin gidan zai masa,bazai ma iya zama ba,saboda babu fitilar gidan,daga qarshe kamar wanda ake umarta,yaji kawai zuciyarsa ta yanke masa ya koma gidan hajjan ya wuni da zahran,idan yaso idan dare yayi ma ya bude tsohon dakinsa na gidan yayi kwanciyarsa,duk da babu komai yanzun a dakin sai katifa,ya tabbatar sai yafi samun relief akan ya kasance tana nesa dashi.
Tunda ya doso gidan yaji gabansa yana faduwa,sanda shamsu ya bude masa qofar gidan ya ga kamar yanason magana dashi,amma bai tsaya ba sai daya isa inda suke aje motocinsu,yana kashe motar kuma yayi sassan hajjan.
Sanda ya shigo yayi dai dai da lokacin da jaririn ke kukan neman nono,baba gaje na kan zahran tana gwada mata yadda ake feeding yaro,tana ta dariyar rashin sabo irin na zahra
“Saiko kin dage,don na fuskanci me gidan nawa acici ne”.
Tuntube ya kusa ci da filallukan falon hajjan saboda yadda zuciyarsa ta bashi amsar zahransa ce ta haihu yana qaryatata,banda ingarma ne kuma tsayayye da faduwa zaiyi qasa warwas,ko takan hajjan dake masa magana baibi ba yayi inda yaji kukan na fitowa wato dakin gadon hajjan.
Kyakkyawan gani kuwa idanunsa suka masa,zahransa rungume da kyakkyawan baby cikin jikinta tana shayar dashi,idanunta a runtse da alama ta jin zafin yadda yake tsotso ne,tashi guda tayi wani mugun kyau,fatarta kamar an qara mata sinadaran kyau,baisan ya isa garesu ba saida yaji muryar baba gaje dake fita tana cewa
“A barshi yasha sosai kafin a cireshi,ruwan maman sai yafi saurin zuwa,idan kin gama saiki magana zaku asibiti su sake tabbatar da lafiyarki”
Qamshinsa ne kawai ya sanar mata da zuwansa,saita bude idanunta a hankali daga runtsesun da tayi,take suka hada idanu,saiya miqe hannunsa a hankali ya riqe hannuta sosai,yasa daya hannun yana shafar fuskarta,ya kasa furta kowacce kalma,idan ta lura da kyau qwalla ce ta cika idanun nasa,itama dubanshi take murmushi na fita a fuskarta,a hankali taji ya qwato kalmar
“Alhamdulillahi rabbil Aalamin,Alhmdlhillazi bi ni’imatihi tatimmus salihat” ya dinga jerowa,saiya matsa gab da ita ya manna mata wani dogon kiss a goshinta kamar xai hada da numfashinsa,sannan yayi kissing bayan hannunta,ya sake matsawa a hankali ya bude fuskar yaron yayi bismillah ya tsugunna yayi kissing goshinsa shima,ya dago a hankali suka hada ido,murmushi yaqi yankewa daga fuskarsa
“Sannu hubby….sannu zahraty” addu’a ya shiga jero mata na fatan alkhairi ita da iyayenta,wanda hakan har sai daya kusa sanyata kuka,sannanna hankali ta zare maman daga bakin yaron wanda tuni yayi bacci ta miqawa haidar din shi
“Ma sha Allah,littale zahra kinyimin kara mai yawa” dariya ya bata,cikin dariyar tace
“Duba dai,little haidar ne” idanu ya fiddo,sai kuma ya narke fuska
“Yanzu fisabilillahi saida kikamin wayo dai….shikenan….Allah ya raya little baba sa’id” sosai maganar tazo mata a bazata,haidar da gaske yake sunan abbanta ya sanya mata?,ya lura da irin kallon da take masa,saiya jinjina kai yana murmushi tare da bata qwarin gwiwa
“Eh,sa’id sunanshi,Allah ya albarkaci rayuwarsa,yasa kuma ya dauko halayyar abba qarami(shine sunan da suke gayawa mahaifin xahran sanda yana raye)” bata iya daurewa hawayen daya cika mata idanu ba saida suka zubo
“No….yau ba ranar kuka bace,ranar farinciki ce,muma mun zama iyali,mun fara aje iri,kimin alfarma karki bata mana ranarmu” yakai qarshen xancan yana rungumeta cikin jikinsa ita da jaririn gaba
“Allah ya faranta maka yadda ka faranta min,ubangijin al’arshi ya kula maka da rayuwarka yadda ka kula da tawa,ya zama jinka ya zama ganinka,ya kuma zama garkuwarka” idanunsa a lumshe yana jin wani yanayin mai cike da sa’a da nasarar rayuwa,gami da katari da macen aure ta gari yana tsumashi
“Ameen mace ta gari”
“Au koke koken rashin son auren dole kuke ko kuwa?” Suka tsinci muryar hajja na shigowa,saiya saketa,suka daga kai suna dubanta,ta wani hade rai da gaske taqi dariya
“Me kuka wani tsareni da ido….zuwa nayi karbar takardar zahra’u,don naga alama idan na qyale wata shekarar za’a maimaita abinda ya faru yanzu”
“Kamar ko kin sani,don saita haife mai sunanki ma…..nida hubby kuwa mutu ka raba…..mutuwa ce kawai zata shiga tsakaninmu,inma zaki murmushi Allah gwara kiyi” ya fada ko ajikinsa dariya ta subuce hajjan,don itama farinciki da take ciki tasan bazata iya boyeshi ba,duk sai suka tayata darawa suna tuna rigima irin tata
“Komai zanyi inayinsa ne saboda rayuwarku,na godewa Allah da ya nuna min hadin kan ahalina gabanin mutuwata”.
Haidar na murmushi yace
“Bamu da abinda zamu saka miki dashi hajjanmu sai fatan gamawa da duniya lafiya,kije ki tadda mijinki cikin aljanna madaukakiya kuci gaba da rayuwa”addu’an fatan alkhairi sosai ya dinga jera mata zahra na amsawa da amin,zuciyar hajjan fari qal kamar tasu ta fita tabar dakin,bayan ta tunawa zahran ta shirya ta fito haidar din ya kaita a sake tabbatar da lafiyarta,ta fita tana sake godewa Allah kan tarin baiwa da ni’imomi da yayi mata.
*_TAMMAT BI HAMDILLAH_*
_Kada ki sake,kada ki bari damuwar wani d’a namiji ta hanaki sukuni,kada ki bari damuwar wani saurayi daya yaudareki tasa ki tsaida taki rayuwar cak,bayan shi yana can yana tashi rayuwar_
_rabu dashi,manta dashi,nuna masa bashi da muhimmanci cikin rayuwarki,kamar yadda ya nunawa duniya hakan a kanki_
_kada ki manta,idan dubu sun qika….dubu ke sonka suke kuma jiranka_
_sau tari abinda kake so saiya zamana ba shine alkhairi a tattare dakai ba,abinda kake gudu kuma shine alkhairi a tare dakai ba tare daka sani ba_
_zama mai hankali ta hanyar zurfafa tunaninka,kada ka yarda ka yankewa wani dan adam hukunci ba tare daka mu’amalanceshi ba,kada ka yarda ya fadi halin wane bayan baka zauna dashi zama na gaske ba_
_koda yaushe ka zama mai kyautata zatonka ga mutane,sai gobenka tayi kyau_
_MAZA kuji tsoron Allah,nasan bazan aureki ba,to bazan soma tsayawa zuwa zance wajenki ba,kona bata lokaci kan layin waya ina qona miki kati ko ina qona nawa katin ba,ina bata miki lokaci,ina dauke hankalinki daga kula maza ‘yan gaske masu niyyar aurenki ba,KADA KU MANTA KAI YAYA NE,WATARAN KUMA UBA NE!,ZAKA HAIFA KO A HAIFA MAKA!,AKWAI KUMA HISABI,ALLAH BAYA QYAKE HAQQIN WANI AKAN WANI TUN NAN GIDAN DUNIYA_
*_muna miqa saqon godiya da jinjina a gareku masoya kuma makaranta litattafan zafafa,wadanda a kullum basa gajiya da sanya kudadensu su siya rubutunmu,ubangiji yabar qauna_*
*_muna neman afuwan wanda muka batawa,ko wanda muka yiwa ba dai dai ba,ko labarinmu ya batawa,ko bai masa yadda yaso ya kasance ba,dukkanmu ajizai ne,duk inda ajizi yake kuwa saiya nuna ajizancinsa_*๐๐ฝ
*_kurakuran dake cikin rubutunmu muna fata Allah ya yafe mana,ya bamu ladan dake ciki_*
*_ubangijin ya sadamu a rubutu na gaba,ya bamu aron rai da lafiya,yaci gaba da riqo da hannyenmu,ya kuma bamu damar rubuta abinda al’ummar annabi muhammadu zasu amfana dashi_*
*SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASHHADU AN LA’ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA’A TUBU ILAIKA*๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ๐๐ฝ