Sponsored Links
Gidan Aunty Book 1Hausa Novels

Gidan Aunty Book 1 Page 18

Sponsored Links

BOOK 1 📕

Free page 18 🦋

Tunda yazauna akan daya daga cikin kujerun dining din bai kara motsawa ba har ummey tayi serving dinshi “thanks “ shine kadai abunda ya iya furtawa, ya dauka kusan mintuna 5 yana kallan abinci kafin ya dauki spoon din ya fara ci a hankali,tunda ya soma cin abincin tahee take satar kallansa ta kasan ido, duk abunda take yanaji aji kinsa ana kallansa,a bazata ya dago da kwayar idanunsa Daidai lokacin da tahee take dago da nata idanun, cikin sauri ta Dauke idanuwanta cikin yar yabar murya ta soma magana “Ummey nagode sosai,Allah ya kara arziki,bari na koma nasan ammi zata iya nemana” ta kare zancen nata tana sunkiyar dakai,”jinjina mata kai ummey tayi kafin ta mike “ am coming “kawai tace mata tare da barin wajan , har lokacin kan tahee na kasa ta kasa kwakkwaran motsi, ba’adau dogon lokaci ba ummey ta dawo da babbar Leda a hannunta, mikawa tahee ledar tayi” wannan naki ne daughter “,girgiza mata kai tahee tashiga yi, ta bude baki da niyar magana ummey ta dakatar da ita “I’m also your mom,karki karamin haka inna baki abu kinji”, cikin jin nauyinta tahee ta amsa mata tare da karbar ledar , sosai tayi wa ummey Godiya da addu’oi masu sanya zuciya tare da barin part din ,duk abun nan da suke king na zaune amma sam hankalinsa baya wajan sabida yadda yake jin wani irin turiri a jikinsa kamar ana hura masa huta,a hankali ya mike “I’m off “kawai yace batare da ya bari tace komai ba yabar part din, zoya sai faman tura karamin bakinta take yau be kulataba sosai , bin bayansa ummey tayi batare da tace komai ba, direct part dinsa ya koma cikin nutsuwarsa lokacin har an kara kyara wajan da su amrah suka bata,ko ina na falon sai tashin kamshi yake, cikin sassarfa ya shige wani daki, jijiyoyin kansa sun fito sunyi rudu rudu, sosai fuskarsa ta juye daga asalin farinta zuwa ja jawur, wani irin tururi ne yake taso masa kamar Wanda ake hurawa huta , gashin kansa da ya sha gyara ya fara batawa,tun yanayi a hankali har yazo  ya fara fita hayyacinsa, gaban mudubin dakin ya karasa, a hankali ya fara fasa kayan gaban mudubin, duk abunda yaci kara dashi kawai ya ke dauka ya fasa , sosai ya farfasan kayan dakin, ganin hakan be masa ba yasashi dunkule hannunsa tare da bugashi da karfi akan madubin dakin, ji kake tasss madubin ya tarwatse gabaki Dayansa, kara yasaki tare da cigaba da buga hannunsa a jikin bango, sosai hannunsa ke Jini amma duk da hakan bai dena ba, wani show glass din da ya hango ya nufa Daidai lokacin da aka banko kofar da karfi, da sauri zaki ya karasa inda yake , hannunsa ya kai da niyar kama da king , be ankaraba yaji king yayi sama dashi tare da bugawa da kasa , sosai ya bugu a kafarsa amma duk da hakan bai hakura ba ganin inda yake nufane yasa zaki dakko wani allura a aljihunsa, a bazata ya tsirawa king a jijiyar hannunsa, juyo da rinannun idanunsa da suka matukar canza kala yayi tare da sauke su kan zaki, wata iriyar shaka yayi masa, sosai ya shakesa tare da bugasa da jikin bango, ko Karin kwacewa zaki yake daga Shakar da king yayi masa amma yakasa, ga idanuwansa da suka fara fito wa waje, cikin kankanin lokaci king ya fara sassauta rikon da yayi masa kafun a hankali ya fara lumshe idanuwansa da suka kada sukai ja sosai, ganin yana kokarin faduwa zaki yayi saurin taro hannunsa tare da kwantar dashi kan gadon, shafa wuyansa da king ya shake ya fara murzawa, saida nunfashin sa ya daidaita kafun ya fara gyara dakin , sosai ya gyara ko ina, wayanda suka faffashe ya waresu daban, ganin irin Jinin da king ke zubarwane yayi saurin futa daga dakin , cikin kankanin lokaci ya dawo dauke da first aid box a hannunsa, hannun king da ya ke futar da Jini yayi treating , yana matukar tausaya wa ogansa wannan yanayi da yake yawanshiga.

*****A hankali tashiga falon dauke da sallama a bakinta, ammi dake zaune ne ta dago fuskarta da kyakkyawar murmushinta “daughter sai yanxu ake ganinki, karaso ciki mana kin tsaya kamar Mara gaskiya “karasa shigowa tahee tayi “ammi kiyi hakuri, su suka tsayar dani”, wani murmushin ta kara saki, “ai sunyi Daidai tunda bakya lekasu,nan gabama tattara miki kayanki zanyi ki koma can da kwata” ta karasa fada cikin zoyala, murmushi tahee ta saki da ya fito da ainahin gap teeth dinta dan siriri , ledar hannunta ta ajiyewa ammi, kallan ta ammi tayi tana san Karin bayani, cikin in ina ta fara magana “da..dama ummey ce ta bani banc….”katseta ammi tayi, shine kike dardar haka , “hope kin gode mata”jinjina mata kai tahee tayi, “good girl ,haka akeso anjima zan kara mata godiya , yanxu ki dauki kayan ki kaisu dakinki”dan murmushi tahee ta saki, “nagode sosai aunty” dan harara ammi kawai tayi mata ,harta juya zata tafi ammi ta tsayar da ita, tare da miko mata wayarta”nasan Kinyi kewar su yaya, gashinan ki kira ku gaisa “sosai farin cikin tahee ya kasa boyuwa har hakan yasa ammi farin ciki ganin ta cikin farin ciki, ta bude baki da niyar yi mata godiya ammi ta tsayar da ita”keje kiyi wayar ki, banasan wannan Yawan godiyar “tana gama fadar hakan ta nufi stair case , itama tahee murmushin jin dadi ta saki tare da nufar masaukinta da yanxu ya kasance kamar dakinta.

🫧🫧🫧🫧🫧
Tunda ta dawo daga bangaran king take kuka a daki, aunty sai faman lallashinta take akan ta fada mata abunda ke damun ta amma bata kulata ba sai faman kuka take, idanuwanta sunyi jajawur dasu, zabura tayi tare da mikewa , cikin kuna ta fara magana” Wallahi aunty na gaji, na gaji na fada miki hakurina ya kara gushewa , dole a auramun king ko yanaso ko bayaso, sannan a kawar mun da duk wanda yayi kokarin shiga gonata , bazan barsu ba, har ita yar iskar yarinyar can sai na kashe ta da hannuna, bama ita kadai ba , duk Wanda yayi kokarin kusantar inda yake bazan barsaba, aunty dole akoma Wayan boka , ko me za ai ma ayi inma dan dole zesa king yasoni yayi ni va damuwata bace”ta karasa maganar tare da sakin wani saban kukan,kallanta aunty tayi “ki kwantar da hankalinki yanxunnan zan kira yaya, aure kuwa kamar anyishine da kanki zaki dawo bawa mutanan gidan nan umarni bawaishi king kadai ba” ta na karasa zancenta ta bar dakin, wani lallausan murmushi amrah ta saki, “finally na zama mrs tahnoon, oh my god , bansan ya laushin faffadar kirjinka yake ba amma nasan ba karamun dadin kwanciya zanyi ba “ ta kare maganar tare da sakin dariya tana shiga bandaki….

🫧🫧…..
A bangaran sumayya kuwa bata shiga part din su direct ba sai da ta wanke fuskarta tare da sassaita fuskarta kamar ba abunda ya sameta, cikin takun yaukin ta , ta karasa shiga part Dinsu, kamar kuwa yadda tayi hasashe, ihsan da firdausi ne zaune a falo suka kallan wania series, kallansu sumayya tayi tana sakin murmushi da be kai zuciya ba, kallan ta firdausi tayi cikin tsokana “kaga matar yaya king bada kanki a sare, ina kika baro kishiyarki kuma yanxu “ jin maganarta ta karshene yasa sumayya Jan tsaki,”gatacan ta gudu sabida kar kuga shatin marukan fuskarta”ta karasa da sakin shegiyar dariya, binta sukai da kallo ganin irin shegiyar dariyar da take, ihsan dake kallanta ne ta dauke Kai tana sakin murmushi dan ta hango dan fashewar da bakinta yayi ga jikinta da ya dan ‘baci da abinci, basu kuma ce mata komai ba suka cigaba da kallan series dinsu hankali kwance.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰
BUNKURE
Tun dazu take safa da marwa tare da zirga zirga a tsakar gidan ko zataga oumma ta fito a haukace, amma har yanxu shiru,ga oumma sai faman aikin ta take hankali kwance ita da taheer da ya dawo tun dazu, ganin hakan yasa ta yafa mayafi tare da nufar gidan boka, “gafaran ku de, boka me share mana hawaye , abun alfaharinmu”wata mummunar dariya aka saki cikin wata kausashshiyar magana aka soma magana” shigo da baya da baya” kamar yadda aka umarceta kuwa hakan tayi sai faman kirari da take masa, cikin bukkar dake shegen wari da zarni. Yana zaune a Inda ya saba cikin Kazan tarsa, yana ganinta ya fara sakin dariya “nasan me ya kawoki ba sai kin maimaitaba, tun ba a je ko ina ba kun fara lallata aikin ku, kije ki dawo da yarinyar da kuka zo da ita kwanaki in ba haka ba kuna cikin tsaka me wuya, rayuwarki da ta yarki Zata mu nana tasu kuma ta daukaka” yana gama fadin haka ya kara babbaka dariya “kije , kije ki taho da yarinyarnan In ba haka ba aikinku na gab da lallacewa”da sauri Dije ta fito sai faman buga sauri taje jin zantikan boka, tana fita kuwa bokan nan ya kara babbakewa da dariya tare da sidar baki….

Comment and share ✍️

Kudin littafin dari uku ne kacal 300 me bukata zai biya kudinsa ta wannan asusun 7041879581 palmpay Ayshatou galadima sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
Duk karfin izzata
Gidan Aunty
Ya fita zakka
Jini daya
Sarki sameer
Baby .

Mss Lee 💖✍️.

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

💖💖GIDAN AUNTY💖💖
(a heart touching love story )

Story & written
By
Mss Lee 💖

PAID BOOK

Duk me bukatar gidan aunty daga farko har karshe yamun magana ta wannan number 07041879581 ,bana da kira please

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button