Dangina Book 2 Page 28
βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 28*
Ina yini”
Ta fad’a a sanyaye tana d’an satar kallon gefen dasu Maryam suke,
sai dai ga mamakin ta sai taga kusan gaba d’aya yan matan dake wajen hankalin su ya karkata ne akan kallon AK,
Ita wallahi dama tasan za’ayi haka, wai mema ya sashi biyota har makaranta ne?
“Lafiya lau Dr ya kike, ya school d’in naku?”
“School Alhamdulillah barka da zuwa ya hanya?”
“Alhamdulillah na iso lafiya, hanya kuma yana can mun baro musu,
Me kuke shiryawa ne haka naga kina tayin dogon list?”
“Surprise zamuyi ma amaryar ku, abubuwan da muke buk’ata na program din da muka shirya zamuyi anan cikin school ne nike rubutawa saboda karmu mance da wasu abubuwan,
Me za’a kawo maka ?”
“Ni bana buk’atar komai naci anan wajen balle kuma kafin in fito ma sai da Hajiya ta bani abinci naci, ke kawai nazo gani dan bazan iya jira har sai kin koma gida kafin in samu damar kallon wannan kyakyawar fuskar taki ba tashi muje wajen nan babu dad’in zama sam!”
Ya fad’a a yayinda ya kai yatsar shi ya lakaci gefen kuma tun ta,
“Ina zamu kuma?”
“Kaiki zanyi in siyar dake”
“To ni ai nazo cin abinci ne anan yunwa fa nike ji!”
“Naga alaman hakan shi yasa nake son in kaiki inda zakici abincin a tsanake ba nan wajen da yake da hayaniyar mutane da yawa ba,
Yama zaki zauna cin abinci anan bayan ga maza nan da yawa duk sai kallon ki sukeyi,
Baki san hakan yana da had’ari ba ai baima dace ki zauna kina tauna abinci a bakin ki maza na kallon yanda bakin naki ke taunar abincin ba dan ba kowa bane yake da tsarkakakkiyar zuciya ba, kenan haka kike zuwa nan kullum da sunan cin abinci? ”
K’asa yayi da murya sosai ta yanda bai zama lallai taji mai zaiceba kafin ya k’arasa maganar shi da cewa,
“Yarinya baki san wani jarababben daga kallon yanayin yanda bakin ki ke motsi ma kad’ai yana iya samun gamsuwa ba”
“Na’am me kace?”
“Cewa nayi kenan kullum anan kuke zuwa cin abinci?”
“Ah ah ba kullum ba lokaci lokaci dai”
“To na kashe zuwa wajen nan da sunan cin abinci daga yau,
Bazan hanaki kizo kiyi take away ba amma dai ban yarda kizo ki zauna kici anan d’inba kinji na fad’a miki”
“To saboda me zaka ce haka ai bani kad’ai nike zuwa ba, in ma kallo ne ba gashi nan ba kaima daga zuwan ka duk kabi ka d’auke hankalin yan matan wajen kalle su ka gani fa dukan su idanuwan su akanka yake ni ban san ma mi yasa ka biyoni nan ba”
Ta fad’a tana juya idanuwan ta gefe da gefe harda wani tura baki,
“Koma ke da waye ni dai ina rokon alfarma kiji tausayina ki rufamin asiri ki dena zaman cin abinci a wajen nan,
Nifa inda hali ma gara ki dunga zuwa da abinci daga gida kinga nifa in abun ya zama haka zan ma Hajiya magana ta d’auki wata sabuwar mai aikin da zata dunga tashi da sassafe tana had’a miki abincin da zaki dunga zuwa dashi makaranta tunda naga aikin yana son yama Aunty Larai yawa amma bazan yarda kici gaba da zuwa irin wajen nan cin abinci ba nagode Allah ma kun kusa kammala karatun madai mutum ya huta ”
Yana karasa fad’in hakan ya mik’e ta bayan kujeran ta ya koma ya tsaya kafin ya sanya hannayen shi yaja kujerar da take kai din a zaune baya,
Zabura tayi ta mik’e tsaye daga zaunen da take dan tasan dan k’ank’ani ne cikin aiyukan da zai iya aikata wa wato yace zai kama kafadar ta ya mik’ar da ita tsaye ko kuma dai wani abun makamancin hakan,
“Ina zaka kaini to?
Nidai ban zuwa ko ina gida kawai zan tafiπ”
“Ni kuma nace ba gida ba wani waje zaki rakani”
Jakarta ya mik’a hannu zai d’auka tayi saurin d’auke Jakar ta rataya a kafad’a,
“Ok muje to tunda bazaki bari in rik’e miki Jakar ba”
Karasawa inda su Maryam suke sukayi,
Sultana ce ta fara gaishe shi da cewa, “barka da zuwa Brother ya hanya?”
“Alhamdulillah Sultana ya kike?”
“Ina lafiya! ”
Ganin haka yasa sauran yan matan dake wajen suma suka dunga tasowa suna mik’o gaisuwa bai damuba haka yaci gaba da amsa musu sai dai tsaf yake lura da yanda yanayin fuskar Meenal ya canza dan haka sai kawai ya waske da cema Sultana d’in idan ta gama abinda takeyi tazo su tafi,
“Ah ah Brother kuje kawai nida Maryam zamu wuce unguwar Malamai ne daga nan zamuyi amfani da motar Meenal din kai sai ka wuce da ita”
“Alright to ba damuwa sai kun dawo muje koh!
“Nidai dan Allah ka tafi nima zan bisu muje can din tare kaji”
“Ai kinji abinda Sultana tace dan haka kodai ki taka mu tafi ko kuma in nad’e hannun rigana in miki irin d’aukar da akema Jarirai, wai bana ce miki saboda ke na shigo cikin school din nan yauba, to wallahi in ma bakya so su kawayen naki su gane alaqar dake tsakanin mune gara tun wuri ki bini mu tafi salin alin sab’anin hakan kuma bazan bar nan ba har sai na tabbatar da nabar musu labari mai armashin da zasu dad’e suna tattaunawa akai kafin in tafi,”
Bata da wani zab’i wanda ya wuce ta bishi d’in,
Dan haka badan taso ba haka su Sultana suka musu rakiya har zuwa inda yayi parking motar shi,
shi da kanshi ya bud’e mata gidan gaba ta zauna kafin ya zagaya ta gefen driver yaja motar suka fice daga cikin school din.
Maryam da Sultana dake tsaye a wajen har yanzun sun juya da niyyar komawa dan akwai sak’on da Maryam zata amsa kafin su wuce juyawar da Maryam tayi idonta ya sauka akan Bash jingine da motar dake gefen su kad’an hannuwan shi rungume a k’irji idanuwan shi kyar a kansu,
Basarwa taso tayi ta nuna kamar bata ganshi ba sai dai kuma shi d’in duk da halin shock d’in da yake ciki na ganin Meenal hakan bai hana shi kiran sunan ta ba domin koba komai yana buk’atar tabbatar wa akan abunda idanuwan shi suka gano mishi,
“Maryam”
Ya kira sunan yana takowa da d’an sauran karfin daya rage mishi zuwa inda take,
Bata iya amsawa ba har ya cin musu,
“Maryam fad’amin dagaske Meenal ne idanuwa na suka gane min ko wata daban?
Meenal na gani yanzun nan fa tare da wannan yayan nasu me nene ma sunan da ake kiran shi dashi?
Uhmm uhmm mai jama’a, eh mai jama’a shifa, wallahi da idona na gansu yanzun nan ya bud’e mata murfin mota bayan ta shiga shi kuma ya shiga gefen direba yaja motar suka tafi,
Mai yake faruwa ne? Dama shine mijin da aka aura mata ko ya abin yake shin ko dai gizo ne ko kuma mai Kama da ita na gani?
Fadamin dan Allah kicemin ba ita bace mai kama da ita na gani ayau, inba haka ba mai zaisa inga Meenal anan bayan an tabbatar min da cewa wani d’an uwanta soja aka aura mata kuma ba anan zasu zauna ba?miye had’inta da mai jama’a kuma? ”
Juyawa tayi bayan ta damk’o hannun Sultana da niyyar subar wajen ganin yana shirin janyo hankalin mutane kan su,
Da sauri yasha gaban su yana had’a hannuwan shi,
“Please Maryam dan Allah ki tsaya kibani amsar tambayoyi na kaina ya d’aure da yawa,
Meenal fa idanuwa na suka gane min bayan tsayin shekarun dana d’auka ban sata a cikin kwayar idona ba”
Sultana ce ta katse shi da cewa,
“Da kata dan Allah bawan Allah ya zaka zo ka taremu a hanya cikin mutane haka, duba kaga yanda kasa jama’a ke kallon mu in ma maganar da kake son yi da ita ya zama dole ai ba anan ya kamata ka tsareta da tambayoyin ka ba sai dai bari ni in sauk’ak’a mata wasu rud’anin da kake ciki a yanzun,
Eh ita Meenal din dai ita ka gani sun fita tare da mijin da zata aura a yanzun duk yanda akayi alamu sun nuna cewa kana cikin samarin ta da aka kasa a shekarun baya, to ko yanzun din ma bana tunanin zaka samu galaba ko nasara a kanta domin kamar yanda wancan karan d’an uwanta ne yayi nasara a kanka wannan karan ma hakan ce zata k’ara faruwa dan haka gara ka shafama kanka lafiya Kaje kaci gaba da zama da yar matar ka ina ga hakan zaifi,
Meenal ba rabon ka bace shi yasa take ta kucce maka,
Maryam idan kin gama abinda kikeyi muna iya tafiya.”
Kusan sumewa yayi a tsaye bai iya motsawa ba har suka kule ya dena ganin su,
“Ke wai waye wancan d’in?”
Sultana ta tambaya,
“Bash ne bash din da nace muku mun had’u dashi s kofar doka shine tsohon saurayin Meenal kafin auren ta da Sarki,
Ban san meya shigo yi cikin makarantar nan yauba gashi duk addu’ar da mukeyi na kar Allah yasa ya bayyana to yau dai gashi ya ganta, na kuma tabbatar da cewa wallahi sai ya nemo ta”
“Bash…. ”
Sultana ta maimaita sunan tana jin jina kai,
“To ai ya riga ya makaro ko yanzun muke da nasara akan duk ma wanda zai bayyana bayan shi,
Domin dai koda bata riga ta furta ma AK cewa itama tana son shiba ina tabbatar miki da cewa akwai son shi a cikin zuciyar ta dan haka kowa ya iya allon sa ya wankeπ€·π»ββοΈ”
Basu b’ata lokaci mai tsayi a makarantar ba suna amsan abunda Maryam zata amsa suka bar makarantar, kamar yanda shima Bash yabar makarantar ba tareda yayi abinda ya kawo shi ba, dan ganin daya ma Meenal yasa komai ya kwance mishi,
Tsayin shekarun nan yayi hakuri da sonta ne kawai tun daga ranar da akace an d’aura mata aure da wanin shi,
Ba k’aramin gwagwar maya yayi tsakanin shi da zuciyar shi kafin ya samu damar mai da son Meenal din can k’asar zuciyar shi ya nemi waje ya birne son nata a ciki ba,
Yasa wuya yasha jinya yasha fama har sai da yayi jinya na watan ni saboda yanda batun auren ta ya mishi mugun bugun da dole ya kaishi k’asa war was,
Yaci buri akan ta burin auren ta wanda a wancan lokacin shine buri mafi girman da yake kwana ya kuma tashi dashi a cikin zuciyar shi, sai gashi kwatsam wai bai tashi jin cewa ita d’in za’a d’aurama aure da wani ba har sai ranar d’aurin auren,
Da badan yana da tabbacin cewa ita ma kanta bata da masaniya ba toda tabbas zaice babu namijin da aka ma mummunar yaudara irin shi,
Saurayin daya riski labarin auren budurwar shi a yayinda ya shirya zuwa wajen d’aurin auren a matsayin zashi auren kannen ta,
Kai shifa wallahi bai taba jin labarin soyayya irin nashi ba.
Bayan fitar AK ba dadewa Ya Sa’eed ya isa gidan Hajiya,
Bayan sun gaisa ne yake ce mata,
“Hajiya akwai sak’on da Sarki ya wakilta ni in ba takwarar ki,
Sai dai halinta dana sani shi yasa nace gara in fara zuwa wajen ki muyi shawara kafin in gabatar mata da sakon, nasan ke zakifi ni sanin yanda zan shawo kanta!”
“Too sak’o kuma?”
Gyara zama yayi kafin ya d’aura da cewa,
“Hajiya nasan kin san burukan da Meenal take dasu a rayuwarta,
Zuwa yanzun Alhamdulillah zamu iya cewa biyu daga ciki sun cika to cikon na ukun ne shi yake son cika mata,
Gidan data tashi da burin ta ginama Baba Malam ne shi Sarki ya siya da sunan ta,
Babu wanda yasan da batun siyan gidan daga shi saini daya damka ma amana saboda baya son kowa yasan cewa shi ne ya siya gidan, sai kuma ke da yanzun nike fad’amawa,
Na fara zuwa wajen kine dan nasan ke zaki san dubarar da zamuyi wajen ganin Meenal ta amsa dan nasan halin ta tana iya cewa bazata amsa ba dan tuntuni take tarin kud’ad’e saboda ta siya filin da zata gina gidan.
*UMMIEE*