Dangina Book 2 Page 2
⚜️🔱👨👩👧👦 *DANGINA*👨👩👧👦🔱⚜️
*~{{MY FAMILY}}~BOOK 2*
©® *UZ-2023.*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*✍🏼
*Page 2*
A wannan dare sam Malam bai samu sukunin yin bacci cikin salama ba, domin kam sosai fa abun ya dake shi bai tab’a zato ko hasaso cewa hakan na iya faruwa a cikin ahalin shi ba sakin aure fa ake magana, auren kuma daya zama auren had’i na farko da suka had’a tsakanin yaran su da fatan karin dankon zumunci a tsakanin su, shine daga tafiya ya dawo ya cimma wannan irin k’atuwar iftila’in.
Duba da cewa suma iyayen su basu kasance mazaje masu sakin aure ba, haka kuma suma da suke a matsayin iyayen nasu yaran sam babu wanda a cikin su ya tab’a tsinke igiyar d’aya daga cikin matan shi,
Amma sai gashi yau an wayi gari nasu Yaron da suke kallo mai nutsuwa da hankali shine ya aikata hakan,
Duk da jawabin da Adamu ya mishi na dalilin da yasa uwar gida tayi tsaye akayi sakin sam shifa bai wani gamsu ba, dan haka ya k’agara gari ya waye ya samu zama dashi Yaron dama iyayen shi, dan bazai yarda da d’abiar saki a cikin zuri’ar shiba, koda ko ace sakin ba akan Meenal ya fad’a ba dolene yabi kadun dalilin sakin balle kuma abu ya fad’o akan ta.
Kamar yanda Malam ya buk’ata cewa Auta ya kira Hajiya akan a dawo mishi da Meenal gida, to dai shi Auta a wannan daren kasa kiran Hajiya yayi har sai washe gari,
Washe garin ma bashine ya kirata ba Mommy ya rok’a domin dai koda kiran Malam din ya riske shi taji sakon da Malam din ya bayar tasan kuma shi Auta bazai iya kiran Hajiya ba dan haka ita da kanta ta kira ta take shaida mata cewar Malam yana son ganin Meenal din a gida saboda zasuyi zama,
Hajiya ko dama tuni damar hakan ta dad’e tana jira dan haka babu musu ta amsa da cewa zasu isa gidan da wuri kamar yanda ya buk’ata,
Duk da cewa Meenal din nada class din safe a ranar amma hanata zuwa Hajiya tayi domin a cewar ta, yanzun lokaci ne na kwatar y’ancin kai bawai lokacin karatu ba.
Shima a bangaren Malam Sulaiman tun daren da kiran Malam ya riske shi sam ya kasa samun sukuni,
Domin shi yasan halin Malam tunda har ya gaza hakurin wayewar gari ya kira shi a daren nan tabbas yasan ba komai bane illah sakon takardar Meenal daya dawo ya riska,
Yayi fad’a sosai dan Wallahi shi dama yasan hakan yana iya biyo baya, dan haka tun daren yake ta kokarin kiran Sarki a waya domin ya shaida mishi cewa koma ina yake to yayi kokarin dawowa Zaria a washe gari dan shidai wallahi uwar gida da d’anta sunja mishi, yana zaman zaman shi bai san farkon matsala ba sai da suka jagwalgwala komai sannan yanzun sun d’auko shi sun sashi a tsakiya,
yanzun haka gobe zaije gaban Malam yayi tsuru² fisabilillahi kai dai ka haifi mutum kawai amma baka haifi halin shiba,
Rashin samun Sarki a waya hakan yasa dole a daren ya aika mishi da sakon Text message,
Washe gari ma yana tashi haka yaci gaba da kiran Sarki a waya amma har zuwa lokacin wayar bata zuwa.
Karfe goma sha d’aya 11am na safiyar wannan rana tayi ma,
Malam Sulaiman,
Uwar gida
Baba Adamu
Innar yara
Hajiya Innah
Meenal
Dama shi kanshi Malam d’in ne a cikin falon shi inda kuma ya bama yaran ahalin maza kaf sallahun cewa dukan su yana neman su da Misalin 12 na wannan rana wato dai bayan ya gama da iyaye kan yaran zai koma.
****
Malam Adamu ne ya bud’e taron da addu’a bayan anyi yan gaishe² ne Malam yayi gyaran murya kamar yanda ya saba,
Duban shi ya maida kan Malam Sulaiman dake zaune daura dashi kanshi a duk’e kafin ya mayar kan uwar gida.
“Sulaimanu hak’ika da kai da Matar ka kun bani mamaki matuk’a domin kun aikata min abunda ban tab’a tsammanin riskar shi daga gareku ba, musamman ma ke Uwar gida!”
Ya k’arasa fad’a yana nuna ta da hannun shi manuniya.
“Shin kun manta shekarun bayane da kuka dunga min zarya a wannan falon nawa kuna rok’on arzikin in d’auki auran Mamana in ba d’anku?”
Ya karasa kalaman shi da tambayar su yana mai jiran jin amsar da zasu bashi,
Malam Sulaiman ne ya amsa da cewa.
“Ayi hakuri ayi mana aikin gafara Yaya, abunda ya faru baya nufin cewa mun manta da alfarmar da Kayi mana na bamu auren ita Mai sunan Hajiya duk da mun san cewa darajar zumunci mukaci, sai dai lamarin muma bamuyi zatan cewa zai juye zuwa gabar da muke kai a yanzun ba sai dai ka haifi mutum ne baka haifi halin shiba”
Yana rufe baki itama Uwar gida ta karb’a da cewa,
“Tabbas abunda ya faru ba abune mai dad’i ba, abune wanda dukan mu bamu tab’a tsammani ba, sai dai na sani cewa laifin duk nawa ne,
Nice naso kaina da nayi zaton cewa idan na aura ma d’ana mata daga cikin Dangin shi hakan zai karkato da hankalin shi zuwa gareni dama yaran shi dake tare damu,
Gaba d’aya son kusanci da d’an da nike ganin yamin nisa yasa na manta cewa rayuwar yarinyar da muka aura mishi zai iya zama cikin kunci,
Nayi zaton cewa d’a mai biyayya na haifa wanda zaiso abunda na bashi ya kuma tattala abun koda zuciyar shi bata so,
Sai dai ina ashe ba haka bane, domin ya nuna min cewa bako wacce zuciya ake cusa ma abinda bata muradi kuma ta k’arb’a hannu bibbiyu ba,
Hakika nayi kuskure naso kaina domin a lokacin baya idanuwa na ya rufe ta yanda bana hango komai sai rayuwar d’ana banyi la’akari damai zaije ya dawo ba,
Ashe shi ya amsa ne kawai dan yamin biyayya bawai dan yana soba wannan dalilin yasa koda muka aura mishi ita yakai ya ajiye ba tareda ya damu da kula da sauke hakkokin ta wadanda suka rataya a kanshi ba, mafi hatsarin kuma shine rashin sauke hakkin shimfid’a”
Katseta Malam yayi da cewa,
“Kenan kina nufin cewa dama tun da fari shi Sarki bai amsa batun auren ba kece kikayi ruwa kikayi tsaki kika dunga taso min keyar Mijin ki a gaba kuna min jele da rokon in baku auren uwata?”
Malam ya tambaya.
Ita ko Hajjaju dake gefe salati ta d’auka tana tafa hannuwa cike da mamaki take cewa.
“La’ilaha illahlahu muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam,
Ke koh dai wagga mata akwai ki da son kai dama na zuciya!
Yo ashe ba iya jikata kad’ai kuka tilastawa auren dole ba shima kanshi mijin cusa mishi ita kukayi! Yo ba dole tak’iyin daraja a wajen shi, ku a wajen ubanwa kukaji cewa anawa maza auren dole? kodan dai kunyi sabon yin ma yaran ku mata auren dole shine wannan karon kuka juya kan maza?,
To dan Allah jama’a ku tayani ganin wannan al’amari fa inba son kai ba in d’anki yayi nesa dake saboda Allah ya had’ashi da wata can k’atuwar mushirika ta shiga tsakanin ku miye na jikata a ciki da zaki sakota cikin dambarwar gidan ki?,
Kai wannan mata wannan mata da son kai kike, lallai ashe alhakin jikata ne ya bibiye ki shi yasa auren yak’i yayi danko, inba haka ba jama’a kina matsayin uwa ace d’anki na cikin jafa’i mai makon ki tashi tsaye kema ki yaki Matar tashi da karfin kudurar ubangiji kisa a taya shi da addu’a kema kuma ki dage, shine kike zaton yi mashi aure ne mafita bayan ita shed’aniyar Matar nashi na raye tare dashi?,
Ashe konton b’auna kukayi min kuka sa na yarda da cewar za’ama jikata auren ne kawai saboda a samu mafitar ciwon marar dake damu ta a wancan lokaci, dan cin amana ashe shigo shigo babu zurfi aka min, yanzun shi yayi saki ya tattara yayi wucewar shi wajen Matar shi ita kuma jikata an barta da zawarci, niko yar iya harda dagewa na wajen nemo mishi maganin sammu, to kowa yaje da halin shi wallahi mu dai bamu nufi kowa da sharri ba wanda kuma ya kullace mu cikin shi tayi”
Baba Adamu da Innar yara na suka dage wajen ba Hajiya hakuri dan sosai fa ta nemi burgewa sai faman maganganu take,
Sai da tayi shiru sannan shi kuma Malam ya amsa da cewa.
“Duk ma masu cewa munayi ma yaran mu mata auren dole ko kuma auren wuri, suna fadane kawai saboda jin dadin bakin su,
Nidai abunda na sani shine hakkin ubana wato ya zab’o ma yarshi miji na gari, sannan ni a wajena ban tab’a hango illah a wajen aurar da ya mace da wuri ba, duba da zamanin da Allah ya kawo mu a yanzun,
Bawai muna ma Allah wayau bane, ba kuma muna gadara akan kasancewar mu Malamai bane balle muyi tunkaho da hakan cewa mu yaran mu bazasu iya fadawa wani halin na rashin d’a’a ba,
Ita ya mace tamkar glass take koda ka adana ta a waje d’aya tofa sai Kayi kata tsan tsan domin abun kadan ne zai iya ture ta ta fado ta tarwatse,
Zaka iyayin ajiya na kayan kwaras na tsayin shekaru a waje d’aya amma fa duk ranar da tsautsayi ya amfa musu lallai zaka sha mamaki domin da zarar sun rushe fa babu wani tsafin da zakayi wanda zaisa su koma dai dai yanda suke tun farko,
Alhamdulillah a hakan muke kokarin bama yaran mu mata kula har zuwa lokacin da muke ganin sunkai kun zalin da zamu aurar dasu su koma hannun mazajen su, su kuma su d’aura da nasu tarbiyar,
Ita diya mace inka dubi rayuwarta kacokam zataga tun daga tashin ta har zuwa tsufanta komai nata a takaice yake, in an haifeta zata samu tarbiyar farko a gida, a tashin ta bata san kowa ba sai yan gidan su, ma’ana uwa uba yayye kanni da kuma sauran Dangin dake tare da ita, soyayyar farko da take tashi dashi shine na ahalin ta,
Mataki na biyu tarbiya na biyu kuma sai ya koma a hannun mijin auren ta da nashi ahalin, a hakan muke bakin kokari wajen zab’o mai tarbiyar da muka san zaiyi daidai da namu tarbiyar da muka d’aurata akai, wanda shi kuma zai daura mata nashi ciki harda yanda zata so shi su kuma rayu a tare,
Mataki na uku kuma shine matakin da mace zata fara hayayyafa itama,
A sanda ta fara haihuwa itama zatayi kokari ne wajen ganin taba nata yaran kalar tarbiyar data samu tsayin rayuwar ta.
Mace ta kasance halitta mai sanyi ta yanda duk abunda iyayen ta suka gabatar mata koda bashine ra’ayin ta ba, gudun b’ata musu kansa ta amshi abun da hannu biyu takuma rayu dashi tsayin rayuwa,
Sab’anin namiji,
Yara maza suna da taurin zuciyar da idan suka ki abun wasun su ba lallai ne su iya daga idanun su suyi duba da abun ko mai nene ba,
Idan kuma an samu masu biyayya zasu amsa din kamar yanda shi Sarki yayi biyayya ya amsa amma daga karshe ya jingine ta duba da cewa ita d’in ba zabin shi bane na iyayene abunda ya zamar mishi dole dama shine yayi musu biyayya kuma yayi tunda ya amshi auren,
Kwarai ina ma yarana mata auren wuri,
Sai dai kuma kafin auren saina bincika waye shi mijin da zan d’auki yata inbashi?
Shin ya cancanta ko kuma a’ah?
Ya addinin shi? Ya kuma nasabar shi? Shin zaima iya rikemin ita ya faranta mata ya kula wajen sauke hakkokin ta?
Sosai nake tsayawa in nazarci mutum kafin in bashi auren yata ciki kuma harda lura da halin ita yarinyar domin dai bazaka d’auko wuta da wuta ka had’a waje d’aya sannan Kayi zaton samun salama ba,
Tsayin lokaci da muke auran yaran mu babu wacce ta tab’a fuskantar wani kalubalen daga wajen mijin da muka zab’a mata alhamdulillah muna alfahari da hakan,
Amma abun mamaki sai auren da muka had’a a tsakanin yaranmu wanda zamu iya kira da tuwona maina shine a yau muka taru saboda shi,
Wa’iyazubillah wannan abu sam baimun dad’i ba,
Ba kuma na ganin laifin kowa sai ku dai ku biyun nan domin ni dai yata nasan kalar tarbiyar dana bata kuma Alhamdulillah duk da bason d’an ku takeyi ba tayi biyayyar zama dashi na tsayin shekaru ko sau d’aya batayi tunanin kawo min karar shiba”
Ya k’ara sa fada yana nuna uwar gida da malam sulaman da hannu,
Baki malam Sulaiman ya bude zaiyi magana amma malam ya tari numfashin shi da cewa.
“Bana son jin ta bakin kowa tukun ku bari in gama nawa maganar,
Ku kun sani cewa zumunci shine abunda na duba kafin in amince da batun bama danku auren yata domin ko babu komai shima din nawa ne dan ban manta cewa nine na amso mishi auren shi na farko ba,
Duk da tarin nakasun dake gareshi haka na ture na biye muku na b’ata ran uwata badan ina soba sai dai nima a lokacin idanuna sun rufe da son ceto ta daga halin ciwon da likita ya tabbatar da cewa aure shine maganin shi,
Kafin ku nuna kuna buk’atar a had’ata dashi wasun ku da dama sun fito sun nuna kwadayin su nason auren ta,
Amma zumunci yasa haka nan na runtse ido naba na kusa dani nayi amfani da kalmar nan da yan magana ke cewa duk dadin inuwar gemu bai kaiga makogoro ba,
A lokaci na farko dani da kaina na assasa auren zumunci a tsakanin yaran mu, a zatona hakan zai kara zumuntan da iyayen mu sukayi tsayin daka wajen ganin kafuwar shi a tareda mu.
Babban abun bak’in cikin shine yanda ya zaman wai ku iyayen su mata kuka kasa gane wani irin zama yaran nan suke gudanarwa tsayin shekarun nan,
Ni nayi ma yata aure a zatona auren nata zai zama waraka a gareta, ashe aikin banza ne shi mijin ajiyeta yayi kamar ka d’auki kudi ka zuba a asusu kasan babu mai tab’a maka har sai randa kai ka buk’ata,
To Alhamdulillah dukan mu dai nufin alkhairi mukayi, na kuma gode Allah daya tsaremin uwata duk da halin da take ciki amma allah ya kiyaye ta bata fad’a cikin wani halin na daban wanda bai dace ba,
Ke kuma bayan kin fahimci abunda ke faruwa dake da kakarta mai makon ku kawo mana maganar gaban mu mu iyayen su mu d’auki matakin daya dace a ah sai kuka nuna mana halin ku na mata kuka yanke hukunci kai tsaye,
Ita ta d’auke jikarta zuwa gidan ta ke kuma kika sa naki d’an a gaba ya rubuta mata takardar saki, to shin wai ma kafin ya saketa d’in kin tuhume shi cewa yana son ta ko a’ah?”
Ya kare maganar da maida tambayar shi akan uwar gida,
“Ayi hakuri Malam amma nidai nayi la’akari ne da cewa inda yana son ta da ba’a d’auki tsayin shekarun nan suna tare kuma ace babu abunda ya shiga tsakani ba, domin ko ban tambaya ba a bayyane yake cewa harda rashin so ya shiga cikin al’amarin nasu”
Uwar gida ta bashi amsa.
“To ai ba shi kadai yake da hakki ba ita Meenal din kuma kinsan meye a nata zuciyar ne?
Wata kila tana son shine shi yasa har tayi hakurin zama a hakan ba tareda ta sanar da kowa irin zaman da sukeyi ba”
Mai makon uwar gida ta bashi amsa wannan karan Hajiya ce tayi tsalam da cewa,
“Ah ah kam wallah akai gaba jikata ma ba son shi take ba, zaman hakuri dai tayi dashi yanzun kuma mai afkuwa ta afku aure ya k’are dan haka kowa yayi ta kanshi,
Kee Meenal bazaki bud’i baki ki fada musu cewa ba kya son shiba sai sun kara k’ak’aba miki shi abu dai kamar dole?”
Ta fada a tsawace tana kallon meenal din,
“Eh Baba Allah kuwa nima bana son shi dan Allah karku matsa min cewa saina koma, kuyi hakuri in kun bani umarni bazank’i biba sai dai zan koma zama dashi ne kawai badan ina soba kamar yanda shima ya tabbatar min da cewa har yanzun ban canza daga matsayin k’anwa a wajen shiba”
Ta k’arasa fad’a cikin muryar rok’o adanuwan ta a kasa batareda ta iya kallon kowa a cikin suba.
“To kun daiji da kunnuwan ku atoh itama jikar tawa bata so, da dai an mata dole amma yanzun kam babu mai karayi mata dole akan auren wanda tace bata so shima kuma din ba son nata yake ba,
Yanzun kuma kai ka gama jawabin cewa kana bada auren yaran ka mata ne ga mazajen da suka cancan ta, dukan mu nan kuma mun shaida cewa yaran nan basa bukatar auren, saki kuma ya tabbata”
“Tashi kije ciki Mamana babu wanda zai miki dole tunda bakya so, Allah ya miki zabi mafi alkhairi, Allah kuma ya albarkacin rayuwar ki hakika ina alfahari dake”
Da ameen sauran jama’ar dake wajen suka amsa.
Dan haka itama Meenal din ta mik’e da niyyar barin falon,
“Ke jirani mu tafi kinji dan dama ba wani karin arziki nayi ba, gara in koma gida in samu inci in koshi tunda Allah ya taimakeni komai yazo karshe yau dai kam bacci zanyi babu jimami”
“Meenal bazata koma tare dake ba Hajiya nan dai gidan ubanta zata ci gaba da zama inda ta rayu tun bayan haihuwar ta, yanzun kuma dan auren ta ya mutu hakan baya nufin zan barta ta koma wani wajen daban da zama, dan a wajena ita din har yanzun yarinya ne dole ta dawo gaban mu muci gaba da kula da tarbiyar ta kafin allah ya fiddo mata wani mijin tayi wani auren”
Kafar wanda ya zabge fuskar Hajiya da mari haka taji saukar maganar shi a cikin kunnuwan ta,
K’ifi k’ifi ta farayi da ido harshen ta har yana hardewa wajen furta cewa.
“Kai Malam Almu ka kiyayeni ka fita idona in rufe tun wuri,
Harni ce zaka kira gidana da wani wajen, kace wai jikata bazata je wani wajen ta tareba,
Nafa gaji da mulkin mallakar da kake gwadamin tsakanina na jikokina,
In mantawa Kayi bari in tuna maka cewa ni nan dai Hajiya Aminatu da kakeji da gani nice nan na haifo Hauwa’u Jidda uwar data tsugunna ta haifo Meenal, yanda nike da iko da Jidda haka nike dashi akan yaranta,
Tun tuni da nake kauda ido akan hukuncin da kake yankewa a rayuwar yarinyar nan darajar Mukhtar kake ci,
Amma yanzun kam tabbas idan ka matsa a shirye nake domin yin fito na fito da kai, wato taci gaba da zama anan haka nan ita zata k’are rayuwarta bazata samu kula na musamman daga gefen uwa mace ba,
Tunda aka haifo yar nan ka kankame ko ina ka hanata shakuwa da uwarta,
Wanda rashin shakuwar nasu shi ya taka rawa wajen lalacewar auren da kuka mata dan da ace akwai shakuwa tsakanin ta da uwarta tabbas bazataki shaida mata halin da take ciki a zaman auren ta ba,
Ko kai dan kana ganin kafi kowa kusanci da ita a naka zaton duk wani damuwarta idan ta taso kai zata tunkara kai tsaye,
To ga karamin misali nan ai ka gani tunda ga damuwar nan amma duk ta tsallake ku duk yawanku a gidan nan ta bini can wani wajen daka kira ta maida min damuwar ta,
Dan haka komawar Meenal gidana kamar anyi an gama dan koshi uban daya haifeta shi Auta bai isa ya hana ni rikon taba wannan karan atoh”
Baba Adamu ne ya shiga maganar da cewa,
“Kiyi hakuri Hajiya bazamu hana ta zama a wajen kiba tunda kin bukaci hakan Allah ya tayaki riko,
Ya’ya Kayi hakuri dan Allah su tafi d’in koba komai a yanzun nasan ita Meenal din zatafi sakewa acan fiye danan, da in ta zauna tunani ma na iya sata a gaba kuma muma bazamu so ganin ta a wani yanayi ba”
“To sai dai ta zauna na wani d’an lokaci amma ba wai zaman din din din ba, kai ka sani yaran mu basa tab’a zama a wani wajen aure kadai shike rabamu dasu”
“Ka daiji da shi” hajiya ta fad’a a yayinda ta riko hannun meenal da niyyar barin falon,
Har takai bakin kofar falon ta juyo tana kallon uwar gida,
“Nace ba! Kar kuce ban fad’a muku ba cikin satin nan zan tura a kwaso min kayanta dake can gidan, dan ba’a barsu babu kowa a gida kayan makudan kud’i su lalace a iska ba”
Suna fita daga falon motar Hajiyar da direban ta ya tuko su suka shiga ya k’ara jansu domin komawa inda suka fito,
A hanya ko sai mita take akan bazata k’ara yarda Malam yaci gaba da mulki akan jikokin ta kamar wani shine uban su ba,
Yayin da a can falon kuma bayan fitar su Hajiyan suma uwar gida da mai gidan ta hakuri suka k’ara ba Malam din da rokon cewa suna fatan bazai rikesu a zuciya ba balle har hakan ya tab’a zumuncin su,
Malam ya musu nasiha sosai sannan ya k’ara jan hankalin su akan kula da addu’a akan yara, kar kaga cewa yaran ka sun girma Kayi zaton cewa shike nan sunyi hankalin da zasu kula da kansu balle kuma hakan ya d’auke hankalin ka akan yi musu addu’a da nema musu kariya akan sharrin masu sharri,
Domin koda Allah ya hada miji da mata nagari tofa yakan iya haduwa da shedanun abokai,
Shedaniyar kishiya,
Shedanun kawaye,
Mahassada dai suna a ko ina wasu ma yawanci dasu muke rayuwa amma bama tab’a sanin hakan har sai ranar da Allah ya kaddara tonuwar asirin su,
Dan haka ya kamata iyaye suyi tsaye wajen koyama yara addu’a tun daga yarinta har zuwa girma,
A kuma dunga kiyaye azkar safe da maraici, sannan sadaqa tana maganin masifa Allah kuma ya tsare mu da tsarewar sa ameen,
Ya dai musu matashiya sosai sun kuma yaba sunyi godiya kafin suka mishi sallama suka wuce zuwa gida,
Itama kuma Innar yara ta koma cikin gida,
Karfe 12 kamar yanda ya buk’ata duka yaran gidan maza da masu aure da marasa shi ba iya kuma yan cikin gidan nashi ba duk yaran ahalin maza yasa aka kira mishi illah wadanda basa gari ne kawai basu hallata a wannan kiran na Malam ba,
Bayan taruwar su yayi amfani da wannan damar bayan ya shaida musu barakar data kunno kai a cikin a halin na mutuwar auren Meenal wanda babu wanda yaji dadin hakan a cikin su,
Yaja musu kunne sosai tunda masu auren harma da samarin cewa duk fa wanda yasan zaiyi aure to ya d’aura damarar zama da Matar har zuwa sanda mai rabawa zai raba domin su dai a ahalin su ba’a musu tambari ko shaida akan sakin auren ba tun daga kan kakannin su har zuwa kan iyayen su da kuma sudin kan su,
Ba kuma zasu zuba ido hakan ya faru akan yaran suba,
Na Sarki da Meenal sun d’auke shi a matsayin kaddara amma sufa sauran kar suyi duba da cewa ai sarki ya bude musu kofa ne suyi zaton cewa suma zasubi sahun shi babu wannan maganar,
Domin dai su dama yaran maza ba kamar mata bane ko wanne ana bashi damar ya zab’o Matar data mishi ne kafin a aura mishi,
Daga karshe suma Malam ya musu tuni akan rike ibada da kula da addu’a kana kuma ya k’ara jan hankalin su akan rike zumuncin dake tsakanin junan su,
Domin yana fatan zaman lafiya da fahimtar juna ya tabbata a cikin ahalin shi ko bayan kasa ya rufe mishi ido,
Haka dai a ka tashi wannan taro jiki a sanyaye kowa na mamakin ya akayi auren Sarki da Meenal ya mutu,
A wannan rana dai mutuwar auren shine ya zama labari mafi zafin daya dunga watsuwa a tsakanin ahalin.
#No aditing 😒
#Team AK
#Team Sheikh Naseer
#Team Hajiya
#Team Malam
*Ummiee Zaria*✍🏼