Arubuce Ta Ke 82
Page 82
Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta.
Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba.
Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa
“Koma kiyi sallama” da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo
“Ikon Allah,ashe tare kuke” hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa.
Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata.
Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din
“Hajiya ina kwana?” Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai
“A’ah yau kece a gidan?” Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad
“Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen” ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta.
Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe
“Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai” aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan?
“Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi”
“Tooo…. ikon Allah,koma to ka zauna” hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba.
Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din.
Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa.
Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana.
Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice
“Tirqashi” ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za’a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?.
Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi.
Motsawa baba usaina tayi
“Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi”
“Haba,kiyi zamanki,duka ba ‘ya’yanki bane” hajiya ta fada da kyakkyawan nufi,dama haka takeso,don haka ta koma ta zauna din tana cewa
“Hakane,ia bakaqi ba,kada aga kamar bakasan matsalar kowa ba sai taka,d’a ai na kowa ne, bare abbas da kowa yakecin moriyarsa?”.
“Ina jinki hafsatu,mene ya faru?,ina fata ba matsala bace” fara matsar hawaye tayi sannan ta magantu
“Matsala ce hajiya, matsalar kuma abban mimi ne da kansa yakeson haifar da ita cikin gidansa”
“Tofa!,tirqashi!” Baba usaina ta fada da madaukakin sauti bayan ta kama haba,yayin da abbas ya bude dukka idanunsa a kanta yana kallonta,tare da sauraren wanne kalar sharrin kuma zatayi masa
“Mene ne ya faru?,gayamin” gyara zaman
“Hajiya,kwata kwata abban mimi bambanci yake nunawa tsakanin da widad muraran,bayason huldarmu ni da ita,qiri qiri sai suzo weekend har su gama bazanga fuskarta ba bare ta zauna a gidanta ba,wasu ma basai suyimin sharrin na hanata zama ba?”
“Laahhhh,da gudu kuwa,mutumin yau da baka iya masa?,tabdi” baba usaina ta karbe zancan
“To bama haka ba,ta yaya zamu shaqu mu fahimci juna da ita hajiya tsakani da Allah,sannan su kansu yaran nan bakiga yadda sukeson zama da ita ba,amma gaba daya basu samun ganinta,a haka kan iyalinsa zai hadu?” Shuru hajiya tayi tana jinjina kai,maganarta ta qarshe ce kawai taja hankalinta,har takega tayi magana me ma’ana,baba usaina nason tsoma bakinta tace wani abu,amma kuma kwarjinin abbas din ya hanata,banda
“Gaskiya ya kamata a aduba,saboda gobesu dana yaran” shi taketa maimaitawa
“Kinzo da magana me kyau da ya kamata a duba,ki kwantar da hankalin ki, za’a gyara lamarin in sha Allah, Allah yayi muku albarka,ya qara hada kanku,ya wanzar da zaman lafiya a tsakaninku”
“Ameen ameen…. yauwa,hakan dai yafi gaskiya,ta nan ne zasusan darajar juna,ita tasan darajar uwargidanta”.
Taso ta sake qirar wani abun,amma hada idon da sukayi dashi yasa ta kasa cewa komai,sai kawai ya miqe ya fice afalon ransa yana masa suya,fita yasoyi amma sai ya kasa,yana daya daga cikin kujerun dake harabar gidan ya zauna kawai,qafarsa daya kan daya yana dan jefata a hankali,bacin ransa yakeson dannewa,ba kasafai ya fiya son barin bacin rai yana masa tasiri ba.
Ba jimawa baba usaina ta fice,daga bisani hafsat din ta fito yaran suna biye da ita,hajiya a bayansu tana rabawa yaran alawa da manyan biscuits data saba basu,daga inda yake zaune yana kallonsu,yasan babu lallai su ganshi,har suka fice daga gidan ya kasa motsawa sai rakiya da yayi musu da idanu.
Sai da aka kira azahar ya fita masallaci yayi sallah,daya dawo sai ya bude setting room din gidan dake farfajiyar gidan ya kwanta,har yanzu abun yana masa yawo a zuciya,shi har yanzu baiyi girman da za’a daina kawowa hajiya da kawunnansa qararsa ba?,har yanzu baiyi girman da kunnuwan hajiya zasu daina jin matsalarsa da damuwarsa ba?,har yanzu hafsat batayi hankalin da zata zauna dashi su fahimci juna su warware matsalarsu ba shi da ita ba tare da duniya taji ba?,kansa ya kada a hankali yana kiran sunan Allah,ya rasa yadda zai rabata da wannan halin,bayan shi din har yau bayajin zai iya tuna wata rana da ya taba kai qararta gidansu ba.
Wayarsa dake saman kansa ya dauko,ya lalubo number dinta dake rubuce da sunan BABY DOLL ya kira, ringing daya aka daga,muneera ce,ta gaya masa sallah takeyi,yace idan ta idar ta gaya mata ta sameshi a setting room,ya ajjiye wayar yana gyara kwanciyarsa.
Minti biyar cikakku qamshinta ya fara marabtarsa,ya rufe idanunsa yana budesu,suka sauka a kanta,hannunta dauke da madaidaicin tray data dora wani glass jug akai da qaramin cup guda daya.
Ido ya zuba mata yana qare mata kallo son ranshi,kamar kowanne lokaci sai yaji damuwarsa tana raguwa,a nutse ta iso ta sunkuya a gabansa tana ajjiye masa jug din,sai ya fara yunqurin tashi,ta miqe zata ja baya ya samu nasarar riqota,yayi mata mazauni saman cinyarsa,kunya ta sanyata boye kanta a kafadarsa,taqi yarda su hada ido
“Ki kalleni please baby…….zuciyata ba dadi,nasan zan samu relief” har cikin zuciyarta taji wani abu ya tabata da fadin hakan,saita daga kanta da sauri,kodai qarar da mommy hafsat ta kawowa hajiya ce ta bata ransa?,ta tuna kalaman mommynta na qarshe
“Banda kai miji qara,abune mara kyau,koni bance ki kawomin qararsa ba,idan ya bata miki rai ki gaya masa ku fahimci juna” sannan ta tuna da kalaman ummunta
“Kome mijinki yayi miki ya isa ne,banason qorafe qorafe dakai qara” sannan tana tuna yadda take sanya yayyensu a gaba da fada duk sanda kika kawo mata qorafi akan mijinki,musamman idan bai gamsheta ba
“Kayi haquri” ta furta da tausasan labbanta da ko yaushe suke burgeshi,har baisan sanda murmushi ya subuce masa ba,ya rabb……ba ita tayi laifi ba,amma ita take bada haquri,ya tabbatar idan zai dige indai ba wuya ce tayi wuya ba zaiyi wahala wannan kalmar ta fita a bakin hafsa
“Zan haqura,amma saikin yarda na taba nan” ya fada yana mata nuni da qirjinta da yadan sake cika,da sauri ta kama hannunsa da yayi mata nunin dashi tana fidda ido waje,saidai kafin tace wani abu ya langabe mata kai kamar ba shine babansu mimi ba
“Don Allah,kiji tausayina mana” kafada ta noqe masa itama tana shagwabe masa
“To na kwanta agun ko na minti daya ne,idan kikace aah fa zanyi kuka” dariya yaso bata,amma tsoro tsoron da takeji ya danneta,kafin ta bashi amsa ya kama dukka hannayenta biyu ya riqe cikin nasa,ya kuma cusa fuskarsa da kyau tsakanin qirjin nata.
Sosai ya zuqi numfashi ya kuma fesar,ta lumshe idonta tana jin yadda dumin numfashin yake ratsa ta tun daga rigarta zuwa brassiere dinta,ya kuma tarar da fatar wajen.
Wani irin abu data kasa daurewa ya zarce dayi mata yana sake cusa kansa a wajen,ta zame hannuwanta daga cikin nasa ta riqe kansa da kyau,sai ya tsaya cak jin yadda jikinta ya dauki rawa,ya kuma zare fuskar tasa,ya sauke idanunsa da suka kada sukayi jaa saman fuskarta.
Sai daya dauki wasu sakanni yana kallonta sannan ya motsa bakinsa cikinn shaqaqqiyar muryasa yace
“Ina da buqatarki baby…..ina da buqatarki gaba dayanki,rayuwata na da buqatarki fiye da yadda ruhi yake da buqatar numfashi” kalaman sun mata nauyi sosai,saita kifa kanta kawai a qirjinsa bugun zuciyarta na qaruwa.
Sun jima a haka kafin ta zame jikinta ta sauka qasa ta bude jug din,smoothie ne na banana da yasha madara data jefawa qananun ice cube a ciki yayi madaidaicin sanyi,ta tsiyaya ta miqa masa a cup.
“Na gode” ya fada yana karba,kunyarsa tasa ta sakin murmushi kawai,ya kurba ya lumshe ido,dadinsa yana ratsa kunnuwansa
“Yaushe kika koyi wanann?”
“Jiya,yayi dadi” sai daya jijjiga kai sannan yace
“Over!” Yadda ya fada din ya bata dariya
[3/18, 4:01 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*