Dabi’ar Zuciya 18
Ya lura da kyau ya fishi kyan fata da kuma kyan fuska,duk da cewa sutura jikinsan ba wata ta az a gani bane,amma sai yaji shakka da kokwanto,kada fa yabar wannan baqon yaje labari yasha bamban,saboda yana da labarai da dama kan irin hakan data faru akan wasu samarin,wasu ma rakiya suke zuwa,amma daga qarshe suke yin wufff da ‘yan matan.
Jin cewa har zuciyarsa bata gamsu ba saiya girgiza kai
“Kai anya kuwa?,aradun Alla tsoro nake,bansan irin zaqin baqinka ba,kada ka janyomin asara” Dariyar dake cin samir ji yake kamar ya saketa,musamman idan ya hango kaltume a tsaye a yadda take,ana zancan wai kada ya qwacewa wani ita,yarinyar da ko ‘yan aikin gidansu sunfita kyan gani.
Abokinsa dan ladi ne ya daki kafadarsa
“Dalla malam wannan baiyi kama da masu cin amana ba,tunda yace zai maka naji na amince dashi,kuma ma ai kai kankarowa kanka girma zakayi ma,ka bashi dama,mu tsaya muga ikon Allah” Dan jimmm haladu ya sakeyi,alamun har yanxu yana kokwanto,daga bisani saiya gyada kai
“Naji na amince,Allah ya bamu sa’a”
“Amin” samir ya fada,a halin yanzu babu abinda yakeso irin ya samu sarari ya kwashi dariya,yadda haladun duka ya rude ya tsure kai kace mai tallan yalone zai shiga fadar shugaban qasa neman aurenta,amma dai yana son ganin qwaqwaf ne,saboda haka yace su biyoshi sanda yaga tana neman hanya tana barin filin,da alamu gida tayi.
Saida suka gota wajen hayaniyar yace su tsaya daga wani waje daura da inda kaltumen take tafe a hankali,suka tsaya suna binsa da kallo,tare da dakon abinda zai biyo baya.
Sai daya dan tsaya yana qoqarin controlling kansa saboda dariyar dake cinsa,wai yau shine lokaci na farko a rayuwarsa zai tsaida budurwa,budurwar ma ta qauye,inama ace Aamirunshi yana kusa suci wannan dariyar tare?,kai yama zama dole ya tattagoshi daga inda yaken ya dawo gida,zaman ya isa haka.
Kamar gaske ya matsa daura da ita ya rangada sallama,da fari ta tsorata,don a firgice ta waigo,sai taja burki ta tsaya gami da matsawa gefe kana ta tsura masa idanu,tana kallon baquwar fuskar da bata taba ganinta ba tsahon rayuwarta
“Yammata….an yini lpy?” Muryarta can qasan maqoshinta ta amsa masa tana sake matsawa nesa dashi,wai koda abun gudu zai taso.
Tsaf ya soma tsaratan cikin mintunan da basu gaza biyar ba sannan ya dora da cewa
“Ni aikoni akayi,dubi can” waiwayawa tayi a mamakance tana duban inda yake nuna matan,inda su haladu ke tsaye,ta gansu sarai,ta kuma dama fahimta take takensa,saita janye idanunta,ta maido kan mutumin da batasan waye ba.
Tsaki takeso taja,amma hakanan sai harshenta yayi mata nauyi ta kasa,haka kawai taji mutumin ya cika mizani da ma’auninta na ganin girman mutane,cikin jerarrun kalamanta wanda bai zaci jinsu a haka ba,duba da yanayinta tace
“Ka shaida masa ni an riga an aiko gidanmu,an kuma bada ni,kada ya sake tsayar dani ko ya aiko wani” abinda bai taba kawowa ba sai yaga ta juya tayi tafiyarta abunta.
“Ya….ya ake ciki?,ba’a dace ba ko?” Haladu ya fada cikin damuwa yana taba kafadar samir,sai ya kada masa kai
“Abokina ai an bada aurenta ashe?”,hayaniya suke da alama musu suke a tsakaninsu,zuwa can hayaniyar ta qara yawa
“Kai kai bashari….qaniyarku” Hannafi daya baro wajen gini ya fada yana nufar yaran da suka fara shirin dambacewa cikin hanzari,sai samir din ya taka a hankali zuwa wajen shima yana dubansu,wani abun sai cikin karkarata.
uniform din makarantar a qa’ida fari ne na yara maza,matan blue da farin hijabi,amma idan ka dubesu a nutse da kyau zakaga kowanne kalar kayan jikinsa ya banbamta dana dan uwansa,wani ma wandon goda ko rigar gida ce a jikinsa,kamar yadda wasu daga cikinsu hijabin gida ne a jikinsu.
Hannafi ya tambaya rigimar m suke,yayin da yaran gaba daya suka zuba mishi idanu,har kwanan gobe basa gajiya da kallonsa,ganinsa suke wani baqon halitta a cikinsu,baisan me yasa ba,duk da cewa shima irin kayan ma’aikata yake sanyawa ba wasu kaya bane na daban,don baya burin su gane koshi din waye. Saidai kafin hannafi yakai ga bashi amsa wani zaqaquri cikin yaran ya soma magana
“Zane aka bamu a makaranta akace mu kawo…..shine nace kattume za kaiwa wadda ta yimin wannan zanen,saboda itace takeyi mana,sai alasan yace shima ita zai kaiwa,duka wadan nan ma sukace itace xata yi musu,nace to ni za’a fara yiwa tunda ni na fara fada,shine labaran yace saidai mu kaiwa yayarsu,kuma kattume tafi iyawa”. Sosai sunan ya bashi dariya cikin ransa,ya maimaita sunan wajen sau biyu,hakanan sai yaji yana sha’awar ganin zanen nata da ake kodawa ana cewa tafi kowa iyawq
“Mu gani” ya fada yana sakin guntun murmushi,saidai kafin bashari ya bashi har mutum uku dake tsaye cikin yaran sun miqa masa takardun hannunsu,ya samu nasarar karbar ta mutum daya daya daga ciki.
A hankali yake kallon zanen yana nazartarsa,ko da wasa tunaninsa bai taba hango masa zaiga kyakkyawan zane haka ba,yayi tunanin zaiga shirme ne kawai duk yadda yaran ke masa bayani,mage ce aka zanata sosai a zaune tana cin abinci,tako inq zanen ya cancanci a bashi maki,abubuwan da ake buqata don qawata zanen da kuma fiddq ainihin taswirarsa kadanne,saiya jinjina kai ya daga kan nashi yana miqa musu zanen yana duban hannafi
“Wace kattumen ne,wace makaranta tayi?” Hannafin na gyara zaman hular dake kansa,wadda ta cimmasa har kunne ya amsa masa da
“Yar gidan amadu ce,ko furamare batayi ba” Da mamaki ya kalli hannafi,har zaice wani abun sai kuma ya fasa,kasancewarshi bamai yawan shiga sharo ba shanu bane,don ua raba gardamar yaran saiya fidda ragiwar sabin kudi dake jikinsa ‘yan ashirin ashirin ya baiwa hannafi ya rarraba musu,yana tsaye daga gefe yana kallon yadda sukeya murna,suna tambayar hannafi inda ya samu kudi sababbi
“Ban sani ba,dan mai da tambaya”haka yake fada idan ka dameshi,har sai daya kammala sannan ya dawo wajensa
“Yallabai….nace ko xamu qarasa kaga filin?” Kai ya gyada masa kawai yana amsar gorar ruwa me sanyi da umar ya iso da ita ya miqa masa.
*********Abu na farko da yazo kanta ta zana shine gida,gidan da take sanya ran zata siyawa ummanta,gidan data ci buri watan watarana zata dauke ummanta ta kaita can,ta zauna ita kadai ta huta da masifar babansu,a shekarunta da basu wuce sha biyar ba,ta koya abubuwa masu tarin yawa a rayuwa saboda yanayin yadda rayuwar tazo ta risketa,duk da abinda wasila tayi mata ya tsaye mata a rai,ta kuma rasa yadda zata fassarashi,amma tayi masa waje can aljihun baya ta ajjiye damuwar maganganunta,tunda dai tasan iya tsahon zamansu ta zauna a wasilan da zuciya daya,bata taba yunquri ko sha’awar cutar da ita ba.
“Yallabai nan ne wajen,idan ka duba da kyau yana kusa da magudanar ruwa” cewar hannafi bayan sun gama zagaya wajen,kai samir yake jinjinawa,wajen ya masa kam,zai kuma dace da gidan gonar da yake da burin yi cikin qauyen,don haka ba tare da yace komai ba ya soma tattaki zuwa saman dan gajeran dutsen dake gabansa,bai tsaya ba sai daya kai qarshensa sannan ya tsaya akai,yana sake qarewa wajen kallo.
Ƙarqashin wata bishiya take,dake tsakankanin duwatsun dake kusa da ruwan,ta duqufa sosai kan abinda takeyi,wanda lokaci bayan lokaci takan dakata kadan sannan taci gaba.
Tsai yayi yana kallonta,daga inda yake yana iya hango abinda takeyi cikin takardar,zane ne,zanen kuma na gida,cikin mamaki yake bin hannuwanta da kallo,yadda take sarrafa alqalamin a hannunta saika dauka taje makaranta ne,kowanne lokaci ita daya yake ganinta,bai taba ganinta tare da wata qawa ba
“Kattume!” Yaji an ambata,ya dauke idanunsa ya maida nahiyar da yaji ana kiran sunan,sunan da baisan ko na waye ba,saiya tuna a dazu yaji sunan a bakin yaran,take qwaqwalwarsa ta dawo masa da abinda yaga tanayi din
“Itace kattumen?,eh kamar sunan da yaji saurayin jiya dan ladi ya ambata kenan.
Lantana ce,riqe da abun diban ruwa a hannunta,fuskarta cike da fara’a ta qaraso inda kaltum ke zaune
“Ke kadai kattume anan?” Takardar hannun nata ya aje a qasa sosai,wanda hakan ya sake bashi damar ganin zanen fes.
“Na hadu dasu wasila ai suna fita,tace kina ciki kina aikin banzan da kika saba” duban lantana tayi tana qoqarin zama gefan kattumen,idanuwanta kan zanen kaltum din
“Kai…..wannan gida yayi kyau,wannan aiki naki kattume dama ana iya yin kudi dashi” maganar ta sanya kaltum murmushin daya bayyanar da jerarrun haqoranta masu sheqi
“Anayin kudi inji nasuru,ya bani labari,yace idan mukayi aure,zai kaini inyi karatu akansa” Dariya lantana ta saki harda tafa hannu
“Kai kattume,anya ba raha yake miki ba,ko kuka tsokana?,banda haka ina ake karatun zane zane?,a rasa wanne karatu za’ayi saina zane?” Cewar lantana,qaramar dariya kaltum ta saki tana dauke zanenta daga qasa,gami da lanqwasa takardarta
“Haka yacemin dai”
“To Allah ya tabbatar da alheri”ta fada tana tashi tsaye
“Bari na qarasa na diba ruwan nan,bayye tana can tana jirana”
“Debo saimu koma ciki tare,nima na dade anan din” can cikin ranta haka kawai taji batason komawa gidan,kamar tayita zamanta anan waien.
“Yayi wajen yallabai?” Hannafi daya biyo bayansa ya fada,saiya sauke ajiyar zuciya yana waiwayawa bayansa,gami da soma sauka daga sakan dutsen,ya cimma umar a hanya
“Kuje ayi ciniki ka biyasu,ayi musu biya mai kyau tunda marayu ne” cewar samir yana barin wajen
“Yes sir” umar din ya amsa masa.
A hankali take takowa cikin gidan nasu,tana kuma kasa kunne ko zata ji wani motsi da yayi kama dana babansu.
Abu taji ta bangaza,ta bugu sosai kamar tayi karo da bishiya,sai taja baya da sauri
“Kaiiiiiii” taji an ambata cikin wata murya mai kama da sautin mutumin da bacci me nauyi yake dibansa,abinda ya sanyata hanzarin daga kanta cikin matsananciyar faduwar gaba,tana fata ba abinda zuciyarta ke gaya mata ba haka bane,hasashe nw kawai.
Auwalu ne,yaron kawu iliya,dan inna laure na farko,yayan asiya,cikin tsoro tsoro take qare masa kallo sanda yaja baya shima yana kallonta tun daga yatsan qafa zuwa fuskarta,yatsunsa biyu saman lebbansa da suka rine zuwa kalar baqi yana zagayasu dasu.
Saman kansa idanunta suka fara kaiwa,yana dauke da wani irin aski da bata taba ganin kalarsa ba kaf fadin karkararsu,duk da cewa a hakan kansa akwai aski,saidai sam ba za’a kira askin da sunan aski ba,don gefe da gefan kan nasa ne kawai a saisaye,daga tsakiya kuwa uwar suma ce,wadda tafi kama da tudun kabari,tayi wani cibiri cibiri da ita,kai kace kamawa akayi aka murmurdeta.
Idan ka sauko ga idanuwansa kuwa gaba daya sun qara qanqancewa sun canza kala,kamar yadda yatsun hannunsa zuwa haqoransa da labbansa suka canza ainihin kalarsu zuwa wasu kaloli na daban,ko ba’a gaya maka ba,kana masa kallon farko kasan bleaching yakeyi,kamar yadda shaye shaye ya hudashi a ganin farko,duk da cewa dama can auwalun kafin barinsa qauyen yana taba shan taba sigari,boyewar da inna lauren da kawu keta qoqarin yi duka a banza,saboda yanzun kiwon mutum ake bana dabba ba,kome kayi idanun jama’a yana kai,kana tunanin cewa ka boye musu ne,yayin da su din suke kallonka tamkar tsirara,wannan shi ake kira da baya babu zani.
Wani kallon qurilla yake mata,kallon data dinga jin kamar ana bugun zuciyarta da dutse ne,tana tuna wani abu daya taba faruwa tsakaninta dashi shekarun baya kafin barinsa garin zuwa kudu neman kudi,abinda ya sanya ta cure jikinta waje guda,ta kuma yi taku uku baya da sauri,dai dai sanda taji ya saki wata dariya da tayi kama data ‘yan daba,cikin muryar ‘yan shaye shaye ya sake cewa
“Kaiiiiiiiiii……haka yarinyar nan ta girma?,lallai na dawo a dai dai” maganar data sanyata juyawa da hanzari,ta kuma nufi sashensu cikin gudu gudu sauri sauri cikin wani irin fargaba da faduwar gaba,so take ta isa ga ummansu taji shin da gaske auwalu dawowa yayi gida ko kuwa?……….
D/Z
19
*_Littafin kudi ne,kiji tsoron Allah kada ki mana sharing dinsa din gudun shiga haqqin mutane,ki biya naki ta nan ki karanta cikin aminci_*
08184017082
Ko kuma
09134848107
Follow us on Wattpad @
*ZAFAFABIYAR*
*INSTAGRAM*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*FACEBOOK*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*TELEGRAM*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
___________