Sponsored Links
Hausa NovelsUncle Datti Hausa Novel

Uncle Datti 3-4

Sponsored Links

Page 3 and 4

Ba shi ya iso gida ba sai wajen karfe takwas da rabi na dare cuz of go slow din da yaci karo dashi a hanya.
Ko da ya iso ya tarar Nana a kan kujerar three seaters tana sharar barci sanye take da riga da gajeriyar wando wanda bai gama rude kanta ba, tsayawa yayi for some few seconds yana kallon ta murmushi ne ya d’an sub’uce mishi” lallai Nana sarkin kiriniya ji yanda take ta sharara barcin ta hankali kwance”, bin kayan jikin ta yayi da kallon sai yaga ta bala’in yi mishi kyau domin kuwa shekarun Nana bai hana bayyana kyaun surar ta ba, yanda jikin ta ya murje yayi b’ulb’ul zaka d’auka kamar ta yaran larabawa d’innan ne. Tsintar kanshi yayi da nufar wajen ta ya tsugunna dafff kunnen ta ya hura mata iskaaaa”, cikin barcin ta taji, ta d’an yi mik’a kamar zata rashi sai ta gyara kwanciya ta koma ta kwanta.
” Cije libs d’in shi yayi a hankali ya kuma kafe ta da ido, komai na Nana daban ne tana da kyau da kan diri, a hankali ya sa hannu biyu ya kinkime ta ya soma tafiya da ita, yayin da ya maida jakan shi da ya shigo da ita d’aya hannun nashi.
D’akin shi ya nufa ya dire ta a kan bed d’in shi kana ya lek’a d’akin Aina ya tarar da ita kan Sallaya ta idar da sallah kenan tana lazimi.
Zama yayi a kan tafkeken bed d’in ta ya jawo pillow ya kishingid’a yana jiran ta har ta idar ta ninke sallayar ta ajiye tare da zare hijabinta shima ta tana ninkewa lokaci guda tai murmushi tana kallon Datti” barka da dawowa mijina”, da murya mai zakin gaske ta fad’a.
Amsa mata yayi shima cikin murmushi kana ya d’an turbune fuska da tsigar wasa yace” shine kika bar min baby angel d’ina a parlour ita kad’ai ko? Wife mun kusa mu bata fa”,.
Ohhhhh damn it!!!!!!!!, na manta Nana batayi sallah ba take barci sai yanzu na tuno ma, mai baby angel tare muke da ita nima sallah ne ya shigo dani amma bari na tada ta”.
Kafin ya bud’e baki yayi magana tuni tayi hanyar parlour ko da ta iso bata tarar da kowa ba ta lek’e bayan kujera nan ma babu ita babu alamar ta, nan idanuwan ta suka cicciko kamar zata yi kuka? Ina Nana ta yi da daren nan ita da ta barta tana barci? Tsoro ne ya d’an kamata a lokacin da wani tunani ya fad’o mata ta safe kirji tare da waro ido waje” na shiga uku kar dai shigowa gidan nan akayi aka tafi da Nana”?
Kuka ta fashe da shi da gudu tayi d’akin ta ta tarar da Datti a inda ta barshi yana ganin yanayin da ta shigo a firgice yace lafiya kika shigo haka? Me ya faru? Banda kuka babu abunda take yi da kyau ta iya bud’e baki tace” banga Nana ba?”
“Kamar yaya baki ga Nana ba? Ya jefa mata tambaya fuskar shi na bayyana mamaki.
Wallahi na duba kafff parlourn nan babu Nana babu alamar ta, nafi kyautata zaton satota akayi”.
Sai yanzu ya fahimci inda ta dosa bai san sanda dariya ya subuce mishi ba har sai da ya kular da ita tace” wato baka damu da b’atan baby angel d’in da kake ikirarin taka ce ba shine ma na zama abin dariya?, ta kuma rushewa da kuka tana tunanin halin da y’ar k’anwar take ciki”.
Ganin abun nata dad’a k’aruwa yake yi gashi ko kad’an bai son jin kukan mace balle na wacce take da muhimmaci a rayuwar shi, wacce babu abunda zai iya saka mata da shi sai addu’a domin irin guduwar da ta bayar a rayuwar shi, ba shiri ya had’iye dariyar shi, cikin rad’a yace” yi shiru daina kukan haka matata idan ba su kike ki saka nima na taya ki ba, guess what? baby angel na d’akina tana barci.
Kuka mai d’auke da hawaye ne ya makale mata lokaci guda tace” Dan Allah? da gaske? ya d’aga mata kai alamar “eehh”
Zolayar ta yayi yana cewa” Ashe Ainata ma ta damu da baby angel d’ina amma tafi ganin ganin ina son baby angel fiye da kowa.
Kin san dalilin da yasa nake son Nana?
Ta girgiza mishi kai tare da yin kasa da kan ta tana murmushi kasa-kasa, ” sabo da wife d’ina tana sonta bayan haka jinin mu ce ma’ana soyayyar Nana a jinin mu yake”.
A tare suka kwashe da dariya daga nan suka d’unguma parlour ta serving d’in shi da abinci dan d’asu suka ci nasu da Nana suna ci suna hira har ya gama daga nan suka nufi d’aki suka shirya tsafffff suka kwanta tare da bama juna baya wanda ya kasance kamar al’adan su ne.
Tana jin Datti na ta sharara barci yana minshari, wannan wace irin bak’in kaddara ne? Anya zata iya cinye jarabawar da Allah ya rubuto mata kuwa? Wai ace aure kusan wata uku kenan su kwana ta tare su tashi tare babu abunda ke shiga tsakanin su?
Anya su Ummi sunyi mata adalci kuwa? Kaiiiiiii!!!!! Allah kana ji kuma kana gani……….., Allah kasa tsare min mutunci na kar biyayyar da nayi ma mahaifana na auren mijin da marar bukata wanda ko kad’an mace bata gaban shi ya yi silan jefa ni ga hallaka………, ka kare ni da mata masu irin matsalata daga sharin son zuci…………, tana kayo nan wani tsiririn hawaye masu d’umi wanda zafi da rad’ad’in kamar ana narka d’alma ne suka suma bin kyakkyawar round kuncin ta d’aya baya d’aya.

WAIWAYE ADON TAFIYA

Aina’u Muhammad Kabeer Danbaba da Nana Halima uwar su d’aya uban su d’aya kuma mahaifan su duk suna raye. Mahaifiyar su mutuniyar Katsina ce haififfiyar garin mamaga ce da ke karamar hukumar Jibia.
Mahaifin su Kuma Alhaji Abubakar haffaffen garin Bauchi ne su uku ne a wajen mahaifan su rak, yana da wa sunan shi Alhaji Isma’il wato mahaifin Datti da kuma autar su Hajiya k’arama usulin sunan ta Halima wato Nana sunan ta taci cikin su ita ce bata tab’a haihuwa ba”.
Datti wanda asalin sunan shi Muhammad wato shima sunan mahaifin Nana aka saka mishi, su hud’u ne a wajen mahaifan su, shine babba a wajen iyayen su, sai Ilham yayi aure a nan Bauchi take da zama a unguwar Federal low coast, sai Fu’ad wanda yannzu yaka yake zangon k’arshe a makarantar jami’a da ke Bauchi wato ABUBAKAR TAFAWA BALEWA UNIVERSITY, bayan haihuwar shi mahaifinyar su bata kuma samun ciki ba sai da Fu’ad ya kai shekaru goma sha d’aya kafin nan aka haifo Mardiya wace zasu yi sa’a da Nana”.
Sunan mahaifiyar su Datti Maryam ne amma ana k’iran ta da “umma” ita kuma mahaifiyar su Aina sunan ta Murja ana k’iran ta da “Ummi”.

Mahaifin su Alhaji abubakar wato Kabeer D’anbaba da kuma mahaifiyar su Sa’adatu wanda akafi dani da tsohuwa duk suna da ransu, kasancewar family d’in Kansu a had’e yake yasa suke zama a family house d’in su dan su kara dankon zumunci amma y’ay’an su kuma suka amince su zauna a duk unguwannin da suke so”.
Marsala ta farko da Datti ya fara fuskanta shine; so tari idan yana tare da friends d’in shi yana yawan jin labarin cewa duk namijin da balaga ya kamashi yana wet deals da dai sauran su, abunda yafi d’aure mishi kai tunda yake bai tab’a jin feelings, ko tayi wet dream ba, hasali ma mace bata gaban shi kuma bai d’auketa amatsayin komai ba.
Wannan marsala tun yana d’aukan shi k’arami har ta kai ta kawo ya girmama yafi k’arfin tunanin shi ya fara tunanin ko aljana ce ta aure shi, wannan dalilin ne ya saka har ya kawo munzalin aure bai tab’a yin budurwa ba, a gida anti anyi ya nemo mata a had’asu aure tun yana boye musu har ya yanke hukuncin Samar da iyayen shi halin da yake ciki game da mata.
Hankalin su ya matuk’ar tashi sosai da suka ji labarin babu kalar maganin da basu nemo ba da na gargajiya da na bahaushe duk sun nema amma shiru, gashi a lokacin yana aiki a asubiti suna gudun kar mutane su mishi mummunan fahimci kun san zaman namiji da kud’i babu mata ana d’auka fasiki ne, da wannan tunanin baban Aina ya yanke hukuncin nema mishi auren Aina a wajen baban shi tare da goyon bayan matar shi domin kare mishi kima da darajar a idon duniya.
Da farko mahaifin Datti bai nuna goyon bayan shi ba a cewan shi za’a cutar da yarinya ne a nakasa mata rayuwa daga k’arshe ya hakura ba dan komai ba sai dan su tsohuwa sun nutsar da shi a cewan su idan ba jinin shi ba wa zata amince ta zauna da namiji irin shi?
A haka har aka d’aura auren ya rok’a a bar mishi Nana wacce tun haihuwar ta taji yana son yarinyar sosai tamkar cikin su d’aya da ita.

************************************

CIGABAN LABARI

Rik’e yake da waya a hannun shi ya shafe kusan dakika biyar sai kai komo yake a d’akin shi kad’ai jefi-jefi yana cizon yatsa. Ba komai ne yake damun shi ba illa sanin kanshi ne tunda yake wato tun da ya fara falin balagan shi har zuwa yanzu dai-dai da kwana d’aya bai tab’a jin sha’awar mace ba, lokuta da dama idan suna hira da friends d’in shi har mamakin su yake wai idan suna kallon blue film suna jik’ewa amma gashi yau kusan goma kenan ya downloading yana kallo amma ko gizau bai ji ba.
Tsaki mai karfi ya sake tare da yin wurgi da wayan a kan gado ya d’au car key din shi ya bar gidan a gaggauce ya wuce chamber d’in su, a gefen wani garden ya tsaya yayi parking ya fito tare da yin ma mortar key, ya tarar da friends d’in shi su uku suna hirar su cikin raha, ko sallama bai yi ba ya nemo kujera ya zauna suna ganin su suka mik’a mishi hannu suna cewa” man yane ka shigo ba ko sallama”.
Tsaki ya kuma ja cike da takaici yana kallon su d’aya bayan d’aya” walle guys baza ku gane bane, kunsan ma me, na fi minti arba’in ina kallon blue film d’in nan amma ba wani feelings d’in da nake ji, kai like ma normal film d’in da babu romantic scene haka nake ji”.
“Whatttttt don’t say this please! cewar wani kenan wanda ake k’ira da Yusuf ya fad’a da mugun mamaki.
” haba man kar ka raina mana hankali mana, kana namiji ace ka kalli bf kace baka ji feelings ba? ko yaron da he is not well matured idan ya kalli bf dolle sai ya d’an ji canji a jikin shi balle kai da kake da mata? We taught duk wannan matsalar ya k’are a sanda aka maka aure ka gane ko so stop all this jokes we are no more kids”.
Sassauta murya yayi kamar zai fashe da kuka yace” wallahi billahil azim Yusuf da gaske nake Allah babu abunda ya janja har yanzu”.
A take suka tsura mishi ido da mugun mamaki, tunda suke basu tab’a cin karo da mai matsala irin na Datti ba, ba dan sun san halin shi baya karya ba da tuni sun karyata shi.
Can Usman ya nisa yace” tabbb inko haka ne ta yiwu ko haihuwar ka akayi da matsalar ko kuma matsalar jinnu ne?”
“No Usman bana tunanin hakan”. Fahad yayi saurin dakatar da shi, a iya tunanina may be process na maturity d’in shi ne ya zo da hakan it might be zuwa d’an wasu lokutan al’amuran zasu dai-daita.
To Allah yasa abokaina amma wannan matsalar babba ne ace kana namiji abu baka jin sha’awa, gayu akwai fa matsala fa”.
Haka ne amma da yardar Allah babu komai”, ya fad’a.
“Ni wallahi matar ka ce ta bani tausayi wallahi, duniya babu macen da zata amince a aura mata miji mai irin matsalar ka, say tari ma hakan ya kan yi silar kashe aure na sha jin labarin cewa mata da yawa sun halaka da irin wannan matsalar auren domin duk hak’urin mutum jiki da jini, ” Yusuf ya fad’a lokaci guda yana kakkab’e jikin shi yace” ku taso muje…………..
Mik’ewa suka yi su hud’u suka shiga mota ba su suka wuce ko ina ba sai club suka zazzauna suna chilling, kwalbar bear ne a jjjjugaban su suna sipping a hankali fahad, Usman da Yusuf suka mik’e suna ta rawa da yammata shi kuma Datti yana zaune a wuri d’aya yana kallon kywawawan samari da yammatan da ke wurin, ga mata iya mata wanda suka amsa sunan mata amma duk ba su ishe shi kallo ba, hasali ma bai ga dalilin da ya saka suka tsaya suna b’ata lokacin su akan mata ba shi ko kad’an bai d’auki jinsin mace a bakin komai ba, he is friendly to them amma kwata-kwata baya jin feelings balle ma mu’amala ya shiga tsakanin shi da mace.
Har ga Allah ba yana iya bakin k’ok’arin shi wajen tilas ta ma kanshi ko zai ji sha’awar Aina amma har ila yau baya jin komai game da ita, kuma yana sane da irin kawaicin da take nuna mishi a zaman su na aure, bata tab’a nuna ta kosa da shi, kuma bata tab’a neman shi da nufin kwanciyar aure ba shi yasa yake ganin kimar ta da darajar ta.
So tari yana tsananin tausaya mata da irin tauye mata hakkin da yake yi wanda shi kanshi ya sani halittane yanda bazai iya canja shi ba, da yana da wata dabara da zai biya mata bukata da tuni yayi, sometimes yana trying best d’in shi ya romancing d’inta amma duk da haka tamkar itace yake baya iya tab’uka mata komai, babu kalan romantic novels, blue films, din da bai nemo ba duk dan ya taimaka mishi wajen biyan bukatun shi amma abu yaci turaaa…., daga k’arshe ya rungumi k’addara ya zuba ma Allah idoooo.
What’s up guy!!!! cewar Usman kenan dan ya ga tund’asu yake zaune shi kad’ai.
Mtswwwwe ya ja tsaki lokaci guda yana lallon wrist watch d’in shi, saurin mik’ewa yayi yace” i need to get going guy”.
Why!!!!! Cike da damuwa Usman yayi maganar yana kallon Datti”.
“Nothing, kawai dai i can’t keep waisting my time ne a nan wajen, i see no reason da zan tsaya ina kallon abunda ma ba burgeni yake ba illa ma haushi da yake ban”.
Alrght, bye then zan fad’a ma guys d’in cewa ka wuce.
Owkkkkkkk yana fad’a ya bar wajen, gida ya nufa ya tarar da baby angel a kwance a kan cinyar Aina tana tsefe mata k’itso zata wanke mata kai, sallamar shi suka ji Aina tayi saurin sakin kan Nana a tare suka mik’e suka fad’a jikin shi suna dariya ya maida hannun ya had’e su waje d’aya kana Aina tayi saurin raba jikin ta da nashi tayi d’akin shi da sauri tana had’a mishi ruwan wanka.
D’ago da Nana sama yayi yana wasa da ita suna dariya sai ma ya ji moment d’in nan ma yafi mishi ganin matan da yayi a waje wanda yake d’auka marar amfani har Aina ta shigo ta tarar da su a hakan tace” dear d’ina wai baka gajiya da yarinyar nan ne? Shiga goma fita goma baby angel ni dai karta gajiyan min da kai.
Saurin sakin Nana yayi tare da mik’a mata tsarabar ta tayi d’aki tana tsalle kana ya yi wajen Aina ya lakaci hancinta da hannun d’aya yana murmushi wanda ya bayyana dimple d’in shi yace” Mrs complainer an bar miki mijin ki d’in what next”? ya d’aga mata gira.
“Take your bath”, cikin muryar shagwab’a sai ya tsaya yana kallon ta.
Me kake kallo bae?
Shagwab’ar ki ce ta burgeni?
How i wish i will have feelings for you da na gwada miki tsantsar soyayya, forgive me wife, ki yafe min na san na gaza ta wajen biya miki bukatan ki, saurin rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tayi, Aina………., ya k’ira sunan ta da daskararriyar murya tayi saurin cire hannun daga fuskar ta tana kallon shi”.
Ba laifi na bane da na zama rago a gare ki”………,
Ba laifina bane da na kasa cika miki mara da ruwa wallahi Aina da da hali da nayi ko zan samu sassauci a zuciya ta domin kuwa zuciyata cike take da tausayin ki da ni kaina”………
Tunda ya fara maganar kwalla ya soma zubo mata ya rungumo ta yana lallashin ta tare da fiddo da hanky yana goge mata a kunne kuma yana binta da tattausan lafazi har sai da ya tabbata ya saka ta dariya kafin nan yace mata ta taya shi wanka, ta waro ido tace” babbar magana!!!!! Ina zata iya cud’a datti sallon taje tayi gane-gene? Duk abunda take fad’a a kasan zuciyar ta ne.

Nace :lol kika sani ko daga nan ya wulla da ke duniyar dad’i? Abunda kike mafarkin samu ne fa.

Kamar ya gano ta ya d’an ja kunnen ta da k’arfi har sai da ta saki ihu a hankali mai d’auke da kissa da kisissina tace” ouch kunnena zafi!!! Zafi dear “.
” Saurin sakin ta yayi da sauri yayi hanyar d’akin shi kana ya juyo ya kashe mata ido d’aya yace” that’s your punishment for disobeying your husband, next time idan kika bijirema umurnina it will be more worsen than this”.
Ta marairace fuska kamar zata yi kuka ya kuma mata gwalo ya haura zaman bene da gudu yana waiwayowa yana mata gwalo.
Tana ganin ya tafi tayi d’an murmushi a ranta tace” Matar Datti kenan, zaman gidan Datti gwanin birgewa sannan kuma gwanin kunci, ba dan matsalar shi ba da zata iya cewa tafi kowa sa’an miji”.
Cije lab’an ta tayi na kasa ta bi bayan shi itama tana shiga ta tarar yana bathroom, direct wardrobe d’in shi ta nufa ta nemo mishi dogon wando da shirt baka ta d’ora zaman bed d’in shi, bata tsaya b’ata lokaci wajen nemo tuarare ba cuz shi kanshi kayan baya bukatan turare, cuz like b’arin turare akayi a jikin kayan saboda dukan su ma’abota tsafta ne shi yasa a kullum k’amshi kama jikin kayan su yake yi”.
Shelve d’inshi ta nufa ta d’auko novel tayi rigingine a kan gadon shi tana karantawa cikin nisad’i cuz story d’in ya d’auke mata hankali matuk’a haka kawai take jin shauki na kamata”.
Some parts na labarin dariya yake bata tayi ta tuntsirewa da dariya wasu kuma ya bata haushi, idan aka zo wajen tausayi tayi ta Jan majina da kyar tana kokarin hana hawaye zubo mata jim kad’an sai gashi ya shigo kugun shi d’aure da towel yana rik’o hand towel yana tsane ruwan jikin shi, kallon ta yayi yace” seams like u are carried away?”
Ta juyo tana fad’in” yeah”, it’s very interested”.
Mikewa tayi a hankali taje kan shelve d’in ta ajiye novel d’in a wajen da ta d’auko, ta d’auko kayan da zai saka tayi wajen shi a lokacin har ya gama yana shafa mai.
Sai da ta jira ya gama ta mik’a mishi ya k’arb’a yana mai zuba mata albarka tayi murmushi ta koma main parlour ta bashi wuri ya saka kayan.
Tarar da Nana tayi da Teddy d’in ta tana wasa tace zo nan na k’arasa miki tsifan, ba shiri Nana tayi wajen ta da sauri ta hau tsefe mata kan.
Da yake kad’an ya rage su gama hakan ya saka basu wani b’ata lokaci ba suka gama daga nan ta jata zuwa wajen da suka tanadar domin wanke kai ta wanke mata tsaffff da shamboo ta had’a da anti-dandruff tana gamawa ta hau drying mata kai da hand dryer.
Fitowan Datti kenan ya tarar babu kowa a parlour kamar zai yi d’akin Aina sai kuma ya fasa ko mai ya tuna ya nufi saloon d’in nan ya tarar da har Aina ta gama drying ma Nana suma tana tufke mata da baby pink na ribbon.
Babu abunda kan Nana ke yi idan banda k’anshin tsadaddun mayuka da kuma turare na kai, ga wani irin sexy shinning d’in da suman ke yi.
Waya ya fiddo a ya hau musu video yana tsokanar Aina wai zata kyau da aiki a saloon ji yanda ta dad’a hasko mishi baby angel d’in shi.
Dariya ta hau tace” na ga wacce zata k’ara tab’a kan Nana da sunan wanke kai tunda abun ya zama da tsokana”.
A wajen ne yake fad’a musu su shirya ya kaisu family house, sunyi murna sosai da d’oki har rige-rige suke tsakanin Aina da Nana shi kan me zaiyi in banda dariya har suka fito suka nufi hanyar fita a tare suka shige mota sai gida.

Ko da suka iso d’akin tsohuwa suka fara nufa suka tarar da Alhaji Abubakar(baba Karami) da wan shi( baba babba) suna hira da mahaifiyar su cikin shauk’i da jin dad’i.
Sallama suka yi suka shigo ko da tsohuwa ta gansu da sauri ta mik’e ta tare Nana tace” oyoyo jikalleta ta”, Aina tace” matsa ni kam tsohuwa na gaida iyayena kin tare min waje, Nana kad’ai kika gani a nan?, ta fad’a da tsigar wasa tab’a botsarewa.
“Iyeeeee ka ji min ja’ira kikayi wasa iyayen naki na naha su amsa gaisuwar taki naga ta fad’in k?”
Dariya Aina tayi” haba aminiyar ai bama haka da ke”.
Gara dai……., ta ja kwafaaa su duka suka saka da dariya banda Nana da tayi jikin baba babba ta fad’a tana cewa” oyoyooo babana.
Bayan duk sun shigo suka zazzauna, Datti da Aina suna zaune a kasa yayin da har ila yanzu Nana ke jikin baba Karami yana mata wasa yana cewa wai bata san ta fara girma bane?

eedatou…….

SHINNING STARS WRITER’S ASSOCIATION*

”’The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.”’

https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45

🍇🍇🍇 *UNCLE DATTI*🍇🍇🍇.
JIKINA YAKE SO!

©
*eedatou✍🏻*
”’Follow and ✅ote me on Wattpad”’: *eedatou*

Masoya littafin Uncle Datti jikina take so bana ganin comments and votes d’inku shi yasa jikina yake mutuwa da yin typing Allah had na canja littafin na fara typing wani sabo sako muku ne kawai banyi ba. Ku daure ku dinga karfafa min gwiwa tunanina ya fara karkata na daina typing littafin UNCLE DATTI JIKINA YAKE SO.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button