KyalKyalin Kauna 82
8/11, 12:17 PM] SAFIYYA: Yan press da Baba gani agaban gate na headquarter nasu saida yay mamaki da kyar polisawa suka kadasu aka budemai hanya yawuce yashiga ciki yana parking yasauko sai kallonshi ake yawuce building naG direct zuwa office nashi kafin ma yay knocking secretary yace “yace kashiga idan kazo”
13:58
bude kofa Baba yayi yashiga ciki zaune yaga IG kan kujera ya lumshe idanunshi yana karkada kafa jin anbude kofa vasa yabude idanunshi dasauri ganin Baba vasa yamike tsaye dasauri yadauki wayanshi ya danna wani video yajuyo da screen na wayan yana nunama Baba yace “what in God’s name is this CP?”
13:59
Kallon video Baba yay kafin ya lumshe idanu yabudesu yakasa magana cikin fada sosai IG vace “ni dinan sama da kowa nasan laifin da yaron nan yamaka
Ibrahim amman turaka nayi nace kamai wannan dukan kokai arresting nashi?
Kakosan mekama kanka CP? Kasan yanda this video went viral now now online kuwa just how many hours da faruwan abun, abinda yafaru around
7:30 this is just 12 a rana, mutane har any lunching campaign a online hashtag #justice for Pablo! #justice for Pablo!kasan yanda video nan ke trending online kana abusing yaron nan kuwa what is this Ibrahim”? Kozakamai wani abu idanun mutane bazaisa ka danne zucivan ka ba look at abinda kama kanka, what is this
3 Ibrahim?” Shiru Baba yay batare dayay magana ba zucivanshi na tafarfasa. Ahankali IG yace “kaga uban press dake waie kuwa”? Nan ma still shiru Baba yayi baice komiba, dan ijiyan zuciya IG yasauke yakoma yazauna yace “taurin kanka CP yana sani in a very very tight spot you have no idea yanzun nan daga faruwan abun nan kawowa yanzu how many calls na amsa sabida kai, kasan irin rokon danayi kada ayi suspending naka daga aiki kuwa ina explaining gravity laifin da yaron yamaka na auren diyar ka?” ahankali Baba yasa hannu yakarbi envelope din yashiga budewa IG na kallonshi yace “FG tayi suspending naka from this case!” Dawani irin sauri Baba yakalli IG, IG yamai nodding kai yace “anyi assigning new officer to the case, dan haka kabama new officer all the files da evidence kakedashi akan Pablo, you are too attached to this case hakan will affect judgement naka, emotional decisions zaka dinga dauka, an bama Obama case din” vanda Baba ke kallon IG saika tausayamai he’s so hurt filled with anger, sosai IG yaji Baba yabashi tausayi he understands abinda Baba yayi but duniya batai understanding abinda Baba yayi ba, daman an tsani police vanzu haka suke trending online kan dama haka police ke molesting mutane, people are not even looking at the fact shi yaron nan in question wato Pablo Escobar is a drug dealer yay kidnapping yaran mutumin nan sannan yazo a aure daya aboye no kallon kawai dukan da CP yama yaron suke da gindin bindiga ana justice for Pablo, just 1 mistake a Baba yaboye asalin laifin Pablo daga idanun duniya, laifin Baba just one yabama = Pablo millions of fans in just how many hours now all eyes are on this case. livan zuciva IG vasauke kafin vamike tsaye yazagayo yazo inda Baba yake a tsaye yaja kujera ya zaunar da Baba shima ya zauna yana facing nashi cike da lallashi yace “Ibrahim kaima kasan yanda nake sonka and want the best thing for u always, FG sun dage suspending naka zasuyi daga aiki gaba daya dan kaja ana dragging mu da nigeria gabaki daya a internet har international organization kiranmu suke kan is that how we handle criminal cases, ur video beating yaron nan up
£3
da bindiga da belt is trending on twitter, kai globally ma infact, kaga kalan dukan dakama yaron nan kuwa?
Is too much Ibrahim, yanzu haka an wuce dashi police clinic pray nothing happens to him dan idan wani abu yasameshi bansan tayaya zanyi backing naka up ba kuma wth, you are too emotional da case din nan, abin is personal for you which I understand, saisa da aka bani wannan offer na karba da gudu gwara wani yay handling case din not you Ibrahim, za’a karbama Yasmeen hakkinta and Pablo would be dealt with but according to constitutional law, kagane dukan dakamai was too bad for you and for our entire organization and the nation at large, kai koda ace kisan kai yake we police bamu da right dazamu mai irin dukan nan dakamai, criminals nada rights fa so let the law take its course, beside ma duniya gabaki daya taga vanda Yasmeen love and care about him!” Dawani irin sauri azucive Baba vace
“bata sonshi!” Shiru IG yay yana kallon Baba yay folding hannu akirji, cikin fushi sosai
Baba yace “bata sonshi hauka ne kawai take dakuma tausayi taga yanda na zaneshi, mene Yasmeen tasani kan soyayya she’s just 20yrs going to 21 yanzu, koma idan tanada feelings for him believe me infatuation ne bawai asalin so ba, en, ene, emmmm
Stockholm syndrome ke damunta yallabai, condition a victims keson kidnapper shi, so nawa muna ganin irin case haka anan, y’ata can never love someone like that believe me, batasan metakeyiba” ljiyan zuciya IG yasauke yakai hannu yadafa Baba yace “I understand, yanzu dai I don’t want you to create any trouble again, dazaran yaron ya farfado yasami lafiya we will charge him to court daganan namaka alkawari zanyi tsayin daka a case din nan prison direct I will make sure anyi sentencing nashi to prison he will rot ? there for life, yanzu katashi ka koma gida kai wanka and sort things out, u can even take the day off idan Pablo ya farka u will know but u are not allowed to interrogate him idanma kanaso kayi zakaje ka roki Obama dan all eyes are on u, go and relax handle Yasmeen and calm her down kaida family ka ku tattauna dan babban abu ne yasameku
Allah ya kyauta kawai, tashi kaje”. Tashi Baba vayi rikeda envelope din yajuya zai fita IG yace “zan aika more men ana gadin gidanka dan nasan mutanen Pablo are still out there” gyadamai kai Baba yay yabude kofa kawai yafita ko kadan baiji dadin abinda akamai ba kaman yay ihu yakeji yana fitowa tsayawa yay yana kallon building na asibitinsu inda nan Pablo yake sannan yajuya fuuuu yawuce wajen motanshi yashiga yaja yabar wajen babu abinda zai bama Obaman ya nema dakanshi.
[8/12, 7:50 PM] SAFIYYA: Kaman ba Baba aka kira ba chakume wuyan rigan Maheer yayi azuciye yace
“nikake gayama love ne? Kai kana ganin idan kafi karfina kabi yanda kabi ka auri y’ata kabata rayuwanta ka wulakantata Allah zai barka ne? Barakaji Pablo ba love ba ko lobayya ne billahillazi kaida y’ata har abada, bazata kara kara ganin kaba har abada kuma indai nine na haifi Fateema ubanta ne ni zata manta dakai namaka alkawarin nan, kuma kaje zaka gani zakas…..” “CP Ibrahim” Obama yakira Baba da kakkausan murya yana kama hannunshi hakan yasa Baba yasaki Maheer dayashake sosai cikeda masifa yace “wat Obama idan yarka wannan criminal din ya aura how will you feel? Don’t tell me rubbish please” Baba yature Obama azuciye yawuce yafita, Obama yaduba wuyan Maheer daya shaku sosai adan hankali yace
“are you okay kona kira maka Dr”?
Batare da Maheer yakalleshi ba magana ciki ciki yace “am fine thanks” cikin fushi Ahmad yace “yallabai idan wani abu yasami client dina I will sue you and sue the entire Police organization, and I will surely document this incident danai
witnessing da idanuna nabada a court” anatse Obama yace “calm down hakan bazai kara faruwa ba” yakalli ogogo yace “is time kaima zaka iya tafiya” azuciye Ahmad yakalli Maheer yace “| will see you tomorrow okay” gyadamai kai kawai Maheer yayi ya lumshe idanu suka wuce suka fita, babu abinda ke ranshi dake damunshi irin Yasmeen, all abubuwan nan bashine ke gabanshi ba Yasmeen ce agabanshi, yasan bataci abinci ba, he knows tanachan tana kuka, he knows tanachan she’s sad extremely sad ma tana tunanin halin dayake ciki, ilyan zuciya yasauke zuciyanshi na bugawa
ahankali. Washegari!
Wuraren 10 yan sanda suka shigo dakin Maheer na sanye dawani riga da wando sababbi wanda Obama yakawomai yau da safe bayan yay wanka yay salla da kayan jikinshi sun babbaci da jini Obama yashigo yace
“it’s time for court Pablo” karasowa gaban gadon yayi ya bude Pablo yace
“kyakkyawan yaro irinka gaka very young just 32yrs, gaka so educated bantaba tunanin zaka iya wasting rayuwanka a nonsense life din nan ba” sauka Maheer yayi yana jujjuya writs nashi dasukai tsami sabida ankwa aka kawo wani ankwa aka samai a hannu da kafa aka rirrikeshi aka fito dashi aka sashi abayan wata mota na daukan criminals yan sanda suka shishiga sannan motocin yan sanda kusan goma suka biyu biya abayansu biyar agabansu su atsakiyan kaman an dauko kasurgumin criminal din nan, har zuwa babban kotun birnin tarayya. Suna parking a kotu aka fito dashi yan jarida dayan news sunfi dari biyu daukanshi hoto ake ana kokarin tambayan shi amman polisawa basu bari ba aka wuce dashi cikin kotu suna shiga cikin kotun ga Ahmad, Hamad, Baba Makaho da Malah duk suna tsaitsaye Obama yabudemai hannu da kafa yace “zaka iya magana da Lawyer ka” aka yansanda biyar, hada idanu Maheer yayi da Hamad dahar idanunshi sun cika da kwalla dan hararanshi
Maheer yayi yace “waikai komi kesaka kuka” hararanshi Hamad yayi ya rungumeshi ahankali saikuma yadago yana dudduba ciwukanshi dan yatsine
fuska Maheer yayi yace “I’m fine, Baba” yarike Baba ahankali ya bubbuga kafadan Malah dan he’s even stronger than them katin ahankali Ahmad yace
“muje ciki” ciki suka shiga daidai alkali na zuwa, aka tashi duka ya zauna yabada izini azauna, wani yatashi yace “ayau daya ga wata za’ayi sharia kan Maheer Maheer wanda akafi sani da Pablo Escobar wanda ke harkan miyagun kwayoyi sannan, Commissioner na Police Ibrahim
Ibrahim yashigar da wata sabuwar kara akanshi kaman haka; kidanaping yaranshi guda uku, threatening diyarshi dakuma aureta dayayi yanzu na tsawon wata daya” dukowa Barr Ahmad yayi yakai bakinshi saitin kunnen Maheer yace “Maheer wannan karan da Baban yarinyar nan yashigar yabata komi I have to talk, daurin rai da rai ne ta wayanda aka kama da kidnapping an chanza hukuncin yanzu kisa ne” Girgizamai kai Maheer yayi yace “idan kai wata magana Ahmad zan cire ka amatsayin lawyer na I will represent myself” shiru Ahmad yayi yana kallon Maheer din dan at this point tsakanin shi da surukin nashi CP baisan wayafi wani taurin kai ba, kiran Maheer akayi to chamber hakan yasa yatashi ahankali ya yawuce wajen ya tsaya yana kallon Baba Baffa Ammi, Yaya da Baba karami dasuke zaune acikin kotun, hada idanu yayi da Ammi dake kallonshi kur kasa jure kallonta yayi yasauke kanshi akasa ahankali. Lawyer dake representing Baba ne yatashi yaje gaban Maheer yace
“dudda kariga kayi admitting kaine shahararren dan harkan miyagun kwayoyi wato drug dealer zanso kotu taji daga gareka kaine Pablo Escobarn
Africa Maheer?” Anatse looking damn compose and charismatic Maheer yace “nine” gyara zama Baba yakarayi, lawyer yace
“kaine kayi kidnapping yaran CP
ibrahim Ibrahim mata guda uku masu suna kaman haka; Fateema Ibrahim, Aisha Ibrahim, Khadija Ibrahim?” Ahankali Maheer yace “nine” Lawyer yace “kaine kuma kai blackmailing diyar CP tafarko Fatima kazo har gidan ubanta ka aureta, kukayi zaman kwana ashirin da takwas amatsayin ma’aurata?” Dan shiru Maheer yay! kafin chan yace “nine” baki Lawyer yabude zai kara wani tambayan Maheer yadagamai hannu yace “I’m guilty of all the charges kadaina wahalar da kanka nazo nan ne to get punished for my crimes bawai nai gardama da kowa ba” sosai Hamad ke kallon Maheer kaman yazo yarufeshi da duka, lawyer yay wani murmushin victory yace “in that case shikenan tambayoyin nawa” yaje gaban desk nashi yakawo all the evidence yaje yay submitting akali ya tambayi lawyer Maheer ko yanada abin da zaice ko yanada ja yace a’a akace yaje yazauna Maheer yakoma yazuba alkali yashiga rubuce rubuce kusan 15 min yabata reviewing everything sannan yay gyaran murya. “Bayan kotu ta saurari wannan shari’an takumayi nazari akai, kotu ta yaba da yanda Maheer Maheer bai wahalar da kotu ba yafadi gaskiya, ga hukuncin da kotu tayanke mal” alkali yay shiru yana gyara glasses na idanunshi yace “kotu ta yankewa Maheer Maheer zaman gidan yari na tsawon shekaru ashirin da biyar for laifinshi na saida miyagun kwayoyi dayakeyi, saikuma kotu ta yankemai hukuncin kisa abisa kamashi da akayi da laifin kidnapping, sannan kotu ta yankemai hukuncin biyan mahaifin yaran dayay kidnapping miliyan goma goma su uku bisa ga tsorata damuwa da kunci firgice da emotional stress dayasa yaran suka shiga, kotu tazo karshe” alkali shiga, kotu tazo karshe” alkali yabuga ganga, Hamad ya rungume Baba gamgam yasaka fuskanshi akirjin Baba hot tears na saukomai jin an yankema Maheer hukuncin kisa, Malah ma idanunshi sukai jazur zuciyanshi kaman zata fito, Baba yataso har zuwa gaban Maheer da ake sama ankwa a hannu za’a wuce dashi yakalleshi yay murmushi yace “only death shine abinda wanda ya wulakanta rayuwan diyata yay deserving, our case bai kare anan ba kajira sammacin sakin y’ata daga shari’a court!” Dawani kalan sauri Maheer yakalli Baba gabanshi yawani kalan mugun fadi dum!.