Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 43

Sponsored Links

โšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ
*BOOK 2*

*PAGE 43*

Bayan fitan su Hajiya kitchen Sultana ta shiga ta d’ibo dambun nama a cikin bowl ta kuma had’o da lemun exotic mai sanyi kafin ta dawo falo ta zauna ko takan su Meenal da Moon bata biba wad’anda suka kunshe kansu a cikin d’aki ko hirar uban me sukeyi bata da masaniya tun bayan shigowar su gidan,
Kuma har hajiya ta had’a gangamin gayyarta suka bar gidan su biyun basu da labarin abinda yake faruwa a cikin gidan,
Wayarta tayi connecting da speakers d’in dake girke a falon tayi playing wak’a kafin ta koma ta nemi waje takame bayan ta zauna ta d’auki k’afa ta d’aura d’aya kan d’aya ranta fess abunta itafa matakin da Hajiya ta d’auka ba k’aramin dadi ya mata ba wallahi,
Itafa dan dai kawai karta koma gidan a yanzun ace ta fiye shegen gulmane amma wallahi da sai tabi bayan su itama ayi komai a gaban idon ta,

Allah dai yasa Hajiya ta jajirce akai k’arshen komai a yau dan Wallahi ita fata take Allah yasa wannan zuwan kawai Hajiya ta fitittike tace bata barin gidan Malam sai an d’aura aure, muga k’arshen mayu,
Inba maita ba Meenal dai kamar ita kad’aice kwallin kwal mace a cikin dangi da za’ace a rana d’aya maza uku sun jeru jerin gwanon neman auren ta,
Cigaba dacin dambun ta tayi tanayi tana gyad’a kai dan wak’ar gwanja take saurare tana kuma bin wak’ar mai taken “Asha rawa rawa mata kusha rawa rawa kusha sha’anin ku duniyace… Sama mataaa”
Kai da kaga yanayinta kasan bata d’auke da ko wani damuwa,

Tayi nisa wajen cin dambun ta kirar daya shigo wayar shine ya katse mata wak’ar da take bi,
“Wani d’an anacen ne yake son takura wa rayuwata ne?”
Badan tasoba haka nan dai ta mike taje ta d’auki Number din Ya Sa’eed ne mai kiran dan haka bata tsaya yanga ba ta amsa kiran da sallama,
“Kuna tudun wadan ne?” Ya jefo mata tambaya,
“Eh “ita kuma ta amsa mishi,
“ina Meenal?” Ya tambaya,
“Suna sama ita da Moon ni kuma ina falo, kai kana ina ne Ya’ya?”
“Ina gida ki…”
Saurin yanke tayi da cewa,
“Yauwa dan Allah karkaje ko ina dan Hajiya tana hanya ita da iyalan gidan nan ta had’o gangamin sun zasu zo nan gidan neman ma Mai Jama’a auren Meenal”

“Ban gane ba! Me kike cewa ne?”

“Allah kuwa da gaske nike fad’a maka Mai Jama’a shike son Meenal da auri nan gidan dai babu wanda bai sani ba kuma tun ranar da akasa ranar su Sarki su Baba Usman sukayi ma Baba Adamu magana shi kuma yace musu zaiyi magana da Baba Malam idan kun dawo daga kano duk yanda ake ciki zai kira ya musu bayani sai suje gidan ayi magana….”
Katseta shima yayi da cewa,
“Shine ke kuma kina zuwa gidan yanzun kika ba Hajiya labarin abinda ya faru na zuwan su Salman wajen Baba yau koh?”

“To shiru kake so inyi ne bayan kuma nasan itama Meenal din AK take so, ni bawai bana son ta da sauran bane ah ah amma dai zanso ace wannan karan ta samu wanda take so”

“Turk’ashi lallai yau akeyin ta” Ya Sa’eed ya fad’a daga can gefen,

“Me ya faru kuma Ya’ya?”
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yace,
“Kin san bayan fitan ku wani Bash sunzo gidan nan shida iyayen shi kuma suma neman auren ta sukazo sannan sun shaida ma Baba cewa wai shi din tsohon saurayin ta ne har labarin abinda ya same shi a lokacin auren ta da Sarki saida suka labarta ma Malam yanzun haka shi ya nemi izinin ganawa da ita kuma Malam ya yarje mishi yanzun haka na tabbatar da cewa yana hanyar zuwa nan gidan wajen ta,”

“Wai kana nufin shima mayen nan yau yaje gida?”

“Kin san shine?”
“Eh na san shi naji labarin shi dama tun a KD da muka dawo kuma kafin biki mun had’u dashi a makarantar su Meenal din kuma wallahi ni dakai na nace mishi AK zata aura bashi ba, wato ashe da bai tunkare ta ba can gida ya tafi kai tsaye kamar yanda nayi hasashe tun farko lallai ma gayen nan to Allah ya kawo shi lafiya, kuma wallahi bazan fad’a mata zaizo ba nan zan zauna in jira zuwan shi”

“Sultana mai kike shirin aikatawa? Kardai kice zaki mishi rashin kunya dan baki sani ba ko har yanzun ita tana son shi”

“Ah ah wallahi bata wani son shi, idan da ace tana son shi ai bazata amsa ma AK ba tunda Maryam ta bata labarin cewa ya dawo k’asar har sun ga juna ita dashi tun lokacin,
Nidai Yaya duk ba wannan ba dan wannan mai sauk’i ne yanzun dai so nike ka taimaka ka wuce falon Malam kayi mana jiran isowar su Hajiya inda hali dan Allah kayi min video d’in komai da zai gudana ko kuma kayi min audio in komai ya kammala ka turo min dan Wallahi ji nake uwa inyi tsuntsuwa in dawo ayi komai a gabana, da ace nasan hakan zai faru da bazan bar gidan ba har Sai sunzo wallahi”

“Oh yanzun kuma ni kike so ki maida ji da ganin ki koh, wato gulma kike so in kwaso in labarta miki”

Saida tayi k’asa da murya kafin tace,
“Gulma na nawa kuma bayan yanzun ka gama bani labarin zuwan wancan mayen,”
Daga murya tayi tana cewa, “nidai ai da Allah na had’aka”
Yanke wayar yayi daga can gefen shi batareda ya bata amsa ba, ita kuma sai cire wayar a kunnen ta tana dariya,

“Kujishi da karfin hali fa dan Allah shima ba gulman ya kirani ya fadamin ba yanzun?”
Wuce wa tayi ta maida wayar a speaker ta dawo taci gaba dacin dambun ta,
sama sama ta farajin sallama mai had’e da nocking da akeyi daga kofar falon a hankali,
Dan tsam tayi a zaton ta ko Larai zatajiyo sallaman ta fito ta duba ko waye sai kuma taji shiru Larai bata fito ba, d’age bowl din dambun tayi daga kan cinyarta ta maida shi a gefe ta ajiye kafin ta mik’e kwalin exotic din a hannun ta tana kurb’a,

“Ameen Alaikum salam wanene ana zuwa”take fad’a a yayinda take takawa zuwa kofar falon

“Kaiii…. ๐Ÿ˜ณ da gaske Ya Sa’eed yake wallahi! Kai kuma me kazoyi a gidan nan kuma?” Ta tambaya tana fita daga falon tayi gaba ta lek’a bayan shi dan taga shi kadaine ko nan d’in ma tareda waliyan nashi ya taho,

Maimakon ya amsa mata sai kawai ya kewayeta ya wuce ta gefen ta ya shige cikin falon,kallon mamaki tabi shi dashi kafin da sauri ta dawo da baya tasha gaban shi tana wani ware hannayen ta tare mishi hanya irin a dole ita ta tare mishi hanya karya wuce d’in nan bayan already fa ya riga ya shiga cikin falon,

“Ina tambayar ka me kazoyi shine kake k’ara shigewa gidan mutane ba tareda izinin masu gidan ba?
To dai koma wa kake nema bazaka samu ganin shiba dan mutanen gidan basa nan ni kad’aice a gidan kuma ni bana maraba da bak’o irin ka dan haka ka juya ka koma inda ka fito an gode da ziyara idan Hajiya ta dawo zan fad’a mata tayi bak’o,
Meye ma sunan ka? Koda yike babu ma buk’atar jin sunan naka”

Wannan karan ma bai amsa taba ya k’ara zagayeta ya isa kan kujera ya zauna ya barta a tsaye ta rike kwonkwoso tana wani jijjiga jiki kamar wata wacce take shirin yin dambe dashi,

“Nace maka fa masu gidan basa nan shine kuma har da neman wajen zama ka zauna?”

“Can you please do me a favor?”
Ya tambaya batareda ya kalleta ba,
Karasawa inda yake tayi tana wani tab’e baki,

“Favor? Me kake buk’ata?”

“So nike ki shiga daga ciki ki kira min Meenal saboda ita nazo nan bawai saboda keba, idan kuma bata nan ina son zanyi magana da Hajiya”

“Tab sannu wato ma nice zan zama yar aiken ka, kuma ai nace maka babu kowa a gidan!”ta fad’a a yayinda tayi wucewar ta takoma kan kujerar data tashi ta d’auki dambun ta taci gaba daci,

Bai k’ara kulata ba shima sai kawai ya cire wayar shi daga aljihu yaci gaba da latsawa,

Harara kawai take ta faman aika mishi daga inda take zaune, saboda tsabar iya hege irin na Sultana duk k’arar speaker din data kunna wanda har a harabar gidan ana iya jiyo shi amma saida ta k’ara volume dan kawai ta takura ma bawan Allah ,
Shiko bawan Allah ko gezau bai nuna hakan ya dameshi ba,

Yarinyar nan fa alamu sun nuna cewa idan bai biyo mata ta bayan gida ba to tabbas bazasu shirya ba,
Dan haka sai kawai ya soka wayar shi a cikin aljihu ya mik’e,
Ita kuma da gefen ido take binshi da kallo a zaton ta ko har ya gaji da zaman ne ya nema ma kanshi sauk’i zai tafi, sai dai ga mamakin ta maimakon ya nufi hanyar k’ofa domin fita daga cikin falon sai taga ya wuce wajen kayan kallon dake falon, bata gama tunanin abinda zaiyi a wajen ba taji falon yayi tsit wato wakar da take sauraro na gwanja mai taken (kuyi ta kanku muma muyi ta kan mu dariya bafa soba) ya d’auke sakama kon zare socket da Bash yayi daga jikin wuta gaba d’aya,

Zabura tayi ta mik’e tana binshi da kallon mamaki,
“Kai ๐Ÿ˜ณ ina ruwan ka dani to da zaka zo ka kashe min? Nan fa ba gidan ku bane da zaka zo ka takura min,”

Ta kowa yayi yazo ya zauna a inda ya tashi ko kallo bata isheshi ba, fuuu ta kwashi jiki zataje ta k’ara kunnawa,

A tsawace yace mata “karki sake kice zaki k’ara kunna min wak’a a wajen nan”

“To ai nan ba gidan ku bane Malam”

Larai ne ta fito daga cikin kitchen,
“Sultana bak’o kikayi ne? shine ko ruwan sha baki kawo mishi ba?”

“Allah ya kyauta niba bak’ona bane”

“Ina wuni” Bash ya gaisheda Larai
“Lafiya lau bawan Allah Barka da zuwa gashi kazo kuma Hajiya bata gida bana tunanin ko zata dawo yanzun kuma!”

“Ah ah ba wajen Hajiya nazo ba wajen Meenal nazo ko zaki taimaka ki kiramin ita?”

“Ke Sultana me yasa to baki kira mishi ita d’in ba”

“Tab tab’ ai wallahi bazan kirata ba, taya ma zan kirata bayan nasan shi din neman takara yazoyi” ta fad’a tana kauda kai gefe,
Wucewa sama Larai tayi dan ta kira mishi Meenal din sai da yaga ta haura kafin ya maida duban shi kan sultana,
“Abokin takarar wa kike cewa?”
Saida ta harare shi kafin ta bashi amsa da cewa, “ai tun ranar da muka had’u sai da na shaida maka cewa ka d’auki na annaba dan ita d’in dai ta riga ta k’arayin maka nisa a karo na biyu amma bakaji ba dan maita sai da ka k’ara biyota, to dai duk ka gama zarya da rawar jikin ka baka samun ta yanzun din ma wallahi”
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau kafin yace,

“Me yasa kika tsaneni har haka? Na tab’ayi miki wani abinda ya b’ata miki raine? A iya sanina dai tsayin shekarun rayuwata babu a inda na tab’a ganin ki balle wani abu ya had’ani dake amma ban san me yasa tun had’uwar mu na farko kike jefoni da bak’ak’en magan ganu ba ko k’awayen ki sun fad’a miki wani maganar ne a kaina ina son sani?”

“Ni mai sa in tsane ka? Allah ma ya tsareni kawai dai ni gaskiya nije fad’a maka dan bana son inga mutum yana cusa kanshi a inda bashi da kwarjini,”

“A zaton ki idan Meenal ta nuna bata ra’ayina a yanzun zan gaza cigaba da rayuwa ne? Ina son Ameena da zuciya d’aya dan haka zan taya ta son duk kan abinda take so koda ace hakan yana nufin cewa ni zata ajiye a gefe ta d’auki wani na, zata bata kwarin gwuiwa saboda duk yanda nake sonta bazan tauyeta akan dole saita zauna dani ba alhalin nasan cewa soyayyar ta wanina takeyi wa bani ba, amma a yanzun bazanyi saurin yanke hukunci ba har sai naji ta bakin ta daga sanda kuma ta tabbatar da zancen ki cewa ta riga ta fidda ma kanta mijin da take ganin cewa shine zab’in zuciyar ta ni kuma zan bita da fatan alkhairi ne dan ba kaina farau rasa abin so ba kuma baza’a k’areshi a kaina ba ina fatan kin fahimta”

Mak’alewa Meenal tayi a tsaye, dan tunda Larai ta shiga ta sheda mata cewa tayi bak’o ita da Moon suka biyo bayan Laran suka fito dan ita Meenal tayi zaton ko cikin su Ya Hashim ne wani ya biyota nan gidan idan sune koh Wallahi rashin mutunci zata shuka ma ko waye a cikin su tunda su basu san lala ma ba ta tsiya zata tafi dasu,
Sai dai tun kafin ta sauko idanuwan ta suka hasko mata fuskar Bash tsaf,
Bash d’inta dai a shekarun baya shine yau zaune a falon Hajiya da sunan yazo wajen ta, itafa harta cire rai da cewa zai nemata tunda taji shiru tun sanda Meelat tace yaje gidan su take sa ran zuwan shi shine sai yau ne zai bayyana a gareta,
Tsayuwar tane kuma yasa itama Moon taci burki sukaci gaba da sauraron hira tsakanin Bash din da Sultana, Larai ko tana saukowa ko lura da ita Bash din baiyi ba ta wuce falo ta had’o mishi kayan motsa baki ta kawo ta ajiye mishi,
Kamo hannun Meenal Moon tayi suka sauko kasan a hankali,
Da sauri Bash ya mik’e yana jin kamar yaje ya tattaro ta ya cusa ta a cikin jikin shi saboda tsabar farin cikin daya lullub’eshi a yayin ganin nata,
“Bash ” Moon ta kira sunan shi fara’a kwance a fuskarta,
“Ashe rai kanga rai yau sai gaka a gidan mu”

Da fara’a shima ya amsa ta da cewa,
“Moon d’in Meenal long time… ”

“No see… “Ta k’arasa fad’a tana dariya,
“Barka da zuwa gaskiya nayi murnar ganin ka banyi zaton cewa zamu k’ara had’uwa ba, ya bayan rabuwa da iyali”

“Alhamdulillah Moon kefa ya kike ya naki iyalin? Ko kema gwauruwa ce kamar dai ni?”

Kujerar da Sultana ke kai ta isa ta zauna dan ita Sultana tun maganar Bash din kafin saukowar su Moon bakin ta ya mace murus,

“Meenal bismillah k’araso ki zauna mana ko bakiyi murna da ganina bane”ya fad’a yana kallon Meenal,

Kwalkwal idanuwan ta suka kawo kwalla tana shirin yin kuka, “waye yace maka banyi murnar ganin kaba?”
Ta fad’a da muryar kuka hawayen idonta suna gangarowa zuwa kan kumatun ta,
Zama tayi a kujerar kusa dashi tana goge fuskarta da tafin hannun,
“Me yasa tun tuni bakazo ba bayan kuma Meelat tace min kaje can gidan su kuma kasan ni bani da number dinka balle in kira ka?”
Sanyi jikin shi yayi dan haka baiyi magana ba har sai da shima ya koma ya zauna,
“Kiyi hakuri banyi hakan da niyyar ba tun lokacin naso inzo in ganki sai dai kuma a ranar jikin Dady ya motsa dole washe gari muka wuce dashi asibiti amma tsayin lokacin nan kullum cikin tunanin ki nake shi yasa muna dawowa na matsa akan dole aje a nema min izinin ganin ki a can wajen Baba Malam yanzun haka daga can nike,”
D’ago kanta tayi bayan ta k’ara share hawayen ta,
“Bash baka manta dani ba?”
“Me zaisa in manta dake Meenal? Bayan na riga nayi ma kaina alkawari cewa koda ace kena rasaki insha Allah zanyi ma kaina makwafin ki a duk sanda Allah yamin arzikin haihuwar ya mace a cikin yaran da zai azurta ni dasu”
Tana murmushi hawaye na cigaba da fita daga cikin idon ta tace,
“Takwara zakayi min?”

“Insha Allah kuwa”

“Nagode” ta fad’a tana goge hawaye,

“baka sha ruwa ba, Sultana zuba mishi ruwa yasha”

“Ah ah bazan sha ruwa daga hannun wannan yar tsanar ba” ya fad’a yana cushe fuska,

“Eh kuma nima bazan baka ruwan da zaka shaba” cewar Sultanar tana murgud’a baki,
Dan haka sai Meenal din ta mike ta zuba mishi ruwan ta mik’a mishi ya kuwa amsa ya kafa kai sai da ya shanye kafin ya ajiye kofin,

“Tashi muje daga waje in baki wani labari”inji Moon,

“Ke nima ina da labarin badawa amma dai yanzun babu inda zani dan bazan bar falon nan aci amanar Yayana ba,
Ke sister ki fad’a mishi gaskiya fa karki cutar dashi wajen kin fad’a mishi gaskiyar cewa wani daban ne a cikin zuciyar ki yanzun ba shiba, kai kuma ai yanzun kace min zaka tayata son abinda take so koh? To ga dama ka samu”
Janyeta Moon tayi suka fice a cikin falon harabar gidan suka zauna anan ne kuma ita Sultanan take ba Moon labarin cewa su Hajiya fa sun tafi unguwar malamai nemo auren Meenal, dan haka sai suka fara kiran waya dan suji ko su Hajiya sun samu isa can d’in ya ake ciki kuma,

A falon ko bayan fitar su kafe Meenal bash yayi da kallo kafin ya bud’e baki yace,
“Kin kara kyau sosai Dr”
Duk’ar da kai tayi tana murmushi, kaima ai ka k’ara kyau sosai bani labari ya bayan rabuwa?”

“Abubuwa da yawa sun faru dani marasa dad’i Meenal sai dai yanzun Alhamdulillah komai ya wuce ya zama labari gashi kuma kema ina fatan wannan karan Allah yasa in dace”

“Iyali fa?” Ta tambaya,

Dan haka saiya gyara zama ya labarta mata abubuwan da suka faru tun daga ranar daya samu labarin d’aurin auren ta a wannan falon da suke zaune, halin daya shiga dama auren da akayi mishi bayan ya koma zama a malesia rabuwar su ikiliman sai dai bai fad’a mata gaskiyar silar rabuwar nasu ba dan wannan sirrine mai girma da yayi alkawarin cewa babu maiji daga wajen shi,
Ta tausaya mishi dan har saida tayi mishi hawaye,
Kafin ta gyara zama itama ta bashi nata labarin a takaice, sun jajanta ma juna kafin ya k’ara jefo mata kalmar d’azun,
“Meenal Baba Malam ya bani damar cigaba da zuwa ganin ki sai dai kuma jikina yayi sanyi dajin maganganun Yarinyar can.. ”

“Sunan ta Amina inkiyar ta kuma Sultana ita d’in yar uwata ce da Maman ta da Babana uwa d’aya uba d’aya suke”

“Bataci sunan taba sai na maketa wata rana idan taci gaba dayi min rashin kunya”ya fad’a yana tab’e baki,

“Sultanar zaka make?”ta tambaya tana dariya,
Basar da zancen yayi,

“Fadamin suwaye suke kan layi a yanzun dan ina son sanin abokan takara na,
Tunda naji Yarinyar can nata maimaita magana d’aya nasan da gaske takeyi dan batayi kama da makaryata ba”

“Me yasa kake son sani tun yanzun?”

“Kina mamakin me yasa koh? Ki dena mamaki ina son sani ne dan in baki goyon baya, idan ni zuciyar ki ta zab’a miki zanyi farin ciki matuk’ar gaske, a kasin hakan kuma bazan takura kiba sai dai in Baki k’arfin gwuiwa tsayawa akan ra’ayin ki ko baki san cewa yanzun an dena yayin auren dole ba? Idan na matsa saina aureki nasan ban miki adalci ba”
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,

Dambun da Larai ta debo mishi ta mika hannu ta d’auko sai da ta d’ibo takai bakin ta kafin ta mik’a mishi bowl din,
“Kaci yayi dad’i”
Amsa yayi ya faraci batareda ya kusa mata ba,
Gyara zama tayi kafin taci gaba da magana kamar haka,

“Bash” “uhumm” ya amsa mata sakamakon abin dake cikin bakin shi,

“Nayi farin cikin matuk’a ayau da Allah ya k’ara hadamu, ka nemi jin abinda yake cikin zuciyata game da kai a yanzun, sai dai zan fad’a maka gaskiyar cewa
Meenal din daka sani a yanzun ba wacce ka sani a shekarun baya bane,
Meenal budurwa kasani wacce ke magana dakai kuma bazawara ce wacce tayi aure shekuru masu dan tsayi wacce da ace tana da rabon ciki da haihuwa da tuni an sakata cikin matan da ake kira iyaye,
Alaqa ta ganin girma da mutunci ne ta had’ani da kai a baya kafin alaqar tamu ta rikid’e ta koma soyayya,
Na soka sosai a wancan lokacin ban kuma tab’a kawo rabuwa a tsakanin mu ba sai dai kuma ba haka Allah ya tsara ba, bayan aurena kuma ban tab’a tunanin rabuwa da Yayana na duk kuwa da irin zaman da mukeyi na kalar na sauran ma’aurata bane, ina so ka sani nayi yak’i da zuciyata sosai a kanka ban sarara ba har saida nayi iyayina wajen ganin na cire soyayyar ka dama duk wata damuwar da zata hanani karatu domin shi kad’ai nasa a gabana ba komai ba, banyi tunanin ajiye sauran sanka a zuciyata ba dan ban tab’a hango ranar mutuwar aurena zaizo ba, komai ya afku da sauri ta yanda auren ya mutu har na zamana ya dawo nan,
Nasan zakaji babu dad’i idan nace maka koda aurena ya mutu ban kawo ka a raina balle in neme ka,
Ka sani na riga nayi rami tuni na riga na burne komai dan haka sabon babin rayuwa na gina ma kaina, a hakan ne kuma d’an uwana ya gabatar da soyayyar shi gareni, abinda banyi zato ko tsammani ba”
Shiru tayi shi kuma sai ya mik’a hannu a sanyaye ya mika mata ruwa, sai da ta amsa tasha kafin taci gaba,
“Bash ina matuk’ar son Mai Jama’a, son da ban tab’a zaton cewa zanyi ma wani namiji ha irin son nike mishi, ina farin ciki idan nagan shi cikin farin ciki ina kuma jin rashin dadi idan ni ko wani ya b’ata mishi rai, ina son shi bawai dan yana matsayin d’an uwana ba, ah ah ina son shine kawai saboda shi zuciyata ta zab’a kayi hakuriยณ”
Sai da ta maimata mishi kalmar kayi hakuri har sau uku kafin taci gaba dacewa,

“Bazan iya raba zuciyata da son shi in zab’e kaba, hakan kuma bawai yana nufin ina k’in ka bane ah ah har yanzun kallon ka nike a matsayin makusanci na domin ma baka matsayi na musamman a zuciyata batun soyayya nedai nike so mu barta komai ya faru akwai dalilin faruwar shi ni dakai Allah bai k’addara zamu zamo mata da mijiba”

Tunda taci gaba da bayani ya maida kanshi k’asa harta gama,

“Ba komai Meenal hakan ma nagode, kuma ina ma Dan mai k’arfin murna”
Murmushin yak’e,
“Baka manta sunan da muke kiran shi dashi ha ashe?”

“Taya zan manta kuwa? Yanzun dai muje ki takamin in wuce, yauwa kuma Hajiya tace tana gaisheki, muje ki takamin in wuce”

“Nagode Bash nima ina gaisheda Hajiya, amma kasan bani da number dinka kuma kake batun tafiya baka bani ba? ”

“Kina buk’atar number na?”

“Eh mana ka sani ko a cikin yan Matan gidan mu in baka d’aya! Kuma koba ma haka ba aidai kasan na dad’e ban tambaye ka kudin anko da kaza ba,
Wai kasan me?”
Yana dariyar maganar ta yace ina zan sani yar Malam, ko yanzun ma kud’in kazar za’a amsa ne?”

“Ah ah wallahi badai kud’in kaza ba aini nafiso a siyo min kazar a gashen ta, dama zance maka ne yanzun fa nima k’atotuwar Hajiya ce wallahi motocina dai dai har uku”
Ta fad’a tana kad’a kai cike da kurari,
Fashewa yayi da dariya sosai,
Ita kuma sai ta d’aure fuska,
“Auw dariya ma kake min mai makon ka tayani murna duk masu tsada nefa yan yayi”

“Sorry sorry nifa dariyar murna nike miki tunda Allah yasa burin ki na mallakan manyan motoci ya cika saura wanne kuma, uhumm dama burin uku ne ai zama likita, matoci manya, sai ginama malam gida koh?”

“Baka manta ko d’aya ba yanzun biyu sun cika saura d’aya insha Allah shima saura kiris”

“To Allah ya sanya alkhairi kawo wayar ki in sa miki number din”

Mika wayar tayi ya amsa ya zuba nashi number din yayi saving da sunan shi kafin ya kira, saida kirar ya shiga ya yanke sannan ya mika mata wayar,

Fitowa harabar gidan sukayi fuskar su d’auke da murmushi Sultana wacce duk hirar da suke da Moon hankalin ta yana kan kofar falon ne ta taso,

“Kai murmushi fa naga kanayi?” Ta tambaya tana zagaye shi,

“Karki k’ara kulani ina ruwan ki dani?”

“Ke Meenal baki fad’a mishi gaskiya bane duk shawarar dana baki”

“Na fad’a mishi”

“Kuma shine naga ya fito yana murmushi?”

“Moon zoki janye yar tsanar nan a gaba na kafin inyi ball da ita”cewar bash,

“Wai nice zakayi ball dani kawai dan nayi tambaya,
To wai kai bakaji kishi bane ai kamata yayi inga ka fito fuska a d’aure kana cin magani”

“Amma kamar kina da ciwon mantuwa koh? Ina ce d’azun nan nace miki zan tayata son abinda take so? To abinda nike yi a yanzun kenan”

“Wai dama da gaske kakeyi? ๐Ÿ˜ณ ashe dai kana da kirki har haka, sannu to Allah ya k’ara hakuri”

“Ka dena biyema Sultana inba haka ba ko kwana zakuyi bazata dena saka kanayin surutu ba,
Nidai muje in nuna maka motocina karma kayi zaton labarin kanzon kurege na baka”

Can parking space suka wuce ta nuna mishi motocin sai da ya zagaye su duka ya kuma yaba, kafin yayi sallama dasu ya shiga motar shi yabar gidan su koma suka koma harabar gidan suka dasa sabon hira anan ne kuma takejin cewa wai ashe Hajiya ta kwashi bataliyan ta sun wuce gidan Malam,
Ita dai ranar yau bata san ko wacce kalar rana zata kirata ta, allah dai ya isa tsakanin ta da mutum uku, Salman Hashim da Aliyu duk su suka jawo mata koma menene suna dai zaune suna jiran jin sabon update daga gidan Malam.

A gidan Malam ko fitowar su Bash da iyayen shi yayi dai dai da dawowar Baba Adamu gida a wannan lokacin dan haka lafiya lau sukayi gaisuwa a tsakanin su, yana tareda gajiya shi yasa bai tsaya ba kawai ya wuce nashi sashen sai bayan da yayi wanka yaci abinci ne Aunty Murja take shaida mishi abubuwan da suka faru yau a cikin gidan na zuwa neman auren dasu Salman sukayi wajen Malam har zuwa kan su Bash da suka bar gidan a yanzun,
Dafe kai yayi cike da jimami,

“Akwai matsala ne?” Ta tambaya tana jiran jin amsar shi,

“Hajiya da su Usman sun nemi auren Meenal a wajena suna nema ma Mai Jama’a nasu tun ranar da mukaje nema ma Sarki auren yarsu ni kuma na shaida musu cewa zan yi ma Malam bayani sai yasa ranar da zasu zo ayi magana,
Wallahi abubuwa ne suka shamin kai banyi zaton cewa hakan zai iya tasowa a yanzun ba kuma, yanzun me zance ma Hajiya idan taji zancen nan bayan kuma su suna da yak’ini akai na shi yasa nasan basu taso sun taho wajen Malam ba tun lokacin”

Mikewa yayi ya fice daga falon dan gara yaje ma malam da batun tun yanzun kafin abubuwa su tab’arb’are Allah yasa dai sanarwar da Malam yaba Sheikh mata ba Meenal din yake nufi ba!
Dan in har ita yake nufi tofa akwai matsala gaskiya dan koshi bazai goyi bayan abunba indai yarinyar ta nuna bata so koda ko babu zancen AK a hannun shi balle kuma su yasan dashi suka dogara,

Malam kad’ai ya tarar a falon nashi saida suka gaisa kafin Malam din ya kora mishi bayani akan zuwan iyalan gidan Master wadanda ya gani, kafin ya koma baya kuma ya bashi labarin zuwan su Salman kamar dai yanda yasamu labari daga wajen matar shi, sai da malam ya gama nashi jawabin duk da ajawabin na Malam ya gane cewa su Salman maganar su bai d’ad’a Malam da k’asa ba,
Bayani shima ya gyara zama ya kora ma Malam din na auren dasu Baba Usman suka nema a wajen shi.

*UMMIEE*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button