Dangina Book 2 Page 29
βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 29*
Babbar magana!
Ashe dai yaron nan d’an kwarai ne kawai rik’on sakainar kashin da yayi ma auren su ne ya hanani gano kyawawan halayen she, to wai dama can haka yake da hannun kyauta amma ni ya wofantar dani ko kodai yanzun ne ya canza?
Allahu akbar in ba d’an daya gaji arziki tsiya na kwance kwancin kwana ba wani mijin ne zai dunga bin macen daya saka da alkhairi kashi da kashi a jejjere irin haka?
Kaga fa dank’areriyar k’atuwar motar daya bata a ranar daya kawo mata takardar freedom d’inta,wanda nasan wannan toshiyar baki ne bayan shi ga kuma wasu miliyoyi daga zuba mata a k’atuwar envelop su wad’annan dai tuni na canza su na tura can Saudiya wajen matar kawunta suka siya mata zinare suna can banki na kai ajiya,
Shine kuma bai gaji ba yanzun ya biyota da wani alkhairin har gida, kai yasa wannan abu dai wallahi dan an riga anyi an gama ne amma da koni ina iya yin tsaye a maida mishi matar shi,kaga shi yasafa ake cewa gaggawa aikin shed’an,
To aikin shed’an ne mana inba haka ba dubi kaga tsayin shekarun da sukayi da aure amma duk bai iya kyauta ta mata irin haka ba balle nima in gani in yaba,
Inda hakan yakeyi tun farko ai da tuni kila sunyi haihuwa uku ko hudu kamar dai ku da kukayi auren tare dasu, ko yanzun ma kuma bazan mishi bak’in ciki ba wallahi tunda shima baiji bak’in ciki ba yake ta hidima da takwarata ubangiji Allah dai ya saka mishi da aljannah mafificiya Allah kuma ya bashi damar yin wani auren dan inbai k’ara aure ba tofa sam bai more rayuwa ba wallahi dan dai waccen shegiyar matar tashi Allah na tuba tooo Allah dai ya shirye ta in tana da rabo a aljannah kaga ko a ciki da falo ta zauna kasan ko ciki da falo a aljannah ai tayi girman Kaduna state da kewayen ta badan halin taba,
Badai zan mishi baki ba amma dai zanje har gida inba ita uwar shi shawara ta k’ara dubawa tacan gefen ta ta nemo mishi wata matar tunda abun ya zama haka, ga dai ku da kanne mata a gida amma nasan ubanku bazai yarda ya k’ara bashi wata yar da sunan aure ba nikuma kaga duka jikokina basa kusa ai da na mishi had’i da wata ko za’a dace ko nima ba sai inyi ta dangwalan arziki ba! ,
Kai koh anyi kyautar gida da mota mai ya rage, next agenda kuma ai sai dai kaji anyi kyautar kujerar makka ina fad’a maka wallahi”
Sosai fa Hajiya ta zage tana ta faman zugagama Sarki ruwan addu’a da sanya albarkha, duk ta mance komai da suka faru a baya alkhairin shi a yanzun duk ya goge komai.
Shidai Sa’eed tunda Hajiya ta fara rattafo zantukan ta dariyar ta kawai yakeyi k’asa kasa, shi din ba bak’on ta bane yasan halin ta ciki da bai,
“Hajiya to yanzun ya za’ayi?”
“Ya za’ayi kuwa d’an nan wannan kyautar ai tunda har ta shigo gidan nan kuma ai bata fita wallahi,
Dafari dai ka fara bani takardun in tabbatar na jimk’e su a hannu na tukun dan gara in jisu a tafin hannu na ta yanda ko addu’a na sun isa sama nasan bazasu dawo k’asa ba,
Maganar Meenal kuma kadai ce amana shi Sarki ya baka
baka son kowa ya sani koh?”
“Kwarai Hajiya saboda ya yarda dani shi yasa ya damk’a min amanar komai a hannuna dan ko k’anin shi da suka fito ciki d’aya bai yarda yasan da batun siyan gidan ba saboda baya son maganar ta fita ta koma kunnuwan dangi”
“Ya kyauta kuma nima ina mai tabbatar maka da cewa zancen nan zai tabbata ne a tsakanin ni da kai sai kuma ita mai gidan da zan shaida mata gaskiyar cewa Sarkin ne ya siya mata gidan daga baya,
Yanzun abunda za’ayi kasan dama nace maka kayan d’akin ta da kud’in dashi Sarkin ya bata sune na siya mata gwala gwakai koh?
To idan tazo zan damk’a mata takardun nan a matsayin cewa da wancan kudin ne nayi amfani aka siya mata gidan,
Kaga daga baya idan ta gabatar ma da Malam gidan sai a fad’a mata gaskiya nasan zuwa lokacin in taji gaskiya ba zatayi bori sosai ba, amma yanzun in har aka ce mata Sarki ne ya siya gidan kachokan ba lallai nema ta amsa ba dan wani zubin itama tana tab’a bak’in hali na gado atoh”
“Eh kuma fa Hajiya kema kina da gaskiya, in haka ne ai gara in yi saurin barin nan d’in kafin ta dawo da dai naso in jirata dan akwai maganar da nike son yi da ita?”
Takardar ya mik’a mata ita kuma tasa hannu biyu ta amsa da bismillah,
“Allahu Akbar kabiran Allah mai maida Sarki bawa,
bafade kuma ya zamo sarki yau dai gani rik’e da takardar gidan takwara ta a hannu na, ko ya zatayi idan taga takardar nan,
Amma fa Sa’eed wannan harkar naku akwai son kai a ciki,
Banbanci zallah ake nuna min ganin idona,
Wato yar nan dai tun tashin ta duka burin ta na duniya akan Malam almu ya k’are ni kuma ko oho, da alama dai mantawa takeyi cewa ni dai nice na haifi uwarta
Yar banza kullum kuma nan take zuwa tana amshe min yan kud’ad’en da d’iyana suke bani na kashewa, zata zo ai yau dai duk tsiyar ta sai ta bani tukwuici wallahi kafin in bata takardar nan nima,”
“Kwarai ina bayan ki Hajiyar mu dan tabbas kin cancanci tukuici mai girma wannan karon, kinga idan ta baki nima sai ki fincino min kad’an kaga ciki insamu nasa mai a mota”
“Kai tafi can wani rashin tsoron Allah ne zai sa in baka kud’ina kuda kud’i basa isan ku iyaye sun tara muku amma kuma kun kasa hak’ura kullum cikin neman su kuke in anyi magana kuce wai kogi baya k’in k’ari,
To ai sai kuyi ta faman tara su a account sai kun mutu a kasa lissafi wasu kudin ma baza’a tab’a sanin inda kuka kai kuka boyeba, yanzun dai jirani in kawo maka sak’o ka kaima jikokina a toh,”
Da kanta ta ciccib’a ta mik’e ta nufi kitchen d’inta bata fito ba sai data shak’o k’atuwar leda taf da kayan kwalam da mak’ulashen da Meenal takeyi ta ajiye musu.
“To gashi kuma ban yarda ka bud’e ba nima amana na baka atoh karma kace ban fad’a maka ba,
Amma dai tunda kazo gara ka jira dawowar nata dan nasan ta kusa dawowa tunda kaga yamma tayi,
Kaga na tuna kuwa, nace injin dai shi Baban naku bai riga ya fara amsa tayin mutane akan ta ba?”
“Wa kike magana Hajiya?”
Shima ya tambaya dan bai gane kan maganar nata ba,
“Ina nufin manema auren ta mana!,
dan kasan halin uban nan naku kar azo ni ina nan zaune da yarinya a gabana azo a k’ara mai maita min abunda ya faru sai aure ya rage kwana kad’an azo a shaida min”
“Anya kuwa gaskiya da wuya dai,
Na daiji ana maganar su Fauxieyerh da sauran yaran amma banji an ambaci sunan ta ba,
Sai dai kuma koni ta nan gefe na akwai mutum biyu da suka min magana a kanta, yana daga cikin dalilin ma da yasa nike son yin zama da ita, saboda dukan su suna son gabatar da kansu a gaban Malam nine na dakatar dasu saboda nasan in sunje shi zai sasu a sahun mane ma ne,
Amma in suka fara gabatar da kansu a wajen ta kinga ita zata tantance da kanta zata zab’arma kanta wanda ya cancanta,”
“Babbar magana wannan shine ake cewa ana wata ga wata!
Kungani koh, ai dama nasan za’ayi hakan shi yasa nike ta son ganin ta mai da hankali ta tsayar da tsayayye dan nasan mai hali baya fasa halin shi,
To ai ba iya gefen ka ni kaina nan ina da tsayayye gangariya anan gefe na sai dai ita kuma yar tutsun ne har yanzun ban gane ina ta dosa ba,
Abinda za’ayi yanzun su biyun nan da kace,
Nan dai zaka fara turosu suzo su gabatar da kansu a wajen ta, saboda wani dalili nawa, sannan karka yarda koda wasa ka bari zancen neman da suke mata ya isa kunnen Malam zanfi so zancen ya tsaya a iya nan,”
Hajiya sun dad’e suna tattaunawa da Sa’eed duka maganar kuma akan Meenal ne da samarin da suka fara kunno mata kai dan ta gefen Sa’eed din dai mutum biyun da yake magana dukan su yan uwanta ne,
Aliyu yaron Maman kano ne shike bin Abubakar tsohon saurayin Raheenat a Yola yake aiki zuwa gaisuwar nan na mutuwar mijin Raheenat ne yaga Meenal d’in,
Sai kuma Hashim shi kuma yaron yayan innar yara ne in baku manta ba a baya na fad’a muku cewa duka matan malam biyu auren zumunci ne dan haka suma Hashim da Aliyu dai dukan su yan uwan Meenal ne na kusa,
Su kuma abinda yasa suka fara tunkarar Sa’eed da zancen son auren Meenal din saboda shiri da sukaga yana yi da Meenal din sosai shi yasa suke son suyi kamun k’afa,
Hajiya ta dade zaune tana cigaba da nazarin yanda zata bullo ma al’amarin nan bayan fitar da Sa’eed yayi zuwa gidan su Billy,
Duka dai wadanda Sa’eed ya gabatar mata yan uwan Meenal din ne na jini kuma dukan su biyun a cikin su babu na yarwa,
To su biyu gashi sun fara bayyana tun yanzun a hakan ma iya su ta sani bata sani ba ko a gefen iyayen ta maza wasu ma sun kai nasu k’ok’on baran akan su ko yaran su,
Idan fa tasa ido tabbas abubuwa zasu lalace ne zuwa gaba kad’an, kuma dai ai duk dad’in inuwar gemu bai kaiga mak’ogoro ba,
Dan haka zatayi amfanin da wannan damar na zuwan da su Baba Usman zasuyi bikin Musty gara su tura su kawai suje su nemo ma AK auren Meenal din a wajen iyayen ta maza kafin abubuwan su cab’e dan tasan har wad’ancan suka gabatar da kansu tofa shi malam nashi yan uwan zai d’auka ita nata jikan ko ohoπ€·π»ββοΈ”
A gefen AK ko duk yanda yaso yaga Meenal ta saki jiki dashi abun ya faskara, dan tunda ta shiga motar duk surutan da ya saki baki yanayi bata wani amsa shi daga umh sai umm umm sune amsar da take bashi,
Dan itafa gaba d’aya a takure take saboda ita sam bata saba irin wannan rayuwar a tsakanin su ba,
Ita dashi sun saba kullum ne da zarar sun had’u fad’ane abunda yafi yawa a cikin hirar su, yau kuma ya d’auko ta yana ta faman yawo da ita ta ina zata sake fisabilillahi ga wani Mayan kallo mai kashe jiki da yake binta dashi dan haka ba k’aramin takura tayi da zamar motar ba,
“Ya’ya dan Allah nidai muje gida, Allah bana ma jin yunwar a yanzun idan munje gida zanci a can”
Ta fad’a ganin yana shirin yin parking a kofar wani k’aton restaurant,
“Karki damu ba shiga ciki zamuyi ba zanyo miki take away ne sai mu wuce gidan, ai na fasa zuwa sai dake d’in kuma dan haka ki kwantar da hankakin ki Dr zamu rayu a tare har tsufa insha Allah,
Yanzun fad’amin mai kike son ci? Ko duk abinda na amso miki babu damuwa?”
Ya tambaya yana kashe mata ido d’aya,
Ita gaba d’aya ta rasa gane dalilin da indai suna tare bashi da halin da zaiyi magana da ita kai tsaye har sai ya had’a da d’age mata gira,
Shi bai san hakan da yakeyi kunya yake bata ba gashi kuma a d’an lokacin itama ta koya ko magana sukeyi da su Sultana sai tayi ta wani d’age musu gira kamar wata yar iska,
“Ka bari dan Allah! Kana sawa ina jin wani iri wallahi,”
Bayan shi ya maida kan kujerar motar yayi relax kafin ya bude baki murya can k’asa yana ci gaba da kallon ta yace,
“Mai zan bari kuma?”
Dage girar da kashe idon ta kwatanta mishi, kafin tace hakan da kakeyi,
Tana k’ara d’age giraren ta,
Ba kad’an ba hakan da tayi ya k’ara tsatso mata kyan daya k’ara tafiya da hankalin shi,
Shidai wallahi komai tayi k’ara kyau take a idanun shi dan haka bayajin gajiya ko damuwa sam a duk sanda zai kasance tare da ita,
“Kina da kyau ππ»”
Ya fad’a yana kwatantawa da hannu, ita kuma sai tasa hannu ta rufe fuskarta saboda kunya ma ya bata wallahi,
Dariya yayi kafin ya tashi ya zauna ya bud’e k’ofar motar,
“Ki zauna a cikin motar karki fito fa, yanzun nan zan dawo”
Da kallo ta bishi tana jin wani irin abu wanda a tsayin rayuwarta bata tab’a jin wani abu makamancin hakan idan tana tare da wani ba sai shi,
Shi kad’aine namijin da idan tana tare dashi a cikin zuciyar ta takejin kamar an cire mata ko wani kalar damuwa,
Nutsuwa takeji da salama a duk sanda suka kasance tare ba kuma zata iya cewa ga dalilin da yasa takejin hakan ba, amma tana jinta a yanayin da zuciyata ce kad’ai sheda akan yanda takejin bata sani ba ko hakan yana daga cikin alamun kamuwa da soyayya, in ko hakan ne sai tace akwai matsala dan itafa wallahi bata shirya ba,
Sam sam sam bata shirya maida hankali akan soyayyar ko wani namiji ba, tana buk’atar isashshen lokaci kafin ta kamu da son wani,
Ta sani cewa idan har tayi saken da AK yayi galaba da sauri haka a kanta tofa itace zata sha wahala,
Natsuwa take fatan samu bayan aurenta bawai auren da zatayi ta gwabzawa da wasu matan akan mijin auren taba,
“Ya dai tunanin me kikeyi haka ne?”
Ya tambaya jin yayi mata sallama har sau uku bayan shigar shi cikin motar amma bata amsa ba, duk da idanuwan ta suna rufe yasan cewa bai isa ace daga shigar shi zuwa yanzun har tayi bacci ba,
Jin shiru bata amsa bane yasa ya mik’a hannun shi duka guda biyun ya ware yatsun shi manuniya ya dannasu akan kuma tunta dai dai inda dimples dinta suka lotsa,
“Auch”
Ta fad’a tana ware idanuwan ta akan shi,
“Ke dai raguwar likita ce wallahi kawai daga shigana shine kafin in fito har kinyi bacci, ko bakya da lafiya ne dan nasan yawon shirin bikin nan bazai barki ki zauna ki huta ma ranki ba”
Sai da ta gyara zaman ta kafin ta amsa mishi a shagwab’e da cewa,
“Ai tun d’azun sai da nace maka ka kaini gida kak’i”
Waiyo Allah yarinyar nan wai me yasa bata neman zaman lafiya ne ita,
Fisabilillahi sai ta sashi a gaba tayi ta mishi shagwaba tana kassara shi da salon ta,
Wannan ma ai d’aukar alhaki ne wallahi,
“Ki dena min wannan abun idan muna tare!”
Ya fad’a yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,
“Me nayiπ³? ”
Ta tambaya tana zare ido,
“Ba komai, zaki iya tuk’amu zuwa gida?”
“Ni kuma?
To ba kai ke tuk’in ba tun d’azun”
“Eh nagaji ne yanzun bazan iya jan motar ba, ki daure ki mai damu gida”
Bude k’ofar gefen ta tayi ta fita ta zaga zuwa driver seat shi kuma tsallakowa kawai tayi ya koma inda ta tashi ba tareda ya fita daga cikin motar ba,
Ruwa mai sanyin daya shigo motar dashi ya bud’e ya kafa kai sai da yasha kusan rabi sannan ya zuba wani ruwan a cikin hannun shi ya dunga zuba su ta saman wuyan shi suna gangarewa cikin jikin shi ita ta tuk’a motar har gidan Hajiya a yayin tafiyar su ta komawa ko zaman shiru akayi a motar shi dai lafewa kawai yayi yana binta da mayun idanun shi, har sai da ta gaji ta mishi magana akan kallon yayi yawa kafin ya juya ya maida fuskar shi gefe yana kallon mutanen dake kai da kawo a titi.
*Ummiee ce*