Dangina Book 2 Page 1
โ๏ธ๐ฑ๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ *DANGINA!*๐จโ๐ฉโ๐งโ๐ฆ๐ฑโ๏ธ
~{{MY FAMILY }}~
ยฉยฎ *UZ-2023.*
*BOOK 2*
*RUBUTAWA*
*ZAINAB USMAN*
*~{Ummiee Zaria}~*โ๐ผ
*Bismillahir Rahmanir Rajeem*
*Ina mai mik’a yabo da godiya na ga Allah mad’aukakin Sarki wanda bai hafa ba kuma ba’a haifeshi ba Ubangijin sammai da kassai,
Sannan ina k’ara salati zuwaga shugaban mu d’an gatan Allah, Annabin mu Muhammad (S.A.W), tareda iyalansa da sahabban sa baki d’aya.
*SADAUKAR WA*
A wannan tafiyar gaba d’aya littafin tun daga farkon shi har zuwa karshen shi zai zamo sadaukarwa ne ga d’aukakin masoya da suka jure wajen bibiyar labarin in daga farko har zuwa yanzun,
Ku d’in kun kasance abun alfaharina, na fara rubutu banyi zaton labarin zai zaga har zuwa inda banyi zato ba, sai gashi a sanadin littafin *DANGINA* na had’u da mutane kalaยฒ wasu iyayena wasu yayye wasu kanni,
Lallai na yaba da kaunar ku gareni, tun daga kan Marubuta dama makaranta da a kullum kune ke bani gwarin gwuiwar ci gaba da rubutu,
Kuna da yawan da bazai yuwu ince zan zano sunayen ku ba, ina dai so ku sani cewa na yaba matuk’a๐.
*Ga masu buk’atar littafin daga farko zaku iya tuntub’ana kai tsaye da wannan number d’in* 08061358462.
Karku manta littafina kyauta ne banyi shi dan in siyar ma makaranta ba, dan haka karkuji d’ar kuba duk wanda kuke so.
*Page 1*
…… Tunda Allah yama Malam isowa da maraicen nan gaba d’aya bai samu zama ba, domin bayan tafiyar shi anyi wani rashi na d’aya daga cikin d’aluban shi wad’anda sukayi karatu a k’ark’ashin shi, dan haka koda ya iso babu jimawa ya shirya ya wuce can wajen iyalan mamacin domin yi musu ta’aziyya bashi ya samu sukuni ba dai har sai zuwa dare.
A gefen Baba Adamu kuwa tun a yayinda Baba Auta yama shi sallama akan zai wuce Abuja a ranshi yaji cewar gudun hijira ne kawai Adamun zaiyi dan baya son gamon su da Malam, domin dama tun zamanin k’uruciya ma in sukayi ma Malam d’in laifi shi Auta Hijira yake yabar gidan har sai Malam yayo bikon shi kafin ya dawo.
Dan haka bai matsa mishi ko tambayan dalilin da yasa zai wuce d’in ba dan yasan Auta dannewa ne kawai yakeyi amma shi kanshi a matsayin shi na wanda yake gaba dashi yasan dole abunda ya faru ya dake shi, domin dai babu ubanda zai so a wayi gari da mutuwar auren yar shi,
Malam bai shigo cikin gida ba har sai misalin karfe 9 da wasu mintuna na dare, a yayin da shi kuma Baba Adamu ya kasa ya tsare a farfajiyar gidan yana jiran isowar shi dan gara ya gabatar mishi da komai a daren nan dan Malam mai iya mishi sai Allah yana iya idan shi yace ya bari sai gobe ya tunkare shi da batun, shi kuma Malam d’in yana iya hau shi da fad’a akan wani dalilin ne ya hana shi gabatar mishi da takardar a yau?
“Ah ah Adamu kai kad’ai zaune a waje lafiya kuwa? To kodai jiran shigowa na kakeyi ne?”
Malam ya tambaya a yayin da hankalin shi yakai kan Adamun dake zaune a kan d’aya daga cikin kujerun da aka ajiye dan zama a kofar falon Malam,
“Eh Malam barka da dawowa an dawo lafiya ya hanya da gajiyar tafiya?”
“Alhamdulillah lafiya lau muka iso, kai kuma sai kazo kayi zaune a nan kai kad’ai ai ko sauro bazasu barka ka sarara ba, da kasan kana jirana ai da ko a waya ka kirani, tunda dai ba komai nikeyi a wajen ba na dai tsaya ne muna gaisawa da makota tunda kwana biyu bana nan abubuwa sun d’an faffaru, kuma ai da ka bud’e falon ma ka shiga”
“Ba komai Ya’ya na daiji zaman a nan d’in ne dama shi yasa ban shiga cikin ba”
“To madallah bismillah mu shiga daga ciki koh!”
Malam ya ambata a yayin da ya tura kofar falon da sallama suka shiga,
Bayan sabuwar gaisuwar da suka sake da tambayar bayan saduwa ne malam ya d’aura da cewa,
“D’azun auta ya kirani cewa sun wuce abuja shida mai d’akin shi zasu d’an kwana biyu kafin su dawo, wato dai Auta take taken shi so yake dai yabar gidan nan dama garin baki d’aya, ni ban san me mutane suke so su zama ba gaba d’aya dai da zarar mutum yaga ya d’an tara yan kud’ad’e sai kaga yana neman ya manta da gidan su, kawai sai ya mutum ya ware kanshi can a gefe shi d’aya, niko gani nike mai yakai zama cikin ahalin ka dad’i fisabilillahi fa, amma yanzun da zarar nayi magana sai ayi min wata fassara ta d’aban, tunda aikin shi ya koma Kaduna ya fara wannan galantoyin tsakanin kaduna da zaria nasan cewa gaba kad’an zaice ya gaji da yawon zai kwashe iyalanshi ne su koma can, yanzun nan fisabilillahi in banda abun Muntari a kadunar har za’a samu wata makaranta data d’ara ita wannan ABU d’in daya bari ne? Ni dai bazan k’ara magana ba ma balle aci gaba da cewa na fiye takura”
Duk surutun da Malam keyi Adamu baice komai ba sai dai d’an murmushi da yakeyi,
“To ina ce dai lafiya? dafatan dai babu abunda ya faru a gidan bayan tafiya na? Koda yake ko wani abun ya faru nasan zaku magance shi basai kun jira dawowa na ba”
Daga kanshi yayi ya kalli agogon dake mak’ale a jikin bangon falon nashi,
“Ashsha ashe dare ya fara haka gashi gaba d’aya na manta dana ware tsarabar uwata ban ce yaran nan su mik’a mata ba harna fita,
Baiwar Allah nasan babu mamaki ta shigo bata iskoni gida ba”
Wayar shi dake gefe ya d’auka kafin ya lalubo Number din Innar yara kira d’aya biyu ta d’auka,
“Na shigo fa tun d’azun amma babu wacce tazo dubani a cikin ku”
Daga can gefen Ita kuma ta amsa mishi da cewa,
“Ayi mana afuwa Malam ita Dije nan wajena ta amshi maganin ciwon kai tasha to nasan babu shakka bacci ne ya d’auketa ni kuma ban san ka shigo ba shi yasa amma zan iso yanzun”
Sai da ya yanke wayar sannan yace da Adamu,
“Kaga halin matan nan koh? Mata biyu amma na shigo tun d’azun an rasa wacce zata shigo ta bani abunci a cikin su”
“Ayi musu uzuri ya’ya indai abinci ne ai koni sai in had’a maka tunda gashi can ai naga an kawo an ajiye”
“Allah mai iko, aiko kaga ni sam ban kula da cewa an ajiye abincin ba, to d’auko sai ka zuba mana muci ai mun kwana biyu dama bamu samu damar cin tuwon dare tare ba”
Duk da cewa Baba Adamu yaci nashi abincin hakan bai hana shi zuba musu wannan d’in ba suna ci suna hira a haka har Ameena ta shigo ta same su,
Koda ta iskosu itama zama tayi sukaci gaba da hiran Malam na basu labarin yanda tafiyar shi zuwa Mai duguri ta kasance,
Bayan sun kammala cin abincin ne Adamu ya yunk’ura da nufin mik’ewa,
“Ah ah ya haka kuma naga kana shirin tafiya bayan kuma baka gabatar min da abunda ya kawo kaba?”
Ba tareda Adamun ya koma ya zauna ba yake amsa Malam da cewa,
“Eh to gani nayi dari ya kawo jiki kai kuma kana tareda gajiya ina ganin zaifi idan mukabar batun zuwa safe”
“Kajika da wani batu fa Adamu, ni da nayo tafiyar jirgi kuma ina ni ina wata gajiya dan Allah fa, kuma tunda dai har naga ka kasa ka tsare kana jiran shigowata ai nasan koma miye yana da mahimmanci dan haka fad’i maganar ka kai tsaye ni kuma zan saurare ka Allah dai yasa lafiya,”
Komawar Adamu yayi ya zauna ita kuma Innar yara ganin hakan sai ta tashi ta shige ciki domin ta basu waje,
Hannu a damu yasa a cikin aljihu ya ciro takardar nan a gaban Malam ya ajiye ba tareda ya iya bashi ita hannu da hannu ba,
Shima Malam d’in bai tambayi takardar kota micece ba har sai da ya mik’a hannu ya d’auke ta ya bud’e,
Shi dai Adamu kanshi na k’asa,
“Kai Adamu wannan takardar kuma ta micece naga rubutun boko ne a cikin ta ni kuma ai kasan dai ba bokon nayi ba balle in gane rubutun dake cikin ta?
d’auki ka karanto min abunda ta kunsa inji, Allah dai yasa ba sammaci bane daga kotu? dan naji ance itama sammacin a takarda ake rubutowa sai a aikawa mutum”
Ya fad’i hakan a sa’ilin daya maida takardar ya ajiye a gaban Adamun,
Doguwar ajiyar zuciya Adamun ya sauke kafin ya iya d’ago kanshi ba tareda ya d’auki takardar ba,
“Kayi hakuri Ya’ya kaddara ce ta aukawa uwar masu gida…… ”
Malam bai bari yakai karshen kalmar ba ya katse shi da cewa.
“Kaddara fa kake magana Adamu, mai ya samu Maman nawa kuma bayan bani?”
“Eh to abune wanda yake halattace amma kuma kunshe yake da rud’ani da sanya faduwar gaba, sai dai sau tari in akayi duba da wani abun sai aga cewa duk da kuncin shi lokuta da dama aikata shi yafi maza alkhairi,”
“Kaga Adamu ni duk ba wannan na tambaye kaba, kasan dai akan wacce kake magana! Magana akeyi akan Mamana mai makon ka fito kai tsaye ka fad’amin mai ya faru kuma naga kana neman wajen mafaka, meya samu Aminatu?”
Shiru Adamu yayi dan Wallahi duk yanda yake da dakiya a yawancin lokuta yau dai sosai yakejin shakkar isar malam da sakon nan,
Jin yayi shiru hakan yasa Malam shima yaci gaba da binshi da kallo, zuwa can kuma ya kwala kiran sunan Innar yara,
“Ameenatu Keee!! Ke Ameena fito nan yanzun”
Yana yin yanda sautin muryar shi ya fita yasa hatta da Adamu sai da yasha jinin jikin shi a lokacin,
Fitowar tayi tana mai amsa kiran Malam d’in,
Tun kafin ta kaiga neman wajen zama ya watso mata tambaya da cewa,
“Maiya samu Mamana a bayan idona?”
“Ah ah wani abu ya faru da itane kuma?”
“Tambayar ki nayi fa!
Mai makon ki bani amsar tambayata kai tsaye shine kema kike maido min da tambayar?”
“Kayi hakuri malam, amma ni dai a iya sani na lafiya lau mai sunan manya take domin dai ko jiya ta kirani a waya, kasan da yike suna kusa da kammala karatun su nasan abubuwan ne suka sha mata kai shi yasa bata samu damar shigowa gidan ba, amma babu shakka gobe kam zaka ganta da zarar labarin dawowar ka ya isketa”
Idon shi ya maida kan Adamu, kirrr yana kallon shi, batareda yace dashi komai ba.
“Nifa Ya’ya saboda ban san ta yanda zaka kalli abun bane shi yasa na kasa furtawa”
“Oh baka san ta yanda zan kalle shiba amma ai hakan bai hanaka tun karana har kazo kana gadin shigowa na gidaba, shin Adamu zaka fad’amin abunda ya samu Y’ata ko saina nuna maka bacin raina tukun? Takardar miye wannan?
Miye alakar takardar kuma da Mamana, domin zuciyana ta faramin wani mugun hasashe wanda ko a mafarki bazan so ya tabbata, ka bude baki ka tabbatar min da cewa wannan takardar ba takardar sakin auren Meenal d’ina bace!”
“Sai dai hakuri Ya’ya domin yanda zuciyar ka ta hasaso hakan abun yake domin ko takardar sakin auren Meenal ce a gaban mu yanzun haka, wacce tun safe Ya’ya Sulaiman ya gabatar min da ita, ni kuma na gabatar ma da Auta da Matar shi kafin kai”
Ba Malam da yayi mutuwar zaune ba harta da Innar yara dake zaune bawai dan tana fahimtar tattaunawar nasu ba jikin ta rawa ya d’auka,
“Takardar mutuwar auren Meenal fa naji kace Adamu?”
Innar yara ta tambaya a yayin da ta samu ta iya fuzgo kalmar da kyat daga cikin bakin ta,
“Kwarai hakan ne Uwar gida tasa Sufyaan ya saki meenal tun ranar da ciwo ya kwantar dashi a asibiti takardar ce dai bata iso garemu ba sai yau”
Kuka ta fashe dashi cikin kukan take tambayar cewa,
“Mai Meenal d’in ta aikata mata haka da zafi wanda bazata iya kawo k’ararta nan wajen mu ko kuma ita d’in tayi mata nata kalar hukuncin ta wani hanya daban ba, dole sai ta hanyar saki ne zata hukun tata?
Dududu yaushe akayi auren ita Meenal d’in har nawa take da za’a yanka mata takardar zawarci da kuruciyar ta,
Sakayyar da uwar gida zata mana kenan bayan irin jelen da suka d’ungayi a wajena da wajen Malam duk dai akan a taimaka aba d’an su auren yarinyar nan, shine zasu d’ibi kasa su watsa mana a ido ko zumuntan dake tsakanin mu basu duba ba,”
Dago kanta tayi ta maida kan Malam daya duk’ar da kanshi kasa gaba d’aya ya b’ace b’at cikin tunani,
“Malam ka gani koh? Ai ga irin ta nan faruwar wannan abun shina guda tun farkon sanda sukazo maka da batun neman auren nan, abun aiba a rufe yake ba, a bayyane yake kowa yasan matar Yaron nan tafi karfin shi, nayi bakin kokari na akan in nusashe ka illar da auren da iya haifarwa a rayuwar Meenal amma fir kaki saurarena daga karshema sai saremin gwuiwa Kayi da cewa inda d’ana ne bazan iya sa mishi ido inci gaba da kallon wata na juya rayuwar shiba,
Yanzun wa aka cutar a tsakanin su biyun? Ita dai namun ita aka cutawa domin ai kowa yasan dama shi yana son matar shi kuka d’auki taku Y’ar kuka cusa mishi ”
Sosai take kuka tunawa da cewa tun farko sai da taso ta nuna ma kin amincewar ta amma Malam sam ya hanata, gashi nan yanzun ai abundai da ake gudun ne ya afku,
“Kiyi hakuri da kukan nan haka dan Allah, shi bawa ai bai isa ya gujema kaddarar shiba, domin dai koda ba Sufyaan din ta aura ba tunda Allah ya nufa auren zai k’are da wuri tofa bamu da wani dubarar hana faruwar hakan, sannan ni dai a gefe na na gamsu da hukuncin da ita uwar gidan ta yanke nayi sakin wanda na tabbata kuma idan kuka saurareni zaku gane cewa hakan shine mafita”
Sai yanzun Malam ya iya magana da cewa
“Mafita!
Sakin auren Meenal din shine mafita?, sakin aure ko zaman nasu duka in akwai matsala ni nan nine ya kamata in yanke hukunci akan hakan domin rayuwar yata ake magana bawai kawai yanzun kai ka kawo min takardar sakin ta ba, komai ya faru a matsayin mu na iyayen su da Allah ya d’aura mana nauyin su ya kuma barmu a raye har zuwa yanzun kamata yayi ace in wani matsala ya tashi mu zasu fara tunkara da ita dan mu nema musu mafita bawai su a matsayin su na yara suyi gaban kansu ba,
Kasan adadin zaryar da matar nan tayi ma falon nan nawa, wanda hakika da yana da ikon magana zai bada shaidan hakan duk akan inba danta auren Mamana, shine har ita da kanta zata sa dan nata ya yanke igiyar auren su ba tareda ni an kawomin abunda yake faruwa gabana ba, maza ka daga waya ka kiramin daga waya ka kiramin su dukan su ina bukatar ganin su anan falon nawa a yanzun basai gari ya waye ba”
“Ya’ya….. ”
Katse shi malam yayi da cewa
“Adamu umarni na baka bawai ina neman shawarar ka akan maganar nan bane, shin da kake son kamin shishshigi nayi shawara da kai kafin in d’auki auren yata in basu ne? Kokoh ta hannun Kane sukayi neman auren? Dan haka ta inda aka hau tanan ake sauka,
Ke kuma Kiyi min kiran ita Maman nawa yanzun nan”
“To ai Ita Meenal d’in bata a gidan nan Malam”
“Bata nan gidan to tana ina? Ko can gidan nashi suka barta taci gaba da zama bayan sun sa ya saketa?”
Adamu ne ya bashi amsa da cewa,
“Tana can a Tudun wada tare da kakarta tun ranar da shi Mijin ya kwanta a asibity wanda hakan ne yayi sanadiyar komai daya faru”
“Can gidan kakanta, kenan ita kakar nata tasan da batun sakin kenan?”
“Eh ta sani”
Hummmm malam yaja doguwar ajiyar zuciya kafin a fili ya furta cewa “lallai kam”
“Yaya dan Allah da kayi hakuri abar maganar nan zuwa safe in yaso sai a kira ita Meenal d’in ta taho suma kuma sai a kira su duk da dai shi Malam Sulaiman yamin bayanin komai kamar yanda matar shi itama ta mishi bayanin, ina ga ayi hakuri kawai kar daga maganar ya janyo sanadin da zumunci zai tab’u”
“Kaji wani zancen banza a wajen ka Adamu, su basu duba zumuncin ba dan su ya sako min ya sai ni, wallahi sai sunzo falon nan sun min bayani dallah dallah akan dalilin wannan cin mutuncin da suka min, dan banyi lalacewar da za’a sako min yarinya in kasa bin kadin dalilin sakin ba, ina fa son abata da maneman ta da komai amma na zabe shi na bashi auren ta bayan nacin da iyayen shi suka nuna akan son ayi had’in, kai kana tunanin in bancin su din sun kasance na jikina naba wallahi in wani ne a daren nan zan sa akai mishi sammaci gobe mu hadu a kotu”
“Na san basu kyauta ba, amma nidai alfarma na rok’a akan a bari gobe sai ayi zaman,”
Sai da malam yayi kwafa kafin yace,
“Wai kai Adamu baka kishina da uwata ne ko yaya?”
Da mamaki ya dago yana kallon malam,
“Eh ai dole in tambaya dan banga alamar kishin a cikin idon kaba”
“Haba yaya ya zaka ce haka? Gani nayi ai abun duk na gida ne babu bare a cikin mu”
“Ah ah kam nasu suke so nawa kuma ko oho tunda gashi sun rabata da dansu shi zaije yaci gaba da rayuwa da dayar matar shi ita kuma zata fad’a zawarci, na dai ce ka kiramin shi Sulaimanun suzo gidan nan gobe da safe ina bukatar ganin su harda shi Sufyaan din dan babu mai maisheni mutumin banza a cikin su,
Kema nace ki kiramin Meenal din kin gagara bari ku gani”
Wayar shi ya d’auka ya lalubo lamban auta,
Bata dade tana ringing ba aka d’auka,
Bai tsaya amsa gaisuwar da Auta ke mishi ba ya fara rattafa mishi nashi jawaban
“Auta kai kanaji koh, to cikin biyu Kayi d’aya kodai ka kiramin Mahaifiyar matar ka ka fada mata ta dawo min da Mamana gida a safiyar gobe a yanzun haka, ko kuma ka bari goben in gari ya waye ka kirata ka fada mata ina bukatar ganin mamana a gida gobe, kai kuma nagode tunda haka Allah yayo ka baka da katabus”
Bayan ya yanke kiran shi da Auta a take ya aikama Malam Sulaiman kira shima, kamar yanda bai saurari Auta ba haka shima bai saurare shiba illah sallahu kawai daya bashi akan yana neman shi da mai dakin shi a gobe da safe, yana kuma son ganin Sufyaan din shima.
Sai da ya gama waya dasu kafin ya juya wajen baba Adamu ya bashi umarnin ya fada mishi komai kamar yanda Sulaiman ya shaida mishi,
Tsaf kuwa ya koro mishi bayani, bayan ya gama karanta mishi ya dade a falon na Malam dan ganin ya sauko yama abun kyakyawan fahimta amma ina duk ta inda ya bullo malam sai ya bulle a karshe dai ganin dare ya ja dole yayi sallama dasu ya wuce sashen shi yana mai fatan allah ya sa abun yazo cikin sauki dan sosai fa malam ya shak’a.
*Ummiee Zaria*โ๐ผ