Dabi’ar Zuciya 62
62
*10:48*
Yana tsaye gaba mudubi yana sharce ruwan kansa,yana kuma kallon kansa a madubin,sosai fuskarsa ta wadatu da murmushi,musamman idan ya tuna abubuwan da suka faru a wunin yau din,gaba daya dukkan wata matsala tasa ta warware cikin ikon Allah,abinda ya rage masa a yanzu kawai shine yadda zaiyi da jawahir ya badda mummunan labari a kanta,don ko shari’ar gidan masu tabin hankali a dazu da safe aka qareta,kyauro da sauran mutum uku da suka taimaka masa wajen ajiyar momma na wadan nan shekarun,an yanke musu hukuncin daurin rai da rai.
Sake murmusawa yayi da ya tuna yadda hajiya qarama ta tubure haiqan da gaskiya aka baro momma sashen daddy,duk da kuwa itama tuburewar da taso yi,saidai rigimar hafsatun tata tafi tata girma.
A yau komai ya kawo qarshe,ya tabbata kaltum ta zama tasa,wadanda ya kamata su sani sun riga da sun sani,sun karba su lamunce masa,iya wannan kadai idan ya tuna yana sanyashi nishadi.
Da fari tausayin kaltum ya fara,bai sani ba so ashe yana farawa daga tausayi,ya fara sonta ne ba tare da yasan sonta yake ba,ya aza cewa tausayinta da tausayin rayuwar da suke ciki yake yi,da kuma sabo da sukayi da da uwanta bilal.
Ja da baya yayi,hakanan yaji a daren nan gangar jikinsa tana buqatar jin duminta,sai ya bude ma’ajiyar kayansa,wadda taci cupboard guda,ya lalubo wasu pyjamas farare qal masu budadden qirji ya sanya,ya feshi jikinsa da lallausan turarensa na bacci,sanna ya zura wasu slippers na fata ya dauki wayarsa ya baro sashen.
A hankali ya tura qofar dakin nata,babu haske kwata kwata sia qamshin dake tashi,da alama ta jima da kwanciya,don lokacin da ya kunna fitilar wayarshi ya hangeta ne duqunqune cikin bargo,kyakkyawar fuskarta ta haska tarwai cikin milk din duvet din da take ciki,sai ya maida qofar,ya taka har zuwa bakin gadon.
Da qaramin haske yayi amfani ya kalli fuskarta son ranshi,murmushi kwance saman fuskar tasa,saboda tunawa da wasu abubuwa daya dinga yi a kanta,wamcan lokacin da ya fara ganinta,cikin qauyensu,a yanzun sai yake ganin kamar ba ita ba,komai dake tattare da ita ya canza.
Jan bargon yayi a hankali ya sauko zuwa saman cikinta,ta sake bayyana sosai cikin kayan baccin da suka kwantawa fatarta,sai ya kasa daurewa,ya raba ta bayanta ya kwanta a jikinta tare da sake jawota cikin jikinsa sosai yana sauke numfashi,abinda ya farkar da ita kenan a tsorace
“Shshshsh….. mijinki ne, keep calm sai tayi shuru tana sauraren bugun zuciyarss dake fita da sauri da sauri.
A hankali ya zura hannunsa saman fatar cikinta ta qasan rigarta,ya fara yawo dashi,abinda yaso tafiya da numfashinta kenan,ya kuma qara bugun zuciyarta,saita riqe hannun nasa jin yana son zarcewa zuwa sama,bayan ta tabbatar babu bra a jikinta,da ya gota din kuwa tasan koma meye zayaji shi.
Cikin kasala ya girgiza kansa
“No….dan kadan please….nima na dana,karki hanani,nafa yi qoqari,ba wani abu bane me yawa…. please” ga tsoro ga kunya,saidai cikij wani salo dake nuna qwarewa a iya tafiyar da tattausar soyayya mai narkar da xukata,ya dinga karantar da ita wasu darussa masu wuyar mantawa,ya kaita duniyoyi da babu komai cikinsu face zallar farinciki da masoya ke tsinta a cikinsa,sunyi musayar kalamai,yadda ya fallasa a sirin zuciyarsa a gareta,hakanan bai qyaleta ba itama sai da ta fidda masa dukkan wani sirri dake ranta,ya jita a jiki da zuciyarsa sosai a ranar,da quar ya iya qyaleta bau zarme ba zuwa next level ba,saidai kuma ya qare da ciwon mara sosai,wanda bai sakeshi ba sai gab da asuba.
Tunda ya fito daga wanka yake son su hada ido amma taqi,sbaoda wani nauyinsa da ya dora mata,ya kaita makarantar da bata taba leqawa ba,saidai ta samu tarin karatu da ilimi,ya kuma sake loda mata soyayyarsa ninkin baninkin.
Allah Allah take kawai ya fice daga dakin,kada wani cikin jama’ar gidan ya ganshi ya gane a nan ya kwana,amma sai ta lura shi kam ko a jikinsa,sabgarsa yake hankalinsa kwance
“Ki daura alwala muyi sallah” ya fada yana shimfida abun salla tare da cije dariyarsa,saboda yana son yaga qarshen pretending dinta.
Baki tadan turo gaba,ta tsammaci xai fita ne ya barta,saboda maganar Allah tana kunya yaga tayi wanka a gabansa.
Daga kai yayi yana dubanta,sai tayi maza ra runtse idanunta,ya saki lallausan murmushin nan nasa,sai ya miqe daga sunkuyon da yayi,ya soma takawa zuwa inda take zaune ta nade dukka jikinta da duvet,saboda yadda ya yamutsa gaba daya kayanta.
Dan zabura tayi sanda ta jishi gab da ita,a dole ta juyo ta fuskanceshi,gashinta daya gama yamutsewa ya rufe fiye da rabin fuskarta
“Don Allah…..zan tashi,amma kaje……momma fa?” Murmushi ya sake,tana qara yi masa kyau,sai yakai hannunsa a hankali yana janye gashin nata zuwa baya,hakan ya baiwa fuskarta damar bayyana sosai,yakai idanunsa kan lips dinta wadanda suka danyi ja,yasan kuma hakan xafa faru,saboda ya tsotsesu son ransa
“Momma ma wajen daddy ta kwana,so kada ki wani damu…..ya kamata ki cire wannan kunyar kwata kwata idan kina tare dani,ni mijinki ne kamar yadda kike matata,halal muke ga juna,amma ban sani ba,ko sai ni da kaina na qarasa cire miki ita gaba daya a wuce wajen ne?” Yayi maganar yana sake matsota,abinda yasa taja baya da sauri,ba shire ta sauka daga gadon sai bandaki.
Bin bayanta yayi da kallo kamar wani zautacce,sai kuma murmushi ya subuce masa,yasa hannu saman kansa yana shafa sumarsa,idanunsa a lumshe yana tuna daren jiya,yana kuma jin yadda alwalarsa ke karyewa,saiya daura sabuwa kenan.
Tun bayan futarsa ya barta kwance cikin bargo bacci ya qauracewa idanunta,kamar yadda murmushi yaqi barin fuskarta,ashe haka soyayyar miji da mata take da dadi da kuma gardi?,duk inda ta juya a kaf fadin gadon qamshinsa ke tashi,ta rasa da wanne irin maye turare yake amfani,ya tafi ya bar mata qamshinsa,tasan kuma shine zai hanata sakewa.
Ajiyan ya dasa abubuwa masu matuqar qarfi cikin zuciyarta,saidai wasu guraren a jikinta radadi suke mata,saboda saqonnin data karba masu zafin gaske daga wajen sarakin,ashe a baya yadda take jinsa a ranta wasa ne farin girki inji hausawa.
Gyara kwanciyarta ta sakeyi a karo na barkatai,saidai saukar sautin kuka daga can waje ya sanyata tsaiwa cak,kafin ta samu kanta tana dirowa daga gadon ba tare data shirya ba,bata tsaya neman dankwali ko hijabi ba,daga ita sai doguwar rigar atamafar da sarakin ne ya zabo mata ita kafin ya fita tayo waje,saboda muryar jawahir takeji.
Kafin ta isa har samir hajiya qarama da momma sun rigata isa wajen,sai securities su biyu dake tsaye a can bakin qofa,daga gefe kuma yadikko ce da amiru.
Momma da hajiya qarama ke riqe jawahir din,wani irin kuka take mai ban tausayi,tana sulalewa qasa suna dagota,jiki da qafafuwan kaltum sukayi sanyi,hawaye ya balle mata,bisa dukkan alamu labari yaje kunnnesu,dama kuma zancan duniya baya buya,duk kuwa yadda kakai ga son boyeshi,sai ta kasa tsaiwa,ta nufi jawahir din da hanzari,tana ganinta itama ta nufota suka rungume juna,suka sake sakin sabon kuka.
Samir ne ya qaraso wajen a hankali ya rabasu,sannan ya kama hannun kaltum,zai kama na jawahir ya tuna a yanzun haramunne aikata hakan,sa ya yiwa hajiya qarama alama da ido,ta kamo jawahir din suka nufi falon gidan gaba daya,banda securities da sukaci gaba da kula da gidan.
Sun jima zaune cikin falon wanda yake shuru,bakajin sautin komai sai na kukan jawahir,babu wanda ya hanata kuka kamar yadda babu wanda ya hanata fadar dukkan abinda ke ranta,kalamai ne da suka sanya kowa kuka a wajen sosai,har da daddy da ya fito daga baya
“Ashe ni din ba kowa bace face wulaqantacciya wadda ta fito ta qazamar hanya,ashe bani da wani cikakken asali?,ashe ni da najwa ba mahaifinmu daya ba?,ashe ya saraki bamu hada alaqar komai dashi ba?,me yasa mommy bata tsaya ta haifemu wajen nagartaccen mutum irin daddy ba?,me yasa ta yiwa Allah shishshigi?,bata tsaya mun fito ta tsatson daddy ba?,tayi gaggawa taje ta haifemu daga wani tsatson na daban?,yanzu ace har bushewar zuciyar ya najwa yakai ta cakawa mahaifiyarta wuqa?,wannan wanne irin bala’i ne?” Sosai tausayinta ya cika zuciyar momma,ta matsa kusa da ita ta rungumeta sosai cikin jikinta,tana bata kalamai na ban haquri da yarda da qaddara
“Ni din ki daukeni tamkar mahaifiyarki,daddynku kuma har abada daddynku ne,babu me canza muku wannan” cike da mamaki ta daga ka daga jikin momma din ta dubeta
“Yanzu bayan dukka abinda mummy tayi miki har zaku iya ci gaba da riqeni?” Murmushi momma tayi,tausayin yarinyar na sake ratsata,saboda ta tabbatar nagartacciya ce saboda yadda kowa ke yabonta,tare da kaffa kaffar kada taji al’amarin
“Qwarai kuwa,ke din diyarmu ce halak malak” saita sake fashewa da kuka,wanda daga baya ta sassauta saboda kalaman ban baki data dinga samu daga wajen kowa,kukanta ya koma ajiyar zuciya.
A sannan samir ya miqa hannunsa ya matsa hannuwan kaltum,tadan dubeshi kadan,qasa qasa yace da ita
“Ya isa….kukan ya isa haka,ki adanashi,kada ki rasa na first night” kamar qasa ta tsage ta shige haka taji.
Ido suka hada da amiru,sai ya sakar masa wani kallon tsokana,dauke kansa yayi bayan ya maida masa da harara
“Idan kina fitowa irin haka,zuciyata zata iya bugawa” da sauri ta daga kai ta kalleshi,saiya wara mata idanunsa sosai yana gyada kai alamun tabbatar mata
“U have no idea how much I love you…..but the time will reveal,jeki nemo hijabi” abinda ya sanyata miqewa a kunyace zuwa daki,sai ya dubi jawahir
“Auta bita kuje,karki sake kuka,ki dauka kamar komai bai taba faruwa ba”
“To” ta amsa a matuqar karye
“Promise?” Ya sake cewa da ita,saita gyada kai tana qoqarin maida qwallarta,fuska yadan bata
“No,ki bude baki ki amsa min” murmushi ne ya taho mata mai hade da hawaye,har yanzu da gaske yana nan a matsayin yaya sarakinta,babu abinda ya canza
“Yes yaayaaa” ta amsa masa da yanayin da aca baya take amsa masa,abinda ya taba zukatansu gaba daya
“Good girl” ya fada yana qoqarin boye rauninsa,suka bita da kallo gaba daya sanda take tafiya zuwa dakin kaltum.
A nutse ya faka motarsa a harabar asibitin,wanda suka dauko jawahir da dukkansu sukayi amannar taje taga mahaifiyarta,shi da kaltum ne zaune a gaban,yayin da amiru da jawahir din suke baya.
Sai da yakashe motar sannan ya waiwaya yada dubeta
“Duk abinda ta aikata miki mahaifiyarki ce,she need your respect,sannan idan kika shiga kika zauna kina kuka?,ki tabbatar bazan sake barinki zuwa ba, understand?” Kai ta jinjina tana boye qwallarta
“Ok” ya fada,abinda yasa amiru bude side dinshi ya fito,itama jawahir din haka.
Caraf ya kama hannun kaltum itama dake qoqarin bude nata side ta fita,ya manne tafukan hannuwan nasu waje guda,dumin jikin kowannensu yana ratsa jikin dan uwansa
“Ina zaki madam?”
“Zan raka jawahir” wani narke mata yayi,tamkar dan yaye
“Haba madam…..wannan wata dama ce fa,da mun koma gida shikenan za’a sanya mana ido,don naji hajiya qarama daxun ta fara wasu maganganu…..” Qasa yayi da muryarsa
“Please,abun jiya za’a dan sanmu na qara ɗanawa” idanu ta fitar waje gaba daya,amma ganin yadda ya tsareta da nasa idanun masu tsananin kaifi saita sauke nata qasa
“A waje muke fa” tana rufe baki taga motar ta soma duhu,saita daga kai da sauri,ashe danne madagar gilasan motar yayi gaba daya,saidai bai juya ba still ya tsareta da idanuwa ne,gilasan kuma sunayin sama har suka gama rufewa ruffff.
“Yanzu fa?” Ya jefe mata tambayar yana sake jifanta da wani tsumammen kallo,saidai kafin takai ga bashi amsa ma tuni ya hade tazarar dake tsakaninsu.
Da zafi zafi yaji ana knocking glass din motar,ya zare jikinsa a galabaice yana duban wanda ke bugun glass din,amiru ne,bai sauke ba sai daya tabbatar ta gyara daurin da kwalinta,ya gyara xaman rigar jikinsa,sannan ya dauki ruwan dake ajjiye kusa dasu ya bude ya kafa kai ya fara kwankwada,zuwa sannan amirun harya qagauta,ya zagayo ta gaban glass din motar yana duban samir,wanda baiyo ko darr ba sai daya gama shan iya yadda zai iya ya miqawa kaltum sauran sannan ya sauke glass din
“Kaima fa dan iska ne da alama inda ka samu waje….ka fito mummy nason ganinka urgently, she’s in serious condition,da gaske nake,jawahir ta kasa riqe kukanta,ni kaina na kasa controlling nata please……” Da sauri ya buda murfin motar ya fito,sannan ya zagaya ya budewa kaltum,ya riqeta sosai cikin hannunsa suka fara takawa zuwa cikin asibitin,kome zaiyi zaiyi ne saboda jawahir badon mummy ba,don ko sau daya a rayuwarsa baya buqatar sake ganin fuskarta indan ta shine.
Duk wanda yaga mummyn yasa a gargara take,banda gursheqen kuka babu abinda jawahir keyi,shigowar samir gaba daya hankalin mommy ya karkata a kansa,saidai duk yadda taso bude baki tayi masa magana abun ya gagara,’yan maganar sun tafi,kalamanta na duniya sun gama qarewa,sai jawahir ta hau girgizata
“Mommy na yafe miki,ga ya sarakin,kice su yafe mikin…..ki fada musu” gaba daya jikinta ne ya saki cikin yan qananun daqiqu,taja wata qatuwar shaquwa me qarfi,abinda ke alamtawa duk wanda ke dakin cikawarta,bayan likitoci sun duddubata suka tabbatar masu da hakan.
Kuka sosai kaltum itama ta saki,mutuwar bilalunta ta zamar mata sabuwa,mikin dake zuciyarta ya dawo sabo,kama hannun samir yayi ya maidata mota ya zaunar ita da jawahir,ya bar amiru ya kula dasu,ya koma cikin asibitin,ya biya dukka wani bill nata dana sauran jama’ar dake dakin,wanda dama ya saba hakan,kusan dabi’arsa ce,bawai yayi ne kawai don ita kadai ba,yayi ne saboda Allah,yayi ne kuma saboda ranar gobe.
********Cike da farinciki take hada kayanta cikin wani qawataccen akwati,duk da cewa tana qoqarin danne farincikin nata saboda ta yiwa jawahir dake zaune a gefanta kara,wadda a jiya akayi addu’ar bakwai na rasuwar mummy.
Bayan shafe watanni masu tsaho da yawa,sai gashi a safiyar gobe zata sauka garinsu na dinya,zata yi tozali da ummanta,zataga habiban ta,yakumbo indo kawu ado umma suwaiba sai kuma lantana,wadan nan kusa sune mutanen da take muradin gani kaf fadin qauyen dinya,masoyan da bata da tamkarsu,ji take a goben kamar zata tafi saudiyya ne aikin hajji.
“Nayi mamakin yadda kika iya jarumta da qarfin hali…..wadda keda miji kamar ya saraki…..amma kika zauna a wancan lokacin ‘yammata na miki farautarsa?,bansan baki da wayo bafa sai da nasan cewa yaya saraki mijinki ne” ta tsinci dakusashshiyar muryar jawahir na fada sanda take zuge jakarta.
sakin aikin tayi,ta juyi fuskarta dauke da fara’a tana kallon jawahir dake zaune saman abun sallah,sanye da hijabi,gefanta alqur’ani ne data gama karantawa,tayi matuqar jinjinawa gami da sarawa dauriyar da jawahir ta nuna,idan ka ganta a yanzu,zaka tsammaci ba itace wadda abubuwan nan suka faru da ita ba,saidai tayi imani da cewa QUR’ANI WARAKA NE kuma ambaton Allah shike sanyawa zukata nutsuwa,tun daga ranar kullum sai kaltum ta yiwa jawahir tofi a ruwa ta bata tasha,daga qarshe sai ya zama ma tofin ne ruwan shanta,bugu da qari da qur’ani take wuni a hannunta,tunda ta samu izifi me yawa a wajen kaltum din,sanda suke musayar karatu da ita,sannan idan xasu kwanta dashi suke kwana cikin wayar jawahir din.
Gefan jawahir ta dawo ta zauna tana murmushi
“Ban taba kawowa cewa akwai randa zatazo da zaya soni ba,ban taba hada kaina dashi ba,saboda nasan akwai tazara me tarin yawa a tsakaninmu,nafi kowa sanin cewa ceto ne yasa ya aureni bawai soyayya ba,amma a yanzu…..banajin akwai wadda zan iya barwa shi” murmushi jawahir ta saki
“Koni bazan bari ki barwa kowacce mace shi ba,saboda ke kikafi cancanta…..” Tsagaitawa kadan jawahir din tayi
“Inaji a raina inama ace nice ke?,inama ace cikin tsanani irin naki na taso?,a yanzu rayuwa tayimin kyau kamar haka?” Qwalla ta cika idanunta sanda takai qarshen maganar.
A tausashe kaltum ta dafa kafadarta
“Ki godewa Allah da yayoki musulma,cikin al’ummar annabi muhammad…..ya kuma barki da imaninki…..sannan ya hadaki da mutane irinsu daddyn,da Allah yaso sai ya halicceki akuya ko tunkiya ko kuma zaki,ko ya halicceki kafura,kinga ko iya wannan ni’imace,duk wani yanayi da dan adam yake ciki mai gushewa ne watarana,a shekarun baya sanda nake cikin tsanani nida mahaifiyata da dan uwana,ban taba kawo cewa watarana komai zai wuce ba,to kamar hakane….kema wataran zakiga kamar komai bai faru ba”
“In sha Allah” ta amsa tana dauke qwallarta,sannan ta miqe ta ciro wata jakarta,ta dawo ta zazzageta,kudadene suka fado masu yawa,kusan dukka sababbi ne,saita tura gaban kaltum
“Kudaden break dinki ne da yaya saraki yake bani na baki,tun sanda kika fara zuwa makaranta wadanda baki taba amsa ba,dama ya gayamin gasunan na baki,amma bai sani ba…..ba lallai bane ki amsa,saboda bakison sababbin kudi bakya amsarsu…..” Ta qarashe maganar qaramar dariya na kubce mata,tayata kaltum din tayi sannan tace
“Bari na baki labarin abinda ya sanya yake tsokanata har yau” tiryan tiryan ta gaya mata,abun da ya sanya jawahir din dariya sosai,ganin labarin ya sanyata nishadi,sai taci gaba da bata wasu labarai na wautarta sanda take a matsayin kattume,har zuwa sanda wayar jawahir tayi qara ta daga tayi magana ta sakanni sannan ta sauke
“Kije ya samir yana kiranki” miqewa tayi tana laluben hijabinta
“Bari naje na dawo na qarasa baki labaran” harara jawahir ta jefa mata
“A haka ake zuwa turakar mijin?” Saita miqe tana qwace mayafin,ta kama hannunta zuwa gaban madubi,duk da jikinta tashin qamshi yake,don bata jima da fitowa a wanka ba,amma sai da jawahir ta sakeyi mata wankan turare tun daga gashinta har qafafunta
“Duk inda zai shanshana yaji qamshi…..kuma karki dawo min,kawai kice min sai da safe” ta fada tana jefa mata wani farin mayafi mara kauri instead of hijabin data saka dazu.
Sakato tayi tana duban jawahir sanda take komawa saman abun sallarta tana zama
“Amma qamshin nan yayi yawa,zan keta ta falo ne fa,yanzu idan na hadu da daddy ko momma fa nace meye?”
“Haram ne?,wurin mijinki zaki fa,lada zaki samo….”kafin takai qarshe wayarta ta sake tsuwwa
“Ki rufan asiri ki tafi,Allah shine yake sake kira” dariya ma jawahir din ta bata,yadda ta hade hannayenta waje daya tana roqarta,saita yi gaba a hankali ta fice,tausayin jawahir din na sake cikata,ta samu zuciyarta da yi.mata addu’ar samun miji nan kusa da zai zame mata sanyin idaniya itama.
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_DA ZAFINSU_*
*_A TSARE SUKE_*
*_SUN TANADESU_*
*_CIKIN SALO NA HIKIMA DA BAN SHA’AWA_*
*_ƘAWATATTU kuma ZAFAFAN DOCUMENTS HAR GUDA 25 na ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR da aka tanadar muku dasu_*
*_tun daga batch 01 har batch 05,duka bisa farashin rangwame_*
*_MAZA TUNTUBESU TA WADANNAN LAMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA_*
_WADANDA SUKESON TURAWA TA ACCOUNT SU YIWA WANNAN NUMBER WAYAR MAGANA_
08184017082
_MASU TURA KATIN WAYA KO VTU KUMA_
09134848107
*_TARON GAMAYYAR ZAFAFAN MARUBUTA…..MASU ZAFAFAN ALQALUMMA_*