Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 34

Sponsored Links

34

Kamar wadda ta tashi jinya haka take tafiya salalo salalo zuwa sashen kawu iliya,hannunta dauke da botikin qarfen inna laure da umma ta bata takai mata,yara suka kawo nan sashen ta suka ajjiye.

Sau biyu tana sallama,saidai kallo daya asiya dake tsakar gida saman kujera ‘yar tsuguno fesa kwalliya tayi mata ta baiwa banza ajiyarta taci gaba da kwalliyarta,tana sa ye da wani tsalelen lace,har sai da inna laure dake daki ta fito,tana sanya slippers dinta da asiyance ma ta siya mata

“Au…au ashe amarya ce,amarya manya,amarsu kin sha qamshi,amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida” kamar hadin baki sai suka kwashe da dariya gaba dayansu,asiya ta fara tsaida tata dariyar

“Ni wallahi Allah har mamaki nake ma yadda kattume ta fito tatsatsanmu,kaf yaran gidan nan babu wanda ya kaita baqi da muni,kiyi haquri fa gaskiyata nake fada,koda yake ma ke da kika kusan tafiyarmi gidan miji….au na manta ban miki Allah ya sanya alkhairi ba,kada ace kana baqinciki,duk da ma kafi qarfin ka yiwa mutum baqinciki,Allah ya sanya alheri,ya kawo tsala tsalan yara” dariya suka sake kecewa da ita

“Ga munu ga talauci,ta ina tsala tsalan yara zasu samu?,don nasan duk wanda ya dauketa dai ajin rayuwarsu daya,tun daga suffa zuwa wadata,ai yara tsala tsala saiku a gidan alhaji uba” farrrr asiya tayi da idanu,kafin su sake cewa wani abu kaltum ta ajjiye botikin ta juya da hanzari,duk yadda taso maida amsa amma ta gagara,kalamansu sun mata muni sosai da bazata iya juresu ba.

A qafa suka tako shida amirun,tun daga makarantar har zuwa qofar gidansu kaltum,amirun yanata mitar yasa takalmansu duk sunyi qura,me yasa bazai bari a qaraso dasu a mota,bai kulashi ba har suka qaraso qofar gidan.

Qarqashin bishiyar dake basa iska a wajen ba kowa sai kawu ado da babban dan yakumbo indo,a nutse suka qarasa da sallamarsu,saiya miqe daga kashingidar da shi kawu adon yayi ya zauna sosai yana amsa sallamar,tare da basu damar zama.

Takalmansu suka tube sannan suka zauna din,sukayi musabaha mai cakude da gaisuwa ya amsa musu,shuru ya ratsa na sakanni,sai amiru yace

“Wajen mai gidan mukazo”
“Wanne daga ciki?”kawu ado ya tambaya yana kallonsu sosai,sabida baqin fuska ne a wajensa

“Baban kal…..kal” samir ya fadi yana kakarewa,saboda son tuna sunan da yake qoqarin yi

“Baban kaltume?” Kawu ado ya qarasa masa,sai amiru ya gyada kansa yana cewa eh

“Ko kaine mijin kaltumen?” Kawu ado ya tambaya yana duban amiru,sai yadan daririce,hakan yasa samir ya nuna kansa

“Nine” kallonsa ya dauke daga kan amiru ya maida ga samir yana qare masa kallo,gami da fadin

“Ma sha Allahu,sannunku dan samari,dama ina bidar ganinka kuwa” kawu ado ya fada yana gyara zamansa sosai.

Kwarjini yadan yiwa samir din ganin yadda kamalarsa ta sake fitowa bayan ya zauna sosai yana fuskantarsu,sai shima ya gyara zamansa yana cewa

“Ma sha Allah,nima magana ce ke tafe dani dama”

“To bismillah mana” kawu ado ya bashi dama

“A’ah baba,ba damuwa,ina saurarenka”.

“To alhmadlh,nasan dai baka sanni ba,bakuma kasan alaqata da kattume ba,kattume kamar diya take a wajena,diyar yayata ce,banu wani boye boye a tsakaninmu,tunda an riga da an zama daya,duk da dai kai din da alama baquwar fuska ne,to amma kattume marainiya ce duk da tana da uba,sannan ita da dan uwanta gaba daya rayuwarsu ta kawo yadda take akaine a yanzu aboda huwacewar ubangiji kawai,yarinya ce da gwara wani marayan da ita,don Allah,don son annabi,ka riqeta bisa gaskiya da amana,saboda tasha wahalar rayuwa,tun batakai haka ba take ci da kanta danuwarta dama qannenta,tana buqatar matallafi,tana buqatar bangon da zata jingina dashi,munso yi mata hakan,amma bamu samu hadin kai daga wajen ubanta ba,sai muka rakata da addu’a,saboda munsan cewa ita din diya macace,kuma komai daren dadewa zata samu miji ne tayi aure,wala’alla wannan shine silar hutawarta daga dukkan wani qunci da matsi,ka duba darajar fiyayyen halitta kayi mata ruqo na mutunci da adalci…..kai din asalin da inane?” Ya zarce da tambayar samir,bayan yakai qarshen kalamansa da suka sauke duk wani shiri na samir din ba tare daya shirya hakan ba,ya buda baki da niyyar magana hayaniyar yaran data tunkarosu ta mamaye wajen,hayaniyar taja hankalinsu,ya daga kai yana duban yaran da suka taso wani saurayi a gaba

“Kaga da wanda akayi shirin bata nan,Allah ya dubu irin maraici da girman biyayyarta ga mahaifiyarta ya musanya mata,tunda kai din muna kyautata maka zaton alkhairi”

A hankali ya daga idonsa yana dubansa,shine wannan saurayin daya kubutar da ita daga hannunsa

“Meye alaqarsu?” Ya samu kansa da tambayar kawu ado sanda yaga auwalun ya shige cikin gidan,bayan badaru dan yakumbo indo ya kora gayyar yaran

“Dan qanin babanta ne,kuma ba haka suka so ba,don ko a yau auren kattume ya mutu sai sunsan yadda sukayi suka liqa mata shi” ya fada cike da takaici,shuru yadan sake giftawa,saiya sake maimaita tambayarsa

“Yaro dan inane kai?” Kansa yadan saddar qasa,yana tunanin yadda zai yiwa mutumin dake a karkara irin wannan bayanin mahaifinsa

“Ni dan garin azaren jihar bauchi ce,amma kuma a kano nake zaune,anan na taso”

“To…to ma sha Allah,to ta yaya yaro zamu iya samunka kenan?” Shuru ya sake biyo baya kafin ya samu abun fada

“Unguwar makwarari,duk wanda ka tambaya gidan malam nura zai kaika,ka cewa malam nura kana neman samir ko saraki,zai kawoka inda nake”

“Samir,saraki….to to….to shikenan,babu damuwa” ya fada yana jin gamsuwa a ransa,bayan ya hada wannan bayanan,da kuma bayanin da malam amadu yayi masa a tsaitsaye kan cewa su aka turo sukayi ginin makarantar da ake budewa yau,haka kawai yakejin wata gamsuwa da nutsuwa kan yaron,yasan unguwar daya fada din,yakan shiga cikin gari,kuma yana da abokima a anguwar,dake zuwa sari wajensa duk qarshen wata na kayan hatsi.

“To malam samiru banji naka batun da kazo dashi ba”.

Shuru ya danyi,yana jin dukkan wani bayani da quduri nasa da yazo dashi yana saraya gami da bin iska,tamkar bayanin da kawu ado yayi masa ya warware komai daki daki ne,sai yaji nauyin mutumin,a yadda kamalarsa take,da irin roqon daya dinga masa da fatan alkhairi,yanzu shi kuma ya buda baki yace yazo sakin diyarsa ne?.

Muryar malam amadu ta ratsa tsakiyar tunaninsa ta tsinka zaren

“Tun yaushe kuka iso malam muhammadu?,kada dai ace daukar yarinyar nan kukazo yi aka barku a nan?” Kallon takaici kawu ado yake bin malam amadu dashi,shi sam.bai damu da sanin komai akan yaron ba?,sai qoqarin cusa masa yarinya yake kamar yar tsuntuwa ba diyar cikinsa ba

“Amm….malam amadu,ni a ganina daukar yarinyar nan yana da buqatar nutsuwa ko kuwa?” Dubansa yayi

“Wacce nutsuwa kuma?,bazai wuce kuce siyayyar kaya ba,yo ku basu kudin kayan mana,sayi siyayyarsu su siya abinda ransu keso,kabar yaro ya dauki matarsa,daga baya maje muga waje” .

A sannan inda ya lura da kyau wani kallo samir ke binsa dashi,ya yadda ya amince ya kuma yi imanin lallai yarinyar batayi sa’a da kuma dacen uba ba,yasan tsaf zai bata ran kamilin mutumin da ya shaida musu suna kawu ado,don haka ya shiga maganar

“Kawu,inaga a barta din kamar yadda kace,idan naje gida na dawo sainazo na dauketan” murmushin takaici kawu ado ya saki

“Babu komai malam samir…..bari amusu magana,ku tafi din,Allah ya tsare hanya,ya baku zaman lafiya” kafin ya dire wannan kalaman ma tuni malam amadu yayi ciki,ransa a bace yana mitar ana shiga gonarsa,shida iyalansa amma ana musu shishshigi?.

Yasan komai yana iya faruwa a cikin gidan,don haka da murmushi saman fuskarsa ya miqe

“Ina zuwa,kuyi haquri don Allah bari a fito da ita,kunsan sha’anin mata,kada suje su bata muku lokaci” a hankali amiru ya gyada wuyansa da yakeji kamar an sauke masa guduma,yayi alamar to,yabi kawu amadu da kallo sanda ya shige cikin gidan yana saba babbar rigarsa.

Sai daya shige ya maido dubansa ga samir,magana yakeson masa amma wanzuwar badaru a wajen ya hanashi magana,bashi kuma da tabbacin ko yaqinin baya jin turanci ko qanqani bare ya juya harshe,saboda ya ganshi fes dashi fiye da yanayin sauran samarin qauyen,yasan kuwa bazai rasa karatu a tattare dashi ba,sai shuru yaci gaba da sukwane musu lokacin,amiru cike da mamakin samir din daya ruguza duk wani abu da yace masa zai aiwatar,kuma ko sau daya bai kalleshi ba bare yayi masa nuni kan ya taso su kebe suyi magana kafin a kai ga fitowa da yarinyar.

Tana daga dakinsu,amma sallama guda daya tak ta mahaifinsu ta haifar mata da wata mummunar faduwar gaba data hanata zama,saita miqe tsaye cak ta tsaya sanda taji yana maganarsa gaba gadi a tsakar gida

“Ke zuwaira..…ku shirya yarinyar nan,mijinta yana waje yana jiranta zasu tafi,kuyi maza maza ku hanzarta” a hankali ta daga kai ta dubi mijin nata,tana jin yadda zallar rashina adalcinsa yakai mata ko ina ma rayuwarta,bazai sauya ba,babu abinda zai sauyashi,saidai ta sani cewa ta roqi Allah,koma meye zai shigo rayuwar kaltum din yazo mata da sauqin da babu wanda ya zata a cikinsu

“Dake fa nake magana,ku hanzarta da Alla kada kubar mutane suna jiranku” daga haka ya juya hankalinsa kwance ya nufi cikin dakinsa.

Tsam ta miqe daga durquson da tayo gaban murhu tana shirya itace,saboda girkin da takeson ta dora musu,sakamakon yadda kaltume din gaba daya ta koma bata iya tsinana komai,mayafinta dake kan igiya ta janyo ta sanya,sannan ta kutsa kai ta fito ainihin babban tsakar gidansu.

Tana niyyar zarcewa zuwa waje tanimu dan maqotansu daya fito daga sashen inna laure ya fito

“Yauwa tanimu,leqa daga waje qofar gida,idan kaga baqin fuska kace musu anason magana da mijin kaltume” tace da yaron

“Nama sanhi ai,ogan ginin makarantar mai tafasa ne”ya amsa mata,saita dafa kansa

“Yauwa,yi maza ka kiramin shi” ya cilla kuwa da gudunsa yayi waje,yayin daya barta da juya maganar tasa,indai hakane kenan yana nufin uban gidan su bilalu ne?,ya akayi har yaje ya karbi auren kaltume da hannunsa da kuma amincewarsa?,tambayar data tsaya mata kenan a rai.

Dan jim samir yayi yana juya kiran da aka masa daga cikin gidan,yana kuma jinjina kalmar mijin kaltume da aka kirashi dashi,sai yaji kalmar shi kansa tayi masa nauyi qwarai,sai kuma ya miqe yana zura takalmansa,cikin tafiya ta nutsuwa ya kutsa kai cikin soron,yana kallon zaizayayyar katangar gidan,yana sake girmama ubangiji da yayo mu mabambanta,hakanan ya bambanta mu cikin rayuwa wadata da samu da kuma jin dadi.

Tunda ya doso soron ta zuba mishi idanu a fakaice,tabbas shi dinne,duk da gani daya tak ta taba yi masa amma ta shaidashi,duk wani karatu irin na hankali nazari da kuma lissafi daya kamata kayi akan mutum tayi namijin qoqarin yi a kansa kafin ya cimmata.

A zahiri bata ga wata siffa ta tawaya ko siffar da zata nuna maka cewa akwai wani matsala dangane da dabi’a da kuma halayyar mutum ba,duk da kuwa cewa bawai ta sanshi bane sani na dabi’a da halayya ba,to amma kuma….data dauko wanna nazarin ta hada da labarai da bilal je basu a lokacin da yake raye dangane da halayya da dabi’unsa,sai taji wani sashe na zuciyarta yana mata sanyi da haske,duk dadai ta hangi tarin tazara da kuma bambanci a tsakaninsu,ta kasa jin nutsuwar cewa shida kansa ya zabi diyarta kaltume,ba zata bari ta yaudari kanta ba,wannan sam baiyi zubi ko suffar irin mutanensu ba,akwai alamun tazara da bambancin duniyar rayuwa a tsakaninsu.

Shuru ne ya ratsa tsakaninsu bayan gaisuwar data gilma,umman ta tattara dukkan kalaman bakinta sannan ta motsa cikin yanayi na nutsuwa irin na uwa

“Duk da cewa babu wanda ya gayamin ko mukayi maganar dashi,amma zuciyata ta kasa yarda gasgatawa ko kuma gamsuwa akan cewa kaine da kanka ka zabi kaltume na amatsayin matar da zaka aura,banbamcin yanayi da kuma yadda aka bada tallanta ko ince sadakarta ya gayamin haka,zuciyata tafi gayamin cewa……ka karba auren kaltum ne saboda wala’alla tausayi taimako ko kuma wani abu daya shafi hakan,toh….koma meye,nidai zan roqeka,koda ka auri kaltum ne don ka nesantata da rayuwarmu zuwa wani lokaci,zan gode maka,aqalla zata samu wani sukuni na taqaitaccen lokaci da muka gasa samar mata….zan kuma roqi alfarmarka akan ka riqemin ita amana,ka kulamin da rayuwarta,nayi yaqini da kuma imani da Allah,tunda har na roqeshi,na kuma nemi zabinsa,toba shakka abinda ya aiwatar a yanzu akan kaltum dai dai ne,kuma ina saka ran alkhairi ne ga rayuwarta,ban damu ba,koma daga ina kake?,koma daga ina ka fito,nasan cewa ubangiji baiyi koma meye ba domin wofantar da addu’ata ba,ALQAWARIN ALLAH NE cewa,bawansa bazai taba daga hannunsa ya roqeshi ba,shi kuma ya dawo masa da hannunsa haka ba tare daya amsa masa ba,ko a kusa,ko a nesa,kaje da kaltum amma bisa ruqo na amana”.

Kowanne gefe idan ya juya sai yaji ya kasa amayar musu da dalilin xuwansa,baizo don ya tafi da diyarsu ba,yazo ne saboda ya warware igiyar data dauru a kanta dalilin amiru,amirun dashi kansa ya aiwatar da komai bisa wasa,wasan da yayi kama da ganganci sak!.

A hankali umma ta yaye labulen dakin,zuwa sannan ta jima ta suman tsaye,fuskarta tayi sharkaf da hawaye,tamaqale jikin bango sai kace mai shirin tsagashi ta wuce ta ciki.

Tun umman bata qaraso ba ita ta isa gareta a sukwane ta fada jikinta

“Ummanmu…ummanmu” sai kuma ta kasa furta komai,cikin wata irin dakiya tace

“Ya isa,a ko ina kike Allah yana tare dake,hakanan kina tare da addu’ata da izinin ubangiji” data daga kai ta kalli ummantata,sai dakiyar umman ta bata tsoro da mamaki,ta bita da kallo sanda take isa inda take tara kayan sawarta ta fara hada mata waje daya

“Ummanmu,bamuyi sallama da habi ba” ta fada hawaye yana sulmiyo mata

“Indai da rai da rabo,watarana zaku gana” kalaman umman da sukazo mata kenan,suka kuma fi yi mata kama da kalaman wanda ke sallamar bankwana izuwa qiyama idan anayi.

Idanunta qyar bisa ga mahaifinta sanda yake sallamata izuwa ga hannun baquwar fuskar da bata taba koda magagin cewa wata alaqa zata hadasu ba,riqe da qullin kayanta da ummansu ta hada mata

“Muje ko?” Ta tsinkayi baquwar murya tana bada umarni a gareta,saita daga jiqaqqun idanuwanta ta dubeshi,ta sauke a hakali ta maida ga bigiren da mahaifinta ya wanzu ashi dazu,wayam yake babu kowa,ta sake duban hanyar da ummanta ta rakota,itama babu kowa sai takun sawayenta,saita sake dubansa karo na biyu,karo nabiyun da zuciyarta ta buga mata da wani irin qarfi,saboda yadda taga fuskarsa a tsuke,cike da wani irin kwarjini da bata taba katarin ganinsa a fuskar wani ba.

A hankali ta fara daga qafafunta tana jefasu zuwa gaba,tana fatan dagasun da takeyi yayi da dai da sunan tafiya,zasu turata zuwa gaba kamar yadda ya buqata,tana iya ji da ganin sanda suka zartata a tafiya,shida amirun da a sannan batasan ko waye ba,taga dai ya qara sauri ya kuma cimma wanda aka kira da sunan mijinta,taga ya kama hannunsa da alama magana yakeasa,saidai bata damu da jin me suke tattaunawa ba,idanuwanta sunfi hango mata zaizayayyen gidansu,da ummanta dake cikin dakinta tana kuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button