Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 32

Sponsored Links

32

Shi ya dinga kai kawo tsakanin biyan bill din kudin bilal dana dan malam salahu,duk da cewa shi bilal nashi kudin ma ba wani masu yawa bane,saboda bai jima ba,duk motsin da zaiyi fuskar yaron yake hanga,wani tausayi yana ratsashi.

Tare da amiru suke komai,duk inda yasa qafa yana biye dashi,saidai bakinsa fal yake da tambayoyi ga sarakin game da su umman.

Bai sake shiga mamaki ba sai daya ji samir din yana bada umarnin sanya gawar bilal cikin motarsu,ya kalleshi,duk da baice komai ba,umman da kaltum daketa rusa kuka cikin wani yanayi mai matuqar ban tausayi suna daga baya,shi da samir din suna gidan gaba,malam salahu na musu addu’ar sauka qalau da samu rahama ga mamacin,samir din ya tada motar suka fice daga asibitin.

Kukanta kawai ke tashi cikin motar,ta kasa tsaida kukan ko dai dai da minti daya

“Don Allah bilal ka tashi,ka tashi kace wasa kake mana” shine abinda take fada lokaci bayan lokaci tana girgizashi,.

Sannu a hankali kukan yaci gaba da ratsa kunnuwansu,harda samir da sitiyarin motar ke hannunsa,lokaci bayan lokaci yakan ce

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil” a sarari,daga bisani saiya sanya casset na karatun qur’anu,qira’ar khusari,wanda hakan ya rage kaifin kukan kaltum.

Suna isa qauyen labarin rasuwar bilal ya ratsa ko ina,kafin kace meye wannan jama’a sun fara cika gidan,habiba na daya daga cikin wadanda suka fara zuwa,sun shigo tana riqe a hannun surukarta tana gunjin kuka,tana faduwa tana tashi,tana kiran bilal din tare da fatan abunda ke faruwan ya zama mafarki,xuwanta ya sake sanyawa kaltume dake ta son bawa kanta juriya sa qwarin gwiwa saita sare,suka taru suka dinga kuka baji ba gani,sai inna da bata jima da isowa ba,tana doje daga bakin qofa tahau musu fada,fadan da badan cikin yanayi yake ba duk sai sun tsaya kallonta,saboda mamakin dama innar tasan Allah?.

Cikin abinda bai gaza awa biyu ba aka gama shirya bilal,a sannan kaltum ta sake aro juriya,ta taka tana rangaji kamar zata fadi,saboda yadda takejin iska tana yawo da ita ta fita harabar gidansun,inda abokan bilal suka cika,harda wadanda kaltum ma bata sansu ba,ba ‘yan unguwar bane.

Abokinsa na kusa kusa ta kira

“Ka tambaya cikin abokanku,ko akwai wanda yake bin bilal bashi?” Kai ya kada cikin alhini

“A iya sanina babu,saidai ma wadanda bilal yakebi….amma bari na tambaya” juyawa yayi ya koma cikinsu,amsoshin dake fita daga bakunansu duka irin wadda ya bata ne daxun kafin yakai ga tambayarsu

Hawaye taji yana sauko mata,haka rayuwarsa ta qare gaba daya,ya nema da guminsa da qarfinsa,yaci iya cinsa,ya baiwa ‘yan uwansa,ya bada bashi ga abokansa,koda zasu cinye bashin ba zasu biyashi ba.

Rudewa gidan yayi da koke koke,yadda gidansu ke cike damqam da mata ashe a waje abun yafi haka,mamaki ya kusan kama kowa na jama’ar da bilal ya tara,idan bakasan waye ya rasu ba,zakayi tunanin cewa wani babban mutum ne ya rasu,saboda yawan al’ummar daya samu,suna ji suna gani bayan an gama sallar ama daukeshi akayi gaba dashi,ya barsu da kuka,ya barsu da kewa,ya barsu cikin gidan da ake yunqurin korarsa,sai gashi tun ba’a koreshi ba,shi ya tattara nasa ya nasa ya tafi inda ba dawo,inda kowanne me rai zaije.

Cikin dare a ranar ta kasa bacci,ganin komai take kamar wani wasan kwaikwayo,kamar wani wasa ne bilal din yake musu,kamar yaje ne zai dawo musu,ta dinga juyi tana kuka,yayin da gefe guda kuma abinda ya faru a wunin duka ya dinga dawo mata,yadda su ya munzali da muzammilu suka dinga rawar qafa wajen hada gawar bilal,sune kawo turare sune kawo sabulu da likkafani,idan ka gani kai ba zakace sune sila ko muzajar mutuwarsa ba,Allah ya sani,ba zata iya gogewa ba,ba zata iya hana kanta kallonsu a matsayin wadanda sukayi sila ko sanadiyyar tafiyar bilalunsu zuwa qiyama ba.

Sai kuma ta hango fuskar mahaifinsu,yadda yaye tsugunne gaban gawar bilal,gawar da sai da aka gama hada bilal din sannan ubangiji ya bashi ikon qarasowa,don bai samu labari da wuri ba,saboda a ranar yayi sammakon zuwa wani waje.

Ganin juyin bana qare bane saita miqe don ta dauro alwala,sai sukaci karo da ummanta,da alama itama baccin ya gagareta ne,batasan sanda wani sabon kukan ya qwace mata ba

“Da kika ce abar habiba ta zauna,da haka zaku zauna kenan ke da ita kuyita yi masa kuka?,kukan da bashi da wani amfani ko rana a wajensa?” Abinda umman tace kenan tana cika buta da ruwa don daura alwala.

To cikin kwanakin zaman makokin abubuwa da yawa sun faru,sunga jama’a masu yawa,wadanda basu tsmmatarwa bilal din ba,jama’a masu kamala da mutunci,wadanda zaka zaci ba zasu zo gun jana’izar yaro ba,yaron ma mata gata irin bilal,amma sai gasu,kowa yazo kuma saiya koka kan rasuwar yaron,saboda yadda kusan kowa ke amfanar sa,bashi da qyuya ko san jiki ko kadan,baisan rashin kunya ko fitsara ba ko kadan,girmama kowa yake,hakanan bashi da abokin fada.

Kudadensa da mutane suka kakkarba bashi masu tsoron Allah suka dinga kawowa ummanmu da kaltum sunyi mamaki,saboda wani ma basuyi tunanin bashi zai shiga tsakaninsu ba,yawan kudin da suka riqe sai yanzu suke biya,inda a zamanin da yake raye suka biyashin,babu shakka da sun isa ya kafa qaramar sana’a,da bai mutu cikin wahalar daya mutu ba,da bai mutu yana neman kudin da za’a masa aiki ba.

Yawan mutanen da suke zuwa gaisuwa ba shakka banda taimakon Allah,da kuma taimakon kawu ado da gwaggo indo da basusan da abinda zasu ci dasu ba,saidai a taimakon wadan nan bayin Allahn aka dinga dafa abinci ana ci.

Inna kuwa rabonta da gidan tun randa aka dauki gawar bilal,bayan an dawo daga binneshi,kawu ado yasa aka sauke buhun shinkafa babba dana wake,saita hau cewa a diba mata,wannan ai ya yiwa zuwaira da ahalinta yawa,ta dauko babbar qatuwar leda baqa ta buda bakinta.

Ran wasu daga cikin ‘yan uwa ya baci,amma saboda kowa yana shakkarta,saboda masifarta da bala’i yasa aka rasa mai tanka mata,sai wasu daga cikin jikokinta da suka fara qananun maganganu.

Ganin da gaske take yasa yakumbo indo ta murje idanunta tayi mata magana

“Inna,wannan kayan abincinfa ba dafawa akace a dinga yi ana ciyar da masu xaman makoki,kuma ko a hakanma yayi kadan,saina aika an sake siyo wani buhun” mita ta hau yi,har sai da taga ran yakumbo indon ya baci,kasancewarta ‘yar gaban goshinta da batason tayi fushi,tilas ta haqura,daga bisani ma ana sallame sallar la’asar tace zata koma gida,ba wanda ya hanata ko ya tambayeta ba’asi,hasalima ma hakan yafi ma kowa kwanciyar hankali.

********Sanyi gami da lallausan qamshi ne kawai ke fita daga qawatacce kuma madaidaicin falon,wanda zai burge duk wani mutum ko da ina matsayinsa da arziqinsa yakai.

Zaratan samarin ne su biyu kacal cikin falon,wato samir da Aamiru,samir din na sanye da wata riga short sleeve shirts da wando da iyakacinsa qaurinsa,dukkansu ruwan toka da adon baqi,wanda suka zauna jikinsa suka fitar da duk wata qira tasa tan murdewar jiki da murjewa, system ne a gabansa,yana duba wasu dokuna da akayi masa tallansu tun daga wata qasar,irin dokunansu ne na can,kasancewarsa mutum mai son dawakai,wanda a yanzu haka yana da guda uku nashi na qashin kansa,hakan duk sanda za’a gabatar da wasan tseren dokuna na polo to yana daga gaba gaba wajen zuwa,ba’a nigeria kawai ba,wani lokaci qafa da qafa yake fita wata qasar idan za’ayi,musamman idan akwai wanda yakeso a cikin wandanda xasuyi gasar tseren dawakan,wannan dabi’a tasa na daya daga cikin dalilan da yasa sunan saraki ya bishi.

Amiru kuwa na kwance saman doguwar sofa yana amsa waya,yanayin yadda yake wayar ya isa ya gaya maka cewa wayace ta masoya,don kuwa iya murmushin da yake fita saman fuskarsa kadai zai gaya maka hira ce ta musamman.

Kowa abinda yake gabansa yakeyi,kuma kowa najin dadin sabgarsa,har zuwa wani lokaci da aamirun ya gama wayar,sai ya miqe ya zauna kana ya zuro qafafunsa qasa,idanunsa akan samir,wanda ya gama zaben dawakan da yakeso cikin wadanda suka turo masa video dinsu

“Yauwa,ina jinka,kace mene?” Inji amiru yana miqa hannu,ya janyo drink din da jawahir ta shigo musu dashi,musamman saboda yayan nata.

Idanunsa masu kwarjini da kuma girma,wanda hasken system ya qarawa kyau ya daga ya watsawa aamiru yana murza tafun hannayensa waje daya,saboda sanyin ac din daya dan fara damunsa,duba da yanayin sanyi sanyi da aka fara a gari

“Kaga malam,yi ta kanka kawai,zama zanyi nata yi maka bayani?,ko dan aikinka ne ni da zan zauna inta maimaita maka zance bayan ka gama gabatar da naka uzurin?” Dariya Aamir ya qyalqyale da ita yana jjiye cup din hannunsa

“Sorry man,amma dai gaskiya ni bazan zauna na tasa aiki a gaba ba,kullum bani da abunyi saishi,tunda dai bashi zan aura ba ko?,bazan kuma biye maka ba,ya zamana daga ni har kai babu wani me qwaqwaran magana akansa,waima tsaya…..ina natun jauhar?” Yayi maganar yana zunkudawa gaba gami da tsare samir da ido.

Dubansa yayi da manyan idanunsa da gasken computer ke sake shiga ciki,sannan ya kauda idon nasa,kamar bazai amsa ba sai kuma yace

“Kaga malam,nifa bazan auri yarinyar nan ba”

“Saboda me?,look saraki,wasu lokutan fa kai kake sake haifar da sabin fahimta tsakaninka da daddy,yarinyar nan she has everything da akeson mace dashi, she’s beautiful…tana da gata tana da ilimi…then…me kake buqata sama da haka?” Fuskar computer din ya rufe ba tare daya kasheta bama,ya tsare amiru da ido don ya gane cewa kome zai fada da gaske yake

“Duk abinda ka fada hakane,tana da komai,but….bazan aureta ba” daga haka yatsaya kawai,sai suka shiga kallon kallo shida amiru,wanda daga bisani amirun shiya dage kafadunsa kawai gami da tabe baki

“Well,da alama you are ready to face the consequences,any way……dazu kamar kana maganar zuwa qauye gobe ko?, right?”

“Dan rainin hankali,ashe ka jini” ya fada qasa qasa,kamar meyin mita,yana buda fuskar computer din da niyyar kasheta gaba daya,bai amsawa amiru ba har ya kashe,sannan ya dubeshi

“Haka nace,saboda ginin makarantar ya kammala,ya kamata a budeta,saboda a samu dama a fara karatu,sannan…..”sai yayi shuru yana jan iska hunhunsa,a duk sanda zai tuna da yaron sai yaji babu dadi

“Akwai ragowar hakkin yaron nan,inason na kaiwa iyayensa” kai amiru ya jinjina,shi kansa daga yadda ya samir ya bashi labarin iya abinda ya sani game da rayuwarsu,da abinda yaji daga hannafi,da kuma abinda ya gani da idanunsa,sai ya tsinci kansa da tausayin yaron duk da ya tafi yayi nisan kiwo

“Hakan yayi,kace na shirya,am in love with garin fa?,nima yanayin qauyen yamin…..sai naji nayi kewar azare,duk daba qauye bane” murmushi samir ya saki,shikam ya soma jin dadin tafiye tafiyensa zuwa qauyukan da yakeyi,saboda ya zame masa tamkar wata makaranta ce daya bude ta qashin kansa,yana ganin salo da nau’in rayuwa iri daban daban,harda wadda mafarkinsa bai taba kawo masa ba,saiya soma baiwa amiru labarin garuruwan da ya jajje,ciki harda qauyen dinya,wanda a cikinsa ne ya soma kwana.

Wani abun yayi dariya wani abun yaja tsaki,amma dariyar da yakeyi din yafi yawa,bama kamar da yake bashi labarin yadda ‘yammatan qauyen suke,da kuma yadda abokinsa haladu ya mato akan kaltum,daya fasaltawa amirun yadda kaltumen take harda fadowa qasa saboda dariya,don a ranar daya ganta ana cikin rudani da alhini ba wani kallonta yayi sosai ba

“Dole muje,nima nayi koda ‘yammata biyu ne na kafa tarihi” harara samir ya jefa masa sanda ya miqe da niyyar zuwa toilet

“Kamar a kunnen khalisa”

“Dama dai kuna shiri” ya amsa masa,sanin cewa ba wani shiri suke sosai da samir din ba,saboda kowa tsarin dan uwansan bai masa ba.

********Tafe take a hankali tana ratsa ‘yan zaman makoki,iskar sanyi na kadata yadda taga dama,kasancewar ta sake wani ramewa da bushewa tun daga wancan ranar,hannunta dauke da geron data auno,wanda yakumbo indo ce tace a auna din,za’a kai ayi gumbar sadakar uku a gobe.

“Yammataaaa” taji an fada,da muryar nan data tsani ji,har ta wuceshi yayu wuf yasha gabansa,ta daga kai ta dubeshi,itakam bataga amfanin rayuwa irin ta auwalu ba,koda yaushe ace mutum ba’a saitinsa yake ba,dai kaga yana gyangyadawa ko yana girgidi?.

Wani busashen murmushi ya sakar mata

“Yas……yaaa kuma wai qarun haqurinmu?,Allah ya jiqan bilale…..eh….ya kuma kyauta eh yane” tsaki taja tamkar xata tsinke harsheta,ta kuma maka masa harara sannan tayi gaba,tana jiyo lafazinsa na

“Zaki bayani eh…..gobe zaki zama tawa” daukar zancan nasa tayi a matsayin shirme da molanka da wadanda suka bugu suka sabayi,don haka koda ta shiga ciki,ci gaba tayi da sabgarta,bata ma sake tuna maganarsa ba bare ta dameta,gaba daya su da uwarsu sun sake fice mata akai,laure tunda aka gama hada bilal aka fita dashi bata sake takowa bangarensu ba,dama ba zatace taga asiya bama sam,duk da yake ita kanta uwarta yanzu ganin nata sai sa’i,sa’i,saboda ta fantsama gari da sunan makaranta,makarantar da babu wanda yasan taqamaimai dinta,amma saboda tsabar ƁABI’AR ZUCIYA na son rai,duka sunbi sun rufe idanunsu daga kallon abinda yake faruwa,da kuma abinda zai biyo baya.

Bayan sallar la’asar,suna zaune a dakin ummanmu ana hada ‘yan tsummokaran bilal da za’a bada sadaka,idanun kaltum jiqe da hawaye,yayin da zuciyar ummanmu ke suya,jarumtar da tayi babu wanda ya zaceta,dai dai sannan babansu ya daga labule ya kirata ita da umman zuwa dakinsa.

Dukkansu a darare suka shiga,bama kamar ya kaltum,wanda ta manta ma yadda fasalin dakin yake da abinda ke cikinsa

“Ku qaraso ciki ku zauna” maganar data basu mamaki kenan,amma sanin cewa zukata a tausashe suke matuqa,cike da rauni saboda rashin da sukayi,sai mamakin nazu ya zama gajere,kowanne ya samu mazauni yana jiran ji daga bakinsa.

“Yauwa,na kiraku nan ne don na tuna muku keda kattume cewa,wa’adin dana deba mata na fidda miji ya cika….tun ranar da bilalu ya rasu,to saboda wannan rashin ya sanya na daga mata qafa,na qara mata wadan nan kwanakin,koda na qara dinma abinda na fuskanta shine babu wani data tsayar,wannan dalilin yasa ni da iliyasu da laure…..muka yanke shawarar zamu baiwa auwalu aurenta kawai,kowa ya huta,tuwona maina”.

Wani irin kallo umman tayi masa,wani abu mai kama da bacin rai yana ratsata,laure?,iliyasu?,auwalu?,inda zata iya tambayarsa zatayi,shin laure ko iliya suka daukar mata cikin kattume har suka haife mata ita ko kuwa?,shin su ke da ahaqqu da ita da zasu dauki ragamar bada shawarar a hadata aure da lalataccen dansu?,wanda suma suka rasa yadda zasuyi dashi?,amma ba zata iya hakan ba gaban ‘yarsu,zaidai bata jin zata iya shuru,saboda haka tace

“Ka aura mata koma waye,matuqar mutuncinsa dabi’arsa da addininsa sun cika amma banda iliya”.

“Zuwaira me kike nufi?,wai ko abinda laure take fada naketa karewa ya tabbata gaskiya ne?” Kallon dake nuna ranta ya fara baci tayi masa,me yasa har kwanan gobe fifita laure yake a kanta?,kamar ma itace matarsa ba ita zuwaira ba?,kafin ta dire fadanta ya fara bambamin bala’i

“Indai zuwara bakison jinin iliya nima baki sona,saboda abinda yayishi shi yayini,kin daurewa yarinya qarqashi taci gaba da zama gandandan a gabanki tana abinda taga dama ko?to wallahi ni nafi qarfin gidana,ba macen data isa ta takani kona mata biyayya,saidai a bini”

Ranta yakai maqurar baci,saita kasa shuru

“Yaushe Allah yayi daren bare gari ya waye?,kwanan kaltum nawa duka a duniya?,banda al’ada a yanzun kaltum bata isa aure a wasu guraren ba,ba abinda zaisa naqi jinin iliya,saboda jinin ‘ya’yana ne,abu daya nace….ka aura mata koma waye,ko daga ina yake,ko wanne jinsi yare ko qabila ne matuqar ya cika sharuddan da za’a bashi aure amma banda auwalu,saboda banga wani garanti qarko ko kwaliti da yake dashi ba”.

Sai a sannan kaltum data kifa kai tana kuka ta daga kaibta dubi ummanta,karon farko kuma a kanta umman tasu ta maidawa babansu magana,abinda bata taba jin ko ganin ya faru ba tunda ta haifeta.

Wannan abun shi ya qara harzuqa malam amadu

“Ni kike maidawa magana zuwaira?,to wallahi wallahi ko ga waye saina aurar da kattume daga yau zuwa gobe,zabi guda uku,inma daga yanzu zuwa sallar magariba ta fitar da miji?,in bata kawo ba zanyi shelar bada sadakarta a sallar magariba ta anjima,idan ba’a samu me karba ba kuwa,babu uban daya isa ya hanani daura mata aure da auwalu a gobe wajen addu’ar uku koda sama da qasa zata hade…..ku tashi ku fitarmun daga daki zan kulle dakina” ya fada yana kadasu da hannu kamar wasu kaji.

Duqawa ummanmu tai ta kama hannun kaltum ta miqar da ita,tana jin qirjinta yana suya,kamar takai gejin da ta fara gaza daukar abubuwan da suketa afkowa cikin rayuwarta ne,tana jin haka cikin ranta.

Sannu a hankali suke takawa shi da amiru zuwa bakin masallacin da byan zuwan samir garin aka masa kwaskwarima aka gyarashi.

Dukkansu suna daure da alwalar sallar magariba kowannensu,saboda mintuna kadan suka rage lokacinta yashiga.

Suna tafe samir na nuna masa guraren da ya dan sani a zamansa a garin,abun sai yake qayatar da amiru,fuskokinsu kawai zaka kalla ka tabbatar da irin nishadin da suke ciki,duk da sunyi shiga ta baina baina,amma kana musu kallo daya zakasan cewa fatarsu da irin fresh da jikinsu yake dashi,basu saba rayuwa a irin wannan gurbin ba.

A haka har suka iso bakin masallacin,sanda liman yake qwala kiran sallar,sai suka shige masallacin gaba daya.

Sahu suka hada sannan suka zauna kafin lokacin da za’a tada iqama,yayin da hirarsu ta yanke,wannan dabi’a ce da suka samota tun asali daga wajen professor,tun suna qanana sanda suke zuwa masallaci salla.

Daga bayansu kadan ya hangi hannafi ya shigo,ya samu waje shima ya zauna,da kadan kadan masallacin ya fara cika,aka tada iqama sannan aka kabbara salla.

Minti biyar aka liman yayi sallama,masu azkar suka fara,masu gaggawar barin bigiren da sukayi sallah,ba tare da sunsan romon xama a inda mutum yayi sallah ba bayan ya idar suka fara gaggawar tashi

“Ah jama’a assalamu alaikum,kowa ya dakata a inda yake,akwai muhimmiyar sanarwa” malam amadu ya fada bayan ya miqe tsaye daga sahun gaba da yake yana fuskantar masallaci,hakan yasa masu niyyar fita suka tsaya cak,na zaune kuma suka bada hankalinsa akanshi,ciki harda samir da amir da suka bishi da kallo.

“Salamu alaikum jama’a a karo na biyu,kowa dai yasan sunana yasan waye ni,sanarwa nakeso na bayar na auren diyata kattume game buqata,inason aurar da ita a asubahin gobe idan Allah ya kaimu,ga duk wanda keso….na dauke masa nauyin komai,ya biya sadaki,shaidu su shaida a daura masa aure da ita” tsit masallacin yayi kafin daga bisaninya rude da hayaniya,kowa da abinda yake fada,wasu na fadin lallai ta tabbata yarinyar ta aikata abinda ta aikata shi yasa abinda ya faru ya faru din,yayin da wasu ke da sukasan ainihin rayuwar gidan malam amadu ke cike da mamakin abunda ya afku a yanzun,a iya saninsu wannan abun tsohuwar al’adace,wadda su kamsu qauyen duk da qarancin wayewa suka daina amfani da ita,cikin masu ganin baiken hakan harda hannafi,wanda yasan komai game da rayuwar gidan malam amadu.

Ganin abun zai zama cece kuce sai liman ya karbi lasifiqa yayi magana

“Jama’a batun nan ba’an kawoshi don a tattauna ba,duk me buqata,malam amadu na cikin masallacin nan sai ya nemeshi su tattauna,ko ya iskeshi a gidansa,kowa yana iya tafiya”

“Nagodewa Allah da haladu baya nan” sukaji an fada daga bayansu,waiwayawa samir yayi,sai yaga abokin haladu ne,ya tuna abinda ya faru tsakaninsu a dandali,sannu sannu mutane suka fara yoyewa,wasu suka kafa sansani daga waje ana tattauna maganar,wasu na nuna sha’awarsu kan abun,amma sun gaza tunkarar malam amadu,sabida baqin fentin da aka yiwa kaltum din,yayin da wasu sukace zasu tsaya su kuwa suga tunqwal uwar daka.

Dariya amiru yake sosai sanda suke komawa gida akan hanya

“Gaskiya dole kaso zama a qauyen nan,abun dariya har gida,kaga yadda ake bada mace kyauta free babu ko sisin kwabonka?,anya kuwa master bani zan saka kaina ba?kasan Allah abun yayi min,kaga idan nadan more kona watanni ne,saina sallameta da abubuwan arziqi na qara gaba abina” Saraki wanda tunda suka taso baice komai ba ya juya ya dubi amiru,saiya sakar masa harara

“U r very stupid amiru,baka da hankali hala?” Fuskarsa ya gyara sosai gami da muryarsa ya koma serious

“Da gaske nake maka man…..wannan fa wata hanyace mai sauqi,aiba zina bace” qaqqarfan tsaki samir ya saki,sai kuma ya bushe da dariya

“Babu abinda zakayi da wannan yarinyar malam, infact ma babu abinda zaka tsinta a jikinta,bata da komai din da kake kwadayi” dariyar amiru ya tayashi

“Ka santa kenan?” Kafin yakai ga amsa masa saiga malam amadu kamar an jehoshi,cikin hanzari samir yayi gaba yana cewa

“Salamu alaikum” dakatawa yayi ya waiwayo yana duban samir kafin ya amsa masa,samir din ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace

“Sunana muhammadu,daya daga cikin masu ginin makarantar me tafasa”

“Toto…eh…anyi haka”

“Yauwa yaronka daya rasu bilal,akwai kudin sallama na aikinsa a wajenmu da zamu biyashi” wani farinciki ya saukarwa malam amadu,saiya fara matso hawaye

“Allah sarki,Allah sarki bilalu,yaro mai qoqarin neman na kai,ai nayi rashi,nayi rashi ba qarami ba” duk da cewa ba komai samir ya sani ba game da abinda ke wakana,amma a yadda yaga kulawarsa kan rayuwar yaron,a ganinsa wannan kukan baikai ko ina ba,tun daga kaishi asibiti,rasuwarsa da kawoshi da sukayi gida….

Kansa ya gayawa wannan ba huruminsa bane,huruminsa ya sauke nauyin dake kansu,don haka ya share wannan daga ransa,ya irgo kudaden da gumin bilal ha samar dasu ya miqawa malam amadun,yasa hannu ya cafke yana zabga godiya ya wuce suma suka wuce.

Ita kadai tana zaune amma cikin jikinta tana jin akwai abinda zai faru,tanajin tabbas babansu bai haqura ba,tunda ya fada din sai ya aikata,tunda ya quduri aniya sai yayi.

Bata sake samun yaqini ba saida qawayenta,tawaga daga wasila sukazo mata wai da niyyar gaisuwar,abunda ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,wasilar dako a hanya bata nuna alamun ta santa bare wani abu ya hadasu?.

Bata nuna musu komai ba,tunda mutum ya nuna don kai yazo,sadai lantana dake tayata zama ko kallo basu isheta ba,har sai daga bisani sanda suka niyyaci tafiya sannan wasilar tace

“Lantana abunma harda ‘yar shariya?,saboda zaku zama amaren gobe da asuba?,muna muku murna,shi auren sadaka ai falala gareshi,Allah ya sanya alkhairi yasa a daura a sa’a,idan auwalunne ta kwana gidan sauqi,idan bashi bane kuma sai munxo ganin wanda aka canka”.

Idanunta ta daga tabi wasila da kallo,wadda ta kusa barin sassan nasu,wani birkicewa kwanyarta taji tana shirin yi,zancan ya fita kenan?,idan kuwa ya fita ba shakka babansu yakai maganar masallaci,idan taje masallaci da gaske auren zai mata a gobe da asuba?,ranar sadakar ukun dan uwanta?,lallai ummansu batasan da za can ba,saita daga idanu ta azasu akan ummanta.

Tana zaune cikin ‘yan uwanta,tanata qoqarin yaqi da damuwoyin dake ranta,indai hakane ya kyautu takai mata wannan zancan ta qara mata damuwa?,baya tasan babu abinda ya isa ya canza qaddararta?,sai kawai ta lumshe idanunta,tana qoqarin ganin ta saisaita tunaninta.

Tabatan da akayi yasa ta bude dukka idanunta,lantana ce,fuskarta da idanunta cike fal da damuwa

“Don Allah kada ki dorawa kanki damuwa saboda zancansu,wani abunma zasu qireshi ne saboda su bata ranki” wani busashen murmushi ta sakarwa lantana,don ta gusar mata da tata damuwar itama

“Ban damu ba lantana,kawai ina tuna bilalu ne”

“In sha Allahu hutu ya samu”

“Muna fata” ta amsa mata,wani girma da qimar lantana take gani,ko meye zai faru da ita tana tsaiwa a gefanta,bata taba lissafa lantana cikin masoyanta ba saida wadan nan abubuwan suka faru,dama baka sanin masoyinka ko maqiyinka sai abu mara dadi ko mai dadi ya sameka,Allah kaci gaba da hadamu da masoyanmu na gaskiya,masu sonmu bilhaqqi amin.

*********Ƙarfe biyar saura na asubahi,amiru na daga tsaye yana dora lallausar sweeter dinsa saman jallabiyar jikinsa bayan ya gama alwala,ya dubi samir dake zaune saman abun salla bayan ya idar da raka’atanil fajr yana qarasa tasbihinsa da yatsun hannunsa

“Don Allah ka tashi haka mu tafi,kada mu rasa sahun gaba fa” sai da yakai sannan ya daga kai ya harareshi

“Wai yaushe ka zama magulmaci ne?,koda kaje da wuri fa baka da ladan zuwa da wurin,don ba manufarka kenan ba” dariya ya saki yana dora hular tashi ka fiya naci saman kansa da yake aje suma

“Allah so nake naga wannan dramer din ya zata kaya,sabon salon aurar da ‘ya’ya mata,sai kace game?”

Tsaki samir ya saki,ya dauko salati adadin yadda zaiyi ya qarasa sannan ya miqe yana nade dardumar da yayi sallah akai,zuwa sannan har amiru yayi waje,ya zura slippers yabi bayan amirun wanda yaketa faman kiran ya fito su wuce don Allah.

*Duniya a yanzu ta cika da abubuwan da kake tunanin babu su,amma har wadanda baka taba kawowa akwai ba akwaisu*

Labarin rayuwar da umma ke ciki gaskiya ne,ya faru,ni ganauce ba jiyau ba,ranar da yarinyar ke bani labarin rayuwar da suke ciki na gaya mata cewa
“Banda ke da kanki kika gayamin zan qaryata ne!”

Ranar da naji labarin rayuwar auren wata mata cewa nayi

“Inda a novel ne cewa za’ayi DAMA AI SAIDAI A NOVEL DIN” saboda bamu rubuta koda kwatar rintsi tsanani da tashin hankalin data fuskanta ba

Yaron dana sauya sunanshi da bilal yayi mutuwa sak irin ta bilal

Na tsaya gaban gawarshi nayi kuka da idona

Tana zaune a gidan sabida bata da wani gata ko kuma tsayayye da zai tsaya mata

Idan tace zata koma gidansu gaban mahaifiyarta bata da wannan gurbin

Yaranta duka mata ne
Duka basuyi aure ba
Gwara umma anan ta aurar da habiba

Me yasa ko yaushe mukafi karkata ga zaqin labari

Soyayya

Dukiya

Kyau

Da jin dadi?

Me yasa bamason mutuwa ko jarrabawa cikin labaranmu?

Me yasa muke gudunsu bayan rayuwarmu a daure take da qalubalensu?

Irin wannan ke canza tunanin marubuta masuyin labarin da zai zama ilimi da izina zuwa rubuta baragada saboda faranta ran masu karatu!

Allah madaukakin sarki yana cewa

“Shin mutane suna tsammanin za’a barsu saboda sunce sunyi imani ba zamu jarabcesu?,haqiqa mun jarrabi wadanda suka gabacesu……..”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button