Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 10

Sponsored Links

tun daga safiyar jiya zuwa yau din nan babu abinda ke yawo a ranta illa zallar farinciki da jin dadi,duk inda ta kalla cikin sassan nasu farinciki ne yake mamayeta,farincikin da take ciki ya sake ninkuwa a safiyar yau,bayan sunje gidan habiba sun mata dukkan jeren daya dace.

Jere ne da ya yiwa kaltum ba zata,don bata taba zaton habiban zata tsira da abinda ta tsira a yanzun dashi ba.

Sun isa gidan sun samu.mahaifiyar yusufa mai tarin kirki da karamci kamar yadda aka dinga gaya musu habiban ta dace da surukai,bangarenta na cikin gidansu yusufa ne,wanda babu kowa daga ita sai bangaren surukar tasu,sai sashen qanin yusufan da yake gini shima yana saka ran aure nan kusa,su biyu ne yara maza da babarsu ta haifa,sai hudu mata wadanda duka an aurar dasu,sai kuma wasu matan su biyu da babarsu ta rasu kafin a auro babar yusufa,babar yusufan ce ta riqesu harta aurar dasu.

Sassan habiba an kewaye mata shi da gajeriyar katanga,ba wata mai tsaho ba can,akwai dakuna guda biyu falle ɗai ɗai,sai bandaki,sai langa langa da ya saka ya kewaye mata wani guri daga yankin faɗin tsakar gidan da langa langa,ya zamana a mazaunin kitchenaka jera mata kayan aikin girki,wanda ummansu ta samu ta ganganda ta hada mata su cikin rufin asirin Allah,ɗaya ɗakin aka sanya mata kayan gado,ɗayan kuma kujerun iron ne guda hudu wadanda kawu ado ne ya mata su,gida dai ma sha Allah,ya baiwa mutane da yawa sha’awa babu laifi,yakumbo indo ce tayi mata labule, labulaye masu kyau kuwa,umma altine da suke uwa daya uba daya da ummansu,itama mai qaramin qarfi ce kamar umman tasu,saboda.mahaifinsu da inna ta aura dama talaka ne mai rufin asirin Allah,ita ta siyawa habiban kayan amfanin tsakar gida,kamar botikan wanka da rabobi,kujerar tsugonno,tsintsiya mafitai abun kwashe shara dama kwandon adana sharar da sauransu,cikin agaji na ubangiji,sai gashi umman tasu bataji kunya ba,yadda suketa fargaba ita da kaltum,kusan kullum rana da wannan fargabar suke kwana suke tashi.

Yamma lis suka dawo dauke da kular abinci qatuwa da babar yusufa da yan uwansa suka dafa musu,kowa ya buda baki sambarka yakeyi,baba laure na daga bangarenta,tunda aka soma abun babu wanda yaga idanuwanta,ko dangin babansun ma da suka zo sai su suka isketa sassanta aka gaisa.

Duka wannan bai damesu ba,tunda tako ina Allah ya rufa asiri saidai su gode masa,shi kansa baban nasu tunda yaji su muzammilu sun bada kudin gado da sif saiya tsame hannunsa yana fadin alhamdlh,daman shine dolensa,tunda ya samu masu dauke masa kuma falillahil hamdi,haihuwar yara maza mai rana.

idan umma ta tanka masa wayar dake hannunka ta tanka masa,ya gama maganarsa ya fice ta tafas bata ce masa ba,kaltum dake tsaye a gefe wadda itama saida ya gama zageta kan cewa munafuka ce,Allah ne kadai yasan me uwar tasu take samu suke hada kai tana xugata tana boyewa,taja hijabinta ya sanya ta fice daga gidan,amma sai komai ya wanke a ranta washegari dataje tana mazaunin ‘yar uwar tata.

Yamma lis suka dawo daga wajen jeren,suna tafe ana hira,da yake ba wata tazara mai nisan gaske bace tsakaninsu,dududu bai wuce tafiyar minti ashirin ko da biyar ba.

Daga nesa suka hangi tahowar wata mata,gefanta yaron ne da bazai wuce shekara goma ba,tun daga inda suke suna jiyo muryarta,duk da basa iya fahimtar me dame take cewa,saidai da alama fada take,fada kuwa irin sosai din nan
“tofa……ga lanti nan,jarabar duniya,ko waye ya tabota kuma oho?,ke kaltume gyara ga sirikarki nan”rakiya maqociyarsu wadda da ita akaje jeran ta fada,maganar tata ta danja hankalin mutanen da suke taren, yakumbo indo ta magantu dab da lanti din zata qaraso inda suke
“oho….wannan ce babar nasurun kenan?”kai rakiya ta gyada
“ita ta haifeshi,danta na fari kenan……lanti daga ina haka?”rakiya wadda bata dire daga basu amsa ba ta jefawa lanti data qaraso inda suke tambaya.

Har wani huci lanti take
“ni za’a yiwa iskanci rakiya,bashi nake bi sati biyu kenan an hanani?,to wallahi yau ko kudina ko kaya kudina”da sauri rakiya ta dakatar da ita ganin tare suke da surukanta,kada taga kamar bata gaya mata ba nan gaba taji haushinta,don kusan kowa yasan halin lantin bai dai masifa da jaraba ba
“kinganmu,tare muke da surukanki ai,iyayen yarinyar da nasurunki ya aika aka tambaya masa”saita koma kallonsu daya bayan daya,da wani irin duba da kaltum ta shiga nazarin matar,tana tsaye daga bayan yakumbo indo itama tana qarewa matar da aka kira da surukarta ta gobe kallo
“aiho…Allah sarki”abinda ta iya fada kenan,saita dubi rakiyan
“nikam rakiya minti daya mana”.

Gefe guda ta koma rakiyan ta bita,dai dai lokacin fatsima ta daukewa kaltum hankali da hirar abinda aka manta ba’a siya ba cikin kayan habiba,saidai yakumbo indo hankalinta na wajen dasu rakiya suke tsaye,yana iya juyo sanda lanti ta soma magana
“kinga rakiya karki sake ganina kiyimin irin haka,don zancan auren nasuru babu tabbas,don mi har yau bannkarbi maganar ba,zaqalqawar dangin ubansa ne,amma a rasa yarinyar da za’a hadashi da ita sai mara gata da galihu,wadda kaf qauyen nan sunsan wahalar da suke ciki?,me za’a jera musu ma a dakin da yake ginawar?,me na sama yaci ballantana na qasa?” rakiya tasan halin lanti sarai,batanda sauqi,gwana ce wajen fada da masifa,bata gajiya da bala’i,kamar ma wani gardi yake mata,ita kuwa ba zata iya biye mata ba,don haka tace
“Allah ya baki haquri”wucewarta tayi ta barta a nan,yayin da rakiyar ta koma cikin abokan tafiyarta,suka dunguma suka wuce,saidai hirar da sukayi din ya tsayawa yakumbo indo a rai,tana ta juya zancan,saidai batason ta shaidawa zuwaira,don ta tabbatar zata sanya mata tunane tunane ne kan lamarin.

washegari aka fara da wankan amarya,wanda a al’adarsu ake sanya yarinya tayi daurin qirji ta zauna saman turmi a tsakar gidansu,maqota ‘ya uwa da qawayen amarya zasu hallara,za’a mulketa da lalle wanda aka yiwa hade hade,sannan daga bisani a wanketa fes,anayi ana waqoqin aure kala kala,ana tafa hannu,a qa’idarsu su kakar yarinya ce keyi, saidai idan babu kakar ta bangaren uwa ko uba sannan za’a je ga qanwar kaka ko ‘yar uwarta ko yayar uba ko qanwarsa.

Tun kusan yammaci gidan ya fara cika da mutane,babban abun alfahari, duk da cewa ummansu miskiniya ce,duk da cewa ummansu bata da komai,bata mallaki komai ba,talaka ce ita tilis,amma kuma tana da kyawun mu’amala,tana da.matuqar kirki da kuma iya mu’amalantar jama’a,hakan shi ya gadar mata samun tarin al’umma,kowa so yake yazo ya nuna mata kara kan bikin farko da zata fara,kowa so yake ya miqo mata alkhairi,duk da ita bata da wadatar da take iya samun yiwa mutum biki bare ta sanya ran za’a rama mata,saidai hakan bai hana mutane miqa mata ihsani ba,saboda kirki da karamcinta,hakan ya sanya ta samu alkhairi sosai,wanda taji a jikinta bata da matsala na dukka abincin da za’aci cikin bikin,wanda a wancan satin wannan shine babban tashin hankalinta,sanda babansu kaltum ya gabatar mata da shinkafa kwano uku man gyada kwalba daya,yace iya abinda yake dashi kenan.

Wannan karon mamakinta ya gaza boyuwa,ta dinga kallonsa,dama yasan bashi dashi,bai shirya komai ba amma ya tashi bikin,ya aza dukkan wani nauyi nasa ya koma saman wuyanta?,cikinsu muzammilu da munzali kuwa babu wanda ta gani bare qwandalarsu ta shiga hannunta,bata sani ba sun baiwa baban nasu kamar yadda suka saba,ko kuwa a’ah,basu bashi bane gaba daya?,saita tattara lamarin ta watsar,tunda dama ko can ita ba dabi’arta bace sanya rai da abun hannun wani,shi yasa take zaune lafiya abunta.

Shima baban bata sake tunkararsa da komai ba,taci gaba da sallar darenta kamar yadda ta saba tana gayawa ubangiji,sai gashi cikin hikima da ikonsa,ya share mata hawayenta kamar yadda yayi alqawarin zai amsa addu’ar dukkan bawan daya roqeshi.

To a daren tun ana sanya idanun ganin zuwan inna ta wanke jikanyarta har aka fidda rai,wasu daga cikin ‘yan uwan umman da sukan halin da take ciki dangane da innar tata suka dinga jinjina abun suna mamaki,mamakin da basu taba kamarsa ba,baya ga rashin zuwan innar,babu ko silin tsintsiya data bayar da sunan gudunmawar bikin jikarta na farko a wajen zuwaira.

duk da bataso ba abun ya qayatar,kuma aka gama lafiyar Allah,kaltum nacan tana taya umman tasu hidimar mutane akace ana sallama da ita inji nasuru,sai umman ta sanyata aje komai ta fita wajensa.

Dab da zata fita zauren nasu ta kusa cin karo da wata,taja baya da sauri tana duban me shigowar,asiya ce ta taho abunta gaba gadi,kai kace saboda ita qwallin qwal aka gina qofar,hasken farin wata ya haskewa kaltum ita,tana sanye da wasu matsatstsun riga da skert na lace,ta yane kanta da qaramin mayafi,kwatankwacin shiga abar Allah wadarai a qauyen nasu,saidai a yanzu wannan itace shigar asiya,da sutturu kala kala wadanda ta tabbatar inna laure bata da kudin siya mata su,bare kuma kawu iliya.

hannunta dauke da wata babbar baqar leda,bisa alamu wani waje suka je da wani yayi mata wannan siyayyar.

Binta da kallo kaltum tayi har sai data gotata,tunda aka fara hidimar bikin babu wani abu guda daya da asiyan ta sanya kanta a ciki,kai kace ma ba bikin vidansu akeyi ba,ba ruwanta da kowa ba ruwanta da komai, iyakacin idan ta dawo daga yawon gantalin makarantar taci gayu ta fice idan tana da wajen zuwa,odan babu kuma ta wuni a daka kwance,baba kaire na fama da ayyukan gida,duk dai ita dinma babu abinda ta sanya bakinkota tanka na bikin,kai kace ita asiyan habiba ba ‘yar uwarta bace,qanwa ma tace a gareta.

Saida ta wuce sannan kaltum ta tafu zuwa qofar gidan,ranta yana mata quna,me yasa idanun mutanen gidan nasu kamar sun rufe ne?,kamar ma basa ganin aibun abinda asiyan takeyi,kamar ba wani abu takeyi mai muni ba.

A jikin dangar gidan ta sameshi tsaye ya jingina da ita,hannunsa riqe da leda,saita qarasa tana mas asallama,ya amsa idanuwansa bisa kanta yana dan murmushi.

Gaidashi ta soma yi,ya amsa yana tambayarta ya taro,ta amsa mas ada alhmdlh sannan ta dora
“muna ciki muna aiki saiga aiken kira”
“wai kaya na kawo miki na fitar biki”ya fada cikin murmushi yana miqa mata ledar hannunsa,ja baya tayi kadan kana ta noqe kafada kamar wanda ya bata wani abun tsoro,tun daga wancan ranar da abun ya faru umman ta hanata amsar komai daga hannunsa bata qara din ba kuwa,duk da ya turo anyi tambaya,amma ta kasa ci gaba da amsar komai nasa,sai data girgiza kanta sannan tayi magana
“Bazan karba ba nasuru,ka barshi na gode”fara’ar fuskarsa ce tadan ragu,yana dubanta
“kamar yaya kaltume?,yar atamfa ce fa na kawo miki kiyi fitar biki”duk da taji abinda ya kawo din,kuma tana da buqatar sabbin kayan,don kala daya ta samu daga ummanta,bilal ya siya mata sabon mayafi da takalmi da madina cikin kudin aikinsa daya siya yadin daurin aure shima yayi ragowa,amma bata jin zata amsa din.

Ganin ya dage ne yasa ta gaya masa dalili umma ce ta hana
“ki karba kice nine na baki ba tare da kin tambaya ba,idan har ta qiya bata yarda ba to zan karba abina”da wannan ya samu ta karba,tana shiga cikin gida kuwa ta direwa umma ledar,suna zaune tare da yakumbo indo suna hira,wadda bata wuce tattaunawa kan sha’anin bikin.

“meye a ciki?”umman ta tambayeta
“nima ban buda ba,nasuru ne ya bani”rai umman tata ta bata
“amma ban hanaki karbar komai daga hannunsa ba?”barin abinda takeyi tayi ta langabe kanta
“amma ummanmu….saida nace bazan karba bafa,ya dage,yace idan baki amince ba zai dawo ya karbi abinsa”
“wai wanne nusurun?,ba wanda ya aiko aka tambayar masa neman aurenta ba?”
“eh shifa”umman ta fada ranta a hade,sai yakumbo indo ta janyo ledar ta buda,ta ciro kayan da suke ciki.

Atamfa leda ce guda biyu da aka yiwa dinkin riga da xani, yakumbo ta janyo ledar tana maidasu ciki tana cewa
“haba yaaya,ke kuwa ki barta mana ta amsa,ai ba’a hana amsar kyauta irin wannan,samarin yanzun ma da ba kowane mai kyautar ba,ki barta ta sanya abunta,tunda ba aikin banza ake ba,ansan da zamansa,akwai maganar manya a ciki…..ke kaltume,dauki abunki ki adana”sosa taji dadi cikin ranta,saita karba din sannan ta wuce dakinta,tana juyo uammansun tana cewa
“ni tsorona daya….gaba kada aje abun nan bai yuwu bafa azo ana zancan maida duk abinda ya bata”
“in sha Alla hakan ba zata faru ba,kuma don dai yau daya ta karba ma aiba wani abun bane”yakumbo indo ta bata amsa,saidai gefe daya na zuciyarta yana tuna mata maganganun lanti na dazu.

habiba ta samu wadda ta fito daga wanka bayan wanda aka yi mata,tana goge jikinta da turaren da umma altine ta bata,kayan ta zazzage tana nuna mata,ga tunaninta sai taga habiban ta kyabe baki
“wato yaya kin gwammace ki amshi kayan wani kina farinciki,amma ni na kada dake na raya ki dauki wasu daga cikin na lefe na kema ki dinka….amma daga ke har umma kowa yaqi,bansan ko wani abun nayi muku ba”murmushi kaltum tayi,tsakaninta da ‘yan uwanta qauna ce sosai,suna son junansu, kowa kuma buri yake ya faranta ran dan uwansa,wannan shine kadai abun farinciki guda daya da suka tsira da shi
“habiba,kinfi kowa sanin yanayin qauyen nan,bawai minqi dauka bane,amma kinason mutuncinmu ya zube ne?,kaf kayan lefenki a qirge suke a idanun jama’a kin sani,ya sa ido sun riga da sun gama gane meye da meye a ciki,kiyi haquri karki bata ranki,wataranma fa ke zaki dinga dinkawa umma kayan sawar nan,idan ta nice kuma,ni dinma ai kinga ba wai jimawa nasuru zaiyi ba zai aiko da saka rana,daga nan nima zan samu nawa lefen ko?”da kalamai.na hikima masu kyau ta cirewa habiba haushin da taji nasu,sai suka shiga wata hirar ta daban.

*************

washegari ne za’ayi kamun amarya da yamma,don haka tunda safe da kaltum ta gama duk aikin da tasan ya kamata tayi,ta cimma umman tasu ita da yakumbo indo da kuma inna altine,tace zata gidansu suwaiba,don jiya bata ganta ba waje wankan amarya,tace mata saita dawo,sannan ta bata saqo gidan wata mata dake saida kabewa can wajen hayin makaranta,tace takai mata kudin,ta gobe ce da za’ayi amfani da ita,ta karba tayi mata sallama ta nufi qofa.

Har ta kusa fita umman ta kirata
“ki biya ta wajen umman asiya,naji dazu tana neman wanda zata aika wajajen,ki karba aiken ki hada gaba daya”.

dan jim kaltum tayi,saboda har ga Allah ita batason hada sabga da inna laure,amma hakanan ta amsawa umman sannan ta fice.

Sau uku tana sallama amma shuru ba’a amsa ba,ga magana qasa qasa tana jiyowa daga dakin inna lauren,da alama akwai mutane a rumfar tata,don haka saita qara matsawa ko zasu jiyo sallamarta.

“ke wallahi zamanin nan kowa a waye yake,duk yarinyar da kika gani tana dan taba tabe taben nan fa,duk ƙarya cr suce basayi”
“kai asiya….nidai gaskiya kamar bazan iya ba,haka kawai duk abi a sassaka maka hannu lungu da saqonka”
“to ai saikije kita zama,yo Allah na tuba taɓawa dai da shiga ba,wallahi indai xaka cemin ungo sakar maka zanyi,to sai me tunda ba nunawa zaiyi a jikina ba?”.

Kadan ya rage numfashin kaltum yayi qaura daga jikinta sabida hirar da taji tana tashi da muryar asiya da muryar kuma wata da batasan wacece ba,kamar ta juya sai kuma ta kasa,ta qarasa da hanzari tana bankade labulen dakin,sai sukayi ido hudu,ita da wata yarinya ce ‘yar gidan malam qaura,sak sukayi da ganinta,ranta a matuqar bace,zuciyarta na tafarfasa ta dubi asiyan
“kiji tsoron Allah,wallahi kiji tsoron ranar da zaki mutu,kin gwammaci saida mutuncinki saboda wani abun duniya?me zasu baki?,zasu baki yanke talauci ne?kome zasu baki dama rabonki ne,da kinyi haquri kinbi ta hanya mai kyau zaki sami koma meye har inda kike din,kome xasu baki idan kudine zasu qare,idam sutura ce wataran tsumma ce,idan kuma abun ciye ciye na kwadayine masai xaki tsugunna ki kasayarwa dasu,zunubinki kuma yana rubuce nan cikin littafinki,yana jiran randa zaki tsaya gaban zatin Allah ki kare kanki…….

Cikin salon na me kama da nade tabarmar kunya asiyan ta miqe
“kinga malamar munafunci,wadda ta damun da sanya ido a rayuwar wasu,ashe haka kika koma yiwa mutane labe?”hannu kaltum ta daga mata cikin fushi
“kada ki sake bakinki ya sake furta wata mummunar kalma a kaina,idan ba haka ba zan miki hauka wallahi”ta fahimci ran kaltum din a bace yake sosai,ta kuma san halinta sarai,kuma bata manta bugun da tasha kwanaki a hannunta ba,don haka ta koma magana ciki ciki
“hauka ai kowa ma ya iyashi”
“banza shashasha wadda batasan ciwon kanta dana rayuwarta ba,ki guji randa duniya zata miki hukunci ta kuma baki darasi”daga haka ta juya tabar bangaren ba tare data karbi aiken ba,hasalima ta manta abinda ya kawota sashen.

Tana tafe ita daya tana tariyar komai,sunanta taji an kira,ta gane muryar waye,saita waiwaya tana qoqarin sakin fuskarta,nasuru ne,ta gaidashi kamar ko yaushe,ya tambayeta inda zata,tace gidansu suwaiba,sai yace suje ya taka mata,ba don taso ba tayi gaba ya bi bayanta,don ba dabi’arta bace jerawa da wani namiji,idan ka cire dan uwanta bilal.

Suna tafe cikin ransa yana yabawa da tsaftarta,uwa uba iya magana da kamewa,komai nata a nutse yake,ya dade da sanin cewa ta banbamta da sauran matan karkarar,abinda yaja hankalinsa sosai kenan a kanta,har yaji sha’awar mallakarta.

A qofar gidan ya tsaya yace zai jirata,ita kuma ta shige ciki.

A tsakar gidansu ta samesu ita da babarta,babar tana gyara waken awara,suwaiban na zaune daga gefe,sanye da rigar atamfa waddabta banbanta da zanin jikinta,hira suke a sake da babartata,saidai kaltum nayin sallama fara’ar fuskar tata ta janye sosai,ta koma kadaran kadaham,kamar ma dai bataji dadin ganinta ba.

Duk da hakan kaltum bata kawowa ranta komai ba,ta tsugunna ta gaida babar suwaiba din,sannan ta dubi suwaiban tana jifanta da harara,duk da fuskarta akwai wadatar murmushi
“aini wallahi nayi fushi,ace bikin habiba guda?,na zaci ko babu ni a bikin habiba sai inda qarfinki ya qare?”
“Bana jin dadi ne?”ta fada cikin halin ko in kula,tana kawar da fuskarta gefa guda
“Ayyah,Allah ya sawwaqe,ai da nazo ne da niyyar inyi miki tas,amma rashin lafiya aita kori komai,Allah ya sawwaqe,amma dai yau zaki zo ko?”
“wataqila”ta sake amsa mata cikin shakulaton bangaro,wanda a wannan karon mamakinua fara kama zuciyar kaltum,batasan me yasa suwaiban ta sauya ba,gaba daya ta canza kamar ba ita ba,amma ita kam iya tsahon canzawarta batasan wanne irin laifi tayi mata ba,bare ta nemi sulhu ko ta bata haquri ba,jikinta a sanyaye ta miqe
“shikena zan wuce…idan kinji dadin jikin naki ki daure ki leqo…..nabar nasuru a waje yana jirana”juyowa tayi daga inda ta maida fuskarta tana duban kaltum,wannan karon fuskarta tada washe ba kamar dazu ba
“au tare kuke?”
“eh,mun hadu hanya ne yace bari ya rakoni”miqewa tayi tana gyara daurin xaninta
“muje na rakaki…..babarmu aramin mayafinki”tace da babar tasu sanda take futowa daga sashen nasu, saita zare mayafin daga wuyanta ta miqa mata,ta daura saman kanta tabi bayan kaltum.

Bakinta a washe da fara’a ta qarasa gaban nasiru
“ranka ya dade,dama ana ganinku?,tunda ita qawar tawa bata da kirki taqi ta hadamu,ai aikai yaci ace kayi zumunci da babbar qawa”murmushi yayi sannan yace
“Alla ne dai bai nufa nazo ba,amma yanzu daya nufa gashi munzo tare da itama gaba daya”,gaidashi ta soma yi ya amsa yana tambayarta wasu abubuwan da ba’a rasa tambayar mutum haduwar farko.

Koda suka gama kaltum tayi tunanin shikenan zasu wuce ne,saiga suwaiba ta zauna sosai tana ta sokowa nasiru hirararki,labarai kala kala,tun kaltum na tsaye har ta gaji ta nemi wajen zama.

Ganin har rana tana qara zafi,suwaiba kuma taqi barin hirar haka,saita dubi nasiru
“inajin zan wuce…..saboda ummanmu na jirana,daga nan akwai inda zanje,suwaiba saina ganki”ta fada tana miqewa, sai nasirun yayi zumbur
“a’ah bari muje,nima zan leqa gona zamuyi magana da baba” tuni kaltum din ta soma yin gaba abunta,sakato suwaiba tayi tana dubansu sanda yake mata sallama,tana tsaye a wajen har suka wuceta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button