Bakar Ayah Book 2 Page 53-54
Page 🖤 53••54🖤
Tun kafin asuba bombee ta tashi,saida ta tabbatar ta gyara Jabeer kafin tashiga banÉ—aki ta É—auro alwala.
Nafilfili tayi kafin lokacin da alfijir zai keto,yanzu tana iya yin ibadunta yanda takeso batareda ciwon kai ba,saidai fah halin rashin haƙuri da ƙin ɗaukar raini takula su sun zama a jininta suke.
Tana nan zaune akan sallayah har haske yafara shigowa ta windown É—akin,tashi tayi ta nufi bakin gadon ta zauna,kaman ko yaushe haka yake a yanda take barshi kullum batareda ya motsaba.
Tsira masa ido tayi ƙyam ko ƙyaftawa batayi,ita kaɗai tasan tunanin datakeyi a cikin zuciyarta,burin a yanzu shine samun lafiyar mijinnata,komai ma idan zaizo daga bayane.
Zamewa tayi ta ɗora kanta akan ƙirjinsa,a haka bacci yasake ɗauketa tana saurare bugun zuciyarsa wanda sai lura take jiyowa a hankali,shikaɗai ne kullum hope ɗinta datake dashi na cewar zai tashi wata rana..
Hayaniyar dataji a ɗakinne yasaka ta farkawa,Hajiyah Zeenah ce da kuma su maleekah,wanda ganin inda ta kwanta yasaka su sosa ƙeya.
Ko a jikinta ta tashi ta nufi banÉ—aki,sai bayan ta kintsa kana tafito.
Ƙasa ƙasa ta gaisheda Hajiyah Zeenah yayinda itama a takaice ta amsa tareda tambayarta ya mai jikin.
Suna nan zaune suma su inna Danejo suka shigo,saidai wannan karon akwai sabin fuska guda biyu,wato ummaruje da kuma Malam Ahmadu.
Duk da bombee tasan da zuwannasa amma ganinnasa bayan tsawon lokaci saida yabata mamaki..
“Baba”
“Na’am bombee ta ykk ya jikin mijinnaki,naji duk labarin abinda ya faru a wajen innarki da daddare,sannu kinji”
Bombee bata bari ya ƙarisa ba ta faɗa jikinsa,so take tayi kuka amma kuma yanzu ba lokacin kuka bane,dan haka kawai tayi shuru luf a jikinsa,innayi ce itama tazo ta baya ta rungumesu,ita kam tayi ɗan kukanta.
Ƙaramin hannu bombee taji ta bayanta ya rungumeta,dariya tayi tareda juyawa ta ɗagoshi jikinta,ɗan ta farincikinta nata na kanta,wato haidar.
Daga shi tayi sama yana ƙyalƙyala dariyah,banda mamma ba abinda yake faɗa.
“Um boy hadda kai aka zo asibiti?”
Ajiye shi tayi ƙasa tana ƙoƙarin boye farincinkinta na ganin ahalinnata saboda halin da ake ciki.
Abdulmaleek ne wanda ya tsugunna tareda kamo hannun haidar wanda bombee ta ajiyeshi a lokacin.
Kallon hannayensa yake da alama akwai abinda yagani daya tuna masa abu,saidai kuma shigowar Hilyan sai ya katse masa hankali daga kan yaron.
Kallonta yake yana kallon abdulkareem ma wanda shima ita yake kallo kafin ya kalli hilyan É—in.
A tsawon wannan watannin gabaÉ—aya da dagula musu lissafi,a rana É—aya saisu haÉ—u da ita lokaci guda, a wurare daban da kaya daban,amma kuma idan su suna tare guda É—aya suke gani,kuma duk saita kallesu tayi musu murmushi.
Sun kasa gane wanne siddabaru takeyi a tsakaninsu.
Kiftawa abdulkareem ido Abdulmaleek yayi kafin yayiwa hilyan alama da ido kan tazo.
Ba musu tabi bayansa zuwa corridorn dayake É—an nesa da inda É—akin Jabeer yake.
Suna nan tsaye baicemata komai ba,itama batayi magana ba har abdulkareem ya iso wajen.
“Uhm shin kinsan wannan”
Ƴar dariya hilyan tayi tana kallon Abdulmaleek ɗin,mai yasameshi kuma yake tambayarta wanene ɗan uwansa.
“Aisha magana nake miki kin sanshi?”
“Na sanshi Dr. Abdulkareem ne É—an uwanka mana”
“Okay to bayanni kina haÉ—uwa dashi?”
“What akan me zan haÉ—u dashi,kaima har yanzu ban amince da abinda yake tsakaninmu ba tukunna,saboda bakasan komai akaina ba, nikuma bazan iya faÉ—amaka ba”
“To amma duk sanda nake tareda ke muna magana sai yacemin shima yana tareda ke”
“Nikuma ohh…..minti É—aya ina zuwa yanzunnan”
Barin wajen tayi da sauri,can anjima saigata ta janyo hannun Inayah sun taho,tundaga nesa da Inayah tagane mai yake faruwa tafara sunne kai,dan da alama ita take haÉ—a komai kenan.
“Kayi mistake inaga bani kake nufiba Dr abdulkareem,da alama Æ´ar uwata kake gani.
Kayi haƙuri ba sunana aisha ba Abdulmaleek.
Sunana Hilyan ita kuma wannan Inayah,mu yan biyune kuma marayu gaba da baya,bamusan kowa anan ba sai anty maryam wacce take tamkar jigonmu,iya wannan zan iya faÉ—amuku gamedamu mu zamu tafi”
Hannun tahaɗa tana roƙon su afuwa,amma Inayah ko a jikinta,saidai kana gani kasan akwai abinda take boyewa.
“Kince masa sunanki aisha,to amma nima cewa tacemin sunan ta aisha,kuma itace take tareda ÆŠan uwana,inna Æ™irashi kuma sai yace daga inda yake yana kallonki a wajen matar babban yaya,wani lokacin har hotonki yake turomin daya É—auka a lokacin. Mu munyi tunanin mace É—ayace takeyin siddabaru”
Juyawa hilyan tayi cikin bacin rai ta kalli Inayah wacce take buya a bayanta.
“Inayah mai kika aikata faÉ—amin”
“Ohh ni babu abinda na aikata,kawai ranar ne naje shopping anty maryam ta aikeni sai ya ganni,najuya zan tafi sai yace min……..’Am kaman aisha koh wacce take zaune a gidanmu’
Nikuma dana gano ke yake nufi da alama kince sunanki Aisha,sai nace eh itace.
Wannan ne fah kawai”
“To meyasa bazakice bake bace toh?”
“To miye dannace nice É—in,kema naga ba sunaki Aisha ba ko?”
Murmushi su Abdulmaleek suka tsaya sunayiwa adorable twin É—in dake sa’insa a gabansu,sun shagala da kallonsu har basaso su daina faÉ—an.
Abdulkareem ne yayi gyaran murya tareda cewa.
“Yanzudai ke hilyan bakece mai É—aukar zafi ba nine koh,to na yafe abinda tayimin,dan da alama naga abinda tayin ya sakata nishaÉ—i sosai,saidai fah bazan yafe dukka ba har sai kin bani dama munyi magana tukunna”
Cuno baki Inayah tayi tareda É—aga kai.
“Uhm nima anyimin Æ™aryar sunan Aisha,dan haka abani damar yin maganar kafin nayafe”
Abdulmaleek shima yafaÉ—a yana kallon hilyan ta gefen ido,wacce duk kunya takamata sai matse hannun Inayah take dayake cikinnata.
“Ke dallah sakemin hannun zaki karyani,duk salon soyayyar ne haka”
Ta faÉ—amata daidai kunnenta,amma Abdulmaleek yaji ta duk da tafaÉ—a a hankali.
“Looovvee is in the air”
Dukka tareda suka juya suna kallon maleekah wacce takeyimusu tafi.
“Sannan kuma ga wani labari dana ji yanzu a gida danaje É—akko abincin da aka manta.
Baban haneef shida anty Lailah suna nan sun saka iyah a gaba wai saita amince da Abban haneef ya karbi kujerar yah Jabeer,tunda bazai tashi ba”
Dukkansu a tareda suka zaro ido gameda labarin da sukajin.
“Hmmm nima danaji abinda ake faÉ—a É—in nayi matuÆ™ar mamaki,kumada alama iyah ta yarda da abinda suke faÉ—a,a kowanne lokaci zakuji an Æ™ira family meeting.
Bayan sati biyu dayin aikin Jabeer aka ƙira family meeting domin tattaunawa akan waye zai riƙe Companyn na ɗan wani lokaci.
Duk da cewar babu wanda zaiso Alhj Abdullahi ya karbi Companyn,amma kuma kowa yasan shine yakamata ya hau.
Alhj aliyune ya fara magana tareda cewar.
“To Komai da ake ganin ya faru muÆ™addarine daga allah wanda ba’a saka masa rana,Jabeer har yanzu yana kwance a gadon asibiti,sannan kuma likitoci sun tabbatar dacewa koda ya tashi toba lallai ne ya koma yanda yake ba a da.
Dan haka na yanke shawarar zan miÆ™a kujerar Companyn a hannun…….”
“A dakata haka Abba”
Muryar bombee ce wacce shigowarta kenan É—akin meeting É—in.
“A Æ™ai’dar tsari na riÆ™on Company,wanda yakeda mafi kason share shine zai karbi shugabancin sa,duk da cewar shine na biyu a kaso na biyu a yawa…..
Alhj Abdullahi bashida lasisin hawa kujerar wannan Company,saboda bincike ya nuna ya daÉ—e da siyarda da share sa a hannun wasu dasuke son karbar kujerar nan,duk tsawon lokacin da takardun jabu yake aiki”
Kowa kallon bombee yake da mamaki wacce take nuna takardun Alhj Abdullahi a hannunta.
Cigaba tayi da cewar.
“Shugaban Company yana kwance halin jinya,mataimakin sa kuma bashida share ko É—aya a hannunsa,shin za’a miÆ™a kujerane ga na waje.
Zuwa yanzu wannan yafara kallon wannan,ciki kuwa harda manyan mutane biyar da aka gayyato wanda sukeda kaso mai yawa suma a cikin Companyn.
Magana suka farayi ƙasa kasa akan kowa nason karbar ragamar Companyn,wasu a cikinsu har sun fara murna da labarin da bombee ta kawo,domin hakan shine babbar damarsu.
Wata harara Lailah taje makawa bombee,yayinda mutanen gidan suke ganin sakarci na abinda bombee tayi.
Faɗa yafara kaurewa a tsakanin mutanen,kowa yana iƙirarin shiya cancanta da wannan kujera,har yazamo hayaniya tafara yawa.
Buga table É—in bombee tayi,saida kowa yayi shuru kafin tayi gyaran murya.
“Wannan kujerar da kuke magana akan ta ta mijina ce,Æ™annensa dukka suna da aikin yinsu,Æ™anin mahaifinsa kuma bashida takardun riÆ™e Company a yanzu. Sannan shi wanda ake Æ™oÆ™arin karbar kujerar sa ai bai mutu ba da ransa.
Dan haka ni matarsa Maryam Ahmad,nayi alƙawarin zan riƙe wannan kujera na tafiyar da ita yanda ya kamata,batareda na bari ta fada hannun wanda bai dace,har zuwa lokacin da mijina zai samu lafiya ya karbi abinsa.
Uhm na manta ma ban faÉ—amuku ba,barona asibiti a yanzu ya farfaÉ—o daga doguwar sumar daya shiga.
Saidai likitoci sun tabbatar da cewar komawar sa normal sai a hankali.
Dan haka na É—aura É—amarar karemasa matsayinsa da kuma kuladashi,har zuwa lokacin dazai iya aikinsa dakansa.
Abba idan ka amince dabani kujerarsa na kulada ita kasaka hannu akan wannan takardar,nizan koma Wajensa a yanzu”
Tana gama maganar ta tsugunna a wajen da Alhj Aliyu yake zaune ta miƙa masa takardar.
Hannu yasaka ya karbi takardar yana murmushi.
Tashi tayi zata tafi taji yayi magana.
“Keda kike buÆ™atar saka hannuna meyasa kuma zaki tafi?”
“Abba ba dole sai yanzu zaka saka hannun ba,miÆ™a ragamar aikin É—anka a hannuna kana buÆ™atar yin dogon tunani,zan jira har sai sanda ka amince kafin kasaka hannun”
Jijjiga kai yayi tareda faɗaɗa murmushin sa kana yayi sign a wajen da ake buƙata,mika mata takardar yayi tareda cewar.
“Na yarda dake É—ari bisa É—ari da dukiyarsa da kuma kulada shi,maleekah tana bani labarin duk abinda kike masa,babu abinda zancemiki sai Allah yayi miki albarka kuma yabawa mijinki lafiya kinji”
Kallon dattijon take cikeda shauƙin jin girmansa a idonta.
“Nagode Abba,ina mai tabbatar maka bazakayi nadamar miÆ™amin amanar dukiyar É—anka ba”
“Ina fatan hakan”
Tashi tayi ta tsaya,lokaci guda ta sauya yanayin fuskar tata.
“Defuty CEO and directors,ina buÆ™atar kasancewarku a office 7:00 am na safe,akwai abinda za’a tattauna”
Tana gama faÉ—in hakan tayi waje da sauri,bata daÉ—e da fita ba sukaji tashin motarta.
A bakin É—akin taci karo da doctorn zai shiga.
“Mr Jabeer kin dawo,É—azu nashiga bakya nan sai nurse kawai na gani”
“Uhm wani urgent abune ya taso,É—azu kacemin ya tashi amma ni banga wani cigaba ba sosai”
“Bazaki gani a haka ba dama,amma yanzu baya numfashi da inji da kansa yakeyi”
Nurse ɗin da bombee ta buƙata a bata ta suna zaune a gefe guda.
“Sister Haleema shin akwai wani abu da kuka gani gameda shi?”
“Ahah babu komai doctor,saidai kaman yatsansa ya motsa,naga ya motsa daga yanda yake”
Ƙarisawa wajen bombee tayi da sauri tana nazarin abinda suka faɗa.
Kafin wani lokaci ƙanƙani kowa labarin farfaɗowar Jabeer yabaza yan uwa,saidai har yanzu baya motsi sosai,abinma sai yafi bada damuwa fiyeda da.
Da daddare bombee kwana tayi tana nazari gameda aikin da Jabeer yake,in bata gane abuba ta ƙira khaleel ta faɗamasa,dan da farko shi ta cewa ya karbi Companyn amma firr yaƙi ya manna mata.
To yanzunma dai kusan komai shizayyi,tunda ita ga kulada Jabeer.
Kaman koyaushe datayi asuba bata koma ba,zama tayi a bakin gadon tana ƙare masa kallo,alamar motsawa taga idonsa yanayi.
Fitila da É—akko da sauri ta haska,tabbas hakane ba idonta bane yake mata gizo,fatar idonsa ne suke motsi.
“Mashallah nasan dama zaka tashi bazaka cigaba da barmu muna jira ba koh,ka tashi ka nuna musu,wanda burinsu shine faÉ—uwarka”
Maganganu tacigaba dayi amma ba amsa.
”Anty Maryam yah khaleel wai yana Æ™iran wayarki,shin dagaskene 7:00 za’ayi meeting É—in?”
Madeenah ce ta tambayeta cikin muryar bacci,ita da maleekah yau a nan suka kwana,tunda ita bombee tana bukatar zuwa aiki.
“Ohh wayar tawa inaga tana silent,kice masa eh yasanardasu nima yanzu zam shirya”
Tana gama faÉ—in hakan ta shiga banÉ—aki.
Bayan ta shirya kafin ta tafi saida su maleekah suka sha kashedi,kan ko motsi ɗaya suka gani suƙirata su faɗamata.
Abin harsai da yabasu dariya,itakuwa babu ruwanta.
Bakwai daidai tayi parking a ƙofar Companyn,ga wani baƙin glass data tare fuskarta dashi,wata tafiya take ta kasaita,duk da safiya ce amma kowa ya fito,don kowa yaci abinda aka faɗa na zuwan sabuwar CEO Mr Jabeer,wato Bombee.
Secretary yace tazo da sauri ta karbi jakarta zuwa cikin office É—in.
A hawa na sha shida yake final floor yake,dan haka saida ta elevator,office É—in ta nuna mata.
Saida ta ƙarewa ƙofar kallo kafin tashiga.
Mashallah wajene a tsare yasha kayan Alfarma irin na zamani.
Office É—in Secretary ta wuce ta nufi na shigaban wato na CEO.
Akan table É—in Ta ajiye mata jakar tareda komawa gefe ta tsayah.
Ƙaremata kallo bombee tayi bayan ta zauna a kujerar tans juyawa.
“Miye sunanki”
“Sunana Fadeela ranki ya daÉ—e”
“Tun yaushe kike aiki anan”
“Shakera uku kenan,amma nakusa dainawa zanyi aure nan da 6 month inshaallah,amma Æ™anina ya cika gurbin aikin zai cigaba da aiki da ogah”
“Good Allah ya taimaka,menene schedule É—ina na yau?”
“Ranki ya daÉ—e basuda wani yawa,iya gabatar dakene ga directors dakuma Share holders,saikuma sign dazakiyi a takardun sabbin ma’aikatan da aka É—auka”
“Ohk muje ki kaini meeting room É—in,takardun dasuke buÆ™atar sign kuma in zan iya yinsu a gida to ki saka min su a mota kawai,dan ba zama zanyi ba”
“Ba matsala ranki ya daÉ—e”
Lokacin data shiga ga iya share holder ta gabatar dakan,sukam sauran dama sun ganta.
Daga nan tabar sauran aikin a hannun khaleel ta koma asibiti.
Tun a wajen fitowarta daga mota maleekah ta tareta tana dariya.
“Anty maryam albishirinki”
“Ahah ba goroba barina je nagani da idona,bazan iya bari naji mai zakice ba”
Dana dariya tabi bayanta da gudu har tuntube take.
Turus tayi a bakin ɗakin ganin likitoci a ƙalla uku zaunar dashi sukayi idonsa yana kallon ƙofah,saidai kana kallon idon kasan babu abinda yake gani dashi.
Wasu ƙarafa aka saka suka tareshi,saidai yana motsa hannunsa da kuma ƙafafunsa.
“Doctor yatashi kenan”
Bombee tafaÉ—a cikin zumuÉ—i
“Eh ya farka amma kuma har yanzu majority na jikinsa baya respond,hakan yana buÆ™atar É—an lokaci,za’a dunga É—agashi anan kwantarshi,idan hakan ya cigaba zamu baku wheelchair a dunga sakashi a kai”
Bayan kwana uku da farfaɗowarsa an samu cigaba sosai,dan wunin ranar yau bombee yi tayi tana kewayawa dashi cikin asibitin a wheelchair,dan yanzu har buɗe baki yake yana ƙarbar abinsha marar nauyi idan aka kai kusan bakinsa.
Sannan in aka kai haske kusan idonsa yakan ƙoƙarin saida kwayar idonsa akai.
Ganin hakan da akayi ne yasa Alhj Aliyu da kansa yanemi a dawo dashi gida,suma likotocin basu wani damuba,saboda zaman sa cikin mutane zai ƙara saurin samun sauƙinsa sosai.
Tsawon kusan wata guda Jabeer yayi a asibiti kafin aka dawo dashi gida,har sannan Jawaheer da Jaleelah basu fita daga sashensu ba,lubnah kuwa run a ranar daya fita itama tabar gidan.
GabaÉ—aya babu wanda yakulada halinda suke ciki,saboda hankalin kowa yana kan jinyar Jabeer É—in.
Su suke tafa abincinsu suci,kana kuma su gyara gidan tsaff,Hajiyah rabi tun tana zuwa akan Jawaheer tazo su tafi harta daina,yanzu sun fara tunanin ko rashin lafiyar mijinnasune ta taba su.
Sanda aka dawo da Jabeer gida,Hajiyah Zeenah taso akaishi shashenta,amma alhj Aliyu ya nuna mata Æ™in amincewarsa,tareda yi mata magana akan tabar matarsa ta kulada shi,dan yanzu kowa yasan abinda Hajiyah Zeenah tayi wajen auro bombee ,shiyasa hatta Æ´aÆ´an ta idan tace ga yanda za’ayi sai kowa yayi shuru kawai.
“Yanzu shikenan duk shirin yatashi a banza kuma haka zamu zuba ido?
Ka duba wannan Jabeer É—in munyi zaton bazai tashi ba,saigashi kullum lafiya yake samu,kaman duk bakin duniya aka haÉ—u ana masa fatan tashi”
“Hmm kedai bari ni narasa ma mai zanyi,babu abinda yafi É—agamin hankali kaman rashin takarduna,da yannzu fah na zama nine shugaba,koda zai dashi daga baya kenan,amma yanzu kiga yanda rishe ya juye da mujiya.
Waccar yarinyar yaishe ma to tasan banida takardu,ko itama wani aikin takeyi a boye?”
“Da alama,ko itace ma tasace takardunnaka ba. Takamar data fito tanayi duk dan Jabeer yana rayene ai,da ya mutu ai kowa yasan kaine mai gadon takardunsa ko kana da naka koda kuma bakada shi,tunda bashida magaji har yanxu.
Kuma dama haka akayi da alhj Aliyu É—in,inba Jabeer kaine mai karba kujera idan Jabeer bashida magaji.”
“Uhm kuma kinsa nafara wani tunani”
“Irin wanda nakeyi koh?”
“Wanne kikeyi ke”
“Na kawar da Jabeer daga doron Æ™asa,ai haka mukayiwa Aliyu ma ka manta,saida yarasa Æ™afarsa kafin ka samu matsayin dakake kai a yanzu”
“Eh hakane amma yakike ganin zamuyi da Hajiya rabi wacce mukeson haÉ—a hannu da ita.
Kimsan dai bazata bari a kashe surukinta ba,musamman datake son Æ´ar ta haifi É—a gidannan”
“Abu mai sauÆ™i saimu sanar da ita cewar Jabeer bazai haihu ba,kuma inka zama shugaban Companyn zaka bawa É—an ta mataimakinka”
“Eh wannan shawara tayi,an gaisheki mamar haneef,nasarar mu takusa zuwa”
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________