Sponsored Links
Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 51-52

Sponsored Links

Page 🖤 51••52🖤

Maleekah ta ƙira ta shaida mata tafaɗawa ilahirin gidannasu halinda ake ciki.
Tana kashewa wayar khmees ta ƙira shima tafaɗamasa halinda ake ciki.
Daga nan tacigaba da safa da marwa tana jiran fitowar doctorn domin jin mai yake faruwa.

*** ***

“Mommy mommy”
Tun kafin ta ƙariso sashen take sabga musu ƙira da waya a hannunta.
“Menene kike zabgamin Æ™ira kaman wata sabuwar makahuwa,kibarni naji da abinda yake damuna ma”
“Mommy anty maryam tasamo yah Jabeer,saidai lokacin data ganshi a sume yake,yanzu haka wai suna general hospital anshiga dashi emergency”
“What hospital kuma,maza-maza shiga ki É—auko min mayafina,barina Æ™ira su abdul na faÉ—amusu,shikamma abdulkareem ai yana asibitin,barina fara faÉ—amasa”
Cikin sauri jikinta har rawa yake tafara danne dannen wayar,yayinda itakuma maleekah tashiga É—auko mata mayafin.

Suna gama wayar ya nufo emergency É—in daga ward É—insu,tun a bakin room É—in yahango bombee wacce take ta safa da marwa tana cizan yatsa,ajima ta zauna saikuma tasake tashi. Kana ganinta kasan tarasa mai zatayi ne.
A hankali yake tafiya har ya isa inda take,sallama yayi mata amma sam batajishi ba,gabaÉ—aya hankalin ta baya cikin kanta.
Maimaita sallamar yasakeyi wannan karon da ɗan ƙarfi.
“Am likita ya ake ciki ya tashi, mai ya sameshi babu matsal…..”
Shuru tayi ta zancen tareda dafe kanta lokacin da taga ashe Abdulkareem ne ba doctorn datake jiraba.
“Ohh ashe kaine am sorry”
“Ahh no babu komai,amma dai ki kwantar da hankalin ki inshaallah zai samu lafiya,inkika cigaba dayin haka to kema zaki iya samun matsala,kowa yaganki yasan…..”
“Ba kayi haÆ™uri amma ba wannan bayanin nakenson ji ba,shin zaka iya dubomin mai yake faruwa,ta hakane kawai zan iya samun kwanciyar hankali”
“Okay to shikenan bari su abdul su iso kafin na tafi,kada na barki ke kaÉ—ai a wajen,kicigaba da Addu’a Allah zai bada mafita inshaallah”
Shuru tayi daga haka batasake magana ba,har Abdulmaleek ne ya iso wajen shida maleekah da saurinsu.
“Yanaganku ku biyu ina mommah take?”
“Uhm ta tsaya jiran Sayyada-tateen wai dole saita jirata,nikuwa danaga haka nafaÉ—awa yah abdul.M mutaho tare.
Anty maryam yadai ya ake ciki,a ina kika sameshi ne uhm”
“A wajen da banyi tsammani ba kuma nayi tsammani”
Kallonta sukayi su ukun da mamakin maganar ta.
“Ba yanzu ne lokacin daya kamata ayi magana akan wannan ba,Abdulkareem kaine likita,akwai abinda Jabeer ya daÉ—e yana boyewa kowa,wanda kuma abune mai matuÆ™ar muhimmanci,kasamu likitan dayake gani kuyi maganar dashi,na tabbatar abinda yake damunsa yanada nasaba da halinda yake ciki yanzu.
Ni kaÉ—ai naga yanayin dayake ciki ku baku gani ba…….it’s so heartbroken”
Hawayen da maleekah take rikewa ne yazubo akan kuncinta,zama tayi a gefen bombee tareda rungumeta,wacce itama take ƙoƙarin wajen ganin zuciyartata bata karaya ba.

Kafin likitocin dasuka rufu akan Jabeer su fito,tuni bakin wajen ya cika da É—umbin mutane,harda Hajiyah rabi da kuma gidansu Jaleelah wanda suma suka samu labarin kwanciyar tasa,banda Æ´an wajen aiki dasuke ta zuwa.
Lokacin da likitocin suka fito daga É—akin aikin su kansu saida sukayi mamakin yawan mutanen dasukayi dafifi a bakin wajen.
Cikeda damuwa babban likitan ya kallesu kafin yayi magana.
“Uhm dan allah wasu dayawa si É—an yi gefe,bamason hayaniya a kuda nan wajen,sannan ina buÆ™atar wasu daga cikin familynsa na kusa zamuyi magana dasu”
Wannan ya kalli wannan,daga ƙarshe dai ƴan biyun ƙannennasa suka tashi domin bin bayan likitan,Hajiyah Zeenah ce ta tashi zata bi bayansu itama,dan dama tun ɗazu datazo batace komai ba tana takure a gefe,su kansu ƴaƴan tunda sukaji abinda tayi jiya babu wanda yayi mata magana.
“Am mommah dakin zauna basai kinzo ba,saboda zai iya yiyuwa abune da bai kamata kijiba a yanayin dakike,Anty maryam ke taso muje domin yakamata aje da matarsa”
Zabin Abdul.K yayi bayyiwa mutane da dama daÉ—i ba inka É—auke maleekah saikuma su danginta wato su hilyan da innq Danejo.
Tashi tayi batareda tace komai ba tabi bayansu. A zaune suka samu likitan yana É—an bubbuga biro akan benci,alamar yashiga tunani.
Sallam Dr.Abdulkareem yayi masa kafin suka É—anyi magana ta likitoci.
Maganar serious Doctorn Jabeer É—in yafara,dan haka dole sukayi shuru suna sauraransa
“Ehh wato da dafarko banyi niyyar faÉ—a muku abinda yake damunsa ba,amma tunda abin yazama haka dole ne na karyah rule na patient akan jinyarsa.
Jabeer yana É—aukene da Matsala ta INSOMNIA,wato cutar da bata barin mutum yasamu bacci da dare batareda magani ba,ko kuma inya samu baccin ma to saiya tashi yajishi a gajiye tamkar bayyi ba.
Shekara uku dasuka wuce yazo shi gwaji nan wajena saboda matsalar cutar,wato lokacin da matarsa tabiyu ta mutu,a lokacin bata yi serious na sosai,amma saboda yawan tension dayake ciki da kuma fargaba a koda yaushe yasa dole muka É—aurshi akan treatment.
Maimaikon dayana karbar kulawa tayi sauƙi sai abu daya cigaba da hawa,musamman ma a mutuwar matar sa ta uku,wanann lokacin saida muka sakashi bacci na tsawon sati guda kafin yake gane mutane sosai.
A nanne ma damu akan yasanar da familynsa abinda yake damunsa,amma duk da haka yaƙi amincewa,a cewarsa koda sunjin babu abinda zai sanja,musamman mahaifiyar sa haka taso ta ganshi kullum cikin aiki dakuma bin umarninta,koda kuwa hakan zai saka watarana ya faɗi ya gaza.
Magani nasanja masa zuwa wanda yafi nada Æ™arfi kaÉ—an,saboda yadunga samun bacci ya wuce wannan stage É—in na damuwar,saidai ba’a daÉ—e ba kuma wani tension É—in shima yashigomasa wanda magance cutar yayi wuyah a lokacin.
Dan ma akwai lokacin dayazo yasameni yana farincikin yake faÉ—amin wai akwai matarsa da idan yana kwance a waje tareda ita ko kuma yashiga sashenta yana samun nutsuwa sosai,har yayi bacci batareda shan magani ba.
A lokacin ni kaina nayi murna da farinciki danaji haka,domin mun saba dashi sosai tamkar É—an da na haifa.
Saidai me…..jiya da daddare nasamu Æ™iran wayarsa yana magana numfashinsa yana fita sama sama,tun a lokacin naketa Æ™iran wayarsa har Allah yasa ita matarsa maryam da É—auka,to itace ta kawoshi asibiti É—azu”
Tun kafin suce wani abun sukaji sautin kukan Hajiyah Zeenah a bakin ƙofah,da alama duk taji abinda likitan yafaɗa akan matsalar ɗannata,anya kuwa zata ƙira kanta da uwa kuwa,wannan abinda ta aikata har yaushe.
“To menene dalilin shiga wannan condition É—in dayayi a yanzu,sannan me ya haifar masa hakan”
“Bansan dalilin daya sakashi shiga cikin wannan halin ba,amma koma mai menene babban abune sosai,sannan abinda ya haifar shine wanda zan faÉ—amuku dana Æ™iraku……..
Matsalarsa tayi girma har ta taba masa ƙwaƙwalwa jini yashiga da wani position,sannan kuma yasha magani fiyeda overdose ma,aikin da muke akan sa tun ɗazu na cire toxin ɗin maganinne daga cikin jininsa.
Munyi nasarar yin hakan,saidai akwai aiki a gaba shine zamuyi masa tiyata akai mu zuqe jinin,hakan zai iya zuwa da abubuwa da yawa.
Idan munyi nasara zai tashi batareda ya manta komai ba,kuma inshaallah har matsalarsa ta rashin bacci zata kau.
Idan kuma aka samu akasin haka zai iya tashi,amma kuma zai rasa tunanin sa,inayayi yawa harda rasa hankali ake samu.
Sannan a kowanne bangare idan aka yi zai iya shiga coma wanda bamusan iyah Tsawon lokacin da zayyi ba yana kwance.
Kowanne possibility a ciki 50-50 ne”
“Idan kuma ba’ayi tiyatar ba kuma mai zai faru?”
Sai yanzu bombee tayi magana tun É—azun datake wajen.
“Uhm idan ba’a yiba zamu sakashi ne a na’urar dazata dunga saka Æ™waÆ™walwarsa bacci duk bayan wasu awanni,wanda hakan is no a solution”
“To kawai ayi tiyatar,na tabbatar inshaallah zai tashi lafiya,batun shiga coma kuma muna masa fatan kada ya shiga doguwa,zamuyi ta masa Addu’a har Allah yasa yasamu lafiya,akwai wanda suke jiran tashinsa,dan haka inshaallah zai tashi batareda matsala ba.
Ina kyautata zaton hakan,idan akwai wajen sign na matarsa ga bani nayi,inason barin wajennan”
Dukkansu basuce komai ba har likitan ya miƙa mata takardar.
Karba tayi cikeda dauriya,duk da kowa yana kulada yanda hannunta yake rawa..
Sign ɗin tayi cikin sanyin rai ta miƙa masa takardar ta fita a wajen,hannu tasaka da ɗauke ƙwallar hawayen da take shirin zubomata.
A bakin ƙofah ta samu Hajiyah Zeenah a zaune tana rabzar kuka,kaman bata ganta ba haka tawuce tabarta a wajen,haushi iya haushi take ji gameda ita,domin duk abinda yafaru da rayuwarsa tana da kaso mafi tsoka akai,shine dan munafurci tazo ta takure tana kuka..
Shirye shiryen tiyatar aka farayi bayan an biya maƙudan kuɗi,sai zuwa washagari zasuyi masa tiyatar,kafinnan jikinsa yayi relax ba kaman yanzu ba.
Sau ɗaya aka bawa su bombee damar su ganshi,shima kuma ta glass ɗin ƙofah ne,daga nan kowa aka bashi damar tafiya gida,domin basa buƙatar kowa ya shiga wajensa.
A gidan baya take a motar,dan yanzu batada ƙarfin tuƙa wani abu waishi mota.
Gidanta direct hilyan ta wuce da ita hadda su sukkansu,domin a halinda take cikin tana buƙatar zama a cikin mutane.
Wanka hilyan tasakata tayi tarama sallolin da ake binta kafin takawo mata abinci.
Nan ma daƙyar taci abincin sama sama,daganan ta kwanta bacci ya ɗauketa.
Tsakar dare bombee ta tashi ta É—auro alwala tafara salloli,tun tanayi har jinkinta ya gaji da zauna,anan ma Addu’a tacigaba da zubawa kala kala,duk akan neman lafiya ne ga mijinnata,wanda yake gadon asibiti rai a hannun Allah..
Tun duru duru ba’a daÉ—e dayin sallahr asuba ba suka nufi asibitin,kasancewar da wuri za’a shiga tiyatar.
Duk da cewa ba magana zaimusu ba ko yasan suna wajen,amma ganinsa kafin ya turashi É—akin ma abune da basaso ya wuce su.
Ƙarfe 7:00 am daidai aka gama shirya tiyatar,suna nan tsaye a corridor ɗin aka turoshi,duk jikinsa an sassaka igiyoyi.
Ƙuri sukayi masa da ido kaman idan suka ƙirfa zai bace,da haka suna kallo har aka shiga dashi ɗakin ƙofah taja tarufe.
Hajiyah Zeenah da sayyada-tateen a tare suka saki kuka suna zubewa a wajen.
Kowa a wajen bashida bakin faɗa musu suyi shuru,alhj Abdullahi ne ma wanda abin bai shigeshi sosai ba yake ƙoƙarin basu haƙuri,itakam Lailah batazo bama tun zuwan ta na jiya,a cewarta ɗanta itama bashida lafiya,intazo ma ba abinda zata ƙara ko kuma ta rage.

Ƙarfe shabiyu daidai aka gama tiyatar,kuma Alhamdulillah anyi nasara,yanzu kuma sai ya farfaɗo aga mai sakamako zai bayar,wanda dama shine tashin hankalin.
A tsawon wannan lokacin banda roƙon Allah da fatan nasara babu abinda dangin Jabeer sukeyi,duk abinda ake a asibitin har sannan su Jawaheer suna sashensu itada Jaleelah,kaman yanda bombee tace kada su kuskura su fito suna ciki,zama daƙyar tashi daƙyar,saboda izayar da hilyan take shuka musu,abinda da jiki irinna masu hutu,duk sun goje sun sanja kama,komai su sukeyi a sashen dan bombee takori duk wata mai aiki daga sashen.
Lubnah kuwa tunda taji ance Jabeer ya bata,kuma ta tabbatar lallai aikinda tayi masa ya karye,saita É—auki abinda takeso na amfani ta nufi gidansu.
Nan ma gidannasu ba daɗi gareshi ba,shi ammar ya tattara yabar ƙasar ma gabaɗaya,daya gane cewar ashe uwarsa ta saida haihuwarsa akan buƙatarta,itakuma matarsa daya narke akan sonta ashe cikin wani take shirin laƙana masa.
Shikuwa gen abdu manga yarasa ma mai zaice da brr na’imah,kokuma mai zai mata a duniyar nan yahuce ko kuma yagyara abinda tasakashi aikatawa na tsawon lokaci.
Dan haka tsinuwa yayi mata ta uwa ta uba,dagannan ya É—au kayansa yabar gidan bayan yayi mata saki uku.
Ita sakin dayayi mata bai dameta ba,halinda Æ´aÆ´an ta suke ciki yafi komai tada mata hankali,gakuma wasu munanan halittu da suke hanata sakat a duk lokacin data rufe ido.
Ganin yadda gidan ya cakuÉ—e yasa lubnah yin hanyar nata É—akin,kuka tayishi har gaji ta sallama.
Ko nan da nan bata zuwa,koyaushe tana kusada banɗaki,saboda abinda yake ciyayowa daga ƙasanta,duk batajin zafi yanzu yazamo da ƙyar take zama kuma take tashi.
Yanke shawara tayi kan zata sayarda gwalagwalanta ta tafi asibiti neman magani,wataƙil sai ta dace,duk da tasan cewar hakan abune mai matuƙar wahala.

Wasa wasa anyi kusan sati guda da yiwa Jabeer tiyata,amma har yanxu bai farfaÉ—o,tun suna saka rai da tashinsa har sun fara karaya.
Bombee ce da Hajiyah Zeenah a wajensa suna kulada shi,kaman juyawa ta kuma goge jiki.
“Yakamata ki koma gida kawai zan kuladashi,tunda ba idonsa biyu ba,babu wani aiki sosai.
A gida kuma Baba yana buÆ™atarki,tunda shima bayida cikekkiyar lafiyah”
“Bombee ce tayi maganar wacce take zaune a kujera tana duba wani abu a labtop É—inta”
“Eh hakane kam mommah kizo mutafi tareda Abdulmaleek,kuma kinga abdulkareem ma yana nan zai dunga leÆ™osu,Abba yana gida daga shi sai Madeenah kawai”
Maleekah ce tayi maganar itama,dan tun jiya suke fama da ita ta tafi taƙi fafur..
Ga mamakinsu kuwa saita tashi ta É—auki jakarta,bakin gadon Jabeer É—in taje inda yake kwance kaman gawa.
“Kayi haÆ™uri nasan banida ikon daina zargin kaina amma……”
Bata karisa maganar ba maleekah taja hannunta suka fita waje,wacce itama hawayenne a fuskarta.
“Anty maryam mu zamu tafi,gobe ta sassafe zan dawo”
“Okay ba matsala maleekah”
Daga haka bata sake cewa komai ba har suka tafi,jin wajen yayi tsit daga ita sai numfashin ta,yasa ta ajiye system tareda nufar inda Jabeer yake kwance.
Rigar da take jikinsa ta cire tareda É—akko lotion É—in da ake goge masa jiki dashi.
Tana zubawa tana gogewa da tissue har saida tagama tass kafin tasanja masa wata rigar.
Kayan baccinta tasaka kana ta hau gadon gefensa ta kwanta..
Kallon gashin idonsa take wanda sukayi zarara,gani take kaman bacci yake zata ƙirashi ya amsa.
“Kada ka cire tsammani da dawowa garemu Jabeer,dan Allah katashi daga wannan baccin daka keyi,akwai mutane masu muhimmanci a rayuwarka da suke jiran wannan farkawar,inka tashi nayi alÆ™awarin faÉ—amaka duk wani abu dakake buÆ™atar sani daga gareni”
A haka tana sambatun a jikinsa har itama bacci ya É—auketa.

*** ***
A zaune yake a zuba tagumi a gidannasa dake cikin barrack,abin duniya ya taru yayi masa yawa yarasa shin ta ina zai fara.
Sati guda kenan da barinsa gida,amma yanda yaga dare haka yake ganin rana batareda ya samu maslaha ba.
Ƙwanƙwasa ƙofar akayi daga waje,saida yaɗau wasu lokuta kafin yabawa mai ƙwanƙwasawar damar shigowa.
Gen sameerah ce tashigo Falon kanta a tsaye fuskar nan a murtuƙe.
“Sir”
“Samu waje ki zauna”
Takulada sauyawar shugabannata,saidai batace komai ba ta zauna domin taji mai zaice.
“Kimsamomin bayanan gameda Gen Muhammad Bello?”
“Eh nasamo sir,baya Æ™asar nan yana India akan matsalar ciwon zuciyar dayake dashi,saidai iya ganin likita zayyi ya dawo.
Iyalansa kuma suna nan a garinnan cikin Æ™oshin lafiya”
“Kin tabbatar baya ga haka babu abinda yake faruwa na matsala gameda su?”
“Ehh babu yallabai,amma mai yasa ka damu dashi dakuma halin da ake ciki”
“Saboda kinsani nima nasani mune sanadiyyar mutuwar É—ansa da kuma silar rashin lafiyarsa”
“Amma yallabai wannan abune daya faru da daÉ—ewa,meyasa kake shirin dawo dashi baya?”.
“Saboda na gyara kuskuren dana aikata a bayan,zuwa gobe zan miÆ™a kaina dana iyalina a kotu har dake. Kan miyagun makaman da muke shigowa dasu,kisan Haidar É—an gen muhammad,barazanar mu na karbar Companyn JAAN,samun babban matsayi ta gurbatacciyar hanya.
Ita kuma matata zan maka ta kotu kan laifinta na rufe mugayen laifuka da kuma yiwa gurbatattun ayyuka shaidar bogi,sannan kuma sun haÉ—a da kisan kishiyoyin Æ´ar ta har guda biyu da suka haÉ—a da Æ´ata suka aikata..
Kekuma naki laifin shine An haÉ—a hannu dake wajen yin wadannan ayyukan dukka.”
Tashi tayi ta tsaya tsaye tana kallon gen abdu,gabaÉ—aya takasa gasgata abinda kunnenta suka jiyo.
“Amma yallabai?”
“Karki ce komai,sannan kuma kada kiyi Æ™oÆ™arin yin komai,gobe nida ke zamu ajiye uniform É—inmmu na khaki,wani satin kuma zamu nufi kotu domin girbar abinda muka shuka,bayan barrack sun zartar mana da namu hukuncin.
Kike gidanki dayake nan ki zauna,domin na bada oder daga kin shigo kar kowa yabarki ki fita”
Jikinta rawa yake tana jijjiga kai,ko a mafarki bata taba tunanin haka rayuwarta zata ƙare lokaci guda ba. Kuma wai a kurkuku,duk bayan wannan abubuwan da tayi? Kai inaaa hakan bazai tana yiyuwa ba.
Tana nan ƙame kaman dutsi har yatashi yafita daga falon.

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button