Bakar Ayah Book 2 Page 39-40
Page 🖤 39••40🖤
“Banjinki sosai Inayah Ki É—aga murya kaÉ—an”
“Ai babu dama ne anty maryam,wani abu muhimmi nakeson faÉ—amiki yanzu,wanda na tabbatar yakamata ki sani”
“Menene ina jinki”
“Uhm É—azu naji brr na’ima tana wani surkulle a É—aki,magana suke da wata mata,bayan kuma batayi baÆ™uwa na,sannan maganar batayi kama da ta waya ba sam.
“””Karki damu yake Komai bai bar hannuna yana Æ™arÆ™ashin ikona,tun kafin ta kasance a cikin komar ki ni tashiga tawa tun bata faÉ—o duniya ba,ita É—in kyauta ce a gareni,kuma gidan aljanuna,dolene na maidata sai abinda na sakata,kokuma na É—aiÉ—aita rayuwarta.
Inta kusada ita,kusa mafi kusanci saidai batada masaniyar hakan,su kansu sauran na san inda suke ta sanadiyyarta,ina jiran lokacine wanda zan aiwatar da ƙudirina akansu.
Ƴar kima kada ki damu,duk da bazata san nice ba,amma zan kulada ita fiyeda yanda kike sani,kedai kicigaba da abinda na muka umarceki dashi””””
“To haka matar naji tace”
“Iya haka kikaji,okay ba matsala kinyi koÆ™ari,amma kisake kulawa fah kada su gane,yawwa kin taba shiga É—akinta?”
“Ehh ina shiga sosai kaimata shayi”
“Madubi nawa ne a É—akin nata?”
“Eh biyune,É—aya yanada dreesing mirror da kayan shafe shafe,É—aya kuma a tsaye yake an rufeshi da wani baÆ™in Æ™yalle”
“Ohk na fahimta,naji abinda nakeson ji,sai an anjima”
Tana ajiye wayar rest room tashiga inda allon plan É—inta yake,zana inna lari tayi da Brr na’imah sai tayi link É—insu da Zilliyyah.
‘Okay inna fahimta daidai zancen da take na nice da kuma ahalina,wato bayan barinsu gyembu sun bata mata shirinta,hakanne yasa ta biyosu nan.
Tace tana kusa dani,amma duk shu’umancinta bazata iya bacewa ba ai,kuma tace tana kusa ba wai tasaka a ganni ba.
Duk yadda akayi tana cikin gidanann kenan kuma tayi badda kama’
Har tazo ajiye marker dake hannunta sai ta tsayah,tsohuwar dake musu aiki a sashen ta tuna,lokacin data tunkareta taji nauyin dayake kanta yana komawa ƙeyarta,data juya kuma taji yana komawa goshinta,maganar datakeji a kanta kuma a lokacin ta tsaya ɗiff.
Kenan aljanun dasuke kanta tsoron tsohuwar suka,kuma dama bata yarda da ita ba sam.
Ayar tambaya tasaka a sunan tareda yin murmushin samun nasara.
“Idan kuwa kece to lallai kinkawo kanki ramin kura……hahahaha”
*** ***
Tun lokacin da Jawaheer tagane wacece Jaleela,shikenan suka É—inke,babu zancen faÉ—a kuma,koyaushe tareda suke komai,sai dare yayi kowa ta tafi É—akinta,wacce Jabeer ke wajenta ya shiga.
Tun zuwansu a ranar ya aiwatar da ibadar aure shida Jaleelah,duk da cewa yanda yake tunanin zaiji bahaka yaji ba,amma kuma yasan babu wata matsala,dama kowacce mace da kalar ta.
A bangaren Jawaheer kam washagari a buÉ—e yasameta,duk sai bayyi wani mamaki sosai ba,dan biri yayi kamada mutum.
Da safe kyauta yayi musu mai tsoka,yaso yabawa Jaleelah wanda yafi yawa,saidai kuma yana tsoro kada yayi ba daidai ba.
Dan haka yabasu iri É—aya,saidai a wajen mu’amala kam yafi nunawa Jaleelah kulawa fiyeda Jawaheer,ga mamakinsa in suna tareda yake yiwa Jaleelah maganar soyayya bata damuwa sosai,yawanci idonta baya kansa yana kan Jaleelah,domin taga wane reaction zata bayar gameda maganar tasa,tana mayar masa martani kuwa zata É—ebi fushi tayi gaba fuuu.
In hakan yafaru haƙuri Jaleelah take bashi,kana daga bisani tabi bayan Jawaheer ɗin,akan zata bata hakuri,ko kuma wani lokacin suje tare.
Shi har yawon ma ya isheshi,ga bombee ko sau ɗari zai ƙira numberta bata ɗagawa,yayi ƙiran watan har ya gaji ya haƙura,ji yake kaman yayi tsuntsuwa ya tafi ya barsu,wani bangare na zuciyarsa kuma yana son zama da Jaleelah a nan ɗin,maybe Jawaheer ce ta bata masa budget. Domin Allah yaga haƙuri yake na nuna mata kulawa,ba kaman yanda zuciyarsa take so.
Watansu guda a dubai suka nufo Singapore,a nan kam barsu yayi ya tafi wani uzurinsa,akan sai bayan sati biyu zai dawo,su suka cigaba da yawon buÉ—e idonsu tare.
*** ***
“Haba Mommy har yanzu baki Æ™arisa bani É—aya mahaÉ—in maganin ba,wani satin fah Jabeer zai dawo,nagama shirin yanda zanyi yakwana a wajena idan baki bani abin yanzu ba taya zan gama shirin to”
“Kaii Dear kinada É—aga min hankali,baki ganin kullum busy nakene,ga Shari’ah sun sha min kai,ga shi wancan shashashan É—an unnawaki,tunda suka dawo Æ™asar jiya ya shiga sashensa banganshi ba..
Shi a dole matarsa tanada ciki,motsi kaÉ—an ya dubata motsi kaÉ—an ya dubata,ni ina tunanin anya ma kuwa É—an cikinta nasane?”
“Meyasa kikace haka mommy,ko shima yanada irin matsalata bai sani ba kai?”
“Uhm da alama,amma bar wannan zancen ba yanzu ba zanyi maganinsu ne idan naga dama,baridai aikina ya kammala.
Yanzu mai kikayi shirin bayarwa kafin aikin yaci”
“Ohh sai an bada wani abu?”
“Ehh Æ™warai ma kuwa,mai zaki bayar a faÉ—ama ta,kuma kada ki manta banda kuÉ—i fah,abinda kuÉ—i baya saya take karba”
“Uhm zan bada mahaifata tunda batada amfani”
“Bakiji nace miki mai amfani take karba ba?”
“Uhmm to nabada lafiya ta”
“Kutt bakida hankali ne wai,taya zakiyi ikon babu lafiyah?”
“Ahah ba iya haka ba,amma da sharaÉ—in idan bazasu karba ba har sai nayi wata ban haÉ—u da wanka nake mulka ba,in mutuwa kuma yayi babu zancen É—aukar lafiyar,kinaga yayi?”
“Hmmm ina jiyewa dabbancinki,tunda kince haka shikenan,saiki kafa masa sharaÉ—i akan kada ya kuskura yayi wata guda baki ganshi ba”
“Ehh hakan yayi indai zan samu biyan buÆ™ata”
*** ***
Tun safe take kulada shige da ficen Zaleeha a gidan.
Hasashenta kuwa ya fara tabbata,tabbas akwai abinda tsohuwar take kissimawa,ba Hajiyah Zeenah take yiwa aiki ba,aikin kanta takeyi kawai,tunda yanzu ai Jabeer baya nan,bai kamata tacigaba da saka ido ba.
Kokai itama Hajiyah Zeenah da hannunta aciki.
Ita kaɗai dai take saƙarta tana kuncewa,har lokacin dataga tafita daga side ɗinnasu ta tafi.
Kamar jira take kuwa da sauri tafito daga sashenta ta nufi É—akin Zaleehan,dan dama shekaranjiya ta Copy key É—inta data tafi banÉ—aki.
BuÉ—ewa tayi tashiga É—akin,tanajin cikin kanta ana bata umarni ta fita,amma tayi biris dasu tacigaba da bincikenta.
Su Æ™oran maganine,kayin su macizai,hadda na jinjiri da gani,magunguna kam ba’a maganarsu su.
Idonta ne yakai kam madubin dake É—akin,sak iri É—aya dana É—akin inna laari wanda tasani,saidai shi wannan maimakon adon yellow,da jini aka shafe gefe da gefensa,wato na ogah kenan.
Saida taƙare share tantamarta kafin ta fito daga ɗakin.
A filin harabar gidan ta zauna sunata waya da innayi,tanayi mata ƙorafin karatu da wuyah sosai.
“Kinga ni ba Æ™orafin karatu na Æ™ira kiyimin ba,bayan ni da kuma hilyan akwai wacce ta taba zuwa gidannan?”
“Ehh…to banda almajirai dai,sai wata mata da ta taba zuwa wai a taimaka mata da ruwa,daga nan banga kowa yaxo ba,saidai bansani ba ko ina makaranta”
“To koma menene ki faÉ—awa sauran dukka su tabbatar baku sake barin wata baÆ™uwar fuska tashiga gidannan ba,kina jina koh?”
“Ehh naji addha maryam,uhm ki cewa maleekah lafiyah jiya naga ta dawo gida da wuri,bayan kuma tace sai yamma?”
“Cikinta ne ke ciwo,nan tazo ta kwantamin ai har yamman.
Kinji abinda na faÉ—amiki ku kula,idan nayi solving wani abuma dukka zaku dawo nan gabana,wajennan jikina bai bani akwai safe ba,kowanne lokaci komai na iya faruwa”
“Hakane kam amma addah ki dunga zaton alkhairi a kullum”
“Iyee wai kurace zatace da kare maye,don ruwa ya doki babban zakara koh? Duk ba uwarkice ta faro komai ba,yanzu gashi duk da ta haukace ban huta da warware abinda ta Æ™ulla ba”
“Kiyi haÆ™uri addah bombee dan Allah ”
“In banyi haÆ™uri na kashe kaina zanyi na barku da ita ta É—aiÉ—ata ku?,
Sai anjima ki kulada kanki da kuma inna,sannan ki maida hankali kiyi karatu kinji?”
“Uhm naji”
“Tamm”
Tana nan zaune har zaleeha ta shigo gidan ta ƙullin leda a hannunta.
Ƙwallamata ƙira tayi da ƙarfi,da sauri kuwa ta amsa tataho.
“Gani Hajiyah”
Wata yatsina bombee tayi,aranta tana cewa Æ´ar wasan kwaikwayo. Tasan dole tayi taka tsantsan,komai tayishi a iya cikin ranta kawai.
“Uhm nace ba jeki sharemin Wajen training É—ina ta baya,kiyi sauri kuma kafin magriba tayi”
“Hajiyah naji kince bazan yi aiki a sashenki ba”
“Dama ina ni nace,to yanzu kuma na sanja magana,na gaji dayin ayyukan gidan,hutu nakesonyi,dan haka kice ki sharemin yanzu,ko kuma kibar aiki a sashennan”
Ga hasashenta kuwa da sauri ta nufi wajen sharar kafin ta koreta,da alama komai zatayi indai baza’a koreta ba.
Kaman yanda bombee ta faɗamata kuwa sai wajen magriba ta gama sharar,lokacin ta tashi a wajen tashiga ciki,bakin ƙofar shiga falonta taje ta ƙwanƙwasa mata.
BuÉ—ewa tayi tareda cewa.
“Har kin gama sharar?”
“Eh nagama hajiya”
“Ohk to jirani ina zuwa yanzunnan”
Bata daÉ—e da shigaba tafito da kwanon abinci a hannunta.
“Gashinan idan zaki ci,nayi yamin yawa”
Taƙarisa maganar tana miƙawa Zaleeha kwanon,tantamar karba tayi da farko,saidai daga ganin yanayin yanda bombee take mata tasan batasan ita wacece ba,dan haka ta tsugunna har ƙasa ta karbi kwanon ta tafi.
Sai bayan tabar wajen bombee tayi murmushi tareda cewa,
“Hmmm zakici bantan ubanki dani kike zancen,inkin fini da rarrafe aradu nikuwa saina fiki da tafiya”
Wayarta ta ɗakko da sauri ta bugawa wani ƙira.
“Hello khamees maza kazo yanzunnan,domin da daddare nakeson ayi komai a gama zuwa safiya,na tabbatar zata ci abincin”
Tunda zaleeha taci abincinta da bombee ta bata,bayan ta gama dubashi babu wani magani a ciki,dan in akwai dole zata gani ne.
Tunda taci abincin ta kwanta a wajen sai bacci,bata tashi sanin mai yake damunta ba saida ta bude ido ta ganta a asibiti.
Bombee ce a tsaye a window tana ta zuba tsuka da mita.
“Haba tsiyarka da tsoho kenan,daga sun kwanta kuma ba kanta”
Tarin da zaleeha tayine yasa ta juyo ta kalleta.
“Hajiya mai ya faru”
“Ohh shine tambayarki,jiya naje yimiki magana akan jagwalgwalon sharar dakikayi min na ganki a kwance numfashinki yana sama da Æ™asa.
Likita yace kinsamu heart failure,wataƙila kinsaka abu a ranki ne.
Yanzu dai gashinan ya cire miki jinin daya taru a gefen Æ™irjinki,ki duba zaki gani,ni zan tafi idan kin gama warkewa ki faÉ—awa likitan zan turo mota a É—aukeki”
Tana gama maganar ta zari jakarta tayi waje,sai bayan ta fita ta tuncire da dariyah.
“Zilliyyah kinshigo hannuna finally,you are my ride to successed”
Ita kuwa zaleeha jugum tayi tana tunanin maganar da bombee ta faÉ—amata.
‘anya kuwa ba wani abu ta saka mata a abinci ba,to kuma ya akayi bataji komai ba,kuma in abu tasaka mata ta tabbatar na mutuwa zata saka mata,wanda kuma aljanunta bazasu bari taci ba,inaga to ciwonne da ita,gaskiya batasan ita wacece ba kam tunda har tayi mata magani’
Tana cikin wasiwasinne likitan ya shigo da magani a hannunsa da kuma plate na abinci.
“Iyah sannu ya jiki,ki dunga kulada lafiyarki sosai,banda takawoki da wuri da tuni abin yayi tsanani,yanzu dai zamu riÆ™eki nanda sati guda kafin ki tafi”
“Sati guda kuma likita,ahah bazan iya zama ba,jikina bayason wajennan,kabani maganin na tafi,zanyi amfani dashi yanda ya kamata”
Da farko yaƙi amincewa,amma ganin yanda ta damu yasa ya bata maganin tareda kafa mata sharaɗu na musamman.
Bombee kuwa a hanya tazo shiga motarta suka ci karo da wata likita,É—agowa tayi zata fara magana,saikuma ta zare ido tareda cewa.
“Kuttt Rahama…..serious kece,yana ganki da farin kaya bayan na khaki?”
“Uhmm labari da yawa Captain maryam,tun bayan da aka miki wannan shunen komai ya rikice,Gen Muhammad yau da lafiya gobe babu,Æ™arshe ma ya ajiye aikin,nima ganin haka yasa na tafi karatun likitar mata,yanzu haka nice babbar likita mai duba mata a asibitinnan,amma muje office mana ki sha ruwa Captain nasan akwai labarai da yawa koh”
“Da akwai kam amma ba lokacin bayar dasu,yanzu haka wai ina aure ne ma fah,amma dai ba standard ba”
“Aure captain ko a mafarki bantaba zato ba,nima É—a guda É—ayane nake da shi,wa kike aure dan ina samun lokaci zanzo miki Shugaba shugaba”
“Hmmm da basai kinzo ba amma nasanki da naci,Jabeer Jaan nake aure,CEO na JAAN Company”
“Wow kin kama babban kifi captain,amma…..naji ance ya Æ™ara aure ai mata biyu koh?”
Kinga bari nayi gaba Rahama,da alama bayan Likitar harda jarida kika karanta”
Dariya ta sheqe da ita tareda cewa.
“Bazaki sanjaba Captain,to sai nazo zaki ganni”
Yau gidan da hidima aka tashi kowanne sashen,inka É—auke na bombee,itace kawai babu abinda take na taryar angonnata.
Hajiyah Zeenah tanayi,Madeenah da kuma iyah sayyada sunayi a nasu sashen,domin sune mutanen Jaleelah,itakuma hajiya ta Jawaheer ce.
Sai shugaba lubnah wacce take shirin taryar mai gidannata da manufofi masu dama.
Maleekah ce a rest room tasaka head phone a kunne,duk ƙiran da Abdulmaleek yake yi mata bata jishi ba,saida ya jijjigata tukunna.
“Ke Dujal É—in gidannan uwar san waÆ™oÆ™i,tashi muje ki rakani É—akko big bro mana a airport.
Ke ana can ana shirin tarbarsu kina nan hankali kwance”
“Ahh to mai zanyi,wacce nake side É—inta kona ce ta taryeshi ma bazata tareshi ba,amma kuma kada kasha mamaki duk welcom É—inta sai yafi burgeka,shima nasan duk itace a ransa yanzu haka,burin sa ya haÉ—u da ita”
“Taya kika sani?”
“Bari kaga,idan mun dawo ka kulada ina zai fara zuwa,zaka ganewa idonka”
“Wai nikam har haka take kikeda confidence a kanta”
“Har yafima,kobaku yarda da maganata yanzu ba zaku yarda,am sure a rayuwa irinta yah Jabeer,anty maryam kaÉ—ai yake buÆ™ata tatsaya a gefensa”
“Hmm ke muje ni”
Su biyu suka tafi ɗakkosu daga filin jirgin,shikam Abdulkareem tunda ya dawo hutun sati guda yayi asibiti suka buƙaceshi ruwa a jallo,ba zama kenan.
Basu daÉ—e da isa ba jirginsu yayi landing,a tare suka fito su ukun kowacce tana gefensa guda,sukam sunyi fresh da kyau,amma uban gayyar kam ba hakan a tattare dashi sam.
Su ukune masu taryar tasu,kowacce ma anzo daga gidansu,babu ya Hajiyah rabi,kaman zata mutse dan murna,ganin yadda Æ´ar tata tayi fresh gwanim ban sha’awa.
Dukka Jaan estate aka nufah,gida ya cika kaman ana ƙaramin biki.
A cikin wanann taron Jabeer yasamu yazame ya nufi side É—insa,duk akan idon su maleekah wanda suka bishi a baya.
Bai shiga nasa sashensa ba sai ya buÉ—e na bombee.
Binsa sukayi a hankali suma,Abdulmaleek da ƙin shiga yayi,amma maleekah tajashi ƙarfi da yaji.
A zaune take akan kujera da waya a hannunta kamar kullum.
Taji buɗewar ƙofar,amma bata ɗago taga waye ba,duk da turarensa ma yabata amsa.
A yanda take zaunen ta yi magana.
“Ƴan yawan amarci kun dawo ne?”
A tsaye yake bai ƙarisa wajen ta ba.
“Can you drop your phone,sannan kuma ki tashi ki tsaya?”
ÆŠago da idanuwanta tayi ta waresu akan sa,wanda sukayi tayi masa kizo a cikin watan dayayi batareda yagansu ba.
Tashi tayi kaman yanda yace,batareda tace komai ba.
Ƙarisawa yayi inda take tareda ƙanƙameta a jikinsa kaman zai maidata cikinsa.
“Uhmm i miss you koda ke baki yi tawa kewar ba,kin kyauta kuma da Æ™in É—aga wayata,ni zan shiga wanka,please ki samomin abinda zanci marar nauyi”
Yana gama faÉ—in hakan ya saketa tareda yi mata peck a goshi.
Haidar ya É—aga sama wanda yake ta yawo a cikin falon akan keken tafiyarsa.
“Boy kai kayi missing É—ina koh,koda mommoynka batayi ba”
ÆŠaki yashige da yaron a hannunsa yana yimasa magana kaman zai amsa masa.
Sai bayan ya shiga ciki kafin su maleekah suka bar sashen.
“To mai nace maka yah abdul uhm?”
“Ehh zancenki gaskiyane,duk cikinsu da alama ita yake yiwa son gaskiya batareda yasani ba,to amma wanann yaron kuma fah,shima naga Æ™wayar idonnasa irin nata ne,inda itama idonta blue bane da saina ce anya kuwa É—an ta ne?”
“Meyasa kace haka,É—an tane mana dashi tazo fah,saidai ta harmata yimata tambaya akansa”
Bayan ya fito daga wankane ya kula ba haidar akan gado inda ya ajiyeshi,sai kayansa na shan iska kawai.
Murmushi yayi na jin daɗi,har saida haƙoransa suka fito.
Sakawa yayi tareda fita falon,batagama abincin ba da alama,dan yaji motsinta a kirchen.
Zama yayi akan kujera ya kunna tv yana kallo.
Tunda Lubnah taji shigowar Jabeer take zuba idon shigowarsa amma shuru har wajen yamma.
In ranta yayi dubu to ya baci,abincin data haÉ—a ta zuba a cikin dust bin,ga matsin datayi da magani tun safe sai damunta yake,kayan kwalliyar data saka ta yage ta zubar,tun tana kuka mai sauti har ta daina bacci ya É—auketa a wajen.
Sai can duhun dare yafara taji alamun motsin mutum yana tashinta.
Ware idonta tayi akan Jabeer wanda yake tsugunne a gaban kujerar da take.
Kuka tasaka masa irinna kirsa tareda kaiwa hannunta kan fuskarsa.
“Kowa yarabani da mijina,sun rabani dakai gabaÉ—aya,tun safe na kasa zama saboda É—okin dawowarka,amma ka kalli sanda na ganka saida daddare,yanzu na cancanci haka honey uhm?”
Sake fashewa tayi da wani kukan,wanda yaƙara saka jikinsa yin sanyi. Jawota yayi jikinsa yana rarrashinta.
Ta kuwa ƙara lafewa dan hakan takeso dama.
A sannu a hankali take jansa da kissa har kan gadonta,da farko yaƙi amincewa,sai kuma ya tuna da tsawon lokacin dayayi baya ɗakinta,duk da kuwa laifinta ne,amma yasan wani lokacin da nasa.
Salo take ta aika masa na buƙata,yayinda shikuma yake ta ƙoƙarin biye mata,duk da baya buƙatar hakan.
BuÉ—e baki yayi zayyi addu’ar ibadar aure,kafin ya furta wata kalmar tayi saurin haÉ—e bakinsa da nata waje É—ayah.
A haka naja musu ƙofa nima na datse alƙalamina akan wanann shafin.
Saikuma Allah ya kaimu na gaba……
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________