Sponsored Links
Bakar Ayah Hausa NovelHausa Novels

Bakar Ayah 23

Sponsored Links

Page 🖤23🖤

 

Ana gama ɗaura auren yaji wani nauyi ya sauƙa a ransa,duk da cewar ba haka yaso auren yar tasa yazo ba,amma kuma yaji daɗi ganin ya aurar da ita kafin tagama fin ƙarfinsa.
Yaso tayi karatu tazama wani abu a wannan rayuwa saboda takare kanta,amma kuma kana naka Allah yana nasa,inaga wannan shine tata kaddarar ba wacce yake zata mata ba,fatansa shine allah yabasu zaman lafiya da mijinnata.
A ranar kuma Daneji ta haɗu abun bazata,wanda bazata ta’ba mantawa ba.
Shatu ce tayi mata magana daga ɗaki kan tafito tayi baƙi.
Yayunta ne biyu maza da kuma dadarta wacce take auren ɗan Yayan baffansu da ƴaƴanta itama masu aure guda biyu.
Kasa gasgata ta tayi,dan har ta fito ta tsayah a gabansu gani take kaman idonta ƙarya yake faɗamata gameda bayyanar tasu.
Saida ta tabbatar da gaskene kafin ta fashe dakuka ta faɗawa tayi kam Addar tata,wacce dama kusan ita tarene ta ba innarta ba.
Fillanci aka juyeyi na ɗan wasu lokuta,kafin tajasu ɗakinnata tafara basu labarin abinda yafaru,yawancin labarin ma bata basu ainihin yanda yakeba,ta boyemusu abubuwa da dama.
“Ahh Danen Baffah kene da auren ƴa ohh,aida mai saƙo ya iskemu wai inji mlm Ahmadu cewar za’ayi auren Bombee munyi mamaki sosai”
Kallonsu Daneji tayi da alamar tambaya,mlm Ahmadu kuma? Dama yasan inda suke?”
“Kinga bai san inda muke ba,inaga yatura masu saƙone da dama wani ya iskemu ya fadamana. Da Allah yasama zamu iso akan lokaci kinga ashe damu za’ayi”
“Koma ta ina yasameku gaskiya naji dadin ganinku,ina innatah tana lafiyah”
Shuru HADIZA tayi Addar daneji jin tambayar da danejin tayi mata.
“Kiyi haƙuri Daneji amma inna kam tayi shekara kusan goma da rasuwa,saidai muyi mata Addu’a Allah ya jiƙanta”
Shuru Daneji tayi tareda sunkuyar dakai,sai can kuma tashare ƙwallar idonta tareda ƙaƙaro murmushi,shikenan babu komai,amma da ansamu wani ai yazo ya faɗamin lokacin?”
“Kiyi haƙuri,amma baffah ne yace kar a faɗamiki lokacin,kema ga ga halin kaɗaicin dakike ciki,kiyi haƙuri kiyi mata Addu’a kawai,dan shi take buƙata a yanzu.
Ina Amaryar ne tunda muka shigo banganta ba”
“Gaban Daneji ne yafaɗi,ita kwata kwata ta manta ma da bikin ƴar akeyi,tsabar ganin ƴan uwanta ya kaɗe mata hankali”
Toh fah ina Amaryah manya,bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida…….!!!
Tashi Daneji tayi tanufi ɗakin su Bombee domin ƙiranta.
A kwance take tana taunar cingam irin na aurenta wanda ta zaro kwali guda ba’asani ba.
Babu kowa a ɗakin sai innayi wacce take taya shatu gyarawa Bombee kayanta.
“Addah Bombee a saka wannan ko kin ban shi”
“Ahah ban baki ba,wai wayace ma ki tattaramin kayana ne dukka,cewa aka ce miki bazan dawo na tafi kenan saikace ɗaukar rai”
“Inji waye yace zaki dawo toh,koni kinga na koma gidanmu,canne gidanki daga yanxu,nasakeji kinyi zancen dawo zaki gamu dani,kenan da shekara ma idan na ganki a gidannan zakiga yanda zanyi dake”
Daneji ta amshe maganr wacce shigowarta kenan tazo ƙiranta,shatu tana ta aikin gyaramata kayan dazata tafi dashi batayi magana ba,dan tasan halin Bombee ba ragamata zatayi ba,wanda bai bar iyayensa ba wazai bari kuma.
“Sannu Innar muruje da ƙoƙari,kina fama da ita koh?”
“Uhm lahh ba komai itada ƴar uwartata ne suke gardamar bankwana,zatazo kuma tayi kewarta nan gaba”
“Hmm batada hankali ai,tana girma tana cin ƙasa,wai wannan akayi aure….allah dai ya kyauta kawai,tashi kixo wata innar taki tana ƙiranki,addah ta Hadiza sunzo dasu kawunan ki,harda ƴaƴan ta,addodinki”
“Hmmm yanzun mai yakawosu kuma,duk tsawon lokaci dakikayi kina tunaninsu da kewarsu basuzo ba sai yanzu,mai yahaɗani dasu mai zasumin?”
Bombee tafaɗa tana yatsina fuska tareda tauna cingam ɗin bakinta yabada ƙarar ƙasss”
Duk Daneji takaiwa Bombee a bombom dinta,dan dama a kwance take tayi bake bake akan gadonnata,wanda zata barshi yau.
Saurin tashi tayi tana zumbura baki,tareda gallawa innayi harara wacce suka haɗa ido,da sauri kuwa ta ɗauke kanta,dan tasan tsaff zatayi mata dukan bankwana kafin ta tafi.
“Dallah wuce muje ki gaishesu,ƴan uwannawa kikeyiwa wannan maganar,sauran kuma idan kinje ki nuna musu ban isa dake ba”
Boll tayi da kayan dasu innayi suka gyara kafin tafita daga ɗakin,itama Daneji tabi bayansu yana jijjiga kai na takaici.
A bakin ƙofar ɗakin ta tsayah,saida ta ƙaremusu kallo kafin ta taka ƙafa zuwa shiga ɗakin.
Wata mai kamada innarta fitik ce,saidai tafi innartata ɗan duhu da kuma manyanta,sai kuma wasu mata guda biyu,wanda a kallah ƙaramar ma zata bata shekara biyu a haife. Dukkan su fararrne ƙall jinin fulani gaba da baya.
Murmushi babbar tayiwa Bombee,da alama tanada sanyin rai ba kamar ƙaramar ba. Suna haɗa ido tasake murtuƙe fuska,ita a dole innarta ta daketa akansu.
A kan kujerar ɗakin ta zauna tana binsu da ido ɗaya bayan ɗaya,sai can kaman bazatayi magana ba tace “ina Wuni” a cikin ƙaramar murya.
Yanda ta kalli Addah Hadiza taƙasan idone kawai zai nuna da ita take,shima dan sun haɗa ido da Daneji ne,wacce take bakin ƙofa ta kafeta da ido.
“Lafiya”
Ta faɗa cikeda mamakin Bombee,sukuwa sauran ko kallonsu bata sakeyi ba.
“Su baki gansu bane ko bazaki gaishesu ba?”
“Inna sufa yarane ba iyayena ba,kuma…..kinsan rabona da gaisuwa na daɗe,ni na manta yanda akeyi ma,tunda sun ganni ai shikenan,basu zo lokacin ina kan gaisuwata ba da sun shata har sun ƙoshi”
“Ohh wato kinsan da kina gaisuwar kenan?”
“Nasani mana,lokacin tun shaiɗan yana dan ƙyauye bansan mai nake ba lokacin,amma yanzu kam hmmmm…….”
Dukkan su zuba mata ido sukayi kaman sun samu TV,yanda Daneji ta basu labarinta ma har yafi haka.
“Amma Ƴar uwa Bombee kina gani sosai kuwa da yanayin idonki?”
Babbar ƴar Hadiza mai Sunan Bombee wato Maryam ta tambayeta.
“Lalumen katanga kikaga inayi dana shigo?”
“Kinga tashi kije zaure wajen kawunan naki suma ki gaishesu,Dan Allah kuma kiyi aikin hankali,banda shiririta”
“Tom”
Tana faɗin haka zuruff tafice,dama kaman akan ƙaya haka take jinta,gabaɗaya an cika gidan da hayaniya,idan akwai abinda ta tsana bai wuce tarin mutane ba,shiyasa tafi kare rayuwarta a jeji gidan Maharbi Uwaisu. Musamman idan dare yayi halittu suna fitowa kala kala,wasu har wajenta suke zuwan sunyi zaton bata kallomsu kaman sauran mutane,yanayin yana yimata daɗi sosai.
Tun yamma gidan yafara karbar baƙuntar mutane ƴan ɗaukar amarya daga rugar su goje,dan dama su sannan ne bikin zai fara idan dare yayi.
Shirye shiriye aka fara na kaiwa amaryah da misalin ƙarfe 11:30 na dare,hakanma dan mlm Ahmadu ya nuna cewar bayason ɗaukar darenne tukunna.
Ɗakin mlm Ahmadu dake zauren Daneji ta rakata,babu kowa a ɗakin daga mlm Ahmadu sai inna laari,saikuma Daneji ta itama ta zauna a ɗaya gefen mlm Ahmadun.
Ita kuma uwar gayyar tana tsugunne a gabansu an rufa mata farin mayani akanta.
“Toh bismillahi da Sunan Allah……Maryama kamar yaune aka haifeki na riƙeki akan tafukan hannuna ina murna da zuwanki duniyah,bayan tsawon lokaci dana fidda rai da rabon ganin jinina a duniyah. Yau kuma gashi na ɗaura miki aure zaki tafi kema gidan mijinki inda zakiyi taki rayuwar.
Nasihar dazanmiki shine,kizama mai haƙuri da kuma biyyah sannan da juriyah,sauran halaye kuma idan ke mai yawo ce nasan kingama ɗaukar su daga wajen innarki a yau da kullum.
Duk da bakan abokiyar zama za’a kaiki ba,amma ina shawartarki da ki kwantar da hankalin ki idan wata taxo ta sameki cikin gidanki,kiyi koyi dasu innarki anan gida,yanda suka haɗe kai suke zaune ƙalau.
In bada ƙwaƙwƙwaran dalili ba banyadda naga ƙafarki cikin gidannan ba dasunan kinkawo kara ko kuma kinyi rigima,sannan karki yarda yakawomin kararki nan. Idan hakan yafaru bazan hanaki zaman gidannan ba a matsayin ki na mace,amma zan fita lamarinki bani bake,dan haka kizauna lafiya da mijinki da kuma ƴan uwansa.
Wannan shine iya abinda zan faɗamiki a matsayina na mahaifi”
Bayan yagama yimata jawabin,itama inna laari tayi mata nata na jan hankali,inda ita harta kara dsyimata bayanin haƙƙin miji dake kanta..
Duk abinda suke faɗa Bombee tana zaune gungurun,bata motsa ba sannan kuma batace uffan ba har suka gama.
Inna laari kam itada Daneji harda ƴar ƙwallarsu,da alama sun tuna sanda suka bar nasu gidan,amma ita wannan mai tafiya yanzu ma,tana zaune kaman dutsi,duk maganar da akayi mata babu wacce tashigeta kaman an tsikari kakkausa.
Inna laari ta tashi ta kama hannunta suka fita,dan dama itace mai rakata ɗakin itada Inna Hadiza.
Babu laifi kofar tata an gyara to sosai,dan ginin bulon siminti ma yayi mata,gashi an ja ƙofar an kewayeta daga cikin gidan.
Kayama mlm Ahmadu yayi mata masu kyau an saka mata,kowa sai yaba kyan ƙofar yake da yanda tasha kaya.
Ɗakine guda ɗaya sai kicin da gefe da kuma banɗaki,saidai ɗakin babbane sosai,dan yacinye dukka kayan harda sauran fili.
A kan kadonnata aka zaunar da itah,wannan aikin inna laari ne,ita ta matsa dole saida aka yimata jere kafin akaita,kuma hakan yakawomsu sauƙi,dan babu wani sake yin jere washegari.
“Toh Bombee ga ɗakinki mun kawoki,mu yanxu zamu tafi,dan mlm yace karmu makwana komin dare mu koma gida. Dan Allah kiyi amfani da abinda aka faɗamiki jiya kinji?”
Shuru Bombee tayi bata kulata ba,saima wangale mayafin da aka nannaɗeta dashi take ƙoƙarin yi.
Da Sakeena suka haɗa ido ƴar gidan Shatu wacce take kusan sa’ar Bombee ce,da kaɗan Bombee tafita dama. Ita kadaice wani lokacin suke maganar arziƙi da Bombee,shima dan tanada shuru shuru ne bata biyeta,hakan ma ba koyaushe take kulata ba,saidai idan tayi wani abun ta tambayeta itakuma da bata amsa.
“Hmm kinajin tanayi miki magana kikayi banza da ita Bombee?”
“Sau nawa zan faɗamiki cewar matar nan batayimin ba,haka nakejin bana sonta a raina yanxu”
“Dama wakikeso tunda kika zama haka bada kanki,ni barikiga na tafi,saina zo miki”
“Dama yanzu zan koreki in baki tafi bama,kinsan ba abinda na tsana kaman wannan wa’azin,inkikace zaki dameni to zan daina kulaki”
“Hmm nina tafi kafin ki huce akaina saikin ganni”
“Hhhhhh wani saikin ganni,saikun ganni dai,nufinku shikenan daga nan na tsayah daga farawa,mai ma nayi toh”
“Bombeeeee!!!! Kinji fah mai Babanku yace idan kikayi wani abun?”
“Ina ubana kikace ba ubanki ba uwar iyayi”
Gum sakeena tayi da bakinta tareda barin ɗakin tabi yan rakiyar amaryah.
Tana ganin sun tafi babu kowa tasake ajiyar zuciya tareda kwantawa akan gadon.
Baje ƙafafunta tayi,ita kaɗai ta saka dariyah kaman mahaukaciyah sabon kamu.
A haka bata saniba har bacci yayi awon gaba da ita…..

 

_*Sadi-sakhna ce*_

Share
Comment
Like
Follow
Fisabilillah 🙏🏼

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK1_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

 

*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

______________****_______________

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button