Arubuce Ta Ke 50
Page 50
Blue black abaya mai sulbi ce a jikinta me rubi biyu,qafafunta saye cikin wasu slippers masu kyau qirar kamfanin DKNY light blue,mayafin abayar kawai ta yafa,bata wani tsaya rolling ba,tana janye da qaramar akwatunta har xuwa bakin motarsa qirar BMW.
Yana jingine jikin motar yana amsa waya,a hankali idanunsa suka sauka a kanta,yana matuqar son ado da kwalliya,wannan dalilin yasa baya rabo da siyawa hafsat kayan qyale qyale na mata,saidai baya ce ga inda take kaisu ba,bata saka ba bata kuma bayar ba,a yanzun data saka abayar favourite color dinsa,sai yaga tayi masa kyau sosai a ido,karon farko kenan.
Gabansa ta tsaya da akwatin,ta langabe kai gefe tana mele baki,tanason gaya masa ba zata iya daga akwatin bane,janye idanunsa daga kanta yayi,ya karanci me takeson fada,sai ya zaro key din motar daga aljihunsa ya soma takawa a hankali.
Zagayawa yayi ya bude booth din motar,yasa hannu daya ya daga akwatin cak ya saka ya maida booth din ya rufe.
Bismillah yayi yana daura seat belts dinsa,yadan saci kallonta,yana mamakin yadda take qaunar turare,gaba daya qamshinta ya cika motar,ya lumshe idanunsa a hankali,yana jin wani yanayi cikin jikinsa,he missed his wife alort,yayi qoqarin,more than two weeks rabonsa da ita,shi yasa yakeso yayi surprising dinta,yau ba mita ko qorafi duka sun qare,abu daya ke sanyaya masa gwiwa,yasan ba lallai ya samu wata tarbar arziqi,infact baisan ma a yanayin da zai cimmata ba,may be su buge da samun sabani kamar yadda ya zame ma hafsat din sunna,duk sanda ya dawo daga tafiya goma,to bakwai a ciki a ranar daya iso sai wani abun ya hadasu,duk kuwa da cewa shi din mutum ne mai yawan kawaici,wanda bai fiya qorafi akan abu ba idan ba cikashi kayi ba.
“Kiyi addu’a” yace da widad yana shirin tada motar,kafin ya gama rufe bakinsa wayarsa ta dauki kuwwa,sai ya qarasa kunna motar ya barta tana daukan zafi ya duba me kiran.
Hajiyansa ce,nutsuwa yayi sosai ya daga wayar a ladabce yayi sallama,ta amsa masa cikin nuna kulawa da qauna,ya soma gaisheta gami da tambayarta lafiyarta,duk da jiya ma da yammaci sunyi waya da ita
“Yaushe zaka zo gida ne?,ka manta kabar wata iyalin naka a nan?” Tambayar yaji banbarakwai,saboda ba al’adar hajiya bane yi masa irin wannan tambayar
“Yanzun haka ma muna cikin mota zamu fito daga Kadunan…..”
“To alhmdlh ma sha Allah” haka kawai yaji zuciyarsa da ransa basu kwanta masa ba
“Hajiya lafiya dai ko?,ko wani abunne ya faru?”
“Babu komai,Allah ya tsare hanya”
“Hafsat ce ta kawo miki maganar?” Ya sake dai tambayar hajiyan
“Nace babu komai,Allah ya tsare hanya,ina widad din?” Waiwaya yayi yana kallonta,ita sam hankalinta ma da alama baya wajen,yana farfajiyar gidan inda mai gadin gidan yaketa gyaran flowers,dauke kansa yayi ya maida gabansa
“Tare zamu taho in sha Allah”
“To hakan yayi,sai kun iso”
“Madalla hajiya,Allah ya saka da alkhairi” sukayi sallama kowa ya aje wayar.
Iska ya furzar yana tada motar,idan ya rantse ko kaffara bazaiyi ba hafsat ce takai qararsa wajen hajiyan,don ya sansano hakan daga muryar hajiyan,yasan ta boye masa ne kawai saboda kare martabar hafsa a wajensa,wai me yasa ita din bata jin kunya ko nauyin kaishi qara?,yanzun wannan abun har ya isa takai qararsa gaba?, just one week daya qara baizo ba?,bayan he explains to her?,baisan sai yaushe zata fahimci illar wannan muguwar dabi’ar tata ba,baisan sai yaushe zata gane zubarwa da kanta kima da daraja takeyi a wajen iyayensa ba.
Ya danyi gudu,hakanan banda sallah basu tsaya sunyi komai ba a hanya,don haka awanni biyu da rabi suka kawosu bauchi daga kaduna.
Ba’a jima da idar da sallar la’asar ba suka shiga unguwarsu,ya faka motar a harabar gidansa,kafin ya sake wani abu tuni widad ta balle murfin motar ta fice saboda hangosu mimi da tayi,suma tuni sukayo wajen,saboda sun shaida motar daddyn nasu.
Binta yayi da kallo kawai,har zuwa sanda ta isa garesu suka rungume juna,sannan suka iso bakin motarsa suna dakon fitowarsa.
Tare suka rankaya zuwa ciki,mimi da nawwara kowacce na bada nata zancan,fuskar widad fal fara’a,har suka isa falon hafsat din.
Kallo daya ya yiwa falon yaji bacin rai ya saukar masa,kullum jiya i yau,dukka gyara da qyale qyalen daya zubawa falon daga bikin widad din tafiyarsu kaduna zuwa zuwansu yau gaba daya sun fara dakushewa,sai ka rantse kayan sunyi shekaru bakwai da sakasu,kai koda shekaru bakwai dinne indai ba qazamar mace ta ainihi ba bai kamata suyi wannan dafewar ba,ko ina tarkace ne dake nuni da cewa babu wadatacciyar sharar da falon yakeso,uwa uba turkish carpet dinta ruwan madara ya fara yin qaura daga aihinin kalarsa zuwa brown, qawataccen center table din daya zuba kudade ya siya mata an soma kwanceshi,ba wasu sassa a jikinsa.
“Ina Mommy din?” Widad ta tambayi mimi
“Tana kitchen,wanke wanke take”
“Muje ki rakani” ta kama hannun mimi din suka wuce kitchen din.
Bata a kitchen din,amma qofar backyard na kitchen din a bude yake,sai suka sanya kai can.
Turus widad tayi tana duban iyayen kwanukan dake yashe a wajen tamkar anyi taron biki ko siyasa an watse,kusan dukka wasu kwanuka na kitchen dinta suna wajen,tana tsakiyar su ta hada kumfa a babban baho tana wankewa,tanayi tana maganganun qasa qasa,daurin qirji ne a jikinta na zanin atamfa,sai rigar shirt,kanta dankwalin zanin ne data masa daurin gaban goshi,daga qasa kana iya hango qananun gashinta sun burtso.
“Mommy sannu da aiki” widad ta fada tana murmushi,hafsat ta waiwayo da sauri suka hada ido da widad din,a take taji ta muzanta,bata taba kawowa a yau idan hajiyan ta kirashi zai taho ba,dukka ta dauka sai gobe,don haka yau taci burin qarar da yininta tana gyaran kitchen,tasan shi da falo da toilet sune abu na farko da yaqi jinin ya gansu ba’a kintse ba,yau din kuma alhamis,ta zaci zai taho gobe juma’a ne.
Sake juya idanunta tayi akan fuskar widad karo na uku kafin ta samu sukunin amsa sannun tata data yi mata,idan idanunta ba gizo yayi mata ba yarinyar qara haske da kuma qiba tayi,ga wani dan banzan qamshin turare da taketa bulawa hancinta,wani abu mai qarfi ya taso ya kama zuciyarta, muryarta ta sarqe,har sai da hakan ya bayyana cikin sautinta,ta jefa mata tambayar muryarta a cushe
“Dake da waye?,da yammar nan?”
“Ni da daddynsu mimi” tayi maganar tana kallon qofar da zata sadaka da kitchen din,saboda tuni hancinta ya shaida mata wanzuwarsa a wajen,sassanyan qamshinsa daya fara yo gaba.
Idanun widad na kansa haka na hafsat,yayin da nasa idanun ke kan hafsat din da tarin kwanukan wanke wankenta,wanda ko ba’a gaya masa ba yasan halin nata tayi,wato tayi girki ta jiqa kwanon,gobe ta bare sabo ko wankakke ta sake wani girkin a ciki.
Tuni idanusa suka cika taf da bacin rai,banda wanda ya shaqa daga falo,da kuma dattin daya hanga akan sumar yaransa,ga qurajen zafi da suka fesowa nawwara,tabbacin ba’a kunna musu gen kamar yadda ya bar sallahy,bayan ya aje kudin komai da komai.
“Sannu da zuwa” ta fada tana miqewa hadi da sauke zaninta data yaye cinyoyinta
“Yauwa” ya fada yana komawa da baya,cikin sa’a ko rashin sa’a,sai ya taka sauran rubabben abincin data kwakwkwafe a kwandon shara,Allah yasa boots ne a qafarsa,yaja da baya ya murje qafar tasa ya fice daga wajen.
Cikin shan jinin jikinta ta soma takawa zata bishi,har tayi taku uku saita waiwayo tana duban widad,zuciyarta na cika da kishin kwalliya da sutturar jikinta
“Zauna ki kamamin wanke wanken nan ina zuwa”
“To” ta amsa mata,babu gardama,ta soma ratsawa ta cikin kwanukan tana tattare hannun rigarta,ta zauna kujerar data tashi,ta fara jan kwanukan tana wank su,mimi na mata hira.
Har ta doshi hanyar sassansa saita tsaya,ta kalli jikinta da kyau,ita kanta ta shaida tsami takeyi,sai tayi ribas,ta koma da baya zuwa bedroom dinta,ta kunna heater a gurguje ta saba sabulu ta dauraye da ruwa,ta tsaya gaban mudubin ta ta balbala turare sannan ta zura wata doguwar rigar baqar atamfa,ta dora daurin dankwalinta sannan ta fito.
Har zata wuce ta tuna tabar mimi a can,saita koma ta tsaya daga qofar kitchen din tana qwala mata kira,yarinyar ta taso,ta kama hannunta suka bar wajen,tana jefawa widad harara a fakaice
“Saikin gane Allah daya ne wallahi yarinya,muje zuwa wai mahaukaci yahau kura”.
A falo ta samu nawwara,tasha chocolate har ta godewa Allah,ta aje mimi a nan ta wuce kai tsaye bedroom dinsa.
Yana tsaye gaban mudubi yana maida maballin wata jallabiyya mai azabar kyau,hade take da wandonta da aka yima aikin zare daga qasa, lallausan qamshinsa daya karade dakin ta zuqa,tana son turarensa matuqa,saidai ko ya bata bata iya jurewa shafawa kullum da kullum
Sarai ya hangeta ta cikin madubi sanda take shigowa,amma bai fasa abinda yakeyi ba,hakanan bai waiwayo ba,jikinta ya qara sanyi,ta tako a hankali kanta a qasa,tayi mazauni a kujerar bayansa
“Sannu da zuwa ya hanya?” Ta sake fadi
“Lafiya” ya amsa mata a taqaice,ya dauki comb yana sake taje kansa,sannan ya daura agogo ya dauki daddumaersa a qagauce
“Zanje sallah na dawo,ki gyaramin sashe na” daga wanann ya juya ya fice a dakin,yana jin yadda shegen turarenta daya tsana yake cika dakin,baisan ita din wace irin mace bace,duk abind yake so tofa sunyi hannun riga,kamar ma tana jira yace ga abinda yakeso ta qalubalanceshi,duk wani abu da zaiyi mata don gyara da kyautata rayuwarta yayi amma ita kamar bata maraba da hakan.
Da kallo ta bishi,kafin ya gama ficewa,tabi qofar da harara tana jan tsaki
“Mutum sai shegen izza da tsari,daga dawowarsa gaba daya ya batamin duk wani lissafi ba,banda ya taho da waccar yarinyar yaushe na gama wanke wanken,na gyara nawa sashen,na gyara nasa?,sannan daga qarshe yacemin abinci yake jira na dafa masa kamar wata jaka,Allah yau saidai kowa yaci takeaway” ta fada tana sake jan tsaki,ta miqe tana kade zanin gadon da tun kafin ya tafi yake shinfide akai ba’a daga ba,kuma ko yanzun bata da niyyar dagawar.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)