Sponsored Links
Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa Novels

Arubuce Ta Ke 27

Sponsored Links

Page 27

Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi.

Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi.

Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba.

Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar.

Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la’asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din.

Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu.

Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba’asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba.

Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan

“Hajiya da alama anty hafsat fa……”

“Na sani muneera” hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai

“Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah” kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi’arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi’unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne

“Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba” amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace

“K’nnnn,ai shikenan” base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera ‘yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?.

Yayi tunanin zata kaishi qara wajen hajiya ko daya daga cikin yayunsa maza kamar yadda ta saba a duk sanda wani rikici data kasa jurewa ya hadasu,amma sai yaji shuru batayi ba,bazai iya tuna rana daya rak da ya kai qarar hafsat din ga danginta ba,duk da tarin matsaloli da laifukanta,shi wanann ba dabi’arsa bace kwata kwata.

Kwanaki biyar hafsat din tana a haka,cikon kwana na biyar din Allah ya jeho qanwar mamanta ita da naty ummee,matar data jima rabonta da gidan,yanzun ma.suna sukazo ta bayan layin,anty ummee ta roqeta su biyo.

Yana farfajiyar gidan shi kadai yana duba jarida,suka gaisa dashi suka wuce ciki,ba jimawa anty ummeee ta dawo

“Don Allah yallabai ka duba mana,hafsatun tana ciki kuwa?” Jaridar ya ajjiye ya miqe tsaye yana gyara shirt din jikinsa,yasan tana ciki,kawai taqi budewa ne tana zaton shine yake bugun,kuma a yau ya yanke zai balle qofar zuwa dare muddin bata bude ba,sai ya gewaye anty ummin yayin cikin gidan,ta bishi da kallo tana jaddada miskilancin sa,har yanzu yana nan dai ba abinda ya sauya.

“Ki bude qofar, ummee ce” ya gaya mata kai tsaye,bai qara minti guda ba sai ga motsinta,ta murza key dun data sawa dakin ta bude.

Wani irin scent ne mara dadi ke fitowa daga dakin,saboda qarancin iska me kyau,duk da akwai ac da fanka ta cikin dakin,amma baya zaton tana kunnasu,jikinta tun kayan daya dawo daga kaduna ya sameta dasu ne,da alama har wanka ta yiwa yajin aiki,ta nan inda yake tsaye yana iya jin sauyawar yanayin jikinta,sai ganshin kanta dake cuccure waje daya da alama bata tajeshi,fuskarta gaba daya ta kumbure,kamanninta sun dan jirkita.

Harara ta watsa masa sannan taja tsaki,tsakin da yakai har kunnen anty uwani dake falonta,tadan kama baki tanason tabbatar daga inda tsakin ya fito.

Ya tsani tsaki a duniya,ta kuma san hakan,shi yasa ta bishi dashi,ko zata samu ta fanshe bacin rai da quntata rayuwarta da yayi kaso daya cikin dubu na abinda takejin yayi mata.

Bacin ransa ya daure,ya juya yana barin wajen,saita biyo bayansa a hankali har ya fita a falon,ita kuma ta qaraso ciki,suna hada idanu ta zube a nan ta saki kuka,ciwon dake danqare a ranta ya motsa mata,don a kwanakin ita daya ke fama da baqincikinta cikin daki,kwata kwata basirar ta gayawa wani bata zo mata ba,hasalima wayar tana kashe tun ranar,saboda abbas din ta kashe,bataso yayi kiranta ma.

“subhanallahi meye haka hafsatu?” Anty uwani ta fada cikin firgici tana dago hafsat din,sai ta dan dauke kanta kadan saboda abinda ke tashi a jikin hafsat din,ta jata ta zaunar kan kujera sannan ta zauna dan nesa kasan da ita

“Lafiyarki kuwa?” Anty ummee itama ta jefa mata tambayar tana kallonta,cikin muryar kuka kamar wadda akace wa’adinta ya qarato ta soma magana

“Na shiga uku na lalace anty ummee,anty uwani wallahi mutuwa zanyi,abbas ne yace zai qara aure” ta qarasa fada tana rushewa da kuka,haushi da takaici ya qume anty uwani,yadda taga hafsat din ta aza hannu aka ta zauna dirshan a wajen tana musu irin wannan kukan na tashin hankali

“Mutuwa fa kike fada hafsatu,kinsan mutuwar kuwa?” Anty uwani ta fada tana harararta

“Sai an bita a hankali ai anty uwani…..sannu yi haquri tashi ki daina kukan” anty ummee ta fada yana dagota daga zamewar da tayi daga kan kujerar.

Da kallon takaici anty uwani ta bisu su duka,ta da jin labarin abinda hafsatun keyi a gidanta,qazanta baqar rowa,ga rashin iya mu’amala da mutane,kuma ko a yanzun ta sake shaida tabbatar qazantarta,saboda yadda jikinta yake tashi ba kowa ne zai juri xama kusa da ita ba,da alama kwana biyar din kenan batayi wanka ba.

Tana jinta sanda take rattabowa ummee labarin yadda komai yake wakana,tasani wanda suka fita ma sun gaya mata ba daukan shawara takeyi ba,ko a yanzun ma tasan idan tace zata gaya matan bata baki ne,don haka sai ta miqe

“Kin gama ko na wuce kya taho?” Dubanta anty ummee tayi

“Aah ki bari mu wuce tare mana”

“Um um,yi zamanki,nikam ina da uzuri,saikin taho,hafsatu sai a qara haquri,ki duba dukka iya kurekurenki da abubuwan da kikasan bayaso ki gyara tun yanzu,Allah ya bada haquri” badon tasan anty uwanin bata da wasa ba,bata kuma daukan wargi da ashar zata maka mata,amma hakanan ta hadiye bacin ranta tace mata ta gaida gida da shaqaqqiyar muryarta data ci uban kuka.

“Yanzu me kika yanke ke?” Anty ummee ta fada bayan ta dawo daga raka anty uwani,ragowar hawayen dake fuskarta ta share,tana jin gaba daya rayuwarta ta juya mata baya cikin kwanakin nan

“Babu wata shawara ko dabara da nake da ita,kawai dai abinda na sani,koda tsiya ko da bala’i wallahi bazan bar wata mace ta rabi abbas ba,bazan iya zura ido ina raye ba abbas ya auro wata mace da sunan matarsa ba” jinjina kai anty ummee tayi

“Amma ina ganin wanann ba dabara bace,kwata kwata ragon azanci ne,kinfi kowa sanin halin mijinki,idan yace yes babu wanda ya isa yasashi yace no,tunda ya niyyata babu wanda zai hanashi…..”

“Niko naci alwashin koda ta qarqashin qasa saina hana shi auren nan anty ummee” ta fada idanunta na sake kadawa suna kuma sake cika da hawaye.

Ajiyar zuciya anty ummeen ta sauke,sannan tadan gyara zamanta

“Niko sai nace wannan din ba hanya bace mai bullewa,face hanya mai wahala da kuma sanya kashe kudi,a matsayinki na mace,mai yasa ba zakiyi amfani da KISSARKI ba?” A hagunce hafsat din take kallon anty ummee,saboda bata fahimci me tafi nufi ba gaba daya,mafita kawai take nema,saboda haka tace

“Kamar yaya kenan anty ummee???”

**********Tun daga ranar bata sake kulle kanta ba,saidai kuma sabgarta takeyi kawai ba tare data shiga sha’aninsa ba,bai damu can can ba,don ko sanda suke shirin ma ba wani abu take dauke masa ko takeyi masa ba,kusan ya saba….fiye da rabin hidimominsa shikewa kansa,saidai ya dan samu nutsuwa,tunda aqalla bata sake tada wata fitina ba,har abun yaso ya bashi mamaki sosai.

********Karfe biyar na yamma tana kitchen tana hada abincin dare taji knocking,ta fito a kitchen din tana gyara daurin zaninta daketa kwancewa tun dazu,don bata daurin baya sai daurin gefe,a cewarta yana damunta ne.

Tana bude qofar sukayi arangama da yaron gidan wanda ke musu aike aike,sai ya danja baya kadan cikin jin nauyi saboda ganinta babu mayafi

“Madam oga ne yace a kawo,masu kayan gado ne da furnitures,zasu kwashe wadancan su saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin” ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din.

“Su bani minti goma ina zuwa” ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to.

Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci.

Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan.

Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito

“Su kuma wadan nan za’a kaisu?” Ta tambayi shazali yaran gidan

“Yace a fiddasu compound a ajjiyesu” kai ta kada

“Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin” kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin.

Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha’awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan.

Ba’a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯[2/22, 2:45 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button