Arubuce Ta Ke 13
Page 13
Kusan suke cin abincin,ita dai tana ta biye musu ne amma cokalin kawai take juyawa cikin plate din,tuntuni sun jima da raba plate din cin abinci dashi,tare dai suke ci,amma kowa kwanonsa daban,tunaninta gaba daya yafi karkata kan yadda zata sake jaddada masa ba zata bishi kaduna ba.
Har ya kammala cin abincin ta rasa kalmar kamawa,ganin yana qoqarin tashi sai tayi gyaran murya,ya dakata da shirin tashin da yakeyi ya aza mata hankalinsa
“Abban mimi,nifa gaskiya ba zan iya binka kadunan nan ba,don Allah ka janye tafiyar nan dani” ta fada tana jin nauyin maganar,a mamakance yake kallonta,tsahon wasu sakanni sannan yayi gyaran murya
“Nayi tunanin mun gama maganar nan dake ko?” Kai ta girgiza
“Bamu gama ba gaskiya,bazan iya tafiya wata kaduna ba” ransa ya sosu,ta yaya yana son kare mutuncinsa da martabarsa ya tafi da iyalinsa don samun kariya daga sharrin shaidan amma tanason ingizashi zuwa ga hallaka?,kadunan bariki zai tafi shi kadai alhalin da iyalinsa ba gauro bane?
“Koda bakiso hakanan zaki tafi,kuma bama kaduna ba,duk inda aiki ya jefani hafsat haka zaki bini muje,wannan shine tsarina” yana kaiwa nan ya miqe tsaye yana shirin sauka daga dining din,sai itama ta miqe,wai me yasa ya fiya kafiya da taurin kai ne?,haka kawai tana cikin garinta cikin dangi da ‘yan uwanta zai cizgeta ya tafi da ita wata uwa duniya?,itakam sam bata ga dalili ba
“Gaskiya babban mimi bazan iya barin dangina da kowa nawa da dan business dina dana fara ba na bika garin da bansan kowa ba,babu kowa nawa ba” ta fada adan hasale,kallonta yayi sai ya dauke kai ya gewayeta ya wuce,bashi da lokacin tsaiwa tanka mata ga yara zaune a wajen,sannan ma shi din ba mutum bane mai yawan son magana,banda Allah ya hadashi da ita mutum ne marason hayaniya,yafi qaunar zaman shuru da kadaici wani lokacin,shi yasa ko sabani suka samu bai fiya damunsa ba,yakan kebe yayi zamansa yana karance karance,idan kuma yara suna nan yayi sabgarsa dasu.
Binsa tayi har cikin falon tana maimaita maganar,yasan idan ya zauna ciwon kai zata sanya masa a banza,don haka sai ya dauki key din motarsa dake gefan tv stand ya fice abinsa kawai,yana amsa adawo lafiyan da mimi ke masa.
Komawa tayi ta zauna jabar saman kujera tana tuje daurin dankwalinta tayar gefe,wannan wanne irin maqalallen aiki ne da basu da aiki sai sassauyawa mutum gurin aiki?,daga can sai nan?,yaushe ma duka duka sauka dawo bauchin tana ta murna ta dawo gida?,to itakam wallahi ta gaji,tana son abbas matuqa tana tsakanin kishinsa,to amma aikinsa zai zama babban tarnaqi a rayuwarsu.
Tana nan zaune tana saqawa gami da kwancewa,mimi nata gaya mata nawwara na wasa da abinci amma hankalinta bai wajen,har sai da yarinyar ta fado da tea flasks dinsu ya fashe a wajen sannan ta farga,sai a sannan ta miqe tana banbamin fada ta nufi wajen,sai data durma mata dundu sau biyu a baya sannan tahau aikin gyara wajen,tanayi tana mita,yarinyar kuwa ta fashe da kuka,mimi ce ta matsa ta ruqo yar uwar tata tana goge mata fuska.
***********
Ranar da driver ya ajjiyesu gidan hajiya tayi mamakin ganinsu,ta danji fargabar ganinsu da uniform ba kayan gida ba,tana zaune a falonta tana lazumi bayan ta idar da sallar la’asar,da yake takan kwashi awa guda kafin ta kammala,ta amsa gaisuwarsu tana maida idanunta ga widad da take baquwar fuska a wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya
“Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga”
“To alhamdulillah” hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya.
“Bari muneera ta zuba muku abinci kuci”
“Zanyi alwala banyi sallah ba” widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba.
Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke ‘yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita.
Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin.
Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya.
Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida.
Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki.
Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida.
Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi
“Hajiya ai ke za’a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara”
“O’o,o’o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan” murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad
“Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida” dariya ta danyi,hajiya ta dubeta
“Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya”
“Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan” dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta
“Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora”
“Ameen hajiya,Allah ya qara girma”.
Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya.
*********
Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?.
Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan.
Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi’unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba.
A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa’ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din.
Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi.
Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami’in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru.
Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen.
“Assalamu alaikum…..lafiya me yake faruwa?” Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya
“Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu” idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace
“Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba”
“Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida”
“Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai” dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa
“Kayi haquri tunda shima ya baka haquri”
“Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka”
“Is okay,nawa ne kudin gyaran?” Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa.
Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace
“Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata”
“Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran”
“Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi” matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye
“Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut…..” A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga matashin
“Ina me shawartarka ka karba”
“Idan kuma naqi fa?” Wani qaramin murmushi na gefan baki abbas ya sake,hankali kwance ya maida kudinsa aljihu gami da fito da wayarsa a madadin kudin,ya danna kira.
Baice komai ba illa adreshin titin da suke kai daya bayar ya maida wayar aljihunsa,ya kuma harde hannuwansa yana kallon yadda yake ci gaba da zuba rashin mutunci,jikin dan sanda yana rawa ya matsa kusa dashi
“Bawan Allah kayi haquri ka tafi,zaifi maka alkhairi,tunda nasan zuwa yanzu ko kudin ma ka rasasu ba samunsu zakayi ba,gwara ka tsira da lafiyarka da mutuncinka”
“Dalla malami sakeni,wallahi yau sai naga wanda ya tsaya masa” ya fadi yana kumfar baki,maganar tasa ta sake hasala abbas,saidai bai nuna hakan ba koda a saman fuskarsa,yana ji ya zama wajibi ya bashi tarbiyya da bashi da ita,sai ya juya ga tsahon
“Kada ka sake bashi haquri baba” hannu ya saka a aljihunsa ya fidda dubu uku ya miqa masa
“Hau mashin dinka ka tafi,Allah ya tsare” zaburowa yayi yana fadin
“Idan ka barshi ya tafi rigimar nan ta koma kanka wallahi”
“Na karba”ya amsa masa yana sawa tsohon muqullin babur dinsa ya kunna masa,dai dai sanda motar ‘yan sanda ta iso,hakan ya baiwa tsohon hanyar wucewa,yana tafe yana jerantawa abbas din addu’o’in samun albarka da gamawa da duniya lafiya.
Matashin bai fahimci waye abbas din ba sai da jami’ai suka cika hannu dashi shi da dan sandan dake goya masa baya,sai a sannan ya nemi russunawa ya fara roqon ya saka a sakeshi,ko kallonsa baiyi ba ya dubi Samuel
“Ku sakayamin su a bayan kanta saina nemesu,mato ya tuqa motarsa a kaita station a ajjiye”
“Consider it done sir” ya fada yana saluting nashi.
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD’AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K’AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*YAN NIJER ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*ππΎππΎ
[2/13, 5:29 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)
*_Arewabooks:huguma_*